← Book details Rayuwar Samhat Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 13

Sashe 2

Rayuwar Samhat Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiru Abbu yayi yana addu,ar Allah yasa ta farka cikin koshin lafiya a basu sallama don yasan lokacin da aka bashi bazasu sauyaba tunda su ba kanannan mutane bane dake canza magana, a wani gefe na zuciyarsa yana tantama akan tafiya da ita yau kamar yanda sukace, wata zuciyar kuma na bashi kwarin gwuiwa akan hakan shine gatan da zaiyi mata, agefe daya kuma yana zullumin rabuwa da ita.......

Daga alkalamin maryam star⭐✍✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Follow this
link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/K8VBORyiBdJCR61hLJ9Hq9

🌹RAYUWAR SAMHAD 🌹( 𝑨𝒃𝒂𝒓 𝒕𝒂𝒖𝒔𝒂𝒚𝒊 𝒄𝒆😭)

𝑾𝑹𝑰𝑻𝑬 𝑩𝒀 𝑴𝑨𝑹𝒀𝑨𝑴 𝑺𝑻𝑬𝑹.⭐⭐⭐✨🌹

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.co/

K8VBORyiBdJCR61hLJ9Hq9 *htps://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*

_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

𝑷𝑨𝑮𝑬 3️⃣

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

بسم الله الرحمن الرحيم.

Zaman shiru sukayi a wajen kafin daga bisani Mamman driver yayiwa Abbu sallama ya wuce gida zuciyarsa cike da tausayin halin da Samhad ke ciki.

Samhad ba ita ta farka ba sai da tayi awanni ukku tana barci. Abbu yaje ya fad'awa doctor farkawata zuwa yayi ya sake dubata tare da yimata 'yan tambayoyi, dayaga babu wata matsala ya sallameta kawai.

Sosai Abbu yaji dadin sallamar don ya riga ya yanke hukunci a yau zai mi'kata gidan mijinta don zuciyarta ta samu salama.

A daidaita sahu ya tare musu suka shiga. Suna tafe Abbu yana bawa Samhad hakuri tare da nasiha me ratsa jiki.

'Dago manyan idanunta da suka fad'a saboda kuka da damuwa tayi ta kalli Abba cikin karayar zuciya tace. "Abbu dan Allah da gaske kayimin aure? Anty zee tace d'an daba ka auramin hakane? "
Tayi maganar harshenta na sark'ewa.

Numfashi Abbu ya sauke tare da kallon layin nasu wanda ha wasu motoci suka jera tun daga farko har zuwa gidan shi dake karshen layin.

Samhad ma kallon motocin take zuciyarta na tsinkewa.

Abbu be sake magana har suka isa k'ofar gidan nashi. Me a daidita yasaukesu ya Abbu ya biyashi hak'inshi yayi tafiyarsa, kama hannun Abbu Samhad tayi tana rarraba idanuwa ganin ambud'e wata jibgegiyar hamshak'iyar mota, wani babban mutum ne ya fito fuskarsa da fara,a ya tunkarosu, yana zuwa ya mik'awa Abbu hannu suka gaisa cikin mutuntawa.

Gaidashi Samhad tayi ciki sanyayyar muryarta.

Kallonta yayi cikin fara,a ya amsa mata a ranshi yana yaba nutsuwarta, tabbas ya yaba da hankalinta kuma daga gani zatayi abinda ya dace saidai wani 'barin na zuciyarsa yana gaya mashi anya beyi son kaiba kuwa, wani gefen kuma yana bashi kwarin gwuiwa akan hakan shine dai-dai.

Maida hankalinsa yayi wajen Abbu suka ɗan tattauna,

Samhad bata fahimci komai ba seda Abbu ya kama hannunta yana mata kallon tausayi, gani tayi wannan mutumin ya buɗe wata wata rantsatsiyar farar mota yace wa Abbu bisimilla,

Janta Abbu yayi ya sakata cikin motar tare da yi mata magana cikin kwantar da murya.
"Kibisu Samha iyayen mijinki ne nasan zasu basu kulawar dana gagara baki tsawon rayuwar da mukayi atare, na yafe duniya da lahira kije ki riƙe mijinkin hannu biyu kiyi biyayya Allah yana tare da ke zan kasance me yimaki addu'a akoda yaushe Allah yayi maka Albarka ya karemin ke aduk inda kike." Yana gama maganar ya saki hannunta tare da ɗauke kwallar data zubo mishi.

Jikin Alhaji Muhammad yayi sanyi yanjin anya basu dauki alhakin yarinyar ba.

Gwauron numfashi ya sauke yana miƙawa Abbu hannu sukayi musabaha, sake jaddada mishi Abbu yake ya kula mishi da Samhad Ammana bata da kowa se Allah sekuma shi.

Tunda suka ɗauki hanya Samhad tayi shiru tanaji a jikinta wannan tafiyar itace mukulin bud'e sabbin ƙofofin da zasu saura RAYUWAR SAHMAD, tanaji akwai babban k'alubalen dake tunkaro rayuwarta.

Tanaji a jikinta akwai babban al'amarin daze faru da ita a yau ɗinan, hannu takai akan kyakkyawar doguwar fuskarta tana ɗauke hawayen da suka gangaro mata. A fili ta furta "ya Allah koma miyene ze faru dani ka sauk'ak'amin yanda zan iya ɗauka, Allah dakai kad'ai na dogara banida kowa se kai Allah ka ji'bnci lamurrana."

𝑫𝑨𝑮𝑨 𝑨𝑳𝑲𝑨𝑳𝑨𝑴𝑰𝑵 𝑴𝑨𝑹𝒀𝑨𝑴 𝑺𝑻𝑬𝑹⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐🌹

🌹RAYUWAR SAMHAD 🌹( 𝑨𝒃𝒂𝒓 𝒕𝒂𝒖𝒔𝒂𝒚𝒊 𝒄𝒆)

𝑫𝑨𝑮𝑨 𝑨𝑳𝑲𝑨𝑳𝑨𝑴𝑰𝑵 𝑴𝑨𝑹𝒀𝑨𝑴 𝑺𝑻𝑨𝑹⭐⭐⭐

: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/K8VBORyiBdJCR61hLJ9Hq9

*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_
Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

________________________
🌹❤🌹❤🌹❤🌹❤🌹❤

PAGE 5️⃣

بسم الله الرحمن الرحيم.

Gaban Mammy yayi wata mummunar faɗuwa har tuntuɓen harshe take wajen Tambayar Samhad, "ke lafiya mike faruwa waya kawoki nan?".

Diriricewa Samhad tayi da kyar ta lalubo jarumta ta tace

"Babu komai dama wani abu ne ya fad'amin ido shiyasa kikaga ina kuka"

Ajiyar zuciya Mammy ta sauke duk da kamar akwai karya cikin maganar yarinyar.

Nannauyan numfashi Mammy taja tare da cewa Samhad, "yanzu ɗauko kayan kizo in kaiki masaukinki".

Ajiyar zuciya Samhad tayi tare da hamdala ga Allah da yasa Mammy bata fahimci komai ba, haba wannan abun kunyar har ina duk ta tsargu da kanta gani take kowama zai iya fahimtar abunda yafaru.

Ajiyar zuciya ta sauke bayan ta dawo daga tunanin abinda ya faru daga zuwanta gida.

A daddafe tashiga toilet dake dakin nata wanda ya ƙawatu da kayan zamani.

Ita yanzu gidan ya isheta batajin zata iya rayuwa cikin shi, gefe guda kuma tunanin yan gida da kewar Abbu sun isheta duk da ba wani sakin jiki yake da itaba amma kullum cikin yimaya nasiha da ban haƙari yake.

Ture tunanin komai tayi ta fara alwala cikin nutsuwa duk da jikinta da zuciyarta babu dadi.

A nutse ta gabatar da sallar isha'i tare da shafa'i da wutiri, bayan ta kammala ta fara kwararo addu'oi cikin zubar hawaye da karayar zuciya.

Ta dade tana addu'a kamin daga bisani ta tashi ta linke hijabin ta ajiye.

Abincin da Salma ta kawo mata lokacin da take sallah ta jawo ta bude fried rice ce tasha vegetables se ƙamshi spices take, se ruwan zafi cikin dan ƙamshin flask da lemon me sanyi.

Tanajin yunwa sosai shiyasa taci abincin amma kwata-kwata baya mata dadi hasalima wani ɗaci-ɗaci takeji bakinta nayi.

Bayan ta kammala ta yi brush ta kwanta kasan tyils tana tunanin rayuwa yanda take garata kamar kwallon kafa, batayi aune ba barci yayi awon gaba da ita.

A 'bangaren Hajiya Turai kuwa ajiyar zuciya ta sauke jin abinda Samhad ta faɗama Mammy, kwata-kwata ta manta da inda take ganin yarinyar ba ƙaramin rudar da ita yayiba, Wanka tayi tana tunanin irin mummunan hukuncin da Mammy zata yimata idan tasan tayi wannan gangancin.

Bayan ta kamala ta fito hakanan haihuwar uwarta ga uban tumbi gaba kamar me tsohon ciki,
Hajiya Turai irin matannane wanda basu da fasala, gata masha Allah doguwa amma babu gaba bare baya sede uban tumbi daya tasota gaba.

Rungume Mamy tayi suka hau aikata masha'ar su ko kunya babu basa tsoron mutuwa ta riskesu cikin wannan yanayin tunda babu wanda yasan ranar mutuwarshi bare ya shirya mata.

Allah kasa muyi kyakkyawan 'karshe Allah kadauki raimu cikin kyakkyawan yanayi🙏😭Allah ka sanyaya makwancinmu Ka haska kaburvuran mu ka jikan iyayenmu kayi musu rahama🙏🙏🙏

ƙanin

🌹RAYUWAR SAMHAD 🌹( 𝒂𝒃𝒂𝒓 𝒕𝒂𝒖𝒔𝒂𝒚𝒊 𝒄𝒆😭)

𝑫𝑨𝑮𝑨 𝑨𝑳𝑲𝑨𝑳𝑨𝑴𝑰𝑵 🌹𝑴𝑨𝑹𝒀𝑨𝑴 𝑺𝑻𝑨𝑹✍️⭐⭐⭐🌹

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/K8VBORyiBdJCR61hLJ9Hq9

*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*

_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

🔴🌹🔴🌹🔴🌹🔴🌹🔴🌹
__________________________

بسم الله الرحمن الرحيم.

𝑷𝑨𝑮𝑬 6️⃣.

Barci tayi sosai don bata tashi se bayan gama sallah shima Habiba me aiki ce tazo ta buga mata kofa.

Tunda ta gama sallah wani barcin ya sake daukar ta annan inda tayi sallar, bata sake tashi ba se da rana ta fito shima ba don barcin ya isheta ba kawaide dan ta saba tashi a irin lokacin tayi aikace aikacen gida.

Hajiya Adama tsaye ta tasa abu gaba akan lallai seya gaya mata inda yakai Samhad, Tunda ya dawo gida ya zauna sukusu dashi ranar ko fita be sake yiba sede lokaci bayan lokaci yana kiran waya.

Zuba mashi ido kawai tayi tana kallonta ikon Allah.

Numfashi Abbu ya sauke tare da kiran cikakken sunan Hajiya Adama.

"Adama wallahi zuciyata ta kasa nutsuwa akan hukuncin da na yanke akan aurar da yarinyarnan, inaji a jikina kamar ban kyauta ba Abun yana damuna wallahi.

Shewa Hajiya Adama tayi tare da tafa hannuwa tace "yau ni naga idi zindir yanzu kai saboda wannan shashashar yarinyar kake wannan damuwar tun jiya nake kallonka ko Abincin kirki baka ciba, Imbanda abinka kaida zakayi farin cikin rabuwa da ita lafiya ba tare da ta janyo maka abun kunya ba, duk da naji mutanen unguwa suna fadin wai ana ganinta a wani kango ita da malamisu suna zagawa yanzu haka....

Be bari ta ƙarasa ba ya yatshi fuuuuu ya fice ya bar mata gidan.

"Mtswwww yaja tsaki tace maganinka kenan ai wajen shegen son abin duniya ka dauki diya ka bawa masu shan jini, waya sani ko har sun halaka ta sunyi tsafi da ƙashinta, su Zee ne suka shigo suna tambayar wai lafiya take surutu ita kadai.

"Inafa lafiya ubnku ne ya zo yana ta damuwa akan waccan kodaddiyar yarinyar wai hankalinshi be kwanta ba tunda suka tafi wai ba tada lafiya gashi tafiyar ta kasance ta gaggawa.

Tsaki Fauzeey tayi tace wai ku bazaku daina zancen waccan yarinyar ba ni wallahi haushi kuke bani akanta kuyita abu wanda be dace ba kubarta manah tayi rayuwarta itama tunda ba shiga harkar ku take ba.

Gum sukayi babu wanda ya sake cewa komai saboda kamar shakkarta sukeji idan tayi magana dole subi kamar itace uwarsu.

Janyo ledojin da ta shigo dasu tayi ta mik'awa Hajiya Adama daya ta fice da dayar tana amsa kira.
Dirarwa ledar Hajiya Adama tayi tana faɗin, Allah sarki yarinyar kirki niko gaskiya na ƙagu wannan Alhajin ya fito ko ayi aren nan nadena ganinki haka a gabana.

Tsuke fuska Zee tayi tana faɗin waike hajiya se kiyita cewa kingaji da ganinmu mi muka tsare maki ne wai haka?

"Baku tsaremin komai ba Ammade idan kukayi aure ai na huta da ɗumim jama.a dake cewa kun tsofe kunki auruwa.

ABUJA NIGERIA
MAITAMA
Chapter 2 · 0% Book details