← Book details Sawun Giwa Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 5

Sashe 4

Sawun Giwa Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ido yawaro ganin yafotoda maisoon cikin sauri yayi wurinsu har yana tuntuɓe bakinshi narawa yake faɗar "muhseen maisoon cefa a'inakaganta Hakan? Miyasameta? Duk atare yake jeramai tambayoyin...murmushi yayi kana yace maisoon ce Abbey bara mushiga daga ciki zanyima bayani,,,Abbey dai basamu damar cewa komai ba illa kallonda yakebinsu dashi,,,ahakan suka nufi cikin gidan abbey na biye dasu abaya har suka shiga. Mama naganinsu tataso dasauri tana salati, yah muhseen bebata damar cewa komaiba yace "mama ruwan zafi kitayata tayi wanka please agasa mata kafafuwanta sabida ɗaurin dasukasha, idan tagama setaci abinci..to kawai mama tace tanabin bayansu domin tuni yawuce da ita bedroom ɗin mamar. Suna shiga ya'ajiyeta bakin gadon kana yace "my lovely sis kiyi wanka kici abinci barana samo Miki magani idan nadawo semuyi magana ko? "Kai kawai taɗaga mishi tana share ƙwallar idonta domin koba'a faɗa mataba tasan ahalinta sunshiga tashin hankalin rashinta, dubada yanayin mama da abbey ayanzu to inaga mom ɗinta da dady kuma wani hali suke ciki kenan....shikam ficewa yayi inda mama tahaɗa mata ruwa tatemaka mata suka shiga bayin.

Shikuwa muhseen parlor yadawo inda yasamu Abbey zaune yayi tagumi yana tunani...zama yayi kusanshi kana yariƙo hannun mahaifin nashi cikin girmamawa yabashi labarin yadda akayi yasamo inda maisoon take harya ɗauko ta yanzu...ajiyar zuciya abbey yasauke yana sakawa muhseen albarka kana yace "to waye yasaceta muhseen? Nima bansaniba abbey mujira tahuta semuji daga bakinta..to shikenan Allah yayi muku albarka. Ameen ameen, daga Hakan muhseen yafice.

Baƙin saudia

Misalin ƙarfe 5 na yamma jirginsu asauka Nigeria acikin garin Abuja,,,inda shugaban ƙasar Nigeria dakanshi yazo tarbar manyan sarakuna masu daraja acikin ƙasar data kasance lamba ɗaya acikin jerin kasashe masu albarka dake cikin duniya, domin tun kafin sutaso hukumar jekadancin Nigeria dake Saudia tasanarda zuwansu....sosai sukayi farin cikin ganin tarbar da suka samu agun manyan Nigeria inda aka ɗauke su cikin mutocin alfarma izuwa bilah dake cikin unguwar asokoro,,,,sudai su Anty meenah kallo ne kawai nasu domin ba yadda basuso suwuce gidaba inyaso daga baya sudawo idan sarakunan sunhuta amma sam sarki Muhammad bilal yaƙi amincewa domin gani yakeyi kamar bazasu dawoba,,,,sosai akashiga karrama sarakunan abin birgewa shugaban ƙasar dakanshi yake gabatar musu da komai cikin mutuntawa da girmamawa. Seda suka huta akayi Isha'i tukkunna sukayiwa megirma shugaban ƙasar abinda yakawosu inda sukace kuma yanzu sukeso tafiya gidansu yarinyar domin ganawa da iyayenta...sosai megirma shugaban ƙasa yayi farin ciki dajin cewar babban malamin addini kuma ɗa ɗaya tilo agun sarkin Dubai keson auren ƴar ƙasar shi wannan abin alfaharine ga ƙasar Nigeria, Sedai ya lallaɓasu akan suyi haƙuri zuwa safe se ashirya tafiyar zefi..Hakan suka haƙura badan sunsoba.

Gidan abbey

Bayan maisoon tayi wanka taci abinci muhseen yakirata parlor abbey bayan duk sun zauna ne yace "ƙanwata yanzu daga office nake ƴan ta addan damuka samu suna gadin ƙofar gidan da aka ajiyeki mun tuhumesu akan waya sakasu dafarko sunƙi faɗa daga baya dasukasha wuya shine sukace wai Hajiya Rukky tasakasu, shine nakeson sanin wacece Hakan ? Kinsanta ne? Kuma mikika mata harta aikata miki hakan? Yatambaya idonshi na kanta...Tunda yafara magana kanta yake aƙasa har yakai ƙarshe kana ta buɗe baki cikin sweet voice ɗinta tace "nasanta my one bro maman yaseer ce Hajiya Rukayya dikko dillah....ido suka zaro atare daga Abbey har yah muhseen suna haɗa baki wurin faɗar maman yaseer dai....!

Autar alheri ✍️

🐘🐘🐘 *SAWUN GIWA*🐘🐘🐘

Book 3

Page 43 & 44

"Suna haɗa baki wurin faɗar maman yaseer dai? "Eh ita abbey itace tasaka aka saceni wai ɗanta yafi ƙarfin ya aureni shinefa bazata iya hanashiba tasaka asaceni, taƙarasa zancen idonta na cikowa da ƙwallah. "Innalillahi wa'innailaihiraji'un shine kawai abinda Abbey ke faɗa

Shikam muhseen mutuwar zaune yayi cikin mugun mamaki yace "to sabida me seta saceki? Idan tanaso afasa auren ai itace da yaron kuma yazo yayimin rashin kunya bayan ashe uwarsace babbar sheÉ—aniya aiko wlh seta gane kurenta daga ita har É—an nata.....cikin sauri abbey yace "a'a muhseen abarzancen bari kawai zan nemeka kutashi kuje kuma karku gayawa kowa wannan zancen kunjiko. Kallon juna sukayi kafin sukace "In sha Allah suka faÉ—a atare dudda kowannensu zuciyarshi tafasa takeyi nasan É—aukar mataki akan Hajiya Rukayya dikko amma abbey yahana, zasu zuba ido suga wanne mataki ze É—auka akai, da wannan tunanin kowanne su yabar wurin.

Washe gari dasafe Dr hareesh yakira Dadyn maisoon yana faɗa masa sun sauka suna Nigeria amma suna fadar shugaban ƙasa zasuzo yanzu tareda baƙi...da mamaki kwance akan fuskar Dady yace "baƙi kuma hareesh suwaye? Sarkin Saudia ne Dady...arazane Dady yamiƙe zaune daga kishin giɗen dayake yana faɗar sarkin Saudia dai lafiya kuwa? Yatambaya aɗan ruɗe

"wlh nima bansaniba dady sedai idan munzo maybe ku sugaya muku, cewar Dr Hareesh cikin alhini, domin har yanzu cikin fargaba yake akan zuwansu Nigeria...nisawa dady yayi kafin yace "to Allah yasa muji alkhairi amma kuwuce dasu gidan yaya Ishaq yanzu zankirashi in sha Allah seku samemu acan..."to dady badamuwa, daga hakan sukayi sallama.......abbey nazaune a parlor shi suna wayada dady inda yake shaida mishi zancen zuwan mutanen Saudia Sega megadinshi yashigo yana sanar dashi cewa yayi baƙo awaje...seda abbey yaƙarasa wayar tukkunna yace wayene? "Alhaji dikko ne abokinka. Okey ceyashigo,,,,daga hakan megadi yafice, bayan minti 3 dafitarshi Sega abba yaseer yashigo parlor fuskarshi babu yabo babu fallasa...miƙewa abbey yayi yatarbeshi kamar yadda suka saba aduk lokacinda suka haɗu batareda yanuna mishi komaiba,,,bayan sungaisane abban yaseer yashiga yiwa abbey magana kamar hakan. "Alhaji Ishaq wani zance naji akan yarinyar ku da yaseer ze aura, ashe yarinyar batama gida shine kuka rufemu baku sanar manaba? Yayi maganar fuska ahaɗe akuma dede wannan lokacin abban fawan yashigo parlor shima zuwanshi kenan yaji wannan abin da abban yaseer ke faɗa sekawai yasamu wuri yazauna bece komaiba....shi kuwa abbey murmushin takaici yayi kana yace "haba Alhaji sam bahaka abin yakeba dama ai inada niyyar nemanka koda kai baka nemeniba domin sam wannan zancen ba hakan yakeba...tun kafin abbey yakai ƙarshen zancenshi abban yaseer yakarɓe dacewa "kamarya zaka nemeni? Idan dagaske zaka nemeni aida kanemeni tun lokacinda abin yafaru bawai seda akazo gobe ɗaurin aure ba, kaga tun daganan kanunamin ɓatan nata bedamekuba tunda damacan tasaba abinta ta kunyi tunanin zata dawo a ɗaura auren kawai batareda bansaniba, segaya tayi abinda bakuyi tunaniba gaya kuma har labari yazo min wlh Allah kaban mamaki Alhaji Ishaq sam banyi tunanin zaka rufeni a aurawa yarona karuwaba koda kuwa take ƴar ƙanenka.

Cikin tsawa da ɗaga murya abbey yace ya isa hakan Alhaji dikko karka sake ka aibatamin yarinya wlh kab zuri'ata babu karuwa ba'ahaifetaba kuma baza'ataɓa haifartaba har abada, kasani ƴata saceta akayi kuma narufe zancenne sabida wani dalili nawa amma kasani cikin iyawar Allah da buwayarsa tadawo garemu sedai kuma zakayi matuƙar girgiza idan kaji wanda yasace tan dudda cewar Allah yaƙi bashi nasara akan mummunar ƙudirinshi, amma hakan behana yayanta san ɗaukar mataki akaiba ninenan nahanashi, sabida mutunci da zumunci amma inaga kai bakasan ko ɗaya ba barana tabbatarma dacewar ƴata tana hannuna. Yanakaiwa nan azancenshi yabuɗe baki daƙarfi yace "maisoon. "Na'am abbey, ita kuwa ta amsa tana daga bedroom ɗin mama....wani rass rass gaban abba yayi domin tunda yaji abbey yace wanda yasace maisoon gabanshi ke faɗuwa domin atunanin shi fawan abbey zece kuma gaya ba'agantaba, amma yanzu da yaji abbey yakirata sehankalinshi yatashi...shima dai abban yaseer jikinshi yaɗanyi sanyi amma benunaba ko afuska...ahakan tashigo parlor sanyeda dogon hijab ɗinta harƙasa taduƙa tana gaidasu kafin tace gani abbey...bece mata komaiba illa kallon abban yaseer dayayi yace "kaganta da idonka? Sekuma yamiƙe tsaye tareda takowa haryazo gabanshi yadda zasu iyajin nunfashin juna kana yace "kuma matarka Hajiya Rukayya mahaifiyar ɗan naka itace tasaka Aka saceta komiye dalili? Abbey yayi maganar cikin tuhuma..

Wani irin waro ido Alhaji dikko yayi tareda zabura lokaci ɗaya kaɗan yafaɗi, irin yayi mugun kaɗuwa ɗinnan kana yabuɗe baki zeyi magana amma taƙi fitowa,,,ganin hakan yasa abbey yin guntun murmushi kana yace "mutuncinka da darajar abotarmu yasa nahanawa muhseen da ita kanta yarinyar ɗaukar wani mataki, amma yanzu zan janye hanasun danayi nabaka nanda kwana ukku inaso katambayarmin matarka dalilinta nasacemin ƴa takaiwa ƙartin banza suna gadinta kuma idan baka dawomin da amsar tambayata acikin kwana ukku ba to tabbas zansaka yayunta sutambayeta wato fawan dakuma muhseen inadaida tabbacin cewar kasan jami'an tsaro ne? Sekuma zance na ƙarshe nasoke auren maisoon da ɗanka yaseer wanda za'ayi agobe domin bazankai ƴata cikin ahallin da basusan mutunci ba.Yaƙarasa zancen yana ɗagawa Alhaji dikko gira ɗaya....acikin kaɗuwa da dabircewa Alhaji dikko yabuɗe baki daƙyar yace "dan girman Allah Alhaji Ishaq tsaya kaji wlh duk bansan wannan abin hakan yake ba kuma koda bakaceba doline zan tuhume Rukayya akan wannan al'amarin amma dan Allah kajanye kallimar soke aure wannan sam badede...kafin abbey yace wani abun cikin sauri abba da tunɗazu yayi mutuwar zaune ganin maisoon yakarɓe zancen da cewa "ai wlh baka isaba Alhaji dikko kazo hargida kacimana mutunci kana kacewai ayi haƙuri zancen aure kam babushi kaji zance ɗaya kuma katashi katattara kabar gidannan kafin yanzu nasaka yarana susa ayimin waje dake, yaƙarasa zancen yana tasa ƙeyar Alhaji dikko agaba sam yaƙi bashi damar yin magana domin sosai Alhaji dikko yaso bawa abbey haƙuri akan zancen janye auren dudda cewar shima ya hau sosai...seda yarakashi har motarshi driver shi yaja sukabar gidan kana shima yashiga tashi mota cikin farin ciki yanufi gida domin yayiwa fawan albishir ɗin fasa auren maisoon da akayi. Humm abba kenan 😥 wato dakasan abinda tafiyarka zehaifar batareda kakoma ganawa da abbey akan zancen maisoon da fawanba tabbas dabazaka tafiba.

Bayan fitarsu abba yazauna yana mamakin mutanen yanzu da sam basuda kunya balle kawaici, wai shi damatarshi tasa aka sacewa yarinya beyi maganaba ko ɗaukar wani mataki, seshi zezo mishi dazancen renin hankali, to hauka yakeyi daze yadda ya aurawa ɗanta ƴarshi ? idan dai ba gawarta yakeso akawo musuba...yana cikin wannan tunanin dady ya iso gidan yasameshi shi kaɗai a parlor domin maisoon tunda suka fara taƙaddama tabar wurin...shigowar dady da minti 3 jiniya tafara karaɗe gidan inda manyan motocin megirma shugaban ƙasar Nigeria suka sawo kai harabar gidan bayan megadi yawangale musu get... abbey nacikin bawa dady labarin yadda sukayi da abban yaseer yanzu sukaji wannan jiniyar hakan yasa suka Miƙe dukkansu sukayo harabar gidan...!

Autar alheri ✍️

🐘🐘🐘 *SAWUN GIWA*🐘🐘🐘

Book 3

Page 45 & 46
Chapter 4 · 0% Book details