← Book details Rayuwar Samhat Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 13

Sashe 6

Rayuwar Samhat Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiru Maman tayi mata kafin tace "Allah dai ya shirya zuri'a amma sam ba ta jin magana yanzu bakiga yanda ta maida kanta farar ƙarf da yaji"

'Shiru Aisha ta na tunano irin yallayar Beela damacan tana shafe-shafen ta amma dai tunda har mamanta ta maganta akan abu to tabbas abin ya munana'

Cigaba da fira sukayi cikin nutsuwa dan kamar yanda Aisha batason magana da hayaniya haka mamanta take itama idan ka ga suna fira ahankali suke magana cikin nutsuwar da Allah ya azurtasu da Ita.

Sai bayan kwana biyu da dawowarta sannan ta shirya ta je gidansu Nabila dan su gaisa.
Nabila tayi farin cikin ganin yanda Aisha ta koma ga tsohon cikinta a gaba wanda ya ƙara mata kyau.

Aisha ba ta daɗeba gidan ta yiwa Nabila sallama ta tafi gidan dan tuda dazo ta lura da kallon da Maman Nabeela ke jefa mata sai duk tasha jikin jikinta.

Bayan tafiyar Aisha babu jimawa saiga Beela ta dawo daga yawon gantalin da ta saba, Maman Nabila ta sakata ɗaki ta gaya mata zuwan Aisha da yanda ta koma kamar wata Hajiya, sosai Beela ta rikice ta na ɗurama Aisha zagi ta uwa ta uba ta na faɗin shienan ta cuceta ta yaudareta tunda taji ance tana da ciki.

Dakyar Maman Nabila ta rarrashi Beela tare da gaya mata wasu maganaganu da suka sanya ta ɗan nutsu dukda a zuciyarta kobara ce ke ci ta tsananin ƙiyayyar Aisha.

Da marice suna zaune a parlo suna fira saiga Beela kamar an jefo ta faɗo musu, tsit sukayi suna binta da kallon mamaki, sosai ƙeya tayi ta gaida Maman Aisha a takaice ta koma kan Aisha tana ta yi mata tambayoyi harda tambayar tare da mijinta tazo da tace "A,a" sai ta kuma tambayar yaushe zai dawo.

Khaleel ƙanin Aisha ne ya ja uba tsaki ya tashi yana yiwa Beela maganar miye ruwanta da mijin Aishar.

Maman Aisha tabason rashin kunya dan haka ta dakatar da khaleel cikin tsawa tace ya tashi ya fice ya basu waje.

Cikin jin zafin abida Beela tayi ya fice daga gidan baki daya.

Beela ganin ba ta samu abinda ta ke so ba yasa ta tashi ta tafi tana sakejin tsanar Aisha na lunkuwa a zuciyarta.

A gidan su Aisha, Aisha kewa mamanta mita akan tambayoyin da Beela keyi akan mijinta.
Murmushi Maman Aisha tayi tana jinjina irin soyayyarda Aisha kewa mijnta da ta kasa ɓoye kishinta akan sa.

A kwana atashi cikin Aisha yashiga watan haihuwa wanda cikin dare suna waya da Muhammad yake faɗa mata zaizo gobe insha Allah Alhaji Bashir ya barshi yazo tunda aikin ya ɗan tsagaita.

Sosai Aisha tayi farin cikin zuwan mijinta wanda saboda zumuɗi ta kasa zaune ta kasa tsaye dukda yau tunda ta tashi takejin ciwon bayan kaɗan-kaɗan.

Bayan saukar Muhammad gidansu ya gaisa da ƴan uwa da abokan arziƙi yasake shiri dan zuwa wajen sanyin idaniyarsa dan yayi mising nata ba sosaiba.

Bayan yaje sungaisa da ƴan uwan Aisha da mahaifanta aka kaushi ɗakin da baban Aisha ke saukar baƙi.

Bayan sun gaisa da Aisha ya lura da yanda take cije baki hakan yasa ya tambayeta ko lafiya?

Bakomai tace mashi amma ganin abin yayi yawa yasa yace kodai haihuwarce? ɗaga mashi kai tayi dan zuwa yanzu dauriyarta ta fara ƙarewa ganin ciwon sai gaba ya ke.

Maman Aisha yasanamawa yace zasuje asibiti akula da ita acan.
Amsa shi tayi da suyi gaba ita zata taho ta kayan buƙatar.

Awa ɗaya shiru awa biyu shiru Aisha ba ta haihuba lititoci sai kaiwa suke suna komowa.

Hamkalin Muhammad yatashi da aka gaya masa haihuwace amma yaron yana kwance abisa bai juyaba dole sai anyi mata CS babu ɓata lokaci Muhammad ya rantaɓa hannu aka shiga da Aisha aiki.

Cikin ƙankanin lokaci aka ciro yaro namiji fari tas kamar uwarsa ƙaton gaske dashi.

Zokuga Murna wajen ƴan uwa da abokan arziki duk wanda ya ɗauki yaron saiya jinjinawa Aisha ganin girman yaron da kuma irin baiwa kyau da Allah yayi mashi.

Labarin haihuwar Aisha ya riski su Beela ahaukace ta tashi daga zaunen da take har tana kifawa tashiga ruwa kuka tana faɗin shikenan ta shiga uku Aisha ta haihu zata mallake dukiyar Muhammad.

Mummunar bugawa zuciyar Nabila tayi jin abinda Beela ke faɗi, kasa tsayuwa tayi ta zauna daɓas tana sakin zafafan hawaye na baƙin cikin halin yayarta kuma ƴar uwarta.

Maman Nabila ce ta lura da katoɓarar da Beela tayi agaban Nabila aiko ta hau naɗe tabarmar kunya da hauka harda cewa idan Nabila taje asibiti ganin Aisha sai ta tsine mata.

Sosai Nabila tayi kukan baƙin cikin halin mahaifiyarta ta ƴar uwarta, ida ba hanata zuwan da Maman Nabila tayi asibitine ya dame ta ba A,a da wane ido zata kalli Aisha baiwar Allah kawarta ta amanah ace wai yayarta ke son mijinta abun sam ba tunani aciki.

Ranar Nabila ɗaki ta wuni tana zubar hawayen baƙin ciki da takaicin abin kunyar da Mama da Beela zasu aikata.

𝑲𝑼𝑩𝑰𝒀𝑰𝑵𝑰 𝑫𝑶𝑴𝑰𝑵 𝑱𝑰𝑵 𝒀𝑵𝑫𝑨 𝒁𝑨𝑻𝑨 𝑲𝑨𝒀𝑨 𝑨𝑪𝑰𝑲𝑰𝑵 𝑾𝑨𝑵𝑵𝑨𝑵 𝑳𝑨𝑩𝑨𝑹𝑰 𝑴𝑨𝑰 𝑻𝑨𝑲𝑬𝑵 𝑹𝑨𝒀𝑼𝑾𝑨𝑹 𝑺𝑨𝑴𝑯𝑨𝑫, 𝑲𝑨𝑫𝑨 𝑲𝑼𝑴𝑨𝑵𝑻𝑨 𝑴𝑼𝑵𝑨 𝑪𝑰𝑲𝑰𝑵 𝑳𝑨𝑩𝑨𝑹𝑰𝑵 𝑻𝑨𝑹𝑰𝑯𝑰𝑵 𝑹𝑨𝒀𝑼𝑾𝑨𝑹 𝑴𝑨𝑴𝒀.

𝑹𝑨𝒀𝑼𝑾𝑨𝑹 𝑺𝑨𝑴𝑯𝑨𝑫 𝑳𝑰𝑻𝑻𝑨𝑭𝑰𝑵 𝑲𝑼𝑫𝑰 𝑵𝑬 𝒁𝑨𝑲𝑰 𝑩𝑰𝒀𝑨 𝑵𝑨𝑰𝑹𝑨 200 𝑲𝑨𝑪𝑨𝑳 𝑫𝑶𝑴𝑰𝑵 𝑪𝑰𝑮𝑨𝑩𝑨 𝑫𝑨 𝑩𝑰𝒀𝑩𝑰𝒀𝑨𝑹 𝑳𝑨𝑩𝑨𝑹𝑰𝑵.

𝑴𝑨𝑺𝑼 𝑱𝑰𝑹𝑨𝑵 𝑫𝑶𝑪𝑼𝑴𝑬𝑵𝑻 𝒁𝑨𝑺𝑼 𝑩𝑰𝒀𝑨 400 𝑲𝑨𝑪𝑨𝑳 𝑫𝑶𝑴𝑰𝑵 𝑴𝑨𝑳𝑳𝑨𝑲𝑨𝑹 𝑳𝑰𝑻𝑻𝑨𝑭𝑰𝑵, 𝑲𝑨𝑹𝑲𝑰 𝑩𝑨𝑹𝑰 𝑨𝑩𝑨𝑹𝑲𝑰 𝑨 𝑩𝑨𝒀𝑨.

𝑮𝑨 𝑨𝑪𝑪𝑶𝑼𝑵𝑻 𝑵𝑼𝑴𝑩𝑬𝑹 𝑫𝑨 𝒁𝑨𝑲𝑼 𝑻𝑼𝑹𝑨 𝑲𝑼𝑫𝑰𝑵 👇👇👇👇👇👇👇👇

9136291920
𝑴𝑨𝑹𝒀𝑨𝑴 𝑼𝑴𝑨𝑹
𝑶𝑷𝑨𝒀.

𝑺𝑯𝑨𝑰𝑫𝑨𝑹 𝑩𝑰𝒀𝑨 𝑻𝑨 𝑾𝑨𝑵𝑵𝑨𝑵 𝑳𝑨𝒀𝑰𝑵
👇👇👇👇👇👇👇👇

09136291920

𝑫𝑨𝑮𝑨 𝑨𝑳𝑲𝑨𝑳𝑨𝑴𝑰𝑵✍️
𝑴𝑨𝑹𝒀𝑨𝑴 𝑺𝑻𝑨𝑹⭐⭐⭐

?RAYUWAR SAMHAD 🌹( abar tausayi ce 😭)

DAGA ALKALAMIN MARYAM STAR✍🏻�⭐⭐⭐

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/FwHkk5nhlvS8HanVoGH6q

*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*

_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐

PAGE 2️⃣0️⃣🌹2️⃣1️⃣

___________________________________________________________________________

بسم الله الرحمن الرحيم.
Sa Beela tayi ta shirya suka tafi gidan ƙawarta dake cikin gari, Suna isa itama ta shirya dan Maman Nabila ta gaya mata zasuzo , mai napep suka tara su ka bar unguwar zuwa ƙarsgen gari can cikin dadi.

Wani baƙin mutumne zaune shi kaɗai ya na zane-zane kamar ma ƴaƴan Aljannu yake zanawa tunda suka isa wajen Beela ke yamutse fuska kamar zatayi amai.

Kora mashi bayani Hajiya Larai tayi akan abinda ya kawosu, wani ƙullin magani yabasu wanda zasuyi amfani dashi, ƙudi suka aje mashi tareda godiya suka bar wajen.

Sosai Hajiya Larai ta gargaɗi Beela wajen yin amfani da maganin.

A ɓangare Aisha tunda aka sallamota Asibiti ƴan barka ke zarya saida suka ƙara sati guda sanan tayi taron sunan da ya jijjiga zuciyar Sarhabila da ta Maman Nabila.

Yaro yaci Sunan Muhammad Mubeen ake kiranshi da Mubeen zallah.

Bayan sunyi arba,in Muhammad ya matsa akan sukoma aiki ya taso masa.

Sosai Aisha tayi kewar Mamanta da ƙannenta su Khaleel da aminiyarya Nabila da kullum sai ta zo ta ɗauki Mubeen.

Tunda su Aisha suka tafi basu sake dawowa ba sai bayan shekara uku sannan mubeen ya girma sosai harta sake samun wani ciki dande Ƙarami ne.

Wannan dawowar a gidansu suka sauk wanda Muhmmad ya sake gyarashi tunda ba.a taɓa zama cikinshi ba sosai gidan ya ƙawatu da kayan more rayuwa.

Sanda Nabila zataje gidan Beela tace itama zata je daga ɗanta Mubeen tadade bata ganshinba,

Badan Nabila ta so ba taje da Beela gidan Aisha aiko a haukace Beela ta dawo dan can ta baro Nabila, tararta mama tayi tana tambayarta ko lafiya?.

Beela ta kwashe labarin komai ta bawa Maman Nabila aiko suka ɗauki mayafai sai wajen malam dan sanar dashi Muhammad ya dawo.

Wani magani ya basu ya ce suyi amfani da shi inda Muhammad ke zama zasu binne wasu layoyi tare da harin maganin da zasu sanya mishi a abici.

Bayan kwana biyu Beela ta je gidan sukasha fira da Aisha harda taya ta girki da yake cikin Aishar ya fara tsufa, bayan sungama ta kuma tarkato ƴan share-share tanayi Aisha ce ta tayata tace dama tanason ta gyara ɗakinda Muhammad ke aiki idan ya dawo gida amma jikinta babu ƙarfi. hartintuɓe Beela keyi wajen zuwa taya Aisha aikin gyara dakin zuwa tayi tana kakkaɓe files dake kan wani ɗan table da kujera ke wajen anan tayi dabarar saka layoyin da boka ya bata ba tare da Aisha ta luraba.

Bayan sungama da Beela zata tafi gida ta haɗa mata sha tara ta arziki tace ta kaiwa Maman Nabila babu kunya ta amshe babu ko godiya tana raya idan ta shigo gidan zata koyawa Aisha hankali.

Bayan kwana biyu Aisha ta kasa gane kan Muhammad, sai daga baya taji labari wai aure zai ƙara tasha kuka sosai ga tsohon ciki ganin babu inda damuwa zata kaita yasa ta fawwala ma Allah komai taci gaba da rainon cikinta.

Ranar da Aisha ta haihu a ranar aka ɗaurawa Muhammad aure da Sarhabila.

Aisha bata san wacece Muhammad ya auraba sai bayan taga wankan.

Sosai Aisha tayi kukan har saida ta fara rashin lafiya aka kaita asibiti tayi kwana biyu aka sallamota.

Sosai Aisha ta shiga damuwa data zauna sai tunani da hawaye wani lokaci sai idan yaronta Sadeek yayi kuka take dawowa daida.

WAI SHIN MIYENE YAYISILAR RASUWAR AISHA?.
BAYAN BEELA TA TARE MIYASA MUHAMMAD BAI KAITA WAJEN AISHA SUNGA JUNABA?

KU BIYONI DAN JIN YANDA ZATA KAYA

KU KASANCE DA ALKALAMIN MARYAM STAR DANSAMUN DADADAN LABARAI MASUZAFI

NAGODE

DAGA ALKALAMIN
MARYAM STAR✍🏻⭐⭐⭐.

🌹RAYUWAR SAMHAD 🌹( abar tausayi ce 😭)

DAGA ALKALAMIN MARYAM STAR✍🏻�⭐⭐⭐

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/FwHkk5nhlvS8HanVoGH6ql

*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐

PAGE 2️⃣4️⃣ 🌹2️⃣5️⃣

___________________________________________________________________________

بسم الله الرحمن الرحيم.

Bayan Alhaji Muhammad ya sungumi gawar Aisha, hospital ya tafi da ita ya kai musu ya na kuka yana faɗin Aisha ba ta mutu ba su ceto masa rayuwarta.

Surutai yayita yi marrasa kan gado damin kuwa duk mai hankalin da ya kalli gawar ya san ta mutu kuma ga dukkan alamu ta ji jiki sosai ganin yanda jini yayi jaga-jaga a jikinta kamar wacce tayi wanka da shi.

Riƙe Alhaji Muhammad likitocin sukayi suka fara bashi taimakon gaggawa ganin yanda duk ya fice a hayyacinsa.
Chapter 6 · 0% Book details