← Book details Rayuwar Samhat Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 13

Sashe 11

Rayuwar Samhat Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

𝑲𝒂𝒓𝒌𝒊 𝒎𝒂𝒏𝒕𝒂 𝑹𝑨𝒀𝑼𝑾𝑨𝑹 𝑺𝑨𝑴𝑯𝑨𝑫 𝒍𝒊𝒕𝒕𝒂𝒇𝒊𝒏 𝒌𝒖𝒅𝒊𝒏𝒆 𝒛𝒂𝒌𝒊 𝒃𝒊𝒚𝒂 400 𝒌𝒂𝒄𝒂𝒍 𝒅𝒐𝒏 𝒎𝒂𝒍𝒍𝒂𝒌𝒂𝒓 𝒍𝒊𝒕𝒕𝒂𝒇𝒊𝒏.

9136291920
𝑴𝒂𝒓𝒚𝒂𝒎 𝒖𝒎𝒂𝒓
𝑶𝒑𝒂𝒚

𝑫𝒂𝒈𝒂 𝒂𝒍𝒌𝒂𝒍𝒂𝒎𝒊𝒏✍️
𝑴𝒂𝒓𝒚𝒂𝒎 𝒔𝒕𝒂𝒓⭐⭐⭐(𝒚𝒂𝒓 𝒃𝒂𝒊𝒘𝒂𝒓 𝒋𝒋𝒊𝒓𝒕𝒂𝒕𝒕𝒖💪🌹).

🌹RAYUWAR SAMHAD 🌹(Abar tausayi ce😭)

DAGA ALƘALAMIN✍️
MARYAM STAR⭐⭐⭐(ƳAR BAIWAR JAJITATTU💪)

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JtdcdPFJlH667ebLi4R0jN

*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*

_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

Typing....

PAGE 3️⃣9️⃣

___________________________________________________________________________

بسم الله الرحمن الرحيم.

Cikin zafi-zafi ya ke yamutse ilahirin sassan jikin Samhad, sai da ya gama rikitata shima ya rikita kansa baiji bai gani, sai da tafiya tai nisa Samhad ta sallamawa Mubeen ragamar rayuwarta kawai Mubeen ya tsaya cak tare da mirginawa gefe ya na sauke numfashi tare da dafe mararsa da ke bijiromai da wani irin azababben ciwo da buƙatuwar san kasancewa da mahaɗin halittarsa.

Lumshe shanyayun idanuwanta tayi ta na byɗewa a hankali jin yanda ilahirin jikinta ya mutu murus sai tsigar jikinta da ke miƙewa wani sassanyan iska mai rura wutar buƙatuwar mijinta ke shiga cikin ɓargo da jinin da ke gudana a sassan jijiyoyin jikinta.

Sauke numfashi tayi tare da yunƙurawa ta tashi zaune amma me؟ fafur ƙafafuwanta suka bijire wajen ɗaukar gangar jikinta, jin zata faɗi ya saka ta koma ta zauna ta na sake ƙanƙame zanin gadon da ta suturta jikinta dashi.

Ta daɗe a zaune ta na mai da numfashi kamin ta lallaɓa a hankali ta tashi a duduƙe ta nufi toilet ta sakarwa kanta sanyayen ruwa dan ragewa kanta abinda ta ke ji.

Duk abinda Samhad ke yi Mubeen na ankare da ita azahiri yayi biris kamar mai barci amma a baɗini tsananin buƙatarta da tausayinta ke nuƙurƙusar zuciyarsa, numfashi ya sauke lokacida ta shiga toilet ya miƙe cikin dauriyar yanayinda ya ke ji ya bi bayanta.

Tsaye take sassanyan ruwa na bin jikinta tun daga tsakiyar kanta har kafafuwanta, ɗif wutar kanta ta ɗauke tare da bugun zuciyarta na wucin gadi dan batayi zato ko tsammani ba kawai taji anyi wuff da ita an ajiye a cikin ruwa masu gumi wanda ke tashin ƙamshi, buɗe idon da zatayi taga Mubeen na sakar mata wani kasalallen kallo mai kashe kuzarin jiki.

Tsit tayi kamar ruwa ya cinye ta dan ita ƙaɗai tasan yanayin da gangar jiki da ruhinta su ke ciki.

Wani munafuki murmushi Mubeen ya dake ganin yanda garasar jikin Samhad ke miƙewa ta na ƙara ƙanƙame jikinta a cikin bahon wankan a zuciya ya furta 'eh lallai za'aje da ke ƴammatana wannan irin karɓar saƙo haka da sauri ummmm gaskiya'.

Ita kuwa Samhad a zuciya ta ke faɗin 'na shiga uku wannan mutumin yanason ya kasheni ba tare da lokacina yayiba miyasa bazai gane ina tsananin jin kunyarsa ba, ji yanda ya wani tasa ni gaba yana kallo kamar ƙaramar yarinya.'

A zahiri kuma rawa jikinta keta faman yi kyaf-kyaf kamar mai jin sanyi wanda hakan yasaka mubeen yake kallonta yana fassara abin da wata manufa ta daban.

Sunkai minti ashirin a cikin bahon a tsugunne ganin zaman ba mai yuyuwa bane ya sanya Mubeen ya wanke Samha tas kamar wata ƴar Baby, da farko ta saka gardama ganin yanda yake wani wanketa amm daga baya ganin ko a jikinsa ya sanya ta runtse ido ta barshi yayi yanda yakeso.

Tas ya wanke ta shima ya wanke kanshi kamin ya naɗota a karamin towel shikuma ya ɗaura babban suka fito, a wajen shirima shi yayi mata sannan ya shirya kansa ya hau kan bed ya rungumeta jikinsa yanajin tsananin buƙatarta amma ya maze, waayarshi ya ɗauko a bed site ya kira number Sadeek dan jin halinda ake ciki akan jikin Daddy.

Ɗaukar wayar Sadeek yayi cikin magagin barci yace "helo Yaya mi kake har wannan lokcin bakayi barci ba na faɗa maka jikin Daddy yayi sauƙi tun dazu da kabarmu ya ke barci har yanzu bai farka ba".
Ajiyar zuciya ya sauke tare da kashe wayar ya aje ya sake tusa kanshi a jikin Samhad ya na shaƙar ƙamshin jikinta da ke sake rikitashi.

Sundaɗe idonsu biyu babu kafin barci ɓarawo yayi gaba da Samhad, shima Mubeen bai daɗeba nannauyan barci me cike da tarin mafarkai yana shan love tare da Samhad.

Mamyce ta fito da ga toilet cikin zullumi dan kuwa har yanzu Hajiya Turai bata ɗaga wayar ba, sake kira tayi amma still ba'a daga ba wani irin tashin hankali ya sake ɗimauta ta dan garaɗin da Hajiya Turai tai mata akan maganin sai amsa kuwwa ya ke mata " Masoyiya kikula sosai dan wannan bokan aikinsa kamar yankan wuƙa ne sha yanzu magani yanzu kuma ba'a wasa da maganinsa dan mafi yawa idan akai sakaci ƙaiƙayi ke komawa kan masheƙiya" . murmushi Mamy ta yi tare da cewa ai baki da matsala indai nice ba wasa karki manta tun ina budurwa nake aikin bin malamai da boƙaye kinga ko ai nasan takan komai dan ita kanta matsalar tsorona take bare ta fuskance ni muyi gaba da gaba da ita".

Miƙa mata hannu Hajiya turai tayi suka tafa tare da sakin shewa a zuciya kuwa Hajiya Turai ce ke faɗin ' lallai dole intashe tsaye akan wannan hatsabibiyar matar dan kuwa so take ta zame min ƙadangaren bakin tulu amma nasan abinda zanyi dan kuwa dole a dama da ni cikin harkarnan'.

Hannu Mamy ta ɗora aka lokacinda maganar Hajiya Turai ta dawo mata dan kuwa ta tabbata akwai gagarumar matsala idan batayi gaugawar saduwa da Hajiya Turai ta sanar mata da matsalarnan ba, key ɗin mota ta janyo tare da ɗaukar mayafi ta fice ta nufi parkin lot harta tada mota kawai ta tuna da ba,a barin fita cikin dare a unguwar da suke sai idan abu emergency ne dannan kuma ba'a barin mata su tuƙa kansu idan marice yayi bare ace dare dan unguwar ta shahararun ɗan siyasa da masu kuɗice, wani irin kuka ta saki ta mai ƙarfin gaske dan kuwa tako ina babu mafita dama Hajiya Tura ce kaɗai hope ɗinta gashi itama bata ɗaukar wayar dan tsabar kiran da take jerawa wani nabin wani ya sanya wayar ta buga low battery.

DAGA ALƘALAMIN✍️✍️
MARYAM STAR⭐⭐(ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU💪🌹).

🌹RAYUWAR SAMHAD 🌹(Abar tausayi ce 😭)

DAGA ALKALAMIN ✍️✍️
MARYAM STAR⭐⭐⭐
(YAR BAIWAR JAJIRTATTU💪🌹).

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

Typing....

PAGE 4️⃣0️⃣
___________________________________________________________________________

بسم الله الرحمن الرحيم.

Wata irin hajijiyace ta ɗauki Mamy dake tafiya ta na tangaɗi, kamin tayi wani yunkuri ji kake rica ta faɗi akan flower da ke wajen, so take take ta tashi amma ta kasa saboda ba ƙaramar buguwa ƙafarta ta haggu tayi ba.

Daddy bai farka ba sai da asuba Alhamdulillah ya tashi lafiya sam bayajin ciwon komai sai dai matsananciyar damuwa da ya farka da ita da kuma kewar mutuwar Aisha da ta dawo mishi sabuwa dan asirin da Mamy tayi mishi da yawa sun karye dan ƙa'idar bokan idan aka samu matsala to har aikin da akayi a baya karyewa ya ke.

Zafafan hawaye ya share ya na jin nadamar cin amanar da ya yiwa Aisha na nuƙurƙusar zuciyarsa, sai yanzu wasu hotuna ke haskowa a kanshi ranar da Aisha ta muku tabbas yaga Beela kuma ta firgita da ganinsa a lokacin sanda ya shiga ran Aisha ya bar jikinta amma hannunta na nuna Beela da ke riƙe da Salma to wai mi hakan ke nufi? ba shida mai bashi wannan amsar sai Beela da kuma Mubeen to amma kuma ai Mubeen ya na kwance a ƙasa a sume baya ko lumfashin kirki, kai dole akwai alamar tambaya a wannan lamarin'.

Badan ya so ba ya tashi ya nufi toilet dan kansa har ya fara sara masa akan tunanin da yake so ya zurfafa kansa.

Bayan yayo alwala ya fito ya tsaya yana ƙarewa Sadeek kallo wasu zafafan hawaye na sake sulalowa a idonsa na tausayin kanshi da ƴaƴanshi dan haƙiƙa ya cutar da su dan wata kalar bahaguwar rayuwa suke gudanarwa sam baya da lokacin yaranshi bai taɓa tsayawa ya saurari matsalarsu ba tun Salma na shige mashi harta gaji ta daina dan ba kulata yake ba musamman idan Mamy na wajen ta dinga mita kenan wai ƴaƴa babu lissafi daga dawowarshi zasu fara takurashi ko hutawa baiyiba suna ji suna gani suke haƙura su tafi.
Wata zazzafar ƙaunar ƴaƴan nashi ce ta bijiro masa dan sam bai kyauta musu ba kuma yasan suna da maraicin uwa dan ma Mubeen da yake babba kuma wanda yasan mi yake ya tsaya musu akan harkokin rayuwa na yau da kullum.

Sadeek ne ya buɗe ido ya ga Daddy tsaye ya kafeshi da ido yana zubarda hawaye, cikin sauri ya tashi zaune ya buɗe baki zaiyi magana amma sai yaji Daddyn ya jawoshi ya rungume tsam a jikinsa yana shafa kansa ya na zubda hawaye.

Wani irin nauyi zuciyar Sadeek ta yi dan tunda ya tashi da wayonsa bai taɓa ganin wani daga cikin ɗan uwansa ya raɓi Daddy har haka ba, shima kukan ya saki wiwi kamar ƙaramin yaro sun daɗe a haka suna ta rizgar uban kuka kamin daga baya Daddyn ya rarrashi Sadeek yaje yayo alwala suka tafi masallaci a tare hannuwansu a cikin na juna.

Wani irin farin ciki ne babaye a zuciyar Sadeek dan kuwa bai taɓa samun wannan kulawar a wajen Mahaifin nasuba sai yau.

DAGA ALKALAMIN✍️

Maryam star⭐⭐ (yar baiwar jajirtattu💪🌹).

🌹RAYUWAR SAMHAD 🌹(Abar tausayi ce😭)

DAGA ALKALAMIN ✍️
MARYAM STAR⭐⭐⭐
('YAR BAIWAR JAJIRTATTU💪🌹).

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GhuhVAo9XfoAsdj82FOnmC

*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

Typing....

Page 4️⃣1️⃣

________________________________________________________________________

بسم الله الرحمن الرحيم.
Chapter 11 · 0% Book details