← Book details Sanadin Party Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 8

Sashe 2

Sanadin Party Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aikuwa dagudu Safa ta isa wurin akasake wata banzar wak'a suka shiga Suka Soma rawa da rungume rungumen juna, wasunsu ma harda kisses kumafa saurayi da budurwa,

("WA'IYAZUBILLAH, WANE IRIN BALA'I NE ACE SAURAYINKI ZAIYI KISSING D'INKI KIBARSHI? KODA BAN FAD'ABA KEMA KINSAN HAKAN HARAMUN NE BAIZO CIKIN ADDINIBA ANCE MACCE TA KAME KANTA AMMA SABODA LALACEWAR ZAMANI DAGANIN WAYEWA TA BANZA ANDAINA AMFANI DA FAD'AR ALLAH DA MANZONSA SABODA ME ZAMUGA DAIDAI? WLLH TINDA MUKA KAUCE FAD'AR ALLAH DA MANZONSA TO BAZAMU SAKE GANIN DAIDAI BA, MATA MAZA MUJI TSORON ALLAH, MUTUWA ZUWA TAKE BATA NEMAN IZINI KO SANARWA ZUWA KAWAI TAKE DATAZO DOLE AJE KODASHIRI KO BABU TO MUJI TSORON ALLAH MU GYARA GOBENMU" WANNNAN SHAWARAR MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱 QUEEN OF WRITER 📝 KAWAI,")

Iskatasoma k'ad'awa dak'arfi take duhu ya maye gurin duk wani Abu dakewurin iskatasoma d'aukeshi su kansu mutanen Bata raga musu ba d'aukarsu take tana jefawa ruwa wasu kuwa saidai ta katsesu gida biyu tamkar rake jini yasoma zarya wurin ihu kawai ketashi na Mutane sai Ihun neman taimako suke,

Iyarud'ewa su Anisa sun rud'e Bayan motar suka lab'e suna rik'e dajuna ita da Rahila duk wata Addu'a datazo bakinsuyi suke,

Anjima cikin wannnan halin Kafin Haske yabayyana na farin wata, Koda suka duba gurin jini yayi Anbaliya har cikin ruwan ga gawarwakin Mutane zube duk an Ragargazasu bakyawon gani, sun tsorata iya Matik'a sun rud'e ihu Suka kurma suduga Sauran domin Yanzu bazasu wuce Ashirin ba sama da talatin duk sun hallaka, juya idanuwanda Anisa zatayi tahange Amarya sarkafe dawani tsinin icce tamkar k'warangwal haka tadawo bakinta saijini kefita, k'ara Anisa tasaki tana nuna musu da Hannu, Koda suka waiga sukagani suka k'ara shiga tashin hankalin, motsi ruwan gulbin suka fara dawani haniniya tamkar dawakai zasu fito cikin, cikin tashin Hankali suka rugu cikin dajin suna gudun ceton rayukansu, Aikuwa Aljanun Suka mara musu baya domin kuwa duk mutanen da suka kashe dawowa sukayi k'warangwal sukabi bayansu, gudu suke Sosai na fitar hayyaci k'afafunsu sai taka k'aya suke domin tuni suka jefarda takalmi amma tsabar tashin Hankali bawanda yakecin zogin k'ayar, dukansu suna tare wani k'aton dutse Suka gani cikin sauri suka shige cikinsa Duka suka b'uya, Koda k'warangwal d'in sukazo basu gansuba Suka wuce, duk sunyi tsit bamai motsi bamaijin bacci dukansu danasanin zuwa wannnan partyn suke, bacci B'arawo ne Kawai yayi nasarar sacesu,

Kiran sallar Assubah ne yatashi daga Mugun mafalkin da yake firgigit yatashi da Sunan Allah abakinsa saida yasake dubawa amma batadawo ba hakan yatabbatar Masa ba lafiya ba, sallah yayi Yajima yana Addu'a yau ko tsayawa karatun baiyiba yadawo gida kiranta yacigaba dayi amma yakasa samu, zaune yayi rafka Uban tagumi, yana Addu'a Allah yatsare matarsa da d'ansa, jiran haske yabayyana yake yaje gidansu yagani,.

Sanyi da iskane yatashesu Koda suka falka sukaga gari ya waye tar masu Sauran imani sukayi taimama sukayi salla da Rok'on Ubangiji yafiddasu cikin wannnan bala'in

Huci suka somaji daga bayansu Koda suka waiga wani k'aton maciji sukagani idanuwansa manya manya bakinsa tamkar rame nufosu yayi cikin tashin hankalin suka ruga waje shima yabisu kamar ta iska haka ya dira gabansu tareda cafkar saurayin Safa, yasoma kalaci dashi domin kuwa had'eshi yasoma yi kanajin k'arar karairayewar k'asusuwan jikinsa da macijin ketaunewa, ihu suke shikanshi saurayin ihu yake iya gigicewa sun gigice, sake rugawa sukayi sukabar saurayin wanda yajima da mutuwa Domin tamas macijin yamasa Yacinyeshi, koda yagama cinyeshi yaga basunan yabi bayansu Yana nemansu,

Sosai suke gudu cikin tashin Hankali sunyi nisa sosai Suka tsaya suna maida numfashi, kuka safa tasaki tana Fad'in"nayi Dana sanin zuwa partynnan nayi Dana sanin sanin k'awancena da diza nayi nadamar k'injin mahanar
Iyayena Danayi nazo Nan gashi *SANADIN PARTY* munata halaka"

Dukansu kuka suke kowa yana tuna yarda Yafito wasu da dama ance kada suzo wasu kuwa sunfi k'arfin iyayensune wasu kuwa dama su fand'ararrune,

Dafe cikinta Anisa tayi tana kuka da danasanin bijirewa mijinta gashi dakanta tawo kanta inda zasu halaka Kuma Abun Bak'in ciki inda ko gawarsu baza'a samuba Kuma su mutu *SANADIN PARTY*

Motsi sukaji suna waigawa sukaga wata Y'ar tsohuwa tanufosu tana tafiya da k'yar da Y'ar sandarta............................

_BASEERATA ITACE ARZIKINA😍_

WhatsApp number 07064904617

*SANADIN PARTY HORRO STORY💀☠️*

_FREE BOOK_

_RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱..._

```MARUBUCIYAR... (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book, (6)Shagala Free book, (7) Silar d'a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9) Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12) Bak'in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d'aukar fansa free book. (14) ZAYYAN 💞 ZEEYAT PAID BOOK. (15) MAKARANTAR KWANA FREE BOOK. (16) SHAGALA FREE BOOK,, (17) SO SIRIRIN ZUCIYA..... And Other's BUT NOW (18) SAURAYINA.. (19)D.S.P ANNUR PAID BOOK....(20) SAKACINA PAID BOOK.... (21) SO!!! FREE BOOK... (22) FATALWAR ☠️ BUDURWAR MIJINA PAID BOOK... (23) D'AUKE D'AI D'AI DUNIYAR SHAID'ANU PAID BOOK...(24) RUHIN JINN PAID BOOK.. (25) JAMI'IN SIRRI C~I~D PAID BOOK 300 ONLY.. (26). SANADIN PARTY HORRO STORY
loading..... Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱 QUEEN OF WRITER 📝```

_Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah mad'aukakin sarki Mai bayarda baiwa gawanda yaso Kuma sanda yaso Ina godiya ga Allah Allah daya sake bani dama had'ida baseerar sake kawomuku sabon littafina maitaken_ *SANADIN PARTY💀☠️ HORROR STORY*
_Ina fatan yabada darussuka dama ilmantarwa Kamar dai yarda sauran littafaina suka bayar....._

*Arayuwa zaka burge wasu Kuma zaka bawa wasu haushi, wasu zasu soka Wasu Kuma zasu k'ika wasu zasu yabeka wasu kuma su kusheka, Haka rayuwa take tafiya idan Kama wani wani bazaka masa ba, dukanin Sak'onninku suna zuwa gareni na Yabo da Akasin hakan, ban Damu da zagin wasu ba Domin kuwa nasan cikakkiyar ni'ima tana Aljanna Amma duk da hakan Ni Mujaheedah Matar mlm Ammyn khausar 🤱 QUEEN OF WRITER 📝 nakakce Alhmdllh Domin Alk'alamina A tsalkake Yake bana Batsa ko shashanci ko cin zarafin wani ko Aibatawa, Ina Rubutu Kan tsarin tafarkin Ilimi domin bada Shawara nasiha Fad'akarwa Wa'azantar ilimantarwa, kuma Alhmdllh Sak'ona Yana zuwa daidai inda Allah ya nufa Kuma Yana ban Lada daidai da Aikina, kuma Ina Samun Masoya daidai nufin Ubangiji ✨ Inaaa Alfahari daku Masoyana Kuma Ina sonku Tabbas _BASEERARA ITACE ARZIKINA😍_ Allah ya k'ara wadatamu yamuna K'arshe nainyau yasa mucika da imani yabamu Masoya Nagari ya karemu daga Mak'iyanmu, Allah kabama k'asarmu NIGERIA zaman lafiya da Arziki Mai Amfani..... AmeenAmeen......... Mujaheedah Matar mlm Ammyn khausar 🤱 QUEEN OF WRITER 📝 HAUSA NOVELS 📚 TAKUCE🥰🥰*

_Friday 6/10/2023 October_

*Page 11 to 20*

Duk zabura Sukayi Suka somaja baya cikin tsoro, nufosu take sukuwa sai matsawa baya suke, ganin sunashirin guduwa Tace"Kuda kata kada kuji tsoro taimakonku Zanyi zanmaidaku gida,"

"Zaki maidamu gida kinsan meya fito damu ne,"? Cewar Safa tana zabgamata Harara

"Ni kuwa nasan meyafito daku dukanku kuna Hanyar halaka domin wannnan dajin bawani mahaluk'i bil'adam daya tab'ashigowa Yafita araye kuma ajalinkune yake kiranku da taurin kai yasa kukazonan dukta *SANADIN PARTY* kuzo namaidaku gida kanku Ida halaka,"

Kallon kallon sukafara anrasa Wanda zaije inda tsohuwar, Can wani yamatso shida budurwarsa yace"mudai munason ganin kanmu gida komake wacece to kimaidamu,"

"Kubani Hannuwanku," tafad'a tanamik'a misu nata Hannuwan

"A'a kada kuyi gangancin yarda da wannan tsohuwar Wallahi ba inda zata kaiku face halaka kada kubita"

"Ke dalla rufewa Mutane baki inke bazakiba tomu zamu,"mik'a Mata Hannu Sukayi takama

Dariya tafashe da ita take take tasauya kala ihu suka somayi domin rik'e Hannuwansu datayi jininsu takesha,

Arud'e Sauran Suka ruga Cikin dajin sukabarsu Hannunta tana hallakasu,

**********************

Haske yana bayyana Yamik'e wanka yayi yasaka manyan kayansa Yafito motarsa yashiga yanata tinani yanufe gidansu, tarba maikyau yasami wurin iyayenta Koda baitanbayaba yasan Bata Gidan yaga zahiri shuru yayi tareda dafe kansa,

"Meya faru tasake Maka halin natako,"Ummansu tafad'a cikin fad'a

"Maganar gaskiya umma batanan ba'a gidan takwanaba daga sunan zuwa biki tinjiya haryanzu batadawoba ni Abun tsoratanima yayi bata tab'a irin hakaba gashi duka wayoyinta kashe"

"Innalillahi wa'inna ilaihin Rajuun, bikinwa taje," Cewar Abba

"Eh to tace k'awartace hinda"

"Au waiduk fad'anda mukewa Yarinyarnan Bata sauyaba haryanzu batajin maganarka kenan,"

"Yanzu umma Bata wannan akeba yanzu kutayamu Addu'a Allah yabayyanata sannna yanzu zanje can gidansu Yarinyar naji,"

"Mujedai tare zamu ai,"Cewar Abba

Tare sukaje Koda sukaje gidan cike saikuka Ake ga Y'ansanda sai sintiri suke, fitowa sukayi nan suka sami labarin wai ba Amarya kuma ba Ango in shout duk wad'anda sukaje bikin basudawoba kuma dukansu anrasa samun kowa awaya, dama Akaje wurin gawarwaki akagani wanda saika tsura ido sosai sannna kagano d'anka,

"Subhanallah wani abu yasamesu kenan Allah katsaremin Anisa koda itace Kawai,"jiri yafara d'ibarsa Saida Suka rik'eshi ya zauna, Abba ne yasami k'arfin halin dubawa wasu gawarwaki ba kyan gani saida yayi hawaye ganin irin mutuwar walak'anci dasukayi,

"Abba kacemun my Anisa batacikinsu,"

"Eh kwantar da Hankalinka Bata cikinsu, ASP yanzu Sauran yaranmu dakecan cikin dajinfa,"

"Eh Alhaji zamu koma dama mundawo saboda kawo wad'annan gawarwakin Dan Asan meke faruwa Kuma amusu Addu'a damu dazamusake komawa dajin Yanzu,"

"Abba zanbisu"

"A'a Ammar bazaiyu ba Kai Amanane gareni bazaiyu Saboda ceton Rayuwar Y'ata nabari taka tahalakaba, koda Anisa tamutu kusan itace tajawa kanta domin rashinjinta yajamata inbanda Rashin Kunya Ina Matar Aure Inazuwa party? hakan daya faru ai zaibada izina ga Y'anbaya masu tasowa, bakomai cikin party face halaka,"

"Dan Allah kabarni naje Abba," dagewa yayi dole Abba yabarshi sukatafi tare,

Motoci kusan guda 4 suka kwasa kusan rabin tawagar duk Iyayen yaranne,....

Iyayen Ammar sunjima da rasuwa saidai Kan surasu sunbashi wasiyar auren Anisa dakuma kula da ita ganin Irin halaccin da iyayenta Suka musu Sanda sukazo garin basuda kowa Amma Abba yad'auke su, Anisa kuwa itace tanuna tanason Ammar badan yana sontaba Dan biyayya yasa ya Aureta da halaccin iyayenta, bayan mutuwar Iyayensa iyayen Anisa suka zame Masa gata wannnan yasa baya iya fushi da Anisa Kuma Ahankali Yasoma sonta..

Sunyi gudu Sosai sannna Suka tsaya sunamaida numfashi,
Kuka Anisa tasa tana rik'e cikinta domin wata irin wuya takeji ga yunwa da k'ishi,
"Sannu kiyi hak'uri Anisa zamu Kub'uta in Sha Allah,"

"Ruwa ruwa Rahila kutaimaka kuban ruwa zanmutu,"Haka kawai take fad'a cikin fita hayyaci
Chapter 2 · 0% Book details