Sashe 1
Rayuwar Samhat Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*🌹RAYUWAR SAMHAD🌹*
DAGA ALƘALAMIN MARYAM STAR✍🏻
⭐⭐⭐
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/K8VBORyiBdJCR61hLJ9Hq9
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mi id=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
𝑷𝑨𝑮𝑬1️⃣
_________________________________
بسم الله الرحمن الرحيم.
Tsaye suke a kanta suna ta sheƙa dariya, ɗayar budurwar wadda take kusa da ita ta fara magana cikin dariya. "Ke yanzu baki da sauran amfani, a haka za ki ka ƙare rayuwarki a auren dan daba wanda ya addabi kowa, waya sani ma ko can wajen yawon iskancin da kika saba kuka hadu har ya biyo ki gida, mu de wallahi an cucemu ambata wa gidan mu suna, Allah kaɗai ya san in da abun kunyar da kika aikata yaje"
" Nifa ba ma wannan ba Zee waifa Abba har wani fankama da tunkaho yake ya aurar da wannan borar. " Haka su ka saka ta a gaba suna ta ci mata mutunci, Duƙar da kanta ta yi ta na zubda hawaye masu zafi, A zuciyarta take cewa wannan wace kalar rayuwa ce? bata jin daɗi a wajen kowa ba ta da me sonta, babu wanda ya damu da ita, mai yasa Mahaifinta ze zama cikin masu yiwa rayuwarta illa, ta gaji da wannan rayuwar wadda babu komai acikinta sai bakin ciki da mutane masu son zuciya.
Ɗago da kanta tayi jin abin da zee ke faɗa. "Samhad ke da jin daɗin duniya har abada, sai dai ki gani awajen wasu ki dauki wannan aure a matsayin 'kaddarar da za ta sadaki da mutuwa, gidan da za ki shiga ki 'dauƙe shi kamar kabari, don wallahi ina tabbatar miki daga yau ko in ce daga yanzu Kin yi bankwana da farin ciki sai dai kiga wasu nayi ba dai ke ba."
Ta 'karashe maganar tana jefawa Samhad kallon tsana. Girgiza kai Samhad tayi cikin sheshshekar kuka tace "Nayi imani da ubangijina babu me kashewa ko rayawa sai shi, kuma dukan wani abu da zai sameni nayi imani daga shi ne, Anty Zee na riga na miƙa al,amarina a wajen Allah na san Allah yana sona tun da har yayoni mace kuma musulma, bari in tuna miki wani abu shi aure nufin Allah ne idan Allah ya nufeka da yin shi babu makawa sai kayi, wannan misali ne da ke, batun yanzu na san kina son kiyi aure ba na san ki na da buk'atar aure tun shekarun baya amma Allah be nufa kin yi ba, kin sha gorantamin cewa babu wanda ze aureni ahaka zan k'are rayuwata, kimmanta Allah shine ya ke tsara al,amurransa. Alhamdulillahi ko a haka aka tsaya naci riba dan na san na riga nayi gaba na barki a baya 'yar gata diyar so" ta karashe maganar tana sakarwa Zee murmurshi wanda ya sanya zuciyar Zee bugawa da k'arfin gaske.
Kallon Zee Haneefa tayi tare da jan hanninta su kai waje, fitarsu babu jimawa Samhad ta fashe da matsanancin kuka wanda jikinta har girgiza yake tsabar kukan, A hankali takai hannunta wajen wani photo tana shafa kuskar wacce ke cikin photon tana murmurshi kamar za,a kirata ta amsa.
"Ummanah farin cikina Ina kaunarki dan Allah ki dawo gareni ba zan iya jure rashin ki ba, rayuwar ta isheni haka nan wai kin san mai Abbu ya yi min? Auren dole Tatum in kuma auren cuta, Abbu ya cutar da rayuwata ba zan iya jure wannan zaluncinba, Ummana kin san mai yayi d'an daba ya auramin kuma bada amincewata ba, na san ke ma ki na jin kwatan kwacin Abin da na ke ji, Ummana zuciyata ciwo take kaina tarwatsewa zai yi in mutu ko na samu salama, Ummanah Ina son in zo lahira in zauna tare da ke, Ina son in yi rayuwa kamar ko wace 'ya a gaban mahaifiyarta."
Kukane me matsanancin karfi ya kwace mata nan take ta fadi awajen kamar matatta bata Numfashi, saurin shigowa Abbu dake bakin kofa yayi saurin shigowa jimfaduwarta, jijjigata ya shiga yi yana zubar hawaye yace "Kar kiyi mani haka diyar Albarka, karki mutu kibarni wallahi Ina sonki wannan shine kadai gatan da zanyi miki ba zan cutar da keba, dan Allah ki tashi shalele "
Jin sauti muryar Abbu yasa mutanen gidan fitowa suna ganewa idansu abin da ke faruwa,
Hajiya Adama ce ta shigo tare da tsayawa akan Abbu dake kuka tace "kai kuma lafiya ka zauna kana uban kuka sai kace karamin yaro? "
Bai tsaya saurarenta ba ya saɓi Samhad tare da fice wa yana zubda hawaye.
𝑨𝑩𝑼𝑱𝑨 𝑵𝑰𝑮𝑬𝑹𝑰𝑨
𝑴𝑨𝑰𝑻𝑨𝑴𝑨.
Wata arniyar farar motace ta fito daga wani arnen hadadden gida, taka motar yake damatsiyacin gudu kamar wanda zai tashi sama. Gudu yake bana wasaba harseda ya isa in da yake son zuwa.
A firgice ya bude motar ya fito daga motar doguwar sumar kanshi me kama da ta larabawa dukta hargitse, manyan idanuwanshi duk sunyi jah kamar gauta, hannu ya sanya a Cikin aljihunshi ya fiddo dalleliyar wayarsa yashiga laluben wata number.
"Saniga please gani na zo har in da kake dan Allah ka zo ka bani sak'on wallahi ba zan iya nutsuwa ba idan ban sha ba kaina tarwatsewa ze yi" daga can cikin wayar akayi magana wanda ni dai ban san me,a ka ce ba se jinayi yace, "No SaNIGA ba zan iyaba wallahi dole kasamomin abunnan ko kuma ka kaini in da zan samo" Dafe kanshi yayi tare da jefar da wayar ya bude motar yaja yabaɗe wajen da k'ura yayi gaba da mugun gudu.
𝑫𝑨𝑮𝑨 𝑨𝑳𝑲𝑨𝑳𝑨𝑴𝑰𝑵 𝑴𝑨𝑹𝒀𝑨𝑴 𝑺𝑻𝑨𝑹✍️⭐⭐⭐
🌹RAYUWAR SAMHAD 🌹( 𝑨𝒃𝒂𝒓 𝒕𝒂𝒖𝒔𝒂𝒚𝒊𝒄𝒆) 🥹
DAGA ALKALAMIN MARYAM UMAR STER⭐⭐⭐🌹

*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v

PAGE 2️⃣
_________________________________
بسم الله الرحمن الرحيم.
Tun bayan barin shi wajen ya samu gefen hanya yayi parking tare da dora kanshi a sitiyari, zafi zuciyarsa ke masa baya jin dadin komai, cikin matsananciyar damuwa ya runtse jajayen idanuwansa da k'arfi ya na tuna yanda rayuwa ta juya masa baya, har yanzu yana mamakin yanda farin ciki yayi k'aura a cikin rayuwarsa, idan dukiyace farin ciki yana da ita wacce har nanda shekaru masu tarin yawa ahalinsa zasu amfana da ita, amma miyasa yakasa samun cikakken farin ciki arayuwarsa? Kode yayi wani babban zunubi wanda be sani ba Allah yake hukunta shi ta wannan hanyar??? Ya rasa waze raba yaji dadi komai ya kwance masa. Daga hannu yayi sama yana addu,a cikin zubar hawaye da karayar zuciya.
"Ya Allah idan wani laifi nayi maka abisa kuskure ka yafemin na tuba, Allah na tuba ka gafartamin, ya Allah idan mutuwa hutu ce a gareni Allah kadauki raina kozan huta, Allah nayi iymani da kaddara me kyau da marar kyau Allah ka saukakamin wahalar rayuwa. "
Yadade yana zubda hawaye kamin daga bisani ya tada motar ya cigaba da tafiya cikin matsanancin gudu, mutane da basu gani su kyale duk inda ya gifta se anyi maganar gudun da yake shararawa, wasu suce "Allah ya shirya wasu kuma su zageshi suna me Allah wadai, wadanda sukasan mahaifiyarsa suce yaron Alhaji Muhammad k'arfe ne yafito yana wulakanci saboda ya nuna shidin wani ne, Kasancewar Mahaifinsa sanannen mutum ne kuma duk motocin gidan nasu suna da tambarin M k'arfe a jiki.
Kuka sosai Abbu keyi sadda suka isa asibitin dake kusa dasu. Allah yaso sanda ya fito da Samhad ma'kocinshi Mamman driver ya ganshi, dawowarshi kenan daga aiki ya hango Abbu yana kuka yana tsaida motocin dake wucewa wajen, saurin karasawa Mamman yayi inda Abbu yake, be jira komai ba ya bude mishi motar yana kama mashi Samhad da zuwa lokacin numfashinta ya fara dawowa amma sama-sma, suna isa asibitin dake kusa dasu aka amshi Samhad tareda bata temakon gaggawa.
Bayan an samu andidaita numfashinta aka saka mata ruwa tare da allurai.
Likitanne ya fito tare da kallon Abbu dake ta safa da marwa cikin tsananin damuwa yace "Baba muje office se muyi magana".
Saurin binshi Abbu yayi yana zullumin jin abinda likitan zace yana faruwa da Samhad.
Bayan sunshiga ya nunawa Abbu kujera yace ya zauna, Bayan ya zauna suka gaisa sama-sama Abbu yace "likita ya jikin Samha? Tade tashi ko? " yayi maganar yana zubawa Dr idanuwa yana jiran jin abinda ze ce. Saita nutsuwarshi yayi tareda kallon Abbu cikin sanin makamar aiki yace.
"Alhmdllh tana cikin koshin lafiya a yanzu haka, Allah yasa kunyi gaugawar kawota asibiti da wuri, a halin da ake ciki yanzu tana barci sede jininta ya hau sosai Amma yanzu Alhmdllh munyi mata duk abinda ya dace sede inaso inyi maka wasu 'yan tambayoyi"
Gwauron numfashi Abbu ya sauke yanajin kaso ashirin cikin Dari na zullumin da yake ciki ya kau. Saide haryanzu hankalinshi be kwanta ba tunda be ga halinda Samhad take ciki ba.
"Ina jinka doctor kayi tambayoyinka".
"Baba duba da yanda naga kammaninka da marar lafiyar nasan cewa dole cikin biyo seya zama gaskiya
A yanda naganka kuna kama sosai ga dukan Alamu kaine Mahaifinta ko kuma wani makusancinta na jini".
"Tabbas 'yata ce, ni na haife ta."
Masha Allah, Amma baba miyasa kukayi sake da lafiyarta?
A gwaje-gwajen da mukayi mata mun gane tana dauke da hawan jini kuma da alama bata samun kulawa akan hakan?
Numfashi Abbu ya sauke yace wallahi doctor ni kaina bansan yanda akayi nakeyin sake da al,amarin yarinyarba gata yarinya me hankali da nutsuwa, ga biyayya da kawaici. Amma duda haka nakasa tsayawa akan lamuranta. Insha Allah A wannan karon nasan nakaita hanya me billewa don kuwa nayi mata garkuwa wacce zata kareta daga ko wane irin farmaki, Samhad baiwar Allah Insha Allah daga yau ta gama zubar da hawayen damuwa, maraici, da bakin ciki sede na alfahari da farin ciki.
Shiru Dr yayi yana kallon Abbu dake magana yana zubda hawaye kuma yana murmushi duk a lokaci daya.
Bayan sun karashe tattaunawa Dr yabada shawarwari yanda za,a kula da ita.
Wai nikam baza,a iya sallamarta yanzu ba doctor? Cewar Abbu yana duba agogon hannunsa.
Muna jiran ta farka ne muga yanayinta sannan idan da yuyuwar a sallameta zamu sallameta insha Allah.