← Book details Rashin Jini Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 7

Sashe 6

Rashin Jini Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dawowarsa daga aiki kenan ya hangota cikin mota tareda Wani ga alama firan ta musu daɗi domin kuwa sai murmushi suke zubawa su duka, wani ɗaci yaji a ransa musamman ganin kusancin nasu da ita, fitowa tayi motar tasa cikin isa yataka har Zuwa inda suke nocking Glass ɗin motar yayi, dukansu suka juyo ganinsa da irin yadda ya ɗaure fuska saida gabanta ya buga amma ta daure cikin dakiya tace"ina wuni Bro"

Bai amsa ba domin ganin waye yasashi jin wani fargaba, ba kowa bane face Junaid Sabo sangartaccen yaro ɗan gidan masu kuɗi babu wanda baisan Mahaifinsa ba mai kuɗine na gaske domin ɗan siyasa ne, shine kawai gare shi namiji hakan yasa yayi bala'in sangartashi babu abinda zai nema ya rasa shi kanshi yaron bai cika zaman Nigeria ba kuɗi ba matsalan sabane iya sanin da yamasa akwai neman mata kamar hauka kuma yana shan giya baida kunya balle kuma a wani abu wai mutunci, ganinsa inda Hismat yayi bala'in ɗaga masa hankali,

Cikin ɗaurewar fuska ya dawo ai nahin Boss ɗinsa yace,"Kee shiga gida,"

Ɗan tura baki tayi "amma Ya......."

Tsawa yadaka mata wanda ba ita kaɗai ba hatta shi gogan naka Saida hantar cikinsa takaɗa yace"ina wasa dake,? Idan kika bari na maimaita magana wallahi karya yaki zanyi kamar take,"

Cikin sauri ta buɗe Motar tana fashewa da kuka ta fice da gudu tayi ciki,

Kallo sa junaid yayi cikin haushinsa yace "Amma kanme Meta maka, zaka koreta,"?

"Kai ina wasa dakaine ko ni Sa'anka ne,? Maza ka barnan kaima, kuma idan na ƙara ganinka da ita wallahi sainayi maganinka,"

"Kai kasan Ni ko waye da zaka faɗamun magana son ranka,"? Junaid ya faɗa yana fitowa daga motar

"Nasani ma Junaid Sabo sangartaccen yaro kangararre ɗan gidan masu kuɗi kuma mara tarbiyya"

Dariya junaid yayi tareda sosa kansa Irin na shaƙiyan maza yace,"lalle kasanni farin sani ma Kuwa amma kuma bakasan kalan Aikina ba, koma yaya take gareka to inaso kasani raina ya biya da ita saidai inason na Aureta ne idan kuma kayi ƙoƙarin bani matsala to lalle zakaga Babbar matsala a aikace wallahi,"

Chakumar kwalan rigarsa yayi "ni kake gayawa wannan Maganar," cewar Boss Haisam cikin zafin zuciya

"Kai nizaka shaƙewa kwala a bainar jama'a dan nazo inda wannan jakar ƙanwar taka,"?

Ɗaukesa da gigitaccen mari yayi wanda Saida ya bugu da Motar

Daidai lokacin kuwa Dr Areef ya ƙaraso cikin Sauri ya shiga tsakiya ya raba faɗan yana janye Boss Haisam

Cikin tsananin fushi Junaid Sabo yace"Ni zaka mara,? Wallahi da ita da kamareni saboda da ita dakai kanka babu wanda zai kuɓuta daga tarkona, sainayi maganinka wallahi domin haukan da kake nunawa ya Bayyanamun cewar kaina kaina Neman soyayyar tane kishi ne yake cinka to wallahi saina nuna maka waye *JUNAID SABO*,"

"Kai kadaɗe wallahi duk abinda ya same Hismat daga ranar zaka tabbatar da *RASHIN JINI 🩸 RASHIN TSAGAWA*,"

"Shikenan muzuba shege kan fasa,!!"

Junaid ya faɗa tareda jan motar sa yabar gurin aguje cikin ɓacin rai

"Haba Boss meye haka yazaka biyewa wannan yaron bayan kafi kowa sanin tsagera ne har kana neman dambe dashi a bainar jama'a,"

"Ai sanin halin nasa shine yasani yin rigima dashi taya zanbarshi tareda Hismat bayan amanarta mahaifinta yabani ko bayan haka ai ina matsayin Jininta saboda haka dole na kula da duk wani responsibilities nata,"

"Haisam kodai da gaske ne kana sonta kamar yadda ya faɗa,"

Harara akwai ya banka masa tareda komawa motarsa yaja da ƙarfi ya shiga gidan

Duk faɗanda akayi akan idanta hakan ya ƙara tsoratata musanman ganin Saida ya fidda ma Junaid Sabo jini tasani Boss akwai ƙarfi Amma dai lamarinsa yana ta'azzara kanta yau tashiga Uku idan baba malam yaji yaya zatayi kuma yaya zata tunkare junaid sa ban haƙuri domin gaskiya tana sanshi, kwasa tayi da gudu tayi sashen Mani ɓangaren mahaifiyarsa tana shiga duka suna palourn hardasu Hajiya aguje tayi Cikin ɗakin mami jikake kaffff ta rufe Ƙofar harda murza kif duk da hakan sai gumi take cikeda tsoro kuma,

"Ke lafiya" Hajiya tafaɗa amma ina tuni ta wuce ko saurarensu batayi ba

"Yarinyar nan sam batada natsuwa wallahi anya kuwa babu iskokai kanta,"? Inji Hajiya

Amna tace"dagani wata maganar ta janyo,"

Kafin Mami tayi magana saiga shi ya faɗo rai ɓace "ina take,"?

"Kai tsaya lafiya? Ya zaka shigowa mutane kamar wani mahaukacin zagi kuma wai kana neman ƴar ƙanƙanuwar yarinyar, wai kai bakada tausayi ne komai? Bayan kasan yarinyar nan marainiyar Allah ce amma kai kullum kana cikin cin zalinta, har Ubanka ya maka faɗa gameda dukanta amma kaƙi bari idan ƙarfi kakeji kaje filin dambe kadaku da maza majiya ƙarfi kamar kai mana,"

"Enough Hajiya is okey kinsan abinda ta aikata ne, idan aure takeso ai saita fito tayi magana a ɗaura mata bawai ta dinga tarawa Mutane ƴan iska ba, to wallahi duk randa nasake ganinta da wannan ɗan iskan Wallahi saina karya mata ƙafa,"!!!

Fuuuuuuu yabar palourn cikin masifa

Sake baki Hajiya tayi tana kallonsa,

Shigowar Dr Areef shine ya musu bayanin komai saidai ya ɓoye irin Alwashin da suka ɗauka kan juna.

"Ah lalle ko inko hakane to lalle bakida gaskiya yoni naga yarinya kamar mai shafar Aljanu ace sai shegen ƙiriniyar tsiya da kwashe kwashe yo meyasa bazaki da ƙattan can gidan Uban naki ba ko gidan Uwarki shine mu dakika raina zaki kwaso muna su, kuma daga ciki sai ɗan Iska, to wallahi kada Nima na ƙaraji,"

Itadai lafewa tayi tanajinsu amma bata fito ba balle ta tanka, kuma ta ɗauke Alwashin babu Abinda zai rabata da Junaid domin tana sonshi........................

_BASEERATA ITA CE ARZIKINA 😍_

Whatsapp number 07064904617 or 07031012948

*RASHIN JINI 🩸 RASHIN TSAGAWA!!!*
_PAID BOOK ₦400 ONLY_

*_LOVE, BETRAYAL, DEPRESSION & SYMPATHY ALL IN TARKON SO!!!_*

_Labari maid'auke da darasin Rayuwa, fad'akarwa ilimantarwa, dama Wa'azantarwa, gamida nishad'antarwa_

_RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱..._

(MRS_MLM GRAPHIX & NOVELS ALƘALAMI DA FASAHA STUDIO 💥 ✨ 💥)

```MARUBUCIYAR... (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book, (6)Shagala Free book, (7) Silar d'a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9) Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12) Bak'in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d'aukar fansa free book. (14) ZAYYAN 💞 ZEEYAT PAID BOOK. (15) MAKARANTAR KWANA FREE BOOK. (16) SHAGALA FREE BOOK,, (17) SO SIRIRIN ZUCIYA..... And Other's BUT NOW (18) SAURAYINA.. (19)D.S.P ANNUR PAID BOOK....(20) SAKACINA PAID BOOK.... (21) SO!!! FREE BOOK... (22) FATALWAR ☠️ BUDURWAR MIJINA PAID BOOK... (23) D'AUKE D'AI D'AI DUNIYAR SHAID'ANU PAID BOOK...(24) RUHIN JINN PAID BOOK.. (25) JAMI'IN SIRRI C~I~D PAID BOOK 300 ONLY.. (26). SANADIN PARTY HORRO STORY..(27) ASHRAF_LOVE 💞STORY....(28) TAWA K'ADDARAR 😢 FREE BOOK..., (29)GUBAR MATSAFA!!! HORROR STORY ☠️💀👹😈... (30)NUR RAINON D'AN FASHI!!! FREE BOOK. (31) ZUCIYA..(32) YARIMA ASHMAN🤴🏻 (THE PRINCE) PAID BOOK 300 ONLY.. (33) SILAR GRADUATION PARTY, HORROR ☠️💀😈👹☠️💀 FREE BOOK. (34) SULTHAN ANEEM🤴👑 PAID BOOK. (35) And know AKAN AIKIN MIJINA🧟👹🧟 FREE BOOK is (36). TANGARAS.... FAD'I KAFASHE PAID BOOK (37). BARRISTER NAZEEYAH PAID BOOK (38).. (39) CAPTAIN AMEESH FREE BOOK....(40) DAREN HANA BACCI ☠️ 💀 ☠️ (41) BARRISTER ARMAN! (42) TARKON SO!
(43) RASHIN JINI 🩸 RASHIN TSAGAWA!!!loading..... Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱 QUEEN OF WRITER 📝```

_Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah mad'aukakin sarki Mai bayarda baiwa gawanda yaso Kuma sanda yaso Ina godiya ga Allah Allah daya sake bani dama had'ida baseerar sake kawomuku sabon littafina maitaken_ *RASHIN JINI 🩸RASHIN TSAGAWA!!!*
PAID BOOK ₦400 ONLY

_Ina fatan yabada darussuka dama ilmantarwa Kamar dai yarda sauran littafaina suka bayar....._

*Arayuwa zaka burge wasu Kuma zaka bawa wasu haushi, wasu zasu soka Wasu Kuma zasu k'ika wasu zasu yabeka wasu kuma su kusheka, Haka rayuwa take tafiya idan Kama wani wani bazaka masa ba, dukanin Sak'onninku suna zuwa gareni na Yabo da Akasin hakan, ban Damu da zagin wasu ba Domin kuwa nasan cikakkiyar ni'ima tana Aljanna Amma duk da hakan Ni Mujaheedah Matar mlm Ammyn khausar 🤱 QUEEN OF WRITER 📝 nakakce Alhmdllh Domin Alk'alamina A tsalkake Yake bana Batsa ko shashanci ko cin zarafin wani ko Aibatawa, Ina Rubutu Kan tsarin tafarkin Ilimi domin bada Shawara nasiha Fad'akarwa Wa'azantar ilimantarwa, kuma Alhmdllh Sak'ona Yana zuwa daidai inda Allah ya nufa Kuma Yana ban Lada daidai da Aikina, kuma Ina Samun Masoya daidai nufin Ubangiji ✨ Inaaa Alfahari daku Masoyana Kuma Ina sonku Tabbas _BASEERARA ITACE ARZIKINA😍_ Allah ya k'ara wadatamu yamuna K'arshe maikyau yasa mucika da imani yabamu Masoya Nagari ya karemu daga Mak'iyanmu, Allah kabama k'asarmu NIGERIA zaman lafiya da Arziki Mai Amfani..... AmeenAmeen......... Mujaheedah Matar mlm Ammyn khausar 🤱 QUEEN OF WRITER 📝 HAUSA NOVELS 📚 MRS_MLM TAKUCE🥰🥰*

................................✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓✓

........................

*INAAA KUKE MATA IYAYEN KWALLIYA DA GYARAN JIKI?? INAA MASU BUK'ATAR GYARA FUSKARSU DAMA JIKINSU? SHIN KINASON RAGE GIRMAN CIKINKI TO KU HANZARTO DOMIN SAMUN NAKU KODA KUD'INKA SAIDA RABONKA MAMAN TEEMA AND MORE 08100100821......... INAAA MASU FAMA DA MATSALAR RASHIN HAIHUWA? INA MASU FAMADA ULCER? INA MASU FAMADA K'IBA ANA NEMAN ARAGE? INAMASU JIKI SIRANTAKA ANANEMAN YIN K'IBAR? INAAA MASU FAMADA SIKILA? INAMASU FAMADA CIWON JIKI?? KAI DUK WANI WANI CIWO DA ALLAH YA HALARTA ADUNIYA TO YAYI MAGANINSA DAN HAKA KU HANZARTO AGUJE DOMIN SAMUN NAKU MAGANINMU BASHIDA MATSALA YASAMU KARRAMAWA DOMIN TINDAGA CHANA YAFITO GHT KENAN KABADA KUD'I MUBAKA MAGANIN MATSALARKA IN SHA ALLAH... HAKA MASU NEMAN MAGANIN MATA KO WANNE IRI AKWAI WANDA HARSAIKIN BADA LABARI HUNNNMMM RIGIJI GABJI WASU KAYA SAI AMALA KAWAI KUYI MAZA KIYI MAZA KAYI MAZA HAD'UWA DA MAMAN TEEMA DOMIN SAMUN MAGANIN MATSALARKI KO WACCE IRI 08100100821 ITACE NUMBER TA DOMIN HAD'UWA DANI KUWA NI MARUBUCIYAR LITTAFAI HAUSA KATUNTUB'I WANNNAN 07064904617 MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱 QUEEN OF WRITER 📝 HAUSA NOVELS 📚 MRS_MLM)*
Chapter 6 · 0% Book details