← Book details Sawun Giwa Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 5

Sashe 1

Sawun Giwa Part 4 Complete Hausa Novel · about 7 min read

🐘🐘🐘 *SAWUN GIWA*🐘🐘🐘

Book 2

Duk wanda yakaranta min book batareda yabiyani hakkinaba banyafeba🙏

Page 35 & 36

"Cikin mugun gudu Akabar gidan....Aisha ce tafito daga cikin parlor gidan manne da waya akunnenta tana magana da sahibin nata wato yah muhseen setaga motar maisoon ajiye cikin mamaki tace "affuwan my only bro ga sweetheat na tazo barana ganta tafaɗa tareda yanke wayar.... murmushi yah muhseen yayi kana yace "Allah yaƙara sakamin sonki my Isha daga Hakan yatashi zuwa sha'anin gabanshi.

Nufar motar Aisha tayi tana faɗar "sweetheat bazaki shigobane ashe harkin ƙaraso, ganin motar wangalam yasa tace au to ina taje kotashiga ne bansaniba tayi maganar tana dannawa maisoon ɗin kira, sedai me atsakanin kafafuwanta Raji ƙarar wayar maisoon ɗin, azabure tayi baya tana kallon ƙasanta aiko jakar maisoon ɗin ce da wayarta anan yashe ƙasa, ɗaukar kayan tayi tana waro ido waje cikin mugun mamaki tanufi cikin gidan tana kiran sunanta maisoon maisoon maisoon, da umma taci karo tafito daga bedroom ɗinta tace "ke lafiyarki kuwa? A,ina kikaga maisoon dakike mata wannan kiran? Bata shigoba? Aisha tajefawa umma tambayar batareda ta amsa tambayar ummar ba. Cikin mamaki umma tace "kamar ya bata shigoba bayanzu kike zaune a parlor ba kikemin wannan tambayar? Ido Aisha taƙara warowa tana maimaita innalillahi wa'innailaihiraji'un wlh maisoon tashigo gidannan umma ga motarta can awaje kuma kinga wayarta da jakarta ayashe nasamesu waje. "Da mugun mamaki umma tace "to ina taje kuma ta yada kayan? "Nima bansaniba umma Aisha tafaɗa cikin muryar kuka kana takwasa aguje zuwa wurin maigadi

Tana zuwa tace "baba iro ina gaka maisoon taje bayan tashigo gidannan? Maisoon kuma aiciki tashiga da motarta. Nasani baba iro to bayan tashigo waye yashigo? Bakowa gaskiya domin bayan na buɗe mata sena shiga banɗaki to bayan ma nafitone narufe get ɗin. "Innalillahi wa'innailaihiraji'un 😲 wlh wani abun yafaru da ƴar uwata nashiga ukku ni Aisha, taƙarasa zancen cikin kuka tareda rugawa aguje takoma cikin gidan, tofa tashin hankali kenan wanda ba'a saka mishi rana, domin kuwa tashin hankali kam umma da aisha sunshigeshi, cikin giɗima umma tashiga kiran Abba yayinda Aisha tashiga kiran yah fawan,

Shidai Abba umma nagama kaya mishi yashiga kiran ƴan uwanshi dudda cewar yanajin haushinta amma yakaɗu da ɓatanta.....shi ko yah fawan cikin mugun razana yamiƙe yana faɗar whatt? A ina Hakan tafaru kuma yoshe? "Cikin kuka Aisha tace anan gidan mana kuma yanzune wlh domin ga motarta nan da jakarta hardama wayarta. "Hum ina zuwa yanzu yafaɗa tareda yanke wayar yanufo gidan.

Cikin ƙanƙanin lokaci ɓatan maisoon yazaga ilahirin family ɗinsu faɗin tashin hankalin da wannan ahalin suke ciki ɓata lokacine, musamman mom tayi kuka harta gode Allah hakama dady da yah jawwal, agidan Abba ma dukkansu hankalinsu atashe yake domin fadeel ne dakanshi yacewa ummansu yanaga yah fawan ne yasace maisoon dubada abinda ke tsakaninsu gaya kuma acikin gidan aka sace ta, umma ma tana wannan tunanin sedai tace yayi shiru da bakinshi gudun kar abbansu yaji wata matsalar takunno kai.....yah fawan dakanshi yatasa maigadi gidan agaba akan seya faɗa mishi yadda akayi har aka sace maisoon cikin gidan....shikuwa yace besan ya abin yafaruba Hakan yasa ya ɗauke shi izuwa office ɗinsu domin yatuhumeshi.... gabaki ɗaya wannan ahalin sun birkice akan wannan tashin hankalin kuma duk wannan abin dake faruwa yaseer bayada labari domin baya samun wayar maisoon tunda Aisha takashe wayar. Kuma yazo gida mom tacemai tana gidan Zainab yayar Aisha Hakan yasa duk abinda akeyi besaniba.

Saudia

Matsalar Sheck Sudais tagirma domin yanzu abin harya kaishi ga fara jinya kullun cikin tunanin maisoon yake yarinyarda besan asalintaba balle inda ze same ta, gaya duk abinda akeyi sarki bilal besaniba domin memartaba sarki Hassan yahana agaya mishi, tofa abin yabirkice sosai, domin yau koda yarima basam yashiga bedroom ɗinshi yana duƙe yana aman jini, jin shigowar yarima basam yasa yayi sauri saka hankey ɗinshi yagoge jinin kana yashige bathroom ɗinshi, sedai beɗauke hankey ɗin ba. Shikuwa yarima basam gyara mishi ɗakin yashigayi haryazo gunda hankey ɗin yake cikin mugun tashin hankali yake kallon jinin dake kai kafin yaduba aƙasama gashinan, bece komaiba kuma be ɗauke hankey ɗin ba gudun kar yah Sheikh ɗin yagano yaganeshi, sauri yayi yagama kana yafice daga ɗakin domin yabashi damar shiryawa atsanake, yana fita turakar mahaifinshi yanufa sedai kuma kafin yakaiga shiga yajiyo sautin maganar antyn su gimbiya saudat, Hakan yasa yafasa shiga kawai yakoma pert ɗinsu kana ya shiga kiran memartaba sarki Muhammad bilal domin yasanar mishi halinda ɗansa keciki....cikin girmamawa yagaida sarki Muhammad bilal kana ya shiga yimai bayanin abinda kefaruwa tun dawowar Sheikh Sudais saudia. Haryanzu...Tunda yarima basam yafara magana memartaba ke maimaita "innalillahi wa'innailaihiraji'un kafin yasauke ajiyar zuciya yace "ka kula dashi sosai basam kakira doctor yadubashi zanshigo saudia gobe in sha Allah...to abbey in sha Allah zanyi yadda kace Allah yakawoka lafiya.

Nigeria

Abufa yarikice sosai, gaya bikinsu maisoon seƙara matsowa yakeyi yanzu saura kwana biyar ayi bikin yayinda har yau babu labarin inda amarya ɗaya take, itako ɗayar duk tabirkice kamar wata zararriya....yau dasafe abban fawan yazo gidan abbey yasameshi zaune shida jafar da muhseen. Cikin girmamawa suka gaidashi kana suka tashi domin subawa iyayen nasu wuri. Bayan sunɗagane Abba yadubi abbey kana yace "yaya Ishaq inagafa yadace agayawa iyayen wannan yaron dakeson maisoon zancen ɓatanta domin kuwa kaga lokaci na ƙurewa karyazama se ranar ɗaurin aure Susan babu amarya kaga za'asamu matsala gara tun wuri susani idan ma fasawa zasuyi to mundai gaya musu domin afita hakki. Yaƙarasa zancen yana kallon yayan nashi domin yaji ya ze ɓullowa lamarin....ajiyar zuciya Alhaji Ishaq yasauke bayan yagamajin bayanin ɗan uwan nashi kana yace "karka damu Umar in sha Allah komai zezezo dede maisoon zata dawo cikin amincin Allah domin kullum muna addu'a Bama Fatar ɓatan maisoon yafita waje sabida wani dalili wanda fitar ɓatanta kamar kwarewa ahalinmu bayane, koshi Usman nagaya mishi cewar kar wanda yafaɗawa mijin nata zancen ɓatanta kawai muyita addu'a domin kuwa itace maganin komai.

Tunda abbey yafaɗa magana Alhaji Umar yaƙanƙance ido yana kallonshi cikin rashin sanin ciwon kai yace "au kenan dai kunsan inda take yaya Ishaq tunda har bakwaso wani yasani awaje domin idan ba hakaba tayaya za'ace dan yarinya ta ɓata wai yazama kwarewar baya wa ahalinmu? Sedai idan tun farko akwai abinda anka ƙulla domin tun lokacinda ka hanawa fawan aurenta nasan cewar akwai abinda kuke ƙulli kaida Usman tunda bakwason ƴaƴana Hakan kuka watsawa yaronnan ƙasa a ido tunda bakune kuka haifeshiba yanzu kuma ga dama tasamu da ze iya mallakar maisoon domin idan iyayen wannan yaron sukasan cewar yarinyar da dansu ze aura ɓata tayi nasan bazasu bari ya aure taba kaga se amaidawa fawan abarshi dama can dashi tadace, amma dayake wani ƙullin kukayi shine kuke zancen wai a ɓoye zancen, to zanga wanda ya isa yahana auren maisoon da fawan idan Allah ya hukuntoda Hakan. Yafaɗa cikin ɗaga murya kamar meyi da sa'arshi.

Da mugun mamaki Alhaji Ishaq ke kallon ƙanen nashi wanda yake ganin kamar ƙwaƙwalwarshi tadena aikine kamin yace "Kanada hankali kuwa Umar ? Kasan mi kake faɗa kuwa? Humm lallai yau na yadda basirarka tatoshe sabida sonkai, tobara nafaɗama abinda bakasaniba kasani ayanzu, bawai dan wani dalili ne yasa nace aɓoye ɓatan maisoon ba sedan cewar agidanka ne aka saceta wanda duka yayanmu suna zargin cewar fawan ne yasaceta sabida ƙudurinshi akanta wanda na tabbata idan wannan maganar tafita tozalcine agaremu Ace ɗan mu yasace ƙanwarshi, shine abinda yasa aka ɓoye zancen, kuma duk abinda suke faɗa beyi tasiri agareniba domin kuwa bana aiki da zargi senaga zahirin abu tukkunna amma yanzu wannan zantukan dakayi anan sunsa na yadda da wannan zargin tobara kaji ingayama wlh wlh wlh Allah kaji rantsuwar Musulmi idan fawan naɗa hannu wurin sace yarinyar nan kagayamai yayi gaggawar fito da ita saɓanin Hakan kuwa duk hukuncin dana ɗauka akanshi Kaine kasiya mishi. Abbey nagama faɗar hakan yabar wurin cikin mugun ɓacin rai....wani irin gumine keyankowa Abba Tako ina seyanzu yake dana sanin yiwa Alhaji Ishaq wannan maganar gaya yaɗaure ɗanshi babu gaira balle dalili, to ina maisoon tashiga? Waye yasaceta? Yafaɗa afili yana ƙoƙarin barin parlor.....!

To muma dai munce ina maisoon tashiga ko awanne hali take ayanzu?🙄

Autar alheri ✍️

🐘🐘🐘 *SAWUN GIWA*🐘🐘🐘

Book 2

Duk wanda yakaranta min book batareda yabiyani hakkinaba banyafeba🙏

Page 37 & 38

"Tunda Abba yafita muhseen yadake zaune a bedroom ɗin shi yadafe kanshi yana maimaita duk addu'ar datazo bakinshi domin yasan wannan abin baƙaramin tashin hankali zekawoba acikin zuri'arsu kuma shi harga Allah baya zargin fawan duba da yadda shima hankalinshi yake atashe gaya duk wani mataki daya dace aɗauka yaɗauka kuma shine yataso tareda fawan yafi kowa sanin waye shi, dayanzu fyaɗe akace yayiwa maisoon to ze yadda sabida yadda ya ƙwallafa rai akanta amma baya tunanin ze iya saceta, da wannan tunanin dai yabar gidan domin samo mafita kafin abin yakoma tsakanin iyayensu.

Dubai
Chapter 1 · 0% Book details