← Book details Mijin Buzuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 6 OF 6

Part din tsohon gidan aka kaimu direct anan aka sauke mu daga ni har yaran da Alkasim duk mun gaji.

Mijin Buzuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 164 min read

Sunyi murna sosai da ganin mu inda aka shiga dawai niya damu da yaran sai nuna min yan uwa akeyi duk wanda yazo gaida mu.
AA ya shigo gidan ya kalli inda nake fakin baiga motana ba a wurin ga gajiyan daya debo ga yunwa na damun sa part din shi ya shige ya fara watsa ruwa ya fito.
Sai bayan magariba ya shigo part dina sin gaisa yana tambayan Altine ina nake ne tace ai tun fitan da nayi da safe ban dawo ba.
Da mamaki ya maimaita abinda tace yace bata dawo ba fa ina tashiga haka da yaran kuma ai shine Altine ta bashi amsa.
Yayi yace ya juya ya fita daga dakin ya kara jin bacin rai fiye dana safe din wayana ya kara gwadawa bai shiga ya haura part din shi.
Abin duniya ya taru yai mai yawa a rai yasha alwashin sai ya bata min rai ranan idan na dawo don bai yarda da fita irin haka .
Kara shigowa yayi part din tara saura ya tambaya suma hankalin su a tashe yake don laraba tace ban taba fita irin haka ba tunda suka ce mai ban dawo ba.
Gaban shi ne ya bada dam yana fadin ina na shiga a cikin ran shi a fili ko cewa yayi OK idan ta shigo kice ta samay ni a wurina.
Abinci Altine ta taya mai don ranan nice da girki duk da ban nan sun girka abinci sun saka mai nashi.
Yace a hada ya tafi dashi shiru shiru ban shigo ba ya kara trying din layina a kashe wayan yake har lokacin haka yasa ya kira momy yana tambayan ta nazo kaduna ne ?
Momy tace dashi bata gane ni ba sai dai idan ina gidan su ya Amina ne amma bata tsammanin hakan don da ya Amina ta kira ta fada mata nazo.
Ta sake tambayan wani abu ya faru ne babangida da zata wuto baka san inda taje ba tun yaushe ta fita gidan ma ?
Kasa amsa mata tambayan nata yayi don yadda yake ji a ransa yace zan kira momy kada ki fada ma hajiyan mu don Allah ko Abba zan maki bayani daga baya.
Tace to shike nan gashi baida lamban maryam kuma yana son ya kirata ba hali Yusuf ne ya fado mai a rai yasan da wuya idan baida layin maryam din don yaga suna dasawa da ita.
Ya kirashi ya tambaya yace yana dashi inji dai lafiya nan dai yake fada mai abinda ke faruwa yace shine baka nemay ta tun dazu ba man.
Yanzu fa fast ten muke yace shiyasa hankali na ya tashi ai nan dai suka dan taba magana yace bari ya kira maryam din bayan ya turo mai layin ta.
Maryam tayi mamakin jin ban gida tace kuma wallahi ban fada mata komai ba balle ta san inda na tafi din itama dai hankalin ta ya tashi sosai.
Tace idan ansan inda nake don Allah a kirata yana dauka wasa ne sai ga abu ya zama gaskiya don har safe ban gidan ranan hankali tashe ya kwana.
Sai tunane yake ina nashiga don da minna naje da daddy mu ya kirashi ya sheda mai mun sauka lafiya ai.
Tun da safe ya kira daddy bayan sun gaisa sai ya rasa abinda zai fada mai daddy na ya tambayi yan jikokin shi yace daddy su na kira inji ko sun zo gidane ?
Bata gidan ne daddy ya tambaya da sauri yace daga dan magana kadan akan karatun ta tun jiya ta fice gidan da safe bata dawo ba har yanzu.
Hankali daddy ya tashi sosai sai dai ya kwantar ma AA da nasa hankalin yace ka barta duk inda taje nasan gida ne saboda nasan halin khadija.
Ba zata inda zamu ce asha ba da ziwanta zan kirata in gani yace daddy wayan ta a kashe yake tun jiya bai shiga.
Shiyasa na kira ina tsoro idan ba wani mugun abin bane ya samay ta a can don yanzu duniya ya lalace da fitina.
Sun rabar da Daddy zai zaga cikin yan uqa yaji ko ina can daddu ya kashe wayan ya fada tunane bayan sun gama magana da daddy ya ce khadija ba matar da ta taba min haka a gidan sai ke.
Yaushe wanan bakin shawaran yazo maki har kika aikata hakan ki fita min da yara haka ban san inda kika tafi ba.
Hankalin shi idan yai dubu a tashe yake ranan ya har zuwa karfe hudu baiji wani labari ba kuma wayan baya shiga.
Lokaci daya ya zabge dashi don yana cikin tashin hankali kwana mu uku na raba tsaranba da na saya masu tsohon gidan yake tambayana yaushe ne komawan mu sai nayi shi.
Haka yasa ya gane ba lafiya muka zo ba gidan nan cikin hikima yake tambayana ban boye mai komai ba na fada masu abinda ke faruwa .
Sukace in zauna in kyale su zasu kirashi daga baya su fada mai kamar illa ina kuna wayana kiran maryam yana shigo min.
Na dauka naji tana fadin khadija ne kina ina don Allah haka kika tayar da hankalin mutane nace ina garin mu Minna tace nace minna garin mu ne.
Asalin mu dai nazo don nasan in naje minna ba zasu share min hawaye na ba niko kin san ba zan bar karatuna ba don shi.
Khadija ai da sai ki tsaya ku fahinci juna nace kina ganin zai saurare ni yadda ya hau din nan bari ke dai in mashi hakan.
Muna gama waya ta dana ma AA kira suna tare da Yusuf ya dauki wayan tare da sallama tace yanzu mukai magana da khadija.
Cikin sauri yace tana inane haka tace wai garin su ta tafi a jahar kebbi garin yake yace what yaya akayi har taje can din Yusuf yana tambayan shi an ganta dai ko ya kada mashi kai kawai.
Sun gama magana da maryam ya dubi Yusuf yaja tsoki tare da fadin wai kaji wanan yarinyar kebbi fa ta tafi don hauka irin nata da yaran nan.
Yusuf yace tunda dai an san inda suke ai yanzu hankali ya kwanta dai ko da ba a san inda suke bane kaga shine tashin hankalin mu ka tafi Niger ma don mace balle nan da kebbi cikin kasan nan.
May ye marabin kebbin da Niger Yusuf ai kusan nisan su dayane dan bambamcin kadan ne ya fada yana jan tsoki.
Yusuf yace dama su khadija yan kebbi ne ashe yace ta taba fada min hakan amma basu san gida ba garin su wai fulani ne su tace min tun kan muyi aure ta fada min hakan.
Daddy ya kira ya fada mai komai sai da Daddy yakai zaune a inda yake tsaye tsakar gidan mu yace kebbi fa kace yace haka ta fada ma kawar ta .
Suna gama waya da daddy na kiran hajiyan su na shigo mai don momy ta gaji da boye mata kada tayi laifi momy bata bar dakin ba hajiya ta daga waya ta kirata.
Fada ta fara mai tana fadin duk inda yar mutane ta shiga ka nemo masu yar su tunda kai baka san mutunci ba yanzun haka akan wanan bakar matar taka yarinyar nan ta bar gidan ka.
Yace hajiya an gasu wai suna kebbi can ta tafi garin su wurin yan uwan mahaifin ta na can fada sosai hajiya tayi mai ta nuna mashi bacin ranta na yarda ya bari har haka ya faru tsakanin mu.
Bata bari yai mata bayanin komai ba tace gobe goben nan kaje ka dawo da yarinyar nan ko in saba maka hankalin shine ya kara tashi da fadan hajiyan tasu sosai.
Agida ko cewa yayi wasu Altine gida naje in gan su ai badon sun yarda ba suka bar maganan a hanka duk yadda suka so su samu layina a ranan ba wanda ya kamani.
Don muna gama waya da maryam na kara kashe wayan dama itama don ta daukan min excuse ne a school na kirata.
Da ko ita ba zata samay ni ba don naso in barsu sai sun sha wahalan sosai ba wanda yasan inda na tafi har yan gidan mu din.
Tunda mukai waya da maryam din ta fada min yadda ya tayar da hankalin shi kan rashin sanin inda muka shiga nace ai duk tsiyan shi sai ya sake ni don ba zan koma gidan shi ba tunda ba sona yakeyi ba.
Tace keke wanan haukan mukan ai mun tabbatar da son ki a ranshi a fili don yadda ya tayar da hankalin shi ga batan ki.
Nace yaran shi dai yakewa amma ba niba zata damay na kashe wayan na barta tare da danna ma wayan off gaba daya.
Nasan zasu ta nema na don fada ma maryam din duk da nace kada ta fadawa kowa inda nake aikin banza ne sai ta fada yasa na kashe wayan nawa gaba daya.
Washe gari ban san irin sakkon da sukayi ba karfe hudu da wani abu suna cikin kaoje tare da Yusuf da wani dan uwan daddy na suka zo har da daddy.
Muna hira a lungun sarakan kakan namu naji wani saurayi yazo yana fadin ga baki nan daga Abuja sun zo wuri na sai naji gaba ta fadi.
Don ban taba zaton zuwan su ba da wuri hakan nan dayar matar tace karya yake yi yace wallahi suka kalle ni sukace mijin ki ne yazo tafiya ya tashi.
Nace ban zuwa ko ina nazo gida ke nan suka sa min dariya sai da suka huta aka tare su da abin arziki sai da suka huta akaiwa su daddy korafi rashin zuwan su gida.
Sai aka dauko zancen mu kuma nan dai aka kirani nazo a cikin hijjab dina har kasa na zauna gaida su da zuwa.
Daddy na dauka zaiyi fushi dani amma sai naji yace kai khadi idon ki ke nan ke mai iyayye kin kwaso kafa kinzo gidan ku ko.
Dan murmushi nayi na noke kaina nan dai kakan namu ya fara magana yace to Alhaji Abdulsamad ga matar ka nan ta kawo muna korafi duk da kawaici irin namu na fulani korafin ta ya zama dole mu duba mata.
Kasan tana karatu ka aure ta komu nan yan kauye yanzu mun san mahinmacin boko ga diya mace don yaran mu nayi sosai balle ita yar birni.
Don haka muna son ji a nan may ye matsalanka ga karatun nata don mu san makomar ta akai ya gyara zama don tunda na shigo ya daga kai ya kalleni ya sunkuyar da kan shi kasa.
Sai yanzu ya dago yana fadin ba manufa in hanata karatun ta ba tunda dashi na samay ta ni matsalana da ita akan yaran da bata fita dasu ne.
Yara ko nan ai naga basu fita dasu zuwa daukan darasi a gida suke barin su don Allah kayi hakkuri yarinyar nan ta samu ta karasa karatun ta yace ba komai malam in Allah ya yarda an wuce maganan.
Yace shi zancen kishiya da zamantakewan gida ba zan ce maka komai ba mu hilani ba a san mu da raki kan kishiya ba ko kadan balle wata buzuwa can ta tayar mata da hankali.
Don haka ba zamu taba wanan zancen ba amma don Allah duk da haka a kula a tsare hakki abawa kowa hakkin sa a daidaita adalci a tsakani.
Sai zancen yaran da tace ka kwace hannun kishiya ka bata wanan bamu dan dalilin ka nayin hakan ba na bata hakkuri akan haka ta sa maku ido dole kana da manufa akan haka.
Nasiha sosai yai muna sun so su juya ranan don Yusuf ne ya tambaya yace ai ba tare kuka zo ba sai ku bari idan mun shiryata zuwa karshen sati zatazo da yan uwa aga inda kuke da zama don sada zumunci.
Mu wanan yarinyar tai muna komai a rayuwan mu don ta farfado muna da abinda muka kasa yi a tsakanin mu sada zumunci tunda tsofin mu suka kare.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/17/21, 6:30 AM - Xxxxx: Yusuf da sai faman murmushi yake saukewa a fuskan shi tunda tsohon ya fara magana AA dake kula dashi ya fahinci murmushin may Yusuf din ke yi.
Saida suka fito don yin magariba yake sake dan guntun tsoki alokacin Yusuf ya fadada murmushin shi mai sauti yace dama ai na fada maka khadija ta daban ce gashi ko kagani yanzu.
Kai a tunanen ka baka ga macen da zata barka don kanta ba ko wani abu sai idan kai ka saka kan ka binta .
To yanzu ka gani mata suna suka tara don khadija dai ta nuna maka ita ba dukiyan ka ne a gaban ta ba nata take nema da incin kanta.
Zama yayi ya fara tatara hannun rigan dake jikin shi don jin dadin alwalan da zai gabatar a lokacin.
Yace kana tunanen don ta nazo nan din ko may yace ina son sanin wanda kayi uwar tafiyan nan don shi din yace kaima kasan saboda yara na ne don ban san halin da zasu shiga ba idan na barsu nan.
Yaran wa ya haife su ko ka dauki yaran ka tafi dasu man ka barta ai ita gida take gaji irin yabon da ta samu kan zuwan nata ai.
Kyale yusuf din yayi ya fara gabatar da alwalan shi yana tunanen maganan Yusuf din lalai khadija fassarata da wuya ita sam abin da ke gaban saurran bai gabanta kullun ita sai yakin neman wakanta mafita take.
Bayan sun dawo daga massalaci ne a gabatar masu da abinci ida idan sun ci zasu wuce birnin kebbi su kwana washe gari su kama hanya.
Wani yayana ne yazo da kanshi ya kirani wai in je mu gaisa kafin su tafi nace ai ba ni na kirasu ba ya barsu kawai.
Yace ke ko ayi hakan bakin mu ne fa har dake dole daya matsa min na fita zuwa wurin su don mu gaisa.
Na samay tsaye a bakin motar su nayi sallama ciki ciki ba tare da furta komai ba na ja na tsaya Yusuf ne yace maman biyu idon ki ke nan ?
Kin gudo muna da diyan mu ba tare da sanin mu ba nan ma da suka zo ai gidane na bashi amsa a takaice.
Hummm naji AA ya fada kawai tare da fadin gida ne amma ba gidan su ba nace dole dai kamar yadda za a ce gidan uban su nan ma ace gidan uwar su ce ai.
Yanzun dai kada ki saka fulanin garin nan su sauke muna sanda a kai duk inda bi gari ba kaji komai sai kodin kodin ba hausa mai dadi.
A haka aka gansu har aka nace masu Yusuf wanda ke gefe dariyan mumuke yake ma converstion din mu yace wai ni yaran ma ba za a bari mu gansu bane ko fushin mu ya shafe su suma ?
Suna wurin yan uwa na ni kuma ba zan iya cewa a kawo su ba yace gaskiya ne kin nuna muna ke bafullatan asalice wurin kawaici.
Yanzun dai gamu a kasa muna kara bada hakkuri bisa ga laifin da mukayi don Allah a yi hakkuri a dawo a cikin lokacin da aka saka din ko don karatun ki ke ma.
Ai ba damuwa da karatun nawa kukayi ba tunda ku kun kama naku yasa kuke son yi min sakaci da nawa.
Yusuf zaiyi magana ya tare shi da daga mai hannu yana fadin haka naki tunanen yake sai nake ganin kamar sauki na neman maki ashe ke a gurin ki ba haka abin yake ba.
Nace sauki may sauki da zama da jahilci akai ko sauki da gadara da abinda ba na ka ba kai kadai ban yarda da wanan saukin na dan lokaci ba nafi bukatan in sama ma kaina mafita da zufa na nima.
Yusuf muje dare na muna don ance akwai dan nisa tsakanin nan da garin kebbi din mu tafi kada dare yai muna anan.
Yaushe kuma ai dare ya riga yai muku nan don almuru ya wuce ko sai kuma na gobe duk da yasan magana na fada mai bai bani amsa ba sukai min sallama wanda Yusuf ne ya samu yin sallama din suka tafi.
Sunyi nisa ga tafiya yace yarinyar nan ta samu damana da yawa Yusuf ya dan nisa yace dama haka abin yake ai ba kullun ake hawa gado ba.
Ya maida kan shi ga seat din da yake zaune yana lumshe idanu sai tunane take a zuciyar shi lalai maganan Yusuf gaskiya ne.
Mata suna suka tara wai yau shine mace ta bar gidan shi don wani dalili nata can bai taba zaton akwai macen da zata iya tsallake shi da abinda yake dashi ba tace nata zabin ta zaba.
Kudi kyau ilimi wayewa da duk wani abinda mata ke so yana dashi don haka yake daukan ko dun dole mace ta bushi ya juya ta yadda yake so.
Sai gashi ita wanan abin ba haka yake gareta ba duk wanan abin daya lissafa ta ketare shi ta wuce don wani dalili nata na banza.
Allah yaso Deedar yana son ta har cikin ranshi haka ma hajiyan mu tana son ta da na nuna mata nafita tsiya wallahi.
Guntun tsuki yaja a fili har Yusuf ya dan juyo yana fadin yaya akayi ne mutumina ?
Wallahi Yusuf yarinyar nan nake tunane a raina ban san ya akayi ta samu waje haka a zuciya na ba har batinta gidan ya sa nake jin gidan kamar ba kowa a cikin sa.
Yusuf yace ba sake kayi ba halin khadija ne ya ja mata haka yanzu in ka bibiya ko su Altine kamar su kama da wuta suke don rashin ta a gidan.
Ai mutum mai mutunci haka yake idan yabar guri sai kowa yaji daban a gidan yace na yarda da dan ko sadiya da take yarinya tasan khadija bata gidan.
Yau din nan Altine ke fada min ta daina karban abinci ko wani abu idan an bata sai fitina take masu kaga ko yaro yasan mai kyauta mai ashe inji Yusuf.
Ban san kunyi haka ba wallahi da na fada ma hakan da zakai mata ba daidai bane ko don kyau cika alkawarin da ka daukawa iyayyen ta kafin ai aure.
Bai iya magana ba sai dafe kanshi da yayi da hannun shi daya yana ci gaba da tunane a ranshi don baiji irin haka da Nafisa ta tafi ba in ba jin da yayi a lokaci daya yana son ya dawo da ita gidan ba..
Na yarda gyara na wurin yan hausa don ni kaina ina jin canji a jikina don irin shaye shayen da akai ta dura min nasu da suke amfani dashi na gida wanda suka sani sukan san ingamcin sa.
Bawai abinda basu san komai aka hada dashi ba wanda suke amfani tun iyayye da kakanni wanda duk wata mace a can ba abin kunya bane a gare ta amfani dashi.
Wancan ta kawo wanan ta kawo duk kuma kakana tana tsare ni sai nayi amfani dasu ba wani zancen boka da malam ko yawan cushe cushe a gaba da zaija wa mutum illa.
Wanan sai ma ya gyara ma jiki fata yai haske ka kara dan magurjin jiki daidaiwa daita da mata biyu zamuyi tafiyan sune zasuyi min rakiya sai wani yayan mu na miji da zamu tafi dashi.
Tun da safe muka dauki hanya har da kuka na na barin su da zanyi don ina jin wani iri a raina ba dadi a lokacin.
Mun sha tafiya sosai sai karfe biyar muka shigo garin har zuwan mu gidan kafin shida na yamma mun shiga gidan.
Da murna su Altine suka tare ni tare da baki na suka bani abinci kamar sun san da zuwan mu a ranan.
Sai tambayan mutanen gida sukeyi ina fadin suna lafiya a yadda na fahinta a cikin hiran mu dasu basu gane yaji nayi ba don shi abinda ya fada masu daban.
Naji dadin boye min sirina da yayi sai naji mutuncin shi ya darsu a zuciyana koba komai ya rufa min wanan asirin dama ina tunanen da wani ido zan kalle su.
Kafin wani lokaci Laraba ta gyara min dakina tsab da dakin da baki na zasu sauka Altine ta gyara yaran sun goya su bai shigo gidan ba sai bayan sallah ishai ya shigo.
Suna falo ana fira yayi muna sannu da zuwa tare da tambayan su mutanen gida sukace suna gaida shi.
Daki ya shiga wurina ina waya da maryam sai kyalkyatan dariya nake ni kadai a dakin kamshin turaren shi ne ya ziyarci hanci na na dago kai ina kallon shi.
Tare da fadin maryam sai anjima na kashe wayan ido ya kura min na dan wani lokaci cikin dakiya nace wanan kallon fa yace ai nasan baki da kunya.
Duk iya gudun naki bagashi yanzu kin dawo ba nace an dai dawo dani indon ta nice ai natafi ke nan ban dawowa wanan gidan da ba a san darajan mace ba.
Maimakon inga ranshi ya baci sai naga yayi murmushi yace goya ki kike son in dinga yi ke nan a bayana ina yawo dake ina fadin ga matar so na komay ?
Ka taba ganin wanda ke goya matar shi a baya ya nuna ma duniya don yana son ta sai dai ya nuna ma duniya kulawa da matan shi a fili.
Kai ya kada min kawai yana fadin wanan bakin mai farsan sa bata farshe da kyau ba gurin wanka.
Bayan fitan shine haniyan su ta kirani na dauka da kunya tare da gaida ita take ce min khadija ashe kun dawo yanzu yake fada min dawowan ku.
Nace eh mama mun dawo dazun tace daga yau na hane ki da barin gidan mijin ki idan ma wani abune ki kirani ko kizo nan wurin mu.
Nayi mamaki da kikai hakan khadija kin nuna min baki dauke ni uwa gare ki ba har yanzu da zaki sa kafa ki fita zuwa wurin yan uwan ki wani kasa.
Nace mama ba hakana bane ta tare ni da fadin kada dai ki sake yin wanan gangancin barin gida da yara haka koma may ye ki fada min ko ki zo wurina.
Nace na gode mama don Allah kiyi hakkuri tace ya wuce ki faki gaba mukai sallama na kashe wayan tare da fadi a fili nace ina zan iya haka mama ai abin kunya ne a gare ni in kai korafin dakin wurin ki ko yaushe.
Washe gari maryam tazo tunda safe ganin yan uwana ta dade dasu tana fira kafin mu koma dakina da ita.
Muna shiga tace min yar iskan mata kin sa mijin ku karamin haukacewa duk da boyen hakan da yake yi wa mutane amma kana ganin shi ko jin maganan shi zaka san baya cikin hankalin shi.
Gado na fada nace ai ke kan gulman ki yayi yawa wallahi duk kin rushe min plan dina naso sai ya wahala sosai kafin ya gane inda nake din.
Tace da ya kwanta asibiti ke kinga yadda ya tayar da hankalin shi ai Yusuf yace min kece maganin shi don ba a taba yi mai haka ba.
Nace maryam kin san da na yarda shike nan haka zai min sheri ya hanani karatuna na zauna nayi nazari sai na fahinci don ya hana Nafisa fita ne ya kirkiro da wanan dokan a kaina.
Tace shima dai wallahi ina zai hada ki da wanan jahilan zaman gida ba ilimi sai tarin jahilci ai karatun mace bawai don aiki kawai ake son tayi ba.
Yana taimakawa rayuwan yayan ta dana mijin ta da ma alumma baki daya karatu ga mace kamar ba gari tallafine.
Nace barshi kawai shi bai gane hakan gani yake kudi suna iya sayen komai da kowa ni bai san zuciya na bai mutu ga abun wani ba.
Wallahi maryam harga Allah ban so dawowana gidan nan ba don komai ya fita raina wallahi tace ke ki bari ko dai yar buzaye ta gama dake ne.
Kai na kada nace ba zan dauki alhakin ta ba koda tayi ban sheda ba kuma ni kin gani nan yanzu duk wani zancen wani asiri ya fita min a kai don Allah keyi ba mutum ba.
Kawai dai ni rayuwan tsarin gidan ne bai mun ba maryam ace mace bata da sani rana ga miji ko wani jin dadi sai idan miji yana da bukatan ta.
Maryam bai fa san damuwan mutum ba shi ko ka fada shi yana ganin kudi sune maganin ko wani matsala na mutum a gidan nan .
Maryam kin sanni kin san halina ni mace ce mai son a kulani amma shi sam rayuwan shi bai san ya lalashi mace ba ko a wuri bukata duk wani abinda ke fada da shawara da ake bani nayi maryam duk a banza.
Sai yanzu nake gane cewa haka yasaba dashi ga matan shi na farko bai da wani damuwa dasu sai ta kudi baida lokacin su ko na diyan su sai dai ya baka kudi kayi ko may nene .
Nasan akwai matan da haka rayuwan su take su dai bukatan su ga namiji shine kudi babu wani jin dadin rayuwa.
Kudi kan nasan akwai su don yanzun haka ina da kudi a dakin nan ni kaina ban san ko nawa bane haka kuma ga account dina don baida keta wurin kudi gaskiya to amma a baka kulawa mana.
Na nuna mashi ni kudi basu bane matsalata ba ranan da namiji zai ware ya baka kulawan shi sai kullun cikin uzuri dare ne kawai zaka kebe da mutun ko shi a uzurce ne.
Tace ikon Allah wai ni khadija ban san halin ki ba wasu nacan suna neman hakan ke kuma ga kudin hakan bai maki ba koda yake banga laifin ki ba tunda ba auren kudi kikai mai ma ba.
Yanzun ai dole ya canza nace Allah yasa sun riga da sun koya mashi haka lokacun da mukaje kaduna sallah da yake dan zama a gida tare damu.
Da kunne na naji Fati tana gulmana wai ni kamar wata fitsarara banjin kunyan zama da miji ko yaushe ina makale dashi.
Maryam tace ke wani amsa kika bata nace bance mata komai ba don nafahinci bata san ciwon kanta ba ita.
Naso mu zauna mu fahinci juna amma hakan bai yuyuba a tsakanin mu don ita bata yarda da kowa ba.
Mun dade muna hiran matsalolina da maryam inda ta dan bani shawara sai dai ban fada mata komai ga irin abinda na fahinta dan zuwa garin mu danayi ba.
Bayan tafiyan maryam na fito wurin bakin na muka dan taba hira akai kiran sallah naje nayi la,asar na fito na shiga kitchen laraba ta biyo ni.
Nan muna aiki muna hira take banu labarin ai babu zaman lafiya tunda na tafi tsakanin shi da Nafisa kulun jidali ne akan yara da kuma zancen fita.
Yasa tsauraran matakai ashe akanta ranan da bakin ta take fadin wai ke ce kikai mata asiri dan kada ta zauna lafiya da mijin ta.
Nace kuma dai ita bata da aiki saina asirine a gidan nan wai wani riba ta samu akan hakane da har yanzu bata saduda ba.
Mun gama mun gyara part din na wuce zuwa part din shi na gyara ko ina banyi mamakin samun part din kamar tun gyaran karshe dana yi yake haka ba ba wani gyara a cikin shi.
Sai da na gyaro ko ina nasaka kamshi don har karni naji dakin yana min na rufo kofan ashe ban sani ba yanzu ni kadai ce keda key din dakin a hannu na.
Sai da na fito naji nafisa na fadin aiko a kwaita wato ni nawa key din ya karbe ya barwa wanan banza nata a hannun ta zai dawo ya fada min abunda yake nufi.
Kamar in wuce ta sai wata zuciya tace daina kyaleta na juyo nace ba komai yake nufi ba illa dai yarda ne ban taba daukan mashi komai a dakin ba kila ke bai yarda dake bace yasa ya karbe key din shi.
Kin san mutum shike sayawa kan shi mutunci idan bai sa ido ga abin wani ba waya sani ko kin masa halin bera ne a dakin.
Tashin hankali nan ko ta hau jidali zaginta dama irin na tab tasha ne daga zagin iyayye sai bakar ashar mai muni nace baki da maraba da yan tasha zama dake ma zunubi ne wallahi
Mace ba sanin Allah ba addini ba ilimi sai jahilci dake cin ki da bakin kishi ki koma ki san Allah zai fi maki ko dan tarbiyan yaran ki.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/19/21, 6:32 AM - Xxxxx: Bayan na gama tanadar komai dana san zaiyi amfani dashi har abinci na jera mashi saman d/table na dawo part dina na samu yan uwana bakina dasu Altine suna hira.
Zama nayi a wurin su kafin lokacin sallah ya karaso ban wani dade da zama ba time yayi na mike na shiga daki wanka bayi kafin alwala na fito.
Bayan na idar da har isha,i na zauna na gyara jikina tsab a cikin doguwar rigar mai kyau don sune kaya na in bada naje kebbi nake kokarin saka atamfa kulun ba a dan kwana goma sha danayi can.
Laraba ce ta kawo Al,amin wai yana rikici na karbe shi muka fito falon muka zauna muna dasa fira Altine tace yaron nan fa yanzu wayo yayi sosai don yasan yayi kwana biyu ba tare da mu ba.
Ina kokarin ciro nono in ba yaron nake fadin wai baba kayi wayo inji gwago kasan dangin uwar ka yanzu ko kabar su gwago.
Na dago kaina ina dariya a yadda Altine ta tsura min ido yasa na fasa dariyan ina kallon ta tace wanan tafiya kamar an canza ki ne baki daya.
Haka ake son mutum yaje gida aga canji a tare da shi ba irin zuwa gidan buzuwa ba dariya zancen ta ya bani nace kai anty ho.
Bamu dade da zama a gurin ba Altine na cikin magana sai ya shigo part din namu gaida baki na tare da tambayan su ba dai wani matsala ko ? .
Bayan sun gaisa ne ya juya ya fita mukaci gaba da hiran mu bai dauki wani lokaci ba mai tsawo da fita sai fa kiran shi ya shigo min a lokacin kira uku gana hudu na daga kiran da sallama.
Yace ki zo ki bani abinci mana sai ya kashe wayan ina shirin fadin ai abinci da duk wani abinda zaka bukata yana nan na aji mashi su sai naji ya kashe wayan nan take ban samu bakin magana ba.
Sai da ba dan bata lokaci wurin har na dan ci abinci na mike zuwa bedroom dina dogon rigan jikina na shafa ma oud kala kala sai body spray dana fesa a gabobin jikina dakyau.
Na fito na nufi wurin shi inda na samu yana waya na juya zan wuce bayan na dan tsaya bai gama wayan ba.
Muryan shi naji yana fadin ina kuma zaki je bayan nace ki kawo min abinci in ci abinci na d/table tundazun na fada a wani irin yanayi.
Yace ba gani ki zuba min mana na fice daga dakin na barshi a ciki ban dade a gurin ba sai gashi ya fito daga dakin .
Ya abincin baci gaba da zuba mai na gama tare da hada sauran kayan a guri daya sai jug din zobo dana sabo garin mu dana hada mai na matsa mai dashi a gaban shi.
Ya kalli jug din tare da fadin wanan may ye a cikin nan din zan bashi amsa sai ga Nafisa ta fado gurin kamar an jefo ta dakin tace Samad gurin ku nazo dama dakai da wanan yarinyar.
Don ke baki iya sallama bane idan zaki shiga wuri ko may ye hakan kikayi yanzu tace ba a koya min ba don bashi ta kawo ni nan ba yanzu.
Nace amma dai ke jan a binciki addinin ki don ragage ne kin ga don Allah malama ki bar nan don na gane manufar ki da kike muna hakan a ranan girkina ne kadai kike muna wanan dabian haka.
Do kawai kiga kin birkita muna farin cikin mu zuwa bacin rai saboda haka yau dai baki zo a sa,a don nariga da na gane nufinki a hakan
Ji wanan dama har wani farin ciki kike dashi a gidan nan miji dai kike kokarin cusa kanki a gare shi kuma baya yi dake yar iska.
Dani dake yanzu ai ansa wa miji ya daina yayi a gidan nan don ko makaho ta laluba yasan gwanatin ki ta kife a gidan nan sai yan dabaru kuma.
Oh dama burin ki ke nan wallahi komai asirin ki dole ki barni don na damaki na shanye yarinya na juya gurin shi nace kaji ke nan da kunnen ka har tana ikirarin da asiri a gaban kowa haka ?
Yace ke ku rabani da wanan shirmay haka Nafisa bar nan don Allah don ba lokacin ki bane yanzu tace nasan ba lokacina bane amma kasan ina da daman shigowa nan duk lokacin da na ga dama.
Wallahi karya ne baki isa ba idan kuma kin ce karya ne ki kara muna haka kiga abinda zan maki a gidan nan.
Kin mata kike kika saka wanan dokan a gidan nan kuma dayake nasan gaskiyan hakan na tsare wanan dokan don may ke ko yaushe kike karya wanan dokan.
Lalai wuyan ki yayi kauri a gidan nan har ni zaki kafa ma dokan ganin mijina komay kai wanan matar da abin dariya kike mijin ki ko mijin mu dai miji kan ai ya tashi a naki sai dai a jam,i don mata uku cur take mallaka daidai kuma kike da kimar kowa a cikin mu har ma mun daraki a wani fannin a gurin shi.
Wani irin bakin ciki da takaicina ya rufe ta a lokaci daya nan ta fara irin zaginta na yan iska zagin banza da baida dadin saurara ko fada.
Ke ya ishe ki kifice nan ai gaskiya khadija ta fada kin zo nan don ki bata muna farin cikin mu ne kawai tace zuwa nayi don in ji dalilin da zaka bar mata key din sashen ka ka karbe min na wurina.
Gyaran part din kike ko may iyakan ki kizo ki kwanta ki tashi ki barshi a haka na ko so kike in bar maki key din ki kwashe min duk wani abin kwarai kiyi gaba dashi.
Iyakar ki min sata ko bincike ki samu abinda na aje ki gaba dashi wani kallo tayi mai kamar zatayi magana sai kuma tayi shiru don babu abin fada.
Yanzu sherin da zakai min ke nan yace may ye sheri a cikin wanan maganan ba gaskiya na fada ba ko kina tunanen ni mahaukaci ne da zan bar maki key dina yanzu ?
Ke nan itace mai gaskiya a gare ka don baka san barnan da take maka ba a boye yace ban taba gani ba ko ji ke ko fa na gani kuma na sani.
Dama tunda an riga da an gama dakai yanzu ai baka ganin laifin ta tunda ta asirce ka ta gama.
Wai ke may kika gane da zancen asirin nan ne baki da tawakkali ga Allah sai zancen asiri may asirin naki ya tsinana maki a rayuwa ki wai ?
Ki yarda da Allah shine mai yin yadda yaso ba wani can ba wanan ma abin kunya ne kina fadan haka a bainan jama,a ke baki jin nauyin haka ko kunya ?
Kunya may zanji ga abinda nasan kinayi ina yi duk akan mutum guda kuma muke tin shi nace kike dai yi don ni banda lokacin haka ga Allah na dogara da al,amarina .
Karya kike yar iska muna fuka karuwan cikin gida mai kwatar mazan mutane nace ikon Allah ai kwace miji ke aka sani da wanan.
Ke da kika raba miji da matar shi har da uwar shi da iyayyen shi Allah bai yarda ba yanzu kike ganin baki na kan hakan.
Ke kana jin abinda take fadi banyi mamaki ba don ke kin fada tunda dama haka ake fadi nace ba gaskiya aka fada ba yanzu mai kika zo yi nan din ?
Ke karamar yar iska dake da wa yanda suka turo ki kimin fitsara duk maganin ku zanyi a gidan nan mu zuba dani daku a gani.
Nace muga alheri gida dai na shigo shi ba fita sai dai ki mutu akan kishi ba abinda za a fasa kuma tace.
Wallahi karya kikeyi sai kin bar gidan nan koda tsiya anga wuein ci an lake kamar kaska ko to fita kamar gobe ne wallahi don, , , , .
Ke dan Allah ya isa haka ban son wanan shirmay tunda kin fadi abinda ya kawo ki kuma kinji amsan ki.
Ki fice min daga shiya tun kan ranki ya baci a gisan nan tace bayi kan ka bane don kai min haka a yanzu zaka dawo a hannuna mu zuba dani daku a ga wanda zai fasa.
Ta juya ta fita daga part din ya juyo yana kallo na ina zaune na harde hannaye na saman kirji na nima ido na zuba mai yace ke ma na lura kun zama daya da ita yanzu.
Nace yar rainin hankali ce bata tashi fitinan ta sai ranan da tasan nice da girki na dade da fahintar haka a gare ta dama.
Ke din yanzu rai kike gyara min da kike guduns komay ni ba gudun ka nake ba kaucewa nayi ma abinda nasan zai iya jawo muna matsala ai.
Yace oh tunanen ki ke nan ashe nace haka shine mafita ba tare da samun sabani a tsakanin mu ba tunda ka hau a lokacin.
Na tura mai plate din abincin da na zuba a gaban shi nace amma bai dace kace tana maka sata haka a gaba na ba ya ja plate din dakyau a gaban shi tare da fadin ke daban ne a gare mu ai gara kiji ki san may ke gudana don ki kula.
Lokacin da ta yaye ni ta tafi dashi ai kina gidan nan amma baki sani ba don haka kina gama abinda kike yi ki dinga rufe min kofa na don Allah.
Haba sai kace ba matan ka ba dai ai yanzu ba zata kara ba tunda tasan ka gane hakan har ka dauki mataki yace baki san halin Nafisa bane.
Zama nayi ina kallon shi tana cin abincin shi hankali kwance na tsiyaya mai ruwan zobin a kofi na mika mai ya ansa ya kurba tare da lumshe idon shi yace ke kika hada wanan din nace eh baiyi bane yace yayi mana sosai.
Akwai abinda zaki hada da hannun ki baiyi dadi bane ya karasa kurbe sauran dake cikin cup din ya aje min lokacin ne nace mai gidan SJJ sun aiko min da katin gaiyatan bukin gidan su wani sati.
Kamar baiji abinda nake fadi ba ganin ya gama ya turo min plate din a gabana na mike tare da fara tattara kayan abincin.
Kallona yake yana jin wani irin son kasancewa dani a lokacin wani abu yake ji yana fisgan shi na dago kai nace ka gama da wanan jug din ne in dauke.
Bar min zan kara anjima yace amma dai kin san babu inda zaki yanzo ko nace kamar ya ba abinci kace inzo in baka ba dama, na kuma baka.
Ke nan har yanzu baki hakkura ba daga gudurin ki na dauka wanan zancen ya wuce ai.
Dago kaina nayi na kalle shi da zuman in bashi amsa sai dai yadda ta tsure ni da idanuwan shi yasa nayi saurin dukar da idona kasa.
Ina sauraren ki idan hakkurin da mukaje har gafin ku muka baki bai maki ba yanzu sai ki fada min abinda kike son inyi kuma , ?
Deedar nasan wani lokaci ban kyauta maki amma kuma ni ina ganin duk abinda kikaga nayi da dalilin yin shi gare ki sai dai ke kin kasa fahinta na ne ko kadan kina ganin haka kamar tauye hakkin ki ne a gare ni.
Har cikin zuciya na na dauka ke kadai ce macen da zan iya sakata tayi abu tayi shi ba tare da korafi ba, ina alfahiri dake a ko ina Deedar bana son rashin fahinta haka yana shiga tsakanin mu akoda yaushe.
Ki tausaya min don ceto rayuwana daga halaka ke kadai ce kike iya tsayawa ki fada min gaskiya in fahinta ya zama min alheri kuma idan nabi shawaran ki.
Kada ki ruguje muna tubakin da muka fara dorawa dake a gidan nan wanda nake fanin zamu girbi alheri nan da dan lokaci kadan idan Allah ya yarda.
Ki daina fadin kalman banson ki khadija ina son ki ina matukar kaunar ki babu macen da keda kaso irin naki a zuciyana.
Na yarda dake dari bisa dari khadija ke din jaruma ce da bakowa ke gane hakan ba sai wanda ke tare dake yasan hakan ki yarda dani khadija don jiki nake kamar ba a matsyin matana kawai na dauke ki ba a matsayin yar uwa ta jini da zata share min hawaye.
Ban kara gaskanta hakan ba sai rike min wa tan nan yaran da kike ganin kamar na cuta maki ne ga yin hakan ni kadai nasan manufata nayin hakan danayi gare ki don ingancin tarbiyan da yaran nan zasu samu daga gare ki nake kwadayi wanda Alhamdullahi yanzu na fara ganin hasken hakan a gare su sosai.
Ajiyan zuciya na sauke daga inda nake zaune don jin yadda yake tsaro min magana daga bakin shi wanda ko wacece dole ta hakkura da wanan kalaman nashi.
Sai naji bazan iya fada mai komai ba a lokacin tunda har ya zauna yana fada min zuciyar shi haka yau ga kuma kalamin dana dade ina son ji a gare shi ya furta min da fatar bakin shi.
Sai naji bai kakata in rike shi haka yadda nayi niya ba a zuciya na don duk sai naji ya wanke laifin shi a gare ni ya zama dole gare ni in kara hajircewa gurin taimakashi a gidan.
Ba zan so in dawo da abinda ya wuce ba gare mu yanzu sai dai mu dora a inda muka tashi a faki gaba kuma don nasha alwashin ba zan sake kyale Nafisa tana juya mu yadda taga dama ba a gidan.
Ganin nayi nisa a tunane yasa ya dan rankwafo inda nake zaune tare da hura min iska yana fadin ko baki yarda da duk abinda na fada maki bane yanzu.
A sanyaye nace na fahinci manufar ka yaya AA insha Allahu ni kuma nayi maka alkawarin duk naga gyara a lamarin mu zan sanar dakai koda a cikin hikima ne da yardan Allah yadda zaka gane.
Rungumini yayi zuwa jikin shi yana mai sauke nunfashi tare da matse ni sosai a jikin shi kamar wani zai kwace ni a jikin nasa.
Wani iri duniya muka lula naji tankar ace daga ni sai shine a wana rayuwan babu sauran wata a bayan mu in gwada mashi so na sahihi duk da ko a yanzu ma hakan bai baci ba ai don kowa gyara kansa yake a gurin miji tunda har na fara samun wanan yabo a bakin shi.
Sake ni yayi yana fadin kai kayan nan ki kara ba yara nono ki dawo daga kai nayi na kalle shi ido cikin ido wani irin abu naji a zuciyana nayi saurin dukar da kaina kasa.
Don nauyin shi da kunya daya kama ni a lokaci guda da kyar na iya bude bakina nace daka bari har yan uwan nan nawa su wuce zaifi.
Ummm, ummmu yace kada ki kawo wanan maganan yanzu ai sun san gidan ki suka zo kuma aure kike yi jin dadin hakan ne ma yasa kika gansu nan.
Nace to shike nan amma nima kayi hakkuri da abinda nai maka a baya ba daidai ba matsalan rashin fahintar junane na fada a cikin sanyin murya tare da dan marairaicewa.
Rungumo ni naji yayi cike da tausayin junan mu yana fadin ki yarda dani Deedar ban rike ki da wani manufa ba a raina idan kin ga haka ki fahinci inda na dosa kafin ki yanke hukunci ina sane da komai da ke faruwa a gidan nan.
Sai dai ban taba daukan zaki dauki hakan a cutarwa ba gare ki don haka don Allah ki gafarce don baki taba min musu irin haka ba har da guduna zuwa wata uwar duniyan.
I am so sorry ga abinda ya faru ba wai na fada don in hana ki karatu ki bane ya isa haka yaya AA na fahinci komai wallahi kaima don Allah ka yafe min .
Kai ya girgiza min yana murmushi yace khadija ke nan babu abinda kikai min na batanci da zaki ce in yafe maki komai kikai min kina da dalilin yin shi tunda ban fada maki manufana ba.
Idan ma kin man na yafe maki har ga Allah don ban taba rikeki da magana ba kara lafewa nayi a jikin shi ina sauke numfashi.
Can na sake shi nace zan duba yaran yaya kada suga na dade ban dawo ba yace ke dai kina gudun sherin mai shegen saka idon nan Altine.
Da kyat na samu na bar wurin shi zuwa kasa ya bini da kallo yana sauke murmushi a fuskan shi tare da kada kai yana fadin kai mata sai a hankali kamar ba ita bace ta so ta birkice min yanzu.
Koda na koma na samu ma yaran suna goye a bayan su don haka na shiga nayi wanka na kimtsa jikina dakyau naso in kara ba yaran nono amma sai Altine tace in wuce ai akwai madaran su yana nan idan sun tashi.
Koda na shiga motsin shi naji a bayi yasa nagane yana ciki wurin daya dan baci na kara gyarawa sai lokacin naga zoben shi dana tsunta a kasan gado danake shara yana fitowa da bathrobe a jikin shi sai dan karamin towal da yake tsane ruwan kan shi dashi yace har kin dawo ashe.
Nayi sauri nace mai sai yai saurin fadin bance ba don Allah a rufa min asiri kada asani kwana maraya kuma nace da momy da ranta da Abba zaka kwana maraya kuma .
Yace ai sin yayeni tuni yanzu sabbin uwaye na samu kuma wanan zoben naka ne na kawar da zancen da tambayan shi.
Kallo zoben yayi yana mamaki yace ina kikaga wanan zoben dana dade ina neman shi a dakin nan karkashin gado na gan shi dazun ina shara na bashi amsa.
Takowa yayi zuwa inda nake ya karba yana juya zoben yace nasan ba kowa yai min wanan aikin ba sai Nafisa zobe ne na tsari da aka bani ta sani takuma san amfanun shi sosai gare ni ya karba yana sa zoben a yatsan hannun shi naga yana wani addua lokacin da yake zura zoben.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/20/21, 6:35 AM - Xxxxx: Satin bakina daya suka koma gida da rarin abin arziki daga gare mu sai albarka suke saka muna mun rabu tare da kewan juna inda suke kara jadda min kula da zumunci.
Bukin gidan SJJ ya tashi ban dauka yana tune da zancen ba sai ana gobe yake ce min daya shigo part dina da dare, kin fasa zuwa yiwa Adam din ne kara ?
Ni na dauka baka barni bane ai yace ai ba zan hanaki zuwa rama abinda akai maki ba kema sai dai kin san dole zaki kai abin buki ko ?
Nace ai shine kuma don dai kasan wanan ba taran kudi suke nema gudun mawa ba yanzu yace idan kinyi tunane sai ki fada min.
Abinda zaki kai godiya nayi mai ya fita tun wanan lokacin nake shawaran abinda zan kai wa amarya gudun mawa idan zan tafi.
Altine da nake fadaw tace shine matsalan mu yanzu sai mutum yace sai ya rama alherin da akai mai nace ba wanan a tsari na abu dai wanda ba zasu zata ba nake tunane komai kankantan shi.
Karshe dai mun yi shawara na hada kaya masu kyau irin na Anty Salbiya sai wani sarkan gold mai kyau da tsada da awarwaro a cikin kit din su da zan ba amarya gudun mawa.
Maryam ta shigo washe gari muka shirya har laraba da Altine zuwa gidan bukin mun samu taron sosai wurin hajiyan gidan.
Ban dade ba muka mika abinda muka zo dashi tare da fadin zamu tafi tace haba tun yanzu jana tayi har dakin ta dani da maryam tare da su Altine.
Muka zauna tace naga kamar wanan sakon naki mai muhinmanci ne a gare mu tana magana tana bude ledan ta ga abinda ke ciki.
Ikon Allah duk wanan abin haka kin ga mutane basu fahinci hakan ba don ba wanda ya maida hankali gurin gyara min kawan tawa.
Don Allah kiyi hakkuri ki dan muna bayanin komai kafin ki tafi na fara mata bayani a cikin kunya tana fahinta na sai godiya take min kan hakan.
Ta bude ledan da akai wraping din sarka da awarwaro a cikin sa sai naga ta bude ido tana fadin wanan ma ya isa khadija ki koma da sarkan nan ko ni ban saya mata shi ba don mijin ta ya saka mata su a laife sosai.
Anty ai wanan nawa ne don ta na kawo shi tayi dan shiru kamar za tai magana sai kuma taja baki tayi shiru ta mike ta fita dan jima kadan sai gata ta dawo dakin tare da amaryam da wasu dauke da kayan motsa baki a cikin tire.
Bayan sun fitane tace da amaryam na kira kine kiwa anty khadija godiya kinga abinda ta kawo maki tana nuna mata kayan.
Murmushi tayi tana zama sai da ta shafa sarkan ta dago tace kai anty nagode sosai wallahi wanan yana da kyau matuka.
Ta shiga godiya kayan ne hajiyan ta fara mata bayani tana sune kai don kunya ta kara fadin anty nagode.
Bamu taba komai ba daga cikin abinda suka kawo muna a dakin nace zamu tafi tace haba wai kodai har yanzu baki sake damu bane a yan uwa muka dauke ki fa gidan nan.
Nace ba haka bane anty a koshe dai muke shiysa tace to tunda ankawo saidai ku tafi dashi ranan jumma,a akwai walima da yinin buki don Allah kuzo khadija don ranan zan hada ki da Alhaji ku gaisa.
Don bai sanki ba sai dai yana jin labarin ki a gurina nace Allah ya kaimu mukai mata sallama muka tafi tana muna godiya.
Maryam ce ke jan mu a motar sai da muka dauki hanya tace humm,umm masu kudi suna inda suke wallahi duk wanan gidan ita kadai ke mulkansa.
Altine tace nima abinda nake ta tunane a raina ke nan tun dazu don Allah ji daki kamar wani shagon sai da kaya.
Ni ba abinda ya ban mamaki sai yadda suke ta yaba kyautan ki gare su nace nima maryam shine ke bani mamaki ai.
Muna shiga gidan buzuwa ta fito zasu fita ita da wata maryam tace wanan ashe ta fara fita bakar yawon nata ko nace dama ina zai iya tsare ta a gida ko yaushe tunda ta riga ta saba da fita kullun.
Ranan Jumma,a bamu je gidan SJJ da wuri ba sai bayan azahar muka isa gidan yau ma kamar ranan haka aka tare mu tana nuna ga yan uwa da abokanta wai ni sister din marigayitace kishiyar ta kuma yar uwar su.
Mun fito wurin waliman ne mun saurari nasiha da akayi inda aka fara hada hadan buki bayan waliman mai kidan kwarya suka dauko ta kida inda mata ke ta rawa da sauran su mudai muna gefe daya a zaune.
Sai abubuwan karamawa ake shigo muna dashi ina magana da Altine maryam ta ya futo ni tare da fadin kinga buzuwan ki gidan nan gaba daya muke kallon inda suke zaune.
Ita da wasu mata da gani masu ji da kansu ne a garin nan suka dasa hiran ta sai naji na tsawala a gurin don kasancewan Nafisa itama a gidan bukin.
Maryam ce ta fahinci hakan tace ita sai ta tambaya taji alakansu da ita nace haba dai akan may zaki tambaya.
Ashe zancen na a ran maryam sai ji nayi tana tambayan hajiyan ta juya tace wacan kike nufi tace eh wallahi ban san ta ba sai dai ina ganin gayan wata yar uwar maigidan nan ne sabuwa.
Maryam tace itace kishiyar khadija ai tace ita wanan din haba ashe a gidan ku na taba ganin ta ina ta tunanen a ina na santa tunda na ganta dazun tun shekaran jiya tana gidan nan yaude ne suka jima haka ai.
Bayan fitan hajiyan ne maryam tace yanzu ai munji dahir can mukaji ana sanarwa daga na hannun daman hajiya wai ana bukatar khadija matar AA perm sec ta fito fili nata ne.
Wani iri naji a gurin maryam tace da gaiya hajiya ta sa a fadi hakan don ki fito Nafisa ta ganki wuri yayi tsit ana sauraren fitowana a filin ga masu kwaraya sai kirari suke min.
Hajiya da kanta tazo taja hannun zuwa filin take na balle jakka ba dai wani rawa nakeyi ba na azo a gani amma sai wuri ta dauki ihu Allah ya taimake ni nazo da kudi a jakka na ina zubawa ana zuba min.
Koda na fito filin rawan ba Nafisa a inda suke daga ita har kawayen nata sun bar gurin mun dan dauki lokaci a gidan kafin ai muna iso gurin maigidan mu gaisa.
Yana ta zuba min godiya tare da fadin ki saki jiki kin zama yar gida kin bamu abinda ba kowa zai iya bamu ba a dalilin ki.
A raina nace badon ka nayi ba ai da zaka taimakawa yaya Adam ya daga zai fi min wanan godiyan da kake min a yanzu duk da yanzu AA na ma ya Adam din kokari sosai sun fita cikin gangin talauci ana danawa dasu sosai.
Biyar daida mu ka dawo gidan motar Nafisa da take amfani dashi muka gani a haraba don ta sayar da wancan na farko daya bata yanzu wani ya kara bata sai dai ko kusa bai kai nawa kudi da daukan idon jamma,a ba.
Muna shiga falon su Altine dauke da kaya niki niki itace zaune falon da mutanen ta kai ba dan kwali sai hayaniyan su ke tashi gidan.
Jin motsin mu shigowa ya dawo da hankalin su a gare mu har mun dan wuce ta tace yau ni naga inda ake cusa kai babu kwarjini a garin nan.
Nace ashe ke makin san gayyan na anya kika je babu gaiyata don kin gani da idon ki kai abin takaici wai mutun yaje bukin da babu gaiyata don rashin sanin ciwon kai.
Wallahi karya kike wai har ke za a kira da matar Samad a fili a cikin matan shi wa kike nace ai da aka kira keda kike wata tsiya a gurin shi sai ki fito tsakiyan filin.
Wata ce ke tare ta da fadin kaiya Nafisa wanan ai ba zancen fasawa bane don rai ya baci ai ita ma tasan ba zata hada kanta da ke ba.
Ke kuma wacece a cikin kayan miya na tambayi matar nace koda yake ba abin mamaki bane an gama cin kasuwa da madam yanzu kuma ku aka jaji bo muna.
Haka dai zaku kare wurin akaita sheri har da bukin da babu gaiyata kai girma dai ya fadi idan an sanshi maryam sai yau ta saka baki a zancen mu tace da an san dashi ne ai.
Tsiyan abin ba a san kunya ba da girma ai da ba, a zubar da mutumci ba ku dai kan kunyi hasara wallahi abin kunya masu buki suce basu san wanda ya gaiyato ku ba.
Ke har kina da bakin magana kullun kina yawo gidan kawa kuna fita yawon iskan cin ku da kuka saba wanan sai dai a fada maku ai.
Don mun san komai har gidan bokaye kuke zuwa suna amfani daku don kawai su biya maku bukata da bai yuyuwa.
Wanan maganan ya ci masu rai sosai take gida ya kaure da fitina security ya shigo yace su zo su fice a gidan Nafisa tace ba wanda ya isa ya kore mata mutanen ta.
Waya ya daga ya kira AA a fusace yace kada su bar mace ko daya a gidan nan kafin yazo nan suka tasa su a gaba sai da suka bar gidan cikin kunya sai faman zage zage sukeyi.
Wai an wulakanta su maryam bata dade ba ta tafi sai bayan sallah magariba ya shigo gidan rai bace falo ya kira mu ya tara mu yana tambaya.
Ta koro mai karya da gaskiya ta fada mai ya juyo gare ni jin tun da ta fara bayani banyi magana ba yace naji nata ke ya akayi fada min naki.
Nan na kora mai duk abinda ya faru ya juya wurin ta a hasale yace banta sanin ke sakarai bace haka sai yau.
Wai ma uban wa kika tambaya da zaki fita Nafisa na fada maki ba zan dauki wanan shashanci ba na yawon banza a gidana.
Nafisa wai ke wata irin mace ce da baki da tunane har kije gurin bukin da ba a gaiyace ki ba kina zubar da kimar ki ana maki gori akan shi.
Ke baki san komai ba a rayuwan ki sai shashanci da tambadewa kina bin tsofin zawarawa kuna zubar da mutuncin ku a gari.
Kana nufin goyan bayanta zakayi ne ko may yace kina rufe min baki ki barni da abinda nake jina raina ko sai ranki ya baci wurin nan.
Mace bata iya ba kanta tarbiya ba ta yaya zata ba yaranta ta tarbiya tace yanzu ne kasan banda tarbiya ko may ?
Na dade da sanin haka ya fada a hasale zatai magana ya daka mata wani uban tsawa wanda yasa har ni ma na kadu a wurin.
Mikewa tayi zata bar wurin yace dawo mara mutunci kawai wace bata san ciwon kanta ba bari kuji duk da ke kadai ce a cikin su ke da wanan halin duk ranan da irin haka ya sake faruwa da dayan ku sai na ba maishi mamaki a gidan nan.
Ku bace min da gani ya fadi daga karshe kowan mu ta mike zuwa part din ta yana gurin yana ta fada a cikin hasala har muka shige.
Nasan tasan bata da gaskiya ne ko may ta gani tayi shiru don bata zaci abin zai juye haka da ita ba idan da dane ba zaiyi wani fada na azo a gani ba.
Sai bayan sati biyu ne yake fada min wai yana ganin bukin Zainab ya tashi nayi mamakin jin haka don ni gida naso inyi hutun da muka samu sai ga zancen bukin zainab kuma ya taso.
Jin da sauran lokaci yasa na yi amfani da damana na shirya zuwa gida in duba su shiri sosai nayi inda na so su Altine ma suje gida da laraba su duba gida kafin buki sai dai ba zai yuyu ba haka muka fara shirin tafiya tunda nayi sa,a ya barni.
Sati mai kewayowa muka ziyarci gida da yarana sadiya kawai muka zo da ita bamu zo da Ihisan ba don suna makaranta har lokacin.
Munji dasin zuwa gida don muna da lokaci har sati daya ya bani inyi a gida haka ya bani daman ziyartan tan uwa da abokan arziki da aka dade ba a hadu ba.
Tafiyan mu da kwana biyu ne ya dawo gidan ta shigo tana fada mai wai ta dafa mai abinci yayi mamaki amma sai ya dauka don bani gari ne take son burge shi da hakan ita ma.
Tana zaune a gefe bayan ta zuba mai duk da abincin bai cika mai ido ba haka ya daure zai ci ya jawo plate din zuwa gaban shi bayan ya wanke hannun shi da ruwa.
Allah Allah take taga ya fara ci yana saka hannu kamar ance ya dubi zoben nan daya saka wanda na tsinto mashi a kasan gadon shi.
Wani sirirn hayaki yaga yana fita daga jikin zoben sai da gaban shi ya fadi sai ya dake ya kara kai hannu zai dibi abincin karo na biyu.
Abinda ya faru da farko ya kara faruwa dashi zoben yana fitar da hayaki yace wanan tsohon yayi gaskiya.
Plate din ya tura mata gabanta yace bisimillah ki fara ci don naga kamar baki ci ba ke ta kakaro murmushin yake tace nikan ai dam nake yanzu naka ne kawai ya rage.
Ido ya tsura mata tare da mikewa ya zagayo inda take ya duka ya dibi abincin tana zaune tana kallon shi.
Zuwa lokavin tayi mutuwan zaune ya dibi ya kai mata a bakin ta kai ta girgiza mashi take ya daure fuska yace ko kici ko in saba maki yanzu wurin nan.
Hakkuri ta fara bashi akan ba zata ci ba yace Nafisa kashe ni kike son yi ko may da kika zuba min mugun abu cikin abinci na ?
Ta fara kamay kamay ita bata zuba mashi komay ba watau ita bai yarda da ita ba ke nan ko ?
Nan suka fara rikici a tsakanin su yace kina tunanen yanzu zaki iya shamta nane ki yaudare ni kar nake kallon ku a gidan nan.
Duk wace ke sheri na sani kyale ki kawai nake yi nan dai ta hau borin kunya inda take shiga banan take fita ba yace kici idan kin san baki zuba wani mugun abu a ciki ba .
Karshe dai ya kore ta dakin yace kada ta kara zo mai daki idan bashi ya nemay ta ba tunda ke jahila ce baki dogara ga Allah ba.
Ranan dai kunya ma ya hanata ko wani dogon motsi a gidan wayan sabuwa ta nema tana fada mata abinda ya faru.
Tace ke yaya akayi ya gane amma wanan mijin naku na yarda da madam ke fadin wahalan banza muke akansu gaskiyane asiri baya kamasu tunda har ya gane wanan shirin namu.
Nandai na sha zagi a wurin su sun dade suna kulawa da warwarewa a tsakanin su shiko yana can rai bace ya rasa matakin da zai daukar mata ya huce.
Kasheni Nafisa take son yi ko may may na rage su dashi a gidab nan da take neman rayuwana tabbas Yusuf dasu hajiya sunyi gaskiya.
Yau ba don na kasance da khadija a rayuwana ba da Allah kadai yasan irin cuta min da Nafisa zataci gaba dayi ba tare dana sani ba gidan nan.
Barci rabi da rabi ya yi shi ranan tun safe ya fice gidan tare da taurara mataki akan Nafisa ba tare data sani ba.
Yusuf yana ganin shi ya fito da safe haka yake tambayan shi ko lafiya kasa fada mai yayi a lokacin don bai san may zaice mai ba.
Sai zuwa yamma ne da Yusuf yaga damuwa yayi mai yawa ya tasa shi a gaba take fada ma Yusuf din abinda ya faru.
Yusuf yace kaga zoben tsohon nan ke nan ya wani yamuste fuska yace Deedar ta tsinto min shi a kasan gadona nasan kuma hakan sherin Nafisa ne ba kowa ba.
Yanzu wani mataki ka daukan mata don ya kamata ka daukan mata mataki yanzu tunda bata da niyar bari.
Na riga na dauki mataki ko sai ta raina kanta a gidan nan don ba saki a tsarina wancen ma danayi bakaji irin fadan da Abba yai min ba ranan.
Don haka a cikin ruwan sanyi zangasa ta sai ta raina kanta gidan nan Allah yasa ta bari indai Nafisa ne ina ganin da shi idon ta ya bude dama yusuf yace.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/21/21, 7:42 AM - Fatima Amarya: Satin mu daya a gida muka dawo sai dai tunda na dawo naga sauyin gidan ya juya a yanzu gaba daya na rasa fahintar komai daga mutanen gidan.
Ban kara gaskata hakan ba sai da ta shigo wurina da safe yana fadin kulun ku dinga saka min abincin dare a part din nan.
Saurin dago kai nayi don jin abinda ya fadi kasa hakuri nayi sai da nayi magana nace wanan kasan ba zai yuyu ba tunda ga matar ka a gidan.
Bani kadai bace matarka kasani sai dai idan wani fitina kake son ka dauko min kuma ga yin hakan yace idan ba zakiyi abindana sakaki ba sai ki bari.
Zan fita waje na dinga ci a can nace idan hakan yayi maki nace indon abincin da zakaci ne ba sai ka fita kaci waje ba.
Yace shi zai fita fuskan shi babu walwala a cikin shi da alama ma bai karya ba zai fita gidan lokacin bishi nayi da kallo ina nazarin shi a raina.
Ajiyan zuciya na sauke tare da fadi a fili Allah ya kyauta koma may nene don banda amsa komai a yanzu.
Naki tasowa da wuri ne don kada in karbi girki a ranan yasa sai biyar muka taso na dare dayake motar mai lafiya ce Alkasim ne driver ya iso da wuri bayan gudun dayai ta shararawa damu a hanya mun iso ana sallah magariba.
Haka yasa ban damu da wani girki ba a ranan duk da nasan idan na tashi yi koda tsiya yadda takeyi zanyi nima.
Wanka nayi na shirya na fito falo wurin su laraba dake faman cire tsaraban da muka dawo dashi tana adana shi inda ya dace.
Zama nayi a cikin rashin walwala a tare dani sadiya da ke kwance nake kallo yadda yarinyar ke dada girma yanzu shi kuma kan dake da matsala yana kara girma sosai.
Naji tausayin ta sosai a raina ga ta dai yarinya ce duk da ba tada alhakin kowa a kanta amma Ubangiji ya jerabe ta da wanan lalurar a rayuwan ta.
Altine ce ta fito daga dakin du tana dauke da mami a hannun ta wuri ta samu ta zauna a gefe na tana fadin kamar in koma minnan nan naku nake ji.
Ban taba zuwa jahan ba a baya sunan girin kaidai nake ji ashe gaein babba ne haka ban sani ba gaku da abunci kala kala a garin.
Duk da naga kunfi maida hankali ga doya itace abincin mutanen garin sosai duk gidan da mukaje shine za a sarafa muna a wani launi.
Nace haba dai inda dai muka je kikaga hakan ai yanzu wasu saboda wayewan kai basu faye son doyan ba sai dai abincin zamani .
Bayan mun dan taba hira ne na mike na fita daga part din nawa gidan nake zagayawa inda tun a falon naga yadda ya koma tankar babu mata a cikin shi.
Din ina ganin ko kara ba a taba a gidan baya dada shara da kazantar da akayi ko ina na gidan kai na girgiza, tare da kwala wa Altine kira tana fitowa nace tazo ta gane min wanan wulakancin.
Nan Altine ta shiga zuga ni har naji raina yana tafasa sosai kira ba kwala ma samiha dake kwance a dakin su taki amsawa.
Part din na fada nace samiha da yanyala su fito tare da su Altine su gyara gidan nan tas ku wasu irin kazamai ne haka kamar ba mata ba zakuyi rayuwa haka a cikin kazanta.
Ku ke nan baku iya gyaran wuri sai dai ku bata kuna jira azo a gyara maku don haka ku fito ku taru ku gyara gidan nan yanzu.
Daga bayana naji muryan Nafisa tana fadin ba zasu gyara ba ke wacece da zaki shigo har nan ki basu umurni wai suzo suyi maki aiki.
Aiki aina kowa ne don su suka bata amma na saka su Altine da laraba a taru a gyara tace wanan ke ya dama don mu ba matsalan mu bane.
Waya na daga na kira AA ya dauka bayan ya dan dade yana ringing yana dauka nace mai cikin ladabi dama na kiraka ne don kaiwa matar ka magana gidan yayi mugun datti ko da muka dawo.
Mun samay shi ba a gyara ba tun tafiyan mu shine yanzu na saka samiha da yanyala dasu Altine su gyara amma ga Nafisa tace wai ba zasu gyara ba.
Yace bata wayan ko ki saka wayan a hand free yadda zata tajini na saka ban yarda na bata wayan ba yace Nafisa kina jina idan mutanen nan bazasu aiki ba kamar yadda aka sakasu suyi su bar min gidana kafin in dawo.
Yana gama magana na juya na fita na barta a wurin da takaici na ba abinda take kallo sai sauyin da take gani a gareni.
Sai mamakin yadda na juye a lokaci daya komai nawa ya canza kamar ma kada inje garin mu taga na wani kara kiba da haske sosai sai yau take ganin abinda su madam suka sha fada mata a kaina.
Wani iri taji a ranta tare da fadin shike nan bakin bakin su madam yaja min tabbatar wanan abin ga yarinyar nan yanzu yaushe har ta bunkashe haka ne wai ?
Lalai tayi sake da yawa da idon ta ya rufe bata hango haka ba tunda wuri anya yanzu kuwa zata iya taron wanan da take gani a gaban ta zata iya shawo kanta kuwa ?
Don idan batayi da gaske ba tana kallo zata kwace mata komai nata a gidan tasan dai idan kyau ne ko fari take rudan mutane dashi wanan ma ba baya ba haka kuma ga ilimin da take dashi wanda take gani dashi take kara amfani wurin ganin bayan ta a gidan.
Kai anya nan gama ko zata iya karawa da Dijan nan da yanzu gaba daya komai nata ya sauya ya zama na hamshakan matan da ake iya damawa da ita.
Duk kokarin ta wurin taga ta shiga sahun matan manyan abuja abun ya faskara sai ta dan jona dasu kwana biyu sai su bare ko don suna daukan ta bare ne ita haka ke faruwa.
Dama ance mutum bai ganin illar shi abinda bata gane ba shine halinta na rasgin tauhidi ke kore mata mutane.
Don da ta dan kwana biyu da kawance da mace zakaji ta fito mata da kudirin ta tana tambayan ta ko tasan gidan wani boka ko malami da aikin shi ke ci kamar yanka ?
Ko tace ita kishiyanta take son kashewa ko ta haukata ta ko ta batar da ita ta shiga duniya a manta da ita gaba daya ire iren wanan maganan ke ba matan da take son mamuwa tsoro suke gudun ta kwana biyu ta daina jin su.
Hakane yasa ta kula da mata masu zaman kansu a Abuja don su basu da lasisi haka take gare su ko ina ta fada rataya ne.
Ina tsaye har suka gyara falon zuwa wajen gidan da ko ina dake da bukatan gyara a gidan suka feshe ko ina da kamshi gidan ya dawo daidai.
Nafisa ko tana daki ta kasa fitowa sai tunane take tana sakawa tana sancewa don komai ya juye mata a lokaci guda a gidan ga samad dake wanan fushin ko kallon inda take baya yi.
Har Ihisan laifin take ganin ya shafa don ya shigo yarinyar na kiriniya ya daka mata tsawa taki dainawa ya kamata yai mata dukan tsiya a gabanta.
Idan da dane sai dai yayi dariya ya wuce idan tana irin wanan halin ta manta ita abinda taiwa uwa da yaranta a baya data hanasu shakuwa ma da uban su gaba daya.
Idan ya shigo ko kallon yarinyar baiyi yanzu sai dai ta sha alwashin ba zata yarda ya mayar mata da ya wani part ba da abinta zata zauna.
Nikan muna shiga nayi wanka tare da dauro alwala nayi sallah nafito kitchen na nufa don dora girkin dare da kaina don ina son burge maigidan yau.
Komai na hada sai da akai la,asar ne na fito na koma daki na dan jima a ciki kafin in fito in duba girki na sai da na tabbatar komai yayi yadda nake so.
Na dawo falo wurin su Altine muka zauna kallo suke wanda ni ba gane kan kallon ban dade da zama ba na mike zuwa ciki don gwada wani abinda Anty salbiya ta taba bani ban taba amfani dashi ba.
Sai yau tunda nice zan karbi girki a gidan nayi kamar yadda tace min ina gamawa na zauna bakin gadona don inyi waya da maryam don naga bata shigo ba.
Mun dan dade muna wayan inda take fada min zancen su da Suraj ya tabbata don karshen satin nan zasu je gurin iyayyen ta a tsayar da magana.
Murna nayi mata sosai tare da fatan alheri gare ta nace zamu koma a innuwa daya ke nan tace ke dai bari ni abin mamaki ma yake bani.
Ba a mamaki da ikon Allah nace baki ganina yanzu Allah ya dora ni akan Nafisa a gidan nan abinda kowa ke min fargaba a baya.
Idan Yusuf yana fadin zan iya sai inga ta ina zan iya da wanan shedaniyar ashe abin daga Allah ne kaidai ka dogara gare shi kaga aiki da cikawa.
Khadija in banda abinki in bamake ba ai wanan buzuwan tana da saurin kawarwa don gata nan da abubuwan fada kala kala tare da ita.
Matar da bautan ubangiji ma sai taga dama takeyin sa bata san wani abu ba sai shirka da bata ina cikin sauraren maryam ne ban san shigowan shi dakin ba don ban masan lokaci yaja haka ba.
Fuskana na kallon cikin dakin na shagala da wayan sai ji nayi an dafa ni ta baya a firgice na juya yana shi na gani a tsaye yana min wani irin kallo a cikin gajiya.
Dawa kike waya haka kika shagala nace maryam ce na kira muke waya don naga bata shigo ba yau tasan kuma mun dawo.
Tana fada maki ke nan wanan satin za a je zancen su ko ban bashi amsa ba nace sannu da dawowa don ban yarda yaji akan may muke magana.
Jin bai amsa ba yasa na dago kaina ina kallon shi shima kallon nawa yakeyi nace lafiya kake min wanan kallon ko wani laifin nayi kuma ?
Ba tare da ya amsa min ba shima yace wai may kika ci haka a gidane kika bun kasa da yawa kin wani koma wata big madam dake , ?
Kallon shi nayi ina murmushi nace kila dai idon ka ne ya gane maka hakan ni ban wani canza ba ai danaji a jikina ko ?
Kara matsowa yayi kusa dani yana gyara corth din shi daya rataya a kafadan shi da kyau yana wani lumshe idanuwan shi yace.
Kun gudu kun barni ina kewan ku daga ke har yaran ya fada yana zama a kusa dani nace ai gamu mun dawo ko har wani dadewa mukayi balle kace kayi kewan mu.
Kanshi ya dora akan kafada na kamar wani karamin yaro yana sauke ajiyan zuciya yace nayi kewan ki wallahi a kusa dani ban taba sanin dadin mata biyu ba sai wanan tafiyan da kukayi.
Najini kamar wani maraya can Deedar ajiyan zuciya na sauke tare da fadin kai yaya banda abinka kai dake da wata a gida shine zakace mun barka maraya kuma.
Tura fuskanshi yayi cikin kaina yana sunsunan dadaden man kitson da akai min kitso dashi tarre da rike min hannaye na.
Yace kowa da matsayin sa a gare ni don haka ki yarda dani I miss you kwana biyun nan da kukayi sosai wallahi.
Wani iri naji har cikin raina a lokacin ina mai jin dadin wanan furcin nasa a gare ni sai naji kamar ba wanda ya kaini a gare shi a lokacin.
Muryan shi naji cikin sarkewa yana fadin wanan kamshin naki yai min dadi wallahi yana kara dora kanshi a saman kaina yana shaka.
Kai na girgiza tare da kokarin jaye kaina daga gare shi ina fadin ka tashi ka watsa ruwa ka ji dadin jikin ka kada wani yazo nan ya samay mu a haka kuma.
Korata kike yine daga nan da sauri nace don may zan kore ka gani dai nayi ka gaji kana bukatan hutu yanzu kafin a kira sallah.
Murmushi yayi tare da mikewa tsaye yana gyara kayan jikin shi da suka dan takure daya zauna ina mamakin yawan tsabatan shi har nakan yi tunane wai yaya yake da matan shi masu kazantar tsiya ?
Mace tun zanin safe dashi zata wuni a jiki wata kila ma ta kwanta haka dashi don ko washe gari dashi zaki ganta ta tashi.
Muryan shi ne ya katse min tunane na da yace may zan samu inci ne yau tun safe rabo na da saka wani abu a cikina dana sha dan cock .
Nace abinci na nan na girka ma sai dai idan wani abin kake so kuma a dafa ma yanzu yace zan dan sha tea kadan idan zan samu kafin anjima inci abincin don hanji na ya warware.
Nace barin kawo maka kafin ka fito wanka yace dakin kyauta min ya juya ya fice daga dakin ajiyan zuciya na sauke bayan fitar shi dakin.
Wai yau nice AA ke fadin yayi kewan mu da bakin shi yake fada min hakan tare da nuna min da gaskiya yake fadi yadda naga jikin shi yana mutuwa dan zaman da yayi a kusa dani.
Mikewa nayi zuwa kitchen na hada mai ruwan tea tare da daukan kayan na nufi part din shi baya ciki yana bayi sai kamshin mai dadi ke tashi a dakin.
Kayan daya cire na kwashe na aje inda muke aje kayan dauda ina shirin fita daga dakin ne ya fito daga wankan muryan shi yasani juyowa yana tambayan ina tea din yake ?
Nace yana dinning na aje ma nan zaki kawo min in sha yunwa nake ji sosai nace kai mai mata har uku biyu a gari zaice yana jin yunwa haka.
Kallona yake mai kama da harara na fice ina dariya yace zaki dawo ai yana murmushi na dawo dauke da kayan a gaba shi na hada mai komai ya zauna a bakin gado ya na sha muna dan taba hira sama sama.
Na dauka Nafisa zata shigo tace na shiga mata lokacin ta duk da saura yan mintuna lokacina ya cika sai dai banda yadda zanyi dole in bi umurnin shi.
Na mike bayan ya gama sha ya miko min kofin yana fadin yagode sai dan zufan daya fara tunane nayi nace wai ita wanan wata irin mace ce da zata bar miji haka ya zauna da yunwa.
Allah kadai yasan yadda yake zama da yunwa da take ita kadai a gidan gasu da yawa saidai yawan ya zama na banza gareshi don babu mai iya dora abinci idan ba yunwa yaci su ba sun kwamce suyi tashan ruwan bakin shayi.
Ina fita ya sauke ajiyan zuciya tare da tunane a ranshi irin saukin kan dake gare ni a dai barni da fadin magana ko yaya yazo min a bakina kuma yanzu ya saba da wanan.
Wanda maganan nawa daidai yake da amsan abinda zaka fada min sai dai ya lura yanzu ina dan rage yaba magana kamar da can baya.
Daki na koma na kara shiyawa don yau nasan zan dadana kuda na a wurin shi yadda yake mazarin nan akaina sai Allah.
Ana sallami isha,i ya dawo gida ranan shiya kirani da kansa kwaliya na caba sosai kamar mai shirin fita wani wuri a lokacin.
Na dauki kayan abincin shi zan fita Altine ce ke min wasa wai su rufe kofa ne na tafi ke nan ina dariya na juyo nace lalai kan idan kunji shiru ku rufe.
Zaune yake a dinning din tunda na shigo ya kura min ido kamar tsohon maye har na iso gareshi da sallama a bakina.
Kallona yake tundaga samana har kasa ya dawo da idon a fuskana na fara gaida shi da wuni ya amsa min tare da fadin in kama maki ne.
Ina iyawa na bashi amsa na aje kayan tare da jan kujera daya na zauna akai nace may zan fara zuba maka bayan na gama jera mai abincin .
Yace koma may na samu don yau ina son in cika cikina da wanan girkin danayi missing na kwana biyu daga nan sai in dora da abinda aka hanani din dazun.
Abinci kadan na zuba mai don nasan ba zai ci ba tunda yana ganin naman kai a gaban shi don yana son shi sosai da bindin sa.
Plate din abincin ya jawo a gaban shi yana fadin kin kara kyau sosai wanan kwaliyan kamar mai zuwa buki nace bako bukin zan tafi ba duk wanan kwalliyan don ka nayi ko zan koma amarya yau.
Kai ya gigizs yana fadin har kina tunanen komawa wata amarya ce ke da kulun sabuwar amarya kike a gurina ban taba ganin macen da ta haihu ba kuna komai nata yana nan a yadda yake.
Wani kallo nayi mai nace dama tunanen ka ke nan ashe barin kara zake damtse na furin gyara kada watarana kaga gazawana .
Ban tunanen akwai wanan ranan a rayuwana ya bani amsa yana debo abincin sai naga ya dan tsaya yana dube duben hannun shi can ya girgiza kai yakai loma a bakin shi tare da bissimillah.
Ashe aune abincin yakeyi ko nima na masa wani sihiri sai baiga komai ba don yanzu tsoron kaidin mata yake gaba daya ba Nafisa kawai zata iya mai sheri ba kowane akan wanan.
Yana ci muna hira wanda hiran akan yan uwanane yake tambayana a cikin hikima nan yake fadin na hana Alkasim din ki komawa ne don a sama mashi aiki ya fara daga baya sai ya koma ya karo karatun shi.
Naji dadin jin wanan maganan don zan su mutanen da muke tare da dadewa suyi alfahari da samu na nima a duniya tun yanzu.
Bayan ya gama na kwashe kayan zuwa part dina na rage wanan kayan zuwa kayan barci na gyara duk wani sassan jikina nayi masu saida safe na fito.
Yana kwance yana jira na ban bata lokaci ba wurin ba bori kai ya hau ranan nice na nuna masa gwanintana ya rasa duniyan da yake ciki sai wani lokaci muka sarara ma junan mu nan ma bamu kwanta ba hira muka dasa akan bukin da zamu tafi.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/23/21, 7:58 AM - Fatima Amarya: Mamaki nake a raina yadda naga Nafisa ta koma wata saliha a dan kwana biyun gashi kuma ba wani hurda dake hadashi da ita a gidan.
Rana girkin nafisa ne duk da na saka mai abinci kamar yadda ya umurce ni sai dai ban kai ba har karfe tara na dare sai ga wayan shi ya tambayan abincin shi.
Dan jim nayi kafin in ce ina zuwa bayan wayan na mike na dauki basket na nufi part din shi a falo na wuce su suna hira na hau sama wurin shi da abincin.
Kallon mamaki ta bini dashi har na shige waya ta dauka ta kira Sabuwa tana fada mata cin fuskan da yake shirin mata don ita a zaton ta har da kwanan ta ya bani duka.
Ki bishi a sanun mu gane mai yake nufi da dakatar dake da yayi a girki tunda bamu san manufar shi ba kan hakan yanzu.
Kuka ta saka mata tana fadin sabuwa Samad ya cuce ni idan yace haka zai min yanzu kan wanan yarinyar baya ganin kowa da mutumci sai ita kadai a gidan nan ga laifin nawa har yana son shafuwar ya ta yanzu don har ihisan haushin ta yake ji gaba dayan mu yanzu.
Ke ma kin san wanan aikin asiri ne idan tace tanan harda yara zata hada sai muma mu koma kanta da yaran ta ga baki daya mu zuba mu gani.
Sai dai ke ma kina da laifi Nafisa don may zaki haifi ya kuma ki nuna mai kina kyamatan ta haka a fili ko Allah zai iya jarabtan ki kan wulakanta wanan yar da kika yi ai.
Sabuwa na kasa saka yarinyar a raina don zuciyata ta kasa hakkura da ita a matsayin ya ta ki duba yadda yaran nan nata yanzu suke tasowa a gidan nan kamar wasu diyan turawa dasu .
Shegu ko kaine wa bakai masu kallo daya ka kawar da kan ka garesu saboda shiga rai da yaran ke dashi farat daya na rasa gane wa suka biyu da wanan kyau din cikin uwar da uban.
Nakasa shegu zamuyi su koma abin kyamata suma ga jama, a ba tana sallo ta haifi na miji ba mu kai dan banza a sakar mashi illa a rayuwan shi.
Yadda uban ma zaiji dan ya fita rashin gaba daya kinga dake da ita mai kurin tana da namiji kun zama daya ke nan sai dai idan samad ya mutu a yanzu kan dan ko mun nakasa shi tafiki kaso a gidan.
Nan dai sukai ta kula sheri wanda kullun cikin kulawa suke basu ganin alfanun shi kuma bai sa sun daina abinda sukeyi din ba.
Tunda na shiga falon na aje mai abincin tare da gaida shi da wuni na juya zan koma part dina naji ya ce dani dawo ki zauna har in gama ki tafi.
Wani kallo nayi mai a cikin mamaki ya sake fadin ki zauna nace in gama ko nace amma kasan in munyi haka mun wuce gona da iri don ba hakki na bane yin hakan.
Babu ruwan ki umurni na baki ba neman ba,asi ba ko wani dogon bayani ya fada don katse wani zance daga gurina din .
Don dole na ja kujara na zauna ina fuskantar shi yana cin abincin ba tare da wani yayi magana a cikin mu ba.
Na yanke zan tambaye shi may ye dalilin sakani yin hakan bayan ya san banice da alhakin kulawa dashi ba ranan ina yi ina dan satan kallon kofan dan barin Nafisa a falo da nayi nasan kuma zata biyoni itama taji dalilina nayi mata hakan.
Sai dai har ya kusa kammalawa bata babu dalilin ta yasa na kara gaskanta da wani abu akasa wanda ni ban sani ba dayake faruwa a tsakanin su.
Yana gamawa na mike jikina ba kuzari yace idan kin hada kizo ki dan matsa min wuya na don yai min tsami yau sosai wanan kan ban san lokacin da nace haba yaya AA kafasan bani ce da alhakin yi maka komai ba a yau.
Kada mu shiga hakkin wata koni idan an min hakan ba zanji dadi a raina ba gaskiya don may kuma zan biye maka mu fasa halaka.
Yace kin fini sanin Allah ne khadija nasan maganan mai girma ce tunda ya ambaci sunana haka yau na bude baki da kyar nace na daiga ba zata ji dasin ganin haka bane idan ta shigo ta samay ni a nan din.
Zaman ta kikeyi ko nawa nace naka a sanyayye yace idan ba zaki min abinda na bukata ba to ki fice min don Allah ban son dogon magana yanzu.
Daukan kayan nayi da niyar fita yace ba zaki mun massage din ba ke nan dole na aje kayan hannu na na nufi inda yake gabana sai faduwa yake kamar wani zai kamani a lokacin
Dan jin nayi kafin in fara sai dai can na dora hannu na a hankali na fara mai sai naga ya gyara zama yana wani lushe ido sama kanshi ya nuna min ba tare da yai magana ba na kai hannu saman kan ina dan cakula mai a hankali.
Jin shitun yayi yawa yasa shi yin magana na dai ga kamar dole kike min kina iya tafiya yanzu yace yana mai sauke ajiyan zuciya.
Nace gaskiya kan a tukure nake tunda nasan ba hakkina bane yi maka haka yau don gudun zargi ina mun dade da gama wanan maganan .
Ai na dauka kina da fahinta amma tunda bayani kike son ji jeki zan maki bayani indan na shirya sai dai ba yanzu ba don kin gama bata min rai da gardaman ki nan.
Akan gaskiyana nake magana don ko ni ba zanso kai min haka ba kaga yanzu da Allah yasa ta shigo duk abinda ta fada a kan mu bamu da gaskiya ai.
Shiru yai min bai ce komai ba don ya matukar kuluwa da ni a lokacin dukawa nayi na dauke basket din kayan dana hada nafita daga dakin.
Kai ya girgiza bayan fitana tare da nisawa yace watau ita komai nata akan tsari yake ke nan da Nafisa ce dadin hakan zata ji sosai ba wani tunanen wani abu.
A falo na samay su zaune da yan uwanta ina fitowa tace Allah dai ya tsine wa mai satan kwana kiyi abinki yanzu lokaci ne gobe ko ance kiyi ba zaki gwada yi ba ai.
Ban kulata ba don dama nasan haka ne zai biyo baya don babu gaskiya ga wanan maganan saboda ta fimu gaskiya yanzu.
Ina shiga su Altine dake zaune suna hira tace kin dawo nace eh sai da nakai kayan kitchen na wanke na fito ina zama nace gaskiya dan uwan ki na son ya ja min magana in rasa bakin bada amsa.
Ya dai san yau banice da girki ba amma ya saka min dokan nice zan dinga bashi abinci ba tare da yai min bayanin komai yadda zan fihinta ba .
Yanzu gashi ina fitowa ta fara zargina tana fada min magana kan hakan dole na kyale ta don banda bakin bata amsa tunda babu gaskiya a ciki.
Maman biyu tunda kinga haka dole akwai wata a kasa gaskiya haka kawai da hankalin shi ba zai ce maki hakan ba ya kamata ki gane hakan.
Itama fa wurine bata samu ba da hakan zatai maki ai koda kuwa babu wani dalilin mai kwari zata so tai maki hakan Allah ne ya taimakeki ya doraki a kanta ai.
Don haka zagewa zakiyi yanzu ki nuna mai naki daman akan shi koda sun shirya a tsakanin su kin riga da kin kara kafa gwaunatin ki a zuciyar shi.
Ke dai mace ce mai ilimi ba sai na fada maki abubuwan da zakiyi ba yanzu dama naki ne a gidan nan ki fito da kalar ki ta gaskiya ga kowa na gidan nan ta yadda zasu fahinci rayuwan ki.
Akoma ana kyamatar ta acikin wana zuri,an ga baki daya kowa ya gane cewa gwaunatin buzuwa na kama karyane a baya tayiwa mutane.
Maganan Altine ya tsaya min sosai a raina don haka na fara neman mafitan hanyar da zanbi in nuna nawa hikimar data ce.
Ban dade ba na shige don in kwanta sai dai barcin yaki zuwa min da wuri yadda nake so sai can dare na samu yazo min duk da haka na samu tashi nayi nafila na mika bukatana a wurin Allah.
Washegari tunda ba school muke fita ba kitchen na fada na hada mai lafiyayen breakfast kafin wani lokaci na gama duk abinda zanyi.
Wanka na shiga na fito na shirya tsab dani falo na fito na samu sanyi ya hanasu fitowa daga daki tunda yau din san ina kitchen din.
Dakin na leka nayi masu ina kwana suna kwance tare da yaran sai dai ba barci sukeyi ba suna kwance ne suna hira nake fada masu zan hau sama a fito lafiya sukai min.
Na samay shi yana shirin jikin shi sai da na karaso inda yake nayi mai ina kwana ya juyo yana amsa min tare da fadin ya kuka tashi lafiya nace mai ina isa inda yake sa botturn din rigar shi.
Amsa nayi na karasa saka mai yana tsaye yana kallona na mika mai ties din shi yana sakawa na nufi gurin takalma na dauko mai wanda ya dace da shigar shi sai dana dan goge na aje mai a gaban shi.
Kallon takalman yayi yana dan murmushi nace ko takalman basuyi ma bane yace sunyi mana ina dai mamakin yadda kika san su zan saka.
Na sani mana tunda nasan shigar ka yanzu dan zama da kai a gidsn nan abinci na table yana jiran ka idan ka shirya.
Ai baki karasa shirya ni ba may ya saura na tambaye shi yace turare ko na juya gaban mirrow din shi na dauko turaren da yake amfani dashi idan zai fita na fara fesa mai a jiki.
Na gama tare da dago kai na kalle shi ni yake kallo na dan daga mai yatsu na biyu alaman yayi kyau yace ya gode na juya zan fita dakin ina kuma zaki yace yana kallo na.
Na gama abinda ya kawo ni ai kada in zake da yawa ba aikina bane taimaka maka kawai nayi ai juyawa nayi zan fice naji ya jawo ni zuwa jikin shi yana fadin ai baki isa ba sai kin karasa na fada maki.
Jin zafin yadda ya juyo ni nayi yasa na dan sake kara kadan nace wasshh mane ni yayi a kirjin shi yana fadin abu biyu zuwa uku ya rage maki ai kafin ki tafi nace.
Ai da ina zaton ka gama shiryawan ne ya sake ni yana miko min tsitsiyar hannun shi alaman in daura mai agogo a hannun nakama hannun na daura mai.
Bayan nagama nace sai na biyun kuma yace muje dining ki bani abincin tare muka fits zuwa dining din sai dana zuba mai ya fara ci ba dama in tafi don nasan wani matsala ne kuma yana cin abincin shi a tsanake har ya kare ya goge bakin shi.
Mikewa yayi nima na mike tare da fadin na ukun fa ko nagama ke nan yace da sauran ki saura nan yana mai nuno min gefen kumatun shi tare da fadin saura sallama.
Na gane nufin shi amma sai nace ba yanzu naga ka goge bakin ba ki ban kiss in tafi kina sani makara fa ba a kuma sanni da makara ba.
Kai na girgiza na nufi fuskan shi in mashi yadda yake so din ina kai bakina na sake mai kiss na juyo Nafisa na shigowa gurin.
Take ya daure fuska yana fadin may ya kawo ki nan may na fada maki akan part dina zaki fice muna ko sai na bata maki rai yanzu gurin nan.
Kamar zatai magana sai kuma ta juyo ta kalle ni ta juya ta fita rai bace nace haba yaya ko mai tayi maka bataci wanan hukinci ba daka dauka haka akanta.
Wani kallo ya watso min nace haba dai kuma a gabana kake fada mata wanan kalaman haka yaya babu kishiyan da zata so ai mata haka a gaban kishiyan ta fa.
Yace ni zan tafi sai na dawo a dawo lafiya nayi mai ina ci gaba da tattara kayan abincin zuciyana fam da tunane na dauko zuwa kasa.
Nafisa ce a main falo ta cika tayi fam da ita ina karasowa take fadin gurin ki ya cika an wulakantani a gaban ki yadda kike so.
Sai kijira zuwan naki ke ma don ba kyale ki zanyi ba akan hakan nace duk da ban san tsakanin ku ba idan kin tashi sai ki dauki raina tunda a hannun ki iko yake.
Kin gani nan nasan abinda nakeyi don ni ba jahila bace irin ki da za aiwa dan uwa abu inji dadi don nasan kambun namiji murdawa ne nima ban wuce haka a gare shi ba.
Amma ki sani umurni nake bi ni yanzu don mijinane a inda ya tsayar dani anan zan tsaya ban kari ko ragi don haka ki shiga taitayin ki ki lalaba ku shirya da mijin ki don ni ban san tsakanin ku ba yanzu haka.
Daga haka ban jira in ji amsanta ba na shige part dina na barta nan tana bakaken magana tana amaye zuciyar ta ko zata ji sanyi daga abinda take fuskanta.
Karyawa nayi na kwanta barci na samu nayi sosai sai zuwa sha biyu saura na falka tare da duban lokaci ga har rana yayi ke nan.
Wayan dake gefena na dauka ina dubawa sai naji ina son kiran shi a lokacin samun kaina nayi da danna mai kira wata zuciya tace mayvzan fada mai idan nakirashi din har wayan ya shiga ban sani ba ina can ina tunane a raina.
Sai muryan shi naji yana fadin Deedar ya akayi ne nayi saurin fadin ya aiki yace gashi muna tabawa lafiya kuke nace eh dama na kiraka ne in tambaya may za, a dafa maka yau.
Dan murmushi naji ys sauke yace duk abinda kika dafa min zanci don nasan mai dadi ne kamar mai dahuwan nace wani zance ke nan kuma.
Ai gaskiya na fada yau dai nasan ba cin haki ai ko don haka a dafa min komai yayi zamzam yadda zan gamsu dakyau don Allah don shekaran jiya am barni ina santi .
Sai anjima don naji kana son sakin layi ni bashi nakira ka fada min ba dana ni ko a yaushe zamzam nake don haka Allah yayi halittana.
Ai basai kin fada ba da zaki bar girki ki zauna ki samu hutu ai ni dakin kyauta min wallahi kin ga idan na dawo sai nima in raba in samu wanan ni,imar daki ka kwasa.
Dip na kashe wayan don kalaman shi sunfi karfin sauraren kunnuwana bai kokai ga aje wayan ba kiran shi ya kara shigo min sai da ya kusa katsewa na dauka.
Yace don may zaki kashe min waya ina magana nace wayan ne ai ya mutu yace to ya na hutar daku girkin komai za a kawo maku abinda zamuci da daren idan kuma akwai abinda kuke so sai ki min text kafin in bar office din nace mun gode na kashe wayan.
Ranan haka muka wuni muna hira bamuyi aikin komai ba don nace kada su girka komai a gidan basu dai tambaye ni ba suka kyale ni.
Da ya dawo ne aka shigo muna da ledoji kala kala lokacin ina daki laraba tazo ta kirani take fada min an shigo da sako don bata bude ko may nene sai idan nafito nace a bude.
Bayan na fito naga ledojin ne na umurcesu dasu bude nama ne na kaji sun sha hadi sai na rago da sauran kayan shaye shaye sai take away kala kala aka hado muna.
Ganin kayan sun muna yawa nasa laraba takai ma su Nafisa wanda na ware masu ita da Ihisan suka dauka na dauka zata bayar a dawo min dashi sai naga laraba ta dawo ba tare dasu ba.
Shirin tafiya buki muka shiga yi tun ana saura kwana uku mu wuce sai faman shiri muke part dina yayin da ita part din su ko a jikin ta.
Sanin halinta yasa ban damu da ita ba don zama muke ba mai shiga harkan wani a gidan ba ina kwana ba sanin halin da dan uwa yake ciki zama dai irin wanda bai dace ba ga addini.
Banda yadda zanyi don dole nima na koya na iya koda kuwa dan uwa zaiga abin cutawa dan uwa na har gara nima nakan dan tanka idan naga wani abinda bai kamata ba a gare su.
Ana gobe tafiyan mu ne ya kiramu a falon kasa kan tafiyan nan dai ta nuna ita bata san da zancen ba ai yace ba dole sai kin sani ba kamar yadda kika ce saidai ya zama dole duk wanda ke gidan nan yayi tafiyan.
Saboda haka ya saura gareki gobe karfe takwas zaku kama hanya ni sai alhamis ko jumma,a zan shi go idan Allah ya kaimu ban son jin komai ya fito daga gare ku kuje kuyi abinda ya kaiku ku dawo.
Ya bude briefcase din shi ya fara ciro kudi a ciki ya mika mata sannan ya miko min nace mu gode Allah ya kara rufa asiri.
Kallo ida take zaune tana faman juya kudin yayi yace yanzu ke bakiji kunya ba mutum haka baisan komai ba sai gadara da jahilci.
Yanzun kuma may nayi yace a gidan ku ba a koya maki godiya bane ko baki ji yadda yar uwar ki tayi godiya ba yanzu.
Samad har abin yakai ka zage ni a gaban wanan yace wanan din tafiki mitumci da sanin ya kamata don gashi tayi a gaban ki.
Yana fadin haka ya mike yabar gurin ta bishi da kallon mamaki kafin ta juyo kaina tace gurin ki yau ya cika a gidan nan sai dai naki kadan ne na baki nan da dan lokaci kadan.
Dariya nayi nace tunda ke ce da lokacin a hannun ki ga lokacin nan yana fadin kanshi wanan shirmay na fada maki yanzu ba shine mafita ba gare ki.
Da zaki koma gs Allah ki dawo hanya madaidaciya a zauna lafiya mutaru mu rufawa kan mu asiri da mijin mu da zaifi maki.
Ina fadin haka na mike ina cewa mudai mun gode Allah ya kara rufa mai asiri duniya dalahira don gobe akara muna.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/24/21, 7:50 AM - Fatima Amarya: Duk yadda yaso mu tashi da wuri hakan bai samu ba don fitan da mukayi tun safe zuwa gurin motar da zata daukan muna kayan dakin zainab din da kayan sobaniya da na hada a nan wanda ba wanda yasan dashi maryam ce kadai ta san da wanan sai yau da ake daure kayan ya gani baidai yi magana ba.
Set biyu yai mata inda idan mun dawo dayan nan gidan ta zamu gyara da dayan don haka shi bamu dauke shi ba.
Sai shabiyu da wani abu muka bar garin da tawaga na na bar maryam a wurin kayan wace ita daga baya zata samay mu kaduna idan an fara buki.
Ban tsaya bin ta kan Nafisa ba don banga alaman kamar zata tafi ba Al,kasim ne zai jamu sai dayan hilux dake dauke da kaya da zata bimu don haka duk a motana mukayi tafiyan .
Mun sauka kaduna lafiya sai dai nayi mamakin ganin duk zumudin zuwan da mukeyi acan kamar ba wani abinda ke faruwa.
Wanan ne karon farko da nazo tun bayan haihuwana wanda yanzu yakai wata ni masu yawa don yarana suna batun shekara daya ne sunyi wayo dosai do , har sun fara takawa.
Abinda yasa ban zuwa kaduna bai wuce abu daya ba shine rashin barkan da Fati batai min har wanan lokacin har wanan lokacin dama a lokkacin da na haihu din ta bugo waya tana fadin ashe an sauka to barka ba wani Allah ya raya ko wani abu.
Hakan baisa na fita zancen yaranta ba don duk karshen wata idan zai tafi nakan bada sakon da za,a kai wa su Affan din da daddy.
Hajiya mama tayi lorafin rashin zuwan mu har ta gaji sai in fake da yanzu karatuna yayi zafi banda halin tafiya ne niko naga zuwan nawa yana takurawa Fati shiyasa na kara dauke kafana.
Ban damu da rashin taron mu da batayi ba don dama da shirin mu muka zo da abinci mu da komai har abin sha mun tanada a bangarena.
Sai dai naji dadin don ashe su Fauziya na gidan hajiyan su ana cewa mun iso sai suka dira a gidan namu har lokacin anty Fati bata fito ba mune kaidai ke ta bidirin mu a ciki.
Baifi awa biyu ba Nafisa da tawaganta suka iso suma sunyi daidai mun gama abincin da nasa a girka aka diba aka kai masu.
Nan gidan ya kici may da hayaniya na riga na fada ma Laraba ta saka ido akan yarana kafin yan uwa na da zasu zo su kara kulamin da diya na don haka ne na hutar da ita ko wani aiki sai kula da yaran kawai.
Munyi sallah na shirya su zasu shiga cikin gida da laraba su gaisa da su momy da Abba inda zasu rika kai dare a can badon komai nayi haka ba don sherin kishiyoyina nayi wanan gudu nai wanan dabaran.
Kamar zuwa na su Fauziya ke jira inda muka fara tsara abinda zamuyi kan bukin sai can ga Fati ta shigo wai ita daga barci ta tashi.
Fauziya ce tace ai da ki bari sai gobe kwa gaisa wanan halin dai naki baiyi ba wallahi ace mutum kullun alamarin sa sai kara lalacewa yake.
Ni dai gaisuwa mutumci mukayi da ita sai da zata fita ne take tambayan yaran nace sun fita kawai.
Daga haka ta fice a dakin kodai ba komai na dan rage jin zafin ta da nake ji a raina din tunda ta tambayi yara ai.
Amma duk da haka batayi wani dadani ba zainab ce ba kunya ta kawar min da tunane na tana tambayana kan kayan da aka saya mata waya na dauko na fara nuna mata inda sauran duk suka rufu muna kallon kayan ina masu bayini.
Binta tace har biyu nace daya a Abuja za a aje mata gidan ta nacan sai dayan azo nan dashi kai amma yayan mu ya fidda zainab inji binta.
Anty Faiza tace har da ita mai bayanin ai badon khadijan ba kina tunanen akwai wanda zai takwasa shi kan haka tunda yaba Abba kudin yin komai.
Ko yanzu Allah kadai yasan irin kai ruwa ranan da sukayi dashi kafin hakan nace wallahi ko anty kamar kin sani harda su kukana sai da nasha da gaba.
Tace ai na san halin mazan nan yanzu sosai don haka muke fama muma dasu ai gara ke ma mun samu yana sauraren shawaran ki ni nawa idan nai mashi zancen sai mun kwashe kwanaki ba shiri tsakanin mu ga ganin laifina da suke duk abinda suka ganin dashi sai suce dan uwan su ne ya saya min shi.
Ban san lokacin da nace dangin miji ai sai a slow ba sai dai idan ka iya zama dasu ne akwai dadi wallahi matsala kaidai kada abinka ya rufe maka ido.
Binta tace watau mu ke nan ko duk aka kwashe da dariya a dakin nace kuka ai yan uwa nane ba dagin miji ba yanzu.
Faiza tace lalai kam don khadija haihuwan tane kawai hajiya mu batayi ba yadda take son ki ma yanzu dukkan mu babu mai fadan nan a gurin ta.
Fauziya tace halin mutum ne ke ja masa so ai don bata so kanta da gidan su ta bar yan uwanta ba nace ni yanzu sai dai idan yaiwa gidan mu alheri su bugo suna fada min amma ban taba bude baki nace kaiwa wani nawa alheri ba duk ko da talaucin gidan namu na rike masu mutuncin su a gurin shi.
Muna ciki motar kaya ta iso gidan nan muka fita zuwa ganin yadda za a sauke kayan sai dai sun bada shawaran a wuce da kayan can gidan Yusuf wanda shima dai a cikin unguwar namu yake.
Sai sauran kayana dake sama suka sauke a gidan na shiga karban key a hannun anty fati na dakin da babu komai ta gama ja min rai ta bani key din dakin akusa da dakin da su laraba suke ciki.
Fita mukayi zuwa gidan Yusuf din dake dan bayan mu kadan aka sauke kayan a gaban mu suna Allah Allah suga kyau kayan.
Sai da na shigo ne zan shiga daki najiyo muryan su na leka dakin ina masu sannu da zuwa ihisan dake dakin tana ganina ta nufo ni sai uwar ta daka mata tsawa .
Kai kina wani shirmay wallahi ina tare muka zo da ita da zan cuta mata da tuni na gama cuta mata ai ba yanzu da alheri ya kawo mu nan ba.
Tace waya sani ko kin cuta mata din don wanan kokarin rabani da diyana da kikeyi haka nace abinda kakeyi shi kake zargin kowa nayi kin gani nan ni ga Allah mahalicina na dogara ba ga wani mutum can ba da shima yake nema a gurin Allah.
Ina fadin haka na juya na bar dakin tare da tunanen yaushe ne wanan matar zata sauya ne tayi saduda tasan Allah dayane a zuciyar ta.
Allah gani gare ka don ina cikin tsaka mai wuya ga Fati babu alaman hadin kai a gurin ta yadda take faman sharewa da basarwa a fuskan ta.
Sai bayan sallah isha,i ne su laraba suka dawo bisa jagorancin momy data rako su gidan sai wani jiji dasu ake a cikin dagi wanda hakan ba karamin dadi yake min ba a raina tunda kowa na son jini na a gidan.
Har umma daba kula kowa take ba momy tace a wurinta sukai magariba zata kwace mata mijin ta don haka take cewa Al,amin.
Washegari bayan mun huta ne naba Laraba tsaraban su ta shiga masu dashi gidan inda babba da yaro kowa ya samu tsaraba na a gidan.
Sai gasu suna layi wurin zuwa yi min godiya tare da sannu da zuwa wanda hakan ba karamin bakanta ran abokan zama na yayi ba sosai.
A raina nace indai kana son a soka ashe gaskiyan Anty hauwa da tace min idan ina son in rabu da kowa lafiya kada in matse hannu na gurin alheri musan man dagin mijina da abokan arzikin su.
Sako har na mutanen zaria dangin hajiya mama sun samu na bada akai mata sai albarka take saka min kan hakan.
Niko da a zatona ban dauka haka abin yake ba don ban so nuna masu haka ba wai don gada su gane ina samu a gurin shi sai take ce min ai matar dake cikin daula ansan tana samu ko yaya ne don haka nuna masu a daula kike don rashin bayarwan shi kan shi matsala ne yin hakan sai yanzu na gane wanda ya riga kwana yana rigaka tashi.
Ban samu shiga gaida sarakaina ba sai washe gari na samu shiga gidan muka gaisa dakin hajiya mama na yadda zango.
Bayan mun gaisa take fadin haba khadija kin dauke kafa gare mu haka har ina murna kin dawo da hankalin mijin ki gida sai gashi ke kuma kina kokarin gudun mu yanzu.
Ina kaduna ina Abuja bafa wani nisa ne a tsakanin mu ba kwarai amma kuke wanan dadewan baku zo gida ba ko yan jikokin nan namu yanzu don su saba damu ai kyazo dasu su san yan uwa ko ?
Hakkuri na bata ban kawo korafin komai ba don taimin uzuri sai hakkurin da na bata akan zamu gyara insha Allahu.
Zancen bukin ta dauko min inda take fadin yara sun zo suna fada min kokarin da kukayi ke da mijin ki sosai an gode Allah yasa albarka ya kara daukaka da nisan kwana a kunyace na amsa da amin mama.
Nace sai zancen gara shine ma ya saka muka zo da wuri don a gudanar da komai yadda ya kamata akan lokaci yace a lissafa abinda ake so gaba daya idan yaso sai ya turo da kudi kafin yazo a saya don shi sai karshen sati yace zai shigo.
Madalla duk da nasan Alhaji ne mai wanan nauyin amma hakan yana da kyau don yanzu lokaci yayi da zasu dauke mai wanan nauyi zan fadawa Alhajin sai ai shawaran abinda za a kai masu.
Nan dai su anty Faiza suka samay ni gurin hajiyan mukaci gaba da shirin da zamuyi dasu haka dai zuwan ya zama min busy bamu da hutu na kan mu sai dare.
Duk yadda nasu in zulle masu indan huta hakan bai samu ba a gare ni don a cikin kwanakin ne akaje yiwa zainab gyaran dakin ta sai dai ina kokarin leka ya Amina na duk wanan ritsin.
Abin gidan yawa sai abin ya koma gulma kuma wai dani kadai suke shawara sun bake sauran yan uwana basuyi dasu.
Yau ya kasance ranan kamun zainab yan uwa da abokan arziki sun hallara a gidan gida ya cike da yan uwa zainab tana gidan mu ana shirya ta don mai makeup tazo.
Wasu yan mata da matasa a gidan namu suke zaune duk wace akacewa zainab tana gidan mu nan suke shigowa.
Sai abin sha dana dan tauna baki muke rabawa wanda Yusuf ne ya sawo ya kawo muna a raba ma baki don Binta ta kirashi take fada mai komai.
Wanda ya rage na sa a dayan dakin muka rufe muka fito zuwa gurin kamun wanda kafin in isa har mun iske an fara program din ko.
A daidai wanan lokacin ne AA ya shigo kaduna ranan yammacin alhamis sai dai yayi mamaki ganin dandazon mata a kofar gidan iyayyen sai gashi ya iso gida ya samu Fati a gida.
Ya haura sama nan ma su Nafisa da yan uwanta suna gida zaune a binsu sai shan bakin tea suke saboda sanyin da akeyi a kadunan lokacin.
Ihisan da ta fara hangoshi tayo wurin shi da murna tana taron shi fuska ba saki ya rikewa yarinyar hannu yana fadin .
Ihisan ya baki je gurin kamun gwagon ki ba ke tace Abba Amin mu tace kada in bi momy ne ya dago kai ya kalle ta daga inda take kwance baiyi magana ba ya wuce dakin shi ya dan jima a ciki ya fito daga kofa ya tsaya ya kwalawa yarinyar kira ta fito.
Ya rike mata hannu suka fita tare zuwa gidan duk yawan matan dake gidan haka ya kusa yana rike da hannun Ihisan zuwa dakin mahaifiyar shi.
Ya samay ta zaune da wasu dattijan mata a dakin yan uwanta da abokan arzikin ta bayan sun gaisa ne hajiyan tace da yarinyar ashe suma sunzo akace yake fadin basu shigo gaida ku ba ke nan tunda suka zo?
Tace mun dai ga khadija da yaran ta don su ko yaushe a nan suke tare damu koda uwar bata gidan har sun saba da mutane hajiya ina Deedar take ya tambaya.
Yanzu kan ai tana cikin wanan taron don sune keda bukin ai wanan yarinyar na kawo mata na samu uwar ta ta hanata fitowa wai.
Hannu hajiya ta mikawa yarinyar duk da tana da wayau sai taki zuwa tana shigewa jikin uban tace ina zata zo tunda bata san mu ba.
Tsawa ya daka mata cikin harshen turanci yace taje gurin grandma don tsoron shi ta taka a sanyaye zuwa gurin ta.
Ai daka barta tunda ba sanina tayi ba daya daga cikin matan dakin ke fadi akan may zai barta ai gara a nuna masu ku su sanku ko.
Wani irin ba dadi AA yaji a ranshi sai yanzu yake dana sanin auren bare wanda babu wani alfanu a cikin sa sai jin dadin rayuwa karshen abin ba kyau yake yi ba ga mutum.
Wai ace yayan shi basu san mahaifiyan shi ba haka kamar an jefo momy dakin tare da su yan biyu dake gurin ta don zata fita ta shigo da yaran gurin hajiya su zauna.
Suna ganin uban zube a kasan carpet din dakin mahaifiyar shi sukayo kan shi da murnan ganin shi aka dauki dariya a dakin.
Ihisan ta baro wurin hajiyan zuwa wurin da suke tana kiran sunan su tare da dariya suma dayake sun saba da juna sai gasu suna wasa a jikin uban da junan su.
Yanzu kan kin san yan uwan ki ai gashi kije gurin su ba tayi anan ya barsu ya fice daga gidan ranshi yana mashi ba dadi.
Ya rasa dalilin matan nashi na kin shiga sha,anin bukin shi sai da zai fita ne yaga shigowan Fati gidan ita da wasu yan uwan ta ya dauke kai kamar bai gansu ba.
Mota ya shiga ya nufi inda su Yusuf ke jiran shi sai dai kafin yaje yayi tunane kala kala tare da hango abinda bai taba yin tunane a kansa ba sai yanzu.
Ya rasa gane may yasa Nafisa bata son zancen yan uwan shi bata mu,amula da kowa daga cikin su duk da kokarin da yake na ganin ya kokarta ma yan uwanta a koda yaushe.
Amma haka baisa ta dauki nashi da mutunci ba kokari ma take ko yaushe ta nisanta shi da yan uwan shi sai lokacin yake tuna wasu abubuwan da suka faru a baya kai ya girgiza yana furta kalman innalillahi har yakai wurin da zai tafi din.
Ya samu su Yusuf din na shirin zuwa wurin kamun ba yadda zaiyi duk da zainab kanwar shi ce yasani amma zuwa wurin ya zama mai dole don kokarin Yusuf a gare shi.
Wuri ya dauka ga angwane sun iso ban san da zuwan shi ba don na dauka sai washe gari zai shigo sai dai kawai na hango shi yana ma Yusuf da zainab liki a tsakiyan fili.
Daga inda muke tsaye ina rike da mami sai Alamin dake hannun laraba ihisan tana tsaye rike da hannu na daya, muna hango shi na kare mai kallo har na shagala ban san ya karaso inda muke tsaye ba sai ganin shi nayi yana muna liki kallo ya dawo gare mu mata nata kokawan kwasan yan dubu dubun da yake manna muna.
Abokan nasu har Yusuf suka dawo kaina da yaran suna manna muna kudi ina kare kaina don kunya ya jawo mu ya rugumay wuri ya kara rudewa.
Ya fice yana muna dariyan keta don ya gama bani kunya a bainan jamma,a ya wuce nan kannen sa da aboka wasa suka shiga min sheri a gurin.
Sai bayan magariba muka dawo gidan ina daki ina cire kaya Alamin yana kukan da ban san may ke damun shi ba don haka yake kwana bibiyu da ciwo shi macen tafishi dama.
Ya shigo dakin shima da ganin shi a gajiye yake lokacin yake yaron dake kuka ya kama sai ga laraba ta shigo da madaran da ta hado ma yaron daki.
Yana tambaya may ke damun shi nace nasan sanyin garin nan ne ya kama shi tunda acan ba fita suke haka ba ko yaushe.
Yace ki bashi nono ba wanan abin ba yaya zaki gane halin da yake ciki baki mamay shi ba a jikin ki ban ki ta nasa ba na dauki yaron ina kokarin zama dagani sai zanin da daura gaba a jikina.
Yana tsaye yana kallon yadda yaron ya kama nonon ya sauke ajiyan zuciya ya juya ya fita daga dakin .
Bakai dakin shi ba Nafisa dake dagon shigowan shi ta tsare shi a hanya tace dama kai nake jira ka shigo inji idan kai ka ce kada a fitar da komai abawa kowa nasa don ban san dalilin matar ka na kule kayan da aka zo dashi ba a daki tana amfani dashi ita kadai don samun wuri.
Wasu kaya ya tambaya da mamaki karara a fuskan shi tace kayan da ka saya aka zo dashi mana ko wani sallon wulakanci ne ka dauko kuma haka yasa kace sai munzo .
Ke ban san zancen kayan da kikeyi ba don haka ban son wanan haukan naki idan cin mutuncin ki ya taso ne in sani.
Idan ma na sawo kayan tayi amfani dashi ke bukin ne ya kawo ki nan ko may ina gida kike baki je gurin abinda ya kawo ki din ba.
Yana fadin haka ya wuce tana fadi cikin daga murya may zanje yi gurin mutanen da basu sona sai dai suga bayana shine fatan su.
A cikin daren nan taje gurin Abban su AA da korafi wai ya hanasu komai sai ni kadai ce nake gudanar da komai a gidan kan bukin.
Abba yace ta koma zai nemi AA din yaji kan maganan idan haka ne kuma bai kyauta ba ya dai bata hakkuri ta wuce zuwa gida.
Washe gari da safe Abban su AA ya tako zuwa gidan mu ya samu su laraba yace a sallama mashi dan nashi sai da AA yayi mamakin jin ga Abba a gidan nashi yau yazo da kan sa.
Yana kiran wayan shi don su laraba sun fada mai cewa basu tashi ba a lokacin yasa shi kiran wayan shi.
Ya sauko da sauri zuwa kasa ya samu mahaifin nasa a kasa ya zauna don girmama mahaifin nashi da yakeyi yace ya tashi ya zauna magana zasuyi dashi.
Bayan ya zauna ne mahaifin nasa ya fara mai da nasiha da wa,azi akan zama da mace fiye da daya sai daga baya yake cewa dashi jiya matar ka ta samay mu da korafin kana tauye masu hakkin su.
Ya dago kai da mamaki yana kallon mahaifin nasa yace kamar ya Abba yace eh kasan maza wasun mu haka suke wani lokaci hankalin su sai ya raja,a agurin mace daya ya manta da hakkin sauran matan nasa.
Don haka ina ga ka saba bata ta halartar da komai yanzun kuma ka janye daga hakan kaga ko dole ka samu wanan korafin.
Nan dai ya kora ma dan abinda tazo mai dashi ya rantse ma uban baisan da zancen komai ba akai Abban yasa laraba ta kiramu dukkan mu a falon.
Nice kusan ta karshen fitowa koda na karaso suna jirana na iso da sallama dauke a bakina na samu wuri gefen kujeran da anty Fati ke zaune na zauna ina gaida Abba da kwana da gajiyan jamma,a.
Kai Abban ya kada ya amsa min ya danyi gyaran murya tare da kallon inda nafisa take zaune yace jiya kin je kin samay ni da korafi akan mijin ku tace hakane Abba.
Don ko gaba daya wanan ta kulle dakin da kayan ke ciki yadda kowan mu nan baizayi amfani da abinda aka sayo ba don bukin.
Dago kai nayi ina kallon ta da mamaki sai na duka don Abban bai gama magana ba a lokacin.
Ya juya gurin dan yace kai kaji maganan ta yaya akayi ka halarta wa mutum daya yace Abba ban san da wanan maganan ba ni.
Ya juyo gare ni yace gwagona yaya akayi muna son bayani na hade miyau dakyat don takaici nace Abba ba shi ya saya min komai dana zo dashi ba.
Sai dai kudin da ya bamu ne nayi amfani dashi don nasan yawancin jama, a anan gurin mu zasu sauka nayi wanan dabaran shima baisan da zancen komai ba.
Ya dago kai yace kinji abinda suka fada ya baku kudin ko bai baku ba kuma tace ya bani da zamu zo Abba yace masha Allah.
Abinda nake son ji gareki ke nan dama AA tace ita kuma Fati gata nan shekaran jiya na turo mata nata nayi mata bayanin komai.
Amma Abba sai nazo gidan nan na samu matan nan ba wanda ya tafi gurin kamun zainab jiya din ni banyi fushi kan haka ba sai ita mai son banza zatayi wani korafi can.
Abba yace a nan dai na fahinci gwago na tafiku da bara da sanin ya kamata tunda mutumin nan ya baku ne don ku fitar dashi da kan ku kunya.
Shiru kowa yayi a falon yace da har nazo da zuman ci ma mijin ku mutumci akan may zai dauki girma da nauyi ya ba karama a cikin ku ashe ita ta sayawa kanta mutuncin komai.
Ba wurin shi ba har gurin mu mu iyayyen shi irin matan da Allah yace ka aura ke nan macen da zata iya rufa ma asiri.
Wanan maganan da Abba yayi yasa Nafisa taji haushin shi sosai watau abinduniya ya rufe masu ido ke nan.
Ta ce Abba ai na dauka don bukatan kan mu ya bamu wanan bukin shi ta shafa don may daga baya za a ce muyi hidima dashi kuma.
Ke rufawa mutane baki a gurin nan kada in kara jin muryan ki a nan don ke fitsararace dama yana fadin haka ta ce Abba na gode ta bar gurin.
Abba wanan ta isheni a gidan nan wallahi don ku nake zaune da ita har wanan lokacin haka ka ganta ka auro ta yanzun ne kake gano illar auren irin su.
Baka da wani kwakwaran dalilin cewa ka gaji da ita a yanzu halin ta ne kai zaka gyara abinka sannu a hankali ta koma kamar kowa.
Ita dai wanan khadija ta nuna muna ita yar tarbiyace ko daga yanayin kamalan ta da mu,amula da mutane mutum zai gano haka gare ta ya dan muna nasiha yayi muna sallama ya tafi suka fita tare da AA.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/25/21, 9:22 AM - Fatima Amarya: Ranan duk yadda naso inyi walwala raina ya baci na kasa tsayawa in yi komai ga anty fauziya sai aiko min in fito mu tafi gidan zainab.
Kiran da maryam tayi min ne tana sheda min tasowan su ita da wasu abokaina yasani fara tunane.
Dama don haka ne na garje nayi wanan don Anty hauwa muna firan bukin a gabanbta tace to kinga shawara zan baki yanzu.
Duk yadda zakiyi ki kokarin a wurin nan ki zage ki fishi nuna damuwa da sha,anin bukin fa blood sister din shi ne za a yi.
Ke kuma sai ki hikimar da zaki kara haska kanki ga kowa a gidan dama zuciyar mijin ki muna hada baki gurin tambayan ta may zanyi ?
Tace bude aljihun ki ki basu mamaki ki shanmaci kowa a gurin kiyi gifts ki bada karfin ki koda ba a son hakan gare ki.
Nace nasai robobi da zan raba a nawa bangaren taja tsuki tare da fadin mijin ki mai hali ne fa khadija kudin nan badaga aljihun ki zai fito ba don may ba zakiyi abinda sai sunji mamakin ba ki nuna kin fishi son yan uwanshi.
Idan kika kama zuciyar uwar miji dana yan uwan miji don dole miji yai maka ragowa kema kuma naki yan uwan da iyayye su kara haske a gare shi.
Wanan daman mata da yawa suke sakaci dashi gurin mallake miji a tsaya ga asiri ba wani hikima a ciki ni kon gani nan tambayi maryam kiji idan sha,ani ya taso a gidan su man yadda yake zama nawa.
Robolan banza abu zakuyi wanda ya banbanta dana kowa da zai ba mutane mamaki har shi kanshi mijin naki ai ba don komai zaki haka ba sai don daga darajan ki dana diyan ki da yan uwan ki gare su ko ba a wa Allah dole a yi dake.
Itace ta ban shara duk wani abinda zanyi tace ga haushin da kishiyoyin ki zasu ji kan hakan sai a koma gulman kin malake miji shiko yasan ba haka bane.
Ina cikin wanan tunanen ne ya shigo dakin nawa daga ni sai yara na a dakin sai sadiya dake gwalanniyan ta daga kwance.
Har ya karaso inda muke kwance ya dan ja kafana tare da fadin yau ba buki ne na ganki a kwance har wanan lokacin.
Ganin yana kokarin zama yasa na dan matsa mashi kadan ya zauna yace ko dan maganan wanan mara hankalin ne yasa jikin ki yai sanyi ?
Kokarin mikewa zaune nayi nace maganan ta bai sani jin komai ba sai ma dadin da naji don haka ya bata daman gyarawa itama.
Yace idan suna da niya ko ke baki san wa yan nan matan bane sune matan da ake kira da masu hana miji mu,amula da yan uwan shi.
Barin fayace maki abinda kila baki fahinta ba dasu don ni yanzu na gama gane halin kowan ku ita dai Fati da kike ganin ta.
Mace ce shasha wace ko kanta bata iya hasala ma komai ki duba fa yanzu buki ake ji yadda take zama a gidan nan ita dai butin ta a bata kudi ta kimshe su.
Ko tabi wani hanya dasu na daban wanda ba wanda yasan abinda takeyi dasu sai ita don ba a gani a jikin ta ba ba a kuma gani ga wani nata ba.
Sai bakin hali da bakin ciki ga zurfin ciki ko kaine wa baka gane cikin ta don ma bata yarda da kowa ba ita kowa macuci ne gare ta.
Ita ko nafisa ba a maganan ta don ke kanki kin fahinci wasu hali nata burin ta shine ta mallake kowa ya koma karkashin ta harni sai yadda tayi dani ta juyani yadda ranta ke so ita zaki iya kiranta da yar tallaka da gadara.
Da farko kan ta samu yadda take so dani amma shigowan ki a rayuwan mu ya maida ita baya sosai don ta kasa juya ki yadda ta samu daman juya Fati.
Don ke baki dauki wajan ba a gareta da kin yarda ta juyaki da an zauna lafiya ko ki bar gidan nan don bata yarda taga ina mu,amula da wata mace.
Nace tunda don ita kadai aka halice ka ko yace rayuwan ta ke nan sai dai ta juyani da duk wani wanda ke karkashina yadda take so.
Ban san lokacin da nace nifa murmushi yayi ya juyo ya lakuci hanci na tare da fadin gaki nan dai har yanzu na kasa kai karshe ga alamarin ki sai dai nasan komai da zuciya daya kikeyi wa mutum ke.
Aiko na samu sheda mai kyau yace tukunna dai ai ba, a gama shedan mutum cikin yan shekaru sai nan gaba idan na karo maki kishiya in gama gane halinki.
Wasa yuka a gaban doki baya tayar da hankalin doki ai yace eyyeh haka kika ce nace kwarai kuwa.
Su wayan nan dake gidan ka muke zama tare ai kidhiyoyinane haka kuma wace zata zo bayana ita ma kishiya ta ce mai zai sa daga baya in tsiro da halin da ba nawa ba sai dai itama idan tazo min da akidar rashin gaskiya.
Ko yanzu kai niya sai ka kara ni ba matsalana bane kaine mai aiki kaida ka dauko abinka wace ta shigo ta samu mata biyu a gaban ta haka wata kishiya kuma zata razana ni yanzu.
Lalai shiyasa nace ban gama tantace halin ki ba sai na kusa kammalawa sai ki tsiro da wani halin da ban sanki dashi ba.
Yanzu dai nazo in ji nawa kika kashe a cikin wanan hidimar in baki kudin ki kamar yadda kowa zai amfana da nasa.
Badon ka biya nayi ba nayi ne saboda Allah dakai da diyana da kuma mama da zainab din ko ka manta zainab kawatace nima kamar yadda Yusuf yake aminka .
To tunda kin ce haka zan kara maki gudun mawa na wuri hidimar bukin hakan yai maki ko nace yanzu kayi magana ya mike yana sa hannu a aljihun jallabiyan dake jikin shi ya fito da rafan yan dubu dubu guda biyu ya dora min saman jikina sai da na zaro ido.
Zanyi magana ya dora yatsa a bakin shi yace min shiiii alaman in kyale duk da haka sai da nayi mai godiya ko abindana kashe din bai kai nan ba ai.
Riba biyu ke nan na samu a gare shi a lokaci daya na anyana a raina yakai kofa yace yau kece da girki kin sani kada ki shagala da buki ki manta dani.
Kafin in magana ya fice a dakin ya barni da tunane koda zanyi girki garin nan ai bani ya kamata in karbi girki ba yau da na gaji da tunane na mike na bar gurin na fada bandakin don yin wanka.
Bayan na fito na shirya ban dauki lokaci ba na fito na samu laraba ma sun shirya sai dai Alamin wai yana gudawa.
Dakin Anty Fati na shiga na gaida ita nake fada mata zan shiga cikin gida tace yanzu nace eh tace sai ta shigo na fice.
A coridor din sama muka hade da Nafisa ta watso min uwar harara ban damu ba nayi mata ina kwana kamar ba zata tanka ba sai dai ta amsa min cikiciki na wuce.
Altine kwana biyu tana gidan su, sai na samu sun shigo da yan uwanta muka gaisa sukai min ya gajiyan buki.
Tare dasu muka bar gidan bayan mun rufe duk dakunan da nake da makullin su ka shiga cikin gida inda muka gaisa nake fada ma momy zancen Alamin din da baida lafiya .
Anan gurin momy na barsu muka wuce zuwa gidan zainab da za a kaita don karasa yan gyare gyare sai lokacin ne mutane ke ganin wanan kayan da AA ya saya mata wanda ba kowa ne ya sani ba.
Don ranan farko sunki zuwa gyaran dakin yau ko harda su anty Amarya muka zo gidan da wasu yan uwa da yawa.
Kafin mu koma fida har zance ya kai kunnen Abba murmushi yayi yace shine samun ai kasamu dan uwanka ya san ka samu.
Umma taso jan zance da tsawo sai Abba din ya katse maganan yana fadin abinda zamuyi farin ciki yaya kuke kokarin maidashi abin tsegumi ne wai.
Ina da kune masu korafin yaron nan bai komai ga kowa yanzu kuma an samu hankalin shi ya dawo gida za a kuma ce bai kyauta ba.
Umma tace Alhaji nina ga ba haka aka saba ba ai a gidan nan hannu ya daga mata tare da Anbatan sunan ta.
Yace ina son ki gane mutum bai lokacin shi yace kuma sai yayi na wasu ku godewa Allah da yanzu nake da mai taimaka min tace amma Alhaji kasan dai an munafunce mu ko.
Yace a cikin zancen nan waya munafunce ki rakiya sai tayi shiru kada ta zake da yawa a gane manufanta hakan yasa ta kulle hajiya mama a ranta.
Suka shiga yar tsama da juna da akazo kai gara aka kirata tace ai an tsamay su a ciki don yin abu ake ba a shawara dasu cikin wanan rikicin muka dawo gida muka samay su a hakan.
Bayan mun gama saurare ne ni dai naja kafana zuwa dakin momy inda na samu ya Amina dasu momy na cire gyale na na shiga sallah.
Har na fito suna magana guda a raina nace manya ke nan suma da tasu kalar kishin ko ina dai abin ba dama ashe yanzun kuma may ye a cikin wanan ?
Dakin hajiya mama na nufa bayan na gama ba yara nono na samay ta da yan uwanta na zaria sun shigo ina shiga muka fara gaisawa.
Hajiya mama take tambayana ko naci abunci nace yanzu dai zanci mama na shige ciki gurin da yayan ta duka suke dakin banda zainab da Binta tace suna gidan mu tare da kawayen su.
Ban dade da zama ba suma dai anan din zance gudane kan bakin cikin da ikon hajiya mama suke ta nanata maganan tambayan su nayi yanzu don bata saka baki ba ba za a kai kayan yau ba ke nan ?
Faiza tace min don may ba za a kai ba ga yan uwan Abba can dana hajiyan mu su zamu fitar sukai a raina nace ashe maryam nada aikin sarakuta da wanan matar da kowa ke fadin halin ta.
Hajiya mama mace ce mai kawaici da girmamawa tasan abinda umma ke nufi amma haka ta shanye maganan a ranta ta hana ma ayi maganan sai murmushi take sakewa a fuskan ta.
Duk yadda hajiya Umma taso taga auren zainab kasa dana diyan ta hakan bai samu ba gare ta don Allah yayi zainab zataci daga arzikin dan uwanta da ake tsegumin bai masu komai a baya sai gashi ya garje ya fitar da yar uwanshi da uwar shi kunya don har da motar shiga mai tsada ya danka mata .
Ban samu dawowa gida ba sai goma na dare na dawo na samu ya cika fam dani kan rashin dawowa in karbi girki kuma ya hana nafisa yin girki sai anty Fati ce tayi girki a ranan.
Isowan bakina ne ya kara sani zama busy a gidan tare dasu muka dawo gida inda na sauke su a dakina su hudu ne suka zo tun zuwan su nasa laraba ta dawo gida don shirya muna abinci da gurin kwana.
Ga zainab gidan tare da kawayen mu ban samu ganin shi ba sai washegari da safe ina kitchen ina hada ma bakin mu abin karyawa ya shigo kitchen din.
A tsorace na juyo don jin mutum gab dani ina juyawa na ganshi nayi mai ina kwana sai ya basar dani kamar bai jini ba yace kin kyauta watau ke van isa yanzu ince ga abinda zakiyi kiyi min ba ko ?
Nace kamar ban gane may yake nufi ba may kuma nayi ma yaya AA au ke baki san abinda kikai min ba ke nan ko ?
Wallahi ban sani ba na bashi amsa may nace dake jiya akan girki sai na dan sake murmushi a fuskana nace a, a ba hakana bane yaya gani nayi ai bani ya dace in karba jiyan Nafisa ce zata karba sai ni ko ?
Ke zaki gwada min yadda zanyi dani da gidana matan ki ko nawa ni na aje kowa a cikin ku sau nawa zan fada maki ki bar zancen nafisa a yanzu ko so kike ki bata min rai.
Kayi hakkuri ban san haka zancen yake ba in Allah ya yarda yau zan ma girki idan kin ga dama kada kiyi wanan ba matsalata bace ai.
Murmushi mai kama da takaici na sauke a fuskana laraba ta shigo dauke da flask a hannun ta shiyasa har ya bar kitchen din ba wanda yai magana a cikin mu.
Bakina sunci sun sha da yan matan zainab da suka kwana a gidan mu duk nayi ta fama da dawainiya da su har sha biyun rana muka gama shiryawa zuwa cikin gida.
Kallon da hajiya umma tayi muna ne yasa duk muka tsargu da ita muka bar part din ta zuwa sauran part din gidan a dakin momy na aje bakina don dakin hajiya mama cike yake da mutane.
Karfe biyun rana da rabi shine lokacin daurin aure tun cikin dare na saka zainab shan abubuwa har zuwa wanan lokacin ina bata a fakaice tana sha.
Adakin momy gaba dayan mu muke har su Faiza da tawagan su anan anty Fati ta shigo ta samay mu gidan sukayi kanta da korafi.
Sai buda baki tace ai ga amaryan ku nan tana maku yadda kuke so ko don haka ba sai mun shigo da wuri ba mu.
Ina jin su ban son abin rashin mutunci ya shiga tsakanin mu ko kadan sai nayi shiru ina dan dariya.
Taci gaba da fadin kin san ku ko wace amarya tazo maku daa kalan rawan ta wanan da alama ta shigo da kafan dama don baga yayan ku kawai abin ya tsaya ba har ku ta gama kwashe kafan ku.
Fauziya tace mu khadija kin san ta wuce matar dan uwa a gurin mu don tun kan ta shigo take yar gidan nan ita ma don haka bata yada mu muma bazamu yadda ita ba.
Faiza ta dora da fadin khadija bata son kanta bane a cikin mu don tayi kokarin abinda ku kuka kasa yi tun farko akan gidan dan uwan mu don aljihun ku kawai kuka sani.
Nan dai abin yaso ya zama masu fada a tsakanin su sai da momy da yan uwanta suka shiga tsakanin su don ta fara fada masu bakaken magana wanda duk a fakaice dani take yin zancen suna mayar mata da amsa.
Nafisa bata shigo ba sai karfe uku na rana da wani abu ta shigo gidan da yan uwan ta ba wanda ya kalle ta yadda take shigo masu da izza abaya sai gashi wanan karon ta shigo gidan bata samu kulawan kowa ba agidan duk kuwa da adon da tasha na fitar buki irin nasu na kasan su.
Bata dade da shigowa ba don ko haduwa bamuyi ba muka koma gidan don shiryawa na samu laraba ta gama girki data koma ta hada miya na karasa hadawa kafin mu shirya ina san ran ya karasa.
Dama tun safe kafin in fita na hada komai yadda nake son yi hankalina ya kasu biyu ga girki n miji ga sha,anin buki.
Laraba ta kyauta min don abinci tayi wadatattace da zai ishi kowa har a raga a gidan sai gashi ya kirani a kuraren lokaci akwai baki da zasuci abinci a gidan na dare.
Shigowan mu daidai ana wankin amarya muka shigo filin shigar mu kawai ya dauke hankalin kowa a gurin don shiga ce ta alfarma.
Alkasim na gefe a mota dake jibge da kayan da zan raba a gurin Altine da fauziya ce zasu raba don su suka san mutanen su.
Da ganin an fara rabo hankalin mutane ya koma can har ana batun rufe su dakyat na kusa nasa Alkasim rufe kofan motar gabadaya.
Nace ya koma gida kawai ta bar gurin duk wanda ya karbi jakka ko roban sai ya karanta hoton yan biyu ne da sadiya suna dariya aka dauka.
Tun maryan da sauran kawayena na nema muka wuce gida ban koma cikin gidan ba sai da muka shiga ne a cikin dare na tura laraba da duk wani gifts din bukin takaiwa matan gidan su AA wanda na ware masu.
Bayan isha,i ne bakin shi suka shigo gidan ga shirin zuwa diner da zamu banda halin zuwa don AA na gidan da bakin shi.
Bakina dasu laraba ne suka wuce a mota na don ban sa ran zuwa guri ba sai gashi yana fada muna mu shirya don tare dashi zamu tafi dukkan mu.
Shiri sosai kowan mu yayi dama akwai kayan da anty hauwa ta sayo min a dubai suna saka sai sai gashi shigan mu yazo kusan daya dashi farin yadin mazane a jikin shi mai tsada.
Anty fati ta fara fitowa sai nafisa na dan bata lokaci don tsayawa gyara sadiya data bata jikin ta da yake yarana suna da kafan su shiya rike su a hannun shi biyu zuwa wuri mota.
Ni kuma na dauko sadiya a kafada na kowa satan kallon shigan dan uwa yakeyi munzo shiga mota a raina nace zanga yadda za ayi yau.
Sai naji yace Fati ke ki shigo gaba su zauna a baya su kamar nafisa ba zata shiga ba sai dai taja ta shiga ya tayar da motar fati sai sauke ajiyan zuciya take yi.
Yaran suna gaba a wurin su zan iya cewa wannan ne karon farko data dauki yarana a jikin ta kota kulasu.
Mun shiga wurin wuri ya cika da mutane yana neman gurin da zamu zauna ne naji muryan Altine na fadin kawo sadiya in kama maki dama sai da nayi tunanen barin ki da mukayi da ita ai.
Ni naga karfin hali a gurin Nafisa ko kallo yar bata isheta ba wai ita ala dole ta barmin yarinyar don nawa ne dama.
Mc da yake abokin su ne ya shiga baradawa ga AA abokin ango yayan amarya da iyalin shi sun iso kallo ya dawo gare mu.
Daga can gefe gulma ya tashi yana gaba tare da nafisa ya dawo muka jera daniyar daukan mami sai yace in dauki Alamin muka jera tare da anty Fati da muke tafe tare muka sakashi a tsakiya sai da ta juyo ne ta gamun a hakan tafe ba yadda zatayi haka muka kai mazaunin mu.
Nan ma yana kusa dani sai dai mun sashi a tsakiya dani da nafisa din Fati tana daga gefe na don ban dauka wani magana yana hadata da buzuwa ba.
Dan rankwafowa yayi yana fadin yau kinga yayan ki baki yaki rufuwa Altine ne ta karaso tana rada min wai su maryam basu samu wurin zama ba.
Tambayana yake yasa ya dan duko min ina fada mai abinda ta fada min sai jin hasken wutan camera mukayi a kan mu ana dauka mu hotuna.
Wani ya yafito yazo ya danyi mai magana bada jimawa ba sai ga wani sit ana gadawa a gurin.
Aka nemo su cikin loundspeaker ana neman su suzo ga gurin zaman su kusa damu suka zauna maryam don gulma ta zauna a setin mu.
Duk wanan abinda ake sai sakon harara yake samu daga wurin nafisa itama fatin ba wani walwala a tare da ita turanci da nuna wayewa ke tashi a gurin.
Duk wanda yazo dani zamu gaisa sai fati dakan dan saka baki gefe zakaga mutum na fadin ya muke ya iyalin mu sai in buge da bada amsa.
Dinner yayi kyau sosai sai dai bai bari an tashi ba yasa mu bar gurin don yara saboda sanyi tayi yawa a gurin don haka muka bar gurin a cikin lokaci.
Baya munyi hotuna da amarya da ango muka bar gurin zuwa gida saboda laraba da muka baro gurin bukin don haka ko da muka dawo ban huta ba don shirin yaran da nakeyi na kwashe su zuwa dakin shi.
Sai gasu maryam sun dawo nadan dade a gurin su sai daina basu komsi don sunce tea zasu sha kafin su kwanta larabs na saka ta dubamin su.
Na samu ya gyara min kwanciyan yaran guri daya ya ajesu su uku don haka muka manne da junan mu a gefe daya mundanyi fira kafin komai ya kan kama muna mukai barci cikin jin dadin kasancewa da junan mu ga yan diyan mu a tsakiyan mu.
Washegari da wuri na fito don shirya abincin baki saboda ranan su maryam zasu juya Abuja ina tsakiyan aikin ne hayaniya ya taso a sama ashe fitowa na nafisa ta shiga dakin shi.
A fusace taje da tambaya may ye matsayin ta a gurin shi ne do bata gane ba don may zai ban girki bayan ita gata yace don tana matana ita din.
May kake nufi da ita matar kace nifa a matsayin may nake gurin ka yace wanan kuma yanzu ba zan iya fada maki ba sai nayi shawara nan gaba.
Nan har yakai suka fara sa in sa har yakai ya mike ya fara jibgan ta suna tonon asiri ga junan su duk wanda ke gidan ya fito.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/27/21, 6:51 AM - Xxxxx: Yanzu kokarin kammala karatun mu mukeyi wanda muna a matakin karshe haka ya jawo min rashin zama sosai a gida.
Sai yamma lis nake dawowa gidan da na dawo kuma na dan huta bayan na gama ibada sai in shege barci don gajiya.
Duk yadda Altine kan so muyi hira hakan bai samuwa a gare ni ban san may yakai Nafisa garin mu ba ranan na fito don zuwa school ina sauri sai ji nayi tana fadin iyayyen ki na gaida ke mun biya munga gidan ku .
Mamakine ya kamani don jin kalamin ta matar da ba wani hurdan arziki yake hada mu ba may ya kaita gidan mu kuma.
Nagode Allah ya bani ikon amsa mata dashi na fice ba tare dana dora wani magana ba akai sai dai a raina ina mamakin zuwan ta minna din da tayi.
Banda lokacin wanan don haka ban tsaya bin ta nata ba kuma Allah ya taimake ni mun gama komai na project nayi sumiting.
Na fara jin shakat a tare dani yasa ina dan zama gida yanzu a cikin iyalina yanzu muna da masu aiki dake girka abincin gida gaba daya wa kowa don haka ba wani aikin komai mukeyi ba mu.
Arzikin AA ya bun kasa sosai bai damu da tsayawa yayi aikin nan gida Nigeria ba ko yaushe yana waje mu kan mu ba kullun ne muke ganin shi ba nan.
Sai dai idan ya zone kasan ba mai hutu a cikin mu don yawan aikin da muke na fama dashi da bakin shi dole sai mutum ya leka kitchen din ya duba abinda sukeyi.
Na fada ma masu aiki abinda zasu girka min yau kafin in fita sai na dawo na samu wai Nafisa ta shiga tace dasu kada suyi abinda nace sai wanda ta fada masu din.
Raina ya baci gashi muna saka ran dawowan maigidan a ranan kuma nice da girki idan ya dawo ga auren maryam daya taso kwatsam a satin da zamu kare satin za a fara bukin.
Part din Nafisa na shiga wanda zance tun da akai wanan gyaran ban shige shi ba sai ranan nayi mamaki ganin part din dam da buzaye yan uwan ta wanda ban san lokacin da suka zo ba ma.
Da farko naji dan shakka yin maganan da ya kaini amma ganin sun gani nashigo ya sa na dake na karasa dakin ta don tsarin ginan iri daya ne da nawa na kwankwasa kofa na shiga.
Tana zaune da bakuwa sun baje kaya a gaban su ana mata bayani wanda ashe akan yarana akai wanan tafiyan ban sani ba ni.
Allah ya taimake ni ban wasa da ibadana duk ko da daulan da Allah ya kaini a cikin sa na dawo khadija na ta farko sosai ban yarda na shagala ba da addinina.
Shima kan shi maigidan yanzu ya canza sosai don koda zan falka zan samu ya rigani tashi yana gabatar da nafila a cikin dare.
Daz mamaki suka kalloni nan ta fara fadan borin kunya wai may na shigo mata shiya yi bata shiga girina va don may zan shigo mata.
Suna kokarin boye kayan da na samu an baje ana kula sheri farin kudine sai dodon alkwato da kan wasu mushen halittan daban san ko may ye ba.
Na gama kare ma kayan kallo a cikin second nace zuwa nayi nima inji dalilin daya sa na bada kalar abincin da za ai min kika shiga kika ce kada su girka min shi.
Jimun wanan yar matsiyatan don Allah zuwa kikayi yanzu ki makure ni ko may ta fada tana min wani irin kallo nace zuwa dai nayi in maki kashedi akaina da komai nawa.
A matsayin ki nawa a gidan nan ke yanzu fa nasan komai akan ki don haka baki da wani bakin da zaki mun maganan banza a gidan nan.
Don naje har kuryan dakin uwarki na gani naga abinda kike mun tunkaho dashi ba komai banda tsiya a gidan naku.
Alhamdullahi tunda muna da gida har kinje ashe nafiki don iyayyena dai ban barsu a kango zaune ba ko bukka ta kwashe da dariya tace karya ke nan wallahi kowa ya ganin yasan gidan dana fito ai.
Dama na nemi gidan ku ne don in kashe maki wanan alfaharin naki a gidan nan don na samu abin fada maki watarana nace nafi kowa sanin haka ai don ba zuwan alheri ya kaiki gidan mu ba.
Sai dai nasan duk yadda gidan mu yake nan yafi gidan ubanki sau dubu albarka koda banje ba ina da labarin komai a kunne na ga wayanda sukaje suka gani.
Ban fito ba sai da muka fada ma juna magana son ran mu na fito dakin da farko abin yaso ya damay ni a raina sai daga baya maryam tace dani akan dan maganan nan zaki damu kanki dashi.
Cin tuwon kishiya fa ranko ne ko birnin masar take sai munje mun gano gidan su wallahi don taji inda dadi hakan balle banga abin kushewa a gidan ku ba ai.
Sherin kishiya yanzu khadija wani iri ne baki sani ba kuma har da wanda batayi niyar yiba kin sani banga abinda zai damay ki ba ni.
Haushinta dai daya yanzu duniya ta daina yi da ita babu bakin cikin ta sai ta bude ido ta ganki a cikin gidan nan dake da yaran ki.
Da wanan maganan na maryam na manta da zancen ranan sai Allah ya taimaka bai dawo ba a ranan ya dage tafiyan sai wani sati mai zuwa zai dawo.
Tun lokacin da muka fara bukin maryam banjin dadin jikina sam zazzabi nake fama dashi sosai dole na samu time naje asibiti don a dubani sai dai result din ya ban mamaki jin wai ciki ne dani.
Sun bani magani na dawo gida na boye takardan naci gaba da ahan magani na banje kaduna na ba jos na wuce inda a can za ai bukin maryam din.
Wanan yasa hajiya umma yin korafi akaina wai na fifita gidan kawa na sama dasu don shi kanshi AA baiso in tafi jos din ba sai danayi ta magiya ya yarda na tafi.
Wahalce nakai jos kwanan mu uku ana shan shagalin buki muka juyo zuwa kaduna a dadafe na shigo kaduna don jikina daya kiya min tuncan.
Fada ya fara wai ai saida ya fada min karnayi nafiyan nan na nace sai nayi dole ya tasa ni gaba zuwa asibiti a cikin daren muka je.
Tambayan farko shine ko ina da ciki ne ya wani kura min idanuwan shi don son jin amsan da zan bayar a sanyaye na daga ma likitan kai alaman eh.
Zama ya gyara yana saurare na likitan yace wata nawa nace biyu sai ya rubuta min magani yace tafiya da jigilan bukin danayi ne ya sa min wanan zazzabi haka.
A raina nace koma may zai fada ya fadi yanzu dama don kada ya hanani sha,anin buki naki fada mai zancen cikin da wuri.
Har muka dawo gida bai min magana ba sai da zan fita mota naji yace baki son cikin jikin naki ne da alama don tunane na ya nuna min hakan.
Dan kallon shi nayi banda bakin magana don yanayin da nake ciki nace ban iya magana yanzu don Allah ina kokarin fita daga motar .
Mun samu masu zuwa gurin dinner nata kokarin zuwa nikan nasan ba halin haka gare ni ina shiga na shige dakina na dunkule.
Laraba ya kira ta hada min tea in sha insha maganin da aka bani tunda ya fita bai kara lekowa ba nasan sun tafi gurin dinner din ne sai ni da laraba kadai muka rage a gida.
Can ma hankalin shi bai kwanta ba don haka ya dawo gida sai dai ya samu ina barci na hankali kwance tare da yarana su uku a dakin.
Sai laraba data gama gyara bandakin dana bata tana saka kamshi a dakin ya shigo baidade ba tunda ta fada mai nasha maganin sai dai nayi ta amai daga baya.
Jamma suna tambayana ake fada masu na dawo banda lafiya ina gida kwance haka yasa mutane da yawa sukaji rashin lafiyan nawa.
Da safe na dan tashi jikin nawa da dama don haka nayi wanka na gyara jikina na koma na kwanta muna waya da maryam din nan nake sheda mata abindake damu na.
Tayi mamaki nace nasan ki da baki tsiya dana fada maki tun farko dayan zu ba ai bukin nan dani ba don idan ya sani ba inda zanje kema kin sani.
Shine ya shigo dakin nace zan kirata daga baya yana wani shan toka a fuskan shi ina kwana nayi mashi tare da tambayan shi gajiyan jamma,a .
Bai amsa min ba sai tambayan da yayi na karya insha magani nace laraba ta fita ta samo min kosai don shine kadai nake ci ya zauna min a ciki yanzu da dan kunun kamu.
Ina taje samuwa nace ban sani ba wallahi ta dai fita ko zata samu yanzu kina sakaci da rayuwan ki da tun farko nasan da zancen cikin nan ba inda zaki je wallahi.
Har ya kare rigiman shi ya fita ban iya tanka mai ba na kyale shi ya fita a cikin fushi laraba ta dawo min da sako na na tashi na danci na koma na kwanta .
Shigowan su hajiya mama da momy ne ya sa na tashi daga barcin da nake muka gaisa suna min yaya jikin nace naji sauki.
Momy tace baki da lafiya haka kika tafi gurin buki ai ciwo ya kawar da komai ga ran mijin ki ya baci sosai wallahi.
Hajiya mama tace tasan ba zai barta zuwa bane ta boye mai amma kuma ai lafiyan ki dana abun cikin ki yafi komai khadija kada ki kara irin wanan gangancin don Allah nan gaba.
Kai na gyada mata kawai tace zainab ma halin da take ciki ke nan ya hanata halartan bukin da kyau.
Sai lokacin nayi magana nace zainab cikine da ita ashe tace cikine irin naki itama mai wahala takeyi yanzu dai naji yace ai zaku fita ne ko ?
Don bukin nan ya dawo dashi dama nayi saurin dagowa ina kallon mama din momy tace kin san babangida ai tun da ya kafe da ita zai wuce har yaran shike nan kuma ai.
Da kyat na bude bakina nace don Allah momy a rokar min shi ban son zuwa kasan nan wallahi ya barni nan zan kula da kaina.
Basu wani jima ba suka tafi sai lokacin Fati ta shigo dakin tana fadin ashe bakiji dadi bane sai yanzu da su momy suka shigo nake ji.
Nace zazzabine naji sauki ai tace Allah ya sauwaka wanan karon Nafisa ba shigo ba wurin bukin sai lokacin nake ji bata shigo ba ashe.
Banyi mamaki ba don karamin aikin tane don ba shiri suke da Suraj din ba ko banza fa kuma maryam da ta tsana a rayuwan ta.
Don gani takw babu abinda muke da maryam sai shige shige akanta da mallake miji shine aikin mu kamar yadda take da kawayen hurdan ta.
Kwana uku muka kara a kaduna su maryam har sun bar garin ko ita da angonta zuwa cin amarcin su tun kwana biyu da tarewan ta.
Mun iso lafiya nan ma dai ba a cikin dadi nayi tafiyan ba don keta kuma ya ki saya min ticket din jirgi in bi ko da nida shine.
Tunda na dawo ban leka waje ba ina ciki kwance gashi shi ba zama yake ba don Yusuf bai dawo Abuja ba shi kadai ke komai a nan yanzu.
Ya dawo a cikin dare ya shigo gurina ya dubani sai yake fada min cewa wai zamuyi tafiya nan da kwana biyu in shirya kuma zamu dan dade a can din.
Fuska na bata tare da fadin gaskiya sai dai kaje kai kadai don ba inda zan tafi a hankan da nake ko ka dauki wata kuje tare.
Kin san abinda kike fadi kuwa ya tambaye ni ni ince kiyi abu har ki tsaya kina min korafi akai wanan tafiyan ya zama dole kiyishi don ba zan zauna acan ni kadai ba alhalin ina da mata.
Dawa kike son in wanan tafiyan cikin ku bayake duk cikin ku akwai mai ilimin da zata taimaka min da wasu abubuwa a can ne ?
Shiru bayi tunda ya fara magana don jin abinda ya fada din nace kasan wata mai zuwa kuma zamuyi buki a gida shine dalilina.
Buki ba wanda zasuyi ne idan kin tafi wai may yasa kike son ja danine kina tsanmani ko kina nan za ai bukin zan barki kije ne a hakan yadda kike din nan don haka ku shirya harsu Altine don yara zamu tafi.
Jin dasu Altine yasa hankalina ya dan kwanta da tafiyan sai dai banso rashin samun bukin yar mama Tani da za a yi ba haka yasa washe gari na tura ma mama tani din kudi masu yawa tare da bata hakkurin rashin halartan bukin da baczan samu yi ba.
Nafisa ta so ta tayar da rigima yake ce mata idan kin je can wanu aiki zaki min a can ita aiki ne zai kaita ba shakatawa ba.
Wani aiki ta iya da zatayi a can yace idan taje zaki gani lokaci ya kure mata don da bata yarda da wanan tafiyan da za ayi dani ba ta nasa a ranta.
Ba tare da na samu sallama da kowa ba mukai wanan tafiyan zuwa waje kasan hongkong muka nufa ba sai na fada maki yadda naga kasar ba kacar dani .
Sai nake ganin rashin tausayin shi da ya jajirce akan sai nayi wanan tafiyan ko ta halin kaka sai na tafi tare dashi can.
Da farko don laulayin da nake yasa banji dadin garin ba amma da bazo ina samun kulawa sosai sai na fara jin dadin yanayin garin a jikina.
Sannu sannu na gane dalilin shi na zuwa dani da farko dai doin kare lafiyan shi da mutuncin iyalin shi sai na biyu don yaran shi yana kusa dasu.
Sannu sannu alamura suka fara canzawa yayin da cikin jikina ke kara girma yana fitowa ba zan iya cewa Nafisa ta san da zancen cikin ba.
Sai dai nasan tana kiran shi suna fina kan rashin zuwan shi Nigeria din wurin ta muna da wata uku da zuwa ya barmu can yazo nageria.
Sai da ya share wata daya ya dawo gurin mu karatuna na koma ina business inda bake turowa Ya Amina da zainab dasu Faiza kaya suna sayar min a tura min kudina in sake turo wasu.
Tsayawa in fadi canzawa na a yanzu bata lokaci ne don gaba daya na sauya na zama wayayiyar mace mai aiki da zamani ga ilimi dana samu a can.
Watan cikin jikina tara yanzu ban fita ko ina sai zuwa daukan darasi kawai ke fitar dani ban ketare wata tara ba na haife dana mai kama da diyana sak yazo duniya.
Allah ya taimakeni yana kasan bai fita ba na haihu nasa rai zamu dawo gida don sunan dan sai cewa yayi ba inda zan tafi karatun yaran shi ya samu tsaiko.
Ya dai buga waya ya sheda ma mutane na haifi Abdulsamad jinior kamar daga sama Nafisa ta samu labarin haihuwa na daga bakin shi.
Ba karamin fitina tayi ba har da dan kukan ta wai ta gane dai yanzu bai son ta har nayi wani ciki na haihu ita ko bata n wata bata kara yi ba har yanzu.
Wayan ya kashe don bai iya sauraren shirmay ta yanzu ya kira fati ya fada mata tayi kokari wurin boye kishinta tayi addua akan jaririn da aka haifa din wanda hakan ya kara daga daranjanta a idon shi.
Hajiya mama da momy ne suka zo dubani inda watan su daya a wurin mu yana nuna masu gata bayan wata daya suka shirya suka dawo Nigeria,
Zainab ma ta haihu ta haifi dan ta namiji ita ma sai maryam suke fada min cikin ta ya girma amma sau daya suka zo kaduna gaida su basu sha da dadi ba wurin umma ya dauki matar shi suka koma tun kwanakin da zasuyi basu cika ba tun wanan lokacin basu sake dawowa ba inji momy.
Hajiya mama ba mau son hayaniya bane sai dai tayi ta kallon mu tana murmushi wanda hakan ke nuna farin cikin ta a fili.
Ana saura kwana biyu ta koma ne take fada min cewa sunyi magana da AA yace yana son akai su Affan karatu saudiya.
Nayi murna kwarai ya yarda da shawaran dana dade ina binshi akai ke nan sai dai maimakon ya kaisu inda nace sai canzawa yayi zuwa kasan saudiya wanda hakan yayi min dadi sosai.
Ban nuna mashi naji ba sai bayan tafiyan su hajiyane yake mun magana na nuna mai farin ciki na sosai yace zai shiga Nageria don shirn yaran karshen wata zai dan dauki lokaci don wani aiki da ake mai a can yanzu.
Ya barmu can yazo sai dai tun zuwan shi Altine ta tayar da gankalinta akan ita fa zaman garin ya isheta hakana gida take son ta dawo.
Na kirashi ina fada mai yayi mamaki yace ko dai wani abune ya hada mu da ita nace ba abinda ya hada mu gaskiya gida daine ya biyo mata a rai.
Yace a bata wayan suyi magana ya dan rarashe ta akan ta bari har ya dawo ai zamu zo gida muma bada dadewa ba.
Niko nasan dan ci gaban data samu ne yasa tayi wanan maganan don taje ta shana a kaduna asan itama ta faso gari don gwargwado AA ba maketaci bane.
Yana kyautata ma duk wanda yake kasa dashi yadda ya kamata dan kudin da suke samu ne ba basu shawaran su dinga juyawa suma suna samun ci gaba.
To wanan daman data samu take ganin yanzu ta wuce zama rainon yara ita ma zata iya tsawa da kafan ta yanzu.
Ya dawo da sati biyu tare da Anty Fati daga wurin kai yara suka wuto zuwa gurin mu, Altine ta barmu can ta dawo Nigeria wurin yan uwanta ban wani shan wahala ba don Laraba mace ce data cancanci yabo ga Anty fati ba laifi tana dan taya mu kula da yaran.
Tare muka zo Nigeria lokacin tana da wata biyu da zuwa wurin mu ko yaron dana haifa ya girma yayi wayau sosai yana rarafe ne yanzu .
Tun isowan mu Abuja Nafisa ta kyala ido ta ganmu don bata san da zuwan Fati ba hankalin ta yayi matukar tashi sosai yau tana ji tana gani matan da tafi tsana a rayuwan ta suna can ashe suna holewa da mijin ta.
Ita tana nan an yada ita kamar wata bora ko taron arziki bai samu ba a guri ta hankalinta ya tashi sosai ga yadda taji labarin nakoma da yarana.
Bai bi ta kanta ba ya fice ga dayan part din da aka budewa fati ta shige ciki shiya kara daga mata hankali sosai don bata gama da batuna ba, ga kuma wata tazo.
Wai may ke faruwa da itane haka komai nata yana shirin lalacewa gare ta sai taga kamar zatai nasara sai abu yazo gaba daya ya rikice mata.
Fatin da take ganin ta gama da batunta a rayuwan su yanzun kuma ta sake dawowa cikin lamarinta kardai aikin ta yatashi ke nan ita ma kan sanadiyar wanan fitsararan da bata jin jifa a kanta.
Daidai lokacin ne da take wanan nazarin laraba ta fito da yaran tana masu burgan turancin data samu a can tana wa yaran.
Galala Nafisa tayi tana kallon laraba ko yaran dake dan wasan su cikin rashin kula da ita a gurin bata taba nadaman rashin karatun ta ba sai ranan don tana ganin da kyau shine nasaba ga komai a gareta.
Dakin ta ta koma cike da bakin ciki da takaicin yaran data gani a jere su uku wai duk wanan yar nufawan keda haihuwan su a gidan.
Ya zama dole ta mike tasan inda take ba zata tsaya kallon ruwa ba balle kwado ya rigata tsalle haka kawai daga shigowa na har na sake diya uku tana zaune dabas.
Kaji jahila wace bata san Allah ke yi ba waya ta jawo tana kiran kande sabuwar aminiyan ta na yanzu Kande dake tare da madam datazo wurin ta maula.
Tana sauraren bayanin su da Nafisa har suka gama tunda Kanden tayi mata alkawarin zuwa Cameron kafin mu koma zata san yadda zata sai dai zance na ya sha ruwa a gidan.
Muna da sati biyu da zuwa naje gida na ziyarce su kowa yaji dadin zuwa na ya Amina tazo muka hade nan da ita ranan raba dare mukayi nuna hira da ita.
Nayi sa, an zuwa don gap da bukin yar mama Tani ta biyu ce sai na roka ya barni sai da muka sha buki muka dawo ranan Fati ce da girki a gidan na samu sun gama fitina da Nafisa.
Duk da rashin son hayaniyar ta ranan saida ta kai karshen ta sukai sa in sa kowa ya gama jin su a gidan don nafisa tace ba zata zauna ba da fati sai dai takoma kaduna da zama.
Ita ko tun a can na kara mata karfin gwiwa gara ta dawo Abuja ta zauna tunda ba kowa a gabanta yanzu da haka harta yarda.
Shine ita kuma nafisan ganin bata da niyar komawa ta tada wanan fitinan na bata yarda da zaman Fati ba a Abuja.
Muna gidan maigidan ya dawo ta tayar da fitina yace akan may kada fa ta daga mai hankali don shi yanzu mace ba dole bane a gare shi.
Dama can bashi ya maida fati kaduna ba itace ta zabi zama can yanzu kuma tace ta dawo nan don haka dakin ta na nan a gidan.
Wayo buzuwa ina wuta ta saka AA ranan don bamu kishiyoyin ta ba har shi maigidan tsanan shi take ji a ranta tayi tunane kala kala ta rasa na dafawa.
Don yanzu bazata iya zama kasan su ba don wacen zaman datayi bata sha da dadi ba ga gorin yan garin daya isheta sai da Allah ya taimaketa yazo ya dawo da ita.
Yanzu yaya zatayi ga duk kawayen ta na farko dake mata shige shige yanzu duk sun gujeta sun koma ga wayan da suke ganin sun fita bayarda ihisani.
Dole dai madam zata nemo ta dawo a rayuwan ta su dora a inda suka tsaya da wanan shawaran ta kwanta tana jiran gari ya waye ta lalubo madam din taji yadda za a yi.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/28/21, 6:23 AM - Xxxxx: Washe gari da dawowan mu kururuwan Nafisa ne ya tayar damu a gidan ta samu waya Allah yaiwa mahaifin ta cikawa da yammacin jiya.
Duk wanda ke gidan ya tausaya mata da wanan rashin da tayi don mahaifa ba wasa bane gaskiya ko da ban san tsohon ba a yadda ake fadin yana jinya shekara da shekaru dole mutum ya tausaya mai da iyalin shi.
Har dakin ta na shiga nayi mata gaisuwa na dan dade a zaune babu mai magana a cikin mu kafin in fito na bar part din.
Gurin Anty Fati na shiga don mu gaisa nake fada mata dagagurin Nafisa nake naje nai mata gaisuwa ne tace zan dai yi daga nan indan yana kai ga mamacin amma ba zan mata gaisuwa ba ita.
Don ko uwata data mutu bata sani ba amma idan cin mutuncin ta ya tashi gidan nan lokacin uwara dake kwance a kabarin ta itace abin zagin ta kullun.
Naji ba dadi a raina amma dai na kara bata hakkuri a fili nace ba a binta nata ai don zama ya hada mu tare komai mutum zaiyi sai ya gyara ramin sa don ba ruwan Allah da kishin mu hakkin zama zai tambaye mu.
Wanan nasihan danayi mata yasa jikin ta sanyi na dora da fadin wanan isan mutum nabin ta nata sai ta kona kanta ta kona ka ai.
A falo muka hadu da AA din nayi mai ina kwana tare da fadin ashe rashi akayi haka kuma yau yace wallahi Fatiha jiya ta kirani da dare tana fada min ya kare.
Allah ya jikan shi yai mashi rahama nace ya amsa da amin tare da jan guntun tsuki yana fadin yanzu abubuwan mutum zasu tsaya ke nan kuma.
Nace wanan ai ya kawar da komai don dole aje akan lokaci yace hakane garin nasu ne ba dadin zuwa ke gare shi ba ai nace ko yaya ne ya kamata aje da wuri dai.
Wayan shine yai kara ya dauka nikan na shige part dina na barshi gurin ya nufi hanyan part din shi yana wayan.
Ashe Fati tace tai mata gaisuwan da rana ina falona zaune na kira maryam bayan mun gaisa ne nake ce mata ke yau fa rasuwa akai muna a gidan.
A kidimay take fadin innalillahi wa ya rasu kuma khadija banji dear na na fadi ba kuma nace mahaifin Nafisa ne ya kare jiya da yamma wani irin tsuki taja tare da fadin har kin sa gabana faduwa wallahi.
Nace maryam musulmi ne fa dan uwan mu tace don haka aishi zan ma addua ba itaba sai kuma tace ashe zuwa ya kama mu Niger.
Da sauri nace kedawa tace dake wallahi ai wanan dama ne ya samu zamuje muma muga gidan su wanan karon sai ta jimu wallahi.
Sai kin dawo nace mata yanzu fa AA ya gama fadin garin ba dadin zuwa jiki da wani shirmay don Allah ba dadi shi yake zuwa wallahi nina fada maki sai munje mun gani in ba irin wanan sanan ba yaushe zamu samu zuwa.
Sai kin dawo nace mata tace sai dai na shigo yanzu aiki nake yi yace zau dawo yaci abincin rana shine nake girki amma idan na gama ganinan zuwa gidan.
Mukai sallama ta kashe wayan ta barni ina mamakin karfin halin ta don ban dauki zancen da wani gaskiya ba aiki yana ma laraba yawa haka yasa nace akawo min yarinya daga gida irin Nufawan doko din nan.
Sai wata yar maman mu tace ga yaran ta nan mata har uku in dauki guda daga ciki ko nawa ma nake so na barsu zasuyi shawara na dawo.
Itace ta iso da ranan haka yasa na manta da zancen Maryam din naci gaba da harkokina a gidan zuwa hudu sai ga maryam din ta shigo.
Bayan mun gaisa ne nayi mata jagora zuwa dakin Nafisa tayi mata gaisuwa inda muka samu suna ta faman shirin tafiya washe gari zasu tafi.
Muna fitowa maryam tace kinga mu kuma sai mu dora idan sun tafi nace wai ke da gaske kikeyi ne don Allah tace insha Allah sai munje munga gidan su muma don mu maida martani.
Ai shege akewa bai rama ba mamaki zamu basu don nasan idan kin fadawa mijin ku ba zai yarda mu je ba don haka kyaleshi kedai kawai ki tambaya muna yadda ake zuwa garin.
Haka akayi dan a cikin hikima na tambayi maigidan yake fada min duk yadda za ayi aje garin washe gari suka tafi tunda asuba mu kuma muka fara shirin tafiya don anty Fati ma tace zata tafi tunda gulma ne.
Momy na fadawa shirin mu tace gata tafe dama tana tunanen yadda za ayi sai gata ta shigo garin da yamma da sunan gaisuwa tazo yi a Abuja.
Muma tunda asuba muka dauki hanyan doso da motar Suraj ya hada mu da sojoji guda biyu muka tafi tun muna tafiyan dadi sai gashi ido ya fara raina fata.
Kowan mu ya gaji da wanan tafiyan shiru mukayi dukkan mu a motar sai da muka fara shiga garuruwan kasar ne muka fara magana muka dauki hanyan tawa inda acan ne zamu nausa a sahara zuwa kauyen nasu.
Ga namu watau mun dauka tafiyan mara nisa ne sai gamu har guraren uku bamu kai garin ba sai da muka bar gari da nisa muka iso garin.
Da tambaya muka samu wanda yasan gidan har akai muna kwatance munga karyan buzaye a wanan garin kowa da dan kitso a gaban kai mazansu da matan su da shiga irin tasu.
Kofan wani gida shi ba gidana ba full ba a kuma kiranshi da bukka gashi nan dai ga kamar shi sai da na raina ma AA ba buzuwa ba kawai.
Yana zaune suna karban gaisuwa muka iso yabi motar da kallo shida yusuf ne yana mamakin motar don daga Nigeria take kuma lamban depences na Nigeria ne.
Momy ce da ta fara fitowa dauke da daddy a hannun ta yana kuka yasa AA dan zabura daga inda yake zaune sai gamu muna fitowa daga cikin motar.
Mamaki zaiyi ko takaicin zuwan mu na wanan kasadan shigo wanan kasar da mukayi hikiman
Zuwa da momy ya taimake mu don bai iya muna wani magana ba a wurin sai cewa da yayi momy kune tafe haka ?
Bayan mun gaisa ya nuna muna hanyar shiga cikin gidan muka nufa kai tsaye kowa na baza idon wurin kallon kwam suna ciki da mutane da ba yawa a gidan.
Mukai sallama sai da ta girgiza momy ce dai gaba sai fati maryam na bi ina bayan su gaba daya matan dake gidan suka dawo da kallon su gare mu.
Fatiha ce tayi karfin halin iya magana tana fadin lalai marhabin kune tafe ashe kuna hanya bamu sani ba tana taron mu a cikin jin dadi.
Ita ko nafisa tayi mutuwan zaune ta zuba muna ido ana kokarin shimfida muna ta barma ina kallon maryam bata zauna ba sai da ta goge tabarman da aka shimfida muna don jan magana.
Nan aka debo muna wani jan ruwa a tukunyar kasa aka kawo muna kowan mu kallon ruwan yayi ya kawar da kai.
Za,a ba dan wurina dake rikici ruwan maryam tayi saurin fadin a,a aida ruwan mu a jakka ta dauko ta mika ma Fatiha fatihan tace ai nasan ba zaku iya shan ruwan mu ba.
Gaisuwa muka fara tare da tambayan mu yaya hanya nice nace ina mama mu gaida ita aka nuna muna wani bukka babba tana ciki Fatiha tace mu zo mu gaisa da ita.
Kai maryam da ta kallama ita da fati suka shiga bukkan sai ni da momy ne muka tsaya cire takalman mu muka shiga dakin .
Mun gaida matar da wahala ya sata tsufan dole tare da mata gaisuwa don bata jin ko zo in kashe ka da hausa sai yaren su na buzaye.
Bamu dade ba muka fito don zamu juya sai lokacin nafisa da bayan gaisuwan da mukayi bata kara magana ba tace ashe yanzu zaku juya ?
Eh don ba kwana zamuyu ba anan nice a kofan su muke magana da Fatiha nake tambayan ta ko zamu samu ninon rakumi a wurin su.
Tace sosai kuwa ai yanzu lokacin sa ne ma na bata kudi akan a samu muna idan ba zai dauki lokaci ba tace nan bayan su akwai inda zata samo muna.
Shije ya dan bata muna lokaci har muka dan makara mun fito zamu tafi inda naba uwar su kudin mu na Nigeria masu yawa da su Fatiha sai godiya suke zabga min muka fito .
AA da ransa in yai dubu ya baci yace ma momy badai juyawa zaku yi ba yanzu momy tace munzo munyi gaisuwa ai gara mu juya komai dare insha Allahu yau gida zamu kwana.
Baiso tafiyan mu ba yaso akaimu cikin gari wai mu kwana da safe mu dauki hanya sai sojojin nan sukace ba damuwa tunda muna tare dasu ai don suma basu son su kwana a kauyen.
Bamu muka kawo Abuja ba sai daya na dare suka sauke mu gida suka tafi wanka nayi na rama sallah dake kaina na kwanta.
Don gajiyan da muka debo sai dai AA yana kiran mu har muka shigo abuja hankalin shi ya kwanta da safe ban fito ba don gajiyan da muka debo acan ko tsaranban da muka saya ban bi ta kanshi ba.
Kwanan shi uku da akai sadakan ukun ya dawo a cikin dare sai dai ba kamar namu tafiyan ba na dare sosai jin dawowan shi ne na fito don har lokacin ina da gajiyan zaman mota a jikina.
Yana waya na shigo ganin yana waya yasa nayi mai sannu da zuwa na juya da zan fita ne yake cewa dakata na juyo dani yake din yace hada min ruwan wanka.
Banki ba na hada mai na fito na samu ya gama wayan yace ku yan kasada may yakai ku Niger ne da mamaki nake kallon shi nace kai may yakaika don Allah ?
Ni kike tambaya nace naga dai abinda ya shafe ka ya shafe mu ai ko zuwan namu kuma laifi ne idan kuma bamu je ba a ce bamu tafi ba don bamu damu ba tunda ba uban mu bane ya mutu.
Bakin nan naki ai sai ke ni dai ban son hakana kuma banji dadin zuwan ku ba tunda baku sanar min ba idan muyi laifi kayi hakkuri bamu sake hakan na fadi tare da barin dakin waini nayi fushi.
A raina nace mun dai je munga abinda ake boye muna din idan shine ba a son mu gani ashe bayan tafiyan mu sai da sukayi kaca kaca da Nafisa a can .
Wai ya munafunce ta bai fada mata zuwan mu ba sai ganin mu tayi kwatsan yaja mata abin fada a gurin mu ke nan shima ya rufe ido yayi mata cin mutumci a gurin sai da aka raba su.
Shine karin takaicin shi damu fati ma da ta shigo sai da sukayi fada tace baka son muje ka hada mu yace gulma dai ya kaimu tace in ma gulman ne mun dai tafi din.
Haka yai ta shan mur shi kadai ba wanda ya kula shi a cikin mu dama momy ta koma tin kan ya dawo don haka bai samay ta ba a gidan.
Ya gaji donn kan shi ya sauko ta nemi shiri damu ni kuma na hau ranan nice da girki sama sama nake dashi na aje mai abinci zan fita yace wai ke mai kike shawa wanan kamshin ne haka.
Nace kamshi akan may inma kamshi ne aikai ka fara sha muda muka sadaukar da ran mu muka bata lokacin mu zuwa maka kara baka gode ba sai ganin laifin mu .
Ashe zuwa gidan kishiya baida dadi ka bari taje namu gidajen sai itane don munje mata abin arziki zakace bamu kyauta ba.
Kin san yadda mukayi da ita dans san taje nifa akan yaran da kuka wahalar min nake wanan ba don komai ba in ma ba gaisuwa kuka tafi ba ai kanku kukaiwa.
Ni ki zauna ki zuba min abinci naci don yunwa nake ji yanzu nace bakai bane a raina, ina zubawa ne yake fadin ya kamata ku koma haka na don karatun yaran nan kada ya lalace.
Kofa wata daya kwakwara bamu cika ba ina gani gaskiya nikan ba yanzu zan koma ba sai nayi wata uku a gida kafi in koma wanan kasan.
Zance dai kike so don naga ke karatun yaran bai damay ki ba ko kadan in ma ya damay ni sai na tauye kaina don su.
Ban kara magana ba na zuba naja kujera na zauna tare da fadin yarinyar da zamu da ita tananan ta iso yace ok Altine din ba zata koma ba ke nan.
Nace naji kamar momy tace aure zata daura fa don tunda muka dawo ta bugo min waya sau daya sai ko da mahaifin nafisa ya rasu ta kira bata kara kirana ba.
Yayi murmushi yace ita tana ganin tayiwa kanta mafita ke nan duk da dai ba a hana aure amma auren ta nawa idan tayi wanan don tun ban karasa cika saurayi ba take aure.
Don ma bata haihu da yawa bane jikin ta bai nunawa aida yanzu ta ragwabe suma mazan dake auren nata ne basu da aikin yi ai.
Nace bakaji masu iya magana sunce guban wani zuman wani kai ke ganin ta ta tsufa sukan shar suke ganin ta ai.
Hiran yasa gaba dayan mu muka mata da zancen fushin da mukeyi da juna muka buge da zancen Altine har wani lokaci.
Zaman mu da fati akwai fahinta sosai don ina guje ma abinda zai kawo wani baraka a tsakanin mu don haka ne muke zaune lafiya da ita bani shiga zancen ta idan ba itace ta sakani ba.
Satin nafisa biyu ta dawo abuja da yan uwan ta gidan ya koma cike kuma sabanin da muke mu kadai sai yaran mu nidai ba a samu matsala dani ba sai dai da AntyFati ne suke dan tabawa akai kai.
Sai da maigidan ya dan tsawata masu kan hakan suka dan bari amma suna dan tabawa a boye don Nafisa ta tsani zaman fati a Abuja.
Na fito da safe mukai kicibis da wasu mata sun fito gurin nafiss ban son tankasu ba sai da naji dayan tace min hajiya khadija mun tashi lafiya ?
Na dakata ina kallon matar kamar na taba sanin ta sai tayi murmushi tana fadin nasan baki gane ni ba ko ?
Nace na dai sanki amma wallahi na manta inda nasan ki tace kin manta da madam mai zuwa gurin Nafisa a baya can.
Nace a, a mama kece wallahi mun dade bamu hadu ba tace wallahi kwanaki nazo akace yanzu waje kike zama da maigidan.
Nace hakane yaya bayan rabo tace sai Alheri dama ina tason mu hadu in rokeki gafaran akan abubuwan da suka faru a baya.
Mota zan shiga don har na bude ne na tsaya muna gaisawa dasu nace baki min komai ba mama in makin min to na yafe maki.
Sai ta fara sharan kwalla nace tafiya zakuyi ne in rage maku hanya don fita zanyi tace dako mun gode don wurin nan naku ba a sanun abin hauwa wasan dadi.
Mun dauki hanya har lokacin tana dan sharan kwalla a fuskan ta sai naji dayan tayi magana tana fadin ki fada mata gaskiya don baki san ranan da zaku kara haduwa ba.
Dan juyowa nayi nace wani abune mama datan tace wai gafaran ki dai take son roka akan abinda sukayi a baya akan ki.
Sai madam ta karbe tana fadin don Allah hajiya kiyafe min nasan alhakin ki na cikin abinda ke bibiyana yanzu don tun wanan ranan dana fadi a gidan ku ban kara lafiya ba har yau din nan da muke magana.
A ranan ma mun yo daukan asiri ne da zamu shafawa diyan ki sai abin ya juye a kaina nan dai ta shiga bani labarin abinda ya faru a ranan da ita.
Tace yanzun ma tazo don nafisa a baya ta gujeta sai yanzun kuma ta nemay ta wai tana son suci gaba da harkan su na baya.
Tana son a illanta yayana dani kaina da kuma fati a rabata da gidan ga baki daya sai dai na fada mata yanzu ba da bane bazan koma wanan harkan ba shine tayi muna koran kare kona mota bata bamu ba.
Zaki iya fadin wanan maganan a gaban maigidan mu mama na katseta da tambaya don jin may zata ce zan iya idan har hakan zai sa Allah ya gafarta min .
Don nasan koda banyi mata ba wata zata nema tayi mata wanan aikin nikuma nasha alwashin fada maki gaskiya dama don ko ban ganki a yanzu ba zanyi kokari in nemay ki.
Ni mama ga Allah na dogara babu ab
inda zata iya min da yardan ubangijina duk abinda take nufa akaina na sheri akanta zai koma.
Tace kawarai kuwa niko nasan hakan don irin daukan da muke a kan ki kina katarewa abin akwai mamaki don ba karamin tsari ke jikin ki ba.
Yaran nan naki ma saai ince sun fiki tsari don su kila kokuwan su na tagwaye ne ya hade danaki yake aiki a kansu.
Kada kiji komai mama ni ina tare da Allah ko da yaushe don gare shi na dogara ga duk alamurana ban shigo gidan mijina da wani sihiri ba ko magani da ayar Allah dai na shigo a bakina.
Na sauke su bayan nayi alkawarin zan nemay ta ta bani nomban wayan ta na bata kudi zai kai dubu hamsin nace tasha magani dashi tana tayi min godiya da fatan Allah ta tsare ni da diyana.
Na wuce gidan maryam ina tunane a raina kan Nafisa wai ita wata irin mace ce kamar dutse wurin tauri ita watau mutuwar mahaifin ta bai shige ta ba ke nan ko.
Ina shiga gidan maryam tunanen yarana da banyi warning kada a bari su fita ba ya fado min a rai nan nakira laraba ina tambayan ta yaran.
Take fada min wai suna waje gurin security suna wasa nan na hauta da fada maryam na falin na shigo ina fada da laraba tana saurare na.
Bata taba jin ina daga ma laraba murya haka ba irin yau bayan na gama ne na aje wayan take tambayana.
Nan nake fada mata abindake faruwa dani duk abinda madam din ta fada min dan lokacin daya wuce tace wai wanan matar may take nema a gare ku ne da har yanzu batai saduda ba.
Nace may ko take nema banda ran mu dai take so maryam idan ta lalata min yara ko tayi masu wani mugun abu wa gari ya waya.
Wanan katon bazan yarda ba maryam idan matar nan tayi comfention bai yarda da ni da kaina wallahi zan dauki mata a kan su.
Wa zai ji wanan abin bai dauki mataki ba sau nawa ake wanan maryam wani mataki kika taba ganin ya dauka a kanta koda ma ya dauka din ai na dan kwana biyu ne ya bari.
Na dade a gidan maryam kafin in dawo gida na samu yaran na falo suna kallo kan su na shafa kagin in zauna ina fadin.
Laraba kin jini hankali a tashe na kiraki ko nan dai nake labarta mata komai ta rike haba tana salati tace haba ina nan ina fadin may na nayiwa hajita yau.
Sai na koma ganin bakin nafisa ko maganan ta ban son a dauko a gidan sai dai ban gama yanke shawaran abinda zanyi ba akan abinda madam din ta fada min.
Ranan dana karbi girki ne ina gurin shi ne muna hira na jeho mashi zancen nace kasan matar nan madam aminiyar nafisa ta da lokacin da ina amarya.
Yace wanan bakar matar wai tana inane yanzu nace ranan na ganta a gidan nan ta fara fada min wasu magana da ban fahinta ba nace ta bari zan nemo ta ta fadi a gaban ka gamay da yaran nan.
Yara kuma may ya samu yaran ya tambaya cikin kura min ido yana son jin ba asin maganan nacw wani magana take fada min wanda ni ban fahince shi ba.
Yace ki gayyato ta gobe tazo karfe biyu zan dawo mu saurare ta muji abinda zata ce amma ina mamakin may ya hadata da yaran kuma.
Nifa ban yarda da wanan matar ba tuncan bata a cikin tsarina haye jayen nafisa ne kawai ta dauko muna ita amna dai ai ka bari tazo muji may take son fada muna ne , .
Na fada maki gobe tazo karfe biyu sai dai don Allah ki una min gobe din idan Allah ta kaimu don gudun mantuwa karna manta da zance.
Allah ya kaimu nace ina kokarin tashi daga inda nake zaune naji ya ja wani uban tsuki na juyo yace ban son cakwalin mata wallahi.
Nima shine ai nake gudu amma tunda ita ta nemo mu ai mu saurareta muji abinda zata ce tazo din muji ai na kwashe kayan nabar dakin zuwa part dina don na samu abinda nake so.
Don haka n fara nemo shawaran anty hauwa tace bafa sakwa sakwa zakiyi ba khadija Allah ya kawo lokacin tonon asirin ta gaban Jamma,a


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/30/21, 6:21 AM - Fatima Amarya: Yau bai fita ba yana zaune a falo tare da yaran shi sadiyace a kusa dashi kwance sai idan taga wanda ta sani yana mata wasa ta kama dariya.
Anan yake karban bakin shi yau kasancewar bai leka ko ina ba sai ko buge bugen wayan da yakeyi daga inda yake zaune.
Hakan yasa Nafisa jin haushin rashin fitan shi ta samay shi gurin a dakile take mai magana yau girkin yar so ne ba a leka ko ina ke nan?
Ya dago daga abinda yakeyi tare da fadin ashe akwai yar so a gidan da wa yanda ba a so ke nan sai da kika fada na sani ai yanzu.
Akwai mana yanzu ga zahiri nan ya nuna da kan sa yau take sabuwar amarci a gare ku ke nan kuma ko wani sabon shirine haka ya taso ma ban sani ba.
Ke kinga ban son daukan magana ke ko yaushe mutum bai maki daidai ne sai kin samu abinda kika daure mutum dashi.
Bake ya kamata ki fadi maganan nan ba tace don may an mun ba daidai ba zan yi magana ba yace ke akwai wanda yakaiki samun dama na a gidan nan bayan ki.
Tace zancen da ke nan kake mun ba yanzu ba da ake kirana banda ilimi bayan ansan bada illimi ka aure ni haka na.
Yace sau nawa ina cewa zan maida ke karatu kina nuna min baki so, haka sai yanzu ne zaki zo da wanan maganan.
Dama can ba so kake inyi ba don kasan abinda kake nufi dani sai yanzu na gane hakan daga yanayin ka.
Yace tunda kin gane may ye na magana yanzun kuma sai a barshi a yadda kika fahinci manufana din suna cikin wanan takkadaman ne na fito na samay su a falo .
Kokarin, zama nakeyi ina sauraren su gani na baisa ta fasa fadin maganan da take fadi ba a lokacin take cewa wai wa nafi boko da wayewa da zai dauke ni ya fita dani waje ni kadai.
Kokana tsanman bamu fahinci nufin ka bane wai duk tsiyan mutum dai wani yafi shi boko da wayewa don ba a kanta farau boko ba.
Ina jin su nace yanzu kuma na daina tsafin da boko nake maki sallo ke nan idan kin yi fushi ai sai ki fara yau koda yaki da jahilci ne ko zaki san Annabi ya faku.
Kece jahila da baki amfani da ilimin ki sai kin hada da tsafi da asiri kin kama miji dan ya fita zancen kowa idan kin kama su shida wanan bakar matar tashi ni ba zaki taba kamani ba kin sani.
Wacece bakar mata muryan Fati ne dake fitowa take tambayan ta a bayan mu tace duk sherin ki Nafisa sai kin gani a gidan nan.
Ke ba a kyamace ki ba sai kece wai zaki kyamaci mutane alkadaein rinki ya dade da karyewa a gidan nan tunda Khadija ta shigo gidan nan ko.
Don duk wani abinda kike takama dashi khadija dai tafiki shi a yanzu don ko kumbar kafanta baki kama ba a wurin komai wallahi.
Tace karya kike wallahi gashi nan ki tambaye shi don ita ma tasan bata kama kafana ba a gidan nan nace gurin sheri ba lalai kam ban kama kafan ki ba kan wanan.
Sai dai duk sherin ki ki sani bai tasiri akaina koda na ke ma fada dake tsayawa bata baki ne ai don matar da bata san Allah ba may zai sa a tsaya bata lokaci a kanta.
Sai dai ki sani idan baki bar shige shige a kaina ba kina gab da haukacewa wallahi tace samad kadai ji may tace da bakin ta.
Barin fada maki in har kin je gun malaman ki ne sun fada maki haka to nafi karfin ki da malaman naki don kar nake kallon ki duk wani iya shegen da kike tunanen kin iya na damaki na shanye a gidan nan.
Kai ya isa haka yace yau dai duk karyan mai sheri zai kare ai don gaskiya zatai halinta don in har naji wani abu da bai kamance ni ba zanyi maganin ko wanene a gidan nan.
Baku kadai bane mata a garin nan kuma ban ce zan zauna da mace daya ba a cikin ku da kowan ku ta aure ni ta samay ni da iyalina duk abinda kuke yi na sani tara maku nakeyi kawai.
Ya dauki waya yana fadin zaki iya shigowa yanzu yana fadin haka ya kashe wayan tare da cewa duk ina son ku natsu ku bani gankalin ku ga baki nan tafe yanzu.
Kowa ya dauka wasu baki ne zasu shigo sai ni da na san zancen ko ni kuma ban dauka cewa ita din bace a lokacin zata shigo.
Mun dai kai wani lokaci ba mai magana a falon sai harare hararen juna mukeyiwa junan mu daga inda kowa yake zaune a hasale da dan uwa.
Sadiya tafara dan fitina ya juyo inda nake yana fadin ki dubata kila wani kazantar tayi kin santa da tsabtan banza naji wani iri a raina sai can na dan mike zuwa wirin yarinyar.
Na fara duba permpers din jikin ta na samu fitsari tayi shine yake damun ta ina kokarin cire mata ne na kai zaune dama da wani a hannuna da na dauko in canza mata uwar sai wani tabe baki take faman yi.
A lokacin madam da wanan matar sukai sallama ya karba masu Nafisa dake zaune ta wani dan zabura sai kuma ta dake tana fadin may kuma ya kawo ku gidan nan yanzu na fada maku ban son bakin nacin tsiyar nan fa kubar mutum ya huta hakana don Allah.
Sai ga madam ta zube a kasa da kyat tana fadin barkan ku da hutawa Alhaji ya amsa mata fuska ba wani walwala sai Nafisa tace wanan akwai makwaidaita.
Mutum baida wani moriya sai bakin nacin tsiya haka ke rufa min baki don ba gurin ki suka zo ba ko ta ce gunki tazo da zaki tare da wullakanci.
Watau kinci moriyar ta yanzu Allah ya mayar da ita haka kike gudun ta ko ke ko kunya baki ji na yiwa wanan matar data rike ki amana da can waya san tsakanin ku.
Madam dake dan share kwalla tace wallahi Alhaji wanan abin yasani yin nadaman sanin wanan matar a yanzu don a sanadinta ne naci karo da wanan halin rayuwan da nake ciki a yanzu.
Nafisa tace da kike min wahala ba biyan ki nake a lokacin ba ko a banza kike min duk abinda kike min din a lokacin.
Haka kika dauka ke wanan dalilin yasa nazo gurin Alhaji yau in fada mai komai da mukayi dake a baya ko Allah zai sausauta min halin da nake ciki yai min rangwamay a halin da nake ciki.
Ta kare magana tana sharan hawaye da gefen gyalen ta yace ke nan kun dade kuna aikata wani abu wanda bai dace ba har kike ganin yana daga cikin abinda zai sa ki samu lafiyan ki idan mun yafe maki.
Tace kwarai kuwa Alhaji Abdul samad don wallahi mun aikata maka abubuwa da dama kai da iyalin ka sai hajiya khadija ce tafi katfin mu.
Don dama an fada muna tun da zancen auren ku ya taso da ita kan idan muka matsa zamu iya ganin ba daidai ba kasan abinda zuciya ke so ni kuma dan abinda take bani a lokacin yana rudina sai idon mu ya rufe ala dole sai munga bayan ta tabar gidan nan da karfi da yaji.
Nafisa ne ta tare ta tana fadin sheri kika zo ki min ki kashe min aure na ko may ke kinki aure don nace na tuba bana wanan harkan yanzu kike son ki kulla min sheri.
Babu sheri a cikin zance na yanzu ke ma kin sani don shekaran jiyan nan kika kirani akan mu dora a inda muka tsaya kina son in sa a lalata rayuwan yaran hajiya khadija ko ta halin kaka.
Mazan a maidasu yan shaye shaye da sata macen kuma a lalata mata rayuwa ta dinga bin maza dakata don Allah yace a hasale.
Madam taja bakin ta tayi shiru ya juya wirin nafisa yana fadin kunyi haka da ita ko bakuyi ba tace yaushe rabona da wanan matar samad.
Tun kan natafi Niger din nan da muka samu matsala dakai na tafi tun lokacin ban kara ganin ta ba sai yanzu yace bata zo gidan nan ba shekaran jiya tace tazo kuma na koreta.
Madam ta dago kai tana fadin kai kiji tsoron Allah matar nan kece kika kirani da inzo kira hudu kikai min kafin wanan yar uwan tawa tace muzo muji may kike nema na dashi.
Tana kokarin ciro wayan ta daga post din ta tace gashi ga kiranki a wayana har yanzu idan karya nake maki tana kokarin nuna mashi kiran a wayan ta.
Ya dan karba ya duba ya kada kai ya kallo nafisa tare da fadin gashi kece kika kirata ya fara fadin lokaci da rana ya sake dago kai ya kalle ta.
Madam tace ba wanan ba ai ina da record din maganan da mukayi dake a ranan don shedan haka don nasan koda ban maki ba wata zaki sa tayi maki tunda kinyi niyar hakan.
Kuna muna recording din muji yace ba tare da ya kalli kowan su ba dan lokaci ta dauko tana neman recording din ta miko mai wayan.
Nafisa ce ta mike zubur tana fadin Allah ya isa tsakanina dake madam sherin da zaki min ke nan bayan yadda na dauke ki a zuciyana.
Zaki rufa muna baki ko sai na bata maki rai taja bakin ta tayi shiru tana mazurai zaune nake na harde hannaye na saman kirjina ina kada kafa a gefen shi tunda na sakawa sadiya permpers nake gurin ban daga ba.
Bayan gaisuwa ta fara fadin dama na kiraki ne mu dora inda muka tsaya don na gane su sabuwa kudina kawai suke ci a banza yanzu.
Aiki dake yafi min dadi sai madam din tace hajiya aiko da ban guje ki ba ban kuma yi tsanmanin zaki min hakan da kikayi kika guje ni ba.
Yanzun dai kada mutsaya dogon bayani dake wanan yar banzan yarinyar nake son a shiga tsakanin ta da maigidan nan suyi rabuwan wullakanci da junan su don ba zan zauna ina kallo yana tafiya da ita ba ina zaune.
Sai yaranta da nake son a lalata masu rayuwan su tun yanzu su danbale ya kasa tsaron su don ba zance ayi yadda akaiwa fati da diyan ta ba don gashi yanzu itama bata zauna ba tana kokarin dawowa cikin rayuwan shi har daukan diyan yayi yakai waje karatu.
Madam haka zan zauna duk buri ba akan Samad ya tafi a banza ina son in gama da wanan fitsarar kafin in dawo kanshi shi maigidan.
Madam tace hajiya Nafisa ba zan maki karya ba gaskiya na daina wanan harkan yanzu wanda ma nayi a baya ina rokan Allah ya gafarta min ne.
Kema da zaki bi shawarana da kin daina wanan harkan na bata don babu komai a cikin sa sai tarin nadama da dana sani mai tarin yawa a cikin sa don ni sheda ce kuma na gani.
Katse ta Nafisa tayi tana fadin dakata madam ba wa,azi nakiraki ki min ba anan taimako na nema a gare ki idan ba zaki iyaba sai in nemo wata tayi min abin kudi ba fa kyauta zaki min ba kin sani.
Haka kawai don guntun wa,azin ki in zauna ina kallon gida nason fita a hannu na tun shigowan wanan fitsararan yar matsafan na kasa gane kan gidan nan ga baki dayan shi.
A nan recording din ya katse sai madam ta dora da fadin nayi mata wa,azi yadda zata fahince ni karshe ma sai koran kare tayi min da mugun fata ta hanani kudin mota.
Haka muka fito muna tunanen yadda zamu koma gida don ko na zuwa aro tace inyi muzo sai Allah ya turo muna hajiya khadija zata unguwa itace ta taimaka muna ta sauke mu a gida.
Shine dalilin da naji ya kamata in nemaku in fada maku gaskiyan irin kuskuren da muka tafka a baya ni da ita don ni gaskiya yanzu na tuba nabi Allah na daina wanan halin ga baki daya wallahi.
Munyi sanadin rabaka da iyayyen ka mun raba tsakanin ka da matanka fati gata nan da diyan ka da ma kokarin rabaka da khadija wace ta buwaye mu ita da yaranta sai aminin ka babba abokin ka yusuf shima mun sha zuwa guri kanshi muga mun shiga tsakanin ku.
Khadija mun hana aurataya a faru a tsakanin ku dayake Allahku yafi namu sai aune da ciki mukayi a jikinta a lokacin gun wanan lokacin na tsuke da lamatin khadijan.
Dama ana fada muna duk inda muka je cewa ita tsaye take ga kai kukanta a gurin Allah ko yaushe ba zamu iyata ba kaji dan abinda na ke da niyar fada ma dama don Allah ku gafarce ni ga baki dayan ku ko zan samu sa,ida a raina.
Bayan ya nisa yace da da fa kikace hajiya wanan zancen ya wuce dan labari ai don rayuwana gaba daya kuka gurgunta dana iyalina Nafisa may nayi maki a rayuwana kike nema kiga bayana.
Shiru tayi sai kwallan da take matsa a fuskanta yace ba kuka zakiyi ba bayanin zaki min yadda zan fahinta.
Shiru falon yayi na dan wani lokaci sai fati ne tace tsakani na dake nafisa Allah ya isa wallahi don ba zan taba yafe maki ba.
A baya ina zargin khadija da tazo ta mallake mijin ita da tazo daga baya ta samu fifiko akan mu da komai sai daga bayane nazo na gane ba haka rayuwanta yake ba.
Ita di mai kaunane da yara na ban kai ga tabbatar da haka ba sai da yazo da zancen zai kai yara karatu madina inda ni da yan uwana muka zauna suka kara fahintar dani kan khadija din sosai.
Dan zaman mu da khadija ta fitar dani daga wani kangin rayuwan da na shiga a baya na gane tana kokarin kusantani da mijinane sabanin ke dake kokarin nisantani dashi a baya.
Zuwan mu can inda suke zaune ya kara gaskanta mun tunane a kanta yadda ta rike ni kamar ba kishiya ba har girki ta bani acan da kuma muka dawo nan ta kwadaita min zama daku a guri daya.
Ke ko fa ba wani alheri ga shigowan ki a rayuwan mu sai komawa baya tirda hali irin naki wallahi madam tace baku gane ta bane tun farko don ta taba fada min a baya so take ta kammala mijin ku ta kwashe komai nasa ta koma kasan su da zama don tasan ba zai bita can ba ya zauna.
Nafisa kinji duk abinda aka fada ba karya a cikin sa halin ki ne kuma zaki iya yin shi ke kuma madam na dawo gare ki kafin in san irin hukuncin da zan yanke a kanta.
Yanzu wanan abinda ya samay ki idan kina da tunane ya isheki ishara akan sa tace kwarai kuwa Alhaji na dade da nadama batun yau ba.
Don ni nasan abinda nagani kan son mu halaka yaran nan kokuwan su ya dawo gare ni shine har yau ban kara lafiya ba don dama ance tagwaye akwaisu da kokuwa a tare da su.
Ba tagwaye na ba kawai duk dana koni duk wanda yayi gigin tabamu a gidan nan zai ga abinsa don banyi wa kowa sheri ba don haka wanda ya nufo ni dashi a kansa zai koma.
Karya kike wallahi an fada min yadda nake tsaye kema haka kike tsaye a gidan nan madam ce ta ba ta amsa tace don ance muna tana tsaye ba ana nufin abinda mukeyi shi takeyi ba na dade da fada maki hakan amma kin ki kiji.
Nafisa you are very stupid har kina ganin kin samu bakin magana a gurin nan yanzu kin san girman abinda kikayi kuwa.
Rayuwan mu ne fa gaba daya gidan nan kike nema a hannun ki don baki da kunya har zaki dauka kinci bulus ke nan ko ba zan sake ki ba ko in kore ki kin ci albarkacin wa yan nan diyan da muka haifa dake.
Amma zaki zauna a gidan nan zama na dake da babu duk daya a gurin kowa kada kiyi tsamanin zan barki ki gudu ba gudu ko zuwa wani guri a wuri ki.
Don duk inda kika shiga a duniyan nan sai na tonoki ki zauna yadda kika so ganin sauran ke ki zauna a haka kuma zan kara fada maki wasu dokoki da zan kafa maki.
Amma kafin nan yanzu barin sallami wanan matan mutanen ki yace su tashi su fita suka mike suna muna sallama suka bi bayan shi.
Ya dan jima waje tare da su kafin ya dawo ya samay mu sai zuba habaici anty Fati keyiwa nafisa bata samu bakin maganan ramawa ba.
Koda ya dawo bai furtawa kowa komai ba ya haura sama ya barmu a gurin naso jin matakin da zai dauka amma sai ya bar mu a duhu ga zancen.
Itace ya kamata tayi girki a ranan sai yace fati ta karba nidai ido na sa mashi har in fahinci may yake nufi da mu kan zancen.
Sai bayan kwana biyu ne na fara fahintar komai don haka zai dawo ya zauna damu a babban falon gidan da yaran mu nan zamu zube ai ta hira da raha ita kuma tana daki da yan uwanta ba wani walwala ko ni shadi a tare da ita.
Ga Ihisan daya hana ta zuwa gurin Nafisa din koda wasa yarinyar ta tsorata sosai dashi bata zuwa wurin nafisa din koda baya gida.
Haka yasa samira ma ta dawo mu,amula damu idan muna falo itama anan zata zauna gurin mu koda uwar ta kirata minti biyu yayi yawa zata dawo inda muke din.
Har komawan mu yayi wanan karon da Ihisan muka tafi Nafisa ta tayar da hankalinta sosai har takai karan shi gurin iyayyen shi.
Abba ya kirashi nan dai ranan ya warware ma Abba komai na zaman su da nafisa din bayan ya gama sauraran shine yace ka kyauta da bakai saurin sakin ta ba.
Don idan mace ta kauce irin haka ba saki ne abin yi gare taba kamata yayi namiji ya horata a gida ko zata gane ta dawo hanya madaidaiciya ta gyara halin ta.
Idan ta gyara zaka gane idan kuma ba mai gyaruwa bace zata koma ma halinta kaga a wanan lokacin duk matakin daka dauka a kanta shine daidai.
Amma sakin baida wani amfani gare ta sai kaga mace bata hakkura ba ta koma ga wani hali wanda bai dace ba yanzu dai idan tana da hankali zata gyara halinta tunda ta gwada taga ba wani riba ga mace mai irin halinta.
Shi saurin saki illa ne gama ga haihuwa a tsakanin ku duk inda tabi dole mutane suyi kwatance da kai suna fadin tsohowar matar wani ne uwar yayan shi.
Sai yara su taso basu san abinda ya hada iyayye fada ba sai su dauka don wance aka saki uwar mu ba sauran shiri tsakanin su da wanan matar ta gida kaga an samu akasi a gurin.
Don haka na gamsu da bayanin ka don ba matar da za a barma diya ta tarbiyartan dasu bane da wanan halin nata.
Yayiwa Abba godiya washe gari muka daga muka bar kasan nan muka barsu da Fati a abuja zaune ba wanda ke shiga alamarin dan uwa.
Bayan wata uku yake shigowa ya koma wanan tafiyan mun dauki lokaci sosai bamu zo Nigeria ba har muka kai sadiya asibiti akai mata aiki a kanta watan mu daya a can Anty Fati ne tazo ta zauna muna da yara har mu dawo.
Alhamdullahi aiki yayi kyau sosai don an gyara kan ya koma daidai yanzu ta fara tafiya bata san uwarta data haife ta ba sai ni ba wani ban bancin da nake nunawa a tsakanin su da diyan dana haifa.
Sai dana kara haihuwa ya bari nazo Nigeria lokacin na bunkasa sosai na kara ilimi yadda ya dace ko wanan zuwa munyi shi ba a cikin dadin raiba don jikin Abba da ya kiya yana asibiti kwance.
Na daukarwa yarana hutu muka shigo Nigeria yarinyar da nake riko itama ina jin dadin ta ban barta ta zauna haka ba sai da tayi karatu a can.
Mun zo da kwana daya muka wuce kaduna duba Abba ranan yayi fada da anty fati na rashin zuwan su duba Abba din don cewa tayi bai bada bakin su tafi bane.
Don haka bamu je tare dasu ba yara kawai muka aje a gidan wurin Binta muka nufi asibiti inda muka samu Abban a cikin wani yanayi na jin jiki sosai.
Yana ganin mu duk da sunce bai magana sai gashi yana murmushi yana son ya yunkura ya tashi ya kasa.
Mun dade a gurin Abba din kafin mu dawo gida washe gari su maryam suka iso da safe da yaranta biyu .
Sai su Anty Fati da Nafisa da suka zo suma ga zainab da yaranta muka cika a gurin Abba din don yace muzo mashi da yaran ya gansu.
Ranan anyi murna kwarai da jin saukin Abba din don alama ya nuna ya dan samu lafiya ina hada mai abincin da zai kara mai kuzari ya kara jin katfin jikin shi sai gripe water irin na yara da nake sa momy ko anty amarya su bashi.
Don yana taimakawa sosai gurin mutumin da ya dan manyanta ya ji karfin jikin shi ba wani hayaniya sai dai na kula da Nafisa dake son jan yaranta a jikin ta.
Yaran daine basu bude ido da ita ba don haka basu damu da al,amarinta ba ko inda take basu zuwa.
Ga na kula har lokacin ba yarda a tsakanin ta da maigidan da ma yan uwanshi dake yawan hattaran ta a kusa dasu.
Satin mu daya Abba yace ga garin ku muka tashi a cikin tashin hankali don ban tabs ganin AA ya shiga irin halin da ya shiga ba a ranan.
Anyi zaman makoki na kwana uku mutane suka watse har mutanen Niger ( minna) sunzo mota uku yan uwa da abokan arzikin mu da yan uwana na Ka,oje suma sai da suka ciko bus sun zo min gaisuwa don muna zumunci sosai dasu.
Satin mu uku kaduna muka dawo Abuja inda yanzu nauyi ya karu akan AA din Allah ya taimaka yana da karfi sosai ya kawo saukin abin.
Don bamu dawo ba sai da ya hada kan gidan nasu ya ba wa kowa abinda yake bukata ya biya wa yan makaranta kudi school fees.
Nan ya gane tsohon ba karamin kokari yake akan iyalin shi ba gashi ya hada kan zurian shi guri daya kafin ya tafi ba wani baraka a tsakanin su sai dai wanda ba,a rasa ba din.
Ranan da muka dawo don su Nafisa sun rigamu dawowa ita da Fati sai daga baya muka dawo nafisa tayi abinci amma da muka iso tace tabar min girki nace a a tayi abinta.
Nasan yana daga cikin halin da take son nuna mashi ne na nadaman ta a yanzu sai dai duk wanan abin bata burge shi ba don tsanan ta ya riga da ya darsu a zuciyar shi ko.
Zaman dai suke hakana bai yarda wani daga cikin mu ya nuna mai banbanci a gida ko kadan wanan abin yana damun nafisa don kishi a zuciya yake haline na halitan mace sai dai na wata yafi na watane kawai.
Idan ya tuna da maganan Abba yakan ji jikin shi yayi sanyi akanta yaso yayi koyi da abinda Abba din ya koyar dashi.
Da alama ba zamu koma kasan waje ba don yaran daya nemawa makaranta anan yanzu suna falo zaune na fito da yara zan kaisu islamiya ko wanin su yasha fararan kaya da hula.
Sai sadiya data rike min hannu muka fito tare tana min shagwaba nayi masu sai mun dawo nafita da yaran ta bimu da kallo.
Lokacin maigidan baya gari yayi tafiya washe gari koda na fito banga motar nafisa ba yasa nasan tafita ne har na dawo gidan maryam ina zaune ina cin abinci wayana yayi kara na dauka.
Yusuf ne muka gaisa yake tambayana ko akwai wace ta fita ne a cikin mu nace ban tsan mani ba sai dai barin sa Sadiqa ta duba min.
Ta dawo tace ance nafisa ce ta fita na kirashi ina fada mai yace to sunyi accident yanzu aka kirashi ana fada mai hanyan keffi.
Na maimaita kefi kuma yace eh gashi ma yazo asibitin da aka kawo su sai dai ance a motar wasu sun mutu wasu kuma sunji ciwo sosai.
Hankalina ya tashi na mike na fito ina fada ma fati tace subbahanallahi.
Dama tunda naga ta fita ko sai dawo batai muna ba nake zargin wani abu Allah dama ba azzalumin kowa bane yanzu haka wurin bakar biye biyen bokayen su ne haka ta faru dasu.
Nace kada tace haka ya kamata musan da wa yanda ta fita samiha tace da yanyala suka fita dawata kawar su.
Munje asibitin mun samu tana a wani hali ba a bari mun ganta ba sai yake fada muna sauran sun rasu ko take a gurin da abun ya faru.
Ita ma dai tana a wani yanayi ya kira AA bai samay shi ba yana dai trying din layin shi har yanzu salati na saka tare da fadin yanyala ce wanan dattijuwar da suke tare.
Sai dare ya samu layin AA din yake fada mashi abindake faruwa yace gamu tare a gurin su yace a bamu wayan ko ya saka a handfree kowa yaji.
Ya fara fadin may yasa kuka fito bada sani na ba ku koma gida kada kuma wace ta kara zuwa asibitin nan a cikin ku dama amana ai gudace na fada mata duk wanda yaci amanan wani a cikin mu Allah ya baiyana shi.
Yanzu gashi ashe bata bar wanan halin nata ba zanyi magana ya kashe wayab shi dole muka dawo gida kamar yadda yace don bin umurnin shi.
Sai dai ina tura laraba ko Sadiqa sukai masu abinci acan saboda Allah bayan kwana biyu ya dawo garin abincin ma daya gane ya hana kuma baije asibitin ba ya dubasu.
Kafanta ance sai an fita da ita waje har kano aka tura su sunce bazasu iya ba sai dai idan yanke mata zasuyi a nan.
Yan uwan ta sunzo daga Niger sani Allah sani Annabi ya yarda ya bada kudi koshi don hajitan su ne data saka baki ya yarda aka fita da ita waje.
Watan su hudu a can ta dawo saman keken ta ba kafa ba zuwa gurin boka miji kuma bai kulata tana dai zama a gidan zaman takaici da dana sani.
Tana kuma kallon gata da ranta anayi bada ita ba ga duniyan ga komai amma jin dadi yafi karfin ta yanzu sai dai ido.
Nikan sai yara nake zubawa a gidan sai dana haihu bakwai dashi na dakatar da haihuwa badon ya so ba ga aiki da nake dan tabawa ina aiki da humanright yanzu.
Masha Allah da fatan kun fahinci darasin da wanan sakon ya kawo maku badon kowa zai gamsu ba sai wanda Allah ya ba ikon gamsuwa da hakan dogara ga Allah shine mafita, ga bawa.
Kyau ko nasaba bashi zai kai mu ga abinda muke burin samu ba kyakyawan hali da dogara ga ubangijin mu shine alfanu gare mu da fatan zaku yafe min kurakuren da na rubuta a ciki sai mun hadu a sabon labarin mu mai suna kanin ajali
Nagode kwarai da kaunar da kuka nuna min wanda ba hikima na bane abin daga Allah ne don Allah mu yafe ma junan mu yan uwa.
Taku har kullun zainab din ku labarina dai sai anyi hakkuri dashi akan zamantakewan rayuwan mu na yau da kullun ne a gidajen mu na hausawa.
Nagode nagode nagode da kaunar ku gare ni da fatan zakuyi hakkuri danu hakana.
Sai mun hadu ma,assalam


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
Chapter 6 · 0% Book details