Part din shi ya koma ya shiga wanka ya kimtsa cikin kananan kaya kamar kullun yana shirin fitane yaji an turo kofan daki.
Mijin Buzuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 234 min read
Ba sai ya juya ba don yanzu ya fara banbance yanayin shigowan mu dakin don zai fahinci wasu abu ga yanayin kowacen mu.
Samad ina kwana tace mai daga inda take tsaye ta kasa karasowa inda yake lafiya ya amsa mata fuska daure.
Don Allah na zo ne dama in baka hakkuri ga abinda ya faru jiya kuskuren fahinta ne wallahi.
Idona ya rufe ina ganin kamar wani abu ya faru ne a tsakanin ku a lokacin ashe ba haka abin yake ba don Allah kayi, , , , ,
Katse ta yayi da fadin idan ma wani abu ya faru a tsakanin zaki hanane ba mata na bane ita kamar yadda kema kike matana.
Ko ansa min dokan cewa dake kadai zan zauna in dinga mu,amula in bar sauran nagaji da wanan halin naki Nafisa ba zan iya daukan shi ba kuma.
Daya ke shiri take so a lokacin sai ta kwantar dakai tana bashi hakkuri don dai kawai ya kyale su ita da yan uwanta a gidan.
Duk fadan da yayi ranan bata bashi kwararar amsa ba don gudun abinda zai yi jawo mata fita yayi karshe daga dakin duk da bai taba ganin ns damarta irin haka ba amma baisa ya nuna mata ya hakura da bukatan ta ba.
A falo ya samay mu ina kwance maryam tana hada tea a kofi shigowan shi part din maryam ta rude ta shiga gaida shi.
Daga inda nake zaune na gaida tare da fadin ina kwana yace lafiya ya jikin naki nace da sauki cikin lumshe ido.
Kinsha magani ya tambaya yana mai kura min idanuwan shi yanzu zan sha idan na karya nazo dazun baku bude kofa ba.
Bamu dade da tashi ba na bashi amsa ya karaso gap dani yana taba jikin nawa tare da fadin zazzabin ya wuce ke nan ko ?
Kai na gyada mashi alaman eh don magana ma nauyin yin sa nake yi a lokacin yace raguwa kawai zan so inga ranan haihuwan ki.
Ban bashi amsa ba don maryam dake falon ta gama hada min tana miko min kofin zata shige yace maryam da zan dan samu ruwan zafin nan yanzu da nasha kafin in fita tace to barin hada maka.
Sai lokacin nayi kwakwaran magana nace haba maryam kada fa yin haka ya jawo muna matsala kuma kin dai san halin matar shi da kishi.
Zama yayi a kusa dani yana fadin ke baki kishin nawa ne komay don nagani a idon ki yanzun haka.
Dariya maryam tayi ta shige kitchen ta barmu a wurin kokarin taba ni yake ina kaucewa tare da fadin yaya samad ka bari don Allah.
Da sauri yace what kema zaki bi jahilcin Nafisa ne kina kira na da Samad bayan kin san ma,anan sunan .
Is better idan zaki fara kirana da wani sunan na daban ba wanan ba don kin san mai sunan haukanta ne yasa take kirana da hakan nasha warning din ta da tabari takine.
Maryam ne ta fito kitchen din rike da ture a hannun ta wanda ta shiryo mashi kayan karyawa a ciki ta aje a gaban mu.
Yun kurawa nayi na mike don in hada mashi yace zauna abin ki na hutar dake na yau zan hada da kaina.
Kallon yadda yake hadawa nakeyi har ya gama ya fara kurbawa a hankali ya dago ya kalleni yana fadin bazaki sha naki ba sai yayi sanyi .
Dauka nayi na fara kurbawa naji yana fadin wani irin mota kike so a rayuwan ki don zan sa a duba maku.
Nace wanda kaga ya dace dani ko wani iri ne na gode Allah saka da alheri yace ba godiya a tsakanin mu don ba zan iya biyan ku ba sai Allah.
Bai dade a zaune ba ya kube tea din ya mike kudi ya miko min na dago kai ina tambayan shi na may nene yace ki karba tukun nasa hannu biyu na karba ina sauraren shi.
Kudin ce fane ne da zaki da na sauran abubuwan da baki dashi a part din ki a shirya min abinci mai dadi don Allah.
Nace amma sai naga ai wanan kudin sunyi yawa ga cefane kawai da kara biyu don ni ina da komai a nan kallona yake daga inda yake tsaye yana fadin.
No haka dabia na yake mai girki zan bata kudi da zai ishe ta lalurata har ta amfana da sauran sai na dawo yace dani baysn ya tsureni sai da yaga nasha maganin.
Tunda ya fita bai dawo ba ga maryam ta nace akan ita zata wuce tunda na samu lafiya na kirashi a waya yace ta dakance shi ya dawo don Allah.
Da taimakon ta na hada girki ta bani kwarin gwiwan zuwa gyara mashi part din shi kafin six na kammala komai da zanyi a bangare na.
Koda ya shigo dare yayi a lokacin hakan yasa maryam bata wuce ba a ranan tun fitan shi dakin maryam ta damay ni sai in je gurin shi kada in barshi shi kadai a daki.
Na nuna mata tsoro nake ji wallahi tace haba mai zai maki yau bayan yasan baki da lafiya kuma.
Haka dole na shirya na fita zuwa wurin shi nakai mai abinci ban dade ba na dawo na kara shirya nai mata sai da safe na wuce part din shi.
Su Nafisa suna zaune a falon duk wanan sintirin da nake suna kallona tana ji kamar ta hade ranta a lokacin.
Na samu har ya gama ya kwanta ya kashe wutan dakin ina ganin haka na dauka yayi barci da sanda na isa bakin gadon na kwanta a hankali kada motsina ya tayar dashi.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Tana tsaye a bakin window dakin ta tana kallona sanda na shiga dakin wani irin shu,umin murmushi ta sauke ta juya da sauri zuwa karkashi gadon ta tare da jawo roban da ta saka.
Wani kallon mamaki takewa kayan nata ganin yadda abin ya rikide ya koma bakikkirin dashi da fargaba ta dauka tana dubawa a hankali tana mamakin ganin sauyawan abin a dan kwanakin da ta dauka bata dubashi ba.
Gabata ne ya kara faduwa sai dai bata saduda ba kara haka shi tayi kamar yadda ta saba hakawa a kulun nayau ma yafi tankuwa da kyau.
Ta gama surukulen ta ta kwanta tana murmushi a ranta tare da dariyan mugun ta tana tunane haka barci yai gaba da ita.
Jin saukan hannun a saman jikina yana gyara kwanciya tare ds sauke ajiyan zuciya yasani razana don tsoro.
Muryan shi naji yana fadin kin cika tsoro Deedar ina kallon ki tun shigowar ki fa kamar wata mara gaskiya dake.
Ai na dauka ba zaki zo bane inje in dauko ki a dakin sai lokacin nayi motsi tare da fadin tunda kai kafi kowa rashin ta ido.
Matseni naji yayi cikin jikin shi ina jin shi yana shakan kamshin gashin kaina yana sauke numfashi yakai hannun shi tare da cire ribon din da na daure kaina dashi.
Yana wasa da kitson dake kaina a hankali naji yace kitso yana ma mata kyau idan sunyi sai dai ku matan yanzu baku son kitso na gani.
Idan bamu so da zaka ga nayi kazamai ne da raggaye kawai basu son yin kitso don kiyya amma ai kitso karin lafiyan mace ne da fitan surar ta.
Au to sura yake fitarwa ashe barin fara duba yarda ya fitar maki da naki suran tun yanzu inda comment in fada maki ki gyara jinayi ya kuna dim light din dakin yana kallon fuskana.
Da sauri na runtse idanuwa na daga kallon shi ina fadin don Allah ka bari kasan fa banda lafiya yau.
Yace bamu da lafiya dai ai tare muke ciwon raki dai kika fini don ni ban nuna ba yinin yau kai nayi fama dashi sosai wallahi.
Na dan yi kokarin juyawa ina fadin ba dole ba mutum ya dawo tafiya bai huta ba ya tsaya ja, , , sai nayi shiru matse ni ya sake yi yana fadin na tsaya may ki karasa maganan ki mana.
Ban tanka mashi ba don jin yadda ya matse ni a lokacin a jikin shi hannuwan shi naji a saman kirjina zabura nayi ina kaduwa.
Yace Deedar mai yasa kika cika rakine ko tsoro haka da yawa wai ina bakin nan naki ya tafi ne mai tsiwan tsiya da fadar bakan magana yau.
Duk wanan abin yana magana kamar mai rada yana shafa na yakeyin shi niko sai faman runtse ido nake cikin wahala.
Naji ya ci gaba da fadin kin shayar dani ziman da ban iya mantawa a safiyan jiya Deedar ina son yadda kika shayar dani zuman ki a jiya ki kasan ce mai shayar dani a koda yaushe wanan ni,imar taki da Allah yai maki.
Yadda kika kasanci mace mai saukin kai da biyayya tun farko a gareni ya kasance ako wani lokaci haka halaiyan ki zai kasance a gareni da kowa na tare damu.
Wasu hawaye naji suna bin fuskana da bansan fitowar su ba hannu yakai yana fadin kuka kuma Deedar godiya yakamata kiyi wa Allah ba kuka ba.
Ki gode ma Allah da ya nufeki da da samun wanan baiwar har kikai tanadin shi yakai a inda ya kamata ina mai fatan samun zuria masu kwatancin tarbiyan ko fiye ma da yadda kika samu a wurin iyayyen ki don ni sheda ne kuma na gani.
Kukan nawa ne ya tsananta naji ya shiga aika min da kiss yana murmushin da nake jin zafin shi a lokacin.
Ta ko ina yake jagwalgwalani kamar wanda yayi sabon hauka akan haka ranan yai dai yi wasa da jikina kamar ba gobe amma bai shiga jikina ba kamar yadda nake gudu yayi.
Da safe ma bai bari na fito da wuri ba daga dakin barcin safe mukayi a tare kasancewa safiyan lahadi ne ranan bai fita ko ina nima ban fita ranan.
Sai tara saura na fito daga dakin lokacin Nafisa da tawagan ta suna a main falo tanayi tana kallon lokaci da kofan dakin don tana da tabbacin bamu fito ba har lokacin.
Jin motsina fitowa ne yasa ta kafe hanyar da idanuwan ta caraf idona suka sauka a nata bata kawar ba nima ban kawar da nawa ba a nata.
Shu,umin murmushi ta sake min ta gefen fuska tare da kada kai alaman kinsha haushi nima nuna mata nayi da alama aiko a jikina.
Na wuce su na shige part dina don na samu maryam yau ta bude min ba kamar jiya ba da na samu wurin a rufe.
Da sallama na shigo na samu ta gyara ko ina yadda ya dace tana jiran shigowa na ta wuce zaune na samay ta a falon ta jirana.
Kallon juna mukayi ta sake min murmushin shakiyanci na kawar da kaina tare da fadawa saman kujera tace amarya kina kamshi fa.
Sake aika mata da harara nayi tare da fadin kun dai cuta min wallahi mutum baida freedom din kan shi yanzu sai ace bai yi dai dai ba.
Dariya ta sake tana fadin may kuma akai maki yanzu ai gara da ke aikin lada kikeyi mu fa kun barmu sai fake maki shiya.
Ni dama ke nake jira ki fito zan tafi ke nan da sauri na dago nace haba wasa dai kike wallahi tace Allah da gaske nake yi dama ke kawai nake jira badon ma in tafi ba in bar maki shiya ga muggayen nan aida kin zo kin samu na tafi.
Nace a lalace ki tafi bamu duba kayan nan da ya kawo ba ki dauki abinda yai maki a ciki don ni yanzu basu gaba wallahi.
Da sauri ta tare ni da fadin ke ko suke gaban ki don yanzu kwalliya yake gare ki kina da wanan kishiyar haka zaki zauna ba kwalliya.
Kin san fa kwalliya na daga cikin abinda mazan yanzu suke so da kuma gyaran gida da daki gami da babban dakin hutun su.
Nace ina ni ina babban dakin hutun shi buxuwa da yan uwanta sun mai dashi wurin zaunawan su ko yaushe fa a lokan nan zaki samay su zaune.
Tace ke tafi can wake maganan wanan falon da ya zama na masaukin buzaye ana maganan HQ taki kina min wani zancen falo can.
Nace Allah dai ya shirye ki maryam mijin ki na da aiki wallahi tace wa zai zauna yanzu ai mashi sake anshani daya baza a kara ba.
Wai ke ai ba falo ba wallahi yanzu gidan naku da mutum ya shigo falon ai wani tsamin buzaye yake tariyan hancin mutum da doyin sakesakin su.
Sai fa kinyi da gaske a gidan nan kafin ki cin ma manufarki don akwai aiki ja a gaban ki khadija duk wani abu wanda kika san ba halin mu bane nan kiyi kokarin kawar dashi a cikin hikima da basira ba a cikin garaje ba.
Da sannu komai zai zo ya daidaita idan kin jajirce baki biye ma halin su kun zama daya ba sai kiga abubuwa na tafiya daidai.
Shiru nayi ina sauraren maganan ta tana ta fada min yadda zan bullowa nafisa a cikin hikima da basira ake gudanar da kishin yanzu ba a haukan da take yi ba.
Kallon ta nayi nace ki jaye tafiyan ki yau sai gobe idan zan shiga school a sauke mu tare ina ganin zai fi ta kalleni nace Allah ko haka nake ganin zaifi sauki.
Tace kan ki ake ji ai nikan bari ki gani yanzu ma zan tafi don ina da aiki a daki dana bari gashi gobe akwai shiga school shiyasa nake son komawa yanzu.
Shigowan shi ya katse muna maganan yake fadin yanzun da safen nan zaki tafi maryam ba zaki bari sai yamma mu kaiki ba.
A kunyace tace yanzun nake son komawa don akwai abinda zanyi idan na koma gashi gobe monday akwai shiga school.
Yace OK bari mu karya ga Yusuf nan yazo sai ya sauke ki a school din idan ya gama ya juya gurina yana fadin akwai abin karyawan ko na sa a sawo muna ne ?
Nace na samu ta hada kafin in shigo a ina za a kai maku kaimun falon sama yace tare da fito da kudi daga aljihun shi yana mika ma maryam din tare da yi mata godiya akan abinda tai muna.
Kai ta girgiza tare da fadin bazata karba don mun wuce haka wurin ta fatan ta dai Allah ya bamu zaman lafiya mai dorewa da zuria masu albarka .
Amin ya amsa mata yana kara mata godiya tare da fadin kusan halin ku daya da kawar ki baku son amsan alherin mutum ko wanan wani sirine bamu sani ba ?
Mikewa nayi daga inda nake na dauki kayan karin na mara mai baya zuwa sama ban samu Nafisa a falon ba nake ganin ta shige part din ta a lokacin.
Na gama zan fito ne sai ga su tare da Yusuf suna hawowa saman da rabewa nayi ina basu hanya tare da gaida Yusuf din yana min yaya jiki nace da sauki.
AA yace ai kasan maganin ta jiya ta shashi sosai shiyasa kaga ta kara samun sauki hararan shi nayi na wuce abina ban tsaya wurin su ba don nasan in na tsaya kunya zai ta bani a gaban Yusuf din.
Na koma muka bude kayan da Maryam sai faman yabon kyawon su take yi nidai ina sauraren ta wani dogon riga da muke ganin yaimin kadan kawai ta dauka daga cikin kayan tana min Allah sa a kashe lafiya.
Ita da kanta ta jera min su a gefe inda ya dace gefen wardrobe dina mun dan dauki lokaci sai gashi ya shigo part din yana fadin ta fito su tafi.
Har bakin mota na rako maryam din tare da fadin sai mun hadu gobe a school na dauka da shi zasu fita sai naga sabanin hakan .
Komawa nayi part dina nayi wanka kafin in fara shawaran abinda zan girka muna na rana sai da na kusa hadawa naji wani abu kamar kaurin hayaki yana shiga hancina.
Allah ne ya bani ikon fadin innalillahi wa, inna alaihim rajjiun a uzubikalamatillahi tamat min shedanin rajin.
Karan fashewan abu naji kamar ya fadi daga saitin window kitchen din part din da sauri na jawo buner dina na debo turaren wuta na saka sai warin abin ya daina.
Garwashi na hada tare da zunbuda turaren wuta na hayake part dina dashi na fito har falo ina yi Nafisa ce naga ta fito dakin ta da sauri sai yanyala da suka hade tare tana bude gwiwan ta taji ciwo sosai a kafan nata.
Bina sukayi da kallo ban tsaya ta kansu ba na ci gaba da turare gidan da kamshin turaren wuta muryan Nafisa ne a kaina tana fadin.
May kike nufi kike muna haka a gida sallon wani sihirin ne haka duk ki hayake mu a gidan ko may ?
Ci gaba nayi da tafiya sako sako lungu lungu ina saka kamshin yana tashi tare da ba falon wani yanayi mai dadi dama turen na waje ne anty Hauwa ta bani shi lokacin aure na.
Ganin ban fasa abinda nake yi ba aiko ta hau fada tare da shewa abinda ya dawo da hankalin AA falon ke nan a lokacin.
Da sauri ya fito daga part din shi yana fadin may nene may ya faru kuma wai may ke faruwa ne haka daku.
Daras nake a cikin kwaliyan atamfar buje da rigar da nasa na daura dan kwalin ture kaga tsiya a kaina juyawa tayi wurin shi tana fadin.
Ni wanan zata raina ma wayo a gidan nan ta fito tana wani turare muna gida haka da rana tsaka don ta raina ma mutane wayo ta samo wani sihirin ta ta saka a ciki zata zo tana muna hillan hayankin turaren wuta take saka muna.
Khadija may ke faruwa ne wai don banji abin dauka ba a wanan zancen nace wani wari nake ji shine na saka turaren wuta warin ya wuce shine ita kuma ta mayar abin fada.
Yace nima naji wanan warin ba dadi a hanci na sai kuma daga baya na daina ji ya juya gare ta yana fadin.
Yanzu may ye abin fada da wani zargi a nan fisabilillahi don an saka kamshi a gidan nan ke baki saka ba an saka zaki tsaya fada haka ba kunya yanzu ko ke baki ji dadin kamshin nan ba a hancin ki.
Zata yi magana sai ga yarta karaman ta fito daga waje tana wasa tana fadin Abbi Yanyala taje saka hayaki a bayan window amaryan ka ta fadi kasa yanzu muna ta dariyan ta a waje dasu mai gadi.
Juyawa yayi yana kallon ta da mamaki tare da mayar da hankalin shi gare ta yayin da uwar ke buge ma yarinyar baki ta saka kuka da karfin najin zafin bugun da tayimata din.
Kallon Nafisa yayi rai a bace yana fadin may kika tura a saka mata a window din dakin ta Nafisa tace ka dauki maganar ihisan da gaskiya ne.
Yace in ba da gaskiya bane may ya saka kika bugeta yanzu ita kuma yanyala mai ya samay ta naga taji ciwo haka a kwaurin ta.
Da sauri Yanyala ta sake dogon rigan da ta rike don zafin da wurin ke mata nikan juyawa nayi zuwa part dina ina rokon Allah tsari.
Ban san yaya suka kare ba a falon na dai ga ya shigo part din nawa ina zaune a falo bai mun magana ba ya wuce kitchen ya duduba ya fito yana tambayana banjin komai ko.
Daga inda nake zaune a harde kafa cikin kafa ina karatu nace dashi ban jin komai Allah dai ya kara tsare mu da tsarewan shi yace dani amin yana kaiwa zaune ya dafe kanshi da hannun shi daya yana tunane.
Dago kai nayi ina kallon shi naga yadda ya zurfafa a cikin tunane nace a hankali wani abin ne kuma ya faru ?
Sauke ajiyan zuciya yayi yana kallo na yaga har cikin raina ban nuna damuwan abinda ya faru din ba kuma nayi hakane don kada ya fahinci na razana da abinda ya faru din yanzu a falon.
Wa yan nan mutane Deedar zaman su a gidan nan yana takura ma rayuwana gasu basu da zuciya nayi korar su sun ki tafiya su barni.
A raina nace baka kore su ba dai kana gudun bacin ran yar uwar su ina ko zakai masu koran da zasu barka amma a fili cewa nayi dashi haba dai ai bakon ka annabin ka ba a korar mutum hakana.
Yan uwar matar kane fa in ma baka son zaman su anan ne aiba korar su haka zakayi ba sai a cikin hikima kada dai ince don dan wanan abin kake bata rai haka.
Deedar baki ganewa ne akwai abubuwa da dama da nake hango ma zaman su a gidan zai haifar zuwa gaba .
Nace da baka hango wanan ba sai yanzu ni dai kada, kasa zarge ni su ga laifina su dauka nice ke zuga ka a kansu.
Yace kin taba min maganar daya daga cikin su ne tun shigowan ki gidan nan idan kai kasan ban taba ba amma su sun san da hakane.
Yinin ranan AA yana makale dani bai fita ko ina ba kamar a kaina ya fara aure niko kunyan shi nake ji don tunawa da abubuwan da na dinga mashi a baya sai inji kunya ya kama gashi a yan kwana kin nan duk wanda yace zai rabani dashi ai ya samu mai shi.
Dan zaman weekend din nan da mukayi a tare na fahinci AA mutum ne mai saukin kai sosai ashe yana da addini sabanin yadda na dauke shi lokacin sallah nayi bai bari ya wuce mu.
Nafisa ko tun lokacin da suka gama rikici ta dauki motar ta zuwa gidan madam uwar daba mai arna ta samay ta da wasu kawayen su biyu suna hiran nasu kishiyoyin sai gata.
Yanayin ta kawai madam ta kalla ta fahinci tana cikin wani yanayi ta ta fahinci sunyo tsiyan a gidan ta tare ta da fadin yau mutumiyar da wace aka tashi kuma.
Don yanzu gidan ki ya zama gidan danja kulun fitina ne ba daga kafa zama tayi tana jan tsuki tare da fadin ba dole ba wanan matsiyaciyar yarinyar kamar mai ira,izai da ke ture min shiri na.
Au har kin manta da abinda na Mando ya fada muna ranan cewa tana da masu kariya sai munyi da gaske a kanta.
Naga alama tace wai duk kudin dana kashe akan yar iska abin bai yi ba na tura yanyala ta turara yar iska ta baya sai gashi ita ta fito ta gaba tana turarani a gidan.
Ddon iskancin yanyala kuma a gaban idon su Ihisan taje yin abu sai gata wai taji kamar tafiya a bayan ta taje waigawa ta fadi duk ta kuje kanta ta kone.
Dariya sosai suka dauka ita ko tasha toka don bata ga abin dariya ba anan taci gaba da fadiin na nuna mata na gane turaren da take yi sai gashi ya fito kamar zaki yana tambaya shi a dole mai lalashin ta kada ta gudu.
Ba sai ga ihisan ta fito tana fada ma uban abin da Yanyala taje yi ba ta fadi yau ai ba karamin rikici muka kwasa dashi ba a gidan.
Sai dana murje mai ido kada inji kunya na dinga zabga masifan karya sanan ya rabu dani ai da ban san inda rikicin zai tsaya ba.
Dayar matar dake zaune hamshakiya ne ta karbe maganan da fadin kin ga irin abinda yasa ban tura kowa yai min aiki ni nake abina da kaina ba tare dana saka wani ba yaje yai min shirmay.
Tace ai dan ba kari mutanen banza ne wallahi ace dan karamin aiki haka sai mutum yayi shirmay a cikin sa wai fa yau sai kusan goma suka fito daga kwana.
Matar guda dake ta faman kada kafan ta tana jin mulki ta amshe da fadin wuri kika basu wallahi ni akawi yar iskan kishiyar da zata kai ko biyar na safe da miji a daki.
Ai da ranan sai tasan ta shiga hurumin da ba nata ba a gidan nan sai na saba mata kamar yadda ta saba min sai dai suyi tsiyar can a sace ban gani ba.
Ke in fada maki ma fa dayar ma sai idan bani gari yake samun sakewa da ita idan ko ina nan basu isa ba wallahi har shi din.
Hankalin Nafisa ya koma wurin mai maganan taji kamar ace itace ta samu irin wanan irin mulki tace haka nake so wallahi yar uwa.
Tace a mai za a fasa mutuwa ko hisabi ni ban daukan raini ga kishiya wallahi balle su duka ukun na girmay masu ga shekaru mijin ma kanshi na girmay shi balle su.
Kina nufin dama sune a gaban ki ta tambaya cikin son karin bayani gare ta tace wlh in fada maki ina ganin shi yai min kawai na aure shi duk da shima yana da abin hannun shi do ya fini nisa ba kusa ba gaskiya.
Badai haihuwa yanzu nake nema ba sai rufin asirin don haka nake juya su yadda raina ke so a gidan ba wace ta isa ta mai tak a cikin su tayi waje road.
Don wace nake bi har ta gwada min iya shege nasa miji ya yanka mata jan kati sai gidan su sani Allah sani Annabi ta samu ta dawo cikin yayan ta.
Madam tace amma sai da kika bari kikai nazarin su kafin ki fara aiwatar da shirin ki ko tace sosai kuwa da farko ai da fuskan musulma nazo masu.
Nice son diyan su nice nuna masu ban damu da miji ba nama fisu son kan su da sauran abubuwa sai da na gama karance su tsab na fara fito masu da kalata.
Da uwargidan na fara don na jata a jikina sosai naji komai na gidan da yadda yake guda ai in fada maki akanta na fara ranan.
Ba baki don ta gama fada min duk sirin gidan na sani kuma tana jin kunyar aji a gurin ta naji komai dole sai lalabawa da biyayya gare ni.
Madam tace to abinda Nafisa bata iyawa ke nan na fada mata ta nasu ta gama fahintar ida suka dosa amma ta kasa hakan don kishi.
Ai in kina son ki san kan gida kafin ki fara aiki fara kama kan uwar gida je mata da fuskan musulma ki nuna kina ra,ayin ta kina tausayin ta yanzu zaki fahinci komai a wurin ta.
Don su gani suke cutar su miji ke yi ko yaushe yafi maida hankali ga amare basu san duk kanwar jace ba kishiya kishiya ce ba mai son taga yar uwa tafita ga miji.
Kai Nafisa ta gyada tare da fadin ni gaskiya ba zan iya jan kowa a jiki na ba duk daya na dauke su ai kafin in zauna da amaryan da uwargidan muka fara.
Wanan fa irin kishin kasar su tazo muna dashi nan bata san abin ba haka yake ba a nan sai ka hada da kissa da kisisina da kutungwila zaka ci riba.
Nafisa tace gaba daya nike masu bugun diyan kadanya don ban yarda da kowan su ba ni mijin nake son in kama ko ta halin kaka abin ya faskara gare ni kuma.
Sai naga kamar zan kama shi sai abu yazo ya jagwule min daga baya yanzu fa yan kwanakin nan samad bai jin kunyar fadin mu bar mashi gida dani da yan uwana.
Matar tace duk ke kikaja hakan tunda ya riga da ya fahince ki baki kaunar ko daya daga cikin su don may zai zauna zaman goyon bayan ki koda yaushe.
Bafa ko yaushe asiri ke tasirin akan mutum ba madam ta karbe da fadin shi nake fada mata ai bata gane ba.
Matar tace kamar ni nan ai da farko wani na samu na kamashi a hannu wani last done ne wallahi har ina ganin na kama shi ashe matar shi ta fini iya duniya.
In fada maki tana ji ba ai sati ba ta shiga ta fita sai batun kake ji yar iska ta kama abinta tamau ta rike ai ke madam kin san labarin don da ke mukai ta bugawa a lokacin.
Madam tace kwarai kuwa na sani Hauwa black yar jos ko kin san har yau kuwa a kule take damu ranan mun hadu a gidan buki baki ga yadda take wasa da naira ba tana muna hura kai.
Ba dole ba yar iskan mata miji ya rike mata kan maciji tana wasa da bindin shi duk tarin dukiyan shi fa ita kadai ce matar shi har yanzu gashi matashi mai ji da lokaci.
Kedai bari yar uwa yanzun ai ba a sanya don wace za ka sama sheri ke da zaki shigo kuma da naki shitin ba, a shiga hannu sake yanzu kowa tsaye yake kamar laya.
Tambayan Nafisa tayi may ye matsalan ta yanzu akan kishiyar tane sai da ta rufe ido ta bude kai tsaye tace wallahi hajiya ni gaba daya naki jin kishine a rayuwa.
Don na kasa tsayawa in fahinci takon yar iska ai in san ta inda zan fito mata don yarinyar gata karamace amma akwai bakin wayo gare ta.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Washe gari bai so in shiga school ba wai sai na karkare murmurewa in fara zuwa rokon shi nayi ya bari in shiga don muna da test washegari tuesday.
Bamu hadu da maryam ba sai da muka fito sallah a zahar muka hade a masallaci da ita kallona kawai tayi ta kwashe da dariya.
Oh kinga abin dariys a jikina ke nan na fada a hasale tace ban gani ba sai dai kina dashi ne khadi daga dan haduwa guda shine har kika wani fada haka.
Kallon jikina nayi na tabe baki nace dama haka kike son gani aka hada baki dake ai wlh ki san da sani konci bashin haka a gurina sai na rama nima.
Yarinya ai sai dai ki ramay wurin ramawa nikan ai ba zanyi wanan rakin irin naki ba kin sani mun dauki lokaci a gurin kafin mu koma ciki.
Biyar da rabi muna fitowa motar shi na iso wa don haka ban samu kara kebewa da maryam din ba na wuce .
Tunda na shiga motar naga shi rai bace ban damu in tambaye shi ba don ba abinda ya shafi gida bane kila.
Mun dan taba tafiya kadan ne naji muryan shi yana tambaya maganan da ya daure min kai dagowa nayi ina kallon fuskan shi ya kara maimaita tambayan shi gare ni.
Nace ina kika je a Napep ke da maryam da bana gari shuru na dan karayi sai kuma nace ban je ko ina ba sai wurin gyaran kai dakuma shago na sawo kayan bukatana don banda mai sawo min.
Khadija kin ko san darajan ki a yanzu garin nan da zaki je shiga Napep da mutuncin ki da kimar ki na matar aure matar ma tawa .
Wai kin san wanda kike aure kuwa khadija idan ma baki sani ba bari yau in fada maki ni ko waye don ki sani.
Wanan aikin da kikaga ina yin shi nake don cika gurin iyayyena a yadda suke so suka kuma gina ni akai ina kokarin ganin akoda yaushe na farantawa iyayyena ransu.
Idan ba haka ba ba abinda zanyi da wanan aikin da kike gani inayi anan kin san wasan polo ko wasan kwalon doki da akeyi .
Kai na gyada alaman na sani yace to ina daga cikin wanda duniya ke alfahari dashi a wanan wasan kin san jackpot na girgiza mai kai yayi dan murmushi yace ki bincika don yafi komai kawowa rayuwana kudi sai dai banson yi idan ba yama min dole ba wanda idan na buga kusan duk abokan karawan nawa sai na doke su.
Ni business man ne ina shigo da karafuna da part na motoci a kasan nan sai dai duk inayin wanan ne a cikin boyen kurwa don idon jamma,a akaina.
Don Allah don Annabi for god sake mai zai sa kije shiga motar haya bayan na aje maki daya daga cikkin motocin shiga na a dinga kai ki duk inda kike so.
Ba wai naki saya maki mota bane tun kafin muyi aure ko mota nawa kike so a gare ni zan iya saya maki Deedar sai dai ina duban abinda haka zai jawo maki ne a gida da idon jamma,a.
Ranan da Nafisa tayi maki gori naji zafin abin don har barci abin ya hana ni samu issashe saboda raina da ya baci da zancen.
Don Allah may yasa kikayi min haka har yaron wajen aikin mu dashi da matar shi suka rage maku hanya yau yake fada min banji dadin jin haka ba wallahi.
Gyalen kaina na gyara tare da gyara zamana ina fadin ni kada kaga laifina akan hakan fa.
Yace a harzuke don may ba zanga laifin ki ba Deedar sunana kike son batawa a bugani a jarida anga matana a motar haya a garin nan.
Ko Fati da take cen duk inda zata da motar hajiyan mu take tafita na kuma kyaleta ne ban sai mata wani ba saboda careless din ta dayai yawa.
Don Allah ka daina zargi kan haka don ko ba laifina ba ka tambayi driver ka ko maryam zasu fada ma idan nice mai matsalan.
Motar da tun ranan da ka tafi iyakar mu da ita kenan a gidan ka ban kara ganin driver ba sai yau da muka fito din nan naganshi a waje yana noke kai.
A dai yi min munafunci ne don ba,a son aga kwanciyar hankalin mu tare da kai shiyasa ban bi ta kan motar ba na ci gaba da tsagogina.
Da ina da power a gidan ka ba za a hanani shiga motar ka ko taba kayan ka ba a gidan nan.
Shiru yayi yana saurarena har na gama san nan yace kina nufin hana mashi umurnin da na bashi akayi komay nace ai ka tambaye shi kaji daga bakin shi ko kuma idan baka yarda ba zaka iya tambayar maryam yanzu ma ba sai gobe ba.
Shiru yayi bai sake magana ba har muka isa gidan ban tsaya ba na kwashi takarduna zuwa ciki na barshi a motar ya biyo ni da kallo.
Part dina na bude na shiga har kullun baki na dauke da addua don nema tsari ga Allah har nayi sallah la,asar na idar part din shi na je na gyara na saka kamshi ko ina tare da wanke unders din shi na shanya mai ta bayan benen shi na fito zuwa nawa dakin na dora girkin abinda zamu ci da dare.
Ban sa lallai dole zaici abincin ba sai dai na girka dashine kawai don nice mai alhakin bashi abinci a ranan duk da ba wani girki mai yawa nakeyi ba.
Na gama na shiga wanka lokacin har magarina ya dan gwauta na fito na tayar da sallah bayan na gama ne na zauna na gyara jikina tare da hayewa saman gadona na kwanta.
Tara saura ya shigo part din nawa daga shi sai wandon crazy fari da farar riga armless ajikin shi sai kamshi yake zubawa haka yasa na fahinci yayi wanka ko a lokacin.
Ban daga daga inda nake ba ina kwance a yadda nake sallama ma dayayi ciki ciki na karba mashi ya iso bakin gadon ya zauna yana fuskanta na tare da cire min handout din da nike karantawa da na dora saman cikina ya dan duba.
Ba tare da ya kalle ni ba idon shi na kan takarda naji yace dani wai fushi kike dani akan maganar da nayi maki dazun ko may ?
Na dan juyo tare da fadin wa ni don may zanyi fushi tunda ina da gaskiya na akan may zan dauki zafi dakai kuma hutawa dai nake kawai.
Murmushi naji yayi tare da fadin ba gaskiya bane idan da baki fushi may ya hanaki zuwa wurina ki dubani ko ki kawo min abincina a can ko baki girka abincin bane ?.
Na girka mana nace dashi tare da kokarin mikewa zaune sai naji ya mayar dani a yadda nake kwance da ya shigo.
Ido na kafa mai shima haka sai nayi saurin jaye nawa idon daga nasa ina sauraren shi inji abinda zai fadi fuskan shi ya sauko zuwa kasa yana nufan nawa dashi.
Kokarin kawar da kaina nayi gefe sai dai ya riga kai fuskan shi din a nawa yana neman bakina ya hade da nasa ban samu kaucewa ba har ya kawo bakin sa a gare ni ya shiga tsotse ni tun ban biye mai har na fara biye mashi na fara mayar mashi da martanin abinda yake min din.
Mun dauki lokaci a hakan kafin ya sake ni ya mirgina gefena yana sauke numfashi a hankali dan gyarawa nayi tare da kokarin tashi saman gadon naji ya rike min hannu na.
Dole na juyo ina dan kallon shi kafin yace ina kuma zaki yanzu nace abinci zanje na hada maka kafin ka fito ko a nan zakaci yace dani duk inda kika bani a shirye nake inci banda matsala ga hakan.
Mikewa nayi zuwa hada mashi abincin a nan falona muka zauna mukaci tare dashi ina jiran ya kara min maganan shiga motar sai naga ya sake yana ta wayan shi ina zaune gefe ina kallon shi har lokacin da ya gama ya mike yana fadin bari in dan leka dakina sai kin shigo.
Don Allah dai ka barni in kwana a dakina mana tunda ka jagule ni ya juyo yana fadin wayo kima zaki min Deedar shiyasa kika taimaka min.
Nace na taimaka ka da may kadai jagule ni kaimin wayon manya kuma kace sai nazo dakin ka may nayi maki ai hakkurine wanan na soma baki don naga kina son fushi dani.
Sai da na karasa hada komai na bar dakin nawa na kashe wuta na fito tare da rufe part din na nufi wurin shi.
Koda na shiga dakin yana zaune a bakin gadon shi ya tasa laptop din shi a gaba yana aiki a cikin sa jin sallamana ne ya dan dago yana amsa min.
Dan zama nayi a gefen shi shiru banyi magana na sai ji nayi yace ina son shiga kaduna wanan satin in Allah ya kaimu.
Da sauri na nuna mashi farin cikina nace Allah sarki ashe anty Fati na da bako ranan don Allah idan an masu AFFAN hutu azo min dasu.
Yace idan nazo dasu ni yaya zakiyi dani ina cin amarci na juyawa nayi na kyaleshi ba tare da nayi magana ba kuma.
Dan dariya yayi yace don nace ina cin amarcina laifine kuma nace wanan ne cin amarcin gida tab da yan sa ido.
Dariya ya soma min tare da fadin nafa lura wanan amaryan tawa wurine bata samu ba da amarcin yafi nan da zan samu ashe.
Yana fadin haka tare da rufe system din nashi ya hawo gadon tare da runguma na zuwa jikin shi ranan kan bai sarara min ba sai da ya debi rabon shi a jikina son ranshi.
Duk da ba wani gudun mawa na taimakamashi dashi ba amma hakan bai hana shi yai min sheri ba nikan wai yaya zanyi da wanan mutumin ne wai.
Ashe shi yana min hakane don tsokana yaji tsiwa na sai dai bai sani ba yanzu baki ya mutu kunyan shi da nauyin shi nake ji yanzu sosai.
Ana gobe zai wuce ne na tura maryam kasu don ban iya zuwa ta sawo min tsaraban da zai kai min kaduna din.
Banyi tunanen komai ba na shirya tsaraban kamar yadda nake bukatan su jira nake ya shigo in fada mai wayana yai kara shine a layin ya kirani falo.
Da mamaki na tashi ban fita sai da na tsaya gaban mirrow na kalli fuskana tare da fesa kamshi a jiki na fito shar dani.
Sai dai may ina fito na samay shi zaune a falon ga Nafisa a gefen shi tana kada kafa daya saman daya ta mike kafafuwan ta kofana dukkan su suka zura ma ido su ga fitowana.
Tunda na tun karo falon na samay su a haka nima na gyara fuska na nadaure shi da kyau nazo da sallama na, shiya dago yana amsa min tare da nuna min kujera da in zauna.
Da bissimillah na kai zaune ina mai sauraren su sai can naji ya ce kowan ku nan ina son ku bani hankalinku ku saurare ni .
Ai kai muke sauraro tace cikin kada kafan da takeyi har lokacin ta yace ina son ku sani kowa a nan auro ta nayi don mu zauna tare mu raya sunna ma,aiki SAW nidai kai kawai na iya gyadawa sai faman tunane nake mai ya kawo wanan maganan haka.
Wani hararan shi takeyi da yake wanan maganan batare da itama tayi magana ba yace Nafisa kin san dai Na sai maki motar ki akan wanan auren na Deedar kika ce baki son wanda na saya maki din kika dauki daya daga cikin wanda nake shiga ban kuma hanaki ko yi maki magana a kan hakan.
Yanzu may ya kawo wanan maganan agaban wace ba ayi da ita ba tun farko yace maganan ya shafe ta ne dole ayi shi da ita tunda haka kike so.
Yace kin san da haka ko baki sani ba tace na sani mana kuma wanan ra,ayinane haka shi nake so shiyasa na dauke ta yace good.
To akan may ita zanyi tafiya nace malam musa driver ya dinga kaita makaranta kika hana shi alhalin kin san itama din mata ta tace tana da ikon yin yadda kikayi a gidan nan.
Ta kalle shi tace eh ni na hanashi din ya kai ta don ban san da wanan maganan ba saboda baka fada min komai akan haka ba.
Kaga ke nan ina da ikon da zan hana wani yin abuda kayan ka a gidan don nice za ka tambaya akan haka idan wani abu ya faru.
Yace malam musa bai fada maki nine na saka shi yin hakan bane da kikai mashi warning akan dauka Deedar a motana.
Ina son ji idan bake bace sai in kira shi yanzu gashi nan a bakin kofa yazo ya fada muna nashi dalilin da zan sa shi abu yakiyi ko yau yabar min gidana da aikina don ba zan dauki wulkanci akan iyali na ba ga kowa.
Samad na fada maka nice na hana a fita da motar nan akan na hana matar ka shiga mota ne wai ka zaunar dani anan ina wani magana ne can na daban.
Yace wanan din naki dauke shi wani magana ba ke nan idan anyi maki hakan zakiji dadi a ranki ki fada min eh ko a, a ya tambaye ta.
Mikewa tayi tana fadin akan matar ka ta fada ma na hana ta fita a mota shine ka zaunar dani nan taga ka wullakanta ni ko may.
Yace baki son gaskiya ke dama do baki san shi ba to bari kuji dukkan ku abina abina nane idan ban ma kowa shamaki da abina daga yau kada wata ta kara yiwa yar uwar ta shamaki dashi.
Dama ai arzikin ta biyo taci ba kuma zataci komai ba daga gare ka sai dan karen wahala kafin ta kara gaba munafuka har kin iya shigewa daki da miji kiyi gulman wani dashi jin dasin may kika samu a gurin shi.
Zagin ne naji yai min yawa har na kasa daure don karshe cewa tayi dole in fita in bar mata gidanta in koma wurin matsayitan iyayyena makwadaita.
Dani dake waya fi tsiya Nafisa ai yanzu ba sai an bincika wanda yafi wani talauci ba anan don ke mai arzikin ne da baki fada ba wallahi.
Ko mutum ya shigo gidan ba sai ya tambaya don ku yunwa ya koro dake da yan uwan ki kuka samu wurin lebewa ki bari kiyi prouding da abinda kika ne ma da kan ki ba abin miji na kowa ba.
Sannan da kike fadi sai na bar gidan nan ki tuna ke ba Allah bace ba kuma kowa kike ba da kin isa ko shigowa ma gidan banyi balle in zauna kina gani na kuma baki da abinda zaki min.
In har kin ga na bar gidan nan sai dai gawa na wallahi amma badon ke da sherin ki ba don kunyi min kadan dake da duk da abinda kike takama a gidan.
Karya kike kema kin san nafi karfiki wallahi don banga abinda zan tsaya ma fada ba nan nace balle ni da banga abinda zan ma kishi ba nan iliterat din banza dake sai shegen bakin karya da cika baki.
Gani fitan naso yai yawa ne yasa shi dakatar damu da tsaya tare da fadin ya isa hakana ban kira ku nan ba don kuyi min fitina na kiraku ne don in ja maku kunne.
Bayan haka zanyi tafiya gobe zuwa gida ban son in dawo in samu kunyi wani fitina a tsakanin idan haka ya faru nayi bincike ko wacece mai laifi zan hukunta ta wallahi.
Ya sa hannu a aljihun shi yana ciro kudi ya aza a saman table din gaban shi ya juya gurin ta yana fadin dauki gudu wani kallo tayi mashi tare da watsa ma kudin harara tana fadin kudin ma da zaka ban sai a gabants zaka bani kuma daidai da nata ko may yace.
Eh nayi hakane don fita daga zargin ku na mata ya kirgo wani yana mika mata tare da fadin wanan dubu goma ne kiyi wa ihisan lalura dashi kafin in dawo .
Yana fadin haka ya mike ya fara tafiya ya juyo yana fadin shike nan kuna iya tafiya bangane muna iya tafiya ba sauran jamma,a yaya kake son inyi dasu wanan matsalan ki ne yace yana tafiya cikin daga murya bayan na kwashi kudin na mike nake fadin mungode Allah umfana arziki.
Nan na barta tana ta masifa wai bai mata kara ba yarsa kawai ya sani ita dayan fa afa yai mata sai yanzu ne da aka hure mashi kunne zaice bai ma sauran lalura sai ita tayi masu ko may ?
Ni kan sai a lokacin ma nake sanin dayar yarinyar mai tsiwan ba diyar shi bace dama abin na daure min kai ina mamakin lokacin da suka haifi yar da ta kai haka girma.
Nafisa ji take kamar ta mayar mai da kudin shi gashi kuma tana bukatan kudi a hannun ta da zaitai sabon lalura ita tai girki ranan don haka sai da ta saka shi daki ta lalashe shi ya kara masu wani abu.
Washe gari tun da safe suka bar garin zuwa kd don yana son zuwa kano ya dawo kaduna a ranan shine dalilin yin sammakon su.
Wanan karon ni kadai ce a gidan tunda na dawo school ban fita koda falo ba ina part dina yau kallo na kunna ina yi tunda ba wani girki zanyi ba ranan.
Idan bai part dina bana wahal da kaina gurin girki sai dai in samu dan snack inci in kwanta jin anturo kofan dakin na kalli kofa ihisan ce ta shigo da kanta boya an tsefe ba kitso ta shigo wurina.
Nace a, a Ihisan ke ce tazo har gurina da surutun ta irin na yara fadi wanan fadi wofi muna hira yarinyar na dan debe min kewa har tayi barci a dakin kwane a jikina.
A hankali nayi dabaran kama kanta ina mata kitso kalaba nayi mata manya irin na yara don bata kwaso uwarta ba ubanta ta fi daukowa sosai ha halitta.
Kalaban yai mata kyau na mike na dauko man kitso a dakina da yan ribos na kama mata kan har lokacin bata falka daga barcin da takeyi ba.
Ashe suna can suna neman yarinyar a falo dakuna har wajen gidan basu ganta ba hankalin su ya tashi sosai har suka buga ma uwar waye ta baro inda take zuwa gida hankali tashe.
Tun a hanya ta kira AA tana fada mashi batan yarinyar shima hankalin shi ya tashi sosai sai fama buge bugen waya yake a duba yarinyar wurare da dama.
Yusuf da yaga yadda duk ya firgice gashi suna garin kano yamma yai masu basu gama abinda ya kaisu garin ba shima ya shiga damuwar batan yarinyar sosai.
Yusuf din ne yace khadija ko tasan abinda ake ciki a gidan naji bata bugo maka waya ba sai lokacin ya tuna ya kira layina.
Hankali a tashe yana fadin kina ina nace gida yace bakiji ihisan ta bace ba ne baki bugo min ba nace kamar yaya ta bace ga ihisan a gurina tayi barci tun Four muke dakin nan da ita fa.
Ajiyan zuciya naji ya sauke ya ja tsuki yana fadin kaji fa ashe tana part din Deedar tana barci tun karfe hudu mahaukatan baza basu duba ba sunce sun duba ko ina a gidan kuma.
Kiran uwar yayi yana fada mata yarinyar na nan gurina tana barci suje su dauke ta tace may uban wa yace ta daukar min yarinya.
Idan tai mata wani sheri fa wani irin magana kike fada Nafisa sherin may zatai mata kuma Deedar fa nace maki ta gidana.
Tsuki taja ta kashe wayan tana isa gidan part dina tayo direct ba sallama ta banko kofan dakin idon ta akan yarinyar dake barci saman kujera.
Direct wurin yarinyar ta nufa ta dago ta tare da fadin uban wa yace ki dauko min diya wani sheri kika kawo tanan ki na mata yar bakin ciki, yar nawa guda daya da Allah ya bani itama neman ta kike da sheri ko may.
Idan haihuwa banza ne ki haifi naki mana ki dinga kallo idan kina son yara a dakin ki daga yau kada ki sake taba min yarinya a gidan idan ba haka ba ranki zai baci kin aza haka ake samun haihuwa a ruwa ko may ke da haihuwa ai sai daki kalla in kin ce naci kika iya.
Ban iya mata magana ba sai kallon ta da nakeyi ina mamakin wanan haukan nata ta dauko yarinyar da karfi tana dube dube a jikin kamar may neman wani abu.
Har takai kofa fita da yarinyar a sabale saman kafadan ta ta juyo tana fadin kuma bari kiji idan wani abu ya samu ya ta nan da sati daya wallahi sai mun shiga kotu dake.
Baki da hankali nace mata kina tunanen kowa ma irin ki ne muguwa ke kika san wanan zancen ni ban san shi yar ki ta kawo kanta inda nake bani na dauko taba kuma ko gobe tazo wuri na bazan koreta ba don ni ba mahaukaciya bace irin ki.
Kije ki mutu ranan don tazo wurin makiyiyar ki, don Allah fice min da haukan ki na banza mara dalili ki sa ido ki gani idan na shiga harkan yar ki in dai ba ita tazo inda nake .
Tace zaki gane baki da wayo duk ranan da wani abu ya samu ya ta, wama ya sani ko saceta kikai niyar ki yi Allah ya tona maki asiri kika fito da ita.
Har ta fita mamakin kishi irin na Nafisa mai kama da kishin hauka nakeyi yanzu may na yarinya a cikin kishin mu bafa ni na dauko ta itace ta kawo kanta inda nake.
Idona na lumshe maganganun ta suna min zafi a rai na nace ya Allah kana gani kuma kana jin Allah kai min mafita akan wanan aure.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Bayan sun dawo daga kano Yusuf ne dauke da kaya niki niki zai shiga gida dashi ya bishi da kallo tare da fadin wanan kaysn kuma haka daga ina suke.
Yusuf din yace dashi sako ne aka bani inzo ma mutanen gidan dashi bishin ya sake yi da kallo yana mamakin ida kayan suka fito sai dai bayi magana ba suka shiga.
Bayan sun gaisa da Fati ne Yusuf din ya mika mata leda tare da fadin wanan khadijja ce tace azo ma su AFFAN dashi wai akwai wani leda a ciki naki ne tanaa gaida ku.
Dagaa inda take zaune ta tace tauuu, ta mika hannu ta karbi kayan tare an gode kallon mamaki ne a fuskan AA ddin karara sai kuma baiyi magana ba ya basar.
Ba wani sako bane a ciki sai takalman makaranta da school baga har da littafai da warmers na makarantan yara masu kyau.
Tun a gaban su ta bude kayan tana kallo murmushin da ta sake a fuuskan tane ya bashi mamaki tace to ashe monday akwai rigima wurin babana sai nayi wa kayan sheda.
Taci gaba da bude dayan ledan turararuka ne a cikin na jiki humra dana daki masu kamashi sosai don ana bude su falon ya dauki kamshi.
Allah yasa ai amfani dashi AA ya fada yana mai tabe baki tare da komawa saman kujera yayi balancen da kyau.
Malam bafa kai ka sayo su ba balle kace wani abu yar kanwar tace ta aiko mata da tsara ta shafa.
Rai fati ta hade da sauri saboda akwai ta da saurin yin fushi da mutum, don haka yana fadin wanan magana ta fuske, dashi ba tare da tayi magana ba.
Yaran ne suka dawo daga gidan mahaifan shi suna ganin shi suka dan zabura don jin dadin gani shi komay suka tuna kuma sai suka ja suka tsaya suna fadin sannu da zuwa Abba.
Kamar yadda ya saba yi da yaran cikin rashin sakewa ya amsa masu Yusuf ne yace a,a Affan an dawo ke nan sai suka nufi wurin shi idon su yana kan school bag din da suka gani a gaban uwar su.
Karamin ne ya rarafa wurin uwar yana tambayan ta cikin kashe murya yana fadin mama Abba ne ya sayo muna ?
Cikin muryan ta a yadda take magana kamar an sata yi dole tace wa yaron Anty ku ce ta sayo maku har da takalma da cooler.
Dayan yaron ma yaje gurin yana tambayan ta mama wace antyn mu ta sayo muna ?
Yusuf ya ce da yaran mommy ku amaryan Abban ku da tazo wancan karon tace a kawo maku murna yaran suka shiga yi tare da fadin mama itace tace zamu hutu Abuja ko ?
Wani tsawa ta daka ma yaron sai da ya gigice tace kai rabani da maganan banza don Allah, ku magana baya isan ku .
Kallon ta mijin yayi yaga yadda ta hade fuska ya fahinci fushin maganan dayayi take yi har wanan karon zata sauke ga yaran .
Kallon yaran yayi shima cikin daure fuska tare da fadin kai ku kwashi kaya ku ku shige ciki ban son yawan surutu fon Allah.
Yaran suka shige gwanin ban tausayi tare da daukan kayan su ita bata dauki lokaci ba ta mike ta mara ma yaran baya.
Nuna ta yayi ga Yusuf yana fadin duba don Allah mutum ya zo daga tafiya ko ruwa ba zata iya bashi ba wai matar mutunce haka tun tasowan mu da safe fa na buga mata waya amma bai sa mu samu taro a wurin ta ba.
Yusuf gajeren murmushi kawai yayi tare da fadin ina ruwan fati ita dai bata taba canzawa haka rayuwan ta yake sai hakuri kawai irin haka.
Kai AA ya girgiza tare da fadin rashin sanin ciwon kaine yanzu ita deedar baga ta can tana hakkuri da halin Nafisa ba tasan komai fa amma bata taba nuna min hakan ko anyi mata sai dain in suyi a gaban idona.
Bata fita kurciya ne sa ba kusa ba Yusuf yace ai ba zaka hafa Fati da khadija ba don yanayin su ba daya bane matsalan ita Fati akwai saurin fushi da kowa kuma bata da sakewa.
Ya karbe Yusuf din da fadin nakasa ne kawai da wulkanci ita ds kowa haka take kamar mai jin warin mutane.
Na fadi shafa turaren zatayi ko ajewa yara su bata wani itin turare ne ban sayo mata da haka zata barshi batai amfani dashi ba yara su zubar ko wani yazo ya dauka.
Ya kare maganan shi cikin jan tsaki yana kiran Affan daga inda yake zaune sai ga yaro yazo da gudun shi yace kace ma laraba ta kawo muna abinci.
Yaron ya kalli uban yace Abba laraba tayi tafiya bata nan da dadewa in fada ma mama ne yace barshi ya mike ya samay ta a daki yace da ita.
Tana kwance baki sa muna abinci bane tace nasa amma ni tunda rana nayi kuma banji kace a kawo maku ba juyawa yayi inda ya fito ya samu Yusuf zaune yana waya.
Ba sai ya tambaya ba yasan bai wuce da zainab yake wayan kallon shi yayi tare da fadin muje gurin hajiyan mu muci abinci don Allah.
Katse wayan Yusuf yayi yana fadin bata girkaz bane ko may yace muje don Allah don yunwa na soma ji rabona da abinci kasan tun safe.
Suna zaune a falon mahaifiyar shi wance ta gama fada da halin Fati din suna cin abinci wayan shi yai kara ya dauka yana dibawa.
Nombana ya gani yayi received din call din tare da fadin slm nace wlsm an wuni lafiya ya hanya ya amsa da fadin Alhamdullahi nace ya su mama da sauran mutanen gidan an samay su lafiya ko?
Lfy ya amsa dashi nace agaida min da su ya su Affan da baba yadda naji suna kiran yaron dashi yace duk suna lfy a huta gajiya a gayar min da anty Fati don Allah, dama na kira inji lafiyan su ne in maka sai da safe yace ya gode ya kashe wayan shi.
Yana aje wayan hajiyan su tana fadin wacece yace khadija ce wai tana gaida ku dan murmusawa tayi tana mai jin dadi har cikin ranta.
KHADIJA
Muna gama wayan dashi na gyara kwanciya dama a kwancen nake don har na kashe wuta ko tun karfe shida da rabi na rufe kofan part dina.
Fruit kawai nasha sai naji na koshi a lokacin sallah nayi na watsa ma jikina ruwa, na haye gadona shine na kirashi.
Tofe jikina nayi da adduan neman tsari a wurin Allah na gama na tofa a hannu na tare da shafe hannaye ga jikina na gyara kwanciya na.
Allah yasa washe gari ban shiga school haka yasa na sha barci na da safe ban ko tashi na nema ma cikina abinda zanci ba.
Sai da yunwa ya damay ni cikin barcin nawa na mike na shiga bathroom nayi brush tare da kewayawa na fito na fada kitchen.
Simple abinci na hada na fito falo dashi na zauna ina ci na bar wayana a kuryan daki ashe yai min har three miscall ina falon ban sani ba.
Sai dana gama na shigo inyi wankane naga kiran nashi diban lokaci nayi naga rana yayi tunane nayi yana ganawa da iyayyen shi a daidai wanan lokacin.
NAFISA
Tana zaune falo gidan tare da yan uwanta fada take masu akan sunki kokarin su kama wani namiji daga irin mazajen birnin nan da suke zuwa wurin AA itama ta samu ta huta da nauyin su haka.
Tunda yanzu duk maganar samad daya biyu zaice ta kwashe yan uwan ta tabar mashi gidan shi tunda bata son a zauna lafiya.
Duk wanda ya ganta zaune a falon yasan Nafisa na cikin wani yanayi dan kwanakin nan.
Kalo daya zakai mata ka hango matsala a tattare da ita wai a cikin ma tana karfin hali ke nan tunda tana samun yadda take so a gidan har yanzu.
Sai dai matsalan ta daya ne shi kuma abinda ke bata mamaki da haushi da takaici mamakin ta da haushinta ta ko shi wai ashe dama zata iya zama da kishiya a gidan nan kwana da kwanaki.
Bata taba zaton ko yar yaren su na buzaye ta shigo gidan ta zata dauki kwanaki a tare da mijin ta ba.
Yau sai gashi yar nigeria ce ta shigo mata gida duk kudin da ta kashe da irin maganin da take banka ma Samad bai hana wanan shegiyar yarinyan ta zauna mata da miji har su kwana a gado daya dashi ba.
Wani irin yawun takaici ta hade a mokoshin ta tare da fadin a fili lalai ya kamata in nuna ma wanan yarinyar ni bata wasa bace.
Idan tsubu ta iya ko tsafi zata nuna mata karya suka iya don bata kaita iyawa ba ita bata taba daukan akwai wata macen kasar nan da zata iya ja da ita ba a zauna lafiya.
Wanan tunane da take yi ne yasa ta rashin jin karan da wayan ta keyi kiran mijinta na shigo mata a lokacin.
Wanan tunanen dashi take kwana dashi take tashi don bata kaunar ta bude ido taga har yanzu yarinyar nan ta saura a gidan ta.
Ta sha alwashin ko ta halin kaka sai taga bayan khadija a gidan nan kuma ta kama mijin a tafin hannun ta idan ta gama da khadija din.
Daga kai tayi tana kallon kofan shiga part dina taji kamar ni take kallo ta watsa ma kofan nawa harara aiko yayi daidai da fitowana daga part dina.
Zan tafi wurin gyaran kai da sauran part din jikina don kusan wata ban gyara jikina ba kaina ya fara min kyakayi don har na sance kitson a haka nake daure shi yanzu da ribon ni kuma ba gwanar barin kai ba kitso bane tare dani.
Sannu fa nace da ita ban sani ba ko ta karba min sannun da nayi mata din nidai na fice ba tare dana kara kallon inda nake ba.
Ita a ganin ta rangwada nakeyi mata bata san haka halittan diya matan yake da rausaya ba ko a banza.
Na dauki lokaci ban dawo ba don na dan biya nayi sayayyan kayan amfani wanda na sawo pad saboda expecting din period dina da nakeyi a cikin satin.
Ko da na dawo gida yamma yayi sosai ban wahal da kaina ba wanka nayi nai sallah na nemi wuri na kwanta .
Waya na dinga yi da yan gidan mu munfi dadewa da ya Amina a wayan muna hira akan yaran ta don akwai ni da son yara sosai a rayuwana.
Har barci ya dauke ni gari ya waye nasan maigidan zai dawo ranan kuma nice zan karbi girki don haka na shiga kitchem tun karfe hudu na fara hada mashi girkin da zaici.
Dakin shi na shiga na gyara komai na fito bandade da fitowa ba Nafisa ta shigo gidan daga unguwa.
Na fito falon gidan ma na bada umurnin a gyara na koma na kammala girkina shida saura suka iso gidan.
Banji dawowan shi ba sai da Yusuf yazo part dina kawo min sakon mommy nasan sun dawo bayan Yusuf ya fita wurina ne na nufi part din shi.
Na samu ya fito daga ban daki yana ganina I a dan sake murmushi yana gyara hannun rigar dake jikin shi haka yasa na fahunci alwala yayi a lokacin.
Gaida shi nayi ban tsaya ba na koma part dina don bin ka,ida sunna don lokacin shiga girki na baiyi ba a lokacin sai bakwai na marance zan shiga lokacina.
Sai bayan sallah isha,i na gama shiryawa kwalliya na zauna na tsara ma fuskana atamfan super na sa wanda maryam ta karbo min su daga wurin dinki kayan sun matukar karbuwan jikina don sun fitar min da surana sosai na jikina
Kallon kaina nayi a mirrow na naga yadda komai nawa ya zauna cas na kara feshe jikina dakyau da kayan kamshi.
Na dauki basket din tare da kulle part dina zuwa wurin shi dauke da basket din dana shirya abincin shi a ciki .
Falon sama din na tsaya sai da na shirya abincin komai na aje inda ya kamata daga baya na naji an rungumo ni.
Dan firgita nayi tare da juyowa ina kallon shi kaina na dan langabar da kaina tare da fadin wallahi kaban tsoro yace Allah ko sake ni yayi bayan ya murza min hannu yace mai aka girka min cikin sakewa da jin dadin ganin haka yake magana.
Abinda na fahinci kafi so ne na girka maka ko zakaci ban sani ba ya fara bude warmer din ke nan sai ga Nafisa a gaban mu tana fadin.
Samad ya naga haka ke may kikeyi anan ta juyo gare ni tans tambaya na tana aje kulan dafa dukan da ta shigo mai dashi da plate.
Ta fara fadin wai may kuke nufi ne a gidan nan ya karba da fadin kamar na may fa?
May ya kawo wanan wurin nan yanzu may tazo nema a wurin ka ko iskancin nata da samun wuri har yakai haka ban sani ba.
Ke ban fahinci maganar ki ba fa Nafisa ki fito fili ki min magana yadda zan fahince ki kin tsaya kina wani sharfi haka.
Tace amma kasan a ka,ida nice da girki yau don ko yau ka dawo daga tafiyar da kayi kaga ke nan nice zan karbe ka yau.
Yace wani makamin ne ya koyar dake hakan ina ranan jumma,a nabar garin nan da safe da yamman ranan ya kamata Deedar tayi giri bana gari .
Washegarin asabar sai wa zaiyi tace ita yace idan gari ya waye fa tace ita ya kamata tayi yace kin ba kanki amsa yanzu.
Tace wallahi baka isa nice ya kamata nayi tunda daga tafiya ka dawo yaudin don haka a wurina zaka sauka ke nan.
Wai hauka kike yi ne Nafisa ko mai tace kaidai ke haukan don gashi kuna son ku dulmiye ni akan hakkina.
Tsaye nake gefen su mamaki ya hanani yin magana don naga haukar kishi a filin Allah yau sai kallon su nake ina sauraren su.
Ke wace irin dakikiyace wai amfada maki ana haka ne idan kinga anyi hakan tafiyace ya kama mutum da zai share lokaci bakuma ance lalai dole mutum sai ya sauka dakin babba ko karami ba.
Zaka iya sauka a ida zuciyar ka ke so ko wancen karon na sauka wurin ki ne badon komai ba sai don a zauna lafiya badon wani abu.
Don may ita zata fahince ni ke ba zaki tsaya ki natsu ki gane mai addini ke nufi da hakan ba sai shirmay ban za.
Tace yanzun kana nufi a wurinta ke nan zaka sauka ko may yace ba itace dani ba yau don may ko ba zan sauka wurin ta ba.
Samad amma kai macucine ashe har zaka iya rufe ido akan wanan mai ruwan fulanin ka tozartani a gaban ta.
Uban may zata tsinana maka a dakin banda kwaciya tana shafa ma janbaki tana bata gado da katifa.
Bayan wanan akwai wani abinda zai shiga tsakanin ku ne da ita bayan na gane hakkuri kake da ita tunda aka kawo ta.
Yace yaya kikayi kiks san hakan ko labe kike zuwa kina muna ban sani ba koko ita ta fada maki photo nake ganin ta ba mace ba.
Ina macen take anan wanan ai mun sani farin mai ne wanda matan ku ke shafawa an shafo don a gwada dani aja hankalin ka.
Ko gashin dokin da take karawa ne ya rufe maka ido kake ganin days muke a wurin ka dariya sosai maganan ya bani ban san lokacin da nace da itaba.
Au haka kike tunane a she diba ki gani yadda Allah ya baki fari da komai haka nima ya albarkace ni da abina kamar ku idan ma gashi na doki ne ai yana samun gyara akai akai ko ?
Ba kamar nake da ke cushe a guri daya ba sai doyi balle Allah ya tsareni da kari a kaina don ni musulmace ina tsoron haduwa da Allah na tunda ya sani.
Tace ina musulma a nan dida karki bata min suna kamar yadda kike bata mashi nashi don ni khadija nake.
Ki koma makaranta don Allah ki fara sanin Allah kafin kizo kina karanta ma mutane kishin ki na jahilai.
Jahila na gidan ku kin bari a hasale na juyo gare ta dan jin abinda ta fadi wanda nasan uwata take nufi da jahila.
Nafisa kina haukane wai da zaki zagi iyayyen ta tace na zage ta ko zaka rama matane ina sauraren ka.
Nace shi ba jahila bane irin ki don yasan abinda yake yi ki koma makaranta da wanan jahilicin naki hakana ko zaki san abinda kikeyi nan gaba.
Tace Ke da ke zuwa makarantar may kika karu dashi banda bin maza da kike fitayi wanan kuma kanki kike fada ma don ke ce kullun a hanya ke ba kasuwanci ba aikin office ba wawiya mai fitsari taye ba kama ruwa ko tsarki don haka banga laifin ki ba idan kina haukan ko zargin wani.
Abinci ne yau ko zaki mutu nice da miji sai yaci kuma mu kwana tare da baki so ki gani kije ki mutu ko ki fada ruwa ki hade ran ki.
Zata fara ihun ta yace Nafisa bar nan gurin tun muna sheda juna dani dake tunda kin san ba gurin ki nake ba yau.
Agaban ka kake jin zagin da matar ka take min yace waya fara zagin wani dake da ita ki bace min dagani nace kafin ranki ya baci.
Tace bazata fita ba yazo ya ja mikewa yayi ina kallon shi ya ficiki hannun ta tana turjewa zuwa waje ya wurgata tare da rufo kofan saman gaba daya ya dawo ya zauna yana huci tare da rike kan shi.
Da fashi nayi don in nuna mashi bai damay ni ba nace kan wanan abin zaka bata ranka kafa saba da halin matar ka ba komai ya kawo ta ba don kawai ta bata maka farin cikin kane ko nawa.
Ajiyan zuciya ya sauke tare da fadin wanan bansan ranan da matsalanta zai kare ba a gidan nan .
Nace hakkuri zakayi damu don haka halin wasu mata yake akan kishi tunda ba mai kaunar kishiya a tare dashi.
Cikin zolaya yace har dake kenan ashe nace ni ba mace bace da zance ban kishi ko wace mace ai tana da kishi sai dai na wata yafi na watane.
Ranan mun sha zagi a gurin nafisa da kyar yan uwanta suka lalabata bayan tayi masu bayani suka ce itace bata lissafa da kyau ba.
Suma sun sha fitina a gurin ta kafin taja kafan ta zuwa daki tana jin maranta yana masifan ciwo a lokacin.
Yau AA ya sha mamaki duk cikin kawar da fushi a zuciyar shi kamar yadda nafisa ke son ta bata muna daren mu dashi yasa na zage nayi mai abinda ban taba yi mashi ba tun fara aurataya na dashi.
Wanda na barshi da mamakin hakan a cikin ranshi can gabsnin asubs ne mukaji dukan kofa da karfi cikin tashin hankali.
Rigan shi ya zura a jikin shi ya nufi kofan yana tabayan waye a kofan muryan Yanyala ce take fadin Nafisa ce ba lafiya jini ne ya balle mata.
Hankali tashi ya bude kofan yafita daga dakin binshi da kallo nayi tare da fadi a fili ikon Allah Allah ka kareni daga sherin wanan matar lafiya a cikin kwanciyan hakali ka, ka haushe ni akan ta ko da yaushe.
Jin shi shiru yasa na tashi da daura zani a gaba na saka hijjab dina na fito daga dakin.
Kowan su hankali shi a tashe yake na dan karasa part din nata sai dai ba isa kusa ba a daidai lokacin da ya fito da ita rungumay a jikin shi cikkn gala baita suka fice daga gidan.
Su samihane suka shiga ba tare da yanyala ba a gurin su nake ji wai cikin jikin tane yake son ya bare Allah ya sauwaka nai masu na dawo saman wanka na yi a cikin daren nan tare da dauro alwala na fito na tayar da sallah.
Ban kwanta ba sai da akai kiran sallah asuba nayi sallah tare da jawo wayana na kira layin shi ina tambayan shi mai jikin yace da sauki.
Am bata gado ana son cikin jikin nata ya tsaya Allah ya sauwaka nayi mai ban kwanta ba na fito na nufi part dina.
Kafin dan lokaci na gama abinda nakeyi ganin bai dawo ba had lokacin yasa nafito ko zan samu mai sauke ni a school.
Nakoyi sa,a don su Samiha zasu asibitin nai ma driver magana ya sauke ni a school yacs ba damuwa hajiya.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Tunda na isa school hankali na wurin su ban cikin natsuwa don a yadsa naga sun fita da ita ta matukar ban tausayi.
Sai dai abinda ba,a saka ka ciki ba kuma nasan ko na saka kaina ba zanyi fari a gurin Nafisa ba idan ma banyi hankali ba zata iya cewa nice na jefeta da wani asirin haka ya samay ta.
Sai dai na kudurta a raina idan na fito zan ji halin da take ciki in gaida ita kafin nan na yanke a raina ya kamata in fara neman shawaran maryam ance wanda ya riga kwana yana rigaka tashi inji hausawa.
Don haka maryan zata fi ni sanin dacewa inje ko in bari sai ta dawo gida mu gaisa da haka naci gaba da daukan darasins a class.
Sai a zahar muka fito daga lectures a masalaci kamar kullun muka hadu na rigata zuwa har na kusa idar da sallah sai ga maryam din ta iso na gama na dade ina addua kafin in bar gurin zuwa waje na zauna ina gyara jikina sai ga maryam din ta fito.
Muryan ta naji a bayana tana fadin amarsu ta ango yau lafiya kike kuwa tun dazu nake tsaye ina kallon ki kina tunane ko anyi halin naku ne agidan.
Ajiyan zuciya na sauke ina shafa weat lips a bakina tare da fadin Allah dai ya kyauta maryam amma fasawa za, ayi tunda Allah ya kawoni gidan matsala.
Dafani tayi tana kaiwa zaune tare da fadin AA ya dawo ke nan daga tafiyan ko ?
Tana mai tsura min ido taji amsa nace cikin yar murya karama ke dai ya dawo jiya maryam kuma har munyi halin namu.
Nan dai na koro mata da abinda ya faru a daren jiya din tsakanin mu da Nafisa da wanda ya faru da ita din zuwa safe har zuwa na school.
Ikon Allah wai ko khadi matar nan tana sallah kuwa nace waya sanar mata tunda ba part din mu daya ba nace balle ma nasan tanayi tunda nasan shi ba kyaleta zaiyi ba.
Sai dai ibadan ragaggene na sani ba cika shi akeyi yadda ya dace ayi ba Allah dai ya kyauta kawai kedai maryam tace amin.
Nace ni yanzu shawaran ki nake nema shin in tafi asibitin ne idan tana can har yanzu ko in bari sai idan ta dawo gida in gaida ita don kin san ita bahaguwar mace ce maryam ba ai mata daidai kin sani.
Shi AA din ya kiraki ne da sukaje asibitin nace bai kirani ba nice dai ma na kirashi ina tambayan jikin nata a guriin shi.
Tace matsalan maza ke nan wallahi ai kamata yayi kafin ma su fita ya sanar dake amma yasa kafa kamar baisan akwaiki a gidan ba akala da suka isa komai yayi daidai ai sai ya kiraki yai maki bayanin halin da ake ciki ko.
Nace ni wanan bai damay ni ba don sun fi kusa shiyasa kike ganin duk irin fitinan da zasuyi bai zurfi a cikin sa dan kai zasu bari a cikin idan ka shiga.
Yanzu zasuyi masifa kamar su kashe junan su amma minti goma yayi yawa ki samu sun shirya don may zan tsaya ina wahal da kaina akan su nidai hakkina na tsare kawai don kada wullakanci da raini yai min yawa.
Tace kin kyauta ma kanki wallahi don irin auren jaraban nan idan kana gidan da akeyin shi wallahi sai su daure maka kai don ga abin haushe na faruwa saidai kai kaji musu haushin kawai su basu damu ba.
Ni yanzu shawaran da zan baki shine ki fara bincikawa idan tana asibitin sai muje can mu gaida ita ai ba don ta zaki ba don Allah ne da shi kuma AA din.
Sanan kuma hakan wani makami ne a gurin ki don gaba koda magana ya taso dai kina da abinda zaki fada masu wanda ita ba zata iya maki shi ba.
Na nisa tare da fadin gaskiya maryam ba zan iya kiran AA ba tunda shi baiyi tunanen ya kirani ba insan halin da ake ciki.
Tace kada ki kirashi nima ban goyi bayan ki kirashi ba ai maza suke gyarawa kuma suke bata gidan su idan sun tashi.
Barin kira Yusuf muji halin da suke ciki kiin ga sai mu san abin yi ko kai kawai na gyada mata ina matse jikina da hannaye na wuri daya ina tunaane tare da takurewa a ida nake.
Kira uku ya dauki waya tare da fadin maryam kuna tare da kanwa tace khadija tace eh muna tare itace ma ta sa in kiraka muji halin da mutanen gidan su suke ciki a asibitin.
Yace eh suna can har yanzu don likita ya bata gado na kwanaki har aga halin da cikin zai yi tukun maryam tace dama muna son jin ida suke ne sai taje ta gaida su.
Yace yanzu kuna free ne ko sai anjima inzo in kaiku tace bamu gama ba amma zaka iya zuwa muje ai ba matsala kada yamma yayi.
Yace kujirani ganinan zuwa insha Allahu tace sai kazo Allah ya tsare take care ta kashe wayan tana kallona tare da fadin ke kinji bama zancen dawowa gida bane fa.
Don an kwantar da itane acan sai anga yadda hali zaiyi idona na lumshe ina tunane rayuwa na sake budewa nace oh mata suna ganin abu akan ciki kamar ba ita bace lafiya jiya fa.
Tace ikon Allah ko mutuwa akace maki tayi yanzu ai ba abin mamaki bane don ikon Allah yafi danan nace kwarai kuwa maryam.
Tace aini abinda nake ji zata zauna ta iya yin bedrest din nan a asibiti wanan matar da take kamar shanshani wurin yawon tsiya.
Zata iya mana idan ya kama tayi dole don lafiyan ta sai dai idan cikin bai damay ta bane mun dan dauki lokaci a gurin kafin Yusuf yazo.
Da ya iso wayan maryam din ya kira yana sheda muna zuwan shi muka samay shi a gurin da yai muna kwatance din.
Baya na shiga maryam a gaba ta zauna dashi sai da ya fara tuki nake gaida shi ya amsa da yaya gida jiya mun iso ban samu shigowa cikin ba ina sauri.
Nace kun dawo lafiya ya mutanen gida yace suna gaida ku Fati tace ai maki godiya sosai sun gode nace kai sai kace wani abu na basu mai yawa.
Yace kin yi kokari sosai khadija ai baki san wani abu ba wallahi macen kwarai ke kula yaranta har tayi masu alheri irin haka.
Ina ta samu haka a baya banda ma idan mijin zai yi idan har Nafisa ta sani hanawa takeyi ko ta amshe kudin da sunan zata saya masu abin sai labarin ga.
Maryam tace wallahi wanan abokin naka yana bukatan gyara a rayuwan shi wallahi ta yaya kana tare da mutum abu ya samay ka bazaka iya fada mai ba.
Yace maganan da muka gama dashi kenan kuka kirani wai cewa yayi ai khadija ta sani kuma ta wuce school bada izzinin shi ba.
Murmushi nayi nace ni ina na kara ganin shi ma yayana tun fa da aka buga kofa ya fita ban sake ganin shi ba har yanzu.
Zan zauna ne akan lalurar wata in bar nawa yace na fada mashi ai da yake fada nace kai ka kirata kai mata bayani halin da kuke ciki shine yai min shiru.
Ki dai kara hakkuri kanwata wata rana sai labari insha Allah irin wa yan nan matan ba abokan zams bane wallahi.
Yanzu a asibiti sai da suka kwashi rikici sosai da ita wai ita bazata zauna ba har tsawon wani lokaci da kyat likitan tayi mata bayanin halin da take ciki kafin ta yarda ta kwanta din.
Allah dai ya bata lafiya nace idan tayi hakkuri kwana nawa ne in ta samu lafiyan ta ba sai ta dawo gida ba duk da an san zaman asibiti ba dadi wallahi.
Yusuf yace lafiyan ta yafi komai fa khadija ita wata irin mace ce da bata da ganewa ne mace har da kanta takewa kyata haka.
Nidai shiru nayi suna ta maganan su a hanya wurin masu fruits ya tsaya ya fita sai gashi da ledojin fruits an biyoshi dasu zuwa wurin mota yace zaku shiga mata dashi kada kuje hannu sake.
Godiya mukai mai yana zama nace ummmhmm ni nasan ko kallon wanan ba zatayi ba zatace wani abu muka saka mata aciki don ko yanzu ba fita zanyi ba a gurin ta.
Kada ki damu da wanan don ko baki fada ba sai ta fada idan kuma baki kai badin ma fada zatayi don halinta ne haka.
Mun isa asibitin motar AA mukai tozali dashi a haraban wurin aje motocin muka fito Yusuf na gaba muna biye dashi a baya shi ya dauki ledan tsaraban kayan dubiyar da ya saya muna din.
Lokacin ganin mara lafiya ne a lokacin ga yan uwanta da kawayen ta harda ma wa yanda ban sani ba a gurin.
Suna hango mu kamar ba asibiti ba idanuwan su ya dawo gare mu caaa sai kuskus ake yi a gurin bani ba ko maryam bata tsaya binta nasu ba muka shige dakin da take kwance a ciki.
Ita kadai ce a cikin dakin ba,a hadata da kowa a dakin ba komai akwai a dakin na jin dadin rayuwan dan adam aciki.
Yana zaune bakin gadon da take kwance ga su madam a gefen zaune ya rike mata hannu suna magana muka shiga dakin.
Yusuf ne ya aje kayan yana gaida ita da jiki muka karaso wurin sai dakin yai tsit a lokacin suna kallon mu.
A bakin gadon muka tsaya muna mata ya jiki bata amsa muna ba sai shi dake zaune ke fadin baki jisu bane ?
Ta wani dako kai tana fadin najisu mana ba tazo ta gani da idon ta ba ban mutu ba yadda taso in halaka.
Murmushi nayi tare da fadin Allah dai ya baki lafiya ya tsare gaba mu duba lafiyan ki ne ya kawo mu ba wanan ba.
Allah ya sauwa ka nace tare da fadin mu tafi ma maryam muka juya mun fara tafiya naji muryan ta a cikin hausan ta dake da surki tana fadin ku zo ku dauki kayan tsiyar ku, ku tafi da sherin ku baku ganni cikin mugun hali ba.
Madam ne tace haba matar Samad wanan wani irin haline ai kya bari ki koma gida duk abinda kike ji kuyi shi a can amma ba anan ba.
Duk wanda yazo gaida kai koda na munafunci ne ai yayi kokari tunda tsabgan gaban shi ya bari yazo ko.
Mudai mun fita daga cikin mu ba wanda yai magana har muka kai bakin mota muka tsaya jiran yusuf ya fito mu tafi.
Ashe a ciki sun kwasa da Yusuf din a kan mu da yaji zagin yai yawa yace mata irin hakane kike jawa kan ki matsala may zata saka maki a cikin ayaba da lemo ko kankana yanzun fa suka sa na tsaya hanya suka saye shi.
Tace koshi an fada mashi yarda tayi dashi idan akwai wanda zai kashe ta farko ai shine don ta dade da sanin haka .
AA ne ya mike tare da jan tsuki ya yiwa Yusuf magana su fita daga dakin tace kai kuma ina zaka ko binta zakayi ne ?
Yace idan na bita laifi ne yasa kai suka fito sun samay mu a tsaye ba mai magana a cikin mu kowa da kalar tunanen da yake yi.
Bayan fitan mu madam ne ta ja tsuki tare da fadin Nafisa ina ganin tafiyan mu ba zaizo daidai da ke ba gaskiya.
Yanzu wa ya saura irin wanan kishin da kike haka koma may ye kin ga yanzun tafiki gaskiya ga mijin ku don tazo dubaki a gaban shi kin mata rashin mutunci kuma.
Yanzu abinda kikai din nan yayi daidai ke nan har karamar yarinya tazo tafiki wayau ta nuna maki hillan mata da kissa.
An san akwai zafi tunda a sanadin ta haka ya samay ki sai ki barin har kiga lafiyan ki tukun na sai kin koma gida ki nuna mata halin ki.
Tace madam ke ma kin san ba zan iya ba wallahi uban wa tazo nema a gurina in ba zuwa tayi tagani ko zan mutu ko ina cikin wani hali ?
Dadai kin koyi boye wani hali a gaban miji don ranan fadin magana tace ba wani ranan fadar magana in ba bayan wanan yar iskan nayi da mijina ba.
Ledan kayan fruit madam ta jawo ta fara budewa tana fadin mukan bari muci tunda bada sunan mu akai aikin ba komai ba zai samay mu ba.
Nan suka far ma kayan da ci kamar jira suke itako wani irin bakin ciki take ji a ranta na bin bayan mu da yayi.
Sai lokacin yake gaisawa da maryam ta amsa tana tambayan shi ya mai jikin yace da sauki ni dai ko kallon shi banyi ba ina kallon wani wurin.
School din zaku koma ko gida maryam tace ni dai zan koma itakan gida zata yanzu ai yamma yayi ko mun koma ba wani dadewa zamuyi ba a tashi.
Barin sauke ku yace nace da sauri da ka tsaya kada kuma kayi laifi yaya Yusuf sai ya sauke mu Yusuf ne yace lalai kan don abu kadan yanzu laifine ga mai ciki.
Tsaye yayi sororo yana kallona ina magana ga mamakina nayi zaton zai yi magana amma sai ya kyale Yusuf din ya tafi damu har muka kai gidan ba sa baki a hiran su ba.
Wanda duk hiran akan Nafisa ne suke yin shi muka kawo nayi wa Yusuf godiya na bude na fita ban san ya sukayi ba naji muryan maryam tana kirana na tsaya tare da juyowa.
Ganin tana magana yasa na koma wurin motar inji mai zata fada min sai naji Yusuf na fadin kanwata don Allah kada ki sa komai a ranki halin Nafisa dai yanzu ba bakon abu bane a wurin ki.
Na dan yi dariyar yake ina fadin ba komai wallahi nagode yace ke dai kici gaba da addua don Allah shine kawai mafita ga wanan shu,umar abokiyar zaman taki.
Murmushi na sakeyi ina fadin ba komai na gode nayi masu sai anjima na wuce ciki zuciya na cike da damuwa ina isa na shiga babu kowa a gidan sai mutum daya da yara a gidan.
Ihsan na ganina ta sheko da gudu ta rungumay ni wanan matar dake gida da suke kira da gambo tazo da sauri tana kokarin daukan yarinyar taki zuwa yar Nafisa babba tayi mata yare naga ta bar ta dani.
Dakina muka nufa da ita tana min yare na bude muka shiga kayan zaki na bata irin na yara ta fita da gudu zuwa waje murmushi nayi na tube don in watsa ruwa a jikina.
Sai da na fito nayi sallah na koma na zauna na gyara jikina a gaban mirrow kitchen na shiga don nemawa kaina abinda zanci may dan karfi don yanzu ina ci abinci sosai gashi tun safe ban ci wani abu a cikina har na fara galabaita.
Lafiyayyen nodles na hada wanda yaji kayan hadi don ya cika min ciki na na debo nazo falo zama sai ga Ihsan ta dawo dakin wurina.
Tayi nayi mata tace zataci na dibar mata waje ta nufa dashi na zauna na fara cin wanda na zuba ma kaina.
Yar wurin Nafisa ne ta shigo sai ranan ta fara gaidani a gidan tana tambayana idan abincin da na dafa ya rage in diba mata yunwa take ji.
Kallon ta nayi kamar zanyi magana sai dai na mike na shiga kitchen din na juyo mata wanda ya saura gaba daya.
Ta karba batare da furta komai ba ta fita bayan na gama ne na fito don gyara part din msigidan na samay su zaune dukan su harda mai tsaron su a gidan suna ci.
Na shiga dakin yana a yadda na barshi da safe sai kayan barcin da ya cire a saman gado ko tsaban rudewa yasa yau ya barshi a wurin ban sani ba.
Wanko ban dakin na fara yi inda na dawo dakin na gyara mai komai tsab na rufo kofan kamar yadda na samay shi na dawo part dina.
Har akai magariba banji ya shigo gidan ba har tara na dare barci ya fara dauka na tashi nayi na kule part din na don na dauka a asibitin zai kwana ke nan.
Sai sha daya da wani abu ya dawo gidan bayan sun gama tsiya da Nafisa daga kwancen amma bata barshi ba don cewa tayi bata yarda ya kwana a gidan ba don ranan girkita ne.
Kada yaje wurina don baiga idon ta ba da alkwari da komai ta barshi ya tafi gida shi dai sai lalabata yakeyi kada cikin jikin ta ya samo matsala dai.
Koda ya shigo gidan ba kowa a falon sai dai wuta a kunne yake har lokacin kallon kofan part dina yayi ya ganshi shima rufe.
Kofan gidan ya rufo ya nufi part din shi don ya watsa ruwa Allah ya taimake shi yayi duka sallah a cikin jamm,i wanka ya rage mai sai dan abinda zaici.
Ya fito yana saye da bathrobe ya tsaya gaban mirrow dakin har ya gama shiryawa cikin pjarm din shi ya sauko zuwa part dina ya murda hardles din yaji kofan a rufe kara murdawa yayi sosai ya ji a key kofan yake .
Gashi yana gudun buga kofan yan uwan Nafisa su jishi sukai mata labarin sun ji shi yana bugun kofa na dole ya juya ya koma part din shi zuciyar shi a cunkushe.
Ban falkaba sai asuba karan agogon dakin ya ta dani duban lokaci nayi tare da saukowa saman gadon na nufi bathroom din daki.
Alwala nayi bayan tsarkin da nayi na fito na tayar da sallah ban kara kwantawa ba kitchen na fada don ina son in dan dafa wani abu in rika wanda zanci don jiya nasha wahala sosai a school din.
Saida na gama hada abincin ne na shiga wanka tare da zuba wanda zan dan karya dashi kafin in fita yau tafa na sa a jikina zani da riga da yake zamay min wahalan idan na daura amma haka nake koyon sabawa da daura zani yanzu.
Falon na dawo a cikin shirina na zauna cin abincin ban jima da zaunawa sai gashi ya shigo dakin dago kai nayi na kalle shi na kawar da kaina naci gaba da cin abincin da nakeci.
Sai da yazo gab dani na ce dashi ina kwana bai amsa ba sai da yakai zaune ya amsa da lafiya maimakon in ci gaba da cin abincin sai na koma wasa da cibin.
Amsan cibin yayi daga hannu ya debi abincin yakai bakin shi tambayan daya jeho min ne yasani dago kai in kalle shi.
Yanzun kika dafa abincin ko may da eh na bashi amsa kawai ina nawa abincin yake ya tambaya cikin tsure ni da ido .
Nace ban dauka zakaci ba nawa kawai na dafa na bashi amsa yace saboda may koni ba zanci abincin bane naji ya fada.
Nace na dauka a asibiti zakaci naka ai daga haka na mike na shige ciki na barshi a wurin bin bayana yayi da kallo yana murmushi.
Koda na fito a ciki shirina na samu ya cinye abincin gaba daya dana bari kujeran dake gefe na samu na zauna akai ba tare da nayi magana ba.
May yasa jiya kika fita baki kirani ba kuma waya sauke ki school din da kika tafi nace ban san amsan da zan bashi ba don haushi sai nayi shiru.
Yace tambayan ki nakeyi kin kyale nace yan uwan matarka da zasu fita na roka su sauke tare dasu muka fita yace OK da izzinin wa kuma kika bisu ?
Amma kasan ina karatun ko da ka aure ni ko yanzun ne kuma zaka ce baka san ina fita zuwa makaranta ba din.
To yau ki zauna babu inda zaki daga haka ya mike ya bar falon binshi nayi da kallon mamaki ban samu magana ba.
Kofa na mike na rufe bayan fitan shi na koma uwar daki na cire gyale tare da aje jakkana na haye gadona ina tunane a raina.
Ba komai nake tunane ba sai hanani fita da yayi don ban san ko may yake nufi da hakan da yai min din ba.
Waya na dauko na kira maryam kafin ta shiga class ina fada mata abinda ke faruwa tace dani kyale shi sa mai ido zanje department din ku in masu complain baki da lafiya .
Amma maryam saboda may zai hanani tsabgar gaba bayan yasan ina karatu ya aure na hakana tace kiyi hakkuri.
Gwada ki yakeyi ko zaki fita ko ba zaki fita ba din ya samu bakin magana idan kin fita kin ga gara da kika kyaleshi ya fita baki magana ba yasan wa yake aure.
Idan mun fito da yamma zan leko ki sai mukarasa maganan nace to nagode na kashe wayan.
Barci ne ya dauke ni a wurin da nake da tsakiyan tunanen sabon rayuwan da nake fuskan ta din a gidan.
Saida ya gama abinda zaiyi ya fito zuwa asibiti kallon part dina yayi ya ganshi a rufe ranshi ne ya baci ya nasa watau fita nayi da ya hana fitan.
Har yaje asibiti ya duba su da kwana nafisa sai korafi take mai yaki zuwa da sassafe ya dubata sai yanzu na barshi yazo ganin ta .
Yana zaune office rai bace yana tunanen iri hukuncin da zai yanke min ji yake kamar ya hana karatun gaba daya yaga tsiya ko bai hanani ba sai ya bata min rai kamar yadda na bata mai.
Zai nuna min a karkashinshi nake a yanzu ba karkashin wani ba yana wanan halin ne Yusuf ya shigo office din ya samay shi a haka.
Sun gaisa ne ya kalli yanayin shi yaga bai a cikin dadin rai yake tambayan shi ko jikin nafisa din ne ya tsanan ta haka.
Kai ya girgiza mai yana fadin taji sauki sosai dani da Deedar ne wanan karon ban san may yarinyar nan ta dauke ni ba .
Wani abu ya faru ne yace zai dai faru don zan saba mata sosai wallah har zance mata kada tayi abu tayi shi.
Yusuf yace ita khadija da kanta ko dai bata fahince ka bane don banyi tsamanin zatayi haka ba gaskiya yace OK karya ke nan nake maka.
Jiya na dawo na samu ta rufe kofa bata aje min abinci ba naje kofanta a rufe da safe kuma again wai bata girka dani ba ta dauka a asibiti zanci ina mata magana kuma tashige daki ta barni a zaune.
Sai gashi ta fito wai school zata nace ba zata tafi ba shine ina fita daga dakin ta fita bansan may yasa take son cudanya da maza suna daukan ta a mota ba ta san kuma ban son haka.
Hannu yusuf ya daga mashi yana fadin kai malam gyara zancen ka don Allah kada wani yaji ya dauka wani harkan banza take yi na daban.
Har wasu maza suka dauke ta ba dai driver gidan ka bane kokai kuma kana bada wanan go ahead din.
Kenan su ba maza bane ya tambayi yusuf din cikin bacin rai yace jiya kayi ta kanta ne ko ka bugo mata waya gaka nan tafe kakai ta daba zata bi wasu ba.
Yanzun ma da kake wanan magana ka tabbatar da bata gidan tana makaranta ko a gaban idon ka kags fitan ta yace dashi a hasale nasan fita tayi tunda na samu part din ta a rufe.
Waya Yusuf ya ciro daga aljihun shi ya kira layina a cikin barci naji kiran na dauka da sallama bayan mun gaisa ne yace .
Kanwata kina ina yanzu don Allah nace ina gida yayana yace yau ban fita school ban san may yake nufi da hakan ba gashi yanzu lokacin tsananin karatun mu yake.
Yace ok zan mashi magana ya barki kiji yanzu zai zo ya dauke ki nace No ka barshi kawai yayana na riga na makara yau.
Na kare da fadin wani abune ka kirani dama yace amma barshi kawai na dauka kin fitane in baki sako wurin maryam.
Dan murmushi nayi nace kai yayana kada ku sani tsaka fa ga sister inlaw kuma ga friend yaya kuke son in yi da raina yace haka shine karin zumunci ai na kashe waya ina dariya.
Kallon AA din yayi cikin zafin rai yana fadin kada ku cutawa yar mutane kai mata wasu suyi maka jiya a gaban ka yarinyar nan tabar karatunta taje gaida matar ka sukaci mata mutunci a gaban ka bakai komai ba.
Yanzu kuma ka nemo wani fitina kana kokarin haddasa fitina a tsakanin ku tun bata iya yiba kazo ka koya mata maka mussu.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Darajan Allah da Annabinsa ya fi komai nauyi ga musulmi koda yaro karami ne yasan darajan wanan kallaman mai muhinmanci ga musulmi ko kafiri yasan daraja da nauyin wanan kalman.
Balle dan musulmi baligi ko baliga har yanzu ba zan gaji da daure ku agun Allah ba da wanan kalman don darajan Allah da annabinsa kada ki fitar min idan ma an fitar yar uwa musulma kada ki karan ta idan baki biya ba don darajan Allah da Annabisa musulman kwarai ce kadai zata fahinci hakan
Idan kuma kin nace da karanta hakkin wani Allah yasan tsakannin ki dashi akan haka don na sauke nayina na fada na kara fada don darajan Allah kada ki karanta hakkina idan baki biya.
Inagama daukan wayan Yusuf kiran ya Amina yana shigo min mun gaisa na tambayi yara ita ta tambaye ni muna lafiya dai?
Nace lafiya muke anty tace jiya ta shiga cikin
gidan su mommy ake fada mata cewa Nafisa bata da lafiya an kwakaina da ita asibiti.
Nace eh hakane anty an bata bedrest a asibiti yau
kwanan ta biyu a can tace da nace idan su mommy zasu zo zan biyo su inzo in gaida ita.
Da sauri nace No kada kizo ya Amina ban son kowa nawa yazo gaida wanan matar don gudun matsala.
Haba khadija daga gaisuwa kuma sai matsala ina laifin wanda yazo gaishe ka ai komai abinta ba zata ce sheri ya kawo ni ba ko ?
Naga yin haka kamar sayen mutuncin ki ne a gurin su ita da mijin ta nace ya Amina na fada maki kada kizo don Allah don ba irin wanan matar akewa haka ba gaskiya.
Idan ita bata gani ba ai
mijin ya san don shi aka zo ko nace harshi din anty halin su daya don ko a gaban shi sai ta ci maki mutunci ba abinda zai yi don haka kawai ki zauna.
Tace kina ganin hakan zaifi nace kwarai kuwa ina hawaye duk da ba ganina take yi ba amma zuciyar ta ya bata ban cikin dadin rai.
Khadija hakkuri zaki aure ya gaji haka don dan kalubali ne aure wata rana ka wayi gari a cikin dadin rai watarana akasin hakan.
Koda kuwa baka da kishi balle ke mai kishiyoyi da yawa don haka sai kin hada da hakkuri da addua kina yawaita kai kukan ki ga Allah.
Sai komai yazo maki da sauki a cikin alamuran ki don Allah yana tare da masu hakkuri da yaiwata ibada a gare shi.
Hawayen dake fuskana na goge tare fadin bakomai ya na gode kudin da na turo sun kare na sadaka ko in turo wasu tace da saura a hannu na sosai kullun ana maki sadaka dashi.
Maryam ta tambayeni nace yau bamu hadu ba don ban shiga school ba tace lafiya nan shiga ba nace banda lectures ne yau na tsaya in hutane.
Dan nasiha kamar kullun tai min tare da kara min karfin gwiwa a zaman takewan rayuwan aure nayi mata godiya tare da kashe wayan mukai sallama da juna.
Kwallan dake fuskana na share tare da gyara kwaciyana ina tunanen yanzu may ye matsalana ko laifina a hakan da yai min .
Ni da ya wullakanta akan matar shi ya manta dani banyi fushi ba sai shine mai daukan mataki a kaina wani abu sai ko aure yakai haka ga mutum.
Kayan jikina na tashi na sauya tunda ba fita zanyi ba kuma ni kadaice a gidan wando da yar riga armless sai kaina da na daure da ribon ko dan kwali ban aza a kan nawa ba.
Falo na dawo bayan nayi sallah azahar na dauko cake da drinks na aje a gabana na kunna tv ina kallo ina kora drinks din a hankali.
Motsin da naji kamar wani zai shigo part din yasani dago ido ina kallon kofan jin an kara murda kofan yasa na mike na nufi kofan tare da cire key a kofan .
Gardawan samarin nan ne buzayen gidan suke shigowa da kayan masarufi zuwa kitchen dina da sauri na koma daga kuryan dakin na zauna harsu bar part din.
Sai da naji na daina jin motsin su na fito na zauna a inda nake ba tare da na kara rufe kofan ba ban kuma je na duba abinda suka shigo dashi din ba.
Sai dai ina tunane a raina ina dadin wanan kayan da ake jibga min babu kwanciyar hankali a tare da zuciya na ko kadan.
Shi ya shigo da sallaman shi a dakin daidai lokacin da na dauki kwalin drinks ina korawa a bakina yana sabale da corth din shi a kafadan shi, sallaman na karba mai tare da kawar da kaina daga kallon shi.
Shima ni din ya tsurawa ido yana kokarin samun wuri yakai zaune don daga ganin shi a gajiye yake a lokacin muryan shi naji yana fadin dauko min drinks mai sanyi in kora.
Ba tare da nai magana ba na mike zuwa kitchen din anan na samu kayan da masu karfin nan suka shigo min dashi a tsakar kitchen din nawa.
Bin kayan nayi da kallo na wuce zuwa wurin fridge na dauko kwanlin five alive da kofi na nufo falon dashi a hannu na.
Gaban shi nazo na dire da zan dago na rusunna irin al,adan mutanen Niger din nan ko mai zakayiwa na gaba da kai sai ka dan bashi girman shi duk da addini ya rage wani abu da wayewan kai kuma.
Wanan dabi,an kowa ya san mutanen Niger da irin sa wurin ba na gaba girma da girmamawa ba su da wari a gurin nan .
Kanshi a sama dage ya furta thanks tare da sauke kanshi hannu na naji ya kamo zuwa baya na fada a jikin shi.
Kokaein kwacewa nake ga jikin nasa yaki bari na kurce mai ji nayi yace kamar mai rada fushi kike dani don na hanaki fita yau ko mai ?
Akan may zan yi fushi tunda a karkashin ka nake kace ba zan fita ba ai dole in zauna fushi na may zanyi tunda nasan yau baka ra,ayin fitan nawa ne.
Kaina ya tallabo ya hada da goshin yana sauke ajiyan zuciya tare da fadin kin dai huce daga fushin naki.
Kokarin mikewa nakeyi tare da fadin wani yace dakai ina fushi dakai dama ni dai naga hakan don ko abin sha sai dana roka yanzu a wurin ki.
Dama ina da niyar dauko maka idan ka bukata kuma ka bukata na dauko ma salin alim shine kuma abin fushi din.
Yanzun dai ba wanan ba zowa nayi inji idan akwai wani abin amfani da ba,a sawo maki ba wanan watan sai ki fada min a sayo yanzu.
Komai akwai na gode nace yaushe kika duba kayan da kike min godiya a kan su nace ko ban duba ba nasan zaka sayo muna komai na bukata ai.
Kwalin juice din ya dauka tare da balle marfin kwalin ya kafa a bakin shi ya fara sha hakana bada cup ba sai da yasha kusan rabi ya aje kwalin ya mike tsaye yana fadin zan koma asibiti in duba su idan na bar nan kafin in isa office Allah ya sauwaka nace ina kokarin dauke kayan da suke falon.
Zuwan maryam ranan yasa na basar da komai dake raina don hiran mu da ita yasa na manta da duk wani damuwa na.
Tana gidan har sai da tayi sallah isha,i ta bar gidan nayi nayi ta kwana tace zamu dai hadu gobe insha Allahu.
Bai dawo gidan ba sai sha daya Nafisa ta barshi ya dawo gida lokacin har nayi barci a dakina don banji motsin shi ba na dauka a can yake kwana.
Wayana ya kira sai da yai min call biyu na falka daga barcin da nayi nisa ga yin shi bude min kofa ya fada bayan na dauki wayan.
Nataso da sauran barci a idona na bude mai kofan dakin ya shigo shima da ganin shi a gajiye yake a lokacin.
Sai dai yayi wanka don alama ya nuna hakan saboda ya sauya kayan jikin shi zuwa dogon riga sabanin yadda ya fita gida da rana.
Abinci fa ko baki aje min ba kitchen din na nufa na dauko mai abincin nakawo tare da fadin sama zan kai ma ko nan zakaci ?
Aje min in ci nan ya bani amsa hankalin shi yana ga wayan shi saida na gama jera mai komai nace na hada ya dago yana kallo na tare da fadin kin rufe kofan nan ?
Kallon shi nayi da mamaki nace na dauka yanzun zaka fita yace yana nuna kofan rufe kawai na tashi ina mamaki a raina tare da rufo kofan.
Mikewa yayi ya nufi dan table din mai kujeran mutum biya ya zauna zuwa nayi na fara zuba mai abincin nagama nakoma dayan kujeran na zauna tare da harde hannaye na ina kallon shi.
Abincin har lokacin da zafin shi sosai tuwo na tuka mashi na farar shimkafa da miyar kuka da naman rago nayi amfani da kayan yaji sai man shanu dana zuba a sama.
Tunda ya fara cin abincin baiyi magana ba har ya kare na mike ina tattara kayan don idona cike yake da barci a lokacin.
Bayan na kawar da kayan ne na dawo falo da zumar zama naga ya mike ya shiga kuryan dakin kashe wutan ko ina nayi falon na shiga dakin .
Na samu yana cire rigar shi daga kofa inda nake nake fadi amma baka fada min a nan zaka kwana ba yau ban gyara wurin yadda ya kamata ba.
Baiyi magana ba sai da ya zauna a gadon yake fadin may ye laufin shi a hakan ai a gyare yake yana fadi ya haye gado ya kwanta.
Juyawa nayi zuwa falon bakomai nake yi ba sai dai na dauki lokaci ban dawo cikin dakin ba sai can na shigo.
A zato yayi barci ne yadda na ganshi a gajiye don haka na dan tako a hankali zuwa gadon can na kwanta na takure a wuri daya.
Can naji shi yana shafa addua a jikin shi tare da sauke ajiyan zuciya ni dai ina wuri daya a takure sai rokon Allah nake a zuciya na kada yace zai taba ni alokacin.
Saukan hannun shi naji a jikina dan zabura nayi a firgice tare da lumshe idona ina jin yadda hannun shi yake yawo a saman jikina.
Sai faman runtse idanuwa na nakeyi kokarin rabani da dan rigar barcin dake jikina yakeyi a hankali na iya furta don Allah ka barni please.
Why naji yace dani kamar mai yin rada nace banjin dadin jikinane kawai shiru yayi na dan wani lokaci sai naji ya matse ni a jikin shi yana sauke numfashi a hankali.
Bai mun komai ba haka muka kwanta da sassafe na tashi bayan nayi sallah kitchen na fada don sama muna abin karyawa.
Nan na barshi zaune yana addua na shige kitchen din don gudun makaran shiga school da nake tsamanin zuwa yau din.
Sai da na gama in son shiga wanka sai gashi ya shigo dakin har yayi wanka a lokacin yayi shirin fita sai lokacin na gaida shi da kwana.
Ya amsa min yana kallon fuskana tare da tambayana yaya jikin naki nace naji sauki cikin wani murya.
Ni zan fita yace yanzun suka kirani daga asibiti wai ana nema na a can dago kai nayi na kalleshi tare da fadin abinci fa nagama hadawa.
Yace banda time din karyawa yanzu sai dana kalleshi nace idan ka tafi wa zai sauke ni school ?
Yace wani school ke da ba dadin jikin ki kike ji ba zaki fita ki zauna ki huta a gida har ki kara walwalewa.
Don girman Allah ka bari in shiga yau kada nayi hadaran point dina jiya banje ba yau kuma kace haka.
Yace eh yana tafiya yana fadin haka naga yafi ga lafiyan ki don ki samu sauki sosai ina kallon shi ya fita naji kamar in saka hannu a kai in kurma ihu a wurin.
Tunane kalakala nayi shi a cikin dan lokaci kan kankani wankan da ban iya shiga nayi ba ke nan ban kuma iya kallon abincin dake gabana ba.
Na dan dauki lokaci a wurin zaune ban iya ko motsawa daga inda nake zaune ba naji wayana daga daki yana ringing kamar in share wayan.
Sai kuma nayi tunanen kila maryam ce ke nema na a layina don haka na tashi zuwa daukan wayan kafin in isa kiran ya katse.
Na duba naga shine a layin kokarin aje wayan nake wani kira ya shigo min nashi na dauka yana fadin kina ina haka waya ke ringing baki dauka ba ?
Ina falo na bashi amsa yace ki shirya min breakfast yanzo zan aiko a daukar min ke kuma ki shirya ya sauke ki a school din idan zaki iya zuwa.
Kamar in ce mai ba zan tafi ba sai naga kaina zanwa sheri nace dashi to kawai ba tare dana furta wani abu ba shima naji ya kashe wayan diban lokaci nayi naga ina da sauran lokaci.
Mikewa nayi na fada bandaki ina tunane a raina ashe haka mata suke fama da ikon maza a kan su mace ita shike nan bata da wani right din kanta sai inda akayi da ita.
A gurguje na shirya tare da shirya mai komai sai ga driver ya iso shiya kirani yana fada min driver na waje yana jirana .
Ban tsaya bata lokaci ba na fito a cikin shirna a waje na samu driver yana jirana fitowa tayi ya karbi kayan hannu na ta sa a motar ya bude min na shiga muka fara hanya.
Tunda ya gaida ni bai kara magana ba sai da na gama tunane nace dashi yana asibiti ne ko office yanzu.
Yace yanzu na sauke shi office ya baro asibiti a raina nace watau akan zuwa asibiti duba matar shine yasa ya fita ba tare da ya jirani ba komay.
Ko kuma wanin sallon ne suka fito dashi a gidan yanzu ya daina saukeni don an hanashi fita dani da wanan tunanen har muka isa school.
Na sauka tare da yima driver godiya na shige ciki na samu har an fara lectures malamin bai hanani shiga ba don ya ganni saye da hijab.
Saboda yana respecting din mata aure sosai yace lalura ke tsayar dasu a wani lokacin haka yasa yake dan rangwanta ma matan aure.
Ban fito ba har sai da mukaje break daidai lokacin sallah azahar wanda a lokacin ne muke dan samun lokacin cin abinci da sauran su.
Yau ma kamar kullun a masallaci muka hade da maryam ina alwala naji tana fadin matar manya yau kin samu fitowa ashe.
Saida na gama na mike nake cewa da ita nikan ai naga iko maryam yanzu na fara ganin matsalan da aure keda shi wallahi.
Bayan mun fito daga sallah muka zauna a inda mukan dan huta idan mun ffito daga sallah kafin mu koma lectures din.
Sai lokacin na fito da abincin da na dan zuba don in karya idan nazo yau kuma abinci zaki ci nace.
Ban karaya ba maryam yau AA yayi bala,in bata min rai sosai wallahi nan dai nake fada mata yadda mukayi dashi.
Dariya naji tana min tare da fadin ai ma ya raga maki cewa fa kikayi bakijin dadin jikin ki.
Kin hana ma bawan Allah hakin shi kice ba zai dauki mataki a kan ki ba ya gane rowa kike mashj ai kyale ki dai yayi wallahi.
Wayana na naji yana verviration na dauko naga sunan shi nace kamar wani wandaa ya damu dani don Allah kirana na may yake yanzu kuma, ?
Ina dauka naji yana fadin yawa kina jina wai su mommy ne suka zo ban san da zuwan su ba yanzun suke sanar dani tasowan su.
Kallon maryam nayi yaci gaba da fadin idan kina free sai ki koma gida yanzu su samay ki a gida idan sun iso.
To kawai na amsa mai dashi na kashe wayan kallon maryam din nayi nake fada mata tace ai dole kije ku gyara gidan ki dan yi masu wani abu ko ?
Tare muka tafi don driver shi ya dawo ya dauke mu zuwa gidan tunda muka isa gidan bamu zauna ba falon gidan ne kawai ban taba ba don ko na gyara buzaye zasu bata shine.
NAFISA
Duk da tana kwance asibiti ba abinda ya rage a cikin halin ta madam na shigowa dakin bayan sun gaisa ne tace madam.
Duk da nasan wanan dan bakan a tamke yake ban cire shi ba a yadda yake tun ranan don gudun su faki idon ya amfa mata yasana barshi a hake.
Yanzun ma jiya da dare nake jin likitocin nan suna magana wai zan kara kwana ki anan na nuna masu bazan iya ba gwamma na koma gida na fake yan iskan nan da idona.
Kai nafisa akwai ki da shirmay wallahi ba zaki batun lafiyan ki ba yanzu ta wani shirmay kike can wai kishiya.
Kishiyar da kika san babu abinda zai taba faru a tsakanin gaban ki ko bayan ki duk dayane a gare su tun da kin dane shegu.
Tayi dariya tare da fadin kai nafisa kin san kan sheri wallahi yanzu kirikiri kin hana komai ya wakana a tsakanin wayan nan mutanen.
Tace ina zan barsu yar iskan koni ta samu haka zata hake ni kin sani tunda ba kishiyar dake son ganin dingo karuwa ga yar uwar zaman ta ai.
Ta kasheni ko in kashe ta shine aure zamanin nan ai don kowace hake take da yar uwarta kowa na sukar dan uwa.
Wallahi indai nice haka zata kare a gidan nan bata gane komai yar iska harta tafi don wanan da ace ta samu ranke ranke ce ni da yanzu taimin yadda naiwa fati.
Da ita da ban za duk daya a gurin miji wallahi madam naki jini a lokacin in bude ido inga wanan bakar fatin gidan samad da yaran ta.
Ina murnan sun tafi ashe zaune bata kare min ba yaje ya kwaso min jikan mayu ya kawo min gida ina hadiyan takaici.
Idan naga yarinyar nan kamar in shake yar iska nake ji a rayuwa na ga shegen feleke wai ita yar boko a dole.
Madam ne tai dariya tare da fadin watau ma waine ko baki tabbatar ba ke nan ke madam tace yanzun kina ganin babu abinda ke faruwa a tsakanin su har yanzu.
Daga inda take zaune tana fuskantar madam din tace ban tsan mani ba duk rawan kan dakikaga yana mata a yanzu wani tsigane na lalashi kada ta tona mashi asiri ace bakai namiji ba.
Dariya suka dauka tare da tafawa kamar ba a asibiti suke suna jinya ba sai faman hanya kulla sheri suke na yarda zasu kasara rayuna da na Fati gidan ya koma nata.
Wanan ai kin gano takon shegeya mai ido a tsaye don idan kika bari har ta fara dandana maki miji ta samu ciki ja dake zatayi sosai a gidan nan don a bude idon ta yake.
Gaban Nafisa ne ya fadi jin abinda madam diin ta fadi a gamay dani na zancen haihuwa da sauri tace madam ranan ko da anyi aika aika ba kadan ba a gidan nan.
Don wallahi na tsani samad ace yana da wasu diya shiyasa ko wa yan nan yaran ban yarda ya saka su a ranshi ba.
Da karfi da yaji sai da naga gaba daya hankalin shi ya fita a gare su bai ko ambanta sunan su ako ina yake yanzu.
Ai mutumiyar baki da wasa wallahi kin huta ganin takaici ba mai maki sallon haihuwan da na namiji har biyu tace shiyasa nake son wanan cikin don in haifi namiji nima.
Badon haka ba ai da tuni na bar da shege na huta da wanan wahalan da nakeyi haka nifa ba haihuwan nake so ba haihuwan namiji kawai nake kwadayi dashi.
Shigowan wasu matar abokan aikin shi ne ya katse masu hiran nasu idan ko nan bata bar halinta ba sai wani jiji dakai tana basarwa take masu.
Basu dade ba sukai masu sallama tare da Allah ya sauwaka suka fice matsn sheri ko wanan bakin Nafisa da madsn basu barsu ba sai gulman su suka dasa kuma a wurin.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Abinci lafiyayye na shirya ma su mommy da ban san su nawa ne tafe ba sa,a na shine ina da komai da muke bukata a gida.
Zakace abincin restaurant ne yadda muka kawa ta komai tuwon faran shimka shine nafiso a rayuwana don haka ban rabuwa da abin sarrafa shi a duk inda nake.
Yauma bayan na tuka tuwon na daure a cikin farar leda ba wasu manyan kwasa nayi ba daidai yadda mutum zai iya cinye kwasar nayi.
Miyar a laihu da manja sai egusi dana daure miyan wanda nama ciki na yankashi da girma yadda zai cika miyar a plate idan anzuba.
Bayan mun gama na shiga wanka nafito na gyara jikina a cikin dogon ringa dinkin kasar Dubai yaji duwatsu har kasa atamfar super ce akaiwa pattern din kwalliya da stone masu kala.
Maryam ma wani dogon riga ta saka a jikin ta muka zauna zaman jiransu ashe sun iso suna asibiti .
Bai samu zuwa ba a lokacin don haka ya tura wani dan ma,aikatan su yayi masu iso inda Nafisa take kwance.
Bai samu sheda mata zuwan su ba don ranan yana busy da baki a office shiyasa ya manta nima zai shiga ne kiran da Abba yai mai cewa sun taso sai yayi tunanen irin taron da zasu samu a gidan idan ban nan shine ya kirani.
Tana zaune saman gado ta baje tana cin kaza gassa da aka kawo mata su madam ma kazar suke yaga daga inda suke sai hira ake kwasa da dararaku irin na shakiyan ci daga bakunan su.
Sallama sukaji a kofan dakin suka waiga don ganin masu shigowa ds sallaman idon tane ya sauka akan anty Amarya dake gaba mommy tana bi mata sai anty Fauziya da Anty Faiza da ya Amina a bayan su.
Take yanayin fuskan ta ya sauya daga dariya zuwa daurewa don batai maraba da zuwan su ba a lokacin don bata ga dalilin zuwan su ba.
Ta dauki zuwan su da munafunci ya kawo su don su zo suga halin da take ciki su koma su baza a dangi ga halin da take ciki.
Don haka ta shiya masu cin mutunci a wurin don sai sun raina kan su da zuwan da sukayi din anty amarya dake gaba dama nafisa ta dade da fahintar son shige mata da take son yi.
Anty amarya cikin kulawa da nuna damuwa a gare ta take fadin Nafisa sannu ashe kuma haka abin ya zo da akasi kuma.
Kazar dake gaban ta ta kawar gefe tana fadin akasi kuma anty wanan ai matsalan ciki ne duk mace mai haihuwa na tare da wanan laurar.
Mommy ne ta yi kamar basu fahinci abinda take nufi ba tace Nafisa ya jikin Allah yasa haka ya zamo alheri ubangiji ya baki lafiya ki koma cikin iyalan ki.
Wanan magana na mommy yai mata tsauri don addua mai kyau mommy tayi mata sai ta amsa da amin mommy faiza da fauziya da kamar zuwan dole sukayi dama sukace sannu Allah ya baki lafiya.
Tace ai lafiya ya samu don gashi kun ganin a cikin sa yanzun ma muna jiran likita ya dawo ne ya bamu sallama mu koma gida.
Fauziya tace ashe ma yadda ake fadi kina jin jikin bai kai yadda yayan mu ya ruda mu ba eh baikai ba tunda ba a jikin ku ciwon yake ba.
Shi kuma da ya damu din ban aike shi shela na a duniya ga halin da nake ciki ba a,a may ya kawo wanan magana kuma haka daga zuwan mu gaida ke inji Fauziya.
Nafisa tace wanan haka yake ai maganar gaskiya na fada daga dan ciwo zai kama tallatani a duniya kamar wani matsala babba.
Allah dai ya baki lafiya inji ya Amina dake kallon ta gaban ta ne ya fadi don kamar da tagani nawa ga ya Amina din sai ta kafe ta da ido.
Mommy ne ta kula da hakan tace ga yar uwar amaryan ki nan makwaciyar mu ne tazo ta gaida ke da taga zamu zo .
Au itama ashe gulma ya kawo ta tazo ta ga ko zan mutu ko ai ban farga ba tun farko har da dangin mayu kuka zo min su karasa ni tana fadi tana jan zani dake jikin ta tana rufe cikin ta da jikin ta.
Haba Nafisa wanan wani magana ne kuma kina nufin gulma ya kawo mu ko may idan ma kin mata ki sani abinda ke cikin ki yana da alaka damu don haka dole muzo muga lafiyan ki.
A, mommy ki dai gyara zancen ki abinda ke cikina da Samad yake da alaka don ko wace ke fili a yanzu ba damuwa kukayi da ita ba a cikin ku.
Kin nuna mata mu yan uwan ubanta ne aka kita don da kin gwada mata mu ai da kinga gatan dakin a gare ta mufa ba don ke muka zo wurin nan ba don mijin ki ne da Abba da yace mu zo mu duba ki.
Kuka dai zo ganin halin da nake ciki amma wace ba a damu da ita da abinda ta haifa a cikin ku ba har aure akai ma Samad aga yadda zan nakasa a gurin shi ko in koma baya don tsabar kiyayyan da ake nuna min.
Anty amarya zatai magana mommy ta tare da fadin bamu san kina kule damu ba ai nafisa da bamu zo ba sai idan kin huce kin fahinci mu ba makiyar ki bane sannan mu zo dubaki.
Don bamu dauke kina rike damu ba a ranki haka sannan ki sani shi aure da samad yayi ra,ayin kanshi ne yayi haka ba ra,ayin mu ba.
Don ba mu zamu zauna mashi da ita ba aure ya nema kuma muja bashi goyon bayan hakan sai dai kiyi hakkuri da kaddara don aure kan anyi shi ba rabuwa sai fatan alheri ta juya tana fadin mu tafin ku Allah ya sauwaka.
Suka juya Faiza ta juyo tana fadin ke kan ki canza halin ki don kina tare da wahala kan ki kika wullakan ta bamu ba don dai Ya AA zai iya rabuwa dake mukuma yana tare da mu har abada.
Nan suka fice suka barta tana jefan su da bakaken magana masu zafi suna fita faiza tace kunga abinda nake fadi tun a gida akaki yarda da magana na yanzu ai gashi kun gani.
Suna mota hanyar zuwa gidan sai masifa suke ya Amina dai shiru tayi mamaki ya cika mata zuciya halin nafisa ya bata tsoro yadda taciwa su mommy mutunci.
Ina gani wani irin zama na keyi a gidan dasu ga yan uwan ta tab a gidan niko ni kadai babu ko abokin hira a tare dani.
Sun iso gidan basu yi mamakin ganin gidan hakana ba gyara ba don yawan mutanen dake ciki zaune ba masu moriya bane.
Don sun dade da sanin halin su ba yauba don haka yanayin da suka samu gidan bai basu mamaki ba.
Part dina yana rufe kamar kullun nan suka nufa ina jin an kwankwasa muna zaune tare da maryam muna hira jin motsin kofan nace da maryam ko sune suka iso maryam ne ta bude kofan sune a tsaye.
Da murana na mike na tare su ina masu sannu da zuwa duk na rude da ganin su in gaida wanan in gaida waccen suna karba min.
Idanuwan su na akaina sai da suka zauna ne na shiga kitchen maryam ta biyo ni abin sha muka fara gabatar masu sai abinci ya biyo baya.
Bayan na gama gabatae masune mommy tace sallah zasu fara kafin su zauna cin abinci din dakin na yi masu jagora suka shiga ana suka fara gabatar da alwala da sallah daya bayan daya.
Bayan su idar ne suka zauna cin abinci yar gurin Faiza ce dauke a hannu na ina mata wasa naji sun sako zancen rashin mutuncin da Nafisa tayi masu a asibiti.
Murmushi nayi ina sauraren abinda suke fadi maryam ce tace ikon Allah ina laifi wanda yazo ya gaida kai gari ya gari haka.
Ni shi yasa ban daukan wanan matar a cikin masu hankali Fauziya tace wai haka kuke fama da ita da wanan bakin halin nata .
Nidai murmushin karfin hali nayi mata ba tare da nayi magana ba haka yasa suka san akwai matsala boye masu dai nake yi a hakan.
Anty amarya dake zuba abinci tace ni ai mamaki ya hana ni magana mata kamar tana jirace damu haka na dauka yanzu fa ta canza.
A wurin ku wanan yake abin mamaki inji mommy tace ni da na zauna nan da iyan bawa ai mu muka ga abu a lokacin bata da yarda ko kadan ga bakin zargi da sheri.
Ya Amina tace ai yau mun ga inda ake kishi a filin wai muna dangin mayu kuma ikon Allah bai karewa a duniya wallahi kishi haka harda na hauka.
Anty ina kika sani ai muma haka tai muna shekaran jiya da muka je gaida ita wallahi baki ga irin wullakancin da tai muna ba a gaban abokan ta.
Kamar dai yadda tai muna ke nan inji Faiza tace yau ai munga mamaki wallahi Fauziya tace ai bari ya AA din ya dawo wallahi zan fada mai idan sha,anin nafisa ya sake tashi kada ya kara neman mu a ciki.
Mommy tace ai ba, a haka ba don ta mukeyi ba don dan uwan ku muke yi yasan kuma muna mashi ai don gashi ya kira yana fadin abinda ya samay ta.
Ba gashi mun zo ba ko bamu samu taron arziki a gurin ta ba bagashi yanzun mun samu anan ba dadin auren ke nan ai da yanzu ina muka san zamu dosa idan ba khadija a gidan.
Anty Amarya tace yanzu ai na kara fahintar manufar yaya na jajirce ma karin auren shi yanzu kin ga ai zaman khadija gidan mudai yai muna rana.
Sai zuwa yamma sosai ya shigo gidan don da su niyar su su juya a ranan su koma kaduna rashin dasowan shi da wuri yasa dole su kwana.
Ya shigo muna zaune a falo ana hira bayan na dora masu girkin dare maryam tana taimaka min don kusan aikin itace mai yin shi.
Zama yayi suna gaisawa yana tambayan su gajiyan hanya da mutanen gida suka amsa da lafiya yace ashe har kun baro asibitin na buga akace min baku can.
Ai dole mu barcan yaya AA mu da bamu ko zauna ba aka tare mu da rashin mutunci da hauka a asibitin wai munzo leken asirine ba zuwan girma da arziki ne ya kawo mu ba.
Haba dai Fauziya nafa sanki da daukan zafi akan dan abu karami ina jin ya fadi haka nace uhmm na mike daga inda nake.
Bina yayi da ido ina dauke da yarinyar a hannu na taci gaba da fada mashi abinda ya faru dasu da nafisa a asibitin.
Wani irin zafi da kunyan su mommy yaji na kokarin da suke mai amma Nafisa tana gwace mai wai shi yaya zaiyi da Nafisa ne a rayuwan shi yake tambayan kanshi.
Mommy ne ta katse shi tana fadin kada wanan abin ya damay ka mudai domin Allah muka zo da kuma kai in ma tayi ne don wata manufa nata tayi karya.
Yace hakane mommy kuyi hakkuri don Allah kuyi hakkuri Nafisa bata da mutunci idan ta tashi halin ta.
Ai tayi da masu yi wallahi sai ta rena kan ta watarana a wurin mu don dai ni ba kyaleta zanyi ba wallahi kallon ta yayi ya girgiza kai.
Ya mike yana fadin barin dan shiga ciki in watsa ruwa in fito lokacin na fito daga kitchen din ina fadin akawo abinci ne yanzu.
Ya dan juyo yana fadin bari har zuwa dare yanzu hutu kawai nake so anty tace da ka dawo da wuri babangida da yau zamu juya gida.
Juyowa yayi yana fadin anty munyi magana da Abba na fada mai yayi hakkuri sai gobe ku dawo saboda yanayin hanyar yanzu.
Ya fadin haka ya fice daga dakin nima kitchen na koma wurin gurki bayan na kammala hadawa na dawo wurin su ina fadin amma zaku shiga kasuwa gobe kafin ku wuce .
Mommy tace dani bamu son dare yai muna a hanya banjin zamu shiga kasuwan nan sai anty Faiza tace mommy don Allah mu dan shiga ko a gurguje mana bamu rasa abin saye a can.
Har lokacin ban samu kebewa da yar uwata ba fita nayi zuwa wurin shi na samu baya dakin na dawo part din na samay su.
Mommy mace mai fahinta tace kuje daki khadija Amina zata baki sako acan nace to mommy tashi mukayi zuwa dakin.
Anan muka samu kebewa da ya Amina din tambayan farko data yi min shi ne Khadija haka kike fama da wanan matar haka, ?
Nace to yaya zanyi ya Amina tunda haka daddy daku kuka zabar min yi kada kice haka khadija muna taya ki da addua a kulun wallahi.
Yanzu yaya yanayin zaman naku yake a gidan nace da dama ya Amina tace komai dai yai sauki a bangaren ki dashi har yanzu ko murmushi nayi mata tare da kama hannun yarinyar dake hannuna.
Nace yayi ke nan amma a yadda na fahince shi komai a tsorace yake yin shi kamar hanyanzu ita Nafisan bata fahinci yana kawai gareni ba don yawan lafazin ta a kullun shine haks zamu zauna sai kallo a tsakanin mu.
Dan dariya tayi tana fadin wawiya ai haka yafi sauki don tana ganewa ba kyale ku zatayi ba wani shirin zata sake kuma.
Nace na fada maki yar maryam ne ta samo min taimakon da abinda tayi muna ya karye ai kila da har yanzun ba abinda ke shiga tsakanina dashi.
Tace ai naso ace ba,a taro muka zo ba da naje gidan nata nace ko yanzu zaki iya zuwa sai mu tafi da daren nan ai anty wayayiyar mace ce bazata nuna wani abu ba sai ku ce kunzo gaida ita ne.
Gaskiya ya kamata inje in mata godiya kuma in ganta don wanan matar takai wallahi nace ai sai ma kin ganta zaki san takai.
Idan munyi sallah sai mu tafi ai ba wani nisa ne sosai da mu ba ci gaba da bani shawara tayi har lokacin sallah yayi muka mike zuwa sallah.
Ina idar da sallah na dauki waya na kirashi ina sheda mai zancen fitar mu din yace kai yakamata dai in sama maki mota haka khadija barin nemo driver da zai kaiku yanzu.
Driver din yazo na fada ma su mommy ina son su dan raka Ya Amina gidan su maryam su gaisa kowan su bai ki ba suka shirya muka fito nan falo ina rufe kofan part dina muka samu su Samiha zaune gaba dayan su sai yanyaka ce dake asibiti bata gurin.
Nan suka samu ganin Ihisan suka tsaya suna tambayan lafiyan yarinyar tare da dan taba ta duk da ran buzayen bai so haka ba.
Wurin shi na haura sama na na sallamay shi na fito muka fita Fauziya ce ke fadi bayan fitar mu daga gidan take cewa yanzu khadija har yanzu wanan taron na nan maku haka a gidan nan.
Maryam tace ai ma sai abinda ya karu wallahi motan biyu ya tanadar ma fitan namu.
Mun kai gidan maryam ta riga fita taima maigadi magana ya bude kofan muka shiga da motacin mu.
Mun shiga gidan anty hauwa suna babban falon su a lokacin ganin mu tare da jamma,a yasa ta dan yin fara,a tana taron mu.
Bayan gaisawa ne maryam ta fara gabatar da su ya Amina a gurin ta dasu mommy sai da ta kalli ya Amina da kyau tace mata kanwa dai tafi ki kyau duk da akwai kama gare ku.
Dariya mukayi falon tace ma mommy amma sai nake ganin kamar na sanki a baya mommy tace ba abin mamaki bane hakan.
Kila mun taba haduwa a wani guri a can baya tace sai nake ganin kamar a federal school na maiduguri na sanki ko ?
Mommy tace kwarai kuwa don can nagama tace kwarai kuwa don nima acan na kare sai dai ban zato mate muke daku don kamar muna gaban ku da shekara daya.
Sai lokacin mommy ta tuna tace sister hauwa black jos tace kwarai kuwa nice nan suka fara hiran yaushe rabo a tsakanin su tana tambayan mommy yan kadunan da ta sani tana bata labarin su.
Maryam tace yanzun dai ashe mommy muka rako wurin sister ta sanun sannu har aka dauko hiran Nafisa nan anty hauwa je basu labarin kungiyar su nafisa din a gari .
Tace ai sai matar da bata san ciwon kanta bane take shiga wanan kungiya ko last week kafin wanan abin ya faru mun hade dasu a wani buki.
Sun ganin na gansu sai dai ba dama su shiga harkana don kar ta san kar dani dasu kuma har yanzu ina ganin basu san nasan ita khadija ba.
Tace aike khadija baki san kan wa yan nan buzaye bane don har yanzu da sauran kurciya a tare dake da sannu dai zamu kai can insha Allahu Nafisan may can don Allah.
Da ita dasu madam din aini duk a tafin hannuna nake kallon su maganin shegiya koku a gare ku dangin miji ku nuna mata idan tana iskancin ta kunsan asakin ta ai basu kaunar a tuna masu asalin na gida don yanzu sun waye.
Basu sha mamakin anty hauwa ba sai da zasu wuce ta bisu da abun arziki na irin kayan da take sayarwa nan suka mutu da mamakin ta.
Zamu fitane take fadin ida na samu lokaci tana son ganina nace to anty zan zo idan Allah yarda mukai mata godiya muka bar gidan.
Ko da muka dawo baya gidan yana asibiti wurin nafisa yaje ya dubata a lokacin tare da maryam muka dawo don tace ina da baki zata taimaka min da aiki da safe.
Suna zama ledan da taba kowa suka shiga budewa atamfofine masu kyau da tsada na mommy ne super daga ciki sai hiranta sukeyi suna yaba kirkin ta.
Daki na shiga na watsa ruwa kafin dare yayi sosai sha daya da rabi kamar kullun ya dawo daga asibitin .
Waya ya bugo min don bakin da ke akwai a shiyan nawa yana fada min in kawo mai abinci cikin shiri na fita na barsu a part din.
Ledan da ya dawo masu dashi ya bani in kai masu bayan na gama jera mai abincin na samu suna ta hira na aje masu ledan tare da fada masu sakon shi ban dade ba nayi ma maryam signal da ido na zan tafi tace mu tashi lafiya.
Ina fita ta rufe part din na samu ya gama cin abinci yana zaune saman kujera yana duban laptop din shi na shigo sai da na shiga ban daki na yi lalura na fito.
Ban tsaya ba na haye saman gadon don a gaskiya na gaji sosai ranan ban dade da kwanciya ba ya rufe laptop din ya hawo yana fadin ina ganin gobe za a sallamo nafisa don taki yarda ta zauna acan yadda suka bukata.
Allah ya kaimu lafiya nace yaci gaba da fadin don Allah Deedar abinda nake so dake shine ki kawar da idon ki akan nafisa da duk wani iya shegen da takeyi a gidan nan .
Don ita ba ciwon kanta ta sani ba bazata damu da abunda hakan zai iya haifa ma rayuwan ta ba don naga cikin bai damay ta ba.
Ni dai ina sauraren shi banyi magana ba don abinsu tsoro ma ya fara bani yanzu yace banji kinyi magana ba mana ?
Nace may zan ce yanzu kuma may zance tunda na fahinci maganan ka kamar nice mai takakan ta ba ita ba.
Yace ba haka nake nufi ba nayi maki magana ne don nasan ke zaki iya fahintar manufa akan haka idan tayi taga baki biye mata ai bari zatayi dole gyara kwanciya na nayi ina juya mashi baya.
Shiru yayi yana tunanen yanzun kuma may ye laifin shi daga fadin gaskiya nayi fushi kokatin rugumoni yakeyi na koma mai kamar dutse.
Har yai abinda zaiyi ya gama ban muda mai ba naji ya mike ya shiga bandaki ya yi wanka ya fito nima mikewa nayi zuwa bandakin na watso ruwa na wanke najasan dake jikina.
A can asibiti kuma bayan sun gama rigima da Nafisa yafito duban yanyala tayi tana fadin dole gobe ki shirya zuwa gida wurin Fatumay don karbo min sakon da aka hada min.
Yanyala ta kalleta tace gobe goben nan kallon tayi a wullakance tana fadin koba zaki je bane in nemi wani ?
Da sauri yanyala ta amsa da Allah ya kaimu don tasan kwanan wasan don ko su ba dadin ta suke ji ba kwadiyi ne kawai irin nasu da son jin dadin rayuwa.
Waya ta dauka tana kirsn madam tare da fada mata yadda suka kwashe da AA din tace idan ba kinyi da gaske ba Nafisa samad na gab da juya maki baya.
Ba komai kuma zai kawo haka ba sai yadda baki da hakkuri akan komai ke baki iya hade magana a cikin ki.
Ai na fada maki bai kamata kiyi wa yan uwanshi da kishiyoyin mahaifiyar shi haka ba namiji fa duk yadda kake ganin ka kama kafan shi idan ka taba yan uwanshi ba kyale ka zaiyi ba.
Ai duk yadda kike ganin kin kama shi kada ki yarda ki nuna yan uwan shi basu da mutunci a gurin ki don zai ji abin har cikin ranshi.
Balle Samad da hsr yanzu ba gama kamashi a hannu kikayi ba yadda kike so ni wanan mijin naki har tsoro yake bani wani lokaci mutum kamar dutse haka anayi kamar ba ayi.
Ni dai ina ganin ko zama da wanan kishiyar taki kamar dai boyon kurwa yake muna wallahi.
Nafisa tace madam kin fi kowa sanin abinda nake kashewa akan samad duk rabin samuna agurin shi akan shi yake zuwa.
Ni wanan fannin banda matsala don nasan shirin da nayi masu ai shiya nake son komawa gida kada ina nan abin yazo ya karye ya lalaba ya taushe yar iska kin san rana da hauka zan maki.
Don wanan zuman na samad sai ni nasan kan lasan abina badai wata mace tazo ta lasa man ba.
Madam tace sai ko fati ko don itama ta rigaki lasawa tace ko ta lasa ta manta kalar zakin shi don shegiya warin jaba na sakar mata bashi ba zuwa kusa da ita.
Haka sukai ta shirmay su na surkule basu san a lokacin har zuman ya fara fita kaina ba don banda jimiri a wanan fanin ko kadan yanzu don dole nake daurewa saboda hudubar mutaneba kaina ko yaushe.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Ga Allah na dogara shine mai komai mai kowa ubangiji ya sada mu da rahamomin sa masu albarka duniya da rahira.
Barkan mu da safiyan jumma ubangiji yasa muga haske a rayuwan mu ta yau da kullun.
Washe gari na samu har maryam ta gama hada abin karyawa jira kawai take ya kara sulala ta sauke na shigo.
Kitchen din na fara zuwa don jin motsinta danayi nan tana gani na ta dan sakar min murmushi tare da fadin amarya kina kamshi fa wurin gas din na nufa na fara bude tukwanen dake sama.
Kamshine da tururin abincin suka doki fuska na nace mutum haka kamar injin gurin aiki tun yaushe kika fara wanan aikin haka.
Ni ina can ina sauri in zo mu dora masu girki ashe ke kin dora ko kin koyi barci wanan aikin haka ?
Na juyo ina tambayan ta harara tayi tare da fadin saurin may kina can kinyi filo ds kirjin mijin ki kin manta da baki.
Ke dai kika sani na bata amsa tare da saurin juya maganan nace Allah kin yi saurin wanan aiki haka yanzu fa shida ke batun yi.
A wurin ku ma,aurata kikaga saurin hakan mukan ai safiya ya dade da yi ko tunda kinga har nagama aikina yanzu saura naki.
Shiga ki kintsa ki fito a fara zuba masu kafin su tashi mun gama komai dakina na shiga inda ya Amina da anty fauziya suka kwana su mommy na cikin dayan dakin da ban faye amfani dashi ba.
Suna kwance suna barci na shiga na shirya a hankali ina shirin fitowa ne ya Amina ta falka ina kwana nayi mata muka dan tsaya hira.
Maryam ta shigo dakin tana kirana na fita na samay ta a falo tana fada min tana jin hayaniya kamar Nafisa ce ta dawo.
Nace da safen nan kila dai muryan yan uwanta kika ji sai dai kuma ba abin mamaki bane don yace yau za,a sallamo ta dama.
Tace kamar mai tsoron asibiti zata dako wanan sammakon haka ta dawo gida ke ko wake son zaman asibiti idan ba dole ya kama ka ba.
Mun ci gaba da zuba abinci ba tare da mun kara bi ta kanta ba jin muryan su mommy a dakin da suka kwana suna hirane yasa nasan sun tashi.
Dakin na shiga da sallamana suka karba min cikin zubo idon su a kofan dakin fuskokin su a sake tare da fadin khadija kun tashi nace eh mommy ina kaiwa kasa tare da fadin ina kwanan ku mommy ?
Lafiya ya gajiyan da dauwai niya mun kawo maku bakun tan na bazata anty amarya ne ta dan dago daga inda take kwance tana fadin wallahi fa.
Sannu da kokari kinji ina murmushi na mike daga tsugunin da nake nace mommy kuyi wanka abinci na falo.
Kin gani ba haka muke so Alhamdullahi gida ya gyaru yanzu tunda mutun zai zo ya samu tarbo haka ke da ki kara hakkuri don yanzu kishi ko wani iri yin shi zata yi na fili dana boye Alkah dai ya dada kare muna ku.
A raina na amsa da amin na mike zuwa ban dakin wanko masu shi na yi tare da kunna masu ruwan zafi na fito har lokacin magana sukeyi akan gidan ban tsaya na fito daga dakin.
Can na koma dakin kwana na na wanke ban dakin yadda zasuji dadin yin wanka a cikin sa duk da shima ba wani ddatin da yayi.
Muna falo na ce da maryam barin leka shi idan ya tashi in gani na fice daga dakin ina zuwa falo na samu buzaye mazan su da matan su sun saka nafisa a tsakiya.
Nace a, a ashe kin dawo sannu da dawowa ya jikin idan ke dake nesa kin karba min nafisa ta karba min ban tsaya ba nai murmushi ina haurawa sama naji tace Allah waddai cusa kai babu kwarjini.
Sanin muna da baki a gidan yasa ban tsaya ta kanta ba na haye sama abina kofan dakin shi na tura naji kofan a rufe na dan murda shiru.
Harna juya zan fito ina tsanmani ya fita daga dakin naya na sai naji ana murda kofan dakin shine ya bude tare da fadin waye fuskan shi a daure.
Ganina yasa naga ya koma yana bude kofan na mara mai baya zuwa cikin dakin ina shiga yake fadin marasa hankalin na rufe na kofa.
Ina kwance sai ga Samiha min a daki wai Nafisace ta turo ta karban abu wurina ban bashi amsan maganan shi sai kokarin fadin da nakeyi kayi wanka ne ko in hada ma ruwa ?
Banyi ba yanzun dai nake shirin yi danaga baki dawo ba don kwance nake tun dazu na gane may yake nufi amma na basar dashi kamar ban gane may yake nufi ba.
Nagama abinda zan mai na fito daga dakin daya shiga wanka har lojacin suna nan a inda na barsu zaune din.
Ban kula su ba na shige part dina a falo na samu bakina sun fito maryam ta na gabatar masu da abin kari.
Mun zauna ana karyawa ana hira ne ya shigo a cikin shirin fita yana gaida su mommy din da yaya Amina dake mai sarakuta.
Tambayan shi mai jiki mommy tayi yace ai ta dawo da safen nan Anty amarya tace har an sallamo tane yace tadai sallamo kanta dai.
Ikon Allah duk shiru sukayi falon suna mamaki sai Fauziya ne tace wai ko yayan mu Nafisa nada hankali murmushi yayi yana mikewa daga inda yake tare da fadin tana da shi mana tsaban wautane mata.
Da kuma zafin kishi inji Faiza ta badi tana kama yar ta dawowan gida mai zatayi banda zaman saka ido da fitina kana ma kokari wallahi.
Kallin ta ya danyi ya kawar da kai zuwa gareni ban ko dago na kallesu ba ina dan shan tea dake gaba na a hankali.
Zan fita in dawo Allah ya tsare nace dashi tare da kawar da kaina gefe daya akan tea dina bayan ya fita ne suka sa topic din Nafisa a dakin.
Fauziya da Faiza sukace ba zasu gaida ita ba don sai sun nuna mata ba kowa take ba yanzun kan basu shayin rama komai zatai masu.
Maryam nabi a daki nazauna a wurin ta a nan ya Amina ta samay mu sai lokacin nake nuna mata kayan da ya sayo min na lefe fita tayi da kayan falo wurin su mommy tana nuna masu.
Nan suka shiga kallon kayan tare da yaba kyauwon su ashe mu kallon tsoro mukaiwa kayan sai yau muka fahinci may ke cikin akwatunan.
Mommy ne ta jawo sarka da awarwaro na zinare har kala uku da wasu set din agoggaya masu masifan kyau kala uku suma kallon juna mukayi da maryam din na sada kaina kasa .
Su mommy ne bayan sun gama kallon kayan sun sa albarka suka fita waje gaida Nafisa da dawowa basu jima ba suka dawo dakin.
Basu ko zauna ba Faiza ke tambayan su idan nafisa ta amsa masu gaiuwa dariya ne ya dan kamani alokacin haka na kumay shi ba hali in fitar aji.
Haka dai har suka shirya tare da maryam su Faiza da fauziya da Anty amarya suka shiga kasuwa suka barni da su mommy da ya Amina a gida.
Bayan fitar su ne mommy ta fara magana tace dama naki binsu ne don mu samu kyabewa dake Khadija da sauri na dago kai ina kallon mommy din.
Tace khadija nasan irin zaman hakkurin da kike da wanan matan don haka ki kara ga wanda kike dashi kada ki yarda daidai da rana taya ta gane kin karaya da alamarin ta.
Don ta haka zata gano takon ki a gidan nan ki zama jarumar mace a gidan ta kamar sauran jarumai matan da suka sha gwalgwalmaya a gidajen auren su kafin su tsaya a kafan su.
Sannu a hankali idan kinyi hakkuri kuma kikaci gaba da wanan dabiar take zaki cin ma nasaran ki da yardan Allah.
Sai dai abin ne dakamar wuya don akwai tafiya amma sai dai kamar gobe a wurin Allah in dai da rayuwa .
Ba wanda ya tsamani zaki samu sauki a wurin mijin ku haka sai gashi Allah da ikon shi na fahinci biyayyan ki gare shi ya jawo maki mutunci da kima a idon shi.
Bawai kwanciyar aure bane kawai jin dadin aure a, a har da yi nayi bari na bari da gyara da hakkuri da rayuwa ga abokan zama.
Ni a fahintar Nafisa danayi ta ta,allakane kawai da kwanciyar aure a tsakan su ba wai ta damu da kula da rayuwan miji bane.
Shi namiji kana sace zuciyar shi ta fanni daban daban irin kyautatawa da kulawa a gareshi da nuna damuwar ki nasan duk kin san da wa yan nan abubuwa amma sakaci dashi da wasu mata a yanzu sukeyi ne ke yawan jawo masu matsala a gidajen su.
Kinga kamar fati ansan akwai asiri amma asiri ya cin ma hali dama don ko banza haka take kamar dutse babu marmari a tare da ita.
Yanzu daman ki ne khadija da zaki nuna naki bajin ta ga kowa na babangida asan ba auren banza ya kara ba.
Ko wace mace dama da dalilin auro a gidan mijin ta amma dan akasi kadan zai iya bata ta ga kowa ba wai ga mijin shi kadai ba kadai ba a, a har ga kowa dake tare dashi.
Don Allah khadija kin dai ga kannen mijin ki a tsatsaye suke ko gare mu matan uban su wani lokaci sai mun hada da hakkuri da su.
Haka ke ma nake mai jan kunnen ki a kansu kada ki yarda ki samu matsala dasu ta ko wani fanni na zamantakewar ku dasu don Allah.
Ko dan zaman nan da mukayi tsakanin jiya da yau ya kamata ki fahinci wani abu daga gare su irin halaiyan su da sauran kalaman su zuwa ga nafisa.
To ke sai kiyi amfani da wanan damar ki toshe wanan kafar da ta sake daman ta a gare su ki gyara ta yadda zai zama kin kawar da duk wani shakku na gidan nan a zuciyar su.
Ina fada maki hakane don daukar ki danayi tankar yar uwata ta jini don albarkacin Amina gata nan shawaran Amina har gobe baya wuce ni da kika ganmu nan .
Haka nima nawa bai wuce ta a haka muke zaune muna rufawa kan su asiri ga matsolalin mu .
Akwai canji kwarai da aka samu a gidan nan ta dalilin ki ne kuma sai ki daure ki rungumi Allah da mijin ki banda yawan fushi kan abinda bai kai ya kawo ba a dauke shi da zafi.
Har yar uwar zama ta fahinci kuna da matsala da mijin ki taji dadi ko a bainan jamma, a yai maki abinda ba daidai ba kada ki yarda ki nuna har mutane su gane hakan gare ki.
Ajiyan zuciya na sauke bayan ta kare maganan ta da fadin Allah yai muna jagora ya shige muna gaba da amin.
Nace mommy na gode in sha Allahu zan kiyayye da yarda Allah ya Amina ne ta karbe da fadin don Allah khadi kiyi amfani da maganganun da mutane suke fada maki ko da yaushe ki jajirce a gidan nan ki mai da komai ba komai ba .
Dawowan su Anty amarya yayi daidai da isowan shi gidan ya dawo ya sallamay shi sai da yasa aka cika masu bayan motar su da tsaraba sukai muna sallama suka tafi.
Bayan tafiyan su ne ya dan shigo bai zauna ba saman dakin shi ya shiga bai dade ba ya fito su nafisa na zaune a falon ya dan tsaya da ita yai magana daga nan ya shigo part dina ya samay mu.
Ina gyaran wuri ya gaida maryam dake kitchen tana wanke kayan da mukai amfani dasu ga bakin mu yace dani ya kamata a samo mai taimaka maki da aikin nan haka.
Nace zan sa hajiya mama ta duba min a kaduna idan za a samu a turo min yace ba zaki magana a samo maki a gida ba.
Fuska na ya mutsa nace mai zan dai fi so a kadunan don can gaskiya ban san wata wace za,a dauko min ba yanzu kan.
Ok zan mata magana muji ko akwai wace za,a turo maki din ni ni zan koma office sai yamma idan na dawo.
Allah ya tsare a dawo lafiya nace mai yanzun na dan sasauta daure fuskan da nake mai kwana biyu a gidan.
Na jin zafin abinda yai min ajan nafisa don ni jin zafina shine bai kulani ba kamar ba mutunce ya bari a daki ya fita ba.
Sai kuma fadan da yai min don may na fita school a ranan duk da na fada mai a motar gida na fita kuma yake ganin laifina dayin hakan.
Bayan mun gama komai ne mun zauna da maryam muka danyi hira har barci mukayi after four tace zata koma school ban so ba sai dai ba yadda zan yi da ita don dole ta koma din.
Bayan tafiyan marya sai naji zaman ba dadi ban kuryan daki ban falo a karshe dai na dawo falo na zauna da takarduna ina dubawa a hankali.
Lokacin aiyukane amma sanin cewa ba nice da girki ba sai ban damu da in aiwatar da komai a gidan ba don ba hurmi na bane yin hakan yau.
Waya na dake gefena yai kara na dauka ya Amina ce ke kirana na dauka take fada min bayan mun gaisa wai sun isa tun dazu yanzun take shigowa gida.
Nace sannun ku da hanya su boy dai nasan sai zuwa gobe za a dauko su ko tace nace a kawo min su yau don gidan yai shiru basu.
Nace wallahi haka nake fama da kadaici yanzun haka dazun nan ma bayan wucewar ku yake min maganan ai in samo mai aiki da zata debe min kewa.
Ni kuma nace ba wadda zan samo sai dai yaima hajiya mama ko mommy su sama muna tace kina ganin a dauko maki wata ta fanin su zaifi.
Nace ni haka nake gani anty don kin ga irin korafin da akeyi akan nafisa da yan uwan ta a gidan ko yaushe to sai kuma ni inje in dauko nawa in kawo gidan anty ?
Ke diban hauka zakiyi irin nata ai ba zai wuce mutum biyo ko uku ba ko nace wai anty na kaisu ina data ma ta isheni ai ya Amina ina zan kai har mutum uku haka anan.
Tace yanzun dai zamu tatauna da mommy muji inda ya dace a sama maki din amma ai ko can gida ba za a rasa irin yan kauyen Doko din nan ba masu neman aiki.
Munyi sallama da ita na kashe wayan tare da tunane a raina mikewa nahi na shiga daga ciki don in watsa ruwa kafin lokacin sallah yayi.
Misalin takwas ya karaso gidan nan falo ya samu nafisa da iyalan ta zaune tana waya gaida shi suka danyi bawani cikin kulawa ba.
Kare wayan tayi tana dago kai gare shi yace da ita ya jikin naki tace da sauki tana kokarin mike kafar ta a kan dan stol dake gaban ta.
Bai tsaya ba yace barin shiga daga ciki in watsa ruwa ya sa kai ya fara tafiya ta kira sunan shi da fadin Samad ya juyo yana kallon ta.
Tace banji kayi min maganan kudin dana tambaye ka ba dazun da zaka fita yai mata wani irin kallo tare da sauke nauyayan ajiyan zuciya.
Cikin bacin rai ya dan runtse idon shi na dan dakikoki sannan ya bude tare da kallon su gaba daya da yan uwan ta yace.
Nafisa na sha fada maki ban son irin wanan dabiar da kike min ke wai kullun baki da zance ga mutum sai na maganar kudi shi kudin nan ko ginar shi mutum ke yi ai yana wahala gurin gina ko ?
Tace idan ban tambayeka ba wa kake son in tambaya ya bani in yi lalurar gabana dashi yace saboda ke baki da wayau ko ya watsa mata hara ya barta gurin.
Har ya shiga wanka yana tunane a ransa alamarin Nafisa yana daure mashi kai ya rasa abinda take yawan yi da kudi haka don kullun cikin jero mashi lalurar kudi take a gidan.
Babu abinda ke cikin zuciyar ta sai zancen kudi bata san ta sauke hakkin ta na aure ba gare shi.
Duk kokarin da yake yi a kanta da yan uwanta a gidan ya lura Nafisa bata ganin haka may ye amfanin bata kudin matar da batasan kimar shi ba.
Ganin alamarin nason damun shi a rai yayi gagawan cire tunanen ta a ran shi ya watsa ruwa agurguje ya fito bai tsaya dogon shiri ba ya nufo part dina don ganin halin da yake ciki don baiji motsina ba a gidan.
Kai tsaye da ya fito part dina ya nufa nafisa da ke zaune tabishi da mayattacen kallo cike da jin hayshin shi da zargi a fuskanta.
Shigowa yayi lokacin ina falo zaune a kasa tv na aiki ga cup din tea da cake a gefe ina rike da takarduna ina assignment.
Kaina na dago ina kallon shi tare da mashi sannu da zuwa ya samu wuri ya zauna tare da fadin dauko min abinci in ci anan.
Kallon shi nayi cikin mamaki nace ba nan kake ba yau ai shiyasa banyi girki ba yace kenan baki girka komai ba ?
Nace cikin girgiza kaina gaskiya banyi komai ba yanzun ma tea na dan hada kada in kwana da yunwa a cikina.
Yace amma kin san dai nafisa jinya take yi ko don haka ba hujja ba ne kice baki girka min abinci ba inba ba, a nan zaci ba ke cikin ki bazaki ci bane ?
Najira ya gama fada in fada mashi dalili na na kin yin girki danayi don yin zai kawo wani fitina tunda dai ita batace ba zata iya yin girki din ba saida ya gama.
Nace ina gujewa abinda zai haifar da wani fitina ne agidan nan tunda ba ita tace ba zata iya hidima da kai ba kuma ni naga ni kadaice yau shiyasa ban girka komai ba tea din ma zai isheni in kwanta ai.
Yar gurin Nafisa ce ta shigo babu sallama ya daka mata tsawa yace ta koma tayi sallama kafin fa shigo.
Ta koma baya sai taiyi sallama ta shigo tace maman su na kirnshi a falo yace yaji koda ta fita ya dan dade zaune a gurin yai waya yana bada sakon abinda za a sawo mai yaci.
Ya mike tare da fadin ina zuwa yana fitowa ya samay ta tacika fam tana jiran shi a gaban yan uwanta ta haushi da fada.
Akan may zai tafi dakina bayan banice da girki ba ita bata son cin amana don an raina mata zai zo gabanta gaban kowa ya shige dakina ya zauna.
Nafisa wai may kika dauki kanki bazan shiga dakin matana ba don kina zaune ko may ina mutanen da kike fadi a gaban su na shige.
Take taji zafin zancen shi don wata ita da yan uwanta ya raina ma hankali yake fadin ina mutanen da zaiji nauyin su.
Tace to barin fada maka in ma mayaudariyar bata fada ma yau nice da girki a gidan nan kaima ka sani don haka banga dalikin shiga dakin ta ba yanzu.
Wai ke kina da hankali kuwa banda shi kamar yadda ke kirana kullun mara hankali sai kai min yace ta yaya za a sallamo ki daga asibiti yau kan lalura kuma likita ya fada maki dokokin da zaki tsare kice wai zakiyi wani girki can a gidan nan.
Dama nasan hada baki kayi da likita ya fada min haka don ka samu damar kebewa da matar ka kun mai dani bi can ko ?
Idan mun hada baki da likita ya fada maki haka hada baki nayi dashi jini ya zubo maki sai tace mai waya sani ma ko hakanen.
Wai kaima baka da zuciya ne may kake tsunta wurin wanan yarinyar daka rasa a wurina bada taya ka kwanan banza da takeyi kullun.
Amma banga laifin ka ba don kayi haka tunda dole ka rarashe ta kada asirin ka ya tono ta gane kai mace ne a gurin ta.
Yace eh lallai Nafisa na yarda yau tunda kin fada da bakin ki ashe kin san sherin da kikayi a haka tace banyi komai ba amma nasan hakane ma.
Idan taya ni kwana takeyi ya zama laifi ne tayi kokari tunda tasan hakkina a kanta ta taimaka min.
Yau dai ba inda zaka tafi ta rike taimakonta an yafe don mai abu ta dawo yanzu ke don Allah ban iya shirmay ki kullun fada a kan abu daya.
Yarinyar nan bata ko san kina wanan haukan ba don ita tana da hankali tafiki kaifin tunane tace don ta fini iya kissa ba.
Ciki dai ne tare dakai mukayi kuma tare zamu raine shi a gidan nan kaji na fada ma ga inda iyalin ka suke suna bukatan taimakon ka zaka shige wurin mara moriya.
Juyawa yayu ya wuce ya barta na baiyi nisa ga tafiyan shi ba mai sakon shi yayi sallama dauke da sako a hannun sa ya karba ya aje masu leda daya ya wuce da sauran part dina.
Bata fasa fada ba dashi tana saman bakin ta yashi ya mika mun keda yana fadin gyara min daya in ci .
Yanzun dai kaima kaji dai da kunnen ka ji da kunnuwan ka abinda nake fada ma yanzu waya ta buga mai yai ta ringing yaji dauka sai cin naman shi yake yi ya kyale wayan yana ta ruri a gefen shi.
ZAINAN IDRIS MAKAWA
SEENABu
1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Ni dai suna cikin rikicin su n rufo kofan part dina na barsu can suna yi barci nayi ranan sosai saboda dan nauyin mutane dana sha kwana biyu.
Ban samu zuwa gidan anty hauwa ba sai da aka kwana hudu don jigilan karatu da nake fama dashi gashi yanzu girki da nawa da ba nawa ba duk ya zama min dole inyi saboda a part dina yake cin abinci.
Duk da Nafisa tana zaune a gida tana bedrest amma haka bai hanata aiwatar da sherin ta na sheri kamar yadda ta saba akan maigidan da ni.
Burin ta kullun shine ta wayi gari taga ta daina gani na acikin gidan gz baki daya don haka ne kawai take gani samun kwanciyan hankalin ta da ta rasa.
Yanyala ta isa lafiya a cikin kwana biyu da tayi a gida mai ma nafisa aiki ya gama hada masu surukulen da zai bata ta kawo wa Nafisa din inda ya jadda mata zasu ga haske sosai ga aikin su .
Bata kara kwana kauyen ba ta shigo mota ta juyo Nigeria cike da gajiya da bautar uwar gijiyan nata.
Bata iso abuja ba sai washe gari bayan ta sha bakar wahala a hanya ta iso gidan a gajiye da ita.
Ina kofar gida na shirya zan tafi gidan anty hauwa naga isowar ta alaman rashin gaskiya karara a tare da ita nikan kallo daya nai mata naji gabana ya fadi.
Lah, illaha illah, anta subbahanaka inni kuntun minal zalumin, na fadi.
Ta gwautani kamar mara gaskiya da ita ta shige na bita da kallo ta gefen ido sai kamay kamay take yi.
Driver yana jirana mu tafi na bude mota na shiga har mun danyi nisa da gida sai na tuna ban dauki tsaraban da na sayawa anty hauwa ba.
Nace ya juya nayi mantuwa a gidan ya juya kan motar muka koma gida na fita don in dauko tsaraban.
Suna falo zaune yadda na barsu sai yanyala dake ta fitar da maganunuwa daga cikin jakka ta tana ma nafisa baya su .
Daidai ta daga wani farin kwalba da ruwa a ciki sa fari tana mika ma Nafisan na shigo falon gaba dayan su sai da suka razana da ganina a wanan lokacin.
Ban bi ta kan su ba na bude part dina na shiga na dauki abin da zan dauka na fito ina rufe kofan ina karanta addunan neman tsari da kariya a wurin Allah.
Na sake ficewa ba tare da na kula suba na samu driver muka wuce har lokacin gaba na bai bar faduwa ba har muka isa gidan anty hauwa da ba wani nisa don a unguwa daya muke dasu sai dai akwai dan jayawa kadan.
Na samu bata nan sai yar ta da tazo hutu daga saudiya da muka zauna da ita muna hira dama mun saba tun a waya da ita idan maryam ta kira ta takan bani mu gaisa da haka har muka saba din da ita.
Sosai muke jin dadin hiran mu wanda ba wani hira bane sai na yanayin karatun nan kasar mu da inda take karatu a saudiya.
Mahaifiyar ta da ta buga ma waya ta sheda mata zuwa na ne ta dawo da fara,anta a fuska take taro na har kasa nakai ina gaida ita zuwa tayi inda nake tana fadin.
Kai haba khadija zauna mana ke fa yanzu ba bakuwar gidan nan bace don gashi ma yanzu naji mamakin ganin wanan mai kama da kura ta sake jiki dake haka har kuna dariya.
Hummaira tace lah mami na san anty khadija fa tun a waya mukan gaisa da ita time to time har zancen auren ta na sani.
Ledan da na shigo dashi ne na mika ma anty a cikin ladani ina fadin ga dan tsaraba nan ba yawa na riko maki anty.
Karban ledan tayi tana budewa da sauri ta dago kai tana fadin kai kai kai khadija wanan tsaraban manya haka duk ani daya.
Gaskiya wanan ba abin fitarwa bane kowa ya gani wanan sai idan na shiga daki ni kadai hummaira dake kallon uwar nata tace mami idan naji kin fadi haka rowa kike son muna.
Anty khadija may kika kawo ma mami take kokarin yi min rowa ta mike zuwa wurin uwar sai ta dauke ledan ta boye nan suka kama yar boya da uwar.
Sun bani sha,awa sosai yadda sukeyi da uwar nata kamar kawayen juna karshe dai sai ta bude ledan hummaira nagani ta fada jikin uwar tana murna tare da fadin.
Wai mami ashe da rabon zanci wanan abin tambayar yar tayi may ye sunan abin ina kallon su ina dariya daga inda nake zaune.
Juyowa anty tayi inda nake tana fadin khadija fada mata sunan shi murmusawa nayi ina fadin kilishi wanan anty ba na nan bane a kebbi na aika aka sawo min don yafi dadi.
Kai bari mu dana muji tace tana bude ledan ta balla kadan ta mika ma hummaira din wai anty tace bayan ta gutsura ta tauna tace wanan wani gari ake yin sa don Allah nace wata course mate din mu ce take sawo shi mijin ta dan can ne wai kilishin gwandu.
Gaskiya wanan yaci sunan sa ainihin kilishi irin na da wanda muka sani ke nan sallaman maryam mukaji muka amsa anty tana kokarin boye ledan a bayan ta don ganin shigowar maryam din.
Nace anty ai ba sai kin boye ba don na dibar mata nata jiya da aka kawo min shi wanan naki ne na kawo maki.
Zama maryam din tayi kusa da ita suka sa ta a tsakiya nan suka far ma kilishin da ci maryam ne take fadin ta buzuwa ashe kin samu shigowa din.
Hararan ta nayi nace ba buzuwa buzaye anty tace kin ga na manta wanan yar kwadan ta cika ni da surutun banza wai ya kuke a gidan.
Murmushi nayi tare da fadin muna nan dai anty humamaira ne ta mike tana fadin mami kawo ledan in kai maki daki boye ledan tayi a karshinta tare da cewa sai mun raba na dibarwa daddyn ku nasa kin san yana son shi sosai shima.
Hummaira ta shige a shagwabe uwar ta juyo gare ni tana fadin kedai ina jinki kanwata nace suna can yanzu ma nabarsu kamar kullun nan nake labarta masu abinda na gani yanzu kafin in fito.
Tace ai indai wa yan nan ne aikin su ke nan ba fasawa zasuyi ba ko basu cin riba ke dai dama abinda yasa nake neman ba wani abu bane sai in kara fada maki ki kula sosai.
Ina son ki kuma classic lady sosai khadija kin ga kwalliyan nan yana daukan hankali maza sosai tundai irin mazan nan naku da suke yara ga kuma sanadarin a hannun su, shine kudi.
Ki dage sosai kada ki ji kiuyan komai ki dinga masa abincin da yafi so kina daurewa a gurin shimfida kinuna mai cewa ke ma gwanace ta wanan famnin har kin fishi iyawa.
Dariya maryam tayi tare da fadin Allah yasa anty wanan kamar kifin rijiya take fa ba abinda ban fada mata ba.
Wanan kuma wani abune dake kara haska kwarjin mace ga miji khadija shiyasa zaki ga wasu mata ba kyaune dasu ba amma miji yanaji dasu kamar ya lashe a gida.
Kin san fa maza su a wanan fannin basu da wasa ko ita buxuwan ai da wanan abin take samun galabarshi ba komai ba.
Don idan ba kin tsaya wasa ba ai duk inda wata buzuwa zata tsaya khadija zaki iya tsayawa may ake so gun mace gyara da wayewa yanzu duk kina dasu sai lafabin aure wanda nasan ko rantsuwa nayi bani kaffaran haka.
Kin fi wanan buzuwa ladabin aure a gare shi So kina da dama da zakiyi amfani da naki baiwan wurin gwada mata ita ba komai bace a idon ki .
Idan har kin rike wanan abin dana fada maki babban makamin ki ya zamo Allah shi zaki sa a gaba ya taimaka maki akan komai da zakiyi.
Wallahi khadija ni na fada maki zakiji buzuwan nan tadawo tana fadin kin kwace mata miji ne da asiri ko wani abu.
Yanzu akwai wata kawata yar libiya ce matar zan turaku wurin ta zata baki training akan komai na rayuwa na riga da na mata magana akan matsalan ki.
Don haka ki daure ki dan yi sequzy din kan ki ki rage lokacin don ki samu ganawa da ita a kullun just three week ko four kawai ya isa ki haddace komai da kike so.
Zan shiga dubai zan hado maki duk wani abinda zaki bukata maryam tace akwai wasu kayan lates da mijin ta ya sawo mata a matsayin kayan lefe.
Tace ok ku kwaso mu bada dinkun nan su a modern design suyi maki express masu kyau na gani na fada najan ra,ayi .
Ki gani idan baki haukata wanan buzuwan da makarabanta ba suma su madam din ai ba don Allah suke tare da ita ba .
Abin hannun ta da mijin ku, ke sake mata ne suke gwadayi a wurin ta dan bata san ciwon kanta ba sam.
Yanzu abinda nake kara son ki dashi shine ki koyi dabara ta tanadin abinda kike samu daga gare shi ta yadda ke ma zaki iya gina kan ki ki zauna a kafan ki, ki kafu.
Shawara mai amfani ranan tayi min sosai wanda ni ban kawo wutan yin shi ba a raina nace ashe magani ne a gonar yaro ba sai nabi wani hanya ba can nike da maganin a tare dani.
Sai da nayi sallah la,asar a gidan tasa drivern su ya kaini gida tare da maryam muka fito zuwa gidan namu.
Mun samu su madam a gidan ana shewa da hayaniya an barbaje ana ciye ciye maryam na biye dani a bayana muna tafe muna hira.
Zan taka falon naji gabana ya fadi addua nayi saurin kawowa a bakina da sallama mara sauti na shiga sai dana karanto adduan .
Alama nagani daga na garin magani a kofan shiga part din da sauri na rike maryam ina mata nuni da abinda na gani idanuwa suka watso muna suna Allah Allah in taka abin da aka barbada din.
Sai sukaga naja na tsaya fita mukayi da maryam din a waje muka tsaya muna shawaran abin yi maryam ce ta kawo shawaran may zai hana mu shiga makwabtan mu muyi fitsari mu zuba.
Dariya ta bani nace kina ganin haka zai yuyu tace ba ance yana kara asiri ba nace ban fa taba shiga gidan kowa ba anan maryam asalima ba wanda ya sanmu.
Yanzu dai bari ki gani ashe suna leken mu maryam ne ta gansu take fada min adduan neman tsari na karanto naji gabana ya daina faduwa shiga muka sakeyi main kitchen din gidan na nufa na dako tsintsiya da mofa suna kallo na share abin maryam na zuba ruwa.
Muka bude part din muka shiga muna shiga maryam tace wai Allah ya somu yau khadija kina da kula wallahi da nice ai afkawa zanyi hakana batare dana halkanta ba.
Nace maryam kullun ido akan komai yake a gidan nan bakina kuma bai daina karanto addua don sanin halin wace muke zaune da ita.
Idan naji gabana yana yawan faduwa maryam tun ina gidan mu nai nitice din haka wani abune mara kyau ke shirin faruwa dani.
Kin san ance ko wani mutum yana da sing din shi na gane abu kula da hakan ne kawai mutane basu yi.
Amma yanzu kin ji zuciyana wasai nake jin shi alaman abin ya gushe ke nan a gare ni Allah ya tsare ya kare maryam tace nace amin.
Madam ta fara magana a falon bayan shigan mu wurina tace Nafisa anya wanan kishiyar taki ita kadaine kuwa.
Ko dai tana da aljannun da ke nuna mata abune haka ji yarinyar nan yanzu abinda tai muna fa ta nuna muna ta gane may mukayi mata.
Kin manta ne madam jikar mayune fa tana ganin har hanji banyi mamakin haka ba don dama malam ya fada muna haka kin manta ne ?
Idan tasan wata ai bata san wata ba don wanan da zan saka a kasan gadon dakin shi yafi zama shu,umi a gare su don ko ta mutu ko hauka kota kwanta ciwon da ba magani.
Ina da tabbacin sosai ga wanan aikin yanzu shigar su kawai nake jira dakin su kwanta da ta kwanta shegiya sai buxunta ba ita ba.
Bayan mun hutane nacewa maryam ta dora min girki zan tafi dakin shi in dan gyara na fito ina saye a cikin dogon rika na zaman gida.
Na daura dan kwalin rigar a kaina rigar free ce don shan iska akayi shi baida wani nauyi sosai.
Na tura kofan da sallama na nashiga dakin nabi da kallo a hankali gadon dakin naga alaman an daga take sai gabana ya harba min dammm.
Wurin na nufa kamar wace ake turawa sai kawai na daga gadon na shiga dubawa abubuwa ne ba zaka gane akwaisu ba a dakin an nade a cikin farin leda a ka cusa can; daga gefe daya.
Ban dakin na shiga nayo fitsari na zuba mai na sharo abin sai dai ban zubar ba na aje a cikon dusbin sai ya dawo in tambaye shi idan ba nasa bane.
Na gyaro dakin ko ina na rufo mai na fito basu falon a lokacin har na koma part dina na samu maryam tayi nisa ga aikin da take min.
Bata tafi ba sai da mukai sallah magariba ta dauki kayan da zata kaiwa anty ta tafi ya saura ni kadaice a part din .
Na dade a gurin zaune ina tunanen kalaman anty a raina lalai ya zama dole gare ni na gyara komai nawa kamar yadda anty tace min ga magani a gonar yaro baisan kan sa ba ke nan.
Shigowan shi ke nan ya nufi gurin nafisa ya dubata yayo dakina daga can daga ida nake zaune a kasa saman center carpet na mike kafafuwa.
Jin an turo kofan ne yasani daga kai na kalle shi sannu da zuwa nai mai tare da fadin ka dawo ?
Na dawo khadija yau ban tsaya kusa ba munyi balaguro ne zuwa keffi acan muka bata lokacin mu yanzu sai wanka ke nan tunda ka kwaso wanan gajiya.
Kinyi tunane mai kyau gaskiya barin dan watsa ruwa in fito kafin nan nasan abinci na ya kammala.
Insha Allahu na bashi amsa ina kokarin mikewa daga inda nake zaune dukawa yayi ya debi corn din danake ci a gefe na.
Har ya kai kofa ya juyo yana fadin hajiyan mu tace a fada maki za a kawo lefen zainab a karshen satin nan insha Allahu.
Da murna na dago ina fadin masha Allah gaskiya nayi murnan jin hakan wallahi ashe zainab ta kusa bin layin mu bada jimawa tunda har lefe zaizo.
Baki ya tabe mi yace kinji dadi ke nan za ai mata yadda akai maki koda yake kawaye kuke waya sani ko matsin ku yasa akai maku hakama.
Wani kallo na watsa mai tare da fadin kana da gaskiyan ka tunda ka tauye ni.
Dariya ya wuce yanayi har ya fita kitchen na shiga na hada mai abincin shi na tsaya na gyara komai yadda ya kamata in yi na fita zuwa wurin shi.
Sai da na aje abincin na shiga daki wurin shi tsaye na samay shi yana juya kwalban da wasu abubuwan da na tsinto a karkashin gadon shi.
Yana ganin na shigo ya juyo gare ni yana fadin wanan may ye kuma haka Deedar ?
A karkashin gadon ka na jawo shi dazu nan dai na fada mai yadda akayi tun dawowana gidan ni da maryam.
Kai kai yace yana zama saman gadon tare da fadin wanan abin wai da may yayi kama haka nace waya kawo shi nan to ?
Yace wa zai kawo kuwa banda daya daga cikin ku tunda daga ni sai kune keda alhakin bude dakin nan yanzu.
Allah ya kyauta nace na dago ina fadin kayi wankan ne yace shi zan shiga ai naga wanan abin a kofa nace nina aje don kazo ka gani da idon ka.
Ya juya ya samu leda ya saka tare da adana abin jirani in fito dakin ki zamu koma sai nayi bincike akan wanan abin.
Yana shiga ban dakin ban zauna a gadon ba na juya inda na hada kayan abincin dana shigo mai dasu a cikin basket.
Ya fito a gurguje ya shirya muka bar dakin zuwa nawa ranan a can muka kwana wanda ina jin dadin hakan don ina sakewa sosai idan yana dakin nawa.
Asuban farko dukan kofan nafisa ne ya falkar damu cikin sababi take fadin iya shegen da kake yi a gidan nan yayi yawa.
Samad kaine ma mai biyo mace dakin ta ka kwana yana son fita na girgiza mai kai nace dashi kyale ta please.
Ya koma ya kwanta sai da akai kiran sallah muka tashi a dakin shima yayi sallah bai fito daga dakin ba sai bakwai da rabi.
Ashe tana falo zaune zaman jiran shi yana fitowa ta fara mai ihu da sowa wai yaji kunya gotaigotai dashi yana bin karamar yarinya dakin ta yana kwana.
Nafisa kina da hankali kuwa ke ba dakin ki nake binki ba yanzu tace idan ka bini ai da amfanina ko dan yanzu da nake cikin wanan halin.
Ita bata da amfanine gareni tace ina taga amfani banda ci takai masai mai take tsinana maka kai nafa san komai na fada ma duk wanan rufa rufan da kakeyi nasani.
Ashe dai har yanzu ke nan labe kike muna kenan tunda har kin san haka gashi yanzu ma alama ya nuna kan shi tunda har kin san a dakin ta nake kwance.
Na sani samad don na damu dakai ne nake haka yace ban saki damuwa dani ba tunda kin san bake kadai ke dani ba.
Wallahi baka isa ba samad sai ka dawo kana fadi da bakin ka a tsakar gidan nan ka kwaso mai farar kafa mara moriya a gare ka.
Yace ban yi mamaki ba don kin san sheri da kika kula zaki ko sha kunya a gidan nan wallahi don babu ida zata tafi.
Banyi mamaki ba don jikar mayu ka aura ta kama ma kurwa baka ganin laifinta a yanzu do an gama dakai ko.
Yace ke mahaukaciya ce kula ki ma hasara ne kiji da hakin da kike ciki zai fi maki alheri sakarai kawai ya shige .
Cikin daga murya take fadin zaka gane baka da wayau samda karka manta a tadin hannuna kake wallahi bai kula ta ba ya shige abinshi ya barta a wurin.
Ranshi a bace har ya karasa shirin shi ya zo ya karya bai kara bi ta kanta ba don ya gane idan ya biye mata zasu sai da haline kawai a gurin.
Koda muka fito yau a tare muka jero dashi don fita zuwa school shi kuma zai shige office abinsa nafisa da tawagan ta suna zaune falon nan ta dasa sabon balai kamar yadda bai kulata ba ni haka nazo cikin shiri na wuce su a inda suke zaune suna banbami.
Tunda muka shiga motar takaici da haushin tozarcin da tai mai ya hana shi magana nima ban bi ta kansu ba hankali na na mayar a wayana.
Mun isa suka sauke ni a kasalance yai magana da cewa yau ma ina ganin keffi zamu je wani aiki da wuya in dawo gida yau.
Allah ya tsare hanya nai mai da a dawo lafiya ina kokarin bude mota naji ya rike ni tare da fadin wai fushi kike ko may ?
Kallon shi nayi tare da dan murmusawa nace fushi akan may ? may ya hadani da maganar ku da zanyi fushi kuma?
No khadija idan ya kira full name dina nasan magana ce ta serious zai yi don haka na mayar da hankali a gare shi ina sauraren shi.
Kada kiji wanan yar fitinar na fadin wai ina kwana a dakin ta ki dauke shi wani abu wallahi banyi hakan don wani manufa ba.
Sai don tsaron lafiyan abinda ke cikin ta kawai nayi haka don hawa saman ta sauko zai iya jawo mata wani matsala again.
Don wanan tunanen yasa, , , , haba dai ni fa wanan ba matsalata bace asalima ban san da wanan zancen ba a rayuwa na.
Tunda ba hakkina ka dauka ka kai mata ba ban damu da duk wani rayuwan da kuke yi a cikin gidan nan ba idan ba wanda ya shafi bangarena bane.
Murmushi yayi yana hade wani kololon bakin ciki tare da fadin take care tunda ya kula ban son maganar da ya dauko min din nace dashi insha Allah.
Na sauka daga motar ya ja suka wuce ni kuma na shige ciki duk da nayi kokarin wanan maganan amma sai naji wani bangaren zuciyana yana kokarin kishin hakan ga Nafisa.
Da sauri na kawar da wanan zancen a bangare nace damuwa na may tunda ba hakkina yakai mata ba alhalin kuma gashi yanzun ma ya fadi dalilin shi na yin haka gare ta.
Ni komai nene suje suyi tayi ai tare na gansu na kuma san gidan da na shigo dole ne sai na yaki zuciyana daga wasu abubu na kawar da kaina gare su .
Muddin ina son kwanciyar hankali a tare dani da salama yawan sa rai ga zamantakewar kishiya da miji da saka ido ga abinda sukeyi shike kawo rashin kwancinyar a zukatan kishiyoyi.
Kamar yadda ita take yawan saka ido akan duk wani motsi nawa shine silar hanata samun salama a zuciyar ta.
Idan na biye ma wanan halin nata nace zan dau fansa a gare ta nice zan sha wahalan haka tunda ance wanda ya rigaka kwanci yana riga ka tashi .
Da wanan shawaran na shiga ciki na kama normal life dina na school mun dauki lectures muna fito wa sallah muka nufi gidan wanan matar da anty hawau ta hadani da ita.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Akwai mata duniya don gaskiya nayi mamakin ganin wanan matar da anty hauwa ta turani gidan ta daukan darasin rayuwa a gurin ta.
Bayan mun gaisa da matar take tambaya tare da maida hankalin ta a gare mu tana fadin daga cikin ku wacece mai daukan darasin nawa ?
Maryam ne ta bata amsa da fadin dukkan ne anty don duk muna da bukatan hakan dariya matar tayi cikin hausanta da bai biye ba tace wacece matar auren maryam ta nuna mata ni da hannu.
Ta kalle ni tare da fadin very nice ai dukkan ku kina da quality din da namiji zai so ku a take idan kin iya rike miji kwana nawa ne kin kama abinki ga hannu basai ki tsaya wanan hali na matan kasar nan ba bin bokaye da malamai bashine mafita ga mace ba.
Sai dai wa yanda suka yarda da wanan akidar a wurin su yake mafita gare su amma idan mace zata zauna tayi amfani da hikimar ta da basira da Allah yaba mata sai taga ta kama mijin ta da hannun ta a saukake.
Ba wani abu mu matan waje mukafiku dashi dan banbancin kadan ne a tsakanin mu daku ku matan nahiyar nan kunya ne ko girman kai yake yawan damun ku.
Zaki ga mace na jin nauyi ko shakkan idon jamma,a ba zata iya sauke nauyin da Allah ya dora mataa kan mijinta ba.
Unlike mu kinga ni nan ko a gaban iyayyena nake ban shakan sauke nauyi mijina a gaban su No bawai kinji nace haka ki tunanen ina nufin kiyi fitara a gaban mutane bane,
Abinda nake nufi shi namiji yana son a riritashi ako wani lokaci ko agaban waye amma sai kiga mace sam bata damu da jawo mijin ta a gareta ba irin haka ne mata da yawa suke samun matsala a gidajen su.
Sai kiga namiji yayi aure daga baya matar tazo tana mashi abinda ke kika yi sake dashi a baya can wanda hakan laifin ki ne.
Ki cire kunya da nauyi kowa a idon ki ki tuna kuma kisa a ranki bautar Allah kike a hakan don babu waani wanda zaki daraja bayan iyayyen ki sai mijin ki.
Aljannan ki fa akace yana ga tafin kafar mijin ki ashe ko bazaki bada karfin ki da lokacin ki wurin ganin kin gina aljannan ki da hannun ki ba.
Zama muka gyara tare da ajiyan zuciya muna sauratlren wanan matar mai bada nashina kamar lectures taci gaba da fadin.
Ke bazakiyi tunanen irin nasa nauyin da yake sauke wa kanshi na hakkin ba kiyi tunanen wani abu zaki masa kwatankwacin wanda shima yake masa ki farauta masa rai.
Ashe ko duk wani abinda muka san zai sasu farin ciki ya zama wajibi muyi shi namiji shine zai ciyar dake ya tufatar dake ya biya maki dukkan bukatun ki nayau da kulun naki dana yan uwan ki.
Ke har da rabo idan ya ratsa a tsakanin ku koda yake ke ina ganin amaryace yanzu ko muka amsa mata da eh.
Tace to Allah ya baku zuria dayyaba muka amsa da amin tace kada kiji na zake ina maki wanan nasiha haka ke da kika zo in koyar dake dabarun mata.
Na dauko maki tunatarwa ne daga farko ta yadda zaki iya fahintar abinda zan fada maki a gaba da fatan kun fahince ni maryam ne ta amsa da kwarai anty muna biye dake ai.
Tace Alhamdullahi tunda kun fahinci inda na dosa taci gaba da fadin shi namiji da kike gani da zaran aure ya kullu a tsakanin ku daga ranan an bude maki wani sabon babin rayuwa ke nan.
Don haka wani jiji dakai da ko musu da sauri fushi ya kare a gare ki daga wanan ranan dole ne ki zama mai biyayya a gareshi.
Duk wani abinda muka san zai saka zuciyar su a farin ciki ya zamo dole mace ta juri yi ma maji shi muddin abin bai kaucewa shari,a ba.
Maryam tace kwarai anty tace kin gane ke nan shin kun san abinda yasa mazan ku na wanan kasar suke son auren matan waje ko wata kabila ta daban da naku ?
Wanan abin yana daga cikin abinda suke kwadayi wanda akasarin matan su sun yarda shi saboda kunya da dahun kai kan aure .
Suna hangen kwaraiwan wasu da kwadayin halaiyarsu na iya tatalin mazajen su da kwantar da kai a gare su.
Ladabi da biyayya ga miji tare da mutunta juna gami da sadaukar taimako tare da jajircewa a cikin zamantakewan aure.
Kun ga wanan abinda na lissafa maku bakomai bane auren facewa wanan gishin kin rayuwan da nai maganan su yanzu idan kin rike wayan takar kin rike kan maciji ne da hanuwan ki don ana son mace tazamo mai wanan halin a rayuwan ta.
Sai kiga ba mijin ba kadai da kowa nasa kin gama dasu a lokaci daya sai dai fa wani kari daya zuwa biyu dana manta ban fada maku ba sune.
Karbi, karbi ga dangin miji da abokai yana kara haska mace a gidan mijin ta sosai haka kuma godiya ga alheri zuwa ga miji yana daukaka darajan mace.
Sannan shi yawan bukata kullun ki ce saya min wancan babu wanan sai ta girgiza kai tare da fadin kin ga abu mai muni dake saurin durkushe mata yanzu.
Duban lokocin da maryam tayi a wayan ta yasa tace damu barin barku haka idan kun kara shigowa ma karasa sauran bayanin kafin mu kai ga darasin mu.
Amma kafin ki tafi yanzu barin baki wani abu don baji amaryan tana kamshi irin na rikakaun amare ba mikewa tayi tashiga daga ciki.
Maryam ta kalle ni tare da fadin kam uban nan duk wanan kamshin da kike zabgawa kinji matar nan wai bai yi ba nace maryam aini yau naji abu wallahi.
Fitowa tayi dauke da kwalayen a hannun ta tana kokarin sakawa a wani leda blue ta miko mun tace wanan idan kin karanta akwai sauran bayani a cikin sa kafin gobe ku shigo ko jibi.
Godiya mukai mata muka miki tsaye don barin gidan Nepep muka shiga muka koma school don acan za a zo a dauke ni.
Har naje gida maganganun ta suna min yawo a zuciyana da yake bai nan tun shigana na rufo part dina tunda nasan ba kara fita zanyi ba ranan.
Ban dade ba barci ya dauke ni a can cikin barcin nawa nai mafalki da Nafisa wai ina duke ban san da zuwan ta bayana ba tayi kokarin turani cikin wani rami Allah ya taimake ni na rike wani farin abu mai tsawo kafana yana daga cikin ramin ban riga da na fada ba.
Na dago na kalleta tare da fadin bazaki taba cin nasara akaina in Allah ya yarda sai ta kara yunkuri turani a ramin razana yasani ambata inna lillah da karfi.
Zubar na mike daga barcin ina yanka wani iri zufa a goshina tsoro ne matuka ya kama ni gashi ni kadai ke a dakin.
Wani irin tsoro nake ji yana rufe ni a lokacin addua na fara karantowa sai wajajen asuba barci ya dauke ni har nakai ga makara.
Wanan mafalkin ya tsaya min a rai sosai haka har na gama shirina na fito ranan nayi mamakin yadda ban samay su a falo ba kamar kullun.
Na isa school na samu an shiga sai dai malamin yana gab da shigowa a lokacin wuri na samu na zauna ina mai ci gaba da nazarin wanan mafalkin a raina.
Har malamin ya fito yayi abinda zai muna muka gama lectures ranan jikina banda wani kuzari sosai .
Haduwan mu da maryam yasa na dan sake kadai sai dai idan na tuna da mafalki nakan karatun Allahuma ajirni fi masibati wa,akalifli hairun min ha.
Bayan mun sallamay sallah da yake ban karya ba a lokacin sai nake jin kamar zan fadi don yunwa maryam ce ta sawo min lemon kwalba da snack na dan sha rabin goran na aje sai dai ko ina bai kai ba na amaye shi duk.
Kin san baki ci komai ba dole sai abu mai dan zafi ne zai zauna maki a ciki dole mikewa mukayi da jikina yadan sake muka nufi gidan anty Salbiya don karin ilimin da muke so na zaman duniya.
Bamu dauki lokaci ba muka isa gidan anty Salbiyan saida akai muna iso saboda tsaron da gidan ke dashi duk da gidan bai kokai rabin gidan AA tsaruwa ba da fasali.
Sai dai rashin tsari da yawan jamma,a da gidan namu ke dashi ya jawo baida wani tsari yanzu ga kowa.
Bamu dade zaune ba ta fito fuska da fara,a da alaman daga barci ta tashi lokacin gaishe ta muka fara tana murmushi ta zauna tare da fadin kun shigo.
Eh inji maryam tana kara gaida matar nima na gaida da ta tace jiya ai nayi mantuwa ban tabayi sunayen ku ba har kuka tafi.
Maryam ta gabatar mata da sunan ta sannan ni na biyo baya tace duk sunayen ku sunane masu dadi ko a addinance ana alfahari da wanan sunan.
Tace amarya zance ko khadija nayi murmushi tace da fatan aikin mu ya fara tun jiya dai cikin kunya nace gaskiya bai fara ba don maigidan bayanan yayi tafiya.
Ok lailai ashe akwai taro kuwa don ya kamata ki haddace lokacin dawowan mijin ki gida kafin nan da rabin awa ya zamanto lalai kina a cikin shiri bawai yazo ya samay ki a ya mutse ba har ya fahinci halin ki ne hakan.
Ya kamata ya samay ki a cikin kwalliya kina zaune falo kina dakon zuwa sa yana shigowa zaki mike a cikin naki irin sallon kina masa sannu da zuwa tare da karban jakkan hannun sa ko leda ko wani abu dai daya shigo dashi gidan a hannun sa kina mai sannu da zuwa da sauran maganganun jan hankali a gare ki.
Nayi mantuwa ban fada maki ba ya kamata ace shi yana waje gurin aiki ke kina gida akalla zaki kirashi cikin ko wani a wa daya kiji lafiyan shi da sauran su.
Har lokacin da zai dawo gidan wanan yana kara kawo shakuwa sosai tsakanin mata da miji don Allah ki kula khadija nace in sha Allahu anty.
Ina fatan dai kina hakan kaina na noke tare da fadin anty ni ba wani shakuwa na soyayya mukayi da maigidan ba sanan kuma yanzu bamu fi wata uku da aure ba dashi.
Maryam tace a cikin na hudu kuke fa yanzu khadija hararan ta nayi Anty Salbiya tace amma ko kin ban mamaki don duk macen da tai jami,a ai ya kamata tasan wanan koda kadan ne.
Aure wata kusan hudu khadija amma baki maida komai serious ba haka a hakan har zaki saci zuciyar mijin naki ina kina da kishiya ko ?
Maryam tace kwarai kuwa kuma buzuwa ce yar Niger ce ta asali don ko hausa bata ji sosai har yanzu Antyn tace ashe irin mu ce sai dai muna da banbanci sosai dasu yanayin mune kawai shigen iri daya dasu don su ma haka suke kamar larabawa ke din ma ai zubin ki baza a ce yar kasan nan bace idan an ganki don kin fi kama da yan kasar Ethopian sosai.
Nakan fada mata amma sai ta dauka zolaya ne nake mata No ba wasa gaskiya nima farko jiya da kuka shigo ban dauka ke hausa bace sai dai da yake ko a cikin hausawan mafi akasarin su ai kyawawa ne kula ne dai da basuyi da kansu yadda ya dace suyi.
Sai kiga mace haihuwa biyu ko uku sun jemay sun fita hayacin su kamar mai shekaru da yawa.
Naga kamar lokaci tafiyan ku yayi ina fatan yau zaki fara daga cikin abinda na koyar dake koda kadan ne don Allah nace in Allah ya yarda anty.
Sosai ta kara yi min yan nasihohi wanda hakan ba karamin tasiri yayi a zuciyana ba don a cikin hikima ta dinga fadakar dani abinda ya dace.
Mukai mata sallama zamu tafi ta dan tako muna har zuwa waje tana fadin gobe insha Allahu zan fadakar dake akan kishiya ko yadda zaki zauna da ita acikin salama don kin san yanzu anbar kinshin fili sai na boye.
Maryam ta amsa da wai banda wanan kishiyar na khadija mai kishin hauka anty bakiga ba fa yadda suke abinsu kirikiri ranan mun dawo daga unguwa kirikiri magani da wani abu muka samu yabe yabe a kofan shiga part din nan dai ta bata labarin abinda ya faru a gidan ranan.
Na dora da fada masu abinda na tono a karkashin gadon AA duk a ranan ko maryam sai a lokacin take ji tana yaba zurfin ciki irin nawa.
Ajiyan zuciya Anty Salbiya ta sauke tace to Allah ya kyauta anan kuma na dora da fada masu urin mafakin da nayi ranan akan Nafisa din wanda abin yake cina har yanzun a zuciyana.
Tace gaskiya sai kin dage da addua tare da yawaita irin su sadaka kyautata da sauran don kin san irin wanan abin ya taimakawa mutum ta ida bai zata ba.
A sanyaye na furta ina yi anty tace da hannun ki kike badaw ko sakawa kike ai maki dai nace cikin murmushi sakawa nake ai min tace shine matsalan mu ai.
Baki san adduan mutum da bakin sa yafi saurin kamawa ba haka kuma abinda kika bayar da hannun ki yafi saurin karbuwa a wurin biyan bukata.
Sauraren ta mukeyi a cikin fahintar abinda take fada muna din, maryan tace anty ai inda mutum zai samu irin wa yan nan mabukatan ne anan har ya basu shine ai.
Kai ta girgiza tana fadin baku dai nema ba maryam amma idan kuka je irin su madala ko maraba nan ma a cikin gwagwalada akwaisu.
Ba wai sai mu saki ba irin masu karamin karfi din nan duk zaku iya basu don ko suna bukata Allah yasan a inda yan amin suke.
Mun rabu da ita cikin farin ciki da kauna muka bar gidan ta wurin anty muka biya nan mukai sallah la,asar mukaci abinci sai dana dan huta na dauko waya na nakira shi.
Kamar kiran zai katse aka dauka da sallama na karba mai yace cikin wani murya a kasalan ce Deedar ya akayi ne ajiyan zuciya na sauke ta yadda har yajini nace dashi ba komai.
Nadai kiraka ne in ji lafiyan ka yace realy nace may ye kuma na mamaki don na kira ka yanzun kuma ?
Ai dole inyi mamaki yau ni Abdulsamad Deedar zata kira kodai kin yi kewan kayan ki ne tsakanin jiya da yau ?
A hasale nace ban sani ba na kashe wayan yana ta kiran layin nawa inaji naki dauka maryam da muka fito take fadin .
Wai wake ta kiranki ne haka kike rejecting din call haka nace kyale shi don Allah shi ai dama ba ai mashi abin kirki yafi son kowa ya zauna kamar yadda matan shi suke ko yaushe.
Ba zaki zauna ba kuwa da sannu zaki gyara komai koda ace ko basu koya ba ke zakici gaba da dasa mai naki akidar a zuciyar shi.
Tun hanya muka rabu yau ban koma school ba na kira driver na fada mai ba sai yazo ba na samu an rage min hanya na dawo gida.
Ina shiga gidan massage din shi na shigo min yana fada min yana saman hanya yanzu an jima kadan zasu iso insha Allahu.
Su nafisa na samu a falo na wuce ba tare dana gaida su ba suma kamar yadda basu min sannu da shigowa ba na wuce hanyar part dina kai tsaye na bude na shiga.
Sai da na canza kaya na fada kitchen tare da tunanen abinda zan girka mai yaci idan ya dawo din ruwa na dora na dauko garin alkama na fara tankadewa.
Na gama na gyara kayan miya fresh na wanke na ciro nama na yanka tare da dorawa akan wuta.
Allah da ikon sa har na karasa aiki basu shigo ba part din har na gyara komai yadda ya dace wanka nayi na shirya sai naji kawai in fara aiwatar da huduban mutane mana yau.
Iya gwargwado dai nasha nasihan zamatakewar rayuwa da fadakar wa ya kamata ni ma in fara amfani dashi hakana in kawar da duk wani nauyi da kunya a tare dani.
Turaren da Anty Salbiya ta bani na shafa na shirya a cikin wasu atamfa mai launin jan watau red colour da dan fari fari a cikin sa.
Skirts and blulawars ne dinkin shi sai dan kwalin dana daura na kawo shi gaba kadan na kara kallon kaina a mirrrow na fito tsab.
Har zan fita daga falon na koma na dauko chewagun mint na bare na saka a baki na direct falon gidan na nufa inda su nafisa suke zaune da tawagan ta a can barin hago inda dakin ta yake.
Wurin dayan set din na nufa tun fitowa na kowan su ya sako min ido caaa suna kallon ikon Allah don wanan shine karo na farko da na taba fitowa falon gidan na zauna tun shigowana gidan.
Zama nayi na dauki kafa na daya na dora saman daya ina taunan chewing gun din a hankali yana bada dan sauti mai kara .
Hankalina yana a wayan dake hannu na ina dakilar wayan ba tare da na kula kowa dake falon ba a lokacin su kuma basu daina kallona suna mamaki ba da tunanen abinda ya kawo nin falon a wanan lokacin.
Yar wurin Nafisa Ihisan ne tayo wurina da gudun ta ta fada min a jiki na dan zabura ina shafa kanta muryan Nafisa naji cikin wani irin kara tana fadin .
Ke, ke , ke kada ki fara ki taba min yarinyar ki kama mata kurwa na fada maki idan kina so ke ma sai ki dage ki haifi naki a gidan.
Ban kula ta ba kuma ban sake yarinyar ba muna magana da yare taiwa Samiha magana tazo ta dauko mata yar ta a wurina.
Samiha ta taso zukwai zukwai taja hannun yarinya ta figeta ta wuce da ita inda suke zaune uwar tace tauraruwa mai wutsiya ganin ki ba alheri ba.
Kin kulla ta nayi don kada ta rushe min plain din kada ya shigo ya samay mu muna fada ko minti biyar ba,ayi ba sai naji dirin motocin shi sun iso gidan.
Ba wanda ya kula daga cikin su da dawowan shi tun a cikin cotton na hango shi tafe ya sagale rigar shi ta sama a kafadan shi.
Mikewa nayi tsam daga inda nake na tare shi bayan ya karasa shigowa daga ciki din a lokacin na mike na nufe shi.
Aiko idanuwan su caa a kaina kamar su cinye ni danya a lokacin hugging nakai mashi tare da sunbatan shi ina mashi sannu da zuwa.
Sai ya rugumoni sosai zuwa jikin shi tare da fadin Miss you deedar wanan kyau da kika sha haka fa nace is for you ya kara kai min kiss shima a tsakiyan kaina.
Mutuwar eacin gadi tayi da kyat ta iya tataro courage din ta tace yau kuma wani karuwanci ne haka a fili ?
Komai dai jarabar mutun dole ya bari har ranan girkin shi yayi jakka shi na zuwa aiki driver ya shigo dashi na karba daga hannun driver din.
Na wuce gaba yana biye dani a bayan shi part din shi na nufa har lokacin banda Nafisan ba wanda ya iya wani kwakwaran motsi daga cikin su.
Ganin na doshi hanyar part din ta mike tsaye tare da fadin malama kya bari sai girkin ki kiyi wanan sallon karuwancin kauyen ko ?
Murmushi nayi ban tsaya ta kanta ba na haye sama abina na barsu a nan tace a hasale dashi.
Samad amma kana kallon takalar yarinyar nan shishigin ta yayi yawa a gidan nan girkin ma yanzu kokari kwacewa take nufin yi a gare ni ko may ?
Da mamaki ya kalle ta yace kamar ya zata ci girkin ki ina yau itace dani kuma time din karban ta yayi har ya shuda yana magana yana kallon agogon hannun shi.
May kaku nufi da maganar ka ina jiya baka kwana gida ba don haka ni ya kamata in karbe ka a yau ai.
Wai Nafisa ke wata irin mace ce da baki da lissafi a rayuwan ki ban fa son irin wanan rikicin kin ji na fada maki.
Amma ai kasan haka muka saba yi a baya dakai idan ka dawo daga tafiyan yanzun ne zaka canza muna tsarin ko may ?
Yace da kika ce ba yanzu ita taga tana iya bar maki nata waccen da kike magana wanan ko tasan right din ta.
Hannayen ta ta taba tare da fadin yau ko zanga yadda za a dulmuye ni ina ji ina gani tsuki yaja ya nufi saman abinshi ya barta nan.
A dakin ruwan wanka nake kokarin hada mashi a ban daki naji shigowan shi dakin ko da na fito yana tsaye a tsakar dakin yana kokarin sasauta nicktie din wuyan zai kwance.
Na fito daga ban daki takowa nayi inda yake na rike mai hannu karban cire mai tie din nayi ina kokarin cirewa sai kallon mamaki yake min yana wani lumshe ido
Ban san shigowan ta dakin ba sai ji nayi an bangaje ni ta baya da karfi sai da na fada saman jikin shi ya tallabe ni da hannun sa.
Tare da fadin kina hauka ne wai Nafisa may ya shigo dake dakin nan wanan lokaci haka ko kishi haukane wai ?
Mace baki son zaman lafiya ko yaushe sai dai ayi fitina shine gurin ki kin sani sarai ba lokacin ki bane yanzu don may zaki tayar wa mutane da hankali haka wai , ?
Zan nuna maku haukan da kake yawan kira min ne azzalumai kawai kuna ganin zaku juyani ne a gidan nan ne komai yadda muka saba idan ka dawo haka za a ba wanda ya isa ya canza min tsari na.
Hannuna na daga ina kokarin karasa cire mai tie din ta daga hannu zata kai min duka ne ko mari ya rike hannun ta da sauri tare da fadin.
Dukan ta zakiyi komay nace barta kin ci albarkancin cikin nan dake jikin ki da yau kin gane baki da wayo da nanuna maki tawa kalar haukan kin gani.
Don ni ban tsayawa fadan baki haka kanki zaki tsunta a waje eh lalai ba laifin ki bane wuri kika samu.
Gashi yanzu kirkiri a gabana kuna son ku dulmuye min hakki na macuta mayaudara ba irin Nafisa ake cuta a zauna lafiya ba.
Ciki kuma da kike maganar sa kokarina ne ya bani shi don ni ba juya bace mai ci takai masai kullun zufana ne kike gani don haka kada bakin bakin ki ya kara tofa zance akan cikin jikina.
Jan hannun ta yayi zuwa waje yana fadin ki koma kasa idan na sauko sai muyi magana amma ba nan ba a cikin hakkin wata.
Samad ni kake kora a dakin ka kan wanan kwailar karuwan yarinyar da ka dauko mai kama da matan titi.
Nafisa yace cikin wani irin tsawa ba ita dake gaban shi ba har ni sai da na kadu daga inda nake ina kallon su ya daga hannun kamar zai make ta sai kuma ya sauke yaja hannun ta zuwa wajw tana turjewa.
Sai zagi take zuba min na cin mutunci da tozarci na fallasa irin na tantiran kishiyoyi din nan suka fice daga dakin ajiyan zuciya na sauke ina binsu da kallo.
Abinda ya fara zuwa min a rai shine ashe wanan akidar ke nan sukewa Fati dole ne Fati ta kasa zama a gidan don wanan irin dabancin na Nafisa kishi da buzuwa sai basira da hankali sai kuma an daure.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Wanan novel fitar dashi cin amana ne karanta shi ba tare da biya ba rike hakkin wani ne akan ki don Allah yan uwa musulmai mu kula da hakkin wani akan mu.
Ki tuna wanan online novel ne kika saya ba booklet don haka ka,idar shi ki karanta ki barshi nan kiyi tunanen wanan maganan yar uwa dubara ya saura ga mai tsoron Allah.
Dakin ya dawo rai bace ya shiga wanka bayan shigar shi wankan, sauka nayi zuwa kasa na kammala duk wani abinda zanyi na rufe part dina na nufo wurin shi a cikin wasu rigar barci masu daukan hankali sosai.
A D/table na samay shi zaune ya fito daga wankan tunda na nufo gurin ya mayar da hankalin shi gare ni ga waya yana yi a hannun sa.
Kulolin na bude na fara zuba mai tuwon da miyar kubewa sai kamshi kaya yaji da sanadarin miya ke tashi.
Ke ba zaki ci bane ya na jan plate din zuwa gaban shi ya dago yana tambaya na ban jin cin komai yanzu don naci abinci around four dazun a koshe nake sosai.
Na lura baki damu da abincin ba sai yan kayan zaki da sauran tarkace kamar sha zumami dan murmusawan dole nayi don abinda ya fadi din.
Sai kuma naci gaba da tunanen da nakeyi a raina ina tausar zuciya akan abinda nake gani anayi akai na, ko yaushe a gidan.
Na zauna a gaban shi yana cin abincin a hankali ido na kura mai zaka ce hankalina yana gurin shi ne a lokacin a yadda muke zaune.
Kula yayi da zurfin tunanen da shiga wanda ba tunanen komai bane sai na rayuwan matar gidan da muke zaune tare, kullun a cikin fitina babu ranan sulhu ko shiryawa a gare mu.
Muryan shi naji tare da dan kada hannayen shi daidai fuskana, na dago kai ina murmushi tare da fadin ina jira ka kanmalane in kwashe kayan a gurin .
May kike tunane haka Deedar har ina magana baki jini ba ajiyan zuciya na sauke tare da mayar da hankalina a gurin shi.
Abinda ya faru yanzun kika sa a ranki ko mai na dan rausaya kaina tare da fadin abin ne kawai yake ban mamaki don naga babu tsarin Allah a cikin harkan ta.
Murmushi kawai yayi ya dauki tsokan nama dake cikin miyan ya kai a bakin shi ya fara taunawa ba tare da yayi magana ba.
Sai da ya lashe abincin tare da turo min plate din a gabana yana fadin kin sani over feeding yau da yawa don girkin yayi dadi sosai.
Haka nake so shiyasa na bata lokacina na girka mashi don nasan zaka so shi saboda na kula da kana son abincin gargaji ya sosai.
Ashe kin fara fahintar halayena yanzu kwarai ina son irin girkin nan idan zan samu don dashi nayi wayau a gidan mu kin sani.
Mikewa nayi ina hada kayan abincin tare da tambayan shi ya zancen da hajiya mama tace tace ka fada na kawo kayan zainab din idan da hali ina son inje ayi sha,anin dani.
Mikewa yayi shima daga inda yake zaune yana fadin ba fa buki bane ko wani abu kayan lefe ne kawai za a kai masu.
Nace ai yanzu kasan an maida abin kamar buki ne duk wani dan uwa na kusa yakan je a tari kayan dashi sai naga zai yi kyau ace wata daga cikin mu ta tafi wurin.
Ita Fati dake can idan taje bai isa ba sai ku dake nan kunje sai dai idan akwai wani abinda zai kaiki dama ba wanan zancen ba.
Ko daya wallahi ban sa ran zuwa yanzu ba ko don karatun dake gaba a wanan lokacin ganin dacewan zuwan mu dai guri.
Dakin shi ya shige ya barni gurin ina gyarawa ba tare da yai min magana ba na gaba hada kayan a cikin basket na shiga na samay shi a dakin.
Ko da na shigo dakin yana zaune yana latsan laptop din shi har na shigo na kara kawar da komai na dakin a inda ya kamata.
Maimakon in hau gadon in kwants kamar yadda na saba yi a kullun sai yana zauna a gefen shi tare da dan kwanto jikina a saman nashi ina sauke ajiyan zuciya.
Muryan shi naji yana fadin Deedar yau may ke faruwa dake ne haka naga wasu sauyi a gare ki.
Ba wani sauyi da ka gani a gare ni dama can haka nake ko ka manta ne da halina kawai dai irin rayuwan da gidan naka ke ciki ne bai gamshe ni ba.
Sosai magana ta taso bashi dariya amma sai ya daure yace dani cikin juyowa yana kallona tare tare da fadin look at me Deedar.
Kallon nasa nayi kamar yadda ya bukata nayi yace gida na ba halin sa ke nan ba ki dai ce matar gidan da kika sama ce halin ta bai maki ba.
Deedar kin san kowa da yadda Allah yayi sa da kuma irin fahintar shi ita rayuwan ta ne haka da zafin kishi irin na rashin fahinta rayuwa nata kawai ta sani bata damu da damuwar wani ba .
Na karbe da fadin wuri dai ta samu nayin hakan don da kunnen ka kaji abinda ta fadi a baya kuna yi watau da kai da ita kun hade kai kuna tauye ma Fati hakkin ta yasa yanzu da ka canza take ganin muna yaudaran ta ko cutar ta.
Murmushi naji yayi tare da fadin kada ki min mumunan fahinta anan mata suke da alhakin saita gida a tsakanin su idan daya ta bada daman da dayar zata taushe jaruntar ta sai alkibilan komai ya koma ga yar uwarta duk kokarin namiji akan yaga yayi adalci a tsakanin su.
Tunda naji kalaman shi na fahinci abinda zancen shi ke nufi watau idan mace tayi sakaci da daman ta sai abokiyar zaman ta ta kwace komai daga miji har gidan a hannun ta yanzu ke nan dabara ya saura gare ni ke nan akan buzuwa.
Bayan dan zurfafa danayi a cikin tunane na sauke ajiyan zuciya ina kokarin mikewa daga inda nake zaune don tuni tun da muka fara magana na raba jikina da nasa ko.
Na juya naji ya riko hannuna ya rike ba yadsa zan iya tafiya naji yace ina son ki fahinci magana ta da kunnen basiri a yadda nai maki shi a dunkule da fatan zaki fahinci mai nake nufi.
Na fahinta na fadi cikin daurewa don nakai iya wuya a lokacin yace ba ina nufin ki biye mata ku dinga hauka irin nata da sunan kishi bane.
Ina son ki gane kamar yadda na auro ta a gidan nan da sunan so a gare ni haka kema na auro ki na kawo gidan nan da sunan so a gare ni.
Sai dai kada ku mata ni namiji ne ina da wanan daman da zan kara kawo wata agaba ta zauna a cikin ku ku zama ku hudu ke nan a gare ni.
Kallon da nai mashi yadan kara jawo ni a gare shi yace ni mijin mace hudu ne Allah ya bani wanan daman kuma ya hore min abinda zan iya karawa dashi ai kin san aure kuma sunna ce ta Annabin rahama.
Don haka ne nake son ki fahinci zama da hali mai kyau ko akasin haka mafitane a ko wacen ku idan Nafisa tana da wani hali da bai gamshe ki ba a gidan nan.
Kina da daman dake zaki amfani dashi wurin toshe wanan kafan ki dora hakin ki na gari ki gyara min wanan gurbin da taba da kafa a gare shi.
Shiru nayi ina sauraren maganar shi wanda yake min kamar nasiha ko fadakarwa a gare ni kokarin janye hannaye na nayi daga nasa sai naji ya rike ni gam ya ki raba hannuna daga nasa.
Yace Deedar ki sa a ranki wanan ne kaddaran ta farko da kika fara fuskanta da fatan zaki rugumi rayuwa a yadda yazo muna.
Yanayin rayuwan zama na da nafisa kowa ya gani zai dauka ta fi karfi na ko wani abu makamancin haka ni na bar wa cikina wanan dalilin.
Yanzu naga kamar magana ta tasa zuciyar ki ta fara kishina jin zan iya karo wata a bayan ki kuma nan gaba.
Yanzu wanan zancen da zai sa ki lalabanj kina ririta ni duk wata mace dake gidan nan dama wace zata zo ki nuna masu cewa ke din ta daban ce daga cikin su.
Fisge hannuna nayi daga gare shi na haye gadon na kwanta tare da juya baya a gare shi can naji ya gama abinda yake ya hawo gadon ya kwanta.
Hannun shi yakai a jikina na lumshe idanuwa na muryan shi naji yana fadin Deedar badai maganar fahintar a tsakanin yasaki shiga wani yanayi ba.
Na juyo a cikin wani courage dana samu ina fadin na rungumi kaddarana tun ranan da na shigo gidan a sunar matar sunna a gare ka .
Zanso ace na kasance daga ciki diyan albarka masu biyayya ga iyayyen ga duk halin da suka riski kan su a ciki.
Don haka ni na dade zama da shirin duk wani rintsin da zan fuskanta a gidan nan ko wace kallace matukar ban saba wa mahalici na ba da hakan.
Wani kallo yake aika min ina maganan a take idanuwan suka canza launi ganin haka na so juyawa in koma yadda nake da farko naji ya riko ni.
Kokawa irin ta ma aurata muka fara a lokacin nayi nasara haye ruwa cikin shi nan wasan tamu ya canza sallo a dakin mun dauki lokaci a tare muna farauta wa juna rai a inda ya sha mamakina a wanan dare.
Ko da gari ya waye ranan mun makara daga tashi sallah a gurguje na karasa duk wani abunda zanyi na fito bayan mun karya muka bar gidan.
Ban hadu da Nafisa ba a falo ashe bata gidan nan ne tayi asubacin batin gidan zuwa wurin madam kan matsalan da take fuskanta.
Ban makara daga shiga lectures ba a ranan duk da lating da nake gani nayi a lokacin sai dai jikina nake jin yawan kasala yana damu na sosai ga wani barci da nake ji wurin kwantawa kawai nake bukatan in samu.
NAFISA a falo madam cikin takaici take magana kan sauyin da take gani ga madam sai data gama fadin maganan da ke tafe da ita iya son ranta madam din ta karbe maganan da fadin.
Nafisa kema kin san wanan yarinyar fa ba irin ta farkon bace don wanan kina ganin ta duk da tana da karancin shegaru idanuwan ta wallahi a bude suke.
Banyi zaton ta shigo gareki a banza ba yanzun dai matsalar mu ai wanan cikin da kika samu ne gashi yazo maki da lalurar rashin yin motsi mai karfi da sai mu bazama mushige duniya can kasashen yarbawa da iyamurai kin san su aikin su tsafi ne kamar yanka ne.
Nafisa ta kalli madam tace ke nifa ciki ba zai hanani yin komai ba wallahi idan zamuje a shirye nake ko yanzu kan wanan yar iskan.
Wai fa a gaba a kan idona na samu wai tana balle samad anineyar rigan shi shiko yayi tsaye kamar wani soko dashi.
Dariya madam tayi tana fadin ke makin san halin maza ai idan suka samu sabon sauyi sai fa kinga abinda ba daidai ba a idon ki.
Ni yanzu shawaran da zan baki shine ki bari har ki haife sai mu san abin yi don yanzu koda munyi wani abin walahi barnan kudin ki kawai zakiyi.
Keda, keda dama yanzu da zaki ta karban kudi da suna cikin jikin ki kina tara ma tafiyan mu kin ga kafin nan kinyi muna tanadi mai kyau da zamu ci kaniyar su da tushe.
Jin maganan kudi ya shigo yasa Nafisa washe baki tare da fadin kin kawo magana madam don ni ban ko kawo wanan ba a raina ina dan banzan hauka kamar yadda yake kirana dashi.
Madam tace kin fahince ni mutumiyar ai ba karamin shiri zamuyi wa shegiya ba sai ta raina kanta da ta shiga ragan da ba nata ba.
Wallahi madam na tsanin wanan yarinyar ban taba dauka samad zai ga wata mace har ya ta so rikita shi ba haka.
Madam ki duba min may na rasa a jikina wanda yasa samad yin aure madam tace ikon Allah kin fasan halin namiji fa nafisa.
Balle shi da iyayye suka bada tasu gudunmawa ga auren shi baki ga sai da suka darje suka zabo mashi mai irin zubin ki ba ta yadda zai iya fudewa a kanta ya barki ba .
Basu san wasa suke damu ba jin mu suke basu san sherin mu ya wuce haka ba ke zan iya cewa gara da yai maki ita yanzu ba sai daga baya ba lokacin girma ya kama ki baki da moriya sosai ba.
Ai babu auren nakasa ga mace kamar sai lokacin da girma ya fara kama ka a auro maki kishiya da zata zo tana haihuwa kina kallon ta.
Badon kin ma yar iska wanan dan bakan ba ai da yanzu tana nab da kunshi a gaban ta wai ciki.
Da sauri nafisa tace dakun daure ni ranan don bansan inda zan saka raina ba shiyasa na haka ma yan iska shi ban sake bi ta kanshi ba.
Shine daidai wallahi don gudun bacin rana kizo baki haka ba azo a samu akasi ya haye yar iska tazo ta dauki ciki asirin mu ya tonu .
Ina ai ba zan ma yarda haka ya faru ba a tsakanin sai dai gani da hange badai wanan ba nasan don haka ne ai yake lalaba shegiya don kada ta tona mashi asiri mutuncin shi ya zube a gane shi mace ce.
Kin gane ke nan amma ya kamata fa ki duba bakan nan don kin dade da haka shi ko yana a haken har yanzu kada azo a samu matsala kuma.
Zan duba yau din nan dana je gida amma inda na aje shi ai banyi tsanmanin wani zai iya ganin ba ma ga kuma kwalban dan agadas shine ma banga wani tasirin shi ba koda yake ai yau suka fara kwana dakin tare.
Dan iskan kamar yasan abinda nasa ranan sukaki kwana a dakin sai dakin ta suka je suka kwana shiyasa nake fada maki ai da shiri shegeya ta shigo maki.
Sun dade suna magana daya a karshe dai ta yarda da shawaran madam din na sai ta haihu kafin su yi wani yunkuri a kaina da maigidan.
KHADIJA.
Tunda nayi sallah nakai kwance sanan carpet din masallacin ina jin dadin yanayin wurin na dan shiga na a hankali.
Maryam ta idar da sallah ta juyo gare ni tana fadin yau yaya dai madam nace wallahi maryam wani irin barci nake ji sosai jikina duk kasala sa nakeji.
Yau ko zamu samu leka anty salbiya ke nan nace zamu bari dai in dan kara hutawa gashi kuma yau ina son attending din last lectures dina wallahi.
Tashi mukayi muja shiga gun lectures din yana fita muka nufi gidan salbiya din don jin dan karuwan da zamu samu a gurin ta.
A gidan anty salbiya ma kwance nake ina sauraren bayanin da take min ka kwalliya da yadda zan dinga shiga wai ko wani lokaci ya kamata ace mace tana yabayin shigar da takeyi tundai idan oga yana gida tare da iyalin shi .
Ta juyo gare ni tana fadin idan kin bi wanan hanyar zaki ci galaban kishiya sosai wallahi don ko wani kasa suna da kalar tufafin da suke jin dadin sakawa a jikin su.
Ashe kin ga ku matan kasar nan ko wani shiga kukayi yana daukan jikin ku sosai don baku dogara yanzu da kayan aladan ku ba.
Kin ga kuma su mazan yanzu abinda ke kara ingizasu kenan gun wasu matan sai ki dage wurin saka tufafi masu jan hankalin namiji nasan ko tace zata koye ki abin ba zai dore ba gare ta don ko bata saba ba da hakan idan ma ta saba ke zaki iya kirkiro naki sallon kiyi.
Yanzu dai kinga ko anan ai mun samu wani babban mafita akanta ko mukace hakane anty sannan ta juya da fadin sai gyaran muhali.
Yazanan to part din ki yana da wani kamshi da sai a gunki za a ji wanan kamshi naki ne ke kadai komai na gurin ki ya karba da wanan kamshin.
Ina mai tabbatar maki duk lokacin da yaji wani kamshi makamancin haka zai tuno dake a ranshi haka nau,in abincin ki ya zaman to kina canza shi lokaci lokaci ba kulun abincin ragayen mata ba irin su indomie taliya da sauran su din nan.
Ke koshi miji fa yana bukatan gyaran kansa daga gare ki kamar kula da tufafin sa da undies din maigida da sauran abin amfanin shi irin su takalma da sauran su bawai sai tufafin jikin shi ba kawai zaki kula akan su ba.
Wani amai ne ya taso min na toshe baki na da sauri na nufi toilet din dake falon su banyi wani abin kirki ba na dawo idanuwan su a kaina har na zauna.
Tace ikon Allah anyah amarya bakin halbu bane kuwa wanan irin amai kuma haka fa nace anty ina ganin rashin karyawa ne da bana yi sosai ya jawo min ulcer.
Dariya sukayi anty salbiya tana fadin Allah yasa ulcer mai tushe ne ya samu to yanzu barin barku kije gida ki huta don kina bukatsn hutu a tare dake.
Don tun shigowan ku na fahinci hakan ki daure dai ki adana wanan sirin idan son samu ne sai idan ya fito a gani a jikin ki.
Don shi ciki kamar hasken rana idan ya haska babu abinda ke boye shi ko mijin ki ki bari sai ya gani da idon sa .
Don wasu mazan yawan doki na saka su jawa mace matsala akan sauran al,umma basai kishiya kawai ke kishin haka ba.
Idan baki yai yawa gun abu sai kiga abin na zuwa da matsala sosai don baka san bakin wani ba don baki dafi ne sosai wallahi.
Nace ba komai yanzu anty hasashen kune kawai hakan amma dai zan kula din idan haka ya faru maryam kan bata samu bakin magana ba sai kallo na take yi.
Mun bargidan ganin banjin dadi yasa maryam ta biyo ni gida yau tunda ba nice da girki ba mun huta ina zaune a falo ya kira layi na.
Nakai hannu na da kyar na dauki wayan tambayana yake idan mun gama lectures din a zo a dauke ni na amsa mai da kyat da gani nan na dawo gida yau banjin dadin jikina ne.
Yadda yaji murya na yace da sauri may ke damun ki nace ulcer ne yace kin gani ba dama nasan haka zai iya faruwa ai na fada maki ki dinga cin abinci bakya ci.
Nace da kyat bafa rashin cin abinci bane ulcer ciwo ne kawai yace yanzun dai ke dayane kuma gashi aiki nakeyi nace muna tare da maryam ne ta rakoni gidan sai ta zauna dani.
Ok maryam ta kyauta ki samu abinda kika ci idan zan dawo zanzo maki da maganin ulcer din kisha mu gani nace nagode .
Yace Ok bye bye take care nace nagode I will ya kashe wayan maryam tana zaune ta kafa min ido sai da naje wayan tace dani.
Karfa kisha magani khadija azo ana magani daban ciwo daban nace yau na fara wanan kuma maryam don Allah bari zancen nan inani ina ciki yanzu ai abin zai min yawa.
Ok kina planing ke nan nace akan may zanyi planing maryam don cikin wai na masan ba zan yi shi a yanzu ba tace ok tana dan murmushi.
Kafin ya dawo yai min kira yakai uku tare da tambayan har yanzun maryam din tana tare dake dai ko nace eh ai anan zata kwana.
Warin tafarnuwa nake ji har cikin part dina da ake girki dashi a part din nafisa yake shigo min a part dina sai ya saka zuciyana wani irin tashi dole na mike ina cewa maryam don Allah mu shiga daga ciki.
Sai dai ban fada mata may nake ji ba wanka nayi nayi sallah ina sallamay wa na haye gado na kwanta abina.
Bai shigo ba sai nine na dare ya shigo dagani ko part din shi bai je ba a dakin ina kwance maryam zaune tana karatu ya shigo..
Gaisuwa sukayi da maryam din tare da tambayan ta jikina tace da sauki ulcern ai ya fada mata tun dazu barci tace tanaji yanzu.
Wurin gadin ya nufo maryam ta mike ta fita daga dakin kafa na ya ja na falka firgigit ina kallon shi sai kuma na dan sake murmushi tare da fadin sannu da dawowa.
Zama yayi yana fadin ya jikin naki naji sauki na bashi amsa yakai hannun shi saman wuyana yana dan tabawa tare da miko min maganin ulcer masu tsada a leda na karba ina fadin nagode.
May kikaci yanzu ya tambaye ni nace tea nasha da cake wani kallo yai min yace may zakuci a samo maki yanzu nace sai dai maryam amma ni na koshi.
No yace yana mikewa tare da fadin barin fita yanzu idan nayi wanka kada ku rufe ku jirani in dawo nace a dawo lafiya ya fita.
Falon na tashi na dawo na samu maryam din bata nan ashe tana dayan dakin ta kwanta nan na samay ta kwanta na shigo na samay ta na zauna.
Hiran anty salbiya muka dauko take fadin naji maganar mamaki yau ai watau dai ita mace da bauta aka santa a rayuwanta.
Da zaran an daura ma aure baka da wani lokacin kan ka isashe a gidan ka saina bautan miji ke nan wallahi khadija ina fanin kokarin ki sosai.
Ni dake tare dake kadai nasan wanan amma gaskiya kina kokari sosai don ba za a dauke a karamar jaruma ba kan don ko zama gidan nan ai sai mutum ya shirya.
Amma ke gani zaune ba abinda ya damay ki murmushi nayi nace to maryam yaya zanyi abinda yafi karfin ka ai sai ido.
Tace hakane mun kai kusan awa biyu da wani abu ya shigo dauke da ledoji a hannun shi ya miko min tare da fadin.
Kici kisha magani don Allah maryam ki tabbatar da ta sha maganin nan kafin ta kwanta don nasan ta da tsoron shan magani .
Tace zata sha ya dan lakato min hanci na tare da fadin raguwa kawai ji yadda kika fada yau kawai da dan ciwon nan .
Nace yau dai ka sani amma ni na dade yana damu na ai yace to asibiti zan kaiki gobe idan Allah ya kai mu ko yanzun ma don dare yayi ne da munje.
Ya fita yana muna sai da safe muka karba da Allah ya bamu alheri na mike nabi bayan shi don rufo kofa maryam ta nufi kitchen bai fita dakin ba sai da ya dan matseni a jikin shi na zille da dabar na samu ya fita na rufe kofan ina dariya.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Tunda ta shigo gidan ta dan zauna falo tare da tambayan su abubuwa na gidan kamar yadda take masu dan kwana bibiyu .
Hankalin ta ne ya koma kan abinda take son yi tsam ta mike zuwa dakin ta ta barsu a gurin tana fadin zan shiga ciki in huta ban son damuwa yau.
Sun san idan ta fadi haka tana son kebewa ne ita kadai shigan ta dakin ta daga gado ta jawo ruban da ta saka dan bakan da ta haka muna.
Yana nan yadda ta ajeshi sai dai yayi wani abu kamar hunhuna ya shamuke ya bushe sosai ba yadda ta saba ganin shi ba.
Ganin shi a hake yasa tasan daurin da tayi mai yana nan yana aiki a kan mu ke nan ta sauke wani shu,umin murmushi ita kadai a dakin.
Ta mayar dashi dakyau bayan ta kakabe abin yadda ta saba aje shi ta aje tana fadi a zuciyar ta shegiya dangin makwadaita a haka zaki kare a gadin don nafiku maita wallahi ga abinda nake so.
Ba zan zauna ina kallo kizo ki mun kutse a gida ba kiyi yarda kike so sai dai ki gaji ki bar min gida yar iska yarinya kawai.
Gyara kwanciya tayi tana jan tsuki duk da abinda samad din yake mata akan wanan yarinyar da take ji kamar ta shake yar banza ta huta da bakin nacin yarinyar.
Lalai ya zama dole yau su kasance tare da samad ba zata tsaya wani bin dokar likita ba can ita da ko haihuwa tayi da anyi suna take like da mijin ta yanzu za, a kawo mata wani sharudda a kafa mata.
In banda wanan yar banzar yarinyar da tai mata shigen bazata a rayuwan samad har ake wani wai raba kwana shi kuma ya biye mata ina zata iya hakkuri dashi haka, .
Yanzun ma tasan don yakan dayi wasanni da yarinyar ne amma ai ba dai a cikin wani gamsuwa ba tunda tasan ta gama daure shi ta ko ina.
Don har yanzu idan sunyi fada yakan dawo ya lalashe ta su koma daidai ta sauke murmushi tana gyara kwanciyar ta tasan babu wata mace da zata shiga rayuwan shi ya gamsu da ita idan ba ita dai Nafisan ba.
Itako indai tana jin dumus a hantu da account din ta ai komai zata iya yiwa samad din don a zauna lafiya bazata taba yarda wata ta kwace mata wanan dama nata ba har takai ga lasan zuman shi.
Haka ta wuni a kwance duk wani shiri tayi shi a gurin don daren yau tana son ta kasance tare da samad din tane saboda tayi kewan shi sosai.
Da dare bayan ya dawo ne yakai muna kaji da drinks da sauran tarkacen ciye ciye ciyen da ya sawo muna ya dawo falo ya dauki nata ya nufi dakin ta dashi.
A kwance ya samay ta tana waya a cikin yaren su ya fahinci da mutanen su ne take waya a lokacin wanda idan ta fara wayan ba kasafai take aje wayan ba.
Don haka ya a je mata ledojin yana shirin juyawa ya fita ta katse wayan tare da fadin ina kuma zaka again yace daki zan koma ga dan abin tabawa nan na shigo maki dasu ya sake juyawa kamar zai fita daga dakin.
Amma kasan a nan yau zaka kwana dai ko wani kallo yai mata kafin yace kin manta cewa kin kashe wanan ranan da na kwana a dakin Deedar don wani dalili.
May kake nufi da fadan haka amma kuma ni kasan dalilin kwanan ka anan yanzun ai akan matsalana ne ko ?
Wani matsala ina kin samu lafiyan da zaki iya hawa sama yanzu tunda har kina iya hawa ki tafi yin masifa sai zuwa kwana gurina ne zai gagare ki kuma ?
Ban gane inda maganar ka ya dosa ba fa kana nufin don na hau ranan shike nan ina da karfin hauwa ko yaushe.
Yace wanan maganan haka yake a zuciya na don ba zan zauna in tauyewa diyar mutane hakkin ta ba ko yaushe a kan ki ba.
Wani hakki take dashi a kanta idan ma kun kwana din wata tsiya take iya tsinana mata bayan bakar fitinar da ta shigo muna dashi gida tana kokarin mai dakai mace mara amfani ga mata.
Wani kallon mamaki yai mata ya bude baki zai yi magana sai kuma ya fasa fadan abinda zai fadi din yadan girkiza kai ya juya tace dakai fa nake magana.
Yace naji ki kuma naji abinda kika fada ai koma bata yi min komai amma ai dole in tsare mata hakkin ta ko.
Tace tunda kai ka zama dan son ba mace dadi ta ko wani hanya ko to wanan dai ka sani bazaka taba jin dandanon ta ba har ta gaji ta fice don nan ba gidan zaman ta bane.
Yace da kyau kinyi kokari kin san sheri da kikayi ke nan shiya sa kike fadar haka ko wani lokaci ashe , ?
To koma may ye haka naganta nake son zama da ita ko da ko bazan taba more mata din ba balle ma ina morewa a wanin fannin.
May kake nufi ta waro ido waje yace kwana da ita da nake yi ina jin kamshi don ta iya gyaran jikin ta a gurin miji ba sai zata fita take gyara ba.
Ga kuma girki da ladabi da nake samu a gurin ta ga natsuwa da sanin ya kamata da wanan halin kike son in barta haka ba tare da kulawa ba.
Ai kema ki mata adalci mana wanda ke baka wanan abin ai bai kamata ka wofunta shi ba Nafisa .
Kema da zaki daure ku hada kai ku shirya da ita nasan da kin karu da wasu daga cikin ni,imomin ta ai.
Samad ta kira sunan shi da karfi tana fadin agabana kake lissafo min wai abinda kake ji a kishiya ta .
Wallahi maganan nan naka yanzu yasa nake jin kamar in shake yar iskar yar banzan yarinyar nan ta mutu kowa ma ya huta shegiya diyan makwaidaita kawai.
Wani murmushi yayi yana fadin dama na fada maki kadan daga abinda nake samu a wurin ta ne don ki ji haushi kema ki gyara halin ki.
Don duk waban abinda na lissafo Deedar dashi Nafisa baki da ko daya a gurina da sunan kinayi miji yaji dadi.
Filo ta dauka ta jefa mai ya cabe tana dube duben wani abin ta jefa mai ya fice dakin yana dariya samun sa,anta da yayi har taji haushi.
Muryan ta yaji tana fadin zanzo dakin in samay ka ai yanzu kafin da safe ita kuma yar banza in san abinyi akan shegiya.
Kafin tazo ta hanashi hutawa ma ya sa ma kofar shi key ya rufe ya zauna yaci dan abinda ya riko ma kanshi ya kwanta tunda ba girki take mai ba sai sa,a .
Kuma ko tayi ba iya ci yake yi ba don abincin baya gamsuwar shi a bakin shi yasa kullun gikin ta dole sai ya samu wa kansa dan abinda zai ci.
Taje dakin nashi kamar yadda tace ta samu kuma arufe ta soma buga kofan da karfi tana kiran sunan shi ta yarda kowa zai iya jin ta.
Da fushi ya zo ya bude mata dakin ta shiga tana huce ta fara fada dashi akan may zai rufe mata kofa tunda yasan zata shigo.
Ko don yaki kwana a dakin ta kuma bai barta da takaicin hakan ba ya fada mata magana son ranshi ya fito yana zaton zata kyale shine wanan karuwan gidan nashi ta shigo inda yake.
Dariya maganan yaso bashi yace yanzu dai ba kinzo ba may ye kuma nasai kin zagi diyar mutane a cikin maganan mu.
Hararan shi tayi tana kaiwa kwance tace idan ba ka sallami wanan yar banzan ba kaima kasan ba zaka taba samun kwanciyar hankali a gurina ba ai.
Don na tsani na bode ido naga wanan yarinyar a gidan nan kuma kasan ba haka mukai alkawari da kai ba tun farko.
Yace da na aure ki munyi rijejeniyar ban kara aure ne ko may ko yanzu wata zan karo idan naga wace tai min ita ma na fada mata hakan ta kuma sani.
Aure fa kace zaka kara again yace kwarai kuwa Nafisa ina son in gado mahaifina kuma inyi koyi da sunnan ma,aikina ne.
Tofar da yawun ka akan wanan magana ko wanan kul ba dade kul ba jima sai ta fita gidan nan ina fada maka kana dauka wasa ne.
Yace ki tabbatar da ranan tare zaku fita da ita don son ta nake na auro ta haka kema so da tausayin ki ne yasa na aure ki ai.
Shiru tayi ta bashi baya tana tunane a ranta ya dauka ma tayi barci ne sai can yaji tace wai samad may kake nema ne a gurin wasu matan wanda ni banda shi a tare dani .
Yace kina da komai na mata Nafisa amma kuma ai kin sa ra,ayin maza ne haka akwai wasu abubuwa da namiji kan hango gun mace yaji yana son kasancewa a gidan shi da ita.
Banga abinda wanan da ka kwaso zata nuna min ba yace a naki ganin ke nan amma tana da quality din da nake son mace ta kasance dashi.
Haushi maganan shi ke bata idan taji yana fadin magana a kaina don haka ta kyale shi ba tare da tai magana ba.
Kwanciya ya gyara ya kwanta sai saukan hannun shi yaji a ga jikin shi murmushi yayi tare da fadin kin san kina cikin dokan likita dai.
Tace likita shi Allah ne ko ubana ne da zai kafa min wani doka yau na fara cikin in kwana tare da kai ko mai.
Da zamu tsaya bin wani dokan shi can muki farautawa ran mu abinda muke so ni tsausayin ka naji tunda nasan kana bukatan hakan kaga nazo da ba haka ba sai in kyale ka da wacan mara moriyan inga iya gudun ka.
Sai dai ina gudun kaje wajen wata kayi abinda ka kasayi a gidane alhalin ina nan ina da abin a jikina nima.
Har suka gama abinda zasuyi yana mamakin karfin halin Nafisa da bata iya boye zuciyar ta ko kadan don ta fito fili karara ta nuna ita ke da hannu kuma bako shakkan fadin hakan da takeyi.
Yanzun ita a zaton ta ba abinda ke shiga tsakanin shi da Deedar yake zaune haka da ita don haukan ta da zafin kishi ya hana ta kwantar da hankalin ta ta fahinci komai akan haka.
KHADIJA
Mun tashi mun yin sallah akan lokaci sai dai bamu kara kwantawa ba don nemawa cikin mu abinda zamu ci.
Yau tunda na tashi da kewan yan uwa na da iyayyena na tashi har na kasa boyewa nayi wa maryam magana a kan su.
Tace ba kuna waya ba nace ba kullun ba don daddy ya kafa muna dokan kiran su ko yaushe yace idan suna son magana damu su zasu kira mu.
Maryam tace kai daddy ho wallahi da daddy ya fito cikin mutanen da, da yayi tsanani sosai nace ai ko yanzun ma akwai tsanani don duk da aure muke bai hana daddy kafa muna doka ba kuma dole mu bi.
Tace ina son irin su daddy masu tsayawa tsaye a kan iyalin su amma wanan mazan yanzu ai adaiyi dai ne wallahi.
Kamar kin sani abinda nake tunane ke nan irin du AA ai ko tarbiyan yaran su basu da lokacin bayarwa kullun ana gurin aiki.
Tace ashe kema kina wanan tunanen nace ba dole ba maryam tunda ruwa ya gaurayu da jini yanzu ke dai Allah ya shige muna gaba kawai.
Tace AA fa saukin kan shi ne yakai har wanan matar ta samu wuri haka wallahi irin su basu damu da matsa ma iyali ba komai akayi mai kyawo ne hali ne na rayuwan turai kowa na da independent din kan shi.
Nace halin banza ba maryam mutum ya yarda addinin shi da al,ada ya kama na wasu shi abin nasa ma har yai yawa wallahi.
Da na dauka diyan Fati kawai yake kin kulawa sai yanzu nake fahintar ko yar nafisan ma ba wani damuwa yayi da ita ba iyakan shi da ita ya dan kama mata hannun yai mata wasa a tsatsaye ya wuce.
Niko kin ga ba haka na saba dashi ba duk tsananin daddy da kike gani wallahi yana da lokacin iyalin shi maryam idan kin gan mu dashi zakice ba shi bane.
Sai dai idan kayi ba daidai ba yanzu zaka sha hukuncin da bakai tsammani ba a gurin shi komai girman ka kuwa.
Mun karya mun shirya har lokacin bai shigo dakin ba waya na dauka na buga mai ina sallama ya amsa min tare da fadin Deedar kun shirya ne ?
Na amsa da eh tun dazun kai muke jira wallahi yace sorry dear wallahi yau na dan makara ne amma gani nan fitowa ku bani minti goma.
Kallon wayan nayi na kashe maryam dake jin abinda ya fadi tace yau ko dai buzuwa ta murda kambun sarauta ne haka ?
Tsuki nayi ina saka wayan a cikin jakka na tare da diban time din agogon daki naga takwas ya dan gwauta kadan.
Ban dade da aje wayan ba ya sake kara na dauko daga cikin jakka ina dubawa sunan shi na gani again na dauka tare da fadiin hello dear.
Ke ba dear ba abu kazar uban ki kada ki kara gigin kiiran wayaan shi idan kin san muna tare da ke ke har waya baki wanan matsayin da kike son kai kan ki ne a gidan nan ?
Sai da nayi dan murmushi takaici nace wani matayi kike jira kuma in kai tunda abinda ya kawo ki gidan nan shi ya kawo ni nima.
AA ne kuma dole ko kin ki ko kin do mu cudanye shi tare da ke ko kina so ko baki so yadda ya ke murzan ki haka yake murzana son rashi dole kuma anjima ki bar min shi ya murjeni son ranshi.
Karya kike wallahi karuwan cin ki bai kai can ba in fada maki sai dai kije gurin wasu su murje ki amma badai samad ba don wanan kayan yafi karfin irin ki.
Ke dashi sai gani sai hange nace a tunanen ki ke nan ruwa ya dade da gaurayewa da jini zatai magana naji ya wafce wayan a hanunta yana fadin.
Wanan wani irin hauka ne wai wanan wani shashanci ne haka zaki dauki wayana ki kirata kina zaginta wai nafisa kishi haukane halan.
Nace idan kun gama muna jiran ka please sai lokacin ya tuna bai kashe wayan ba ya kashe.
Kallon maryam nayi nace wanan mahaukaciyace wallahi bata da wayau ko kadan ana kira mata hauka yana binta.
Kara zagewa ki nuna mata ke ma fa matar gidan nan ne don Allah cire wani tsoro da kawaici ki din ga nuna mata ke ma kina da power a gidan nan.
Haba abin yai yawa wallahi har da kiran mijin mutun sai an saka mashi dokan haka kuma wanan abin yai yawa wallahi.
Maryam fitinane banso wallahi kuma shi din ya rokeni akan in dinga kyale ta idan tana yi kinga idan ina biye mata sai mu koma daidai da ita.
Tace wani ain ake kyalewa maryam wani kan idan an maka shi yafi gaban kyalewa wallahi tunda ba garejewa yake yana rama maki ba.
Daukan wa kanki mata ki a fito a gwabza tasan kema mace ne kamar ta amma wanan abin nata yayi yawa wallahi.
Maryam nima bashi ba ke damuna sai yawan fadin da take min wai ni dashi sai gani sai hange din shine yake daure min kai da ita wallahi.
Yau idan munje wurin anty Salbiya zan fada mata wanan kalamin ta sama muna mafita akan shi don fadin dz takeyi yayi yawa.
A kin san a tunanen ai tariga da ta shiga tsakanin ki dashi ba zai iya aiwatar da komai na kwanciyar aure dake ba abin da take nufi kenan ba wani abu ba.
Dariya nayi nace badai wanan mugun mijin nata ba da bai san daga kafa ga mace ba da kulun sai ya lalabe ni ya kwashi rabon shi.
Kyale ta surprise zamu bata sai tasha mamaki a gidan nan tasan an dade da tsere mata tun 1900 ita ta makara take haukanta da bugun daji.
Yana gama shiri a gurguje yasan ba abin karyawa zai samu kusan tare suka fito daga dakin sai dai ta riga shi saukowa ne ta zauna falo tana dakon shi.
Yana fitowa ya tunkari kofan part dina tace tana mikewa tsaye samad ina zaka kuma yace gun Deedar mana mu gaisa kuma in fada mata nagama su fito mu tafi.
Daga haka ya sa kai ya shiga ya samay mu muna zaune muna dakon shigowan shi dakin sai gashi gaida shi muka fara na nuna mai kamar komai bai faru ba damu.
Shiko sai kallon fuskana yake ko zaiga na daure mai fuska akan abinda tayi min din nace zamu makara sosai yau wallahi don an kusa shiga lectures yanzun haka.
Muje yace dani tare da fadin maryam kuyi hakkuri don Allah wallahi yau makara nayi yana gaba muna biye dashi muka fito daga part din.
Har lokacin tana tsaye cikin jin fitina shiga na ta fara kallo tana ana mazuru ana shahu da sunan karatu mai zuwa daukan darasine aa hakan mu da muka ga turawa basu bamu tsoro ba.
Juyowa nayi ina mata gwalo kan aiko ta fara sababi da zagi tana goranta min wai a haka zan kare yadda na shigo haka zan fita cikin labani kullun a mota.
Tundaa muka fara tafiya bai wanda yai magana a motar sai can naji yace ki shirya jibine tafiyan mu da safe .
Naa juyo nace Allah ya kaimu lafiya ya sake fadin akwai yan sayayyan da nake son ai su hajiya yau ko gobe zan turo maki da list ki duba ki gani wanda baiyi ba sai ki gyara naji nace dashi.
Amma yau ba zan dawo da wuri ba don zan tafi gyara kaina tunda muna da tafiya a gabana idan nace sai gobe zan iya makara gashi kace zan maka sayayya kuma.
Mun isa maryam ta bude motar ta fita na bude zann fita baji yasa lock din motar na juyo na dube shi da sauri.
Dan langabar da kan shi yayi yana fadin kiyi hakkuri Deedar nasan ba, a kyauta maki ba wallahi bada sanina ta dauki wayana ba na shiga wanka a lokacin.
Ai na sani nace dashi ba komai wallahi zata zo ta daina wata rana da yardan Allah kaidai kai muna addua kan hakan don Allah ji nayi ya rugumoni da sauri nace na makara fa yallabai kadubi lokaci ka gani.
Ina fadi ina aika mai da hararan wasa nace bari matar ka ta biyo ka ta ganka haka yace da haukan ta yayi yawa ai idan ta biyo ni nan.
Zan sauka yace miss you nace miss you too na sauka na rufo mai motar tare da jan guntun tsuki ina fadin munafuncvin maza kawai wani miss dina zakayi can adai tafi a hakan kawai.
Yau ma mun dade cikin makarantar don exam ne ke gabato muna baifi sati uku ba mu fara hakane yasa muke dan jimawa yanzu sai yamma lis zamu dawo gida.
A gurguje na biya gidan anty Salbiya ina sheda mata kwana biyu ba zata jini ba daga nan na wuce wurin gyaran kai haka yasani kai dare ban dawo gidan ba gashi kuma nice zan karbi girki a ranan.
A salon din shiya biya suka dauko ni muka juyo gida dasu tun a mota yake faman matse min hannu na a cikin nasa yana yaba kyau da nayi da gyaran da akai min din.
Mun shiga gida kowa ya nufi part din shi dan rage kayan jikin mu sallah nayi na fito na shiga kitchen don kada mukwana da yunwa.
Cus,cus na dafa muna sai cabage dana yanka da albasa mai yawa acikin don yaba da ma,ana mai dadi.
Soyayyan nama nayi amfani dashi sama sama a ciki ina gaf da kamalawa ne ya shigo kitchen din ya samay ni a ciki.
Saukan hannuwan shi naji a saman weast dina sai na dan zabura kadan tare da juyowa in kalleshi fuskan mu ne ya hade a wuri daya yake fadin may kikeyi yanzu anan ?
Nace abinci na hada muna kada ka kwana da yunwa ya juyo ni gare shi yana fadin wa yace dake zan kwana da yunwa bayan gaki.
Murmushi na sauke tare da girgiza kaina ina fadin kadai baka jin kunya wallahi kana wanan maganan haka a gabana.
Yace au ke kin saura da kunya na ashe har yanzu shiyasa kike son ko yaushe mu kasance a cikin duhu idan kina lalabana ko ?
Ikon Allah nine kuma nake lalabanka ma ashe bakai ba hannu na dana mika in gani idan dahuwana ya sulala yasa shi sake ni a lokacin.
Sai da na kashe gas din na gyara wurin har lokacin yana tsaye yana kallon yadda nake aikin yana tsaye ya jikina jikin shi daga kofan shigowa kitchen din.
Juyowa nayi nima ina kallon yadda ya tsaya din yana saye cikin three quarter fari da rigan armless na shan iska murmushi na sauke a fuska na tare da fadin dan gidan hajiya mama ko yunwa ne haka ya fara damun ka ?
Kai ya girgiza min yace gyara zancen kice dan gidan mommy don hajiyan mu kan na bar maku ke dasu zainab da Binta.
Nace realy yace of course don kun fini fada a gurin ta nace halin kane bata so yasa kuke yawan fada tunda ka zama yaro mai lefi kullun.
Murmushi yayi yana karasowa inda nake na fara ja baya tare da rike kunnuwa har bayana ya tsaya a jikin sink din kitchen din.
Yace fada min laifin da kika san ina mata in ji yanzu don kunfi kusa ni dai ban san ina mata laifi ba nace kayi tunane mana da kan ka.
Hannu yakai kamar zai danko ni na zille daga kasa na fice falo ina mashi dariya falon ya fito yana murmushi tare da girgiza kan shi.
Yace zan kama ki ai sai kin fada min mara kunyar karya kawai ya juya ya fice dariya nayi na girgiza kaina kitchen na koma na hado mai abinci nasa a basket .
Falo na fito nazo na shiga daki wanka nayi na fito na zauna na gyara jikina tare da shafe kusurwan jikina ko ina da turarukan da ke saman mirrow dina.
Na dauko rigar barcina na saka tare da zanin da zanyi sallah asubah dashi da hijjab na daura zanin hijjab din kuma na sa a wani jakka tare da sauran tarkace na na bukata.
Basket din na dauka na kashe wutan part din na rufo kofan gurin na nufi sashen nashi yan gidan suna falo har kullun basu gajiya da aikin saka min ido idan zan tafi gurin shi.
Yauma hakan ne ya kasance dasu kamshi da shiga na ya dauke masu hankali Ihisan ce ta nufo ni tana hausanta da ya dan surku da yaren uwarta.
Dayake akwai kaya a hannu na ban samu taba taba nadai kira sunan ta tare da dan mata wasa na wuce ashe yarinyar ta biyo ni a baya.
Ina jin suna hada baki gurin kwala mata kira ina bude part din uban ta fada ciki da gudu Samiha ce ta biyo bayan mu.
Zaune muka samay shi a dinning di ya tasa laptop din shi a gaba yana aiki a cikin sa jin hayaniyar mu ne yasa ya dago kai yana kallon mu tare da fadin wai may ye haka ne ?
Fuska a daure ya juya ga Samiha din yana fadin may kike nema a nan cikin dan tsarguwa take fadin dama ihisan ne tabiyo wanan nazo daukan ta.
Wani kallo yai mata ta juya da sauri tabar part din ni dai ina tsaye ina jera kayan abincin saman table ihisan din ke fadin Abincine zata ci.
Tare da iban taso suci yaki kulawa nina jawo ta na fara bata a baki tana ci muna hira dasu jefi jefi taci abincin sosai har uban ya tsaya yana kallon ta.
Shigowan Nafisa ke nan gidan aka fada mata yarta na sama wurina sai gata a sukwane ta fado dakin tana huci.
Ke ban yata nan idan kin yi zuciya ki haifi naki yanzun nan an gaya maki haka ake samun diyan a nakashe ko asha a ruwa.
Daga yau nayi maki kashedin taba min diyana sai ranki ya baci a gidan nan kin jawo ta nan don ki lashe mata kurwa kamar yadda kika lashe ma ubanta nashi kurwan.
To kurwan mu kur a kanki mai bakar aniya kawai kina son burge miji ai ba ga diyana zaki burge ba sai ki zage ki haifi naki ki burge shi dasu.
Hankaka maida dan wani naki kin zama bata irin macen sai ci akai masai kullun kinga nan ta nuna cikin jikin ta tace mai kika gani.
To dake dashi a gidan nan sai irin haka watau hange an shigo aci gado a baza diya a gidan to gaba ba a nan ba yar iska mai kutsen tsiya mai hana farin ciki a gida.
Ina zaune na harde hannaye na saman kirji na sai kallon ta nakeyi ina murmushi mai dauke da takaici sai da ta gama nace zakiko sha kallo a gidan nan.
Idan ban sha kallo ba zan sha dariya ai ki matsa idan kin ce naci ne zakiga tsiya a gidan nan yadda kika shigo haka zaki fita daga ke sai ke wallahi.
Murmushi nayi na mike ina hada kayan abincin ta bimu da harara ta matso zata dauki yar ta data dafe uban nata ya dago da idanuwan shi da sukai ja yace kina taba ta ina marin ki wurin nan sai kin raina kan ki.
Ki bace min da gani daga wurin nan kafin in makeki yanzu yarki ce ko tawa idan kuma kika ce tak akan yar nan sai na shayar dake mamaki ke da ita sai idan ta girma ta nemay ki.
Samad akan yata dana haifa a cikina kake fada min haka idan kana son ta rike ya ai kun san yadda ake samu dan kuyi mana kusamu kuma.
Anga ya yar tubul, tubul son kowa kin wanda ya rasa ake son lashe min kurwanta watau kowa ma ya rasa ke nan ko wallahi ba zan jure daukan wanan hukuncin ba a kan ya ta a gidan.
Tana kokarin jan yar ya mike da sauri nace haba dear kabar mata yarta mana Allah yaba kowa nasa ba shike nan ba akan may za, a tsaya ana fada akan ya abinda Allah baison hakan.
Ta juyo gareni tana fadin may kike nufi da haka kanaji ko kaine sheda idan wani abu ya samu yata kotu ne zai rabani da wanan ta nuna ni.
Ta fice da diyar tana kuka wani iri naji a raina amma a fili na wayance ina fadin kai Allah dai ya kyauta naci gaba da hada kayan.
Muna kwanciya yace yarinya bagaki ba yanzu may kika fadi dazun a dakin ki maimaita yanzu mana da bakin ki.
Dariya nayi nace ai maganar ya wuce ko don munyi shi tun acan ai yace to be frack Deedar na rasa may yasa hajiyan mu take min wasu abubuwa na daban wallahi.
Nace ka fasan halin iyayyen mu da alkunyar dan fari ba wani matsala bane kawai kawaici ne take maka a hakan amma ni ban dauke shi wani abin damuwa ba.
Bazaki gane bane Deedar idan ba muna tare da Yusuf ba bazan taba ganin fara,ar hajiya a tare dani ba tun ina jin wani abu har yakai yanzun na saba da haka.
Shine dalili dayasa kikaga ina shuga da Yusuf idan zan tafi nace kai ya kamata ace ka bata hakkin ka na uwa a gare ta.
Har gobe fa kai yaro ne a gurin ta wani shawara da ita ya dace ka zauna kayi shi amma kana nuna kamar kana gudun ta yanzu da shawaranta.
Ya kamata ace kaja yan uwan haihunka a jiki ta wanan hanyar na tabbatar da idan ka gwada zakaji dadin ta sosai amma ba dadi ace naka nada shi a gida amma baiwa yan uwan sa abinda ya dace.
Sun bukaci wani abu ne a gurina ban masu ba a, a gaskiya yaya AA kasan fa irin tarbiyan gidan ku bazasu taba rokon abu ba kaima ka sani.
Iska naji ya furzar daga bakin ya sauke ajiyan zuciya yace na yarda da maganan ki don Bintace ta taba rokona in saya mata laptop tun farkon shigar su school.
Ban san abinda ya matar dani daga saya mata sai yanzun nake tuna wanan abin nace ka gani kuma nasan hajiyar ce zata kwaba mata kada ta sake ma magana tunda ta fada ma da farko.
Idon shi ya lumshe na tsawon wani lokaci shiru dakin yayi na wasun sa,oi kafin yace wai ke ina kika san wanan abubuwane haka ?
Baristet khadija Adamu ce a kusa dakai yace natuna dama ance nine farko da za a fara lauyewa idan an zama barister nace dane ai.
Yace au yanzu kin fasa ke nan nace kila don ban tabbatar ba ya kara sauke ajiyan zuciya yace think before tommorow may ya dace in wa Fauziya da Fa,iza .
Wai ka bani aiki mai wahala saboda ba sabawa nayi dasu ba kamar binta da zainab don ko gidajen su ban sani ba.
Amma ina ganin zaiyi kyau inda hali kakaisu saudiya ko ka gyara masu dakunan su da dai sauran su yace insha Allahu da halin yin duka ma don yan uwana da iyalina nake neman kudina da zufa na.
Nace amma may yasa bakai wanan tunanen ba tun farko sai yanzu yace nima ban san dalili ba Deedar yanzu dai ne da muke wanan magana abin yazo min a rai na.
Allah ya kyauta nace mai yace amin yana kamoni jikin shi dasafe da muka tashi bayan mun idar da sallah ne na duka na gaida shi kamar kulun yace kibani accout din ki zan tura maki kudi ai sayayya azumi ko nan ko idan munje kaduna.
Don ban sa zan koma ba kafin azumi Allah ya saka da alheri idan mun dawo sai ki saya ma mutanen Niger nasu driver yakai masu can.
Shiru nayi nama kasa magana a lokacin sai can nace angode ubangiji ya kara ma arziki albarka yace amin mikewa nayi na fice daga dakin zuwa part dina.
Yinin ranan busy nake sai yamma na dawo a gajiye ga jikina banjin dadin shi amma haka na daure naiyi ta zirga zirgan tafiyan da zamu gobe.
Washegari na shirya tsab shi kawai nake jira sai da ya leka office din su ya dawo muka dauki hanyar kaduna wanda kafin mu tafi din sai da suka kwasa da nafisa a gidan.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Kamar kullun yau ma shigan dare mukayi garin inda kai tsaye gidan shi muka nufa da kyat naga mun kawo kaduna din don wani irin amai dake taso min a motar yayi magana na nuna mai kaina ke ciwo kawai.
Motar na tsayawa na fitaa da sauri na rigashi shiga gidan don jirin da nake ji a lokacin banyi tsammanin anty Fati tasan da zuwan mu ba
don yadda muka samay ta ba a cikin shiri ba.
Ganin mu yasa ta fara dan kamay kamay tana fadin ashe kuna hanya tafe ne yau nace eh ina zama saman kujera.
Dafe da hannu na akaina karshe ma kwantawa nayi don jirin ya sake ni shigowwaan shi gidan idon shi ya sauka a kaina.
Dashi da Yusuf suka shigo wanda ya wataa biyu bai abuja a lokacin yana waje wurin wani business da AA din ya tura shi yai masu.
Lafiya may ke faruwa yake tambayana cikin kura ma inda nake ido har suka kara so gare ni Fati tana mashi sannu da zuwa ya amsa mata sama sama.
Har ya iso inda nake kwance ya dan duka yana taba jikina tare da fadin may ke damun ki ne kuma ?
Yusuf ya tambaya dama banda lafiya ne da muka fito gida yace lafiya take sai dai ina ganin tun a motar ne bata jin dadi zuwa yanzu.
Yaran ne suka fito daga dakunan su ganin mu yasa su jin dadi sukazo wurin uwar su suka tsaya suna kallona suma.
Har lokacin ban iya daga kaina ba ina a yadda nake kwance ko muje asibiti ne Yusuf ya fada sai lokacin da naji ya ambaci asibiti na dago kaina da idanuna da suka kada sukai ja nace jiri nake gani kawai amma lafiya ta kalau.
Ok zai sake wani lokaci haka yakewa mutum ai idan ya kwana biyu baiyi tafiya ba ya hada min da fadin sannu na gyada mai kai.
Daga inda Fati take zaune ta jefo min sannu na amsa mata tare da karfin halin fadin Affan kuna lafiya ina mika masu hannu su zo gareni.
Affan kawai yazo shi karamin yaki zuwa inda nake din na rike hannun Affan din ina gaida shi sai yayi saurin fadin sannu anty ya jiki.
Murmushi nayi nace da sauki Affan kunyi hutu ne yaron ya gyada min kai tare da fadin eh munyi hutu last week.
Zama AA din yayi saman kujera ina jin ta kara gaida shi ya amsa gaisuwan nata ya kara maida haankalin shi a inda nake kwancen yace.
Ko ruwa baki samu kisha ba don gidan ba,a iya ba boko ruwa ba ki daure ki shiga ciki kidan watsa ruwa ko jikin naki zai sake maki.
Namike batare da bata lokaci ba na nufi hanyar hawa saman ida dakunan kwanan gidan suke tare da ciro key a cikin hand bag dina na bude dakina na shiga.
Dakin yana nan kamar yadda yake sai kura da yayi saboda rashin mutum a cikin sa na kwana biyu da ba a zauna ba na bi dakin da kallo na rasa ta ina zan fara da dakin.
Zanin dake saman gadon a shimfide ya yaye na jefa ga abin zuba wanki dake gefe daya aje a dakin na nufi ban dakin akwai ruwa kamar ko yaushe duk da yanayina sai dana wanke bandakin don in akwai abinda na tsana shine rashin gyara bandaki.
Na fito na dauki tsitsiyar dakin na share jakkana ba bude na fito da sabon zanin gado a ciki na shimfida na feshe dakin da room fresh ya dauki kamshi a lokaciya daya.
Ban daki na shiga a can na tube kayan jikina wanka nayi tare da dauro alwala na fito na tada sallah ina gamawa na haye gado na kwanta duk da yunwar da nake ji a lokacin.
Barci ne ke son dauka na naji an shigo dakin tun daga kofa ya fara magana yana fadin har kin kwanta ne ko ?
Kin ci wani abune da kika kwanta haka na da yunwa ?
Ko baki jin yunwa ne yanzu da kika kwanta hakana ?
Ya karaso bakin gadon tare da zama yana dan taba min jiki nace ai ba zazzabi nake yi ba gajiya ce dai kawai ya kama ni kamar yadda yayana Yusuf yace.
Har wani tafiya zakima gajiya haka kamar wace taje Egypt da kafan ta akawai dai wani abinda ke damun ki may be ulcer din kine ke son tashi maki kuma.
It may be don yanzu danayi some a hours banci abinci a kan lokaci ba haka yake min naji yace kai wanan ulcer da tonon asiri yake bai tashi kamaki ba sai yanzu da kike gida.
Ya sake kai hannun shi saman wuya na cikin dan shagaba nace dashi haba ya AA don Allah ka bari barci nake son yi fa yace ba zakiyi barci ba sai kin samu a binda kika sa a cikin ki tukun na.
Bari Yusuf ya dawo yanzun nan ya fita ya samo muna abinda mukaci nace laifin ka ne ai dabaka bugawa Anty Fati waya kana tafe ba yau da ta maka tanadin abinda zamuci.
Tsuki naji ya buga tare da dagawa daga rankwafen da yake a kaina yace wai ma ko kin sha ruwa da muka iso nace banjin kishin ruwa ai dana sha ko.
Fita yayi daga dakin sai gashi ya dawo dauke da goran ruwa da cup a hannun shi ya zauna a bakin gadon tare da fadin oya tashi kisha ruwa ko da kadan ne.
Cikin yanayin jin jiki nace har yanzu fa jiri nake dan ji ban son in daga sosai wallahi yai kamar ya tallaboni na mike da sauri tare da fadin kana son mushiga hakkin da ba namu ba ke nan.
May ye kuma na cin wani hakki anan din na karbi goran ruwan ba tare da nayi mashi magana ba na tsiya na shanye na mika mai cup din.
Ina kawai kwance kallo ya bini dashi har na kwanta ya ja tsuki tare da fadin kai dana san wanan tafiyan haka zai zama maki ai da banzo dake ba wallahi.
Zanyi magana wayan shi yai kara ya duba tare da mikewa tsaye ya bar dakin bai dade ba sai gashi ya dawo dauke da leda a hannun shi.
Take away ne na karba tare da godiya ya tsureni da ido yana fadin tashi mana kici sai ki kwanta dole na tashi na sauko a kan gadon bandaki na shiga na kurkure bakina na wanko hannu na fito na samay shi a zaune.
Sai da yaga na zauna kasa ina bude ledan ya tashi ya fita daga cikin dakin tare da fadin kici sosai fa don Allah sai da safe nace yace ba yanzu ba ai.
Kilama anan zan kwana tare da ke da sauri nace rufa min asiri don Allah mu rabu lafiya da anty Fati yadda nazo yace ita bata san ciwo bane halan ?
Yana fita na mike nayi ma kofar key na dawo na zauna ban iya cin abincin ba don dandanon shi bai min ba na ture gefe drinks din na dan sha namike na kurkure baki na kashe wutan dakin na kwanta bayan nasha magani na .
WASHEGARI
Wasai na tashi banji komai ba bayan nayi sallah na koma na kwanta har inji motsin mutanen gidan in fito mu gaisa dasu.
Anan kuma barci ya kara dauka na gurin bani na tashi ba sai goma da wani abu mamakin barcin da nayi haka naji na mike na shiga wanka na fito har na shafa mai ina shiryawa naji ana kwankwasa min kofa.
Na tuna tun jiya kofan yana rufe na bude Laraba mai aikin gidan nagani tsaye a kofan tana dauke da kayan abinci a hannun ta kula guda biyu.
Murmushi na sakar mata tare da kai hannu in karbi kulan tace haba hajiya aiki na ke nan ai gidan nan ta shiga dashi ciki ta aje tare da fadin yaya karfin jikin jiya kun iso ance baki da lafiya.
Nace nace naji sauki mama na gode ta juya zata fice daga dakin nace mama don Allah fita da wanan kayan abawa mai ci shi a waje.
Ta duka tana daukan kayan ta dan bude tace a, a hajiya ai ba sai ankai waje ba ma ni nan ina da bukatan shi yaushe rabon da inci nama haka a gidan nan sai idan Alhajin gidan nan yana gari koshi baifi inci tsoka biyu ba don matar gidan kan raba idan na gama.
Murmushi nayi nace ayyah dauka to kije dashi amma sai kin dumama shi don yayi sanyi tace bama zan tsaya dumamawa ba wani ya ganni dashi.
Ta fice ta barni da mamaki a raina tare da tambayan kaina amsan da ba mai bani shi a lokacin na gama shiri na bude kulan abincin data aje min doya nagani busashe sai dan kwai a ciki da baida yawa.
Dayan kulan kuma jeloup din taliya ne ne kai na girgiza don ban iya cin ko daya daga cikin su dama akwai kayan tea ne sai insha tea din in tashi.
Bakin gado na koma na zauna na tasa kayan a gaba ina tunane kala kala a raina naji an turo kofan dakin AA ne ya shigo dakin.
Da alama ba daga barci ya tashi ba ya nufo inda nake zaune kafin ya karaso nace ina kwana bai amsa ba sai da ya karaso inda nake.
Kin tashi lafiya yace yana taba fuskana tare da fadin ya jikin naki da sauki nace ina dago kaina gare shi.
Hajiyan mu tana gaida ke da jikin da sauri na dago ina fadin ka fada mata ne kai ko yace eh nace tare muka zo amma tunda muka iso baki jin dadin jikin ki ne kina kwance.
Nakan naji sauki nace dashi yanzun ma nake son shiga can in gaida su daga nan in wuce gidan ya Amina itama in gaishe ta.
Har kinji saukin yawo haka ne nace naji ai dama ba ciwo nakeyi ba gajiya ce kawai ta kamani dama.
Idan kin shirya sai ki magana a kaiki yace kin ma karya kuwa yana kallon kaya abincin kai na girgiza mai tare da fadin banjin cin wanan da akayi sai idan naje gurin mama zanci.
Tsuki yaja tare da nufar kulan yana budewa sai ya daga ya kara jan tsuki bai iya magana ba ya fice daga daki bin shi nayi da kallo har yafita na sauke ajiyan zuciya na mike na dan kara gyara jikina na dauki hand bag dina na fita.
Ina sauka faln na samu ya fito daga dakin Anty Fati rai a bace na fito nace dashi ya dago ya kalle ni idanuwan shi sun canza launi a lokacin.
Ya amsa min da kyat tare da fadin muje in sauke ki ban gaisa da anty ba nace mai bai yi magana ba sai kama hanyar fita waje da yayi.
Ni kuma na wuce dakin anty Fati din da sallama na shiga dakin tana zaune saman dogon kujeran dake dakin nata tana gani na ta kakaro murmushi a fuskanta da kyat.
Cikin dan rusunnawa na gaida ita da kwana ta amsa min da lafiya nace zan shiga gidan su hajiya in gaida su tace min a dawo lafiya karamin dan nata yana zaune yana cin irin doyan da aka kai min din.
Nace daddy ba magana ko san mun doya inci ya dauki kwanan ya nufi uwar shi tare da jingina jikin shi da nata sai na dawo nace mata.
A waje na samay shi zaune cikin mota yana jirana na bude na shiga ya ja motar muka tafi duk da bawani nisa bane a hankali yake jan motar.
Mun kai na bude motar zan fita naji yace dani kayan da kika zo dashi suna nan a cikin mota sai kin dawo ki zauna ki kasafa.
Nice mai kasafa kayan kuma ya gyada min kai da alama har lokacin yana a cikin fushin da yake yi don shirun da naji yayi min har muka zo gidan banda wanan maganan bai kara wani ba.
Fita nayi daga motar na shiga ciki ba tare da na tsaya wani abu da Anty amarya na fara cin karo a gidan tace a, a khadija ashe tare kuke da babangida .
Nakai kasa ina gaida ita daga nan bayan mun gama gaisawa na nufi dakin hajiya umma na gaida ita a na dan kai minti goma na fito zuwa dakin mommy .
A gurin mommy na dade don na samu ya buga mata waya ta hada min abin karyawa don ban karya ba na fito don haka na samu kafin in shigo wurin ta tana hada min breakfast.
Ban fita gurin ta ba saida ta tsare ni na karya muna hira da ita wanda hiran bai shafi komai na rayuwan zamana gidan AA ba ko wani nasa sai hiran Abuja dana karatuna.
Nagama nace barin gaida hajiya mama tace ai tasan kina nan kina karyawa tun a kofa nake jin hayanin su zainab da Binta.
Da sallama na shiga duk suna zaune a falon da ihu Binta ta taso ta rungumay tana fadin tun dazu naso zuwa dakin mommy wai zamu hanaki karyawa da kyau.
Kasa nakai na fara gaida sarakuwan nawa tana amsa min cikin dadin rai cike da kulawa a gare ni bayan gama gaisuwan ne zan juya wurin zainab hajiya mama tace min.
Khadija kina sakaci da cin abinci kina haka kada wani ciwo ya samay ki fa mace mai lalura karami irin naki ba,a son tana wasa da cin abinci.
Duk ido suka zubo min ni kaina ban fahinci mai hajiya ke nufi ba a lokacin tace wanan abin abin farin ciki ne aure a bazata haka gashi kuma an samu karuwa.
Na dago kai na kalli hajiya mama da sauri sai kuma na dukar da kaina kasa cikin kunya.
Binta da ke manne danu tace min ko kuma zaki ma hajiyan mu mussun haka ne kin fa san hajiya ko cikin kwana daya ne tana ganewa a jikin mutum.
Dakuwa hajiya tai mata ta rufe baki tana dariya sai hajiyan ta kawar da zancen da fadin nace ya fada maki zancen kawo kayan zainab da za,ayi gobe.
Nace eh mama ya fada min shine ma nace dashi ina son zuwa ta karbe da fadin sai ya hanaki ko ya kirani kuma yana fada min wai zaki zo amma ya hana.
Dana san kina cikin wanan halin haka ai da ban sakaki wahala ba wallahi tunda lefe ne kawai za a kawo ba wani buki za a yi ba.
Mama nu fa lafiya nake shine ya fada maku banda lafiya don gajiyan motan da na iso jiya dashi kawai ya dauka wani ciwo ne.
Ikon Allah irin wanan lalurar ai ciwo ne babba khadija Allah dai ya rabaku lafiya ya bamu mai albarka ai kinyi kokarin zuwa haka wallahi.
Kunya da nauyi ne ya kamani sosai a gurin kamar kasa ya bude in shiga naji alokacin ta lura da hakan tace gashi kin zo khadija.
Idan yan uwan ki sun karaso sai ku tatauna abinda za, a tari bakin dashi gobe koda yake gida ne duka amma hakan ai ba zai hana ai masu wani abu ba.
Tunda yanzu abin ya zama kamar al,adan aure , wasu ma saboda wanan zasu matsa idan za a kai kaya aje dasu .
Nace mama akwai kayan da muka zo dashi wanda yace na azumi ne za,a raba suna cikin mota har yanzun ba,a sauke ba.
Ya fada min Allah dai yai maku albarka ya kara yawan arziki ta hanyar alheri nace amin mama tace yace kece kika san kan kayan idan kin huta sai a ba kowa nasa kamar yadda kuka tsara nace mama dadai akawo nan din sai a raba zaifi.
Tace da sauri a,a ku barshi can idan kin samu lokaci ku raba a can a aiko ma kowa da nasa idan kun kawo nan ganin laifin juna za, a dinga yi .
Shiru nayi ina nazarin maganan ta sai dai a fili cewa nayi to mama ta katse min tunena da cewa Allah dai yayi albarka ya rabaki da cikin nan lafiya kin yi kokari khadija kwai mafalkina yana shirin zama gaskiya a kan ku.
Tun yanzu na fara hango alherin wanan auren a tsakanin ku yau ga babangida a dakina tun safe har wani lokaci muna hiran matsalan shi dani.
Kin san bai iya boyo ba shi da yasan ina mamaki ganin ya dade a zaune tare damu sai cewa yayi wai ke kika saka shi kin san halin mijin naku haka yake abu kamar dan fari ashe shi.
Muka sa dariya da Binta zainab ta dago tana kare dan uwan nata dacewa hai hajiyan mu kina fada mata kuma don ta raina shi.
Binta ta cabe da fadin ai khadija ba ta da raini ga mai rena shi dai can yar haure hankaka maida dan wani naka sai lokacin hajiya take tambaya cikin katse muna dariya.
Tace tasan da cikin jikin ki kaina dukar kasa tare da fadin ban sani ba nima mama na dan kwanta jikin Binta ina fadin nii fa banda komai wallahi.
Binta tace hajiya kinji mai take fada wai bata da komai wallahi kiban dakine ko inji hajiya mama duk muka sa dariya.
Shigowan su anty Fauziya ya katse muna hiran wanda dama na matsu abar zancen sai dai cikin zuciyana tunane fal ke damuna kan maganan cikin da mama ta ambata min.
Gaisaw mukayi dasu suna min yaya hanya Anty Faiza tace ina buzuwar gidan ku yar sheri nace tana lafiya sun shiga aibanta tane hajiya ta katse su da fadin ku bar wanan dabi,an tunda zaune take da dan uwan ku.
Kuma ta fatan shiryuwa idan zata shiryu banji kowan ku ya tabayi yar ta ba wanda jinin ku ne ita ai laifin uwarta bazai shafi yarta ba ko.
Tunda yar jinin ku ne ita don haka ta samu ragowan wanan yar da abinda ke cikin ta yanzu tunda dan uwanku ya dauko yaya za a yi sai hakkuri kowa da halinsa ake zama dashi.
Dazun ya tashi nan ya kawo min karan Fati sun zo bata basu abinci ba yau da safe kuma tasa laraba masu abincin banza.
Kunga ke nan kowa da nasa halin ake zama dashi araina nace saura ni aji nawa problem din gaba tunda yanzu anji nasu su.
Dangin miji akwai matsala sai naji hajiyan tace wanda kuma anan ita fati ta fishi gaskiya don dana kirata ina mata fada cewa tayi bai fada mata zuwan su ba.
Kinga ta fishi gaskiya laifin ta daya da bata tashi cikin daren ta sama masu abinda zasu ci ba ta bari aka je waje sayowa.
Hajiyan mu kin san halinta fa da shegen mako yanzun haka bata saya ba ma sai dai a turo mata da kudi ta haye sama ta zauna tabar yara da yunwa inji Faiziya.
Fa,iza tace ita kan tana da matsala wallahi bata ci bata bari na tare da ita yaci kuma ba a gani a jikin ta shine matsalanta.
Hajiya mama tace Allah dai ya kyauta haka abubuwa sukan zowa mutum wani lokaci ta baibai binta tai caraf tace saura musan matsalan khadija kuma.
Hajiya tace diyata bata da matsala insha Allahu sai dai wanda ba,a rasaba yanzun dai kuyi abinda ya kawo ku muji yaya za, a yi.
Hajiya yaya kika tsara abin ne inji Faiza tana tambayan mahaifiyar tasu wani abu zan tsara kuma yanzu gaku ga khadija sai dai inda gyara in gyara maku idan kun da bukatan hakan.
Sunyi ta tsara abinda zasuyi ni dai ina sauraren su tunda ban san kai ba sai in sun tambaye ni ince yayi daida.
Karshe nayi masu sallama akan zan leka gidan ya Amina na barsu a dakin zainab da binta suka taka min muka tafi.
Ya Amina ta riga da tasan da zuwa na garin a gidan suka barni bayan mun dan zauna dasu suna fita ya Amina ta kalle ni tace khadija ciki ne dake ?
Kai ya Amina haka ma mama fa tace min yanzu ina ciki don Allah anan banda abin ku tace cikin murmushi gashi ko har ya fito ana gani.
Ganin may kuma ina shafa tunbina da hannu tace wai ke da gaske baki da komai ko may don Allah ki fada min gaskiya duk alamomin ki sun nuna ciki a jikin ki wallahi.
Gabana ya fadi ina kara kallon kaina nace haka fa kowa ke fada min ya Amina tun a abuja tace rabon ki da mesturation wata nawa yanzu ?
Nace nima har na manta wallahi kin san tun ina gida yakan min haka wani lokaci ai shiyasa ni ban damu ba.
Tace kajiki da wani shirmay yanzun a gida kike ko a gidan mijin ki da zaki fadi haka tsaya inzo tace tana mikewa tsaye ta shiga dakin ta.
Sai gata ta fito da wani takarda fari mai dan tsawo a hannun ta ta kokarin yaga ledan tace na sawo shine da nake ganin kamar cikine dani.
Sai kuma kafin in amfani dashi sai ga jini yazo min na aje ashe da rabon ke za aiwa gwaji dashi tashi kiyi fitsri mugani ki dan debo cikin wani abu mu gani.
Nace fitsarin nawa kuma ya Amina tace eh mana tunda ke har yanzu yarinya ce baki san komai ba don wauta irin naki .
Kina kwana da namiji ki tsaya gardaman abu gashi kirikiri ana ganin shigar ciki a jikin ki kina gardama kuma.
Shiga nayi ban dakin nayi na kawo mata kamar yadda ta bukata ta saka tsinken ciki sai gashi ya nuna alaman wata uku ke na yanzu.
Nashiga uku na furta tare da kara tambayan ya Amina din nace ya Amina wai ciki ya nuna ina dauke dashi don Allah ?
Tace bagashi kin gani ba da idin ki kina tambaya kuma tana fadi tana dariya kai na girgiza mata ina fadin wallahi ya Amina da matsala.
Ni ina zankai wani ciki can yanzu ina tsaka da wanan karatun na ga rikicin wanan gidan nashi ba mai karewa bane kullun.
Kai amma khadija ke har yanzun dai yarinyace wallahi shiyasa nake matukar tausaya maki a gidan nan wallahi iyakar ki baki amma idan kinyi wani abu sai mutum yaji kamar ya mangareki don haushi.
Yanzun saboda karatu zakiki gina rayuwan ki ko saboda matsalan gidan mijin ki sai ke ki, ki haihuwa yadda kowa ya haihu dashi a gidan.
Idan kina barin wanan wautar ki bari tun wuri kada ki kuskura ki bari mijin ku yaji wanan shashancin naki don duk yadda yake son ki zaku samu matsala dashi.
Ya Amina ni bama zan yarda ya sani ba sai dai idan wani ya fada mashi ko ya gani da idon shi ni kunya ma ai ba zai barni na yi maganan dashi ba gaskiya.
Shawara tayi ta bani barci nayi sosai har yayi ta kirana a waya ban sani ba sai dana tashi yin sallah ne nags kiran shi a wayana har uku.
Na kira shi fada ya fara dani wai ina na shiga haka waya na ruri ban dauka ba tun dazu nace barci nake kuma wayan na cikin jakata ba, a ji.
Yace ok yanzu kina ina nace gidan ya Amina na nake yace ok ganiman zuwa daukan ki ki dawo gida hakana tunda baki jin dadin jikin ki.
Naji sauki fa nan kuma ai gidane gare ni ya kashe wayan dole na fara shirin komawa gidan ba a dauki lokaci ba sai gashi har ciki ya shigo ranan suka gaisa yai mata alheri muka tafi.
Ina shiga motar ya kalle ni baya ya zauna yake fadin kinga yar uwar ki kin manta da mutane ko nace kai da ke ganin naka kullun fa.
Gidan ya kaini bai bari na shiga gidan su ba in masu sallama gidan shi muka nufa a falo na samu su Anty na dan zauna nagaida su na haura sama dakina .
Kayan jikina na rage na dauko wani dongon riga baki nasaka irin mai matse jiki din nan watau hook gaban mirrow naje na kalli kaina ina mamaki kai ni daya a dakin.
Kallon cikina nayi naga yana nan a lefe nace abin da mamaki wallahi ya za, ace wai cikine dani ina shafan cikin nawa.
Wani abu naji cikin ciki na da jikina gaba daya ya amsa min abin na motsi bol bol daidai inda na dora hannu na akai.
Tsoro naji nayi saurin cire hannu na saman cikin ina mamaki da abinda naji yayi din na kara dora hannuna ya dan kara yin hakan again.
Nafisa buzuwa ce ta fado min a rai ashe duk gorin da take min Allah ya riga da yayi nasa ikon akai na ko ita ke nata kalar shirmay.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Yau da wuri na tashi na fada kitchen sai da na gyara komai na dora girki lafiyayyen abin karyawa na dora da dan abinda na gani a kicltchen din ina aiki zuciyata fam da tunanen yadda na samu kitchen din nasu.
Na rasa ta inda laifin yake shin daga bangaren AA ne ko na anty Fati sai dai zuciyana tafi bashi laifi don shi nake zargi da rashin basu kulawan da ya dace dasu.
Tausayin uwar da yayan tane ya kamani a raina na duba yadda acan yake aje muna komai amma nan ba makamancin irin sa kafin wani abin yakai rabi ya kara labto muna irin sa don amfani.
Sai nazo na samu anan ba haka abin yake masu ba a store kan gaskiya ba laifi don akwai komai na kayan masarufi sai dai a kitchen ne irin su nama mai wadattace da saura kayan amfanin gida ga mace duk sai a hankali.
Muryan Laraba ne ya katse min tunane tana fadin hajiya ashe har kin fito ina jiran fitowar uwar dakina ne ta fada min abinda zan yi shiyasa ban fito ba.
Nace basu fito ba nima karanbanin nayi na shigo aikin don kada a makara hajiya hakan ba karan bani bane tace min don hakan na da kyau Allah yasa a dore da hakan .
Murmushi nayi nace mama laraba don wanan aikin ai ba komai bane don mun riga da mun horu da aiki tun a gida.
Nace yanzu ko za, a samu masu kayan miya don naman kai nake son a sayo muna ta amshe da may zai hana hajiya yanzun sai in je nan bakin kasuwa zan samay su sun fito.
Daki na koma na dauko kudi na bata tare da lissafa mata abinda zata sayo muna kudin ta kalla tare da fadin hajiya kudin sun yi yawa ai.
Nace ki je dashi ki sawo na yadda ya dace don gobe ma da jibi sauran canji kyayi amfani dashi tace kai madallah barin yi sauri in dawo.
Ta juya zata fita nace kuma kada muyi rashin hankali da ki dan saurara matar gidan ta fito muji ra,ayin ta.
Kai hajiya dai ai tasan da irin hakan dole ne idan miji yana gari dole a gyara mai balle irin mijin ku mai yawan jama,a nan barin yi sauri in tafi.
Nace to shike nan sai kin dawo naci gaba da aikin gabana cus, cus nayi na da ganye don shi nake ganin zai dan ciwo da safe ga kowa sai ferfesun sauran kayan cikin ragon da na gani a fridge din.
Daga baya na dora ruwa tea wanda na saka kayan kamshi a cikin sa sallaman mama laraba ne da har ta dawo daga aiken da nai mata din.
Nace mama abin ba wuya har kin dawo tace aikin abin hawa ne ai kuma a nan kasuwan cikin unguwa na tsaya don in sauri.
Nace na gode mama ga abin karyawa nan na hada sai ki dibi mai isar ki ki zuba wa kanki kafin in kwashe ma saura tace ai ayi haka dadai kin zuba min yadda aka saba zai fi.
Tana miko min canjin da ta dawo dashi nace kai mama banace ki bar canjin ba yanzu dai nuna min kulan da kuke zubawa direbobin abinci idan sun zo dana maigidan.
Ta nuna min wani karamin kula nace kai haba mama su uku ne fa wanan ko mutum daya ba zai isa ba ai na jawo wani babban kula na zuba masu a ciki karamin shi na zuba masi ferfesun kayan cikin.
Nace mama sai akai masu ko tace to yar albarka ta dauka ta fita na gyara kulan da na zuba masu AA da Yusuf tare da na Anty Fati da yaran ta sai kuma laraba a karshe na cika mata kulan data nuna min na direbobi da farko.
Sai kayan tea din da na gani na ce idan tazo sai ta dauka mu a dauko wani ai amfani dashi cikin wanda za a rabawa mutane da muka zo dashi.
Ta dawo nace ga ruwan zafi nan akai masu sai kice su dauki gwangwani madara da millo a mota da suga na amfanin su ne tace to hajiya tana washe baki.
Ta dauka suka hade da Anty Fati take tambayan ta ina kuma zaki da wanan tace aike na akayi hajiya amaryan ku tana kitchen din.
Bin laraba tayi da harara ta nufi kitchen din ganin ledan cus cus a dustbin din kicin din cike ya hanata min sallama sai cewa tayi wanan ai barna ne duk wanan ledan cus,cus din may akayi dashi haka ne ?
Fuska dauke da murmushi na juyo gare ta ina fadin anty kin tashi ina kwana ta amsa min sai kuma ta kara maimaita maganan ta gare ni wanan cus cus haka da aka dafa fa?
Nace anty amfani nayi dashi wurin hada breakfast tace amma wanan duk ina za a kaishi haka kamar abin ya zama barna nace yi hakkuri anty gani nayi kamar zai isa .
Ta nufi kitchen din tana bude kulan abincin na fara mata bayanin komai ok kawai tace fuska a daure ta juya wurin ledan sakon da laraba ta sayo min tana fadin wanan kuma fa.
Nace wanda zan muna amfani dashi ne da rana tace shiya bada kudin ko ya sayo nayi kasa da murya nace nice na aiki laraba ta sayo su yanzu shi bai fito ba ai.
Tace Ok tana ja da baya sai gashi kitchen din da kansa yace na duba daki bakya ciki ashe kina nan ina kwana nace mai ya nufo ni ba tare da ya amsa min ba.
Ya dan kai hannun shi a saman wuya na yace jikin yayi sauki ko nace tun jiya ai na watsake sosai wanan aikin da kikayi haka ai yanuna alama.
Yanzu kuma may kike yi nace abincin rana zamu dora don kasan bamu da time yau sosai laraba ta shigo ganin da gwangwanayen kayan tea danace ta dauko a mota tana ganin su sai zata juya nace.
Yawwa mama sai ki aje a dinning barin fito da wanan kayan nace da ita anty fati tace da ki bari tazo ta kwashe ai yana fita ya juyo yace mata sai aikin bada commad baki iya motsa jikin ki ke ko kadan.
Nace ai ni kamata inyi tunda ina nan ita kuma ta huta ko ya wuce bai ce komai ba waje ya nufa nasan gun direbobin shi ya nufa su gaisa.
Mun gama jera komai muka dora girki abincin ranan da za a ci suna falon ya turo Affan ya kirani nazo.
Zaune suke sin fara karyawa na gaida Yusuf da kwana yace a, a kanwata wanan irin girkin haka tun da safe gaskiya naga wuyan mutumina yana dada kauri yanzu.
Murmushi nayi nace aikin su anty na ne da buzuwa idan kaga haka tana gefe zaune da yaranta suna cin abincin su hankali kwance tace wata fati aikin kune dai amare masu lokaci.
Murmushi nayi nace ni inani ina wanan aikin haka na samu abiku da a cikin yanayin sa AA ne yace ke zauna ki karya nace nasha tea a kitchen yanzu na gama karyawa.
Wani kallo yai min nayi saurin fadin Allah ko baka yarda bane anty fati tace may nagaya ma Yusuf yanzu ka gani shine ma mai sata ta karya ai.
Kamshi a duke baiyi magana ba sai nine nace ai anty ya rigaki ne don ke ya kamata ki min maganan karin.
Tace to angon ki ya rigani ai don shi yasan zafin ki fiye da kowa anan gane manufar maganan ta yasa nayi dariya tare da wasance maganar nace ni abincin daddy zanci ina nufar inda yaron yake zaune yana ta aika cibi a cikin shi.
Yana ganin na nufo shi ya jaye plate din shi yana fadin banyi banyi dariya aka kwaishe dashi Yusuf yace in banda abinka daddy ai ita ta girka ma zakai mata rowa kuma ko baka son ta karama wani ne.
Sai ya miko min plate din nace na koshi ci abincin ka baba na fada ina juyawa zan bar wurin yace kunyi magana time din da za a shigo da kayan Yusuf nasan sani don zamu zaria ne yau ?
Nace eh to naji kamar suna fadin Four na yamma ko yace ok lokacin mun dawo ke nan don naga yayan naki a zumude yake yau.
Nace kada kaga laifin yayana kai kariga da ka tara naka a gida ko Yusuf yace kyaleshi kanwata ni biyu ma zan yi kusan lokaci daya.
Nace kai haba dai yayana tun kawata bata gama cin amarcin ta ba zakai mata kishiya yace wanan an fada maki da gaske yake yi ne bafa jarumin gaske bane shi.
Yusuf Yace I mean it ku bari ku gani kuwa zan baku mamaki ai ita zainab ta sani don na fada mata komai tasan da maganan .
Jikina ne yayi sanyi da jin maganar shi ban iya furta komai ba na nufi kitchen din zuciya ta yana tunane itama zainab ke nan irin rayuwa na zata fada zama da kishiya.
Sai da na dora komai na haura sama inyi wanka na fito ina zaune ina shafa mai ya shigo dakin ya fito daga gidan iyayyen shi.
Inda nake zaune a gaban mirrow ya nufo yana fadin daga wurin su hajiya nake tafe yanzu nayi mata maganan mai aikin ki tace zata diba ta gani idan za a samu kafin mu tafi.
Nace tare da su Affan nake son zuwa suyi min hutu a can tunda zan samu hutu in two weeks coming sai su dan debe min kewan zaman gida.
Yace kunyi magana da hajiya ne nace banyi na dai fadawa maman su wancen zuwan da mukayi yace ok bari zan mata magana muji sai dai kin san ni zuwan su zai takura min.
Nace wani takura kuma duk mutanen dake gidan ka basu takura maka sai wa yan nan yaran kananane zasu takura ma.
Baiyi magana ba sai hannun shi dayakai saman wuyana ya shafa na dan noke yace zan bar maki driver guda da zakuyi zirgazirga dashi don aike.
To nace tare da furta angode kada ki manta da yan uwan hajiyan mu fa na zaria a wurin rabo nace ni ina nasan su yaya, ?
Yace waye yayan naki ya tambaya yana matsowa inda nake again nace cikin dariya gaka kuwa ko zaka banbantani da su zainab da binta na tunda ka zama kifi yanzu, , , ,
Bakina ya kaima cafka ban samu karasa zance na ba ya ce shiyasa naman shi keda dadin don da yan uwansa ya girma.
Karni dai na bashi amsa bakina yana makure da hannun shi yace wanan bakin zanga ranan da tsiwan sa zai kare ?
Sai ranan da ka bar tsokana na zai daina tsiwa nace mai tare da fadin da su anty Fauziya da Anty faiza da antyn nan gidan ai zamu kasafa kayan yace kin yi daidai.
Ruguma ya kai min daidai ina mikewa zuwa wurin jakkan kayana ajyan zuciya na sauke da ban san yazo min ba tare da lumshe idona.
Yace you miss my hug ko two days nace na fada ma haka tunda na saba an hanani auren mara mata a inda zan samu kulawan mijin ko yaushe a kaina.
Murmushi yayi ya sake ni tare da fadin kin makaro yarinya sai dai diyan ki su samu kila au dazun hajiya take wani magana da ban gane kansa ba nace na may fa ?
Dauka kamar suke kina da ciki ko nace haka suks ce min nima basu san canjin yanayi bane kawai yai dariya ya fice dakin.
Nagama shirina na sauko kasa lokacin shima ya fito da shirin shi zasu wuce ke nan a falo inda na bar anty na samay ta zaune.
Na gaida ita tare da dan zama a gurin ta nace anty dama akwai kayan da muka zo dashi na rabon azumi da yace su anty Fauziya da anty Faiza zasu shigo sai a raba.
Tace wanan aikin ki ne ai khadija tunda bai taba yin haka ba na gani nace anty ai yin hakan yana da kyau may ne amfanin kana da baka yi wa yan uwanka abinda ya dace dasu.
Ko mutum nada hali ai yana son kari ko tace wanan kuma dai yanzu naki shawaran ke nan dai nace bai yi bane anty tace yana dakyau hakan ai.
Nace ko dacen sai nake ganin laifin ki ne da baki lurar dashi abinda ya dace yayi wa yan uwa da abokan arziki wai laifina kike nufi mutumin da baida lokacin kansa balle na wani .
Nace ko yanzun haka yake anty a haka dai zaki matsa ki ta saka shi a hanya daya dace tayi murmushi a gitsire a fuskan ta.
Kitchen na nufa wurin girkin miyan dana dora na bar ma laraba dafa shin kafa fara na samu komai yayi yadda nake so.
Wutan na kara ragewa na kara ruwa na barshi ya dahu da kyau daki na koma na kira binta take cewa gamu tafe munga yanzun mijin ki ya bar nan ai zai tafi zaria.
Nace ni ida ma kuzuwa bashi na kiraki ba tunda nasan zamana daku yanzu kiran ki nayi ki ban lamban anty Fauziya don Allah.
Maimakon tayi magana sai kara ma anty Fauziya waya a kunne tayi naji tace hello khadija yanzun muke maganan ki da hajiyan mu ai.
Nace Allah sarki anty dama ina son ku shigone akan zancen kayan nan da muka zo dashi na azumi tace yar halas yanzun hajiyan mu ke min bayani gamu tafe gidan.
Sun ji dadin wanan abin don da farko har sun fara zance na suna fadin ni kuma da iyawa na shigo sai nice zan raba masu abu sai gashi na kirasu akan maganan.
Hajiyan mama tace baku da hakkuri akan abu wallahi ni nasan baza tai haka ba don yarinyace da zuciyar manya tasan ya kamata sosai ai.
Sun shigo gidan a lokacin kowan mu na dakin ta sai laraba dake gyaran wuri sama suka hau suka fara shiga wurin anty Fati daga nan suka shigo dakina.
Mun da jima muna hira suna fada min komai ya kammala na taron baki da suka tanada sai zuwan su ake dako yanzu.
Falo muka fito na tura laraba ta kira driver da zai shigo muna da kayan ciki ni da kaina na shiga dakin anty Fati na kira ta tana kwance nake fada mata ita ake jira ta sauko.
Tace muje a raba kawai dan jimm nayi tare da fadin anty ina fatan ba fushi kikayi ba akan haka idan ma kin dauka wani abu ne Allah yaga zuciyana wallahi.
Ban shigo cikin ku da zuciya biyu ba sai alheri tsakanina dake don baki min komai ba a rayuwana tarkan yayata na dauke ki a gurin na.
Don haka ina mai baki hakkuri idan ni na saba maki badon niba sai don Allah ki daure ki fito ki bada umurni a matsayin ki na uwar gidan nan.
Kada ki sakaci da daman da Allah ya baki a kan mu Allah ya gani ba zan taba shige maki gaba a kan hakkin ki ba a gidan nan da yardan Allah.
Murmushin nan irin nata tayi kamar dole tace khadija na gode na kuma fahince ki sai dai nima bana fadi haka da wani manufa bane gaskiya na fada maki ban son irin wanan abin ganin laifin ne.
Nace yaya zakiyi Allah ya baki wanan girman sai dai ina kara baki shawara badon nakai ba ko na cancanci na fada maki kina sakaci da daman ki don ko ke ce babba a cikin mu kamata yayi wani abin ke ce mai daurewa ki fada koda ba zai dauka ba a lokacin nasan zai duba daga baya yai amfani dashi.
Yanzun dai khadija na fahinci dole sai naje kasa ke nan ko nace haka nake so anty don ke ya kamata ki komai a matsayin ki na matar gidan nan .
Kinga yanzun ana ta shirin kawo kayan zainab alhalin hajiya mama ta kiraki baki kuma leka ba har yanzu.
Mikewa tayi daga kwancen da take tana fadin gaskiya ta fada min kamar kwana bakwai da ya wuce sai dai ban samu lekasu ba din.
Nace anty yin haka kamar kina sakaci ne da daman ki da Allah ya dora maki tunda ko banza wanan abin ai ya shafe ki amma ki gafarce ni idan na fadi ba daidai ba.
Tare muka fito da ita daga dakin zuwa kasa inda na samu su Anty Fauziya sun kulu da dadewan mu a ciki.
Nice na basu hakkuri nace na samu tana bayine na tsaya jiran ta anty Faiza tace na dai dauka tana halin nata ne data saba ai don dukkan su sun girmay ta ga shekaru.
List din nabawa anty Fati tun muna saukowa nayi mata bayanin komai ta karba ta zuwa kuma sai ta mikawa anty Faiza anan na fahinci halin ta irin mutanen nan dake da halin ko in kula akan abu.
Na suka shiga bin komai yadda ya kamata tun nan suka tayar da binta da driver aka fara mika na mutanen cikin gidan su kafin wani lokaci a kaiwa kowa wanda ya kamata anyi yadda ya dace.
Kitchen na koma na duba girkin yayi na shiga rabo tare da laraba tana mikawa a falon karshe na fito ma laraba da nata .
Abin ya daure ma laraba kai sosai tace hajiya har dani sai kin biyo ni da nawa kason kuma nan ai da ki barshi a can in dauko.
Nace haba dai mama kina gaba dani zan bar maki abinci acan ki dauka karma ki koma irin maganan nan don Allah kije ki huta yau mun aikatu da yawa sai zuwa anjima a kai makarde shikafa da zamuyi sinasir dashi.
Ta karbi abincin tana godiya nace sai dai kada ki manta da markaden don ya dan samu rana ya tashi.
Tace yanzun kuwa dana gama zan mika insha Allah jinayi anty Faiza tace uhumm, ummm laraba yau ke ma dai kin ga canji a gidan ku ko.
Yanzun dai Fati dabara ya saura gare ki duk da baki son afadi matsalan ki ya zama dole ko mu fadi don ke din dole mu ce.
Yanzu dai ga abokiyar zama kin samu kamata yayi ku hade kan ku ko bazan kune yan kasa al,adan ku daya kabila daya kin ga komai zai zo maku da sauki idan kan ku yana hade.
Anty Fauziya ta karbe da fadin naji dadi danaji yayan mu na fadin da yaran Khadija zata tafi suje can suyi hutu a gurin ta haka ya nuna ita mai son muce mai kuma kaunar mu.
Don ance wanda duk yaso yayan ka ya gama son ka a duniya koda kuwa ya nuna kai bai kaunar ka balle gashi yanzu mun gani rabon kayan nan ki duba fa bata yarda an taba komai ba sai da taje ta kira ki dakin ki kizo aka fara.
Sanan kuma muma gare mu abin farin ciki ne ace yau gamu gamu gidan dan uwan mu muna raba abin arzikin da ya fito a hannun shi may yafi wanan farin cikin a ran mu sauran sukace babu wallahi.
Mu dai fatan mu yanzu ku hada kai sosai ku jawo muna hankalin dan uwan mu ya dawo jikin shi ko kwata muna shi daga kaidin wanan shedaniyar matar tashi.
Anty Fati tai wani murmushi tace kayyah anty wanan wazai iya da ita a cikin mu kike gani kun fasan duk ta girmay muna a shekaru ba kusa ba.
Zainab tace bari fadin haka mana Anty Fati ita tayi kamar Allah ne ga Allah duk damu daku za,a dukufa wurin kai kuka mu ga Allah.
Ai tunda har khadija takai haka a gidan nan tare da Nafisa alama ya nuna hakan Allah yana karban adduan mu.
Yanzu dai mu hadin kan ku muke fatan don kada kuma kawunan ku ku yazo bai hadu ba abin yafi nan lalacewa kuma.
Nan dai sukai ta magana wanda yawan maganan duk akan anty fati yafi yawa don inda take da sakaci duk basu boye mata ba a gurin ranan.
Karfe uku daidai suka bar gidan zuwa cikin gidan su nace zamu shigo da anty Fati idan mun shirya da ga baya.
Fitan su gidan yai daidai da dawowan su AA da Yusuf bayan mun tare su ne na shige daki na shirya ban fito ba sai da nayi sallah la,asar na fito na samay su a falon har lokacin bata shirya ba.
Nace anty lokaci yana gabatowa fa shima Yusuf din mikewa yayi yana fadin zai je ya shirya motan da zasuyi amfani dashi ya bar gidan .
Falon ya rage daga ni sai shi a zaune ina jiran ta tashiga yace dani zo nan Deedar hanya hawa saman na kalla inda tabi sai na mike na isa gurin shi din.
Jawo ni yayi zuwa jikin shi tare da fadin wanan kwalliyan yai maki kyau sosai na gode nace ina kokarin dagawa saman jikin shi din.
Ji nayi ya kara riko ni da kyau ya kokarin kai min kiss nace kaima Allah ya AA ka bari kada anty ta fito ta samay mu a haka kasan ranta ba zaiyi dadi ba fa.
Yace and so what idan ta samay mu a haka budurwa taga na rungumay ko farkana nace koma dai may don Allah ka daina don ba dadi irin hakan aiwa mutum sake ni yayi yana sauke ajiyan zuciya tare da fadin yau dai kin san ke ce da girki ko ?
Da sauri nace dashi girkin may kuma ana zaune kalau may zai sa in yi girki anan bayan ba lokacin mu bane kada ki kawo min wanan zancen anan don ba a kanki aka fara haka ba.
Nace ni kaina na sani ai abinda banso kuma bazan ma wani ba bai kara kulani ba tunda na fadi haka sai ya share ni ya mike zuwa sallah.
Fitowa tayi muka fice daga gidan mun samu yan uwan haihuwan su kaf sun zo a lokacin muna shiga suka hau yi wa fati sheri kamar yadda dangin miji kanyi wa uwar gida wani lokaci.