← Book details sawun giwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 6

Sashe 5

sawun giwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin zumuɗi suka fito itada A'isha suka nufi cikin gidan da hanzarin su...da kallo muhseen yabisu har suka ɓacewa ganinshi kana yasauke ajiyar zuciya. "Miyafaru ne ƙanana? Kodai acikin waƴannan yammatan ne kafaɗa irin wannan kallo hakan? Gayamin wacece acikinsu? Yafaɗa yana sakin murmushi. Lumshe kyawawan idanuwanshi yayi kana yace "maisoon yaya ina mugun son yarinyar nan Allah yasa ta amince dani, yafaɗa cikin rauni. "Wow Masha allah gaskiya kuwa idan kasameta kayi dacen mata bro Allah yasa ta karɓe ka amma kayi gaggawar fito mata da asalin buƙatar ka domin kuwa inba hakanba wani ze iya riganka..dam ƙirjin muhseen yabuga cikin fargaba yace "in sha Allah yaya zan yi ƙoƙarin hakan. To Allah yasa mudace,. Ameen y Allah, yafaɗa kana suka nufi cikin gidan.

Sukuwa yammanta suna shiga suka samu mom zaune a perlor, wani mugun ihu maisoon tabuga tanayi kan mahaifiyar Tata cikin cikin farin ciki da ɗauki ganinta. "Oyoyo my lovely I miss you so very much wlh, tafaɗa alokacinda ta maƙalƙaleta tana manna mata kiss a fuska. Cikin farin ciki mom tace "ikon Allah maisoon karyani zakiyi wannan murza hakan? Ashe dai kunma iso yanzu nake waya da Ameenah tace ai tunɗazu kuntaso keda muhseen yana inane? "Ta tambayeya tana waigen bayanta, Murmushi A'isha tayi cikin sanyin halinta tace "mom yah muhseen yana waje zeshigo yanzu, inawuni. ",Eyee Uwar Muminai kice tare kuke aibangankiba wannan sarkin figar hankalin duk ta maƙalƙaleni, to y kk y hajiyarki? "Tana lpy qalau mom. Masha Allah maza kuje ciki to kuyi wanka kuhuta sekuzo kuci abinci. "To mom suka faɗa atare suna barin perlor akuma wannan lokacin muhseen da yah Jafar suka shigo. Cikin girmamawa suka gaisa da mom. Aiko taji daɗi sosai domin yaran nasu suna da kirki kuma tanajin daɗin yadda suke nuna kulawarsa ga autar Tata. "Mom ga little sis nan naɗaukewa meenah please dan Allah tadena irin wannan tafiyar menisa ita kaɗai koba komai a gaya mana inbazamu iya zuwaba samu saka arakata sabida awannan zamanin mutun baya sakeda abinda yake dashi please. "Kaji ƙanen sojoji aidoli kam kace hakan, cewar yah Jafar. Murmushi mom tayi cikin sakin fuska tace "in sha Allah kuwa muhseen idan ma tace zataje to takiraku ta tagaya muku tukkunna, tafaɗa tana Murmushi. "Yawwa my sweet mom hakan yasace Bara muƙarasa gida yanzu. "To shikenan agaida min Hajiya, Jafar agaidamin ƴata..in sha Allah zataji mom, daga haka sukabar gidan.

Su maisoon kuwa seda sukayi wanka suka huta tukkunna sukaci abinci daganan suka shiga firar yoshe gamo A'isha nabata labarin yadda bikin ƙasarsu maimoun zekasance, haka suka wuni aranar har Dady yadawo yasamesu, sosai yayi farin ciki jin cewar muhseen ne yaje har Saudiya yazo da,ita...aiko tazuba taɓara sun ranta agaban Dady domin maisoon ƴar lelece agun iyayen nata. Sedare liss tukkunna yah jawwal yamayarda A'isha gida.

Washe gari dasafe tana kwance akan makeken bed ɗinta tana bacci, wayarta tadameta da ruri, cikin maganin bacci taɗauki yawar batareda tadubaba taɗora akunne. Tana faɗar "hello. "Hi beautiful lady y kk? Taji saukar muryar da take tunanin tasani. Ai babu shiri tamiƙe zaune tana wartsakewa tare da cire wayar akunnenta tana duba nomber, nomber Nigeria ce sedai batasan kota wayeba, kafin Takoma yin magana akace "hello beauty kinajina? "Waye ne? Yatambaya atsaitsaye. "Humm bakiganebako? Nasan dama bazaki ganeba.."luck kagayamin kowaye banason shirme kona kashe wayana, tafaɗa cikin ɗan hasala. "Uhm I'm very sorry please yaseer ne wanda kuka haɗu a saudia. "Niban haɗu dakowa ba a saudia idan zakayi bayanin kokai waye kayi idan bazakayi ba shikenan tafaɗa tana ƙoƙarin yanke wayar..."Karki kashe please sunana yaseer wanda kika temaki kakarshi a saudia acikin masallacin harami itace tace kibani contact ɗinki domin idan kindawo Nigeria kizo gidanta, to shine yanzu tace nakiraki naji idan kindawo kuma yoshe zakizo? "Humm aisakeyimin bayanin cewar Hajiya ce tace kakirani tun farko, shikenan kace mata nadawo kuma in sha Allah zanzo cikin kwana kinnan ina gaidata please, tafaɗa cikin alamun gajiya da zancen.."okay in sha Allah zataji please kiyi save contact na mana ƙanwata Kinga Hajiya bazata dena sakani kirankiba nikuwa bazanso duk nakira kicemun wayeba. "Okay I'll do it in sha Allah daga hakan batajira cewarshiba tayanke wayar...daga gefen yaseer kuwa murmushi yayi yana faɗar "agaskiya Muryar yarinyar nan kaɗai abin so ce balle Gara kyakkyawa, uhmm Allah ya karkato min dake my beautiful lady. Yafaɗa yana manna wayar a ƙirjishi..

Saudia

Kwana biyu dayin rigimar Basam da kursum Sheikh sudais yashirya komawa Dubai, ba yadda Sarki Hassan beyiba akan yazauna yace aiba zama zeyi acanba sedai ze ɗan jima domin akwai abinda zekaishi sa'annan tare da Basam zeje..ba yadda Sarki ya iya doli yabarshi yatafi..sam wannan tafiyar batayiwa kursum da mahaifiyarta daɗi ba domin su ƙullah wani ma kirci dasukeso ai watarwa akan Sheikh sudais ɗin wanda zesaka doli ya amince da auren kursum kobaya so sadai sun makaro yau kam Sheikh sudais yaɗaga zuwa ƙasarshi ta haihuwa sedai sujira dawowarshi...agefen gimbiya zaitun kuwa baƙaramin daɗi tajiba domin koba komai Basam zetsira daga tarkonsu domin muddin Sheikh sudais yabar gidan to sesun ƙullah mishi wani makircin.

Nigeria

Yau rana ta ukku kuma yau ne jirgin daya ɗauko fawan yasauka agarin Abuja. Anan airport yasamu zugar sojojin shi da ƙanen shi fadeel suna jiran isowarshi, rungume juna sukayi shida fadeel cikin farin ciki da ɗaukin juna domin dai wannan ahalin kam akwai son ƴan uwa sam basason wani abun yasamu ƴan uwansu musamman najini... sojojin shi kuwa sara mishi sukeyi cikin girmamawa haryashiga mota, kana suka ɗauki hanyar gidansu, cikin azababben gudu kamar yadda suka saba....suna isa gida sukayi Perking yafito cikin sassarfa yaƙara cikin gidan fadeel na biye dashi abaya..azaune suka samu mama da Abba a perlor suna fira se A'isha dake kwance kamar me Bacci amma kuma azahiri ba bacci takeyiba. "Oyoyo my son soja mazan fama y to yagajiyar tafiya? Cewar Abba tunkamin fawan ya gaidashi. Ƙarasawa yayi yana mannawa mahaifin nashi kiss agoshi kana yace "lpy qalau alhmdllh abbana ya gidan ? "Lpy qalau son. Good, mama barkada rana. "Yawwa barka fawan andawo lafiya? Tafaɗa tana Murmushi domin Hajiya Bintu akwai sanyin hali da Dattako. "Lpy qalau mama. Ɗan shiru babiyo baya can Abba yace "son miyake damunka ne naga duk kazama wani iri? Please gayamin idan akwai matsala? Ajiyar zuciya yasauke kana yace "akwai damuwa Abba, "last time abbey yayimun zancen aure kuma wlh lokacinda yabamu yakusa nikuwa gaskiya ƙanwata Nakeso bansaniba ko zaku bani, yafaɗa ashagwaɓe. "Tofa Masha Allah ai wannan abun farin cikine mizesa muhanaka kuwa wannan wacece? "Maisoon ɗin Dady, yafaɗa kanshi tsaye domin yayi alwashin seyayiwa muhseen baƙin ciki.. "kai Masha Allah amma gaskiya wannan zancen yayimun daɗi yanzu sabida kanason maisoon shine kake wani cin magani kana ɓata rai? Humm to shakuruminka Indai maisoon ce tazama taka anjima in sha Allah zansamu yaya Ishaq dazancen ayi komai aƙare..yawwa my sweet Abba haka nakesonji wlh, fawan yafaɗa yana rungume abban nashi...wani irin faɗuwa gaban A'isha yayi domin jitayi kamar itace za'ayiwa wanan kutsen yah fawan da sweetheart ɗin kuma batareda saninta ba inaa sam bazata bari hakan takasanceba, tanacan duniyar tunanin taji muryar mama tana faɗar....!

SAWUN GIWA paid book ne akan nera 1k kacal 👌 free page yakusa ƙarewa kuhanzarta biyan naku domin kusamu damar karanta shi har karshe domin bazan lamunci akaranta min wani abuna batareda anbiyani hakkinaba, please akiyaye🙏 idan kinshirya biya saki iya tura kuɗinki a wannan account ɗin 👉 2276776261 sha'awanatu ƙasim UBA Bank kana kitura shaidar biyanki awannan nomber 👉 07037092176. 🙏

Autar alheri ✍️
🐘🐘🐘 *SAWUN GIWA*🐘🐘🐘

🐘
🐘🐘
🐘🐘🐘
🐘🐘🐘🐘
🐘🐘🐘🐘🐘

Romantic love story 💋💓💞

Daga alkalamin✍️👇

Dr Yasmeen Ahmad

(Autar alheri ✍️)

Marubuciyar 👇

SIRRI

SOLDIER'S FAMILY

INGARMAM NAMUJI

MEJO NAJEEB

WAYE MIJINA

TANTIRANCI SABON SALO

IZZAR MULKI

BIG LADY'S

MY LITTLE SISTER

JEJI GIRL

JIKAR IYA DELU

SHUGER DADY

And NOW 👇

SAWUN GIWA LABARIN GIRMA AKAN GIRMA SOYAYYA MULKI ISA FINƘARFI RIKICI BAN MAMAKI DADAI SAURANSU DUK ACIKIN BOOK ƊIN *SAWUN GIWA*

Free

Book 1

Page 21 & 22

Last free page 🙏

Duk wadda ke buƙatar karatun SAWUN GIWA har complete tayi hanzarin biyan nata kuɗin domin samun damar karatu cikin aminci, ban yadda kowa yakaranta min abuna batareda yabiyani hakkinaba dan Allah akiyaye🙏

*Masu yimun document ɗin book bansaka kowaba kuma wlh duk wanda yayi banyafeba idan kuma nakama mutun dayimun hakan wlh ko aina yake senayi shari'a dashi domin besan wahalar danayiba kafin nayi abuna* 😥

"Tana faɗar "ko kusa Alhaji wannan ba Dede bane kafara tambayarshi shin maisoon ɗin tasanda zancen shi kuwa? Idan tasani shikenan babu damuwa amma idan batasaniba to kaje kafara neman soyayyarta tukkunna daga baya se ayi zancen aure dukkanmu zamuyi farin ciki da hakan, kuma kaida nahaifa umurnine ba shawaraba tabbas idan maisoon bata amince dakaiba to kaje kafara neman yaddar ta tukkunna. Tanakainan azancenta tamiƙe domin tasan yanzu Abba zega laifinta kuma tayi hakanne dan tasan tabbas maganar taje gun Abbey ko maisoon bataso se anyi acutarda ƴar mutane sabida son zuciya...ajiyar zuciya A'isha tasauke domin baƙaramin daɗi maganar mama tayi mataba.....shikuwa fawan wani mugun takaici yaji domin yasan zesha wahala kafin maisoon ta amince dashi dubada rashin tsoron yarinyar dakuma tsiwarta gaya besan abinda muhseen yakitsa mataba. Ajiyar zuciya Abba yasauke ganin yadda yaron nashi yayi kici kicin da fuska yace "kabarta my son kayi haƙuri ai bawani abin damuwa bane nasan ƙanwarka bazata ƙikaba domin Kanada duk wata nagarta daya dace ace namiji nada ita doline kowacce mace tayi alfaharin samunka amatsayin mijinta, sabida hakan kaje kawai kanemi soyayyar Tata kamar wadda mahaifiyarka tabaka umurni, nikuwa daga ranarda ta amsa aranar zan cimma yaya Ishaq asaka muku ranar aure, yaƙarasa zancen yana dafa shoulder ɗin shi sabida ya ƙarfafa mishi guywa. Ɗan shiru yabiyo baya nadan lokaci kana fawan ɗin yace "shikenan Abba in sha Allah zan yi hakan acikin satinnan zandawoma dazancen soyayyar maisoon. "Yawwa jarimin namiji ai nasan zaka iya domin soja da jarumta akasanshi, tashi kaje Allah yayima albarka.."Ameen Ameen Abba daga hakan yamiƙe yanufi bedroom ɗinshi.
Chapter 5 · 0% Book details