← Book details Sanadin Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 3 OF 6

Part dinta ta koma ta gyra tayi wanka ta saka wani 3qtr da riga mara hannu ta shige kicin cikin karfin hali domin jikinta ciwo yakeyi

Sanadin Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

Breakfast ta had'a domin komai na bukata akwai shi a kicin

Tana gamawa ta kwashe ta kai kicin ta zauna tana jiranshi

Bashi ya shigo ba sai karfe 7:14 tana ganinshi ta mike ta rungumeshi

Murmushi yayi yace"yi hakuri na Dade ko? naje gun Ammine take min maganar auren MARWAN da ilham,wai ta gaji tana son ayi auren nan da sati biyu,ta gaji da zancen nasu da baya karewa gomma ayi auren kowa ya huta"

IMAN tace"hakane amma sati biyu yayi kadan domin ya kamata ayi planing wedding din"

Yace"no yayi a two weeks din zamu d'auko event planer,kuma za a hada ne da na sule da ihsan"

Tace"ok"

Yace"iya na gaishe ki"

Tace"ina amsawa"

Zama sukayi tayi musu serving din fried Irish da kwai ta had'a me tea

Yace"har kinyi girki?"

Tace"eh wallahi bana son SULTAN yaji yunwa"

Kadan yaci yace"ya koshi "

Tace"ka ci mana ko beyi maka dadi bane?"

Yace"yayi wallahi amma ni na saba da d'umamen tuwo bana son irin abubuwan nan"

Tace"sorry ban sani ba amma bari in anso maka a gun iya"

Yace"no zan aika"

Tace"ok no problem,dama ina son muyi magana"

Yace"name?"

Tace"please so nike inje nigeria in duba wasu companies dina domin nayi kwana biyu banje ba tunkan in fara rashin lafiya inason in...."

Bata gama magana ba ta gan ya jingina da kujera ya lumshe ido

Tace"ok sorry na fasa"mikewa yayi ba tare da yayi magana ba ya shige ciki

Murmushi tayi tace"hmm d'an iya sai iya"
Chapter 3 · 0% Book details