Sashe 4
Rayuwar Samhat Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ɗayan sashen zuciyar tane yake tambayar ta wai mi Mamy take nufi ɗazu? taga sanda tayi wani makirin murmushi da kuma sanda ta ɗagawa Mubeen hannu tai mashi wata alama wanda ba kowa ya fahimta ba....
tunanita ne ya katse jin tana neman faɗuwa daga tsayen da take rungume da Mubeen da zuwa yanzu sautin kukanshi yafara fitowa.
cikin rawar jiki tafara ja baya hankali har ta dangane da jikin gadon dake dakin.
Cikin dabara ta lallaɓa da nufin ta zauna amma takasa saboda ya sakar mata dukkan nauyinsa.
A ƙoƙarinta na zama ƙafarta ta zame baya ba shiri suka faɗa kan kagon atare.
runtse ido tayi jin yanda ya sake matse ta ajikinshi kamar ƙaramin yaron da beson uwarsa ba tashi ta barshi.
jin hawayen nasa munƙi tsayawa ya sanyata zame hannunsa da ya riƙeta tashi ahankali.
Bayan tayi nasarar ɓamɓareshi daga riƙon da yayi mata ahankali ta janye jikinta daga nasa amma ba dukaba.
Tallabo fukarshi tayi ta siraran hannayenta tashiga share mashi hawayen da ke gudana daga idanuwansa kamar ambude famfo.
Dafa kanshi tayi ta na kallon jijiyoyin da sukayi raɗo-raɗo a gaban goshin, addu,oi ta shiga karanto wa ta na shafa mashi.
kwanciya ya sake gyarawa a jikinta yana jin wata nutsuwa na safko masa a cikin barcin.
kallonshi take tana yaba kyawun da tsarin hallitar fuskar ta, a zuciya ta ke faɗin wai dama rayuwar duniya haka take? ko wa da irin ƙalubalenda, ga misali nan tana kallo babba dashi yana kuka akan rayuwa, kenan ba kuɗi bane jindaɗin rayuwa? kenan ahali ba sune farin ciki ba?.
"Ya Allah ka dubi rayuwar mu ni da wannan bawan naka, Allah ka bamu ikon fuskantar ƙaddararmu, Allah ka bashi juriya akan rayuwa, Allah ka sassauta mashi raɗaɗin da yake cikin zuciyarshi ALLAHUMMA AMEEN."
Tana kammala addu,ar taɗan janye jikinta da ga nashi ta kwantar da kanshi akan cinyar ta tajingina da filo yana lumshe ido alamar barci.
ahankali nannauyan barci yayi awon gaba da ita.
Daddy ne ya tashi daga kan dinning ɗin cikin sanyi jiki, kwata-kwata baya son abin da Mubeen keyi, shi yanzu abin da yasa ya kasa nutsuwa be wuce yanda ya ɗauki yarinyar mutane ya fita da ita ba.
Alhaji ka daina damuwa akan lamarin wannan yaron tun da kasan halinshi, ka kyaleshi kawai bade matarshi bace kuma ya ɗauka, to suje can su ƙarata.
Ficewa Daddy yayi daga sashen ba tare da yabi ta kan maganar da Mammy ke yiba.
Sashen Mubeen ya nufa dan zuciyarshi tunzura shi take akan yaje ya dawo da Samhad kar Mubeen ya cutar da yarinyar mutane tunda yasan halinshi da baƙar zuciya kamar kuturu.
Yana isa ya tarar da ƙofar parlon abude, aiko zuciyarshi ta doka da mugun ƙarfi,dan har ya fara hasaso ya riga da ya cutar da Samhad.
ƙofar bed room ɗin da suke ya buɗe,
turus yayi yana kallon ikon Allah, dan abune da bai taɓa faruwa ba.
murza idomshi ya sakeyi dan ya tabbatar da gaske Mubeen ne ke barci haka cikin nutsuwa ba tare da ya sha abinda ya shaba.
Muneeb ne yau kwance a gado kamar kowa yana barci cikin nutsuwa babu surutai kuma babu warin aman giya ko kwalbar magani.
Hawaye ne suka gangaro idon Daddy, saurin fita yayi yana jinjina girman ikon Allah, dama ance aure na nutsar da mutum tabbas wannan gaskiya ne tunda ga sheda ya fara gani wajen Muneeb aure duka kwana biyu matar da ko tare wa batayi ba amma harta fara nitsar dashi.
Godiya yayiwa Allah tare da yima Mubeen dan Samhad addu,ar zaman lafiya da haɗin kai harda zuri,a ɗayyiba.
Yana tafiya ya na sakin murmushi kamar ba shiba har ya iso part ɗinsa....
𝑫𝑨𝑮𝑨 𝑨𝑳𝑲𝑨𝑳𝑨𝑴𝑰𝑵 𝑴𝑨𝑹𝒀𝑨𝑴 𝑺𝑻𝑨𝑹✍️⭐⭐⭐
𝑳𝑰𝑻𝑻𝑨𝑭𝑰𝑵 𝑹𝑨𝒀𝑼𝑾𝑨𝑹 𝑺𝑨𝑴𝑯𝑨𝑫 𝑵𝑨 𝑲𝑼𝑫𝑰 𝑵𝑬 𝒁𝑨𝑲𝑰 𝑩𝑰𝒀𝑨 200 𝑲𝑨𝑪𝑨𝑳 𝑲𝑰 𝑴𝑨𝑳𝑳𝑨𝑲𝑰 𝑳𝑰𝑻𝑻𝑨𝑭𝑰𝑵.
𝑨𝑪𝑪𝑶𝑼𝑵𝑻 𝑵𝑼𝑴𝑩𝑬𝑹
9136291920
𝑴𝑨𝑹𝒀𝑨𝑴 𝑼𝑴𝑨𝑹
𝑶𝑷𝑨𝒀.
🌹RAYUWAR SAMHAD 🌹( abar tausayi ce 😭)
DAGA ALKALAMIN MARYAM STAR✍🏻�⭐⭐⭐
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GMLNwj2j2i9Kh8AsHDRpMf
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
Page 1️⃣6️⃣⭐1️⃣7️⃣
___________________________________________________________________________
بسم الله الرحمن الرحيم.
Mamy tunda ta je office ta ɗauki abinda ya kaita ta kamo hanyar hotel ɗin da Hajiya turai ta kamamasu.
Tunda ta isa suke aikata masha,arsu babu ko kunyar ubangiji.
Basu dawo dai-dai ba sai bayan la,asar Sanna suka fara tattaunawa akan abinda ya kawosu.
Bayani Hajiya turai ttayiwa Mamy akan maganin da ta amso mata wajen bokansu da bisa tsauni,
"Aminiya kinga wannan idan kikayi amfani dashi sai kinyi min babbar sallama saboda saida Malam ya tabbatar min da babu makarinshi annan kusa, Barima in taƙaice maki zance lokacin barin yaron cikin rayuwarku yayi dan Malam yace muddi aka zubawa Uban cikin abinci yaci kamar yanda yaci abincin ya haɗe cikin ciki haka ƙauna da tausayin da ya ke wa yaron zasu fice daga ranshi, daga nan komai zai iya faruwa".
Tafawa sukayi cikin jin daɗi Mamy tace Babban abinda zai mani shamaki da cikar burina zan kawar dashi, lode innunawa Aisha nafi ƙarfinta akan komai dole ta yadda da cewa dukiyar Alhaji Muhammad Ƙarfe tawace ni kaɗai nasan wannan saƙon nawa zai risketa har cikin kabarinta" ta yi maganar ta na ɓaɓɓka irin dariyar bosawa.
Jinjina kai Hajiya Turai tayi tana mamakin saanin ta kan mugunta da Mamy tayi, Idan baza ta manta ba farkon haɗuwarsu wajen wani boka ne da taje amso asirin da ta ke amfani da shi tana yima manyan mata sata ba tare da an gane ta ba.
TUNA BAYA WACECE MAMY؟.
Sarhabila Umar shi ne asalin sunanta, ƴar asalin jahar sokoto ce Babanta Umar mutum ne mai rufin asiri dan buƙatun gidansa basu fi ƙarfisa ba, amma Allah ya jarabceshi da samun mata marar godiyar Allah komi yayi mata bata godeyi saima kushe abun da zata dingayi a gbanshi.
Umar mutum ne marar son hayaniya da tashin hankali sai dai Allah ya jabceshi da samun ƴaƴa masu irin halin uwarsu dan kaf cikin ƴaƴanshi ɗayace kawai ta biyu halinshi wato Nabila ɗiyarshi ta biyu.
Sarhabila sam bata da kunya ko kaɗan duk girman mutum baya hana ta gaya masa magana idan ya shiga gonarta.
Aisha ƙawar Nabila ce wadda suke bayan gidansu Sarhabila, bakin gwargwado mahaifin Aisha Alhaji Ahmad yanada rufin asiri dan yafi Umar samu sosai kasance warshi ɗan kasuwa.
Kullum tare da Aisha Nabila ke zuwa makarantar Islamiya kuma su dawo tare, da yake ajinsu ɗaya duk randa aka basu assigment a tare sukeyi a gidan su Nabila, idan Aisha ta zo gidan sarhabila ta kama zage-zage da harare-harare kenan tanajan tsaki tana ce wa, haka kawai Nabila ta kwso masu me kama da zabiya ta kawo masu cikin gida.
Sarhabila nada matuƙar kishi musamman ace taga wanda ya fita wani abu to ranar anshiga uku dan mita zataitayi tana jan tsaki.
Aisha yarinya ce nitsatstsiya sam ba ta da hayaniya gata shiru-shiru, Aisha farace Sol ga ta da diri ga dogon hanci da ƙaramin baki.
Aisha tana da kyau sosai shiyasa Sarhabila ta tsaneta sosai.
A wata rana Sarhabila ta tashi da sha,awar zuwa makaranta tunda safe ta ɗauko uniform ta wanke ta goge tana jiran lokaci yayi.
Ba komai ya sa take son zuwa makarantar ba sai dan tayi waya da ƙawarta Sajida zata kawo mata wani sabon man bleching.
Tunda akayi sallar la,asar Aisha ta biyowa nabila dan su tafi makara, tare suka fito da Salhabila dake ta ɗauke kai gefe tana yamutsu fuska.
Suna tafiya Sarhabila ta lura da wata jibgegiyar mota da ke bin bayansu, mamaki ne ya kamata ganin su motar ke bi yasa tace.
"Nabila kuzo mubi ta wancan layin zan amshi saƙo".
Bimta sukayi suna tafe ta na jansu da fira abinda bata saba yi ba idan Aisha na waje.
Cikin dabara take kallon motar tana gasgata lallai binsu take.
Har suka iso makaranta ba,a daina binsu ba Wanda hakan ya bawa Sarhabila mamaki sosai.
Shiga sukayi cikin makarantar kowa ya nufi aji, cikin jindadin kulatan da Sarhabila ta yi tace wa Nabila.
" Wallahi yau naji daɗin kulawar da Yaya bila tayi mani sosai Allah yasa ta ɗaure a haka nima kinga nayi Yaya kamar kowa".
Murmushi kawai Nabila tayi bata ce komai ba suka nufi wajenda suka saba zama.
Bayan antashi Sarhabila ta sake ganin wannan motar tana binsu hakan yasa tayi dabarar jan Aisha da fira wai tazo suje gidansu zatayi mata kitso idan an gama sallah sai su rakata gida.
Amsawa tayi tanajin daɗi sosai yanda yau Yayar ƙawarta ta sake da ita.
Ita kuwa Beela dabarace tayi wai kar su rabu me motar yabi bayan Aisha.
Suna zuwa unguwarsu motar ta tsaya dai-dai wajen masallacin da kekusa da gidan su Beelah.
Zaune suke suna ta fira abisu ganin shiru ba'a biyo bayansu anyi sallama ya sa Sarhabila tace.
"Ki tashi mu raka ki kar dare yayi"
Ansawa Aisha tayi da to tare da yiwa Ummunsu Beelah sallaha suka tashi dan rakata.
Cin karo sukayi da yaro zai shigo, ganinsu yasa yafaɗi saƙon kai tsaye yace.
"Wani me mota ya ce ana Sallama da Aisha ƙawar Nabila."
Ras gaban Beelah da Aisha ya buga a tare.
Nabila ce tace "kace gatanan"
Amsawa yayi da to ta re da tafiya abinsa.
Jan hannun Aisha ta yi suka fice suka bar Beela tsaye saboda tsabar takaici da hassada har idonta ya kawo ruwa a zuciya take faɗin.
'yanzu duk abinda nayi ya tashina banza saida yabiyo ƴar iskar yarinyarnan' fuuuu ta wuce cikin gida tana goge kwallar data zubo mata.
Matashin saurayi ne da bazai wuce shekaru talatin ba jingine jikin wata arniyar mota yana sakar musu murmushi tunda suka fito.
Sai da su kaje gab da shi kafin Nabila ta saki hannun Aisha da ta sunkuyar da kai tun zuwansu wajen.
Gaisawa suka yi da Nabila har yana ɗan tsokanarta, da ya ke tafi Aisha sauri sabo dandannan suka saba har tana mai da mashi idan yana tsokanarta.