← Book details Sanadin Party Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 8

Sashe 8

Sanadin Party Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Haushin ubansu yashafesu cikin masifa tadaka masu tsawa tace"zaku d'agani kosaina wullardaku k'asa? Bakuda hanakaline zaku fad'amun jiki ko jimin ciwo zakuyi? Kud'agani nace,"!!! Ta Ida Maganar Cikin tsawa

Kuka yaran sukafashe dashi suna nufar Daddynsu

Zubamata ido kawai Yayi yamakasa magana danbaimasan silar Wannan fushin nataba kama yaran yayi yalallashesu yafita dasu Sosai yamusu siyayya Nishad'i kawai suke sunmanta har bacci yakwashesu sannan sukadawo gida, zuwa wannnan lokacin tacika tayi famm ganin yafita ko lallashinta baiyiba Kuma hardare tana Zaune palourn Suka shigo ko kallonsu batayiba balantana ta ansa sallamarda yake, kaisu d'aki yakaisu yakwantardasu yamusu Addu'a Saida yayi wanka sannna Yadawo d'akin nata bataciki palourn yakoma indayabarta tananan Bata tashiba,

Zamayayi kusa da ita yayi yace"waimeke faruwane meke damunki tinda mukadawo Asibiti duk kinwani firgice harkina saka yaranki kuka,"

Harara tabankamasa tace"Ai dole kazomun dad'in baki bayan kagama cutar dani yarinya k'arama dani tashin farko nahaifo yara har biyu Kuma Yanzu ace gawani ciki shibansan mezan haifaba yaranma ko shkea basucikaba dan kawai sunada jiki maikyau ne yasa sukayi saurin girman kuma Ace wani ciki yabayyana gareni Wallahi saidai Azubar dashi,"

"Azubar? Azubarfa kikace Anisa kinacikin Hankalinki kuwa,? Cikin nawa Za'a zubar da ubansa dakomai,"?

"Eh shifa dole Azubar Dan Wallahi Bazan iyaba bazaiyu banmagama wahala da wad'annanba Asake had'ani dawata wahalar kodan bakai ke renonsuba bakai ke wahalar Haihuwarba iyakacinka kayi Cikin kabarni da wahala rurrutsafa kenan Dan Allah kataimaka muje acire wallahi bazan iyaba," kuka tafashe dashi tana Rok'onsa

Tausayi tabashi amma bayajin zai'iya barin cikin Yafita Gaskiya domin yanason Abunsa," lallashinta yafara"kiyi hak'uri Kinga bakisan mesaki haifaba cikinsu bakisan waye zaizama maiceto garekiba Kuma Yara Rahamane wasu nacan sunanema Amma Allah baibasuba kingamu yabamu to godiya zamu Masakada mubutulce,"

"Kaga Ammar Wallahi yanzu bawani dad'in Baki dazakamun Kacutar dani ko kaso ko Karkaso Kota halin k'ak'a wallahi saina zubda cikin, wallahi bazan Barshiba saina zubar da.......,"

Tassss yawanketa damari harsau biyu saidata durk'ushe k'asa Cikin zafinjin kalamanta yace"kije kizubard'in dan Allah kadakifasa dankega Ina Lallab'aki? Tokije kizubar wallahi duk Abunda Yasami Yaron Cikin naki na rantse saina Sab'amiki fiyeda Yarda Baki tunani zand'au mummunan mataki kanki banza Mara Kunya da Addini kawai shasha,"Mtssswww yaja tsaki tareda barin wurin Cikin fushi

K'arafashewa dakuka tayi tana masifa itak'ad'ai Wallahi saita zubar,..

Haka Ranar gidan akakwana kowa dak'uncinsa Arai, shiya kwanta dayaran dasafema yunwa tasata Neman Abinci iyacikinta kawai tadafa tadawo tazauna tad'aura k'afa d'aya kan d'aya jira take yafito yatankata susakeyin rigima,

Shiyamusu wanka Yashiryasu dakansu kuka suketa masa duksun rud'ashi su Mommy sukeso tabasu Abinci duk Yarda yayi k'inshuru sukayi dole yafito dasu lokacin tana saka mayafinta tad'auko jaka

Yaransuka ruga indatake juyowatayi tabankamusu Harara dole Suka tsaya domin suna matik'ar tsoronta "duk Wanda yasake yamatso inda nake saina karyashi,"

Mommy"inzuwa"

"Kujedai da Ubanku niba inda zanjeda d'ankowa kuma duk Wanda yasake mun magana cikinku saina karyashi,"tana K'arasa maganar tanufe Hanyar fita yaran kuwa sukasake sakakuka Sosai

"Wai inazakine,"

"Inanacema zanje tinjiya? Wallahi saina zubda cikin canzani Kuma bawanda ya Isa yahanani ehe," Tak'arasa maganar tana murgud'a baki

"Anisa ya kikeso nayi kinga saboda wannnan rashin kunyar dajin maganarki yasa Kika fad'a sharrin jinni shinbazaisa kisamu darasiba, haba Anisa hakanfa dakike zaisa kihad'u dafushin Allah,"

"Aishine matakinku kucutarda Macceba datayi niyar kwatar Y'anci kuce taji tsoron Allah, cikin Rashin tausayi kasa Hannu jiya kadakeni Marinafa kayi wannan daidaine Kenan,"?

"Naji nayi kuskure anan kuma wallahi b'acin raine yasani Kinsan dukan Macce bayacikin halina kinfi kowa sani Amma kiyi hak'uri dan Allah," cikin Muryar tausayi yayi maganar

"Nifa cikine dai nacesaina zubar bawanda ya........," tassss tassss tassss saukar marukanda taji yasa tahad'e ragowar maganar juyowa tayi taga Umma d'aga Abba kuwa wayardake Aje gefen kujera ya d'auka yanufota da ita, ganin hakan yasa tasa kuka takoma bayan ammar dagudu tarik'eshi da b'oyewa bayansa tana kuka tana Fad'in"Dan Allah Abba kayi hak'uri bazan sakeba ya Ammar kace yayi hak'uri Kada yadakeni wallahi nafasa na hak'ura bazan zubarba,"

"Ah K'arya kike aikince bawanda ya isa yahanaki zubarwa tozokije ki zubar yausainayi maganin rashin kunyar taki,"

"Wallahi Abba nadaina nafasa Dan Allah kada kadakeni,"

"Kaga Ammar mik'omin itanan nace"

"Ah Abba tinda tagano laifinta kayi hak'uri kuyi hak'uri Umma yawuce,"

"Kaganiba Kaine kagama sagarta Yarinyarnan kabari Ahukuntata kawai,"Cewar Umman

"A'a Umma Ayi hak'uri Dai dan Allah"

"Shikenan kinci Albarkacinsa amma Wallahi Anisa kinji na rantse muddin Kika zubda cikin to banyafe mikiba saidai kinemi wata Uwar,"

"Nima haka Saidai kinemi wani Uban Kuma Kika yarda Kika rabu da Ammar Saidai kinemi wasu uwayen banza shashasha Mara munya,"
Wucewa sukayi itakuma tazube k'asa tanakuka sosai, Zama yayi yasoma lallashinta dakyar Yasamu ta hak'ura Saidai Kanta Yasoma ciwo sannan tayi shuru,

Had'esu yayi jikinsa itada Yaran sukayi baccin mata da miji sai Allah shirya kansu sukayi bayan Kwana 2 kuwa komai yawuce, harda zuwa gida taresukayi tabawa iyayenta hak'uri

Rahila tahaihu yaronta Namiji ansha biki sosai indacikin Anisa yayi girma,.

BAYAN SHEKARA D'AYA

Hangosu nayi Dukansu Zaune saifira suke suna Dariya suda yaran nasu Ayanzu Yaran Anisa 4 Rahila kuwa 2 zaman Lafiya da k'aunar juna suke,

"Mommy Inason nayi birthday party na abakin ruwa Zamuje muda Y'an school d'inmu" Cewar Aziza k'aramar Y'arta

Azaburetayo kanta zatadaketa Saida Rahila tahanata masifa tafara"idan Nasakejin bakinki da kalmar Zaki birthday party wallahi halakaki zanyi"

"Mommy Kiyi hak'uri bazan sakeba"

"Kima sake banza shashasha Kawai kutashi kubani guru"duk suka Mik'e suna bata hak'uri sukayi sama

Ammar dake lab'e bakin k'ofa Yashigo yanata dariya harda rik'e ciki, itama Rahila dariya tasa

"Au maidani mahaukaciya zakuyi,"?

"Ah maida wuk'ar kawai Yanayin tsoronki yaban dariya Lallesu Anisa antuba,"Cewar Ammar

"Yoba doleba Wannnan bala'in damuka shiga aidole mudawo hanya"

"Lalle kuwa *SANADIN PARTY* Yasa wasu dawowa hanya"

Aikuwa suka sake tuntsirewa da dariya Dukansu wannnan karon Harda ita.....................

ALHAMDULILLAH ANAN NAKAWO K'ARSHEN LABARIN NAWA MAITAKEN *SANADIN PARTY HORRO STORY ☠️☠️👹* ALLAH KABAMU IKON D'AUKAR DARASI MAIKYAU DAKE CIKI MARA KYAU KUWA ALLAH YAKAREMU.......

_BASEERATA ITACE ARZIKINA😍_

WhatsApp number 07064904617
Chapter 8 · 0% Book details