← Book details Rashin Jini Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 7

Sashe 7

Rashin Jini Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

```Gamasu buk'atar A tallata musu hajjarsu k'ofa bud'e take zaku iya Aiko tallanku A rubuce nasaka muku cikin shafin littafaina Akan farashi Mai sauk'i, .. Inakuke Y'an kasuwa Kuma kuzo Inayin logo graphics ko wanne iri had'ida cartons Art's design kudai kugarzayo domin mallakar naku cikin sauk'i...... Domin magana dani A WhatsApp 07064904617 OR 07031012948 ✍️ Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱 Queen 👸 of Writer's Hausa novels 📚📖📚 And design graphics```

```Ina kuke ma'abota ƙamshi Mata da Maza nesa tazo kusadaku BINTOUR ALIEY PERFORM Duniyar ƙamshi Cikin rahusa da Rangwame muna maraba da masu dasayen ɗaya koma Y'an sari muna turaruka kamar:~
sandal flasks, sandal wood, sandal bangi, Senegalese kajiji, kabbasa, humra fara, da brown,musk, turaren gogawa Kala Kala, turaren tsinke, dadai sauransu.... Zaku iya Nemanmu A 07048605381, Or 07040154174 Whatsapp ko kira,... BINTOUR ALIEY PERFORM, DUNIYAR ƘAMSHI DA KECE RAINANI...... MUNA MARABA DA ZUWANKUUUU```

_MARCH 2026_

_25/3/2026 MARCH_

_FREE PAGE 41 TO 50_

_LAST FREE PAGE, DAGA WANNAN FREE PAGE YA ƘARE IDAN KINA KANA BUƘATAR CIGABANSA WATO COMPLETE KABIYA ₦400 KAWAI ZAKA IYA NEMANA A 07064904617 A WHATSAPP NUMBER NA... IDAN KINSAN SABODA KI FIDDAMUNSHI WAJE ZAKI SIYA DAN ALLAH KIBARMUN KAYANA! PLEASE KADA KI SIYA KI FIDDAMUNSHI WAJE DAN ALLAH!!!_

................Cikin tsananin ɓacin rai ya isa gidan gonarsu tun daga nesa yasoma danna Hong da ƙarfi a gigice maigadin ya wangale masa gate Cikin sauri ya daka tsalle ya bashi hanya ko ida buɗe gate ɗin duka baiyi ba, da ace baiyi zafin nama ba to lalle da yabi takansa, baima ƙarasa inda ake parking ba ya fito a fusace ko kallon sauran security dake masa Sannu baiyi ba ya shiga ciki,

Buɗe fridge ɗinsa yayi ya fito da wasu kwalabe har biyu kala daban daban zama yayi kasa dirshan ya buɗe kwalaben haɗasu yayi guri ɗaya ya ɗaga kwalbar sama ya kafa kan bakinsa bai ɗauke ba Saida ya shanye tass ya sake buɗe ɗayan itama ya shanye kafin yayi wurgi da kwalaben yasoma magana Cikin maye

"Saina..... Ɗauke... Matakihh... Gaah duuuh kansuuhhh..."

Sai yanzu na kalle kwalaben naga anrubuta Alcohol,

"Latee wancan ba kamar bro Junaid ba kinga yarda yake driving anya kuwa lafiya," cewar Zeema dake tareda latee dake duma sun biyo titin suka hangosa,"

Tsaki Latifa tayi"ya wuce yayi shaye shayensa daya saba ne? Daddy ya sangarta bro dayawa wallahi ya buɗe masa taska yana abinda yaga dama,"

"Ya buɗe masa taska kodai ya buɗe muku? Latee kiji tsoron Allah fa koshi kansa Bro Junaid duk buƙatar da kika nema gurinsa yana miki so kidaina yin Hakan,"

Gyara zama tayi kafin tace"kina da gaskiya kuma muna kan gaɓar da nake neman taimakonsa domin nasan bro Junaid da nacin tsiya komai yasa gaba lalle zai samu komai wahala ba zai sare ba har saiya samu nasara kuma bashi da tsoro inaga dole na gaya masa kan cewar na kamu da son wannan Guy ɗin,"

"Waiko latee kina Cikin hankalin ki? Daganin Wannan guy ɗin fa kinsan ba tsaran kibane Wallahi mutumin kirki ne nasanshi sosai amma kuma har yanzu Ban taɓa magana dashi ba domin yanada izza miskilanci dama jiji dakai, lalle ne Yanada kyau amma kuma har yanzu babu wata macce daya faɗawa kalmar so duk da mata dayawa suna kaima sa tallan kansu amma bai ansama kowa ba, Unguwarmu ɗaya dashi,"

"Kinga shikenan faɗuwa tazo daidai da zama tunda kinsan shi, zancen wai baya karɓar soyayyar wasu matan kawai bai haɗu da mai aji kamar Ni bane shiyasa komai taurin kansa lalle Ni zanyi maganin sa Domin Kuwa *RASHIN JINI 🩸 RASHIN TSAGAWA* zan gwada Sa'ata, inason ki samamun number wayarsa dakuma inda za'a sameshi zan haɗu dashi,"

"Shikenan bari yanzu ma nayiwa wata sister ɗinsa magana ta turamin"

Cikin lokaci kaɗan suka samu number

"Kai Gaskiya Nagode ƙawata sosai muje nasake wanka muje mugani koma samesa a office"

"A'a yanzu kam yamma tayi kinsan dole yana gida kawai kibari sai gobe, yanzu bayan bro Junaid zamubi domin ganin meke damunsa"

"Oh Zeema lalle yayan nan nawa yayi ciki dake dayawa,"

"Sosai Kuwa Latifa amma kuma sam bana gabansa," tafaɗa cikin nuna damuwa

"Kada ki damu zaidawo hanya ne kidai cigaba da shiga jikinsa zai amince miki very soon,"

Already Latifa tasan bazai wuce gidan gonar ba hakan yasa sukabi bayansa can saidai koda suka isa ya gama buguwa ya fice hayyacinsa har yayi bacci nan ƙasan, dole suka barshi suka wuce.....

Hismat kuwa Saida taji muryan Mami mahaifiyar Haisam tana buga mata Ƙofar kafin ta buɗe,

Faɗa tamata cikin hikima da nuna kulawa tareda na siha, tamkar ta ɗauka haka tayi saidai tanaji a ranta babu wanda zai rabata da Junaid Sabo,
Sake sulalewa tayi tabar gidan batareda kowa yasani ba domin tasani idan tabari sukayi Arba da Boss Haisam bazata sha ba,

Gidan baba malam ta koma, kiran Junaid tayi ganin bai ɗauka ba tayi masa text mai ratsa zuciya, tun daga Lokacin bata sake komawa gidan Hajiya ba domin Bata shirya haɗuwa sa Boss ba,

Cikin sati ɗaya kuwa sun shirya da Junaid Sabo sosai yake kashe mata kuɗi kan graduation ɗinsu har zuwa lokacin kuma bai nuna mata kalan nufinsa gareta shiyasa taƙi yadda kan cewar mutumin banza ne,

A Yau suke graduation ɗinsu sanin duka ƴan uwa da abokan Arziki sun hallaya a yau ta shirya Bayyana Junaid Sabo ga Ahalinta shiyasa shima ta gayyace shi,

Yana zaune office ɗinsa yaji nocking tinkan yabada permissions na shigowa yaga taturo Ƙofar ta shigo, wata budurwa ce sanye take da wasu riga da sikert a tamfa ƙaramin gyale yana kan kafaɗanta tasha kitson ATTACHMENT wanda ya yazubo har bayanta fuskarta tasha makeup ga wani ƙaton Glass no respect tasaka duk ya rufe rabin idanta, tasowa tasoma zuwa inda yake zaune kai ka rantse idan ta mosta kayan jikinta zasu yage saboda matsuwanda sukayi mata jikinta Kuwa sura bayyane musamman kalan wuyan da akayi mata zaka iya hango rabin na shanunta ga wani uban turare data zuba duk office ɗin ya ɗauke ƙass ƙassss ƙassss kawai kakeji da ƙaran takalmin ta da cingom ɗinda take ci.

Ɗagowa yayi ya zuba mata ido ganin yanayin shigar Tata Cikin sauri ya ɗauke kansa ya cigaba da duba wasu file dake gabansa,

Zama tayi kujerar dake facing ɗinsa tana wani kisisina da karairaya,

Cikin lanƙwasa murya tace"Barka da aiki handsome"

Bai ɗagoba yace"waya baki izinin shigomun,"?

"To ai zuwa inda kyawawa ba'a buƙatar samun permission, kada kayi mamakin zuwana gurin nan domin Hausawa sukance Garin masoyi baya nisa, nazo maka ne domin neman soyayyarka, tun Randa naganka a airport Zuciyata takasa samun sukuni Haisam inasonka ina fatan zama mata agurinka!!,"

Sai a lokacin yasake ɗagowa fuska ɗaure yace,"Nagode zaki iya tafiya,"

"Haba Haisam meye laifin wanda ya furta maka soyayya inada aji kuɗi amma duk na barsu gefe nazo gareka ina ƙasƙantar da kaina amma kana ƙoƙarin walaƙantani ka tausayimun haisam wallahi ina sonka,"?

"Enough please get out of office" ya faɗa cikin tsawa tareda miƙewa yana nuna mata hanyar fita

MiƘewa tsaye tayi cikin damuwa tana ƙara marairaice masa tace"dan Allah ka amshi soyayya ta koda bazaka aureni ba ka zauna dani a soyayya wallahi zan iya shiga wani hali idan bansame kaba, inada kuɗi Haisam zaka hutu Senator Sabo ne mahaifina nafi ƙarfin yiwa namiji magiya amma duka na aje girma nazo gareka saboda ina sonka,"

"To bana sonki sanin waye mahaifin naki yasaka na ƙara tsanarki, ki tashi kificemun daga office kuma idan kika ƙara dawomin koda da kuskure ne wallahi sai kin san waye Boss Haisam, mezan dake ƙaruwa mara aji,"

Kiran security ɗinsa yayi"Amun waje da ita kuma duk randa tasake dawowa kuka bari ta shigomun wallahi koma waye zai rasa Aikinsa," yana gama faɗin hakan ya fice daga office ɗin, motar sa yashiga gida yanufa saidai a junction ya hange Junaid Sabo tareda Hismat tsallaken titin sun fito daga wani mall dukansu da murmushi a fuskarsu sun shiga motar sun wuce

Karya motarsa yayi yabi bayansu aguje, abin mamaki makarantarsu suka nufa har ciki yashigar da ita kafin ya sauketa tare suka jera suka isa wani table ya zauna Kafin itakuma tashiga cikin sauran yan graduation ɗin, ransa wani Irin suya yake masa, zamansa yayi a motar bai fito ba har suka gama bikin ta karɓo gift ɗinta cikeda farin ciki ta tsaya gurinsu baba Malam da suna magana can ya hango junaid sabo ya ƙaraso gurinsu Cikin ladabi kamar na kirki harda kai ƙasa yana gaidasu, cikin raha kuwa suka amsa masa, sosai zuciyarsa take zafi kenan sunan da zuwan Junaid Sabo gurinta amma suka barshi, har ya tada motarsa da niyar barin gurin kuma saiya kashe motar ya fito gurin ya nufa cikin izzarsa da ƙasaita, ganinsa yayi bala'in ɗaga mata hankali take ta rikice kasa riƙe kanta tayi cikin sauri taja baya takoma bayan baba malam tana zare ido,

"Wato so kike ki nunawa duniya ban isa dake ba ko,"? Ya faɗa cikin tsawa da ɗaure fuska

Cikin rawar jiki da tsoro tace,"A'a yaya Haisam wallahi ba haka bane dan Allah kayi haƙuri,"

"To meya kawo shi nan dakuma zuwa shopping,"

Zare ido tafara tana kallon baba malam daya kafeta da ido yana Neman ƙarin bayani

Hannuwansa sanye cikin Aljihun wandonsa fuskar sa cikin Glass ɗinsa, yace"kai bana maka gargaɗi akanta ba,"?

"Ya Haisam dan Allah kada kamin haka wallahi inasonshi kuma nice na gayyato shi,"

Gyara tsayuwa Junaid Sabo yayi yana jifansa da wani shu'umin murmushi kafin yace"kada ka takura yarinya kan abinda bataso,"

"Na gaya maka Abaya Yanzu zan sake maimaita maka cewar kafita harkan yarinyar idan ba haka ba,"?

"Mezakayi," Junaid ya faɗa yana ɗaga masa gira tareda lashe lips ɗinsa bayan ya lalle Hismat

Cikin tsananin kishi Haisam ya cakume kwalan rigarsa, tareda ɗaukesa mari, "wallahi a Yau saina saka ka fahimce cewar *RASHIN JINI 🩸 RASHIN TSAGAWA*

wannan karon Junaid bai ƙyalesa ba shima ya cakumesa take suka kacame da faɗa.................................

KASH LAIFIN DAƊI ƘAREWA GASHIDAI MUN KORO SAIDAI LOKACI YA MANA HALINSA BAWAI LABARIN YA ƘARE IYA NAN BA A'A FREE PAGE NA KYAUTA SHINE YA ƘARE ANAN AMMA KUMA LABARIN MAI ZAFIN GASKE YANA CIKIN CIGABAN LABARIN ₦400 KAWAI ZAKA BIYA DOKIN SAMUN CIGABAN LABARIN..........

SHIN YAYA ZATA KAYA DA WANNAN RIGIMAR DATA ƁARKE?

SHIN WAZAI AURE HISMAT?

SHIN WANE MATAKI JUNAID ZAI ƊAUKA KAN HAISAM?

SHIN HISMAT ZATA AURE BOSS HAISAM?

WACE AMANA BABAN HISMAT YABAWA BOSS HAISAM?

SHIN WANE ALƘAWARIN NE TSAKANIN HAISAM DA BABANTA DA MAMANTA KUMA?

SHIN LATEEFA ZATA HAƘURA DA HAISAM KUWA?

SHIN ZEEMA DA ZUCIYA ƊAYA TAKESON JUNAID KUMA TAKE ƘAWANCE DA LATEEFA?

MEZAI FARU NAN GABA?????????????

KINA KANA MUNA KUNA SUNA BUƘATAR SANI?

TO KUBIYONI NI MATAR MLM CIKIN WANNAN ƘASAITACCEN LABARIN NAWA MAITAKEN RASHIN JINI 🩸 RASHIN TSAGAWA! ₦400 KAWAI ZAKI BIYA DOMIN SAMUN COMPLETE ƊIN WANNAN LABARIN.. NICE DAI TAKU HAR KULLUM WATO MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR QUEEN OF WRITER'S HAUSA NOVELS MRS_MLM GRAPHIX & NOVELS ALƘALAMI DA FASAHA STUDIO 🔥 07064904617.............

_BASEERATA ITA CE ARZIKINA 😍_

Whatsapp number 07064904617 or 07031012948
Chapter 7 · 0% Book details