← Book details Mijin Buzuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 3 OF 6

Part din hajiya Umma aka gyara don taron bakin masu kawo kaya muna dakin mommy zaune na mukaji shigowan su gidan .

Mijin Buzuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 260 min read

Ba bada wani yawa suka zo ba su shidda ne kawai an tare su a cikin mutunci suka gabatar da kayan ga manya akai masu godiya suka bada kudin dinki dubu dari biyu tare da fadin suna so jin lokacin buki.
Daga inda nake nayi murmushi naji hajiya Umma tace wanan maganar maza ne idan an shirya za a sanar dasu lokacin nan dai aka gabatar masu da drinks da su snack da kajin da aka soya don su tare da basu tukwaicin alherin da suka zo dashi aka rabu lafiya da kowa a wurin.
Yan gida suka shiga duba kayan suna yaba kyaushi da yawan shi suna sa albarka tare da fadin abu yayi kyau wallahi.
Dakin hajiya mama na shige na samu zainab ita kadai na fara mata guda akai tare da fadin amaryam mu na gobe ta dan hararane tare da samun wuri na zauna a kusa da ita.
Ta kalle ni tace ai amaren suna da yawa khadija don ya ce ba ni kadai zai aura ba wai kina nufin wanan maganan da yake da gaske har ke ya fadama shi.
Tace a kasale cikin wani murya haka yake fada min wai kuma ke kin san ko wace matar kuma kin san halinta don haka in kwantar da hankalina.
Gabana ne ya fadi nace a fili ni ni din nan nasanta yace maki tace kwarai kuwa da sauri nace wallahi haram idan bashi bane da sai ince yai min sheri don ya hada ni dake yace hakan.
Murmushi tayi tace indon nice fa khadija kada ki damu da wanan don nima kamarki ce auren biyayya mukeyi wanda muke fatan muga riban hakan.
Don haka wallahi kadama ki damu khadija kin san dai ni ba zan taba fadawa wani wanan maganan ba idan bashi ya fadi ba akaji.
Jikina ne yayi sanyi don ta kawar da hiran sai ce min tayi kinga ni yanzu ba wanan ba wani shiri kika tsara akan bukin kafin lokaci yayi.
Ajiyan zuciya na sauke nace Allah dai ya kaimu lokacin lafiya don shine mai wuya tace ai shine fa shigowan Binta dakin yasa mukai shiru a lokacin don ta shigo tana yaba kyau kayan da aka kawo.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENAB
1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Sai daga baya ne bayan mun dawo gida na lura da AA yana fushi dani kan maganar da mukayi na girki ina gama cin abincin da na girka na shige daki tare da kargamay kofana.
Da safe shiya tayar dani daga barci wai a ranan zamu koma Abuja bance komai ba illa gaida shi da nayi da kwana har yakai kofa nace ina son shiga gun yaya Amina kafin mu tafi.
A,a yace min ya fita kawai dakin wani irin bakin ciki naji a raina kan hananin da yayi dole sai a waya na kirata mukai maganan da zamuyi.
Muna a falon hajiya mama zaune a gaban ta yana gurin Abbasu suna magana dashi mama tace dani ya kuma banga kun fito da yaran ba nace ban san may ya hana ashirya su ba.
Ta dauki waya takira anty fati tare da fada mata cewa ta shiryo yara yanzun da laraba ta turo su gidan ta ina son ganin laraba yanzu.
Labara suka shigo tare da yaran tace ina ita fatin take binta maza kira min ita ai maganan ya shafe ta yanzu.
Fatin suka shigo tare da Binta suka gaisa tace dani ashe baku tafi ba har yanzu nace eh yana tare da Abba ne.
Hajiya mama tace dama kiran ki nayi in fada maki cewa yaran nan yanzu dasu khadija zata wuce suje can suyi mata hutu a can idan hutu ya kare su dawo.
Sai maganan Laraba da nake son yi yanzu kin san kwanaki mun taba magana kanta cewa kin gaji da zama da ita kina son a kawo maki yarinya har karo biyu kina min wanan korafin akan laraba ina baki hakkuri.
To yau Allah ya kawo iyakar zaman ku da Laraba don kin san Laraba yar uwatace ta jini bazan cire ta a cikin jini ba kamar yadda nasha fada maki haka ita din jinina ne ita din.
Don haka yanzu zaman laraba zai koma Abuja wurin khadija ke kuma sai ki dauko wanan yarinyar da kika ce an maki magana a kanta.
Shiru tayi sai can tace amma hajiya da an fada min a shirya su ko yanzu gaskiya basu da shiri don ko wanki ban masu ba.
Shirmay banza ke nan ai in don wanki ne idan kin yi tunda Yusuf yana hanya ko yaushe sai ya kai masu .
Laraba aka kira hajiyan ta sheda mata zancen zuwan ta a gaban mu tace tau hajiya can kuma Allah ya maida zama na tace eh don ita din can yanzu tana da bukatan mai taimaka mata da wasu abubuwan gama kin ga yanzu gashi azumi ne tafe kuma ga yara zata dasu.
Kinga zaki dan rage mata wani abin a can tace hajiya banda zabi duk yadda kuka ce haka za ayi yanzu zan dan je in kwaso komatse na sai nazo mu tafi sai dai zan bar sauran kayana sai a aika dasu gida daga nan wurin ki.
Tashi tayi zuwa shiri inda ta bar anty fati zaune bata ce komai ba sai zuwa can ta mike tana fadin zata je ta hado kayan yaran.
A gaskiya banji dasin yadda akai mata din ba sai dai babu halin magana a wurin don ba wurin magana bane.
Amma a gaskiya ta yaya ta zaune da ita kalau yanzu kuma a dawo ace ta koma gurin kishiyar ta ke nan nima watarana za a iya rabata da wurina din don bata yin kanta sai yadda aka juya ta ke nan.
Muryan hajiya ne ya katse min tunane na tana fadin kada ki damu dama zaman Laraba da Fati ya ishe ita Fati din don tasha min korafi yar uwata ce Laraba ta gurin uwa kin ga ita din jini na ce sosai.
Ba zanso kaita inda baza a kula min da ita ba yadda ya kamata ba dai sai na fada maki komai ba a yanzu zaki komai a gurin Laraban.
A raina nace ai kaji matsalan nikan an barni a ciki dana sani in dauko a bangare na kamar yadda ya bukata inyi tun farko.
Mikewa hajiya mama tayi ta samay shi a falon Abba tana mashi bayanin halin da ake ciki na zancen tafiyan da ta tsara yanzu.
Ba wanda ya musa mata don bayanin da tai masu akan haka sai Allah tsare hanya da Abban yayiwa jikokin nasa a lokacin.
Fati bata aiko wa yaran da wani kayan kirki ba hajiyan ta fara fada ina shigowa daga dakin mommy dana fito wurin ya Amina da ta shigo nace ai babu komai Allah dai ya kaimu lafiya.
Tunda muka fara hanya ba wanda yai magana a motar sai da mukai nisa ne daddy yace zai sha ruwa na dauko goran swarm na bude na bashi ya soma barci.
Allah ya sauke mu lafiya duk da gajiya muka fito daga motar tundai ni dana jirkita irin na ranan da muka je kaduna wanan dalilin yasa yai min magana ya sauke fushin da yake dani akan kin amsar girki a kaduna da banyi ba.
Muna shigowa na bude part dina muka shiga kafin kace may labari ya samu Nafisa na dawowan mu gidan har da yara muka dawo da wata mace.
Tace what in dai ba Fati bace tazo wa zaizo gurina da yara kuma mun shiga inda na barsu zaune a falo ban daki na fada sai da na amaye dan abinda ke cikina na karin safe danayi na samu sa,ida a raina.
Duk da yamma yayi sosai a gagauce nayi sallah na fito daga dakon na samay su har laraban zaune a takure falo.
Nace don Allah mama kuyi hakkuri na dan shiga ciki rage lalura ne ku taso muje daki ina kokarin shiga dayan dakin da kayan ta.
Tashi tayi ta biyo bayana inda na aje kayan tare da cewa sannu da shigowa sabon rayuwa mama ubangiji ya kawar da shedan a tsakanin mu ya bamu zaman lafiya da juna tace amin yar nan.
Kitchen na koma na dora girki a gagauce na hada muna abinci duk da dare ne bai hana in girka abinci mai inganci ba a lokacin.
Sai tara saura ya shigo dakin muna zaune a falona muna cin abinci a plate daya da yaran sai mama laraba dake gefe daya tanas cin nata ita kadai.
Wuri ya samu ya zauna saman kujera ya fara gaida mama laraban da gajiyan tafiya sai ya juyo gare ni yace ya jikin naki yanzu ?
Da sauki na bashi amsa ina ci gaba da cin abincin da nake wanda dama bawani ci nake ba tsakura nakeyi don ma in dan ci yasa na hada hannu da yaran muna ci.
Yace mama yau gaki Allah yai dawowan ki Abuja kuma da fatan za a zauna lafiya da kowa a cikin amana da yarda tace insha Allahu.
Ya mike bayan ya gama maganan da zai yi ya fita nayi mai saida safe nace yara suyi mai suma sukace mai saida safe Abba ya amsa ya fita.
Laraba dake gefe tace uhumm sai dai kin koya masu ai sannu a hankali zasu iya ai din babu wannan shakuwar a tsakanin su irin haka.
Murmushi nayi nace komai yanzu sai a hankali ai mama bamu jima ba muka shige kwana.
Washegari ko da na tashi jikina ya matukar mutuwa sosai yai min nauyi ga kasala da kyat na iya fitowa na hada masu abin karyawa suka karya nikan daki na koma na dunkule.
Barci nayi sosai a wurin har mama taiwa yaran wanka ta shirya su ban fito ba sai da AA ya shigo ne yana tambayan ina cikine mama ke fada mai ai tun safe na shige banjin dadin jikin ne take gani.
Dakin ya shigo tun daga kofa ya tsura ma yadda nake kwance ido har ya karaso gare ni inda nake kwance bargon dana rufa ya yaye na bude idona da yai min ja na sauke a kan shi.
Yace may ke damun kine Deedar nace a kasalance jikina dai ke ciwo na kwanta in huta yace oright idan dai wani abin kike ji ki fada min muje asibiti a duba ki nace lafiya ta kalau.
Mikewa yayi yana fadin yau bazaki shiga school ke nan ba nace sai dai gobe idan Allah ya kaimu gaskiya .
Ni zan fita yace idan akwai abinda kuke so sai ki kirani a waya nace idan zaka dawo dai ka riko muna pop corn wasu daddy da sauran abin yara dan Allah ?
Kallona yayi ya girgiza kai nace da kyat please don Allah kaga yau ni ban fita zanyi ba yace yaji Allah ya sauwaka ya fita.
Mikewa nayi na shiga ban daki na fito wayana yana kara na dauka maryam ce a layin ina dauka take fadin ke yar dadi miji yau ke nan ba zaki fito school ba ko ?
Wallahi maryam jikin nan nawa yau sai a hankali sai dai gobe idan Allah ya kaimu tace ai ganinan zuwa na dubaki idan mun fito sai kinzo nace na kashe wayan ina kallon lokaci.
Sha biyu da wani abu na rana nace kai ashe lokaci ya shige ne tashi nayi zuwa falo na samu su laraba da yaran a zaune ko tv basu kunna ba.
Gaida su nayi nace mama shine ba a tayar dani ba ga har rana yayi sosai kallon yaran nayi ina tambayan su may za a dafa masu abincin rana ne ?
Wanan yace indomie wanan yace taliya nace bari mu raba gardama yanzun barin maku taliya din gobe sai ayi indomie din.
Na juya wurin Laraba ina fadin mama ai zakici taliyan ko tace zanci mana uwar dakina may ye bamu ci acan mu.
Kitchen na shiga na hada kayan miya na jajjaga tare da dauko tukunya na zuba ruwa na dora kan gas din fridge na bude na dauko nama na yanyayanka na wanke na zuba a tukunyar tare da zuba gishiri na kawo
albaaa na yanka a sama
Haka dai har na hada abincin yadda nake so na rage gudun gas din nawa na fito falo wurin su na zauna muna hira dasu.
Gaskiya ko ba komai ashe zama da mutum dadi gare shi ga yau kawai naji dadin kasancewa dasu a tare dani part din.
Da ko sai ni kadai zan zauna idan ba waya ba ko tv banda abokin fira a a part din shigowan maryam yasa muka mayar da hankali a gare ta tace ke shegun buzayen nan su tare ni waje sai tambayoyi suke min wai may na dauko a jakata sai na bude masu sun gani don basu yarda dani ba.
Nace ga yan wulakanci zanyi maganin shegu kuwa tace bakiga yadda suke wani zare min ido ba wallahi har tsoro ne ya kamani.
Mikewa nayi na fita zuwa wurin su a bakin get din ko hijab ban tsaya sawa ba a jikina tun daga nesa nake kwala ma wanda nagani a kofar kira ya wani nuna kan shi wai shi.
Zuwa nayi a bakin get din nace wa ya baku ikon bakona idan zai shigo gidan nan sai kun caje min shi yace hajja dokane muka samu yin hakan daga sama.
Wayan dake hannuna na kira AA dashi suna kallo na nace da ya dauka kai kaba wa yan nan buzayen dake get din gidan ka doka idan bakuwa tazo wurina su caje ta don yanzun haka sukai ma maryam har da so taba jikin ta.
Yace what wa ya basu wanan dokan haka gurin bakin ki nace haka sukace ina juyawa ciki bayan na gama masu masifa da warning din su don nasan inda dokan ya fito yanzu.
Ina shiga rike da hannun daddy dayan su shima ya shigo ya nufi gurin nafisa dake zaune falo yanzu cikin jikin ta ya girma sosai.
Na barshi nan ya duka yana fada mata sai gashi wai ta aiko in je kin zuwa nayi don nasan maganan banza zanji idan naje din abinci na juyo muna na na kawo falo.
Mun baje muna cikin cin abinci sai gata ta shigo falon da kanta ba sallama kamar kulun na dauki wanan dabianta ne haka ta saba shiga guri tunda har mijin ta naji yana korafin hakan.
Zata fara magana na dakatar da ita da fadin malama may ye haka kamar wace ta shiga church babu sallama kuma.
Tunda zuwan ki nan ba alheri bane ki fice min daga shiya don bakiga kafana a gurin ki ba ke fitsarariyar mara kunya nace dakata may kika gani anan yara ko.
Don Allah kada ki bata ma yaran nan tarbiya da halin nan naki mara kyau kamar yadda kika bata wa naki tarbiya kallo takai ga yaran da laraba tace aikin banza sai kuma ta fasa fadan daya kawo ta tace.
Idan mutum ya isa ai ya haifi nasa ya daina karice karicen diyan mutane a furin shi a haka dai zaki kara da kalar diya a shiya badai ki haihu ba.
Nace idan na haihu tunda kece Allah sai ki kashe diyan mu gani gaki bakar manya kike kiran wani maye ashe tunda har kin san gaibu.
Ta hayyako na mike tsaye ina fadin Maryam rufo min kofa nan don Allah yau in koya ma matar nan hankali a gidan nan .
Jin haka yasa ta fara ja da baya baya tana fadin dama an fada min haka kuke yan cin mazan mutane idan kunga anfi karfin ku sai ku nuna karfin doya ga mutum.
Har ta fice da wayo tabar dakin dariya muka sa maryam tace shegiya yau kin gano takon yar iska a gidan nan ai ashe dama tana da tsoro haka take iskanci.
Laraba tace ina ina za a hada girman jikin su ba daya ba idan uwar dakina ta danke ta aisai buzunta dama haka hajiya uwar yaran nan ke tsayawa ta kwaci yancin ta ai da abin bakai haka ba.
Amma yadda kika san uwa da yar ta haka muka zauna a gidan nan a baya lokacin ba a nan muke ba dawowan munan kuma abin ya kara lalacewa tsakanin su da maigidan.
Maryam tace ai ma kasa ki yarda ki hada jiki da yar iska don ance tsiya yake kawo wa a gida fada kana hada jiki da kishiya haka.
Nace nima ai hauka nai mata ina zan fara taba ta da wanan tsohon ciki haka a samu na bin gari dani ana nayi kashin kai.
Ashe tana fita ta kirashi ta kwashi karya da gaskiya ta fada mai sai gashi ya kirani yana fada da daukan wayana babu ko sallama sai fadin Deedar kina haukane da zaki biyewa Nafisa da tsohon cikin ta ki nakasata ki mai da ni baya.
Duk abinda tai maki bazaki jira in dawo gida ba sai ki far mata da fada har kina shirin dukan ta a wanan yanayin da take ciki haka.
Sannu mai mata nace mai tare da fadin ai bansan mijin tace kake ba sai ka nuna min yau na kashe wayan abina.
Maryam tace wa mama laraba kin gani ko kirashin fa tayi yanzu ta kwashi karya da gaskiya ta fada mai shi kuma ya hau ke nan.
Nace idan ma ya hau ai sauka zaiyi don ba zan yarda da rainin wayon kowa ba a cikin su yai min kira yafi a girga naki daukan wayan ina gani ban daga ba.
Muna gidan da maryam sai bayan magariba ta bar gidan zuwa gidan anty ta tace acan zata kwana don yanzu zaman hostel din bai mata dadi da ban nan.
Sai dare kamar yadda ya saba shigowa ya dawo gidan sai da ya watsa ruwa ya sa jallabiya ya shigo dakin namu rike da ledan popcorn daya sayo yana shigowa ya mikawa yaran sun karba babu godiya nace baku godewa Abba mana ko ya karbe abinshi ne sukace sun gode suna hada baki wurin fada.
Gaida laraba yayi ya juya ya na fadin kai min abinci nace naji ya juya ya fita daga dakin nawa sai da ya dan jima na mike na shirya bayan nace mama ta rufe ta ciki idan na dawo zan kwankwasa sau biyu tace to.
Na riga da nayi warning din yaran da kada su fita ko ina idan ba dani ba koda wani na fice zuwa wurin shi kai mashi abincin.
Yana zaune a d/table din na shigo da sallama ya amsa min ciki ciki na isa na fara jerawa baiyi magana ba sai dana gama na juya nima ba tare da na yi mashi magana ba naji yace.
Ina zaki na juyo nace mai daki zan tafi yace dawo ki zuba min ina zubawa har na kusa gamawa yace don may nake kiranki baki daga waya ba.
Ban kusane ina kitchen na bashi amsa yace da kikazo kikaga miscall dina fa shiru nayi mai ban tanka shi ba.
Ya ja plate ya fara kai abincin sakwara ne da miyar agushi maryam ta taimaka mukayi tunda nafisa tai maganan doya muka sha dariya.
Shiru wurin ya dauka ba wanda yai magana a cikin mu wurin sai da ya kusa gamawa ya dago kai yace nice mijin tace ko ?
Nace in ba haka ba daga jin magana ta bangare daya zaka hauni da bugu don ni naza juyan da take fada min ko may ?
Haka kawai zan zauna ta shigo min har part dina da cin mutunci amma naka laifinta ba sai ni da ta sama din tunda ni ban san daukan ciki ba ko ?
Kinga bashi na kiraki nan ki min ba yanzu sai dai abinda nake son ki dashi shine ki kula da halin da take ciki yanzu da hankalin ki zaki far mata da duka.
Au ka dai yarda da dukan ta nayi niyar yi ke nan daga haka naja bakina nayi shiru yana gamawa na kwashe kayan zuwa kasa na barshi a gurin zaune.
Koda na koma dakina ban fito ba na zauna muna hira da laraba har sai da yara sukai barci na kaisu daki bayan na saka sunyi fitsari daki na koma don in shirya na samu waya na ruri.
Dauka nayi na duba shine a layin ban daga ba sai da na gama shirina tsab na fito naiwa laraba sai da safe nace ta rufe kofa tayi addua kuma ta kashe wutan dakin .
Ina shiga yana zaune a bakin gadon shi ya tasa laptop din shi gaba sai dai ba dakila yake yi ba har na aje jakkan hijab da zanin sallah na na kwanta bance dashi komai ba.
Jin sauka hannun shi nayi bayan ya hawo gadon ya kwanta ba kula shiba yai abinda zai yi ya tashi kamar yana taba dutse.
Shima bai min magana ba ya mike zuwa ban daki yana fitowa nima na mike na shige ina fitowa na tsaya nayi na fila ban kwanta ba sai da na kwanta naji murya shi na fadin.
Wanan magana yasa kije min haka idan ban yi maki magana akan aikata ta,asan da kike son jefa kanki a ciki so kike in kyale ki kiyi.
Ban iya magana a lokacin sai dai a raina nace lalai namiji sai dai a barshi da halin shi yanzu yana nufi ya dauki maganan Nafisa da muhinmanci akan abinda taimin ko don ban haihu dashi bako kuma da gaskiya dai din Nafisa ce kawai a gabam shi.
Da asuba tunda mukai sallah na sauko daga dakin shi duk wanan sakkon da nayi na samu mama laraba ta gama gyara part dina.
Sai kamshi ke tashi komai tsab ta gyara har na shiga dakina nan ma komai tsab har toilet din ta gyara sai kamshi ke tashi.
A raina nace lalai tafiyan mu zaiyi kyau da mama Laraba fitowa nayi zuwa falo muka hade da ita a falon ta fito kitchen nace a, a mama aiki haka da wanan safen.
Tace uwar dakina ai tun kan a kira sallah nake idona biyu ina idarwa na hau abinda ya kawo ni yanzun ma kitchen na gama gyarawa.
Sai dai ban san may zaki girka ba yau amma dai duk da haka na dora maki ruwan zafi a wuta har ya tafasa ina ji nace kai nako gode mama gashi kuma guri ya dauki kyau haka.
Tace to uwar dakina shifa ya kawo ni nan yanzun ma zajen nan nawa kawai nake jiran tashin su in masu wanka.
Nace gaskiya mama nagode fa aiki haka gwanin yabawa Allah yasa mu dore a hakan tsakanin mu.
Tace insha Allahu mun riga da mun saba da wanan ai ko can abinda ke yawan hada mu da hajiya ta kaduna cewa take na faye kakalen aikin da ba a sakani ba ni kuma ban iya keta ba a rayuwana.
Kitchen na nufa na dora girki har wanda zasuci da rana idan na fita farar shimkafa na dafa sai da yayi wara wara na sauke yasha kayan hadi sosai su karas da koren wake da kabeji dahuwar tayi kyau sosai don haka na kwashena zuba a inda ya dace ma kowa.
Na samu tsoka zalla na yanka na tafasa da gishiri da maggi bayan ya dahu na dauko attarudu da tatasai albasa na dan daka su a turmi nayi miyar jajage don yafi dadin cin shimkafa.
Sai cooker outh dana dama na hado da madara zuwa falo su karya dashi don bai sayo muna sabon bread ba ranan idan zai dawo da dare yake shigowa dasu gidan.
Na samu an gama ma yaran wanka har ta shirya su cikin wasu kayan da uwar su tabayar da zamu zo nan falo na zaunar dasu suna karyawa na shige wanka a gurguje na fito na shirya don kada ya girshe ni.
Zamama ke nan zan karya sai gashi part din suka gaisa da laraba yaran nace ma ga Abba ku gaisa mana suka ce ina kwana.
Ya amsa masu tare da zama in kawo maka breakfast ne nan yace eh sai dai kiyi sauri kin san zaki makara fa na wuce zuwa kitchen na hado mai na kawo mai ya karya suna dan hira da laraba sama sama.
Muna gamawa ya mike ya fara fita ban fita ba sai dana kara jawa yaran kun ne na tsorata su nakuma yiwa laraba magan akan su rufe kofa kada su budewa kowa kofan.
Tace a tsorace ai ko murai ban budewa nasan halin gidan ba yau ba ai nayi masu sallama na tafi ta kargamay kofan ta ciki.
Mun dauki hanya shiru ina kallon titi naji muryan shi yana fadin wai ke kina nufin dan maganan da nayi maki kike wanan hura hancin haka.
Ko kina nufin a barki ki yi yadda ranku ke so ki biye nata ku zama daya kuyi aikin rashin hankali tunda kin san bakin ki take nema.
To wallahi bari kiji ban yarda da fadan duka ba ko babu lalurar ciki kaddara akewa gudu ai don ba karfin ku daya ba kema kin sani.
Kuyi na farko kunyi na karshe kada ku mayar dani sakaran namiji mana da baisan ciwon kansa ace gida ana irin wanan fadan.
Na dago kai na kalle shi sai na kawar da kaina gefe don kwar jinin da yai min a fuska da na kalle shi yadda ya dake fuska yana min fada acikin serious voice .
Muka isa na fita ranan bance dashi komai ba ya ja motar shi yabar gurin na shige cikin school din kai tsaye.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: A falon anty Salbiya muke zaune bayan barin mu makaranta mun gaisa na mika mata tsaraba da nazo mata dashi tai min godiya tare da tambayana mutanen gida.
Suna lafiya na bata amsa dashi kawai naci gaba da sauraren su ba tare da nayi magana ba bayan dan hiran kadunan da sukayi ta dubeni tace yau ko lafiya kike nace lafiya anty.
Tace to mu fara abinda ya kawo ku don nima fita nake son yi dan anjima kadan zan shiga barka anan makwabtan mu ne.
Kai na rausaya tare da sake dan guntun tsuki nace dama dai an barshi anty don ni banga amfanin yin hakan ba gaskiya.
Subbahanallahi tace dama kallon ki nake kawai don nasan da matsala tunda na ganki a haka nace anty may amfanin kai kaita kokarin gyarawa namiji rai shi bai san kanayi ba ma.
Dariya tayi tace zaka ko gyara kanwa ta don su din Allah ya dorasu akan mu dama haka zaman aure ya gada ko da kuwa baka da kishiya balle ke mai kishiya kishiyan ma kuma buzuwa buzuwa ko yar baruwan mu ce ba abin yarda bace kice ki bar mata miji don ke zaki sha tarin takaici.
Yanzun dai may ke faruwa nace wallahi anty mutumin nan mijin tace ne nan dai na kwashe labarin abinda ya faru tun a kaduna har dawowan mu nan Abuja na fada mata komai.
Allah sarki kanwa ta yo ai haka halin maza yake al,amarin sun dama sai hakkuri zaki ga abin magana su bashine abin yi a wurin su ba tun dai na miji irin naku da kullun a cikin ci da sha yake na saddabarun mata.
Yau da kin samu kanshi gobe juyewa zai yi kamar bashi ba sai ke ce mai tarin takaici shi bai san yana yi ba ai kamata yayi ki kara kaimi ba kice wai kin jaye ba kamar yadda kikace yanzu.
Ke ki fa gode ma Allah don wallahi kishi da wa yan nan mutuane ba abin wasa bane ke gashi har kin samu miji na kulaki bata samu yadda take so gaba daya ba a gurin ku.
Gyara kan da addua ai yanzun kika sa hannu khadija don ba fasawa zakiyi ba don shi gyaran nan da muke yi yana hana wani abu ko don kimar hakan da kake dashi.
Gaki a ganuwan cin ribar auren ki kike yanzu idan shakuwa da kauna bai shiga tsakanin ku ba a yanzu yaushe kike tunanen zakuyi shi sai gaba kun fara tara iyali kike ganin wanan abu zai yiyu a tsakanin ku komay.
Ke ki bar maza a inda kika gansu wallahi halin sai Allah daya halicce su don komai iyawan mace sai sun lasa mata wannan nakin cikin da namijin da suke dashi.
Ajiyan zucita na sauke nace nasa abin ne yai yawa wallahi anty anty tace nasa dai kike gani shida kike zaune dashi idan wata ta zauna dake ta fada maki halin nata mijin sai kiga aike mowa ce a gidan ki.
Mike ki gyara ki tofe shi da addua komai zaizo sai Allah ya kawo abin a cikin sauki gare ki ko yanzun ai ba haka taso abin ya tsaya a tsakanin ku ba kika san shirin da akai maku dan wanan tafiya na kwana biyu da kuka yi.
Akwai abinda yafi ciwa kishiya rai kamar miji yai tafiya da yar uwanta koda da yardan ta ne sai ya dan sosheta a rai wanan kishi a jinin mata yake sai dai ana son idan zakayi kada kayi na wuce wuri.
Yanzun missalin in tambaye ki tsakani da Allah ki fada min ke baki kishin su a ziciyar ko kadan don Allah ta fada tana kallon cikin fuskana da idonuwan ta.
Murmushi nayi na dukar dakai ina dariya tace kin gani haka abin yake ai kamar fagen yaki ne aure sai idan inda karfin mace ya kare ga mijin ta.
Ai tunda kika ga ko wani kabila na kishi akan mazan su to ki ji tsoron kalman nan ta kishi da kike ji don kishi na iya kai mace aljanna yana iya kaita wuta Allah yasa mu dace muka amsa da Amin.
Don haka barin baki wasu sirika yau irin na kasan mu banan nan ba sai dai zan fassara maki sunayen su da amfanin su a cikin kalman hausa yadda zaki gane muhinmancin su dakyau.
Ta mike ta shiga ciki sai gata ta dawo hannun ta dauke da wani jakka mai ruwan zaiba ta zauna ta dauko wani kwalba da aka nade da takarda mai ruwan gold tace cikin kallon inda nake kin ga wanan.
Na gyada mata kai tace shi muke kira ina gaban ki uwargida da yaren mu turare ne na sihiri ana shafa shi a wuya da duk wani gabobi na jikin ki amma banda gurin mamanki don gudun kansa gare ki.
Sai zaki gun maigida zaki shafa shi zaki iya gwadashi ko yau idan zaki girki ki gani kin gashi aikin shi shine yana sa dadin saduwa a tsakanin ku.
Idan kina amfani da wanan zaki mallaki mijin ki don sai yaji duniyar nan babu kamar ki zai dawo hannun ki ba sai kin je gun malami ba don hadi ne na sosai akayi shi ba kowa ne yasan shi ba ko ke don na soye maki ne kuma da wace ta turoki gareni akwai mutunci da yarda sosai a tsakanin mu
Shafa shi kuma yana sa wa mutum farin jini da kwarjini yana kara kafiyar soyayya a tsakanin miji da matar sa sosai dama wa yanda suke mu,amula tare.
Tamika min na karba ina kara juya dan kwalban a hannu na sai naga tayi murmushi ta dauko wani ta miko min na karba.
Tace muna kiran sa da bilkisu ma,ana sarauniya bilkisu ana dan zizara shi ne bayan kin shafa kwali karyan mutum yace zai kalli idon ki ya gaya maki maganan banza don kwar jini yake sa mace mai amfani dashi.
Ana amfani da shi ne musanmam mace mai irin kishiyar ki don ki rika yiwa kishiya kwarjini ko idan zaki shiga taro ko wurin dangin miji .
Zakiga suna haba haba dake ba wanda ya isa ya rainaki ko yai maki kallon wullakanci saka shi a idon ki kinga zai saka kaunar ki a gurin maigida yasa ki mallake shi a hannu ya samaki farin jini a gare shi.
Ajiyan zuciya na sauke ina jin kamar har na kama AA ga hannu nane kamar yadda take bayani yanzu tayi murmushi ta dauko min wani leda da akai siling din shi baka ganin abinda ke cikin sa sai ka bude.
Bayan na karba ina dan juya ledan a hannu na tace kin ganshi nan muna kiransa da mujallabul sheri ma,ana da turan ci back to sender.
Shima dafa,i ne sosai hayaki zakiyi dashi karfi gare shi sosai wallahi akwai na ruwan sa kamar turare da sabulun sa sai dai ban samu ba a lokacin da naje kasar mu.
Iddan kika turara shi a jikin ki duk wani aike da akai mike ko dako bakin aljani ke jikin ki sai ya kone shi ssamu ko sihiri ke ko tsafi ne akan ki idan kinyi hayaki dashi sai ya karye.
Yana magance duk wata matsala na cuta da ba,asan yana ajikin mutum ba yawan hayaki dashi yana kawo waraka da ikon Allah ga mutum.
Sai wanan da ace kina sana,a ne zaki ga fa,idar sa sosai shi sunan sa majabul khairi hayaki ne karfi gare shi sosai shima yana sa ka tara jama,a idan kina harkan kasuwanci kina amfani dashi jama,a zasu zasu rika tururuwa wajen sayen sana,ar ki.
Yin hayaki dashi a yadda kike zuwa makarantar nan da yadda mijin ki yake da jama, a idan baiyi hankali ba duk zasu dawo wurin ki don haka yawan hayaki dashi yana kawo ki rika samun alheri ta inda baki zata ba ma.
Tana kawai nan ta koma da jikin ta ga makarin kujera ta jingina tana murmushi tace ki gwada wa yan nan mugani akan su duk abinda kika gani kizo ki ban labari don zan yi tafiya zuwa sudan bukin yar uwata dake can.
Ajiyan zuciya na sauke tare da fadin na gode anty maryam tace anty mun gode amma nima gaskiya da anbani don abu ga hannu shine abu.
Dariya muka saka mata tace ke da baki aure ba tukun tace anty ai yin zanyi nan bada dadewa ba idan Allah ya yarda.
Tace to bari lokaci yayi kilama a lokacin naje kasar mu kinga sai in maki hadi mai kyau daga can tace to shike nan amma fa kin san alkawari kika dauka tace na sani.
Bamu dade ba mukka fitoo naso zuwa gaida anty hauwa don na kwana biyu ban je gidan ba saboda zuwa wurin anty Salbiyan da muke yanzu.
Ko da na dawo sai dana kwankwasa kofa sau biyu kamar yadda na fadama laraba amma hakan bai sa ta bude min ba sai da ta tambaya waye nace mama nice khadija ta bude tana min sannu da dawowa na amsa ina shiga.
Zama nayi a falo wurin su Affan ina tambayan su idan suna da damuwa laraba tace sai dai shi wanan mai kiriniyar ba wai sai in bude mai yaje waje nace dashi ya rufa min asiri ina zan sake dan mutane cikin wanan gardawan haka ni laraba.
Nace mama ai da kin bude mai sai ku fita tare ku dan sha iska amma yanzu barin dan kaisu su sha iska kin san ba yadda zaka iya tauye yaro a guri daya haka ai.
Idan ya kama sai ka iya uwar daki na sai ayi ai kin san komai daurowa ne Fati bata da yarda balle yadda tasan halin matar gidan nan a baya shine abinda takewa jiyewa zuwan su nan din ai kikaga tun farko bata yarda ba.
Yanzu ma ai don hajiya ta nuna mata fin karfi ne ga hakan don tafita tunane zuwan su nan zai kara kawo shakuwa tsakanin su da mahaifin su kamar yadda naga kinayi din nan.
Nace mama ashe kin gane manufana nazuwa dasu nan da nayi a yanzu tace duk wani mahankali da hange zai hango hakan ai yar nan.
Ciki na shiga na dan kewaya na fito na samay su zaune a falo nace ku tashi mu dan ja waje da sauri yaran suka mike tsaye.
Bamu tsaya falo ba na zaga dasu wajen gidan har inda nima ban taba kai kafana ba tun shiga na gidan mun taka da yaran ranan don dai su dan sake jikin su.
Leken mu naga Samiha tanayi ta window falon tsayawa nayi nace da ita duk da ta sake labulen falon idan an turo ki ne ko ke kika sa kanki gulma je ki karas da abinda kika gani yanzu kada dan kuda ya riga ki.
Bayan mun dawo a falo inda suke na zauna dasu wani tasha aka kai suna yaren su kuma babu mai kallo a lokacin.
Mikewa nayi na dauki remote din tv na mayar masu mbc cartoon suna kallo ganin wata garmaka daga cikin su ta mike ta shiga ciki yasa ni gyara zama da yaran ina jiran tsammani.
Talge baki shan rada sai ko gasu tare sun fito da ita daga dakin remote din tv na a hannu na rike tana zuwa ta tsaya a kaina tana fadin .
Ke may ye hujjan ki na canza masu chanal da kikayi suna kallo ko son iko da mulkin naki har yakawo akan yan uwana ya tashi ga maigidan kuma ya dawo gare mu ne.
Ban ko kalli inda take ba balle in san Allah yai ruwanta a wurin ta sake maimaita maganan ta a cikin tsawa nace ke ke ke wai wata irin fitinaniyar mace ce.
Ina nan dai gidan yaran nan ne kuma don jin dadin iyalin shi ba wasu ba ya saka wanan kayan haka na nuna mata kayan falon da hannu.
Ahhaye nanaye inji yan mata naki ikon da mulkin ke nan dadin abindai baki cikin gadon gidan nan idan ma don iyalin shi ne ba dai don ke ba bakar manya mai bakin nacin tsiya.
A haka zaki kare wurin kalan diya kina fadan gado dasu gadon da bazaki ci ko sisi a cikin sa ba kuma ki sani gidan nan gidanane kije can ki nemi gidan ki.
Nace gado gado yan cin gado manya to kin sani ko ki riga mai dukiyan mutuwa ko a lahira zakici gadon naki ke nan.
Bakar manya kurwa na kur akan ki ko kina yawo da maita a fili ne nafi karfin kamun ki wallahi ke har kin isa kizo ki samay ni kice ga yadda kike so a gidan nan.
Nace gashi kuwa na nuna maki isa ta a gare ki idan kin isa zoki kwata da karfi ki canza masu inda suke so din na juya wurin munafukar nace ke kuma sa aranki kamar kin bar gidan nan kun gama zama mu zuba dani daku agani.
Na kama karkada kafana daya tana kallon bata bar wurin ba sai da nasha gori ta kare da fadin bari samad ya dawo yau in san inshi ya baki wanan damar na takamu yadda kike so nace Allah dawo dashi lafiya.
Sai gab da magariba muka shige ciki ga yarinyar ta nason zuwa wurin yan uwanta amma sun hana karshe ma suka turata part din uwar nata aka rufe.
Abinci na dora muna dayake indomie zanyi dama yasa ban dora da wuri ba na fita da yaran shan iska waje.
Sai da nayi sallah na fito na dora ban fito ba sai da dahu na kwashe muna a babban plate ni dasu na zubawa laraba nata daban muna zaune muna ci ya shigo falon yana gyara nicktie din wuyan shi zuwa sasautawa.
Gaidashi da zuwa mukayi dani da laraba sai Affa ya gaida shi ya kalli karamin yace kai ba zaka gaida ni ba nacewa yaron daddy ka gaida Abba mana kamar yadda suke kiranshi.
Ina sauraren yai min magana akan Nafisa sai naji shiru bai ce kala ba ya juya ya fita daga dakin nan na fara ba laraba labarin abinda ya faru a falon.
Tace ikon Allah mata da son kai haka diyan gida ma ba zaki barsu suyi yadda suke so da gidan uban su ba.
Nace shine dalilin da yasa kikaga ban son su fita idan bangidan su kadai haka kuma rufe kofan da nake saki yi sanin halinta da nayi ne don zata iya shigo maku tace kunyi mata wani abin can daban.
Yanzun jiran shi nake ta fada mai yazo inji abinda zai fada kuma tunda bata laifi ita a gurin shi sai naga laraba tayi murmushi tare da fadin uhumm uwar dakina ai abin naki da sauki ke.
Ga yadda ta shigo gidan nan ta mayar da uwar yaran nan ko wata bora tafi ta albarka a gidan nan amma ke gashi har yana shigowa duba ki kuna tafiya a tare har kina iya mayar mata da martani ai abin naki da sauki sosai wallahi.
Ita fa mai gaba daya tai mata a gidan nan daga ita har yaran na ko ya koma bai ma kaunar ganin su ga baki daya sai da uwar shi ta tashi tsaye sosai fa akan lamarin.
Nace ko may akace wanan matar tana yi ai ba a mussu da hakan don ban taba fanin karfin halin kishi irin nata ba ni dai.
Shiru shiru har aka kwana biyu banji yayi magana ba kuma kullun idan na dawo zan kai yara su sha iska a wajen gidan.
Ashe abinda ban sani ba shine tun ranan tayi mai magana yace so kike in hana yara na jin dadin rayuwa in in ganta yan uwan ki a kan su .
Wai ke may yasa baki tunane kafin ki aikata abune don Allah nan dai suka dan kwasa da ga karshe ya fice ya bar mata part din ta.
Wanan dalilin ne ya sare mata gwiwa bata sake tayar da zancen ba sai dai zaman yaran a gidan yana matukar dagz mata hankali sosai da ta kalle su sai taji wani irun bakin cikin da ba gaira ba ta dalili ya rufe mata zuciyar ta .
Gidan madam ta nufa duk da cikin jikinta yayi nauyi yanzu madam ta tare da sheri ta ga ranta a bace yake take tambayan ta may kuma ke faruwa ne wai ?
Ta cire dan karamin gyalen da ta yafe a jikin ta tana fadin na gane wanan shegiyar yarinyar idan banyi da gaske ba a gidan nan madam wata rana zata iya cin duduniyata.
Wai ki duba yar iska da wayon banza zuwa tayi ta kwaso diyan samad daga kaduna wai sun zo mata hutu anan garin da sauri madam ke tambayan yaushe haka ya faru ?
Tace ba nakiraki nace sunyi tafiya ba satin can a aiko min da abinda zan saka ma shegiya a kofan ta madam ta tambaya tace kin saka din taja tsuki tace na saka mana amma banga komai ba wallahi.
Shegiya banda kyau da kara bajewa ba abinda take yanzu ni kaina na hango abinda samad yasa y auro ta ashe.
Madam ta kumshe dariyan ta tace lalai wanan yarinyar ba karamar yar duniya bace kinga hakan da tayi zai saka ta haskawa a idon shi yo wanda ke son dan ka ai yana son ka ke nan.
Kinga tafi mu dabara dauko yaran nan da tayi sai yanzu nima na kara gaskanta maganar Sabuwa na ranan da tace muna ganin ta hakana tunda tayi karatu kada ji mamakin tafi mu wayo .
Nafisa dake gefe tace komai aka ban inyi a kanta nayi amma banga wani ci gaban hakan ba dole yanzu sai idan na haihu in dire ma shegiya Niger ayita ta kare acan wata kila ma kafin in dawo ta kara gaba.
Ke yanzu ma fa zuwan nan gidan ki da nayi akan yadda take kokarin juya zuciyar shi da zancen yan uwana ne nazo.
Don indai yace sai ya kore min su to lalai nima ba zan zauna ba dama ni zaman ya zamay min kamar dole ne an takura min wallahi.
Kai haba Nafisa may ye matsalan ki yanzu a duniyan nan banda zancen kishiyan nan komai kika nema kin samu a gurin shi yai maki yaiwa yan uwan ki aiko Alhamdullahi ko.
Ta tabe baki tare da fadin hakane kuma inda wanan da wanan gaskiya ba abinda na nema a gurin shi da bai mun ba .
Gashi har yau asiri na aiki kan yar iska ko motar shiga ya kasa sai ma yar banza wai duk da haka baisa tayi ziciya ba ta fita.
Tana ganin yadda nake shiga ina fita ina saka gwalagwalai a gidan ina yadda raina ke so itako iyakarta part din sai kuma idan zata fita ya sauke ko yasa driver ya sauke ta.
Madam tace to mai yafi rai dadi ga hakan aiko wanan abin alfahari ne gare ki kinga taso muje ma wani guri da aka fada min wani kafirin kasan Togo ne yazo aka ban labarin shi ina Allah Allah dama in fada maki sai gashi kin shigo ma.
Da sauri tace shine baki sanar dani ba tun wuri ai irin su sun fi dadin aiki tunda kikaga har an dauko shi a kasan nan kin san ko yakai aiki kenan.
Suna a gaban arnen togo ya baza farin kudi irin na da da yake aiki dasu a gaban shi suna kallo mai mashi fassara yana gefen su zaune.
Sai da ya duba ya kada kai ba tare da sun mashi bayanin abinda ya kawo su ba ya fara bayani mai fassara mashi na fada masu.
Jikin Nafisa har rawa yake sai da ya gama bayanin shi tace ita dai kafin ma in kai ga ciki din har in haihu tana son in fice daga gida gaba daya.
A sa masu tsanar junan su ta daina burge shi yaji komai sunan ta aka kira a gaban shi ya tsane ta suka baje mai kudi ya basu iya sanin sa sukai godiya suka fita yace sati daya ya bata zan bar gidan nan kafin sati ya cika idan aiki baiyi ba zai bata kudin ta .
Jikina tsuma suka bar wurin arnen da farin ciki don zumudi ko gidan madam bata samu komawa ba ta wuce gida don fara aiwatar da abinda arnen yace tayi.
A dai dai lokacin ne kuma muke zaune a dakina da maryam take tambayana ko na aiwatar da abinda anty Salbiya ta bani inyi.
Nace kai maryam ni fa yanzu komai ya fita min rai wallahi irin abubuwan nan ni ba cika son su nake yi don ba yarda nayi dasu ba.
Wani kallo tayi min tace amma ke din nan to ki sani samu yaci annabawan Allah balle ke din nan khadija idan kina tashi tsaye ki tashi tun kan dare yai maki a gidan nan don wanan matar ba zaune take ba akan ki.
Nace taje tai tayi mana indai mijine gata gashi ai tayi ta kayan shi kai maryam ta girgiza tace lalai ba banza kila ta barki ba.
Nace kai maryam har kina ban dariya wallahi nifa duk abinda zatayi taje tai tayi ina kaya suke maryam ta tambaya nace suna a cikin jakkar da na fita dashi ranan har yau ban cire su a ciki ba wallahi.
Miko min su nan idan baki so nace kwasa duka ki ta kaya don Allah dauko min to nako mike na dauko mata ta duba sai naga ta falke ledan wanan hayakin ta mike boner din saka turaren wuta ta dauko a falo ta dawo kuryan ta turara min har yana hawa min kai sosai.
Nace gaskiya maryam ke ma shuumace dama anan zaki saka kikace in baki zaunar dani tayi ta fadakar dani sosai akan zamana da nafisa din a gidan har sai da jikina yai sanyi sosai.
Nace in Allah ya yarda yau din nan zanyi amfani da sauran ni da sabulai da na gyaran gashi kawai nake amdani dasu wanan din wagalan yi nake gani gare su.
Da dare bayan na gama komai a gaban maryam nayi amfani da komai yadda tace inyi dasu don a gidan maryam zata kwana tare damu.


ZAINAB IDRI MAKAWA
SEENABU
1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Madam zaune a dakin Nafisa sun baje suna shan ferfesu da aka sayo masu don ko tace su Samiha su dafa yanzu da take da cikin nan sai ta dinga jin karnin shi a bakin ta.
Madam tace wai shi wanan mai auren budurwan dai yau kwanaki sun kusa cika naji shiru mana .
Nafisa tace au kin dauka mu din na wasa ne ai wasa yake damu wallahi don haka zata bar gidan nan batare da ya san yar iska diya mace ba.
Dan bakar da na dana ma shegu na nan dam na aikin shi har yau dan yadda na daure su ko kallon yar iska da sha,awa bai iya.
Dariya suka sa madam tace aini na kosa inga yadda yar iska zata bar gidan nan ranan insha dariya don Allah da an fara ki kirani inzo insha kallo.
Ai tafiyan nan da yayi kwana biyu ne ya kofsa muna da yanzun kila ta dade da ficewa gidan nan kema Nafisa wani lokaci akwai ki da sanya wallahi ai da tun yana nan kikai ta masu overdoze din shi wallahi.
Samad akwaishi da shegen wayau wallahi ko ranan ina hayaki ya rutsa ni sai da na wayance mai da fadin turaren maiduguri nake bulawa gida.
Kin san ina ganin ganeni yayi sai dai baiyi magana ba don shi haka yake bai faye saurin magana akan abu ba da sauri..
Nan madam ta kara kitsa mata yadda zatayi abin yai mata aikin sauri ba tare da bata lokaci ba tace ai da ya dawo za,ayi ta ta kare gidan nan.

Daddyn mu ne ya kirani awaya yana sheda min alherin da AA yai masu na alheri tunda daddyna ya fara bayani ban iya magana ba shiru nayi ina sauraren shi.
Ajiya zuciya na sauke tare da fadin bai fada min ba daddy bai sanar dani wanan alherin da zai maku ba.
Daddy yace haka ake so khadija biyayan ki ne ya kaimu ga haka ai idan baiji dadin zama dake ba hakan ba zai samu ba kidai muna godiya don Allah sosai a gurin shi.
Mun gama waya da daddy ina mamaki a raina yadda AA yai wa iyayye na alheri bai sanar dani ba duk da daure mai danakeyi a kwanakin nan .
Gashi yanzu bai gari sun tafi jos wani aiki filin gwaunati da yace zasuyi acan kwana biyu kafin ya dawo wanan godiya ba awaya ya dace in mashi shiba sai idan Allah ya dawo dashi lafiya.

Yau tunda na tashi banjin karfin jikina tun cikin dare zazzabi da amai ya damay ni sosai har washe garin ranan monday din gashi zamu fara exam a ranan.
Dole haka na daure na fita na rubuta exam din cikin rashin walwala na juyo na dawo gida a falo na zube maryam da ta fito ta kirani nace da ita gani gida kwance banda lafiya.
Hankalin maryam ya tashi cewa tayi gata nan tafe hankalin laraba ya tashi sosai sai amai nake kwarawa a gurin.
Maryam ta shigo fitowan ta ke nan daga gurin exam bata je hostel ba ta wuto gidan daga school.
Tana zaune ta tsura min ido wayana dake gefena yai kara har ya katse ban iya dagawa ba wani kira ya sake shigowa again da kyar na amshi wayan hannun maryam da ta dauka tai recieving tana fadin AA ne fa.
Da kyat na dauki wayan na kara a kunne na da sallama da kyat shima na iya yi don yadda nake a galabaice kasan ties din falon.
Yadda yaji muryana yasa yace da sauri Deedar lafiya kike kuwa kafin in bashi amsa wani amai ne yazo min na mike da sauri don zuwa yi a toilet.
Maryam ne ta dauki wayan tai mashi bayanin halin da nake ciki yace please maryam ki taimaka kuje asibiti zan ma driver waya yanzu yazo ya dauke ku.
Ba a jima ba driver yazo muka fita zuwa asibitin Nafisa dake daki har labari ya samay ta dariya tayi tace wa Yanyala kilama mutuwa zan yi don ta hadani da wani katon bakin arne ne yai min aiki.
Dariya suka sa a lokaci daya Yanyala tace ita dama zamana a gidan yakai mata ko ina tana gudun inzo watarana in fara zama wani abu a gidan.
Yadda jikin nawa yake yasa dole aka daura min ruwa sai dai sunce ba kwana zanyi ba idan ya kare sunga yadda jikin yayi zasu iya sallamana inda sauki.
Yana jos ya matsa ma Yusuf sai su taso ranan da sauran abokan tafiyan shi dole suka kamo hanya dawowa Abuja din ba shiri.
Barci na samu sosai nayi da aka samin drip din tunda na falka around five na sake mayar da barcin sai yanzun da na falka kuma lokacin tara da wani abu na dare.
Tsaye suke a kaina shida Yusuf da wani daya da ban san shi ba sai laraba da yaran dake zaune a gefe na tayi tagumi maryam kuma tana shigowa dauke da kulan abinci daga kofa.
Dan murmushin karfin hali nai mashi tare da fadi da kyat yaushe ka dawo ne ?
Yace yanzun muka iso khadija ya jikin naki nace da sauki cikin rufe idona ina yunkurawa kamar zan tashi da sauri suke hada baki gurin fadin yi a hankali fa akwai ruwa har yanzun a hannun ki.
Kallon hannun da yai min nauyi nayi na mayar da idona ga sauran ruwan daya rage saura kadan ai Yusuf yace.
Maryam AA din ya juya ya duba tare da tambayan ta mai likitan yace yana damun ta ne ?
Tace Allah dai ya rabasu lafiya tace mai tana dariya Yusuf ne yace da ita kina nufin aure yai albarka ke nan dai tace insha Allahu ciki har ya girma haka.
Hararan ta nayi na lumshe idanuwa na cikin jin nauyi da kunya daya rufe ni a lokaci daya tambaya ya sake mata da cewa shi likitan ne ya fadi haka maryam ?
Yusuf yace muje mana muga likitan zaifi sauki ji a bakin shi suka juya zuwa wurin likitan tare da maryam da tai masu rakiya.
Likita yai masu bayanin yadda zasu gane yake sheda masu stress ne yai min yawa sai dan maleria da ya kamani amma sunyi min alluran maleria din insha Allahu zan samu lafiya ko yanzu idan ruwan ya kare zasu iya tafiya dani gida.
AA yace wa likita da sauri da dai an barni har zuwa gobe a gani likita yace ba damuwa zamu iya komawa gida ai.
Sai sha daya saura muka dawo gidan har shi don sai lokacin Nafisa tasan da dawowan shi garin.
Da yake ba nice da girki ba a ranan muna shiga muka rufo kofan part dina daki na shiga nayi wanka na fito ban jima ba zaune na kwanta sai safe.
Koda gari ya waye maryam da laraba suna kitchen har lokacin ban iya fitowa ba gashi dole in shiga school don exam din da nake dashi ranan.
A dakin ya samay ni kwance ya tako zuwa bakin gadon da nake kwance idanuwa na suna a rufe jin an shigo dakin na bude idona.
Sai da ya zauna yake tambayana jikin tare da kura min idon shi a kaina nace naji sauki ina son shiga school in anjima don ina da exam yau.
Haba Deedar ciwo fa ya kawar da komai a yadda kike din nan har kina tunanen wani yin exam can a ran ki.
Banson in missing din wanan exam din don muhinmancin shi a gareni bansan may zakiyi da karatun nan ba haka da har kike son wahal min da baby na haka akan wanan karatu.
Dan harara nakai mai nace da abina kuka ganni don haka ku barni in karasa don Allah na hada da kalman roko gare shi saboda kada ya hanani.
Yace shike nan amma sai idan kin kara jin sauki zuwa anjima zan kaiki don ina gida yau zanyi jinya baby na tare da ke yana kokarin cusa hannun shi a sanan cikina .
Nace wai wa ya fada ma cikin gareni don Allah na fada a shagwabe ina kawar da kaina gefe daya dan murmushi ya sauke yayin da hannun nashi ya sauka saman cikin nawa yace.
Yanzu Khadija kin kyauta min ke nan da kika ki sanar dani zancen ciki nan har saida ya girma haka naji gun wasu ?
Yana kokarin juyo fuskan shi gare ni nace to ni may kake son in fada ma akan haka tunda bashi ne na farkon ciki a gidan ka ba.
Amma a wurin ki shine farko ai ko don may ba zaki sanar dani wanan abin alherin da ya samay ni ba muyi farin cikin shi a tare.
Nace nima bansan da cikin ba sai zuwan mu kadunan nan ne hajiyan ka ta fara fada min a gurin ta na fara ji.
Yace serious har hajiya ta sani ni ban sani ba ashe zancen da take min ke nan ban fahince ta ba ranan da take fadin kina bukatan taimako a yanzu shiyasa ta bamu laraba muzo da ita.
Nace ashe kuma alherin da ka aikawa su daddy ke nan ranan sun bugo min suna sanar dani an gode Allah ya karawa arziki albarka yace amin yana ja min hanci na.
Tare da fadin ba sai kin min godiya ba deedar don nima yanzu iyayyenane su yanzun dai ki kwantar da hankalin ki ku rage yawan fitinan nan ki renan min cikina cikin koshin lafiya don Allah.
Nace cikin dan marairaice murya na ai kasan ni ban shiga alamarin kowa a gidan nan sai dai idan an tabani ne ban kyalewa.
Yace yanzu ina rokon ki da ki kyale don ni deedar ina matukar son haihuwa a gidana sosai yasa kikaga ina kafakafa da ciki jikin Nafisa ma.
Banyi magana ba shima shiru ya dan yi a inda yake zaune muryan Nafisa ne a falona tana fadin wanan wani sabon cin amana ne ya dauko komay a gidan.
Mikewa yayi zuwa falon inda ya samay ta tana sababi yace lafiya may ke faruwa ne wai ?
Tace nifa gaskiya ba zan yarda da wanan halin ba ka shigo dakin wanan ka dauki lokaci haka a ciki kansan kuma nice da girki wani rainin hankali kake son ka jawo min a wurinta ko may ?
Har kuna wani shigewa kuna shiru a haka wani lalashin ta zakayi a daki tunda bata da moriya a gurin ka sai ci takai a masai.
Mamaki ya kama shi sosai yace wai nafisa wanan wani irin kishi ne haka harda bata da lafiya din ban da halin in zo in duba halin da ta kwana ke nan ?
A wurin ki ne kila bata da mori a wurina kar kiyi mamaki inkinji irin moriyan da take min tabe baki tayi tace banda abincin da take girka ma kana ci kana santi wani moriya take ma bayan shi.
Zaki gani da idon ki idan lokacin haka yayi yanzun dai ki fice mata a shiya tunda ke baki da tausayin gaida mara lafiya idan yar uwarki bata da lafiya.
Yace ni dana jawo mata rashin lafiya aikin ga nazo in duba abina ko don haka ki fice muje kada ki damay su da surutun ki.
Gaba ta sashi suka fice kamar yaro suna fitane maryam ta shigo dakin ta kawo min tea na tashi na dan sha kadan mikewa nayi ina zufa na shiga wanka don gudun kada mu makara.
Hakana na daure na shirya muka tafi school cikin yanayin rashin jin dadin jikina ko a mota sai korafi yake min nashi fa kada inje wani abu ya samu cikin shi.
Nidai ban iya magana ba sai kaina dana dora saman glass din motar ina sauraren shi da kyat na gama ranan sauki na daya banda wani exam kuma sai wani monday.
Shi da kanshi yazo ya dauke ni muka koma gida ban iya komai kwana biyu naji jiki sosai na samu na murmure namike tun lokacin kuma ban kara jin komai ba tare dani.
Na murmure nayi wani irin fresh dani kyau na ya kara fitowa farina yayi wani fau kamar wata halfcas dani.
Damun kebe dashi zai shiga yaba irin kyau din dana yi a lokacin yana zuzutani irin na maza masu mata biyu zuwa hudu yadda suke wa mace idan suna su kadai.
Sai na lura ko a gabankowa muke dashi zai bini da manyatacen kallon shi yana mamaki irin canzawan da nayi wanda dagani sai maryam muka san sirin abin.
Ga wani ni,imtacen kamshi da nakeyi koda kuwa na bar guri ne zai dade yana bada kamshin jikina hakan na yawan haifar mai da kasala .
Wanan kamshin ko may yake dana ratso zai dago yakalle ni duk abinda yake zai iya dakatar dashi a lokacin .
Gulma haka su yanyala suka kai mata haka yasa ta zauna ta kula da abinda ke wakana a tsakanin mu ta sa ido ta gane ma idon ta fitina.
Ranan sunyi tashin hankali dashi sosai a gidan ranan suyi tujara a cikin dare ni dai ina part dina gashi ana batun fara azumi a washe garin muna ciki muna shirin abinda zamuyi sahur dashi.
Sai da suka gama ne ya shigo dakin namu ina zaune a kasa dogon rigan body hock a jikina rigar ya kama jikina daram ya fitar da suran jikina a waje dan cikina ya baiyana a fili kaina ba dan kwali baida kitso na daure shi a baya.
Daddy yayi barci yayi filo da cinya na sai da ya kalli inda yaron yake kwance yace dani wanan ai sun maki nauyi a jiki ko ?
Nace barshi so nake barcin shi yai nisa yanzun ya gama min fitina kallon yaron dake barci yayi yana makale da goran bobo da yake sha yai barci.
Dukawa yayi ya dauki yaron zuwa saman kujera ya shimfide shi tare da fadin zanga yadda yaran nan zasuyi idan sun koma wurin uwar su duk kin bi kin shagwaba su yanzu da riritawan ki barci ma sai yaro yayi a jikin ki.
Dan murmushi nayi nake fadin haba dai kamar daddy kuma za, a ce wai an bata duka shekarun sa nawa a duniya.
Yanzu dai may kike kuma a zaune haka nace haba yaya kasan fa azumi za a dauka gobe kuma ma kaida ke can kuma sha,anin ku da matarka falo.
Ya harare ni tare da fadin niba shirmay na tambaye ki ba idan kin gama kizo ina jira ki a ciki yana shigewa bed room dina nace na dauka ai an hanaka shiga nan idan ba nice dakai ba.
Aiko bai karasa shiga ba sai ga Nafisa a dakin ni dai ranan naga masifa saidai duk fitinan ta idon ta yana akaina yadda nake zaune da kammanina take kallo.
Da kyat taga safiya tun da safe gidan madam ta yiwa tsinke madam dake barcin safe na masu azumi take kwalawa kira.
Dole ta fito a gigice daga dakin ta zani na sabule mata tana fadin lafiya Nafisa anyi mutuwa ne komay naganki haka.
Madam ai da mutuwa akayi min nasan maishi ya tafi ke nan ko madam ta kara tambayan ta ko aikin mune yaci tace don Allah madam bar wanan shirmay naki yanzu ki saurare ni.
Mu zauna tace mata tana nuna mata kujera tun kan sukai zaune take fadin madam jiya banyi barci ba wallahi ina Allah Allah gari ta waye in zo nan.
Ki tayani duba madam yariyar nan wai bata da aljannu kuwa don ni abinta yana ban tsoro wallahi kinga yadda yarinya take nema ta zuzutani nida gidana kuwa.
Madam ina yi kamar banyi nan dai ta koro mata komai madam tace bari tai wanka taje gidan don ita bata fahinci wanan zuzutawan da nafisa ke nufi ba.
Ina daki sai ga Samiha wai inzo ga madam tazo gaida mu mu gaisa nace yau madam ta saba zuwa da za ace in fito mu gaisa tafice taje ta fada mata.
Zuwan anty hauwa yau kenan na farko gidan mu tazo dubani da jiki ita da anty Salbiya sun kawo min tsaranban tafiyan da sukayi.
Mun dan jima a dakin muka fito na raka su kafin in dawo su na falo a zaune dukan su ina shigowa idanuwan su a kaina ya sauka.
Na wuce ciki rike da hannun daddy dake biye dani kamar bindi shiga madam tayi sauri mayar da hankakinta ga Nafisa tana fadin shike nan kuma yanzu Nafisa kun zama daya da wanan yariyar a gidan nan.
Tace don ta sauya shine zama mu daya da ita ko may tace kina nufin baki ga abinda na gani ba komay kuna gida daya da ita.
Tace nifa har yanzu ban fahince ki ba madam ki fito fili ki magana yadda zan fahince ki tace bakiga abinda idona ya gano ba ke nan .
Ban gani ba tace mata cikin rike habanta tace nafisa ai ciki ke ga amaryan ki tsoho ko don har ya tasa sosai gashi a na gani a filin Allah.
Madam ci may tace wallahi ciki don ko ba gizo idona ke min ba ciki na gani a jikin ta yanzun tunda nafisa ta dafe kirjin ta maranta ya yanka bai daina ciwo ba sai gaba abu ke mata wasa wasa duk suna kanta.
Har aka kai ga kiran mijin ta yazo suka kwasa zuwa asibiti can suka rike ta don sunce cikin bai isa haihuwa ba a lokacin.
Bata san inda take ba don drip di ruwan munje gaida da ita da laraba har lokacin tana barci bamu zauna ba muka dawo gidan don an kusa shan ruwa.
Sai da tai kwana bata san inda take ba ta falka washe gari sai dai har yanzu da damuwa a ranta sosai farkon maganan ta shine AA na shigowa tace dashi baya ya gasheta.
Samad ciki ne ga matan ka komai sai a lokacin ya gane asalin ciwon ta yace cikin wayan cewa ciki kuma wata matar tawa wai kike nufi.?
Ajiyan zuciya yaga ta sauke ta mayar da idanuwan ta ta lumshe bata kara budewa ba saj da ya fita daga dakin Yanyala dake zaune gefen ta ta tambaya a cijin yare ko ta ga ciki a jikina itama.
Yanyala tace ita dai taga na sauya mata ainun ba kamar yadda nake ba a baya ko cikar dakine nayi hakana itama bata sani ba gaskiya.
Fada ta hau yanyalsn dashi wai dama haka suke basu mayar mata da hankali kan abu har sai abu ya lalace hakkuri ta shiga bata a wurin sai da ta gaji tayi shiru.
Samihace ke fada mata wai ai mun zo dubata tana barci fa kuma hausu da fada don may suka bari na shigo inda suke tai masu fada sosai a wurin .
Har da fadin su basu ganin laraba iya inda na tsayar da ita take tsayawa bata gusawa a gurin dana ajeta idon ta na saman aikina.
Kwana biyu tayi asibitin ta matsa zata dawo gida aka sallamay ta ta dawo zuwa madam tayi tace anya babu hannu ga wanan matsalan naki.
Tace na dade da sanin haka madam ina kuma kokarina ga hakan wanan shegiyar badon nafi karfinta ba ai da yanzu ta halakani gidan nan don da karfi ta shigo min gidan nan.
Ko mafalkin ta zanyi ba mai dadi bane gareni shiyasa kike ganina tsaya kyam a kanta kamar layan wuya .
Madam tace kinyi bincike akan cikin ne a jikin ta ko kibane tayi ido ta lumshe tare da fadin na binke shi yace bai san da zancen cikin ba.
Zai fada maki gaskiya ne kike tunane ko may namiji ai makiri ne kila ma dashi aka hada baki a rufe maki kada ki sani ki dauki mataki tun farko.
Yanzu isan ya kosa ai ba wani abinda zamu iys sai dai idan ta haife mu illanta diyar ko dan cikin wani murya tace don Allah madam kibar wanan magana don ma ba cikin bane ni dana daure su daga shi har ita ina wani zancen ciki kuma zai fito gare ta yanzu.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Azumi da kwana goma Nafisa ta haihu lokacin muna gida mun fara hutu hayaniya dana ji cikin ji muryoyin su, kamar waka a falon, yasa ni laikawa waje.
Ashe itace ke labour zasu asibiti suke addua hakana banyi gigin zuwa inda suke ba na dai yi mata adduan Allah ya raba su lafiya.
Diya ce mace aka fitar mata sai dai kuma yar tazo da lalura don haka hankalin kowa ya tashi saukin abin uban yar na da hali tun tashi farko sai da ya zube kudi masu yawa aka fara mata amfani dashi.
Mu dai samu labarin ta haihu don da farko theater aka tashi mata sai Allah ya kawo saukin abin ta haife da kanta a cikin sauki.
Maryam ne tazo min da labarin halin da ake ciki na matukar tausayawa baby da iyayyen ta acikin dan lokacin kankani na shiga damuwa a raina.
Ban ko tsaya mamaki ina maryam ta samu wanan labarin ba sai halin da yarinyar ke ciki nake tausayawa.
Haihuwan safe ta yi don haka ranan tun fitan su da safen ban kara ganin AA ba yana asibitin gurin su sai bayan sallan la,asar ya shigo part din namu.
Lokacin mun rarage girkin da zamuyi don shan ruwa ya shigo falon da sallama a bakin shi na dago kai ina amsa mai sallaman tare da mashi sannu da zuwa.
Sai da ya kai zaune ya amsa min tare da tambayan ya muke nace da Alhamdullahi laraba ta fito kitchen ta gama gyara min zobon da zan hada muna na shan ruwa tace Babangida barka da arziki ashe an sauka lafiya.
Yace barkan mu dai laraba ya gida ya aiki kuma yanzun ma na dawo ne ko zan samu ai min kunun tsamiya in buda baki dashi.
Kallon mamaki nayi mai da abinda naji yace din sai naga duk ya fada min a lokaci daya daganin shi kasan yana cikin tashin hankali.
Laraba ta kalle ni nace akwai sauran garin ai bari tashi in dama mai ki huta don tasan nafi son in girka mai abinda zaici da hannu na ban son wani yai masa.
Nace bari idan na tashi zan dama mai yace ok nace mai barka fa ashe an sauka Allah ya raya muna yasa dadin musulmine yace amin sai dai yarinyar bata da koshin lafiya haka tazo da lalura.
Subbahanallah nace da sauri tare da tausayawa ga maganan nan na jero mata adduan samun lafiya ga Allah yace amin tare da fadin.
Likita yace kila sai an fita da ita waje a acan kila a samu nasaran mata surgerier don matsalan da abin ke da.
Nace Allah yasa a dace yace amin yana dagawa daga inda yake zaune din a kasalance ya nufi hanyar fita part din cikin damuwa.
Ya dade da fita ina a inda ya barni zaune cikin jimamay maganan da ya fada min din laraba data zo ta zauna baya fitan shi tace irin wanan abin ishara ne ga mutum wani lokaci.
Sai dai yanzu uwar daki na karshe akan ki maganan zai dawo don kin san ance mai kishiya bata mutuwar Allah dama.
Nace ni may ye nawa a ciki kuma mama tace kin manta da halin matar gidan nan ne da rashi yarda da Allah bata san kadara ba fa irin su.
Nace hakane fa mama maganan ki dutse wallahi Allah ya gani banje ko ina ba akan ta balle yar da bata ko zo duniya bna
Tace ai zama da irin matan nan sai su bace su batar da na tare dasu don shirka da yai masu yawa yanzun haka wurin shige shigen ta da tsohon ciki taje ta hadu da gamon ta can Allah ya sauwaka nace na mike zuwa kitchen do dama masa kunun da yace.
Sai da na dora na jira ya tafasa na dama na na zuba mai a jug gundun kada ya huce duk da lokaci ya karaso sosai na shan ruwa.
Daga kitchen na fito zuwa part din shi na gyara mai ko ina tunda yau ni kadaice a gidan dole aikin komai nasa ya dawo kaina.
Duk da dama ita ba wai tana gyara mai part din bane iyakan ta ta kwanta ta tashi shike nan nata girki ma ba kullun yake samu ba sai idan tana da bukatan yaci wani abu ne zata sa a girka mai ta barbade shi da abinda zata sa mai shi kuma ya lamshe cikin rashin sanin kai.
Zaune suke shi da Yusuf wanda tunda aka fara azumi a tare suke shan ruwa yanzun ma daga asibiti suka yo nan tare don buda baki.
Da sallama na isa gurin su suka amsa min gaida su nayi da shan ruwa tare da kara tambayan su ya mutanen asibiti sukace da sauki.
Yusuf ne yace kanwata kina yin azumin nan akai akai ga lalurar ciki kuma ki dan sahirta ma ki dinga dan hutawa ko kwana bibiyu ne mana.
Murmushi nayi ina kaiwa zaune nace banda matsalan komai yayana bari kawai in bi sahun jamma,a in sauke nauyin shi a kaina.
Yace na fada mata bata jin magane na yanzu kinga inda rashin jin maganan Nafisa ya kai ta taja wa yarinya wahala don rashin tausayi.
Amma ai kaji ita basu yarda rashin kulane kamar yadda likita ya fada ba ya jawo haka ita ba dauka take wai wani ne ya sa mata hannu kamar wai sheri akai mata na sihiri.
AA yace kyale ma haukaciya naji duk haukan da take fadi ai, yau aka fara haihuwan diya da wanan matsalan haka.
An fada mata ta yi bedrest don ciki ya samu ya tsayu yarda ake so amma matar nan ta tayar da hankali wai ita gida zata dawo ta dawo gidan kuma bata zauna ba kullun tana cikin yawo in ma wani abune ai ita tajawa kanta shi wurin bakin yawace yawacen ta na banza.
Tunda ya fara magana nayi kasake tare da tagumi ina sauraren shi tare da son in gano wani matsala ne ga yarinyar har yanzu banji sun fada ba.
Kin ci wani abune da aka sha ruwa naga baki debi abincin kin ci ba tundazun yace min yana kallo na sai lokacin nayi ajiyan zuciya nace wallahi tausayin yarinyar dai nake yi a raina.
Yar jaririya tana wahala irin haka abin akwai ban tausayi sosai wallahi Yusuf yace indan an bi yadda likitan yace ai ana iya mata aikin kan da cibiyar nata insha Allahu.
Wani irin tsoro naji har cikin raina ya mamaye ni sai nake ganin nima wata kila haka zan haifo abinda ke cikina da matsala din kamar yadda nafisa ta haifi nata.
Sun kula da yadda na shiga damuwa a lokacin Yusuf ne ke fadin kada fa wanan abin ya tayar maki da hankalin ki yanzu ki jawa kanki wani matsala kuma.
AA yace tambayan ki nayi kinci abinci yanzu ko kuwa idan baki cin abinci fa zan dakatar dake ga azumin nan tunda Allah da kanshi ya sawaka ma mai irin laluran ki yin azumi.
Yanzun zan je in ci na basu amsa ina kokarin mikewa tsaye jawo plate yayi ya fara zuba min farar shimkafa da kayan hadi ya turo min gaba na yace zauna nan kici in gani.
Dole na fara ci kira ne ta shigo a waya shi ya dauka banji may ake fadi ba sai dai na fahinci Nafisa ce akan layin tunda ya kasa kunne sauraren ta yake baiyi magana ba.
Sai data gama yace nafisa so kike nima in fadi da ciwo ne komai ina yanzun nabar gurin naku da zaki ce nazo gida na zauna na manta daku.
Kashe wayan tayi naga yabi wayan da kallo sai Yusuf ne yayi dan murmushi yace ita matsalan ta ke nan idan abu yazo bata binsa a hankali.
Wayan yake kallo baiyi magana ba sai dai yanayin fuskan shi daya nuna bacin rai karara a lokacin ya gama kallon wayan ya dago ya kalli Yusuf din yana fadin.
Idan ka gama muje muyi sallah daga can sai mu wuce tace wai likitan yazo yana nema na yanzu.
Yana fadin haka ya mike tsaye dama ba cin abincin nake yi ba tunda nayi cibi uku naji ya fita raina bazan iya ci ba yace ki tabbatar da kin cinye wanan abincin kai kawai na gyada mashi.
Sun fita na tatara kayan gurin da sukai amfani dashi na kwaso zuwa kasa ina shiga dasu laraba dake zaune ta taso zata karba nace mama barshi ki zauna ki huta ke ma hakana.
Juyawa nayi na fita zuwa kwaso sauran kayan da na bari sai ga samira yar wurin nafisa babbban tace anty akwai abinci a gurin ki ki bamu yau basu girka muna komai ba suna asibiti kuma an rufe store din.
Akwai abinci nace mata tare da tambayan ta da ku nawane kije can mama tana ciki ta zuba maku na wuce zuwa sama sauran katan da zaiyi amfani dashi idan ya dawo na sa a dakin na sauko kasan .
Na samu ta karbo abincin suna zaune su hudu a falo suna ci ban tanka su ba na wuce abina zuwa part dina mama zaune da yaran suna kallo Affan ya tasa fruit's a gaba yana sha.
Sai dana tsinki aya daya na zauna ina barewa naji laraba tana fadin kudai yaran yanzu baku da tadan abinci idan dane ai ba zakici wanan ayaban ba don cewa ake yana saka turken yaro yayi tauri cibi yaki faduwa da wuri.
Da sauri na mikawa daddy ayaban dana bare din ya karba duk da ban fahinci maganan nata sosai ba sai dai banci din ba.
Tace waini wani irin lalura aka haifi yar dashi ne na sauke ajiyan zuciya ina fadin mama ban tambaya ba don gudun magana.
Saidai ina ganin matsalan a kaine da cibin da kike magana yanzu a yadda na fahinci maganan su sunayi shida Yusuf yanzu.
Allah ya sauwaka tace tare da fadin Allah yasa wanan abin ya zama mata ishara ta daina halin banza nace amin .
Gobe idan Allah ya kaimu ai zamu shiga mu gaida su duk da dai nasan zuwan nawa wurin ba zata so shi ba amma ai dole in lekasu ko dan mijin ta kada yaga rashin kyautawa na ko mama ?
Tace kwarai kuwa yar nan ai ba don ta zakiyi ba don Allah zakiyi da mijin naku amma in don itace ai ba kya je ko ina ba wallahi.
Waya na dauko ina kiran maryam nake fada mata da safe idan tana da lokaci ta shigo muje asibiti mu gaidasu.
Khadija ke baki da zuciyane komay matar da za, a ja gayarwa taiwa mutane tijara zaki ce mu koma gaishe ta kuma.
Nace maryam ba don ta zanje gurin nan ba kin sani saboda Allah da mijin mu zan tafi don kinga rashin zuwa na bai dace ba gaskiya tace sai kin dawo ta kashe wayan ta barni da kallon wayan a hannu na.
Bai dawo ba ni kuma nayi kwanciyana a part dina saida asuba na shiga na tayar dashi don sahur saboda nasan ba zai kwana dai a can ba.
Fada yai man na rashin zuwana dakin nace baka nan dawa kake son in zo inzauna anan ka dai so dora min laifi ne.
Na fito na barshi a dakin bayan na gama hada mai abinda zaiyi sahur din dashi yana bandaki na fice part din.
Nayi masa hakane don yasan abinda yayi din bai kyauta min ba don ya gyara saboda har sha biyu da rabi ya wuce muka kwanta da mama laraba bai dawo gidan ba har lokacin.
Idan kuma na kyalesu ga sanin halin Nafisa da nayi don burin ta shine taga ta kuntatamin ta ko wani hali a gidan.
Washe gari da safe sai da muka gama gyara part din mukai waka muka kwanta har lokacin yaran na barci basu tashi ba yasa muma muka kara kwantawa bayan tanadar masu abinda zasuci idan sun tashi din.
Sun sake jiki sosai dama karamin ne ya so yai fitina daga baya kuma ya daina ya sake jiki sosai dani ga kuma mama laraba da tun farko sun bude ido da ita akwai sabo a tsakanin su sosai.
Ina cikin barci muryan maryam ne ya falkar dani daga barci tana fadin iyyeh kin hanani barci akan wanan bakar kishiyan taki ke gaki kina abinki hankali kwance.
Idona bude da sukai min nauyi ina fadin ai na dauka baki zuwa din tunda kin fadi haka takai zaune a bakin gadon tana fadin.
Ai ba don ta zan je ba don AA din ki ne kawai wallahi saboda mutuncin dake akwai a tsakanin mu da banje wurin yar iska ba yanzun dai ai taga ishara akan ta bakin halin ta ya jawa yar cikin ta matsala dama irin su a haka suke ganin abinsu.
Allah dai ta sawaka nace da ita ina kokarin mikewa zaune nace ai jiya mama ta lurar dani wani zance maryam nan dai nake fada mata yadda mukayi da laraban.
Tace ai dama kema kin san abinda zai biyo baya ke nan ga zancen din dauka suke kowa haka yake kamar su ai ke dai yanzu ki kula da addua Allah ya sauke ki lafiya.
Nace ina yi maryam ke nima auren dai matsala ne wallahi yanzu shi yasa nake tausayin yan mata idan suna rawan kai wai su zasuyi aure kiga yarinya yanzu ba kunya tana fitsara.
Tace rashin sanin ciwon kaine mana tunda hankali bai kai ba sai idan an shiga ido ya raina fata kuma don mazan yanzu ko wata ba a rufewa za a fara saida hali idan kuma ka samu kishiya tace dawa Allah ya hada ta bada ke ba irin naku din nan.
Wurin wardrobe dina na nufo na fito da wasu material da zan saka a jikina tsab na shirya a cikin su ni kaina nasan kayan sun matukar karban jikina.
Tace gara da kika saka kayan nan don nasan yanzu gurin nan kamar kasuwa da a bokanta yan duniya irin ta.
Waya na dauko na kirashi ina fada mai zan fita yace ki jira driver yazo yanzu ya kashe a yadda ya amsa min wayan yasa na fahinci a gaban Nafisa yake a lokacin.
Don idan suna tare muna waya dashi yanzu ina ganewa ga yanayin da yake amsa min wayan daban ne da idan bata a kusa dashi.
Bamu dade da jira ba driver ya iso yace mu fito tare da laraba da yaran muka nufi asibitin gida tsit kamar ba kowa a cikin sa.
Maganan mu ya zama gaskiya don muna zuwa driver ne yai muna jagora dakin da suke tun daga nisa muke hagon su sun sako idanuwan su akan mu.
Canjin yanayina gaba daya ya basu mamaki don zakace ko baturiyar asalice tayi shigan hausa yadda komai nawa ya bude a lokaci guda ga traning din anty Salbiya da anty Hauwa na aiki.
Nayi masu kwarjini sosai a idon su yaran da mama larabane a gaba suna bin driver sai ni da maryam a baya da muka jero tare muna magana.
Gab da zamu shiga dakin ne wata buzuwa da ban santa ba take muna magana tana fadin ba,a fa barin kowa ya shiga daga nan ake mika masu gaisuwan su.
Ni kan mamaki nake na yadda naga yan yaren su a gurin da yawa haka ashe suna da hadin kai ne haka sosai nan dai gasu madan dasu sabuwa a gurin su ma.
Tsayin mu yayi daidai da fitowan Yusuf ciki yana ganin mu ya washe baki tare da fadin a kune tafe ashe ku shigo mana ko suna ciki AA din ma yana nan yanzu muka shigo.
Nace wa yan nan sunce ai ba a shiga inda suke ko yace akan wani dalili ba gaida ita kukazo yi bane mujen ku dan Allah ya fada yana fara tafiya muka bishi a baya.
Ya tura kofan dakin da sallama muna biye dashi na hango AA ya zaune da hannun nafisa dake kwance a saman gado duk ta sauya saboda damuwa.
Ga yar a kwance a gefen ta an rufeta da shorwel fari kallo daya nayi wa yar da sauri na kawar da idona shiko duk yai wani daburcewa da ganin mu.
Gaida ita muka fara yi tare da mata barka da arziki tayi kamar bata jimu ba shine yadan matsi hannun ta yace bakijin su Deedar na gaida ke ne ?
Ta dago kai ta kalle mu wani iri ta watsar tace kai ka san su don ni ban gaiyace su ba tunda nasan gulma ya kawo ai don suzo suga abinda ake fadin na haifa din.
Murmushi nayi ina gyara tsayina tare da dafa gadon nace mu bashi ya kawo mu ba don inda sabo mun saba da wanan zuwa mukayi muyi maki barka kuma mu gaida babyn mu.
Hannun ta ya sake ya nufi yar zai dauko ya bamu tace kabar min ya a inda take duk da take hakan tana ganin banson abina inson ta a hakan.
Nace dama ka barta ai tana barcin ta, ke banda abinki ina kika taba ganin jujin yara kowa ya haifi da ai yana son abinshi ya haifa.
Dauko yar yayi ya mikawa laraba ita tace yanzun ma zuwa kikayi nan ki karasa ta komay tunda baki so yar ta fito duniya tana numfashi duk da sherin da kikai mata tun a ciki.
Ba laifin ki bane hakan da Allah kike son yin jayaya mu bashi ya kawo mu ba daidai laraba na mike mun yar kamar kada in karbe ta nadai sa hannu na karbi yar tare da fadin ubangiji Allah ya baki lafiya kinji.
Na mikawa maryam sai sababi take muna muka mika mashi yar muka ce Allah ya raya muka juya yace wanan wai wani irin haukane akan yaran ma fada zakuyi ko may yarinya nata kanta cikin wanan halin.
Tace idan haihuwa yana da dadi tayi mana mu gani na juyo ina fadin zaki gani idan muna raye kwana nawa ya rage inji maye .
Haihuwa kan tunda ina tare da mijina ai yin sa zanyi da yardan Allah yadda kowa yayi shi kuma ki dai gani anayi nace yaushe kuma Allah ya fiki don dan zaki ya girma ko na nuna mata cikina na fita.
Samad wai may yarinyar nan ke nufi ne da maganan ta yace abinda kika tambaye ta ne ta baki amsa da nuna maki mana tunda ke baki san yakamata ba.
Kina cikin wanan halin haka har kinga wurin fada bazaki ji da abinda Allah ya jarabi mutum dashi ba wai kana nufin itama ciki gare ta komay yace baga shi kinga ta nuna maki ba.
Kururuwan ta ne yasa yan wajen saurin shiga dakin hankali tashe suka samay su taci kwalan mijin tana fadin wasau maganga nu da bata san tana fafi ba a lokacin.
Ya banbare hannunwanta daga jikin shi yana fadin wawiya mara hankali bazakiji da abinda ke gaban mutane sai kin jajibo wani fitinan kuma.
Ita din ba matana bace da ba zata haihu dani ba komay da kishi zai rufe maki ido kina wanan hauka haka yanzu ai kinji ma kanki wani tashin hankalin tunda haka kike so.
Samad Allah ya isa tsakanina dakai da yan uwanka yadda kukai min sai Allah yai maku shi kuma munafukin banza kawai azzalumi.
Madam ne tayi mai magana akan yaiwa Allah ya fice daga dakin ya kyale ta yan uwanta buzaye kuma na magana a cikin yare suna fadin may ye haka take yi ne wai.
Ciki ina bama zai yuyu ba wallahi tasan dai inda ta kwaso cikin ta take son kakaba maka kaiko daba kasan ciwon kan ka ka yarda dashi.
Ya juyo a fusace yana fadin gada ki soma sheganta min cikin jikin matana don nike da abina ni nasan kuma zafin abina.
Munyi dake ne idan na aure ta ban haihuwa da ita ko may ke da nake haihuwa dake fa madam ta samu ya fice dakin da kyat a lokacin mu har yusuf ya saka mun bar asibitin ko.
Yafito a hasale yana fadin shine dalilin da kaji nace muzo wurin nan yanzu don sanin halin Nafisa da nayi don kada suzo ta nemi salwanta min wani cikin kuma ta gama yiwa nata ta,adi.
Don Allah ka daina biye mata kuna haka mana AA a bainin jama,a tunda kasan halin abinka yace ina amfanin kullun a boye mata cikin jikin Deedar Yusuf ai gara ta sani idan ma mutuwa zatayi taje tayi wanan matar halinta ya isheni yanzu.
Hakkuri zakayi ka san halin mata akan kishi yanzu wanan abin kunyan da take damay yai kama AA yace ita ta sani yana tsuki.
Yanzun Nafisa kin tabbatar tun kwanaki nake fada maki ciki ne da yarinyar nan kika ce Samad yace ba ciki bane shi baisan tana da ciki ba a ina ta samo ciki.
Ai yanzun dai kinji ga bakunan su ko madam tace duk da cikin ne mun tabbatar din ai mu kwantar da hankalin mu muga cikin to mujira hauhuwan shi mukagani mana.
Damu take wasa ba har tana iya nuna wai ita mai ciki bane shi a dole ga mijin mai cikin fari a haihu din mu gani in shari ne ai kowa ya iya ko.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Tafiya muke a motar babu mai magana a cikin mu kowa da abinda zuciyar shi ke saka mai a lokacin duk mu a cikin motar sai maryam ne ta kawar da shirun da motar yayi a lokacin.
Khadi tunda kuke fada da buzuwan nan a gabana baki taba burge niba irin yau mace haka bata san Allah ba ita.
Ko wanan yar dake gabanta haka saye da naura bai ishe ta ishara taji tsoron Allah ba a zuciyan ta abinta ne fa Allah ya fara nuna mata.
Laraba ne ta karbe zancen da fadi ai irin uwar dakina sune daidai da irin wanan matar ina fada kullun don macen da ke nuna masu tsoro sai su kara zama shedanu a gurin su.
Ba karin abu muka gani a wurin taba wancan zaman da mukayi da ita da hajiya uwar gidan saboda ita sam bata da baki a gurin ta.
Idan sun fara sai dai mu shige daki ba dama mu leko ko na minti daya yanzun zatace dawa Allah ya hada ta ba da mu ba.
Ba girma ba arziki muka koma kaduna da zama don abin har yaso taba ta a lokacin sosai wallahi Allah dai ya gyara da yake iyayyen miji suna bayan ta ai da yanzu basu tare.
Don gaba daya ta juya kan babangida ga kowa ko iyayyen sai da suka tashi tsaye akan shi don gaba daya ya juya masu baya ne a lokacin.
Kowa yayi mamakin jin zai kara auren uwar dakina damaganan ya fito fili sai ana ganin ko ita ba zata iya dasu ba ai.
Abin mamaki laraba na rufe baki driver ya karbe zancen ta yace ai ba karamin dadi naji ba yanzun da naga hakan don mun sha wuya a gurin wanan matar.
Kafin ta fara tuka mota irin yadda muke fita daku din da zaran mun fita da ita sai mun sha fada a gurin oga ranan don sherin da zata kulla muna tace mun mata abu kaza.
Shi kuma ya rufe ido yaci muna mutunci ido rufe a kan ta kuma fa ba gurin alheri mutum zai kai ta ba.
Matar dake tambayan mu idan musan wurin wani mai asiri mu kai ta ko nawa yake aiki zata biya mu idan mun kai ta.
Wanan mace ai shu,umace kwanaki akan oga yasa musa ya dinga kaiki school da yai tafiya Allah dai ya gyara ba a kore shi ba sai da muka bi ta kan oga yusuf muka kai maganan shi muka samu yai wa ogan namu magana aka barshi sai dai aka maida shi office.
Kinga kuma zama office ba so shi muke yi ba don irin haka mutum yafi samu don idan anyi tafiya dakai ko aike wani guri zaka samu alheri dabaka zata ba a gurin shi.
Mussanman ke hajiya da kowan mu ke son ace ya kaiki wani guri saboda Alherin ki da girmamawa a gare mu.
Laraba tace komai akace tayi zata iya ba sheri a cikin sa don halin ta ne ake fadi ko ita hajiyan tawa tace ai ba kanwar lasa bace ita ma guri ne bata samu ba dai yanzun.
Dariya driver yayi yace hajiyan can kan gaskiya akwai rowa ba abinci ba kuma kulawa a gare ta sai nakasa.
Gaskiya yanzun kan muma muna fadin oga yakai ga mata kulun muna rokon Allah yasa wanan matar ta barki ki zauna a gidan nan don tsaye take a kan ki sosai yanzu.
Emanuel yace min ya kaisu wani guri da wanan kawar nata bakar nan mai jiki ya je ya kai mata wayan da ta bari a mota yaji tsoron inda ya gansu kuma ya samu ana maganan ki a cikin bukkan da ya shiga.
Muushi nayi daga inda nake zaune sai dai ban masu magana ba illa cewa danayi malam sani kaimu sahad don Allah daga nan mu dan yo sayayya a can.
Nau,in kayan girki na gwagwani da na kwalba zuwa na leda na sayo don Azumin da muke ciki akwai yawan amfani da kaya da muke kai da kai.
Gurin kayan yara na nufa na zabo ma yaran yan tufafi da takalma don na fara rage hanya sai yar baby daa nayiwa sayayya itama daga nan muka wuce wurin kayan sha dana ci muka dan taba muka fito zuwa gida don har da maryam can zamu tafi don anty ta bata gari.
Maryam ne take cewa wai kina nufin har da yaran wanan matar kika sayawa kaya komay ?
Nace maryam da yara nake kishi ko da uwar su gani nayi na sayawa wa yan kada yaga ban sai ma nata ba kin ga ba dadi zaiga na banbanta a tsakanin su.
Shiru tayi batace dani komai ba har muka kai gida ta lura ban jin magana don duk maganan da suke tun farko ban tanka masu ba.
Don irin yadda nake ji aa zuciya na ba dadi na farko yarinyar dana gani a cikin wani hali na biyu kuma zancen mu da Nafisa a asibiti yadda ta rufe ido tayi muna cin mutunci az bainar jamma,a kamar wace tayi cikin daba na sunna ba.
Zaman mu a a falon bamu jima da zama ba na fara fitar da kayan da muka sayo muna kallo daidai nan ya shigo falon fuska a daure.
Bin kayan dake baje a kasa yayi da ido sai kuma ya dago yana bi mu da kallo har lokacin fuskan shi babu walwala a cikin sa.
Nima daure fuska nayi ban ko samu gaida shi da dawowa ba sai laraba ce ta fara mai sannu da zuwa tana kokarin tatara kayan dake gurin a kasa.
Wuri ya samu ya zauna daga gefe haka yasa maryam dake daga kwance mikiewa zata shige daga ciki ya dakatar da ita da fadin zauna abin ki maryam ba wani abu bane ai.
Ya joyu gare ni yana fadin Deedar may yasa baku da hakkuri ne dukkan ku kunje asibiti kuna sayar min da hali a gaban mutane da matan abokaina.
Yaya AA nine
ma mai rashin hankalin ke nan ba ita da mukaje gaiyarwa ba ta tare mu da bakar magana yace a fusace dukkan ku baku da hankali.
Na gane ni kuke son tozartawa a idon duniya idan ita bata da hankali ke baki da shine don may ba zaki kyale ta ku fito bakin ku alaikum ba tunda kin san halin ta.
Wani irin takaici da bakin ciki ya zo min a wuya ya tokare ina jin wani bacin rai na zo min kamar zan fashe.
A cikin wani irin murya nace a fusace ni wanan abin ya isheni ya isheni wallahi kulun mutum shine mai laifi a furin ku baka ganin irin cin mutuncin da take min ko yaushe magana ya taso sai kayi kokarin dora laifi a gare ni.
Gaskiya na gaji da wanan halin abin yai min yawa a gidan nan da wannen kuke son inji wai daga ciki ?
Yace ni ba ruwa na da abinda ke a tsakanin ku mutunci nane ba zan yarda kuna zubar min a idon jamma,a ba ko yaushe.
Idan ita bata da hakkuri bata dauki girman ta ba don may ke da ilimin ki zaki tsaya kuna irin wanan sai da halin akan titi haka.
Yanzun dai nice mai laifin kake nufi ke nan tunda ance inda fata yafi taushi nan ake duka ta gama karanto maka hauka kazo ka sauke a gurina ko .
Hawaye ne ya kawo min bayan na gama maganan mikewa yayi a hasale yana fadin ban son irin wanan halin da kuke na zubar min da mutuci a baiyanan jamma,a
Har yakai kofa nace cikin daga murya mutunci kan ai koda nazo na samay shi a zube gidan nan ya juyo ya kalle ni ya girgiza kan sa ya fice.
Labara dake daga kofan kitchen tana sauraren mu tace kayya uwar dakina ai da baki biye mai kunyi haka ba shifa hakkuri bai baci.
Nace ina hawaye mama na gaji ne da abinda mutumin nan yake min yanzu fa a gaban ku akai komai da ya faru, amma yanzu kin gani akaina yake son ya maida maganan.
Tace indan wanan ne fa kinyi kuskure babba domin ba wani abin halitta da rayuwa take zuwa mai daidai a yadda yake son ta.
Ba tare da ganin akasin ta ba kuma may zaisa ki damun kanki da abinda yace yanzu ai gaskiya ya fada don ke mai ilimi ce gaba da baya.
Ke din yake gani zai wa magana yaji sanyi ke kuma din yanzu kin bultsaye masa ina kuke son ya dafa yaji saukin wanan alamarin.
Ga ya masa mara lafiya a asibiti cikin halin ka, in dana in ku kuma ga taku rikicin yanzu kin san iya irin bala,in da sukayi a bayan mu kan zancen cikin jikin ki ne ?
Sha,anin kishiya ko ba irin wanan ba sai mutum ya hada da hakkuri yakanci riba duk mai gaskiya fa ki tuna shike da riba akan komai .
Don haka kada ki kara wanan irin gangancin da kikayi yanzu ai komai ake a sane yake ina jiye mata ranan da zasu hadu mutum mai hakkuri ba a iya kaisa bango ba.
Dama ita amarya a duk inda ta samu kanta dole sai tayi hakkuri da biyayya kan takai ga gina kanta yadda take so.
Kaina na duke kasa ina share hawaye nace nagode mama tace nice ai da godiya da kika fahince ni kikai amfani da magana ta.
Don haka kada wanan magana kice zaki rike shi a rai inda kukayi shi ku barshi gama kin ga cikin wata mai alfarma da muke.
Ita bata tsaya ta nemi falalan sa ba ke da keyi ta kawo maki cikas acikin sa dama kuma burin ta ke nan taga ta dakushe ki a wurin miji ko ta halin kaka.
Maryam da sai yanzu tai magana tace dadin zama a kusa da manya ke nan don ni har na goyi bayan yadda khadija din tai mai yanzu amma maganan ki mama ya sa na hasaso wani abu a yanzun haka.
Ganin yake idan khadija tana kyaleta a bainan jamma,a zaifi da su dinga saida hali ana masu daukan baidaya .
Kin gane ke nan yar nan ai ki rabu da shu,umar mace a gurin kishi Allah dai ya tsare ya kare kawai za a ce.
Ranan ban shiga kitchen ba su sukai aikin komai yadda ya kamata tun kan ya dawo na shiga part din na gyara na jera komai yadda ya kamata na shan ruwa.
Samira ma tazo ta dauki nasu zuwa part din su a falo ya hadu da ita dauke da kayan abinci ta fito daga part dina zuwa nasu ya shige bayan ta gaida shi a tsartsaye.
Yana shiga yaga ranan har na aje mai kayan abincin sa ko ba kamar yadda na saba ba idan nayi girki sai ya dawo nake kawowa part din.
Wanka ya shiga kafin a kira sallah sufita inda suke sallah dasu yusuf mama laraba takai masu kayan buda bakin su acan sai sun isha,i suke shigowa suci abinci su dan taba hira kafin su watse.
Sai dai yanzu da zancen asibiti yazo ne naga da sunci abinci sai su bar gidan zuwa asibitin wurin Nafisa.
Mun idar da sallah a nan falo nayi sallah kasancewar azumine ina zama nan muyi buda bakin mu gaba daya wanda bayan ruwa sai diyan ice dana kan danci sai zuwa dare kuma in dan sha tea shine abinda nakan iya ci kawai in kwanta ban dogon hira sosai don nakan gaji da ansha ruwa nakan kwanta wani lokaci a falo sai idan sun gama kallo mama ta tadani.
Ranan da nake da girki kuma ban jimawa sosai a part dina nakan shige wurin shi in kwanta yakan so matsa min da sai naci wani abu ganin idan ya matsa min din naci ina wahala yasa ya kyale ni hakana.
Yau da shan ruwan su yace suje asibiti ya duba su suna zuwa tana zaune har lokacin cikin ba sakewa tare da ita yanayin ta ya nuna tana cikin tashin hankali.
Yusuf ne ya iya gaida su tare da tambayan jikin yarinyar sauran mutanen dake gurin ne suka karba mai da sauki har tasha nono da likita yace a bata.
AA ya zagaya ya dauki yarinyar ya dan dubata ya dade da ita a hannu kafin ya mayar da ita ya shimfide ta saman gadon ya dago yana cewa Yusuf su tafi.
Sai lokacin tayi magana kamar cikin fada tana fadin ku tafi ina kuma yanzu yace zamu gida ko da magana ne kuma.
Ba laifin ka bane hakan tunda ka auro makirar mace gidan ka ana fada min ban yarda ba sai yanzu na kara tabbatar da hakan jikan mayu .
Idan suna takama da maita gida tazo don sai na nuna mata ita ba kowa bane a garin nan don sai na wullakanta ta kafin ta kai ga nufin ta a kaina.
Ganin Yusuf bada niyar tafiya ne ya fara tafiya ba tare da yayi magana ba Yusuf din yace Allah ya sauwaka yabi bayan shi ko minyi talatin basuyi ba a cikin asibitin suka fito.
Direct ciki suka shigo sai bayan sun zauna ne Yusuf ke fadin yau banga kanwata tazo gaida mu ba mana yace tana ciki da maryam.
Au tana gidan nan ke nan har yanzu yace ina ganin haka bayan sun gama cin abincin Yusuf bai dade ba yace zai tafi don ganin yanayin abokin nasa yau ba dadi.
Jin cewa suna gida har yanzu a wurin laraba da tafita dauko kayan da sukai buda baki dashi waje yasa nayi mamaki a raina.
Har wani lokaci na kara tabbatar da yana gidan bai fita ba kamar in share shi ganin ina hamma don ranan na wuce lokacin da nake kwaciya idona biyu muna hira da maryam.
Laraba tace dani da kinje ki kwanta don barci kike ji wanan mijin nawa ko kawar daga mai son jiki ne sosai.
Ba yadda zanyi in share shi haka na daure na shiga na shirya na fito nayi masu sai da safe suka rufe kofan part din mu ni kuma na tafi wurin shi.
Koda na shiga dakin na samu shima ya kwanta sai dai baiyi barci ba don na ga fuskan shi a dum light din dake kunne a dakin dake dan haska dakin kofan nayiwa key na nufo gadon na kwata dan can nesa dashi.
Shiru ne ya biyo dakin na tsawon wani lokaci daga cikin mu kuma babu wanda yayi barci a lokacin.
Sai can naji muryan shi kamar daga sama yana fadin ya kamata ki sauke wanan fushin karki haifar min diya masu fushi irin ki ko su dara ki.
Kanzil bace dashi ba sai gyara kwanciyar danayi na bashi baya yace na dauka ke din mai ilimice da zaki fahinci saidai na manta da halin mata da haka kuke komai ilimin ku.
Shiru nayi mai yace bakya jinane dake fa nake magana Deedar ina matsayin mijin ki ina magana kin bani baya wanan tarbiyan a ina kika samo shi ?
Ya mirgino yana taba ni nace kada ka tabani don Allah ka barni inji da abinda ya damay ni please .
Dan shiru yayi sai kuma naji yace becouse of what zan daina taba ki kina matana da zaki ce in daina taba ki ina a matsayin mijin a gare ki kuma.
Nace kadai san inda matan ka suke da suke bata ma wasu rai ka goyi bayan su kuma dama ba sona ake ba nuna fin karfi da iko yasa aka kawo ni gidan nan ba don so ba.
Sai don cin ma wani manufa taka ta daban a kaina kada kuma kaga na zauna a gidan ka kace zaku hade da matar ka ku gasa ni cikin ruwan sanyi yadda kuke so.
Na zauna gidan ka ne saboda biyayya ga magabata har ka ganin haka don haka enough is enough dakai da matar ka don kun fara kaini makura kada ka dauke ni yarinya kace ko ban gane inda ka dosa bane dani.
Shiru yayi yana sauraron kalamai na da nake fadin cikin zafin rai da yaji nayi shiru yace kin gama maganar ki nace yanzu na fara yace to karya kike fada da kikace wai zaman biyayyan iyayye kike dani.
Don kowa yasan da kina so na ai ba haka ake zaman biyayyan iyayye ba dakikace kina fada a kaina kice wai ba son ki ake ba ko baki sona.
Kyale shi nayi na bashi baya ba tare da na juyo ba balle in nuna naji maganar shi yace hakkina zaki ban kafin ki kai ga barci ni shine bukata na yanzu ba wani abu ba.
Dama baka da zancen da ya wuce wanan ai a gare ni don shine kawai tsakanin mu dakai murmushi baiyanane yayi ina iya jin shi daga inda nake kwance.
Ranan dai ban yarda na bashi abinda yake so din ba duk da maganan da yake min cikin sanyin rai sai na dauka yaudara ce kawai irin ta maza idan suna son kasancewa da matan su.
Duk sayin nan bai a cikin natsuwa abubuwa sun taru sun rikice masa a kai ga wurin Nafisa ba dadi sai fitina take masa da yaje asibitin akan cewa da yayi sai an sallace zasu fita da yarinyar waje.
Nan ta haushi da masifa tana fadin don ciwon ba ajiki shi yake ba yasa yace hakan don kawai yana da ida yake rage dare a gidan sa.
Gashi kuma har lokacin ba wani sakin fuskan da nake mai a bangare na kamar baya ko magana daga eh sai a, a idan yai tsowo kuma ba mai yawa bane.
A dole nima ina son jan nawa kambun na mata ina nuna nima mace ce ban san haka halin sa yake ba mussanman ma idan mace tana da ciki.
Yana matukar tausaya mata sosai don acewar shi bakanta wa mace mai ciki yana jawowa yaron dake ciki matsalane.
Har wanan lokacin babu wani dan uwan sa da yazo daga kaduna duba su Nafisa din don Abba yace ba wanda zai sake zuwa harka idan na Nafisa ne gidan shi.
Sai lokacin kumane abin ya bata mata rai take yawan korafin akan haka tana fadin dama nasan ba,a sona da kai tunda gashi har na haihu ko dan aikin gidan ku ba,a turo min ba.
Yakance da ita laifin wa da suke zuwa dubaki kina masu wullakanci su ba zuciya ke gare su ba da zaki dinga koje su suna biye dake.
Dama don ni suke zuwa yanzun kuma sun gaji sun ba kan su lafiya ga irin wullakancin da kike masu din don haka kada kiga laifin su.
A gun maryam na fara jin wai wani sati zasuyi tafiyan su nai mamaki rmtare da tambayan ta ina taji wanan magana haka ?
Tace min a bakin da baya karya taji don har angama shirin tafiyan su yanzu haka lokaci kawai ake jira sai ban dauki maganan da wani muhinmanci ba a raina.
Tunda nasan da gaskiya ne da ya fada min ai sai shirin sallah da aka fara inda yasa in mai list din abubuwan da zamu bukata da wanda zai aika gidan su.
Banyi sanyi a gwiwa ba na zauna nayi list din duk abubuwan da yace din nayi zaton zai rage daga ciki sai banji yayi korafin ko daya ba sai cewa da yayi zai min kari a sama koda bukata hakan ka taso.
Daga haka muka bar zancen sai bayan kwana biyu ne ina zaune naji alent ya shigo min na duba naga irin kudin da ya turo min ga account kirasa nayi ko bani yai niyar turowa kudin ba yace shiya turo idan ya dawo gida zai min bayanin komai.
Bayan ya dawo gidane Yusuf ya zo sunyi buda baki ya wuce mun shiga kwanciya yana zaune yana aiki a laptop di yace dazun kinga kudi ko ?
Nace eh sai dai bansan ko na may ba kudin yace zancen list din da nace ki min shekaranjiya ne sune na turo maki don jibi zamu fita da yarinyar nan zuwa india a dubata.
So kiga banda wani time issashe da zance zan leka kaduna kuma tun da tafiya ya kamani tunda ya fara maganan bance tak ba har ya gama nace Allah bata lafiya na gyara kwanciyana .
Yace baki ce komai ba mana ina magana kinyi shiru nace bayan Allah ya bata lafiyan dana fada kuma may kake son ince kuma ?
Murmushi yayi yace at list ai zakice kudin sunyi ko ba zasu isheku ba har in dawo ko nace zasu isa din ai daga haka bance komai ba yakara cewa babu ko Allah ya dawo damu lafiya ?
Baka so in fadi haka ba ai daka fada min tun farko bawai sai yanzu da tafiya yazo kusa ana gobe zaku tashi.
Kai mata may kuma kike son in fada maki bayan wanan yanzu ba gashi na sanar dake zancen tafiyan ba.
Ban face komai kar kuma ace ina bakin ciki ko kishi akan za a kai yarinya wurin neman magani.
Ida ni mai halice nima da naba da nawa gudun mawar kaita asamo mata lafiya yarinya mai taimin ita yar mala,ilar Allah da ita nima kaina mai maganan ai ban wuce nan ba ga Allah.
Amma ai ya kamata ki muna fatan samun nasara kk dana fada maki yanzu din nace bayan wanda na furta idan bakina kake son ji kan haka bazakaji komai ba ubangiji Allah ya bata lafiya yasa aje a cikin nasaran ubangiji yace amin haka nake son ji tun farko.
Kyale shi nayi na kakaro ma kaina barcin dole kafin ya gama abinda yakeyi din sai nasari na yaji a bayan shi na fara barci.
Bai zauna ba washe gari tun safe da ya fita yana wurin fafitukar tafiyan su laraba ne ke tambayan shi nace kin san zasu fita gobe da yarinyar nan zuwa india nasan yana can yana shirin tafiya ne.
Bamu dade da magana ba ya shigo lokacin har an sha ruwa anyi sallah ko part din mu ya nufo yaran suna rige rigen gaida shi ya amsa ya samu wuri ya zauna anan falon.
Laraba ta gaidashi ya amsa ta tabaye shi ya mai jiki yace da sauki
Gobe in sha Allahu da safe zamu fita zuwa waje da ita da yardan Allah takama addua da fatan samun sa,a.
Ina kallon shi ya dan kalle tare da fadin madam ya gida kuma nace muna lafiya yace ce kun gani sai yanzu matsala aka samu kan pasphot din yarinyar ya dan kawo muna tsaiko.
Nace yanzun an gama komai ko yace insha Allahu yana mikewa tare da fadin to mama nasan da safe koda zan fita baku tashi ba.
Tace hakane ubagiji Allah ya kaiku lafiya yasa ai farar tafiya ya amsa da amin nace Affan kuyi sallama da Abba zaiyi tafiya gobe suka shiga ce mai Abba Allah yakai lafiya ya amsa da amin.
Sai da ya dan jima da tafiya na samay shi a dakin har yayi wanka yana cin abinci nace yau ina yayana yake baizo cin abinci ba.
Yace tare muke yanzu ya wuce gida ya huta don kowan mu ya gaji yau ina hada kayan abinci guri daya yake tambayana ba wani matsala a kara muna kudi ?
Nace ba kudi bane matsala ta ni don haka kabar kudin ka nagama hada kaya na shige nabarshi yana mamakina a gurin.
Sai da ya shigo ya kwanta naji yace ke may matsakar ki ne wai khadija nasan maganan serious ne tunda naji ya ambaci sunana in full nace bada matsalan komai illa a dinga bani hakki na a yadda ya dace ba amai dani wata bican ba cikin ku.
Sai da kuka gama shirya tafiyan ku ne zanji daga shanun talla wanan abin da kake min kai mun adalci ke nan yace shine kawai matalar taki.
Na kyale shi shima shiru yayi haka muka kwanta kowa da abinda ke a zuciyar shi hudu saura ya fara shirin tafiya ina jin sa na kyale shi har ya shirya sai lokacin ya tashe ni inyi sahur da ruwa da nake sha.
Nace zanyi dan ajima kadan kafana naji yaja tare da fadin ni zan tafi Yusuf yana waje suna jirana na bude ido tare da mikewa zaune nace Allah ya kai lafiya yasa aje a sa,a.
Yace amin ya dauki dan case din shi ya rataya bai dauki wasu kaya ba taee dashi ya tako zuwa inda nake yace ki kula da kanki da gida nace insha Allahu.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Tun tafiya shi ban koma barci ba karshe ma na tataro na dawo part dina sai dana dade ina dan kwankwasawa mama laraba ta bude min.
Ina shiga tana fadin masu tafiya sun tafi ke nan eh kawai na bata amsa dashi na shige ciki ban tsaya ba.
Na isa dakina kan gado na kwanta ban koma barci ba don lokacin sallah da ya gabato mamaki ne fal a cikin zuciya na da tunanen a haka zan zauna da wanan mutmin ba wani kima da daraja sai idan na biyan bukatane tsakanin miji da mata kawai.
May yasa zai min haka bayan ina zaman zama na a gidan mu yasa aka zarga mashi aure dani alhalin yasan matar shi ba bari zatayi ya zauna da wata mace ba a rayuwan su.
Duk wani abinda aka ce inyi na jan hankalin miji daidai gwargwado ina kokari yin sa don dai inga na jawo hankalin shi a gare ni.
Sai naga saukin daga wurin shi lokaci daya kuma sai abin ya kara birkicewa a tsakanin mu nace a raina wanan wani irin zamane haka.
Gaskiya sai aka kamar kishiya ta tsoron kishiyar ta ko mijin ta bazata iya mata komai ba idan tana iya shege a kan su da miji kamar yadda nake gani da da ban shigo gidan ba.
Sai nake ganin Fatine kawai ke kyale ta don haka ta samu wuri tana iya shage ban san cewa abin bada nan bane ashe da zaran miji ya goya ma mai iya shege baya dole ke ki zama yar bi a tsakanin su don a zauna lafiya.
Nace a raina ba komai yaje idan ma wanan matar tashi ce da yake rawan kafa a kanta nasan da wuya su kare lafiya a can din.
Ina cin wanan tunane ne agogona ya buka na mike na shiga bandaki na dauro alwala nazo na tayar da sallah.
Ina tsaka da sallah ne laraba tazo dakin ta tayar dani sai ta samu ina sallah ta juya ta fita ta koma falo don tafi zama a nan.
Na idar na dade zaune ina kai kukana ga Allah wanda yawan addua,a na yanzu biyu ne Allah sauke ni lafiya ya ban komay ke cikina mai albarka sai kuma fatan in ci jerabawa na dake gaba na yanzu.
Na dade zaune sai da gari ya haska sosai na tashi na koma saman gado na kwanta barci ya dauke ni wanda na jima inayin sa a dakin.

INDIA
Saun sauka lafiya basu tsaya neman masauki ba asibiti suka nufa direct daga nan airport din already an riga da an masu bucking din likitan da zai duba yarinyar acan.
Haka yasa basu wani sha wahala ba sosai sai dai wanda ba a rasa ba kawai a garin da ba naka ba idan kaje.
Likitan ya duba yarinyar inda ya tabbatar masu zasu iya mata aikin a wuein cibiyar ta yanzu sai na kai din ne zasu dan duba su gani idan zai yuyu ai mata shi yanzu saba da kankantan ta.
Gado aka ba su wanda uwar zata dinga shigowa bayan awa bibiyu tana bata nono tare da duba yar sai bayan kwana uku idan sun gama aune aune zasu yi mata aiki su rufe gurin da yake bude din wanda tun a Nigeria likitoci suka so suyi mata aikin uwar tace bata yarda da hakan ba sai dai suje waje.
Masauki suka nema wanda baida nisa da asibitin don samun saukin zirga zirgan su zuwa duba yar tasu dake cikin halin hau,ila,i yanzu.
Wanka ya fito ya canza kayan jikin shi i zuwa masu sauki da ya saya da saukan su indian don bai dauko wasu tufafin kirki ba da zasu zo don gudun wahala dasu.
Abinci yai masu odo aka kawo masu ga abincin ba wai dandanon shi ya mai bane cusawa kawai yake kada ya zauna da yunwa ga azumi da yayi .
Sai dai zuciyar shi yana cikin damuwa damuwar yarsa dake cikin wani hali sai kuma damuwa akan yadda muka rabu dashi ba a cikin dadin rai ba duk da na yi kokarin nuna mai da babu komai.
In ya tuno yadda ko rakiya ban mashi ba da zai bargidan ina daga gado zaune tankar ba wani guri zai tafi nisa da gida ba.
Ke nan kishi nake akan zuwan su ko fushine haka na duk da yasan da na fadi korafina akan rashin fada min da baiyi ba da wuri sai da tafiya tazo masu gap ya fada min.
Idan kishi nake akan ya kawo yarshi asibiti nayi hakan may yasa ban kishi akan su Affan illar cusa yaran da nake kokarin a gurin shi.
Ya kuma yi tunane zaman Nafisa a asibiti daga part dina yaran nafisa da yan uwanta suke dauko abinci suci ai duk da halin zaman da nakeyi da uwar su din don haka ba akan fita da yarinyar nakewa ba sai dai fushine na ba gaira ba dalili irin namu na mata nake tsira mai.
Don haka yace a ranshi bari yaga iya guduna ba zai kira ba sai idan nice na nema shi ya kwanta yana kokarin share zancen a ranshi.
Yusuf kawai ya kira ya sheda mai isar su sai kuma bayanin da yai mai na abinda likitoci suka ce akan yarinyar.
Yayi mashi fatan samun sauki tare da nasara a guri aiki yace zai kira da safe yaji halin da suke ciki kashe gari sukai sallama ya kashe wayan.
Nafisa dake ta waya kwance a gefen shi sai hira take da madam akan wata da za,a hada ta da ita a india tai mata iso wurin wani bokan indiya .
Shiyasa ma ta nace akan sai sunyi tafiyan don tana ganin kamar a kasan ne sa,an ta yake don yanzu idan tana son mutuwar ta to tana son zamana a gidan AA.
Ko nawa ne zata kashe don ta riko kudi sosai a tare da ita wanda tasan zasu isheta shige da fice a kasan na indiya.
Zancen yar ta ma bai damay ta ba don bata ki yar ta mutu ba ta huta don tana ganin ba wani rayuwa zatayi ba a hakan da take ta manta da Allah ne mai yin komai yadda ya so.

KHADIJA
Ko dana tashi na yi mamakin barcin da nayi ranan don har sha biyu ya gwauta ko sai dai damuwar da na kwanta dashi ya rage a zuciyana don tun barci bai dauke ni ba na yanke wa kaina shawara gara inji da abinda ke gabana in fita batun su can.
Wanka nayi na fito falo na zauna laraba suna cikin daki da yaran ina jiyo hayaniyar su daga inda nake zaune tv na kunna wanda karan tv ya jawo hankalin su gare ni.
Sai gasu sun fito daddy ne sarkin son jiki yana fitowa ya nufo ni na dan rugumay shi a jikina tare da fadin daddy mama an tashi lafiya , ?
Laraba tace daddy ko sarkin rigima wanan tsohon naku akai fitina yanzu wai shi dole sai rigar dan uwan shi zai sa a jikin shi bai son nasa tun dazun rikicin da mukeyi ke nan dasu.
Nace ina jawo yaron jikina kyale mama kaji da Affan idan mun fita zan sawo ma sabbi kasa kai kadai bada Affan ba.
Haka yasa yaji dadi sai ya murmusa ya sake ranshi sosai naga kaman shi da mahaifin su da ya dan murmusa din da da Affan nake ganin suna kama da AA din kawai.
AA ne ya fado min a raina nace ko a wani hali suke ciki yanzu a can Allah dai yasa su dace ai wa yarinyar nan wani abu a can din da sukaje.
Mama ne take fadin yau kan kinsha barci ai zasu tayar dake nace don Allah su barki ki dan runtsa don ana son mai ciki tana samun barci irin haka.
Nace aiko na runtsa din sosai wallahi mama dama ga gajiyan jerabawan da nayi yana bina ban samu hutawa ba wanan zancen haihuwan yazo kuma.
Tace suna can dai ko a wani hali suke ciki yanzu ko kunyi waya da sune kiji ko sun isa nace idan bashi ta kiramu na samu lanban shi tace ba ai waya bai yi a tsakanin mu yanzu.
Tace hakane abin ashe ai dana dauka zai yiyu ki kirasu ki samay su a can da tasu nomban ta nan da suke amfani dashi ai.
Nace sai dole su sa na kasan idan sun kira mun samu layin su da suke amfani dashi can ne zamu samay su.
Tace amfanin bokon ke nan ai dariya nayi nace mama ke ko dan primary din nan bakiyi bane ashe tace wa ya bamu wanan gatan a kauyen mu lokacin mun ai mata basu karatu sosai har zagin masu yi din akeyi a lokacin.
Nace ikon Allah gaskiya da anyi abu wanda diya matane akafi cutawa ga rashin barin aikararun din don su maza ai sunayi ba a faye sa masu ido ba kamar diya mace.
Wayana yai kara na duba hajiya mama na gani nace a fili yau hajiya ce ta kirani kuma wanda dama nice kwana bibiyu nakan kirata mu gaisa.
Na dauki wayan da sallama tare da gaida ita ta karba min da fara,a tare da tambayana yara da mama laraba.
Nace suna lafiya gamu tare ma dasu tace ki gaida mun su nace zasuji insha Allahu.
Dan shiru ne ya biyu baya sai can tace sai kuma nake jin wai mijin naku ashe sunyi tafiya zuwa kasan waje ne kai yarsu asibiti shine bai sanar da kowa ba.
Mamaki naji a raina nace wai may AA yake son ya zamane duk ya rude akan wanan matar tashi yar matsala.
Sai dai a fili cewa nayi mama kila tafiyan a bazata yazo mai don nima sai da tafiyan tazo gap ne na samu labari a wurin shi.
Yanzu khadija abinda yaron nan yake yana kyautawa kan shi dani ke nan sam bai dauke mu da wani muhinmanci ba a rayuwan shi.
Wanan bakar matar tashi tana kokatin sai ta rabashi da kowa nasa ta huta shine farin cikin ta ita.
To idan haka take so sai ta zuba ruwa kasa tasha don ta samu yaje tunda ita ya zaba akan mu sai yaje gata gashi mun bar mata.
Sai dai abinda zance dake shine ki kara hakkuri a zaman ki a cikin su nasan kinayi sai dai ince ki kara din.
Nace mama na gode sai dai don Allah zan baki hakkuri kan danki kada kice haka don samun haske a gare shi ko yaushe udan kince haka mama kamar kin yafe shi ke nan a cikin diyan ki baki daya.
Tace khadija idan bance hakan ba may zance shi kadai ne da namiji da Allah ya hore min yanzun baki ganin Suraj kanin sa ne na baya amma baya wuce magana da shawara da mahaifiyar shi.
Mama don Allah kiyi hakkuri insha Allahu shima zai dawo kamar yadda kike so har ma ya dara duk wani a gidan .
Murmushi naji tayi tana fadin kai kina son ki kare mijin ki ne a gurina khadija bayan kema a yanzun kina shirin zama uwa ga wasu kin kuma san sherin kishiya yadda yake.
Yaya ba zan saka damuwa a kan haka ba kin san ko ba ai magana a fili ba dole ne ayi shi a boye yau bakiji urin bacin ran da nake ciki ba dana samu wanan labarin.
Nace mama kiyi hakkuri bai kyauta ba kan gaskiya don ko bai kira kowa ba ya kamata ya kiraki tun farko ya sheda maki halin da ake ciki ku sani adduan ku ai shine jagora a gare mu.
Tace ke kika san wanan amma babagida sam narasa gane inda ya dosa da irin wanan rayuwar tashi baiko tunanen shima ya fara tara iyali a bangaren shi yanzu.
Ni dai hakkuri na bata don banda shi ba abinda zan iya cewa nasan kuma duk maganan ta gaskiya take fadi.
Don babu uwar da zata so ta haifi da yace bai shawaran komai da ita komay kuwa ya zama a duniya.
Laraba ke fadin hajiya ranta ya baci ne hakan akan maigidan ku kuma nace abin ne sai hakkuri mama don kyautawa bai kyauta ba gaskiya.
Ni ina ganin bai kyauta min ba ashe ga idan bai kyauta ba din da tushe Allah dai ya sa ya gane gaskiya ya daina hakan don mama tana da gaskiya wallahi .
Ai yanzu kin samu abu yayi sauki ke nan idan da sabo ai yakamata itama hajiyan ta saba ni nake ganin kamar dai haka rayuwan shi take ba mai son yawan magana ba ne shi .
Shiru nayi ina tunane kafin in mike tsaye tare da fadin Affan kuzo mu dan zaga kafin a kira sallah ko.
Muka fice daga part din muna fita falo buzayen nan suna zaune ga butar shayi sun dora a tsakiyar falon yana tafasa sai abin ya ban mamaki a raina har na kasa daurewa nayi masu magana.
Wanan wani irin dabi a ce haka kuke wa mutane wanan ai ya zama ganganci a gare ku koda baku san zafin kayan dake cikin falon nan ba ai kuma kun san zafin amfani dashi tunda kun fi kowa marar abinda ke cikin falon don kullun kune a cikin sa zaune.
Dije munyi wanin abinda bai dace bane kike fadar haka inji yanyala tana dagowa daga kwance nace yanzu don Allah haka ya dace ku saka wanan abin anan haka ?
Ko da masu gidan basa nan ai ku kuna nan ko kuma kuna amfani da kayan wuta a gurin tace yo ai in wanan ne ko masu gidan da suke nan muna amfani da abin mu.
Don haka dabiar mu yake buzu baya yayi sai da shayi kowa ya sani nace idan ma bakuyi sai da shayi sai kuyi a cikin kitchen don ban lamunci kuyi shi a nan ba din.
Idan kuma kunce ba haka ba yau sai a raba falon in san bangare na da naku yanzu a cikin wanan watan da muke mai albarka a wanan lokacin ne mace zata fito tana shan abu da rana kiri kiri haka.
Tace yo Dije sai dai idan wani zancen na daban kike nema a kan mu ko Alhajin dake da gidan ya gamu ya kyale mu a hakan.
Nace yau ni ba zan kyale ba don ban taba ganin kuna haka ba cikin yare naji samiha tana magana wanda na fahinci tsageranci take son yi.
Zuwa nayi with full confidence na dauke abin wutan a gaban su zuwa kitchen din gida wanda tsami da dauda ya cika shi na kai na aje na fito.
Na dawo falon na zauna ina jin suna zuba yare akaina wanda nasan zagi na sukeyi ban kula su ba sai sai samiha ce tace wanan dai jan magana kike son yi a gare mu.
Kin san kuma ba kyale ki zamuyi ba tunda kafin ki shigo gidan nan kin samay mu da yar uwan mu a nan ne don haka ganin bata nan zaki zo ki kafa muna naki ikon a kan mu.
Nace yar uwar taku gidan ta ne nan ko may yadda take a gidan nan haka nake auro ta akayi auroni akayi don haka ba fina tayi ba ga maigidan.
Duk abinda kuke bawai tsoron ku nake ji ba kyale ku nake yi don kawai a zauna lafiya idan kuma wata tace zata fada min maganan banza yanzu zaku gane kalana a gidan nan.
Wasa wasa maganan ke girma gare mu na ko haukace masu a gurin har yakai mama laraba fitowa a part din mu ta tsoma baki akan su bari don samiha ta dauko dahuwar tasu ta dawo dashi falon wai taga abinda zanyi.
Cikin ikon Allah muna haka sai ga Yusuf kamar wanda aka kira ya shigo gidan duba mu ya samu ana wanan fitinan .
Rai bace ya daka masu tsawa yace baku da hankali ne mace da ciki haka zaku tarar mata wanan samun wurin yayi yawa haka gare ku.
Ya zama dole yau a raba falon nan kowa cen ku ta rike bangare ta har maigidan ya dawo yasan yadda zaiyi daku a gidan nan ku ishi wanan yarinyar tana hakkuri da halin ku dana yar uwar ku amma duk baku ganin hakan.
Bai bar gidan ba sai da ya kira wasu da ban sani ba yace suzo gidan har wajen karfe hudu ana magana daya a gidan dole aka raba set din kujerun biyu aka bar hanya a tsakiya yace ba zai kore su ba yanzu don maigidan yai tafiya amma su kwana da shirin idan ya dawo dole ne asan abinyi kan su tunda ba don Allah ya kawo shi ba da bai san abinda zasu yi min ba.
Yai masu iyaka da mu da komai na fanni na yace idan yaji wani abu ya taso kuma zai dauki mataki sosai a kan su don sai ya sa an daure su.
Karshe dai sukace don yaga yar uwar su bata nan ne ya wullakan ta su yace idan da tana nan ma abinda zai masu daya fi wanan don da basu kwana a gidan bai mai zuwa shida sai gashi da yan sanda mutum biyu yace su zauna a get din gidan su kula da komai na gidan.
Wanan abin ya kara tayar da hankalin su sosai madam suka nema suka fada mata halin da ake ciki shawara ta basu akan sai sunyi hankali don Yusuf din nan kamar ya shanye maigidan ne.
Don haka suyi hakkuri su bimu yadda muke so har yar uwar su ta dawo gidan yanzu ba komai ya daga masu hankali ba sai yan sanda dake gadi a kofan gidan da bindigogin su shine tashin hankalin su.
Ya kuma kira maigidan yace yai wa nafisa ma gana idan yan uwan ta suka taba ni sai ya masu wulakanci sosai tare da mashi bayanin komai dake faruwa.
Ranshi ne ya baci ya samu nafisa di yai mata tas dama kuma gashi suna rikici a tsakanin su da zuwan ta ta tsiri yawo har lokacin zuwa ba yarinya nono yayi bata a masaukin su.
Kiran su tayi ta tambaya yadda akayi suka fada mata ashe dama ta basu go ahead idan nai masu wani gani gani su doke ni har sai cikin jikina ya zube idan kuma sunyi ban kulasu ba din su san yadda zasu tsoratani a gidan.
Sai gashi kafin suyi din ni na fara magana da har yakai akai min iyaka dasu komai zai faru da mutum idan ba mai kyau ba sai ubagiji ya kare shi ta wani hanya.
Sudai gurin su yanzu shine yadda zan rasa cikin da ya baiyyana a jikina yanzu shine babban bakin cikin duk wani na tare da Nafisa din.
Suna kallo na da yara muna shige da ficen mu a gidan babu yadda zasuyi shima yusuf bai faye zuwa ba don yace yana gudun sherin su.
Sai dai yazo ya tsaya a waje ya turo a kai mai abimcin buda baki ya tafi dashi idan ya gama da safe ya bayar da kayan a shigo min dashi ciki.
Tafiyan su da kwana uku na fita muka tafi yin sayaya kamar yadda ya umurce ni da motar shi muka fita tare da maryam harda ihisan da yanzu ta lake min da ba uwar ta a gida.
Sayaya mukayi sosai komai kamar yadda yace don Yusuf ne zai kai ma mutanen kaduna nasu idan zai tafi weekend.
Can kuna nafisa ne da ta dawo a fusace tana fada dashi don may zai bar min makulin motar shi inyi amfani dashi.
Yace ke da na saya maki mota kin fita ne ko may a wurina kada kiga ban sai mata mota ba har ki dauka wani abu ne ya hana bari nayi har ta gama karatun ta kada ya dauke mata hankali.
Kuma har yau ita bata san da manufana akan haka ba bata kuma taba nuna min bacin ranta kan rashin sai mata mota da banyi ba kamar yadda ke kika nuna min a baya.
Don haka itama matatace tana da iko da abina kamar yadda kike da iko dashi kuma ki fada ma yan uwan ki da suke bugo maki waya don gulma in ba suyi hankali ba abin akan su zai koma don nagaji wallahi ba akan ki bane faraun kishiya don ke ma wata ki ka shigo kika sama a gidan.
Kada ki dauki kamar wani daki ko wanda bai san abinda yakeyi ba nan dai sukai barsm baram da ita a dakin hotel din da suka sauka din.
Washe gari akai ma yarinyar aiki har lokavin kuma bai kirani ba sai dai da yayi tunanen ai banda layin shi koda yaso ya kamani da laifi tanan ne ya sa shi kiran layin nawa.
Muna zaune dukkan mu a falon da na dawo na samu samiha akwance tana barci tayi ale ale da ita na buga kujera ta tashi gani na ta da marairaice tace kanta ke ciwo tazo nan kada a damay ta a can.
Ban mata magana ba illar alama da nayi mata da ta bar gurin ta wuce muka zauna sai ga kiran shi ya shigo min.
Ba kuwar nomba dana gani na kasar waje ne yasa na gane shine a layin har kiran ya katse ban daga waya ba na share shi.
Ya kara kira kusan zai katse na daga da sallama wani iri yaji dajin muryan ya amsa yana fadin watau ke idan ba,a kiraki ba bazaki nemi mutane kiji saukan su ba ko ?
Nace cikin dakewa tunda naji shiru nasan tafiya yai dadi ne don ance shiru alaman lafiyace ya mai jikin da fatan an yi nasara ga tafiyan.
Yace jiki da sauki yanzu aka fito da ita gurin theater an dinke cikin dake bude din kan ne dai sukace bazasu taba ba yanzu saboda tayi kankanta da aikin shi sai idan Allah ya raya ta ta tasa nan gaba zasu taba ta.
Nace Allah ya bata lafiya yace amin ya wajen su mama da yaran nace duk lafiya muke sai yayi shiru.
Kawar da shirun nayi da fadin ka kira mama ka fada mata halin da ake ciki ko don su sani ?
Yace ban samu kiran ta ba har yanzu nace amma dai kasan baka kyata ba iyayye fa ba abin wasa bane mussanman uwa da Aljannan ka ke karkashin ta.
Yace may ya kawo wanan maganan Deedar nace gani nayi baka kyauta bane dai yace ai sun san na fada masu an haifa min ya mai lalura ko ?
Wa yazo dubata daga cikin su nace amma kuma kai kasan halin matar ka ai suzo kuma tace gulman ganin yar ya kawo su kamar yadda tai masu a baya.
Shiru yayi yace na fahinci dai kunyi waya da hajiyan mu ke nan ko nace ni ba muyi waya ba sanin halin ka dai nayi ba zakai tunanen ka kirata ka fada mata halin da ake ciki ba ka kuma san a karkashin wani take ga ta da abokan zama.
Naji zan kira yanzu idan mun gama waya sai na kara kira nace agaida su muna masu fatan alheri duk da nasan ba fada mata din zaiyi ba nadai fada ne kawai.
Yace zasuji ya kashe wayan nima na bi wayan da kallo na sauke ajiyan zuciya tare da gode ma Allah dana taushi zuciya nayi mai magana yadda zai fahinta.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Idan kin san darajan Allah kuma kina tsoron haduwa dashi kada ki karanta idan baki biya ba kyale mai cin amana taci ita kadai don ramin kowan daban ne kada ta halaka kan ta ta halaka ki yar uwa.
Ina falo zaune wayana yai kara na dauka hajiya mace a layin bayan mun gaisa ne take fadin kunyi waya ne da mijin ki don ya kirani yau.
Nace a, a mama ya kwana biyu bai kiramu ba nan tace haba khadija nasan kece zaki mai magana ya kirani ai.
Don yanzu ya kira yana min dadin baki na zage shi tas tunda shi har yanzu bai san ciwon kanshi ba.
Nace mama ayi hakkuri don Allah in Allah ya yarda zamu gyara haka ba zai sake faruwa ba tace idan ma ya ga haka shine daidai yaje yai tayi ai duniyace ita ta ishi kowa.
Nan dai na dinga bata hakkuri ta bar zancen tare da min kuma godiya a karshe tana fadin nagode khadija duk da kin boye bakece kika mai magana ba amma ni nasan ke din ce don wanan ba dabara shi bane.
Nace wallahi mama ban san cewa yana irin wanan dabi,ar ba da tuntuni na nuna mai kuskuren hakan da yake yi tace fushin shi na banza wa yake son yazo a wullakanta dama dai mommy ku ce mai wanan kokarin ita kuma Alhaji yayi mata iya ka da al,amarin Nafisa din tun wancan zuwa da sukayi don haka ne bata kula ba ma wanan karon.
Idan dai sun dawo zanyi kokari in zo da kaina in duba su in gani koni ma din zatai min rashin mutuncin nata data saba ne.
Nace wane ita mama dako ni ranan na isheta ai da takai karshen rashin mutunci gidan nan hakan dana fada ne yasa ta sake murmushi har ina iya jin ta mukai sallama na kashe wayan.
Sai shirin sallah muke ta faman yi da yanzu baifi sati daya ba idan Allah ya kai mu duk wani shiri da zanyi a bangare na nayi shi .
Yau muna zaune muka kira Anty Fati a waya bayan mun gaisa ne na ba yaran waya su gaisa da ita take tambayan su yaushe zasu dawo ne ?
Daddy yace da ita mama ni anan zan tsaya wurin anty tana kaimu yawo tana sai muna abin dadi ina ci kuma tana muna karatu a gida.
Daddy kaida kanka kace baka dawowa gurin maman ka yace eh mama ni anan zan zauna muna zuwa masallaci da Abban mu.
Dariya muka sawa yaron ta gama gaisawa da Affan ya miko min wayan nace ina nan kawo maki daddy ki mun maso muzo nan muyi maki sallah ne sai kuma ga zancen tafiyan mai gidan india.
Tace haka dai nake ji dana shiga wurin hajiya ashe kuma haka abin yazowa Nafisa wanan karon nace wlh anty ikon Allah yafi da nan ai.
Tace ta dai gani ga rabon ta dama idan mutum yace aikin sa yiwa mutane sheri ne da bin bokaye tafar ganin sherin ta na fita mata ai.
Tayi nisa Allah dai ya taro ta don ko wanan abin daya samay ta baisa jikin ta yai la,asar ba ta tuba ta daina wanin abin sai ma ai abinda ya karu gare ta ita.
Khadija ai ina ganin kokarin ki da kika iya zama a tsakiyan wanan nan mutanen don ta riga da ta gama da maigidan shiyasa kika gani gaba daya ma lamarin shi ya fice min a raina yanzu.
Nace hakkuri zakiyi ai don goben ki anty ki bar duba da tuna abinda sukai maki a baya ki dube gaban ki ki gyara goben ki.
Don ita dama gurin ta ke nan abar mata shi ita kadai ta yi yadda take so dashi tace bazan tsaya bata lokaci na akan su ba ni gaskiya nace anty nima na iya hakan balle ke don Allah dai ki gyara tsakanin ki da mijin ki da yan uwan shi tace nagode sai na kara kiran ku mukai sallama ta kashe wayan.
Laraba dake gefe tace wani abin ne baya mantuwa ga mutum ai amma in kana duban wanan sai kaima ka bata goben ka a banza.
Gwama da kike iya fada mata gaskiya ake lamarin ki yana da kyau don ka zauna da mutum tsakani da Allah kuma ka fada mashi gaskiya a idan yake da gyara ai shine kyau.
Muna a gurin muna zancen maryam ta shigo sun gaisa da mama ta juyo gare ni tana fadin ke uwar biyu zaki ko iya fita anty Salbiya ta neman mu fa yanzu mukai waya da ita.
Nace yau din nan banjin fita ta tace naga alama yadda kika zauna turus din dake kamar wanda ta kumsa cikin diya goma wallahi cikin nan kamar kada a bayana shi naga ya kara maki wani bunkasa yanzu.
Duk kin wani koma jagwal yanzu gaba daya nace ai ko biyu na haifa da a gidan zaki tare tace zancen kike so lokacin kika sani ko ina gidan nawa mijin nima ?
Nace Allah dai ya nuna muna ranan wanan auren da aka ta fata kuma ni banga ana da niyar yin shi ba a zahiri.
Ke wallahi ni yanzu tsoron maza nake yi anshani farko banji dadin su ba ina zan yarda su kara shana.
Dariya nayi ina mikewa nace aure kuma dole yarinya tayi ba don ko ba fashi a gare ta tace haka dai antyn ki ke ce min.
Daki na shiga sai dana watsa ruwa a jikina na shirya na fito mukai ma mama sallama muka nufi gidan anty Salbiya din.
Mun samu tana falo muka shiga ta tare mu da murna ta fadin khadija kin yi wuyan gani a garin nan komai yayi daidai ke nan dai da alama.
Zama nayi ina fadin wanan shu,umar ai halin ta sai ita anty yanzun haka ba su kasan nan daga ita har mijin sun na indiya sun kai yar su da bata da lafiya nan dai nake fada mata abindake faruwa.
Ta tausayawa yarinyar sosai tayi mata adduan samun lafiya tace dama irin masu bakar asirin nan ai haka ke faruwa dasu sosai amma sai kiga kamar ana bushe masu zuciya ne.
Yanzu dai ai ba zancen biye biye tana fama da yar ta nace Allah yasa ni tunda suka tafi wlh hakalina ba akwace yake ba da ita don da zaran na kwanta ita nake ganin taza min a wani irin yanayi da ba dadi fassarawa.
Nace yanzu ko sunan ta aka kira wlh gaba sai yai mugun faduwa tun rikicen gida da mukayi da yan uwanta anty Salbiya tace dani.
Kina ko ibadan ki yadda ya dace don kin san irin yanayin nan da kike ciki yana sa mace raggata yin ibada sosai sai kin kara jajircewa.
San nan yanzun haka kiran nan danayi maku an turo min da kaya da na ba da sako ne kasar mu ke ce farkon fado min a raina wlh barin dauko maki ku gani don Allah kada ki wasa da amfani dasu don tunda kike yawan wanan mafalkin da ita dole akwai abinda take shiryawa ne a kan ki.
Kema nasan kina da farfarun mabiyane dake sanar dake suke baki kariya daga sherin nata shiyasa kike ganin wasu abubuwan a cikin mafalki haka.
Mikewa tayi zuwa dakin nata sai gata dauke da wani katon jaka dake da rubutun arbiya a jikin shi tazo ta aje a gaban ta mudai muna kallon ta ta fara fitar wa daga cikin jakkar nata tare da fara muna bayanin shi.
Tamiko tana fadin wanan da kike gani aikin sa shine koda ace irin yadda mijin nan naki yake da mata da yawa ne idan kina matsa wanan din a jikin zai ji koda yaje gurin wata matar tai mai dandano na daban.
Hakama idan namiji yana da yawan neman mata insha Allah zai dogara gake matar shi ta gida da yardan Allah don duk inda yaje sai yaji dandanon bai gamshe shi ba sai ya dawo gurin ki.
Ta kara dauko wani tace wanan sabulune na hadi da akayi na gargajiya bake ba ko yaran da zaki haifa idan kika malaki wanan kuna amfani dashi zai maku aiki sosai matuka gaya.
Ko yau kika haifi yar ki ko yaron ki kina gudun irin wani abu na sihiri ya shafe shi zaki iya lakata dan kadan a wanke al,auran yaro dashi haka ma ke ma fa dan kadan zaki diba amma kada ki amfani da wanan a yanzu don yanayin cikin dake tare da ke baida wani chemical a cikin sa kayan gargajiyane masu karfi aka hada dashi.
Yana da kwai sosai matukar kina amfani dashi ko da kishi tana jifar ki da sihiri ne da yardan Allah bazai yi tasiri akan ki ba.
Ta kara dauko wani tace ga wanan kuma poweder ne kamar irin da ake fadar aljani ya shafe ka ko kuma wani sihiri haka zaki iya amfani da wanan din wurin karya shi musanman ke mai kishiyoyi hakan nan zaki iya amfani dashi ki shafa a hammatarki da wuya da sauran gurare na jikin ki haka da yardan Allah zaki ga na miji yana bin ki sau da kafa da sauran su.
Wanan kuma da kifi ake cin sa mallaka ne sosai sahihi idan kikai amfani dashi sau uku zaki raba shi zaki iya yin miyar kifi ko soyayyen ki ki dan barbada a sama wallahi yana da kyau da amfani sosai don mutum zai dinga jin shakkan ka da kuma baya iya ketera maganar ka ko diyan zaman nan ke gare ki zaki ya masu amfani dashi bazasu iya ketare maganar ki ba.
Ajiyan zuciya na sauke tare da fadin ni ya su a raina yanzu dole aure ya koma sai da irin wanan abin idan kana son zaman lafiya da maigida ke nan.
Ta miko wani tana fadin wanan turaren wuta ne shi ake kira da turaren sakata zaki dan zuba a kaskon garwa shi kizo karkashin gadon da kuke kwana ki aje sai turaren yabi ko ina ya dauka.
Zaki cire abin hayakin a wurin hmmm idan kina amfani da wanan a hankali a hankali in Allah yayi duniya don manzon sa sai an wayi gari yaji ba wata mace a ransa saike.
Shiya bamu son ba mai kishiya wanan din amma ke ya zama dole mu baki shi don wanan shu,umar sai da hakan gare ki don ke ma baki san iya sherin da take maki ba ai.
Ta aje ta dauko wani tana fadin kinga wanan kuma shi muke kira da dan lalai idan zaki kumshi zaki dan zuba kadan a ciki ki kwaba ki kumsa idan kiyi yana jawo yawan alheri gun namiji sosai zuwa ga matar shi.
Wanan kuma turare ne ana kiran sa dan mara zaki shafa ga maranki da goshin ki yana da matukar amfani sosai yana saka dandanon jima,i sosai tsakanin miji da matar shi.
Wanan matan da suka san kan su sosai suke amfani dashi ko a kasan mu saboda yana da wuyar samu sosai kin ganshi nan.
Sai hummara da zan baki da turare da powder da kwali na fari jini both yan mata da matan aure zasu iya amfani dashi don saka kwarjini a idon jama, a so kinga idan har kin daure kinyi amfani da wanan zamu zubawa sarautar Allah ido mu gani Allah yasa mu dace ya kare mu daga miyagun kadarori.
Muka amsa da amin ta fada min kidin su naji shi a sawake don na tabbatar ita Nafisa Allah kadai yasan irin makuden kudin da take zubawa a kaina don dai kawai in bar gida.
Tace akwai addu,oi da zan baki wanda zaki tsare sosai ki dage a gurin yin su shi addua kin san shine gaba da komai wa yan nan munayin su don Allah yace tashi in taimake ka.
Idan gari ya waye kafin ki ci komai zaki komai kuma kafin ki magana da wani zaki dinga karanta li,ilafi kafa tara ko wace da bissimillah ki nayi kina tofa a tafin hannun ki.
Da kin kammala sai ki shafe jikin ki daga kai zuwa har tafin kafan ki da yarda Allah idan kika juri yin haka sai ubangiji ya fifita ki kan makiya ya kuma sanya masu tsoron ki a zukatan su.
Ina fatan kin yi karatun arabic sai maryam tace malamace wurin nan ai anty don na gani da mukaje garin su bukin ta abin har mamaki ya bani.
Tace to masha Allahu to lazimci karanta tabara kulun idan zaki kwanta don yana daga darajan mace a vikin kishiyoyin ta.
Komai aka nufike dashi zai koma akan maishi da yarda Allah ko a makaranta ko wurin aiki duk yana da amfani ga mutum ya dinga yin sa idan kika daure kina wanan abinda na fada maki dayardan Allah duk wani sheri zai koma kantane.
Nayi mata godiya sosai tare da bata kudi duk da nasan nadai bata sune ba wai kudin kayan bane don ma batayi niyar amsa ba sai da nace tasai wa yara abin sallah ta karba.
Maryam ne har mun daga tace wanan jirgin dankaro Allah yasa tai amfani da su ko tayi abinda kika ce din yanzu duk ta sukurkuce ga baki daya wallahi.
Nan Anty Salbiya tace haba kamar fa kina abakin kura ne da wanan kishiyar taki ko bakin rami ko ta turaki ko ki turata haka abin yake yanzu gidaje da yawa wallahi ko da baka da kishiya ma.
Wata tana waje tana maka hassada da bakin cikin zaman da kake yi da mijin ka akace ko kana da kyau ka kara da wanka.
Idan ita tana shirka tana kaucewa mahaliccin mu ke a saukake zaki kama mijin ki kuma kauce wa kai,din ta da yarda Allah don Allah ki kula ki yi amfani dashi kamar yadda nayi maki bayanin komai.
Ai yanzune daidai kiyi su don bata gidan kinga kafin ta dawo duk abin ya fara zama jikin ki insha Allahu.
Gidan anty hauwa naje na gaida ita don nasan da wuya in kara fitowa a yadda nakejin kai na kafin sallah kuma nan na samu sakon ya iso na kwaso wanda kayan yara ne sai nawa da na su mommy mamana da su ya Amina da hajiya dana saya masu.
Ko da na dawo gida sai naji zancen ta ya tsaya min a rai gama yadda ta hada ni da Allah in amfani da abinda ta ban yau din dama wa yan can na farkon.
Bayan nayi sallah na zauna in lakaci wancen in shafa in goga wanan na fito falo na samu laraba ta dora girki abinda zasuyi buda baki dashi.
Na fito zuwa kitchen din wurin ta a nan na tsaya muna hira da ita ina dan tayata gyara ganyen da naga ta fitar zatai amfani dashi.
Kusan a tare mukai aikin da ita muka gama na shiga sallah la,asar ne naji shigowan ihisan part din nan na fito na samay su da yan uwanta suna wasa nace ta kira min samira yar ta yarinyar ta fice da gudu zuwa kiran Samira din.
Sai gasu sun dawo a tare nan na bude kayan sallah su da na sayo masu amma fa da kudin miji na bawa ko wace nata har na su yanyala nace takai masu.
Abin mamaki bai karewa ina zaton ba zasu karba sai gasu har part dina sun zo min godiya nace ba komai suka fita anan suka bar samira da ihisan a wurina suna kara duba kayan su din.
Anty da maman mu tana garin nan ba zata bari mu karbi kayan nan ba ko su yanyala sun fada yanzu da na kai masu nasu sunce kada mu bari maman mu taji doin idan ta sani zatace a mayar da kayan ni kuma wallahi ina son abina don bazata saya muna irin wanan ba na sani.
Nace idan tace kada kusa sai ku dawo min da abina ina da wa yanda zabawa su saka tace nima ina son abina wallahi.
Abinci laraba ta debowa yaran zasu suci sai samira tace itama zataci nace haba samira babba dake baki koyon azumi har yanzu tace aiko su samiha basu azumi wai basu isa yi ba sai sun haihu biyar zasu fara azumi.
Abinda ko maman mu bata kanyi tace bata isa fara azumi ba sai ta yi haihuwa biyar ko fiya da haka zata fara.
Innalillahi nai ta maimaitawa har yarinyar ta rude tace ko sallah fa sai da malamin mu na islamiya ya koya mun ne nake koyawa maman mu dasu samiha suma basu sallah.
Gabana ne ya fadi a raina nace ashe dole abin yaiwa Nafisa yawa don babu kusanci tsakanin ta da Allah har yanzu.
Mamakin mijin mi ne ya kamani a raina nace yanzu yaya yake zama haka da mutanen da basu sallah a gida nai tsoron Allah ya tambaye shi wanan abin gobe kiya yaya irin macen nan zatayiwa yayan ka tarbiya mai kyau a haka ?
Ranan dai da wanan damuwan na kwana a raina har dare ina kara nanata maganan ga mama laraba tace ai haka suke har mazan su idan kinga namiji ya fara sallah wai sai ya aske gashin kansa nan na kitson su ya fita samar taka ke nan imani ya fara zuwa mai.
Ikon Allah ni kuma nan Allah ya kawo ni idan baka mutu ba baga gama ganin duniya ba ashe tsoron al,amarin naji a raina sosai ranan nayi nadaman kasancewa na da su a gida daya.
Bayan kwana biyu sallah saura kwana biyar muna zaune da dare falo sai ganin mutum mukayi kamar anjefo shi ina kwance a kasa a wurin da nayi sallah naga shigowar shi sai da naji gabana ya fadi.
Don ban sa zasu dawo a wanan lkacin ba tunda sunce an wa yarinyar aiki ne na dauka sai bayan sallah kamar da sati biyu zasu dawo sai gasu.
Addu,oin tsara naja daga inda nake kwance din ina mikewa zaune da kyat yara na mashi sannu da zuwa da laraba.
Har inda nake ya karaso ya zo ya tsugun na daidai saitin fuskana tare da fadin ya akayi ne nagan ki haka har yanzu kina azumin ke nan baki hutawa ko ?
Nace tafiya irin haka babu sanarwa kuma sai kuyiwa mutane girshi yace hakan nake tafiyana ba sai wani ya sani ba ko Yusuf yanzu na kirashi suzo su dauko mu a airport shima korafin da yake min ke nan.
Nace dole yai maka korafi ai sannun ku da zuwa ya hanya ya kuma mai jikin ina kallon fuskan shi inji may zai fada don a zatona ko yarinyar ta rasu ne ma.
Yace lafiya kalau take ta samu sauki sosai shima kan yana dan ragewa don sun bada maganin da za, a rika mata amfani dashi idan munzo nan sunce kan zai rage girma.
Ya mike tsaye yana fadin barin dan watsa ruwa ko zan rage jin wanan gajiyan dana debo na hanya mikewa nayi bayan fitar shi na mara mai baya.
Na samay shi a falon bai shiga part din nashi ba yana fadan don may aka kai mai kaya part din Nafisa a dauko mai kayan shi.
Nidai na wuce shi nan na nufi saman yana a rufe har lokacin na bude da key din wurina dakin yana a gyara sai kamshin turaren dana bude dakin dashi ke tashi ciki.
Bandakin na shiga na hada mai ruwan wanka na fito na samu suna shigo da kyan dake daure kamar na mahajjata yadda aka daure su.
Ga ruwa na na hada sai dai yau mama tuwo ta girka masu wai shi suke son ci mai za a dafa ma yanzu kaci ?
Yace tuwon ma ai is ok zanci ai in akwaishi don ya zama abin marmari a gare ni yanzu da wancan cimar nasu da na baro yanzu kai wanka kafin ka fito na hada ma abincin.
Na barshi ya fara cire kayan jikin shi na fita daga dakin zuwa hada mashi abinci lokacin an gama shigo da kayan ban ko kali inda kayan suke ba na fice.
Sai da na dan jima a part dina don mun tsaya hada mai da dan abu mara nauyi da zai sha muka gama na shiga na gyara kaina na nufi part din.
Ina shiga na rufo kofan na samay shi zaune da waya a hannun shi yanayi na jera komai a inda ya dace a jera din na samay shi ija fada mai na hada abincin ko.
Ina zaune gefen sai da ya gama baiyi magana ba har ya kare na hada kayan na samay shi a dakin guri na samu nakai kwance don tunda ya dawo amsa waya yake yi har lokacin.
Acikin wayan da yake yin din ne na fahinci dawowan baram baram sukayi da Nafisa din don yana fadin ace mutum baisan ciwon kansa ba kamar ba itace ta haifi yar da cikin ta take cikin wanan lalurar.
Bansan Nafisa tayi nisa haka ba sai wanan karon wai zaka yarda har gurin boka taje a india wai ya duba mata ya akayi ta haifi yar haka ?
Wani iri naji a raina daga inda nake kwance yace wallahi alamarin nafisa ya fara fita min rai don bata san Allah ba sam a rayuwan ta in dai taje boka ta iya bi ai tajiyo makanta matsala a can daya tada mata da hankali banji may wanda suke wayan ba yace sai dai shi danaji yace.
Ni ina zan yarda da wanan shirkan da shashanci iri nasu na mata wa take zargi yanzu tace ya hurhura mata yar yanzu.
Ya gama na sauke ajiyan zuciya dama yanayin sa ya nuna ba dadin rai ya dawo don yadda na ganshi a cikin rashin walwala a fuskan shi.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Bamu yi nisa ga barci ba tazo tana dukan kofa hankali tashe na farka naji muryan shi yana fadin kwanta abinki tayi abinda zatayi din.
Da safe ko da na sauko lokacin tara na safe ya gwauta a falo na samay ta zaune ta harde a cikin masifa da bala,i take ban muna arba ta soke kanta a kasa.
Na shige ban mata magana ba sai da naje nayi wanka na shirya na fito na nufi part din ta cikin rashin dadara nayi sallama na shiga.
Tana zaune ta jingina bayan ta a gado kafanta a harde tana waya kamar bata son aji maganan sai gani nayi sallama har kuryan dakin inda take.
Wayan ta kashe da sauri ta dago tana kallo na nace maman ihisan sannun ku da zuwa kun dawo lafiya ya mai jikin kuma ?
Tace lafiya kan muka dawo tunda kin ga miji har kin iya shigewa wurin shi kin san kuma bake ce dashi ba mai jiki kuma gata nan idan za a karasa ta ne da zai fi.
Murmushi nayi nace wanan kuma Allah ne kadai yakai can Allah ya bata lafiya yasa kafara ne gare ta .
Dama nazo in gaida ku da hanya ne in kuma dubs mamana Tani da jiki Allah ya sauwa ka na juya ina jin tana fadin muna funcin banza da wofi idan ma karasata kika zo yi ai gaki gata da yafi min wanan wahalan da kuka samu ciki.
Na kada kaina ina murmushi na wuce nace kodai ba komai na sauke nauyin da Allah yace ka sauke tsakanin ka da abokin zama.
Dakina na dawo na shige na kwanta barci nayi sosai ban falka ba sai wuraren karfe dayan rana na tashi don lokacin sallah da yayi.
Ban fito falo ba sai da nayi sallah na fito na samu mama laraba a falon yaran sun fita laraba ke fada min shigowan shi biyu part din nawa ya samu ina barci.
Zama nayi ina tambayan ta yaran tace yanzu baban su Yusuf yazo suka bishi tace kina barci ba an tayar da fitinan kujerun falo da aka raba ba gidan nan Yusuf yana zuwa yace a mayar dasu yadda suke a gyara .
Tace na fita in gyara wurin mu ne sai gata ta fito a cikin masifa kai wanan yarinyar bata da mutunci wai ni zatacewa maza in gyara kujerun a yadda suke a da can.
Tsoro da ya kamani yadda naga ta fito min dole na juya na shigo nan na barta tana ruwan bala,i a falon nasan tasa an warga zasu ne sai dazun da Yusuf ya shigo ne yake tambaya wanda ya hadesu tace itace tasa a yi hakan.
Yace yan uwanta su gyara a yadda suke anan gurin namu suka zauna yanzun haka badon sun tafi sallah ba tun dazu nan yake karban mutanen shi ai yau mutanen ki sun samu fita falo suna yadda suke so.
Nace ashe yau daddy ya samu sake, sai kinji ke nan dama abinda yake so ke nan a rayuwan shi dan ni har tausayi suke ban duk a takure suke dama.
Ai kina ma kokari tunda kina dan fita dasu acan in dai ba gurin kakan su ta turasu ba ko cen ko yaushe suna gida kumshe.
Shine ya shigo part din yake fadin kin tashi ke nan nace eh yace idan kin huta kije dakina kaya na nan saman gado ki dauko.
Tsaraban ki ne nace mun gode na bashi amsa yana fita na mike zuwa dakin a nan na suma kayan indian sari ne zube a saman gadon da kayan yara a cikin buhun nan na saka su na mayar na dawo na kira mama tazo ta dauka muka nufi part dina da kayan .
Nan dai muka baje ina duba daya bayan daya kayan suna da matukar kyau sosai da gani suna da tsada sosai sai set na dan kune da sarka masu kyau suma har guda uku.
Na gode sosai don kayan sun min kyau sosai gashi lokaci ya kure sosai duk da ina da kayan da suka fisu a dakin ke.
Zaman dai babu dadi sam don duk da mutanen da ke shigowa gaida su da dawowa bai hana Nafisa yin halin ta ba a bainan jamma,a duk dai a kan cikin dake jikina ne.
Shi da kan shi a wani safiya da ta tayar da fitina yace dani kada in kara kulata idan ta isa ta zuba da cikin a gani tace wai yana fada akan cikin da ba shine yayi min ba don tasan ba yadda za ayi ya iya min ciki din.
Yace saboda kin san sherin da kikayi yasa kike fadin haka to na dade da gane hakan sherin ki baiyi tasiri akan mu ba.
Fadan hauka ta fara yi dashi wai ita zaiwa kazafi yace kazafin may tunda yanzu ta fada kowa yaji bayan sun gama ta shiga daki sai gata ta kwaso kayan sallah dana sayawa yaran ta nufo dakina dashi yaran na biye da ita suna kuka.
Kukan yaran ne ya fito dashi yana tambayan su may ke faruwa nan samira ke fada mai abinda uwar ke niyar yi part din ya nufa ya samu an bude kofan ke nan tana shirin shiga ya dakatar da ita yana fadin.
Ba yaran nan kayan su idan ba so kike ranki yau ya baci a gidan nan ba tace akan kayan raina zai baci yace kwarai kuwa.
Ganin da gaske yake ga ihisan tana fisge kayan ta a hannun uwar ta rugumay su a jikin ta ta koma bayan uban ta tsaya.
Diya nane ko naka yace yar ki da nawa tace to kayi iko da yarka kabar min nawa yace haka kika ce tace eh na fada yace yau ko idan kin hana ta amfani da wanan kayan sai dai samira ta bar min gida.
Eh lalai Samad an wanke an baka kasha ka tsuma to bari kuji wallahi ko damay take tsafi sai na nuna mata tsafin ki karya ne kada kiga kin salwantar min da wanan da na haifa ki dauka na kyale ki ne kin ci bulus.
Yanzu ma kin saka miji ya yi min gori akan wanan kuma yadda kika saka yai min ki dauka kinci bashi ne a guri na idan na tashi nawa na fiki iya sheri.
Duk wanan hayaniyar muna jin su don kofan har lokacin a bude yake bamu rufe ba tace yau har kana ikirarin Samira ta barma gidan ka saboda na hanata saka rigan tsafi a jikin ta ko ?
Tsafi kece mai yi ai tunda har kika iya zuwa wurin boka a india don rashin imani irin naki kina dauka kowa haka yake kamarki komay to ke da bukan kunyi kadan ku juya ni yadda kuke so.
Kinji na fada maki kaya ne idan har samira kika hanata amfani da wanan kayan ni kuma ki tabbatar da tabar min gidana ta gama har abada.
Sai dai ta koma gidan ubanta can ta zauna ni hadin kai nake so a gidana ba watsewar kai ba yadda kika kasa wata tazo tanayi ya zamay maki kuma abin bakin ciki da sheri tunda ke baki iya hakan.
Nan ya fice ya barta tana jidali tare da ihuce ihuce can naji hayaniyar su da yan uwan ta ana ta koke koke ashe baiyi nisa sai gashi ya shigo gidan rai bace yace duk su fito daga su bar maigida.
Nan ya tsaya lalai ranan ba zata zauna mai a gidan shi ba daga ita har yan uwar nata duk yadda ta bada hakkuri yaki amincewa da hakan karshe ya fice tare da ba yan sandan bakin get baki akan su tabbatar da kafin biyar na yamma.
Ranan kan sun gamu da halin shi ashe Yusuf ne ya yi mai tas yace badon Allah ya kawo shi ranan ba da yaya zai samu anyi ni kadai sai laraba suka wuri su shida a kaina .
AA kan san kuna daukan alhakin wanan yarinyar duk da bata magana akan haka kyale ku fa tayi ta barka ga Allah idan kun cuce ta.
Kuma sai Allah ya kama ka da laifi akan hakan don kaine ka tauye ta ba wani ba nan dai ya kawo musalan irin tauye nin da zaman su ke yi a gidan.
Ashe shine turje matan da yayi dayazo ya samu tana fada dasu wai don sun karbi kayan sallah a hannu na shine dalilin fadan ta dasu tayi masu yankar kauna.
Dole ta kwashi angayan ta maza da mata suka wuce gidan madam madam tana gani su tace yo ni Nafisa ina zan kaiku duka haka.
Wanan dawainiyar ai sai mijin ki shi daya dauka abinda nake fada maki ke nan kin kasa ganewa gashi gobe jajibirin sallah.
Don may ba zaki hakkuri dakomai ke cikin ranki ba abinshi a sannu har hankali ya kwanta da sannu gani Allah ta samu ta karbi matan da ita ga yar tana ta tsala ihu tana neman nono.
Haushi ne ya kamata tace yar banza mai cin tsiya da shegen taurin rai ta mutu taki mutuwa tana lake dani.
Madam tace nafisa baki da hakkuri ne ga yar nan ko bukin suna ba ai mata ba kin debi rabon ki dako ta wanan yar idan kin kwantar da hankali ai sai ki cuta ma khadija.
Cikine fa a jikin ta take dauke dashi da kinyi dabara nuna mata bakomai a zuciyar ki ki tsiri tura yar wurin ta da itama haka zata haifo cikin ta tankar wanan yar na hannun ki.
Kin manta ace mace mai ciki wanda take arba dashi duk safiya kamar shi sak take haihu dakin daure kina iza mata yar ai da itama sai ta haifi sherin ta taji inda dadi.
Amma ina kin kasa hakkuri don zafin kishin da baki iya boyewa kin kaiga yadda ba a son akai yo ko ciyar daku yau kawai ai aiki ne gun mutum.
Wurin kwana kan zan iya baku sai dai ki nema muna abinda zamuci dagani harku a gidan nan yau gobe ki samu ki lalaba mijin ki ki koma dakin ki yafi sauki.
Tayi mamakin jin kalaman madam din sai dai ba yadda ta iya tunda duk yan uwanta da saka shigo ta gujesu yanzu tunda tana ganin ta fisu yanzu.
Don haka abin kunya ne ta nemay su akan su taimaka mata ta kwamace ta zauna hakanan wurin madam din in yasoda safe zata nemi mijin ta su shirya dashi.
A gidan kuma ban san har sun fice daga gidan ba sai da laraba ta fita har sau biyu bata ga ko dayan su ba ta dawo tana fada min.
Fita nayi na duba sai banji dadin hakan ba da yai masu ko don yar nan mara lafiya da take dauke da ita nasan ko yayane dole tana jin zafin kasancewar yar ga hakan.
Maryam na fara nema ina fada mata dariya ta kwashe dashi tana fadin dama a ce ina gidan da zasu tafi in dauke su in watsa shegiya a duniya.
Tace ke tsaya kin yi amfani da wanan abin sai nace nayi wasu banyi wasu ba sunan aje tace kai ke wai wata iri ce khady wanan matar fa ke taso aiwa haka rashe ya juye da mojiya sherin da ta dauko ya koma kanta.
Ke bari dai yau komai dare gani nan zuwa gidan wallahi gaba zan sakaki sai kinyi amfani dasu dariya nake mata nace maryam baki da tausayi wallahi.
Mata da danyen jegon ta zaki ce kinji dadin tafiyan ta ki kwanta haka da kan ki fa idan kece bazaki ji dadin hakan ba ai.
Tace amma ke ai da cikin taso kibar gidan ki koma gidan ku ki kayan goyo da ciki tana jin dadi don nasan wallahi idan itace ba zata tausaya maki ba ko kadan.
Nace wanan kuma ita ta sani nidai da zuciya daya nake zaune da ita a gidan nan tace ita kuma da zuciya biyu take zaune dake ba.
Karfe bakwai da wani abu ta iso gidan tun daga kofa take fadin wai Alhamdullahi Allah mun gode ma yau gidan nan kamar bashi ba wallahi.
Laraba ta dinga mata dariya tace don Allah mama ki tayani gani dajin wanan matar ko itama ba mamaki buzuwan nan ta shanye tane dai bamu sani ba wai fa mama tausayin wanan matar take harda kirana ta fada min maganan takaici.
Nidai ina zaune ina tasbihi ina kallonta ina murmushi na shafa nace ke dai baki da tausayi wallahi ni banga abun farin ciki ba a nan.
Laraba tace ni ai tun dazun ina zaune imani ya kashe ni wallahi wanan da ba a nan nake zaune sai in ce yar nan itama takai ta isa.
Amma sanin ko waye ita yasa na kara tsoron alamarin ubangiji yanzu duk balain da matar na ta dauko a kasan yan tsafin nan yau sai gashi abin ya juye da ita a gidan nan.
Shiyasa aka ce mutum wanda ya dogara da Allah baya taba kunya a duniyan nan don Allah yana tare dashi a ko wani lokaci.
Matan nan saboda bakin fitinan irin nata tun ranan da suka dawo take sama da jidali a gidan nan har rana mai kamar tayau bakin ta bai huta ba kan wanan boyar Allah.
Maryam tace ai yanzu ta kai ga yadda take so don da tsamani take mijin ba zai iya mata komai ba tana ganin ta gama dashi .
Bata san Allah ba ai mashi haka ba sai ya girgiza bawan sa ta inda bai zata ba Allah dai yasa ta tafi ke nan yar iska daga ita har angayan nata kowa ya huta.
Tara maryam tabar gida har lokacin kuma bsi dawo ba sai goma ya shigo part din mu ya nufo ya gaida mama da shan ruwa na fita na bishi da ga bayan don dama nakai mai komai na jera acan .
Koda na shiga na samu yana sallah sai dai baiyi wanka ba a lokacin na shiga na hada mai ruwa na fito ya rarage sallah yana zaune fanin na fito ya mike yana rage kayan jikin shi ya shiga ban dakin har ya fito ina zaune da waya na a hannu ina dubawa muna charting da binta.
Nan ya barni zaune ya nufi dinning na mike nasamay shi a girin abincin na fara zuba mai kafin in zauna yace kina ganin yau zan iya cinye wanan abincin haka mai yawa ?
Nace haka fa na saba zuba ma sai dai yau idan baka jin ci abincin ne kawai in rage ma yace barshi mu gani tunda kin zuba ko.
Idona koma gefe na zubs mai tare da harde hanaye na wuri daya na zuba mai ido yana ta cin abincin shi hankali a kwance.
Can ya dago kai yace min lafiya kikai shiru haka nace hakkuri nake baka bisa ga abinda ya faru yau a gidan nan don wallahi ban yi zaton zaku dawo bane yanzu kuyi sallah a gida yasa na hada dasu nasai masu kayan cikin kudin ds ka bar muna ai amfani dashi din..
Ai ba laifi bane don kin yi hakan yace ba tare da ya dago kan shi gare ni ba ya kalle ni nima shiru nayi na dan lokaci sai kuma na sake fadin.
Don Allah kayi hakkuri su dawo gida hakana ko don yaran ka dake wurin su din sai naga kamar hakan da kayi bai dace ba gaskiya.
Don , , , , hannu ya daga min tare da fadin ya isa haka don Allah koma may ye ya riga da ya faru ai ban son wanan maganan again.
Yaci gaba da cin abinvin sa sai can yace gobe kaduna zamu a can zamuyi sallah in Allah ya yarda.
Yana fadin haka ya dauki cup ruwa ya kora ya jawo tiesui yana goge bakin shi dashi ya mike binshi nayi da kallo har ya shige ciki.
Sai lokacin daya shige nake mamaki watau dai halin shine hakan na tafiya babu sanarwa sai yazo yaiwa mutum girshi Allah yasa ina da dan shiri na sai kuma goben zamu shiga in karo abinda nake so.
Mikewa nayi na shiga dakin na samay shi zaune yana waya gado na hau na lafe kamar yar mage ya dade yana wayan kafin ya gama.
Yace shirin sati daya zakiyi don ina son indan huta idan munje can na sati daya idan haka ya samu a gare ni.
Allah ya kaimu nace tare da fadin sai a shirya su Affan ke nan su koma gaba daya don hutun su ya kare one week after sallah zasu koma school.
Akwai wani abinda zaki kara sai masu ne ya tambaya yana hawowa gadon nace sai dai sayayyan school da nake son yimasu da dan abinda ba a rasa din ba dai.
Ok yace yana jan bargo tare da fadin kada muje can kuma kice zaki kawo min kabali da badi din da kika saba fada min idan munje don hutu nake son muje ba bacin rayukan mu ba a can.
Ciki ciki nai magana ina fadin mutum dai ya rika shuka gaskiya a lamarin sa shine kyau yace may ne may kika ce nace ai kajini.
Murmushi naji yayi nace ai dama kaji may ye na bukatan in maimaita kuma kin dai ji na fada maki tun anan ko in nuna maki kala na acan.
Nace ko yanzu ai nasan kalan ka don ka zama sabo da kaza bai hana yankata ina jiye min ranan da nima zaka iya korana da abinda zan haifa dakai a gidan ka.
Tunanen ki ke nan dama dako kinyi kuskure don ba haka nake ba hukunci nakan yanke dai abinda mutum yayi ne.
Ba mamaki idan halin ki ya sauya in yake maki makamancin hukunci da kike ganin banyi daidai ba kansa.
Shiru nayi ina nazarin maganan har lokacin da naji ya rungumoni zuwa jikin shi yana fadin ku dai mata ba a gane gaban ku na gaskiya ko ?
Washe gari banyi wani barcin safe isashe ba na shirya muka fita mun dan taba sayaya muka dawo muka kara shiri kusan maryam ne ta hada min komai da zan bukata acan idan mun tafi.
Duk damuwan rabuwa da yaran da zanyi yana cin raina suko ba abinda ya damay su sai ma murna zasu kaduna da sukeyi.
Karfe sha biyu da rabi muka bar garin Abuja zuwa kaduna baysn yasa an rufe gidan ya bada umurnin kada a bude ma kowa gidan idan bashi ya dawo ba.
Yai masu ihisani muka tafi bamufi minti ashirin da dagawa ba Nafisa dasu madam suka iso gidan tare da wasu yan yaren su dattije da wasu da madam taiwa magana su zo aba shi hakkuri abindai a wullaknace.
Nan sojan dake gadin kofan yai masu nuni da su koma da hannu kada su karaso kofan sai da kyat suka samu ya saurare su yace masu gidan sunyi tafiya.
Tace ina suka je cikin tshin hankali take tambayan shi gashi ko kayan sakawan yaranta bata dauka ba suka tafi.
Yace shima bai sani ba amma da gani zasu dade inda suka tafi din ya kuma ce suyi maza subar kofan kafin ranshi ya baci dole suka bar kofan gidan.
Tunda suka shigo motsa madam ke fadin da sake gaskiya don sun damay ta da hayaniya a gidan tace nafisa abinda nake fada maki ke nan kullun baki ganewa.
Na fada maki ki bi alamarin nan a sannu tunda kikaga yarinyar nan ta shigo gidan nan da karfin ta ta shigo kikaga kinyi asiri bai yi wani tasiri akan ta ba har wanan lokaacin to ki bita a sannu.
Yanzu gashi kinjawa kan ki komawa baya a gaban idon ta ya nuna mata ke ba kowa bace a gurin ta wanan abin damay yai kama ?
Duk rashin hakkurin ke ne yaja muna wanan koma bayan yanzu ina kike son in kaiku kuda yawa hakan nan a gida na ?
Bakin magana Nafisa bata samu ba a lokacin abin mamaki da alajabi yake bata wai yau itane ake tagaririya da ita ana mata wanan wullakancin haka a gidan samad.
Ita ce samad ya wullakanta a kan wata abin ita har yanzu kamar a mafalki take ganin sa a idon ta ba wai ta yarda samad ne yai mata haka ba.
Ta tuno ko a indiya kudin da ta kashe zai iya sai mata gida da abin hawa a garin Abuja su zauna ita da ya uwanta ba sai sin rabo a gidan wata ba ana masu wullakancin akan abinda tafi karfi shi a yan shekarun da suka shude kai bama shekuru ba a jiya jiyan nan ma.
Dole ta fidda da kudi da madam din ta bukata masu yawa wanda zasuyi amfani dashi domin sallah da ake sa ran za a tashi dashi gobe.
Mun isa kaduna a wahalce duk dauriyan da nake yi sai da ya gane ina cikin wani hali sai ga amai da ya biyo baya da kyat naga mun kai garin kaduna din.
Yau ma kaman wancam karon a jirkice na iso garin muna shiga na nufi sama amai nayi ta shega yasa wai dole in kara azumin dake baki na nace naji yasa laraba ta hado min tea kafin ys shigo na dan kai rabin bayi na koma na lafe kamar nasha tea din sai barcin wahala da ya dauke ni.
Bayan nayi sallah na dade ina barci sai da aka kira sallah magariba na tashi nayi buda baki wanka nayi nazo nai sallah ban dade ba kuma na koma na kwanta.
Bani na samu kaina ba sai washe garin sallah da akai sanarwa da anga wata garuruwa daban daban na kasan nan dama wasu kasashen duniya
Ga kayan da muka zo dashi ba a bude ba don rashin lafiyan das nna iso gartin dashi dole na fito a cikinn karfin hali na bude kayan ya bawa kowa nasa tun da safe.
Abinda ke ban mamaki ya daure min kai shine lamarin anty fati ko wancen zuwan da nazo a haka matan nnan bata tako dakina dubs ni da jiki ba haka kuma batai min sannun kirki ba.
Hakane ma wanan karon tunda na shiga bata leko ni ba a dakin har zuwa lokacin da na fito ina bawa kowa abinda muka zo dashi garin.


ZAINAB IiDRIS MAKAWA
SEENABU
1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: ZAINAB IDRIS MAKAWA
08036959275

Kitabbatar da hakkina a kan ki idan kin karanta baki biya ba kibar wace bata san darajan Allah da Annabisa da hakkin data dauka kada son zuciya ke ma yakai ki ga halaka alhaki bin maishi yake ta inda baiyi zato ba.
Ina kara jaddada wanan maganan don akwai ranan tambaya yana tafe kan mu ko yau ko gobe ko kuma yanzun da kike karanta hakkin da ba naki ba .
Musulumin baya so ma dan uwan sa abinda shi baya so akan sa ba shiyasa a kulun nake maku wanan tunin a matsayin ku na musulmai da suka isa dauka hakki akansu.
Na gama abinda nake na koma dakina na kwanta don har lokacin jikin ba ya gama warwale min bane waya nayi gida ina sheda ma daddyn mu mun sauka lafiya jiya mun iso bana jin dadin jikina ne ban samu kiran su ba daga nan kuma inda nake na kira ya Amina ina sheda mata halin da nake ciki.
To wai idan kin ce kin biya ya zama naki kina da ikon kiba wanda kike so amma ko da kin jahilci sharudan ciniki wanan a haka yazo don online novel ne mai shi tace ga ka,idan abinta dake mai tsoron Allah ce ai ba zaki biya ki saya ba sai ki barta da kayan ta tunda karatun novel dai ba ibada bane.
Muna cikin waya da ya Amina nake danji murya alaman fada a kasa da sauri na aje wayan ina saurare daga ina maganan ke fitowa nan na fahinci a falon kasa ne dai a cikin gidan kuma.
Jin abin bai kare ba yasa na sauko kasa don gane ma idona abin dake faruwa a gidan kuma da wanan safiyar sallah da kowa ke cikin fari ciki da barka da buda baki na wanan shekaran da Allah ya nuna muna lafiya wanda wasu Allah bai nufa suga shi ba.
Wasu sunga farkon shi amma Allah bai nufa suga karshen shi ubangiji ya gafartawa magabatan mu na kusa dana nesa idan namu yazo mucika da kyau da imani.
Kina ban dariya wai karfin hali barawo da sallama shi malamin da yace haka kin masa bayani ga yadda mukayi dake kafin ki saya akwai ka,ida a tsakanin online ne ba takarda bane da zaki dauka ki kaiwa wasu.
Yanzu dai idan kin nace da fitarwa alkalin mu Allah da ku don duk abinda akace abarwa Allah idan kana da hankali da imani kaiwa kanka hisabi tun nan cikin duniya.
Hakina na ban fara ba sai dana roki Allah akan hakan na fara a cikin baiwar sa na kuma samu a cikin iyawarsa yanzu zabi ya saura gare ki dake damasu biye maki ku halaka ku halaka zurian ku akan novel din da ba ibada bane.
Isowana yayi daidai da furcin shi yana fadin nawa na turo maki akan sallah nan dubu dari biyar nasa Yusuf ya kawo maki don ban san halin da tafiyan mu zaiyi ba acan .
Shine yanzu zaki tare ni da wanan maganan banzan wai ba a sai komai na aikin abincin sallah ba don baki san zamu zo nan sallah ba.
Idan ma banzo ba ai ina da iyayye da yan uwa da zaki ba abincin sallah ke kanki ba don karki gani ga wani na tura maki kudi haka Fati ni na rasa gane may kike da kudi ne haka wai.
Ke ba a gani a jikin ki ba ba a gani ga diyan ki balle dan uwa kowa korafi yake da rowan ki ba wanda ke tare dake yake jin dadin ki saboda bakin halin ki na tsiya.
Tace idan ka bani ne don kasan abinda nake dashi kabar bani mana yace haka kika ce ko tace hakane mana tunda kabani kaba kowa na sani yanzu kan wanan magana danayi zaka aza min wanan tujaran haka.
Yace oh baki komai ba ke nan ko tayi shiru yace yau zaki gane baki da wayau baki san kalman da ya dace ki fadawa mutum ba komai ya fito bakin ki zaki iya fada ma mutum shi kai tsaye.
Wanan dalilin yasa baki taba ganin fuskana don a gaban kowa ba abin kunya bane gareki ki disga ni baki san komai ba sai bakin rai da hassada dake cin ki.
Don Allah dai ku bar wanan magana na fada daga inda nake tsaye nace indai don wanan kuke wanan abin kuyi hakkuri ga komai nan nazo dashi wanda na saya can a zatona acan zamuyi sallah da naga nan ne na ce mama ta kwaso muzo dashi nan ga baki daya don girman Allah dai kuyi hakkuri wanan maganan ya wuce.
Inda nake ya kalla ya nuna ni da hannu tare da fadin you see kinji abinda tace kinji ma kunnuwan ki kudin dana bata baiko kai wanda ke na turo maki kuyi hidima dashi ba nan.
Amma ji irin abinda ta sayawa yaran ki suka dawo dashi ke da kanki kike nuna min yanzu babu ko kunya wanda ke kin kasa yi masu hakan kuma ke kika haifi abinki fa.
Yaya don Allah kayi hakkuri kabar gurin nan idan ba ka kauce ba zancen baya karewa a tsakanin ku itakuma fadi take wanan munafuncin ni ban iya ba.
Wani sheri ne na kishiya mitum bai sani ba kuma yace idan munafunci ne yin haka ke kiyi mana a gani ai shima ribar zamane.
Kince Nafisa bata da kula bata son ki bata son diyan ki wanan kuma kin kirata da munafuka ke wace kala ce to a cikin ku yanzu.
Tace dama idan ba kaci min mutunci ba ai hankalin ka baya kwanciya yace idan magana akan gaskiyata ce cin mutunci naci maki din sai ki abinda zakiyi.
Kitchen na wuce na kyale su kayan da mukazo dashi nake tambayan laraba da take tsaye a cikin damuwa wajen kitchen din ta fito tana fadin gasu canbda aka shigo dasu aka aje su daga can.
Nufar kayan nayi don mu fitar a dora girki dasu nan dai muka shiga aiki da laraba ban san lokacin da suka gama suka watse ba.
Na fito naga Affan zaune a cikin damuwa daddy kuma yana wasa nace Affan ba zaku je ku shirya kubi abba masallaci ba ne ?
Yaron yace maman mu batai muna wanka na nace ku tashi muje kuyi wanka da sauri na wuce suka bini a baya zuwa dakina na gama masu nace su karbo kayan su in saka masu sai ga shi ya dawo yana fadin maman mu ta koro ni.
Mikewa nayi na nufi dakin da sallama a baki na ta dago kai ta kalle ni nace anty kiyi hakkuri don Allah kada ki sa wanan abin a ranki mana.
Bani kayan yaran in shirya su kada su rasa falalan wanan ranan ta wuce su ko kuma a rasa wanda zasu bi zuwa sallah idan shi ya wuce.
Kayan ta nuna min saman gado na nufa farar shadda da maryam takai aka dinka masu na dauko da hullan nan su na fice daga dakin.
Bina tayi da kallo mai kama da harara taja tsuki nikan tsab na shirya yaran suna fitowa daidai shima ya gama shiri ya fito da sauri kada ya makara.
Nace ga su zasu bi dan kallon mu yayi batare da yai magana ba suka fice nace adawo lafiya banji ba ko ya amsa kitchen na koma na samu laraba mukaci gaba da aiki.
Kafin wani lokaci mun hada tuwon farar shinkafa sai miyar ganye kadan stew yafi yawa da kaji da akaiwa yakan ci muga iyakar ka nan fa akeyin ta don babu kula na kwarai da zan kai abinci cikin gidan su.
Ba kuma dama in tambayi matar gidan da tahau ta cika nasan ko na tambaya bakar magana ce rabona sai wanan karon naji nima ya kamata in samu kayan aiki a gidan fa.
Don nima ai yanzu matar gidace dai mama ta gane may ne tunawa bayan mun gama saka tuwon a leda mun cika babban kulan da nazo dashi shake da nama a cikin sa.
Wayana na dauko nayi wa ya Amina bayani tace barin shiga nan makwabta na dubo maki akwai matar da sana,anta ke nan sai in hado maki da wanda nake dasu anan.
Ba a dauki lokaci ba ko sai ga shi anyi sallama wata yar matashiyar budurwa ne tazo da set uku na kula duka na saye nace ta karo min biyu idan akwai.
Ta fice tana murna mai girma daga ciki guda biyu na cika da abinci nace wa mama daya na Abba daya na cikin gida ne dayan kulan kuma na sawa su AA a ciki don yafi kyau da tsada.
Kafin masu shigo gidan don nasan sun tsaya cikin gidan su ne su gaisa da mutane yasa basu shigo ba har lokacin.
Yar uwa ina typing ne wa jama,an Annabi masu tsoron hakkin wani fa don hakkin su da ke kaina ina son in sauke nayi kina damuna da zancen bati.
Idan kinga zaki iya da hakkin wani ki ta karantawa ba nawa na duk wace zaki iya karanta ki dai sani akwai nauyi babba a kanki na mutumin da baki san ida zaku hadu ba kila sai a gaban ubangijin talikai wanan sarkin kowa da komai da aka hadaki dashi kika yiwa daranjan saboda son zuciya don Allah ki barni haka zabi ya rage akan ki yanzu ko yaron yasan akwai ranan haduwan shi da Allah.
Yana zaune dakin hajiyan su laraba ta shigo da kayan abincin tare da mommy duk yan gidan sai magana sukeyi a tsakar gida suna fadin ikon Allah yau abincin sallah gidan babangida ne a gidan nan.
Hajiya mama daga daki da aka dosa da kayan tace kai mommy yara kuje can kuji dashi da ai ba abincin gidan shi muke ci mu san munyi sallah ba ko.
Mommy ta karaso ciki tana fadin ina zan dashi ai sai kin gani kin sa albarka wanan sabon sauyi da ya samay mu haka ko hajiya ummu tasa bakin albarka gata can tana addua ai.
Yana zaune yana murmushi daga inda yake tace yanzu kai wanan abin don Allah bai ma dadi ba kokai fa yanzu shine muhinmanci auren wace ta san darajan iyayye din da muke nuna maka haka tun farko.
Yace yanzun mai tun da safe muka kwasa da fati hajiya da mommy na hada baki suri fadin kai don Allah bar zancen wanan sakaran da bata san inda ke mata ciwo ba fati kan bansan halin ta ba wallahi.
Nan dai ya kora ma su bacin randa sukayi da ita ya kuma labarta masu halin da suke ciki da Nafisa kafin yazo.
Hajiya mama tace dama kai ka barta tana iya shege nidai abinda zan fada ma shine kada su kuskura su taba lafiyan diyar mutane don Amana take gare mu girma da darajan iyayyen ka yasa aka bada ita ba tare da wani dogon bincike ba .
Shiru yayi yana sauraren bayanin da mahaifiyar shi ke mashi din Yusuf ne yayi karfin halin yin magana yace insha Allahu hajiya hakan ba zaima faru ba.
Don yanzu ai dole ya ya dauki mataki a gidan tunda iyali khadija itama zata fara ajewa kinga ko barin su haka a gidan ai bazai yuyu ba don ko yaran nan da sukaje mata hutu sai kafa kafa take dasu a gidan saboda su.
Tace to don Allah ji yara da gidan uban su basu da dama suyi wani dogon motsi wallahi kaji na fada ma ya zama dole yanzu ka dauki mataki akan alamarin gidan ka.
Ita kuma wanan mara wayon ko wanan kokarin da yarinyar nan tayiwa yaran nan bai sa ta kawar da duk abinda ke ranta ba.
Ta yi kokarin itama gyara auren ta don abin ita nata miskilanci ne shitasa na dawo daga rakiyan ta yanzu don ba yar goyo bace lalaci da son kai yai mata yawa a rayuwa har bata iya tsinana wa kanta komai na rayuwa na ci gaba.
Sun dai dade a zaune gurin hajiyan suka mike zuwa gida ban samu shiga gaida su ba a ranan don muna gama girki nayi wanka na kwanta sai barci.
Damana na aje masu komai da zasu bukata na kuma aje na sauran mutane duk na halartawa laraba na shige na kwanta.
Can cikin barci nake jin yana ja min kafa na a hankali na bude idanuwa na sauke a kanshi yana tsaye saman kaina yace kizo zaku gaisa da childship dina mikewa nayi zaune.
Zaki iya tashi yace min na kada mai kai ya fita ban fito ba sai da nai makeup a fuskana na dan gyara tare da dora gyale a kaina.
Tun ina saukowa suka sako min idanuwa naji suna magana kasa kasa har na karaso inda suke su biyar ne bakin namu.
Ina zuwa nayi sallama tare da dafa kujaran da yake zaune a kai na zube kasa ina gaida su da zuwa tare da masu barka da sallah.
Masha Allah naji sin fada tare da fadin maye gaskiya Allah yakaimu ga danshin ka wanan zukeke haka ga ladabi da sanin ya kamata gaskiya kai muna wayo ka kuma falkar damu ko muma Niger state zamu koma ne ?
Suka sa dariya wa wanda ke maganan mikewa nayi na shiga kitchen na hado masu abinsha da naman kajin da akai pepeying sai cake din da maryam ta ai min.
Na fito masu dashi wani daga cikin su ke fadin wanan ai ba maraba da buzuwar taka har ma ince tafi buzuwan taka komai gaskiya ka gode ma Allah.
Ban sake fuska ba don maganan su ya nuna yan duniya ne ba kunya gare su ba don basuki in zauna cikin su mu taba ba idan sun hadu da yar duniya kamar su da sai in biye ai ta darawa.
Kitchen na koma bayan na gama gabatar masu da abin sha din usualy mama laraba dama kamar a kitchen din ne wurin zaman ta.
Tambayan ta nayi idan yaran sun ci abinci da suka shigo tace ta basu sunci sai dai uwar su ce bata fito ba tun dazun nace mama ki shiga ki huta daga ciki mana.
Tayi murmushi tace ai banda hutu yar nan kamar can umurni ne haka daga uwargidan nan tace in dinga zama nan kusa da kitchen kada in nisa da nan irin wanan lokacin .
Na juyo nace haba mama mutum ai anason shi da hutu wanan aikin da muka sha kuma ba zaki zauna ki huta ba hakana.
Ta danyi murmushi tace haka na saba ai shiyasa da naje guri ki can ai naji daban do kin dauke ni kamar ta jikin ki.
Mama kada kice haka ke fa uwace a gare mu kuma ko banza ma kin haife ni don haka ki bar wanan tunanen ki daina daukan kanki a matsayin yar aiki a gidan nan ke uwa ce a gurin mu.
Muryan AA ke kira na daga falo na amsa da naam na nufi falon wurin su tire din dake gaban su yace in shiga dashi ciki na kwashe kayan zuwa kitchen.
Dakin anty na shiga na samay ta a kwance tana waya nace anty baki fito ba har yanzu abinci fa ko a kawo maki nan daki ne ?
Tace bayan amsa sallaman barshi ai yanzi zan sauko idan nayi wanka nace to barkan mu da sallah Allah ya kara maimaita muna tace amin daddy nagani yana barci a kasa nace daddy barci kayi ne ai na dauka kana gurin hajiya ne tace yana nan tunda suka dawo yaci abinci yazo ya kwanta.
Ban san sun dawo ba fa su nake jira su dawo muci abinci ashe har sun shigo ina barci na fita bata kara min magana ba dai.
Inda na idar da sallah ina zaune AA ya shigo da kudi masu yawa a hannun shi yana fadin bakin ki sun wuce sunce a baki wanan yana miko min kudin.
Anty ya kamata kakai wa nace dashi wani kallo yai min ya nufi gado yana aje min kudin tare da fadin idan kin ga zaki iya bata sai ki bata wanan dai ni ke sukace a bawa na dawainiyar da kikai masu ne .
Ya fice daga dakin ina idar da sallah kasa na sauka muka gyara ko ina na gidan har kitchen na feshe ko ina da kamshi ferfesu na dora don nasan ba abinci za a iya ci ba da dare.
Four ya gauta na gama komai na dawo na shiga wanka na kara sa wasu tufafi sai dai kayan nawa nasaka wanan karon don atamfar da na saka ya damay ni.
Rigar yai matukar karban jikina har zaka iya gano cikin jikina da ya baiyana yanzu falo na sauko muka zauna da mama laraba muna hira.
Binta da zainab suka shigo gidan muna ganin juna muka dauki ihu dasu sai kuma na juya da fadin Binta ai nayi fushi tace tambayi zainab Abba ne ya hanani zuwa.
Saboda gidan ku baida dadin zuwa ga mutum don babu kwanciyar hankali inji Abba nace kada ki dorawa Abba laifi Binta tace kin tambayi zainab idan baki yarda ba.
Mun gaisa na mike na shiga kitchen na hado masu tire na kawo gaban su na aje ina zama Binta tace ashe abin har ya fito haka ne ?
Nace ya fito sai ki shirya dama kece uban shi ai tace ko yanzu shiga daki ki haihu ki gani idan banda shiri nace uhumm kwana nawa ne Allah yasa Abba yace auren ki dana zainab za a hada inga tsiyar wanan bakin.
Muna gidan tare dasu har dare sai da sukayi sallah isha,i suka tafi tafiyan su da kama minti biyar bakin mu suka shigo gidan.
Ina kara gyara falon babu sallama sai ganin mutum nayi ta fado gidan har na firgita nace a, a sannun ku da zuwa ashe kuna hanya tafe ?
Kamar ba zata karba min ba sai kuma naji tace eh Ihisan na gani na tayo gurina da gudu ta fada min a jiki nace Ihisan nayi missing dinki.
Wani yare taiwa yarinyar naga ta kara makale min a jiki na rike ta tare da fadin tafi gun mamaki kinji.
Sama ta nufa ta bude dakinta ta shiga ruwa na dauka damai sanyi da mara sanyi nakai mata a dakin sai dai ban shiga daga ciki ba.
Yanyala ta fito ta karbi ruwan tana fadin angode na juya na fito Ihsan ta kara biyo ni karo na biyu muka sauko kasa.
Nan suka hade da daddy suna wasa irin ta yara Anty Fati da tun safe sai wanan lokacin ta fito muka gaisa ta kalli yarinyar tana fadin wanan fa?
Nace yar gurin Nafisa ce yanzu suka iso tace cikin wani irin yanayi ai sunzo ne suma ina Affan yace min basu gidan koda kuka taso.
Nace haka ne daga shi ban kara magana ba ita ma haka ta zauna tana cin abinci da bataci sai yanzu da tafito din
Sai tara ya shigo gidan yana shigowa idon shi akan Ihisan ya sauka yace ke kedawa kika zo tana ganin shi ta ruga wurin shi ta rungumay shi.
Hannun ta ya rike suka hau sama zuwa dakin su a daidai lokacin Samira tafito tana ce min anty Abinci yunwa nake ji tare da zama a hannun kujaran da nake zaune rabin jikin ta a nawa.
Nace barin hada maki kikaiwa wa su Ami din ki ko tace No a nan zaci gurin ki tana gyara zama kitchen na nufa na hada masu abinci naba ta takai lokacin yana tsaye suna fafatawa da ita a gurin.
Yana zuwa ya tura kofan tana zaune tana waya saman gadon ta yace ke wa ya baki izzinin shigo min gida cikin iyalina ?
Banza tayi dashi sai da ya kara maimaita abinda yace mata din ta juyo tana fadin naga nims gidan miji nane kuma gidan uban diyana.
Rai bace yace ku fice min daga gida kafin rayukan ku ya baci yanzu awanan lokacin samira ta shigo da abincin dakin ya bita da harara.
Tace gidan miji nane don haka babu inda zan tafi yace ok haka kika ce tace eh yace ok barin zo yanzu ki gani ya juya ya fita.
Kallon abincin tayi tana tambayar yarinyar wa ya bada abinci tace anty ce tace in kawo maku wani irin bacin rai taji a zuciyan ta cikin yare tace yar iska munafuka zanyi maganin ki a gidan nan.
Yana fita ya kira waya ba,a dauki lokaci ba sai ga yan sanda har biyar mata biyu maza uku sun shigo gidan kai tsaye yana gaba suna biye a bayan shi
Muna ganin haka muka bisu da kallo yaran dai suna gurina suna cin abinci hakalin su kwance can mukaji hayaniya daga sama inda dakunan suke.
Nan yan sandan mata suka taso su a gaba kamar a falki sai ga Nafisa tana share hawaye yanyala na goye da yar baby a bayan ta Nafisa ce a falon ta kalli yaran take fadin su taso Samira tace Ami na gaji da wanan yawon haka ku tafi ku barni gurin anty don Allah har ku gama.
Yace maza ta tashi tabi uwar ta da sauri nace please yaya kada kusa yara a cikin zancen ku dan Allah wani kallo ya watso min sai da na dukar da kaina kasa.
Ya kuta ya bi bayan su tana kan zagin shi na fitar arziki Allah ya kyauta nace Anty Fati daga inda take zaune take fadin Allah nagode ma da ka nuna min wanan ranan da raina da lafiyata.
Can rikici ya kaure masu tace bazata shiga motan yan sanda ba tunda gidan shi yace ta fito ta fita ai sai da yaga wucewanan su daga unguwar ya koma cikin gida bai tsaya falon ba ya shige dakin shi muna zaune munyi tsit a inda ya barmu zaune sai dai wanan karon ihisan ta gama cin abinci ta kwanta tayi filo da jikina da ita da daddy.
Ashe bata wuce ba Family house din su ta shiga gurin iyayyen shi da kuka tace tazo ya kore ta gidan shi ko tausayin yarsu da take fama da ita baiji ba.
Don inda yanyala tabi tanata da sun bar yar a gidan bata tafi da ita ba ga yarinyar tana callara ihu gwanin ban tausayi amma haka ya rufe ido ya kora su daga gidan.
Mommy hajiya mama ta aika a kira don dare ne kowa na part din sai ga mommy don binta ta fada mata ga buzuwa tazo yayan su ya korata daga gidan shi.
Har su umma an kira sun zo da anty amarya Biinta ta shige daki ta kira yayyun su tana labarta masu dan abinda ta sani daga cikin zancen.
Mommy ne tayi karfin halin magana bayan ta karbi yar daga hannun yanyala ta dubata tana fadin Allahu Akbar Allah mai iko sai kuma ta dago kai ta kalli nafisa tace
To Nafisa abinda ake gudu ke nan ya faru samun wuri yasa kin wuce iyakar ki kina taka kowa yadda kike so baki tuna akwai Allah.
Nan muka je gaida ke akan lalurar rashin lafiyan cikin yarinyar nan kika rufe ido kikai muna cin mutunci a gaban kawayen ki da kowa.
Mu dai mun san babangida namu komai ko ya faru bazai taba kin mu ba don mune dai iyayyen sa mudin da kika wullakanta.
Yanzu kuma ki dauko kafan ki kice kin zo wurin mu wai neman sulhu ko kin manta da maganar ki na ranan da kikayi akan zuwan mu.
Anty Amarya tace irin wanan ranan akewa gudu duk abinda bawa keyi Allah yana kallon shi ai don yanzu tun a duniya Allah yake fara hisabinsa.
Ke baki zauna lafiya da miji ba, haka kuma yan uwan zama ki baki zauna lafiya dasu ba kin bi gida duk kin burkuce mai da bakar fitinan ki.
Ga magana suna ta zuba mata babu daman ta basu amsa don ita yanzu bukatan ta kawai a samu a shawo mata kan Samad din ta takeyi daga baya sai ta san abinyi.
Hajiya umma ne tai magana karo na farko bayan ta gama kallon yar tace yanzu da kika zon nan din may kike son muyi maki ?
Wanda ke zama dake ya gaji da halin ki yace baiyi mu may ye namu a ciki ko lokacin da ta auro ki ya kawo ki gidan shi mun sani ne ?
Ba irin wullakancin da baki wa yaran gidan nan dama yan uwan mijin ku suda gidan dan uwansu kin hanasu zuwa kin tare gaba kin tare baya.
Yanzu ki koma don mu ba abinda zamu iya maki tunda kince ba son ki muke yi ba sai kije gun masu son ki su gyara maku zancen tana fadin haka ta mike ta bar dakin.
Hajiya mama tace kin ji abinda yaya tace don haka ki koma inda kika fito yaje can ya samay ki shida yaji yana iyawa don yanzu ban san may zan fada ba don in ina tuna abubuwa raina kara baci yakeyi.
Hajiya umma ne ta dawo dakin tana fadin ki taso Alhaji na kiranki ta juya tace hajiya Binta ku taso muje gurin Alhajin .
Suka fito banda yanyala da bata bisu ta zauna a dakin hajiya mama din don ita hajiyan tace babu inda zata.
Yanyala ta kala bayan fitar su tace kunci abinci tace yanzu Dija amarya ta aika muna dashi muna shirin ci yazo ya kore mu daga gidan.
Dabiar yar uwaku baida kyau bai kuma da dadin ji samun wuri ai ba hauka bane tana ganin dama Allah bazai tambaye ta wanan fitsaran da take bane wa mutane.
Yanyala tace hajiya hakkuri zakuyi don Allah ku taimaka muna mun sha wallah sosai tsakanin shekaran jiya zuwa yau abin ba dadin fada.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Washe gari na tunda safe na hada breakfast ina gamawa na aika laraba ta mikawa kowa nasa don guje wa fitina kuma.
Girkin rana na dora don firlta hakkin mutane kada in fita banyi ba alhaki ya hau kaina a gurguje na gama komai na zuba again takai masu.
Wanka nayi na shirya na nufi cikin gidan su part part na shiga nagaida kowa na dawo gurin hajiyar su.
Mun dade a falon tare da ita tana kara min godiya irin canji da take gani a tare da dan nata take fadin sai kin kara jajircewa don wanan matar tashi ban yarda da nadamar ta ba har yanzu.
Babu komai nace mama adai taya mu da addua tace fauziya suna fada min abin arzikin da ya samay su jiya sai dai kin san ba abu bane da za ai saurin bayyanawa a fili sai in maganar ya tabbata ko ?
Nace gaskiya ne hajiya tace banson ko mommy ku taji wanan labarin sai idan abin ya tabbata gaskiya ya mika masu takardun a hannu kowa ya sani.
Don mijin nan naku ne baida tabbas a al,amarin shi yasha yin alkawari irin haka karshe ya barni ana yaba min magana a fakaice.
Mama ki kara hakkuri don Allah muma haka muke dashi alamarin nasa sai da addu gaskiya don zakaga ya bi hanya kwana biyu kuma sai ya kauce kamar bashi ba a rasa gane kan shi.
Sai naji tace Alhamdullahi dana samu wace ta fahinci hakan gare shi wanan abin yana ci min tuwo a kwarya khadija yanzu ki duba dan wurin hajiya yaya ummar ku nan.
Surajo ai ba kaishi yayi ba ga komai amma yadda yake kula da mahaifiyar shi da yan uwan shi a dakin su sai abin ya baka sha,awa ni nawa sai sunan kudi amma babu amfani gare mu daman ma yanzu ne nake dan ganin haske abin.
Tausayi ta bani yadda ta zauna tana fada min damuwar ta nasab abin yana cin ta sosai a rai tunda har ta iya zama dani tana fada min hakan.
Tace bandamu da sai yai min ba amma ya dinga kulawa da mahaifin shi da yan uwan shi bawai dole sai nawa ba a,a duk dan da ke cikin gidan nan yanzu shine babba a gare su ai yakamata ace suna alfahari da abinsa ai.
Shiru ni dai nayi ina sauraren ta tana kuma ban tausayi ga maganan ta wanda gaskiya take fada koda ba a cikin kishiyoyi ko take ba kowa nason ace nasa na kwarai ne.
Mun gama nake cewa zan leka gidan anty na in gaidasu da sallah tace to a dawo lafiya zaki leko ta nan ne kafin ki koma gida ko nace insha Allah mama.
Har na fita gidan ina tunanen wanan magana Binta ce ta rakani don zainab tana kwance tun safe wai bata jin dadin jikin ta.
A kofar gidan Ya Amina muka hade da mijin ta a get zai fita tun daga nesa yake min dariya na karaso inda yake nace ya Adam abin dariya kuma na zama gare ka ko yanzu ?
Yace mamaki nake wai yar khadijace haka ruku ruku da ciki nace ai haka kuke son gani na dama kuka lakaka min aure binta ne ta amshe auren bagaki kin sake ba kin zama wata basaraka dake.
Baki na tabe yace kyale ta binta kinji tana matar last done haka takewa mutane korafi yanzun zaki koma ko kina nan zanje gidan hajiya in dauko yara ne dama sun maysa a dauko su suzo wurin ki tunda sukaji kina gari.
Nace ina nan har dare tare daku yace barin je in dawo mu sha hira ashe iya matar manya duk kin wani canza ga baki daya wallahi.
Nan dai na wuce ya na barshi ya shiga mota yana min sheri muna shiga na samu anty tana gyara falo su tana ganin mu ta washe baki tace mutanen Abuja.
Wallahi yanzu na gama magana yau idan azahar tayi ban ganki ba zanje gidan naku in ganki nace ai gani nazo yanzu.
Muna waje da mijin ki yana min sherin shi da ya saba ina ganin sai munyi fada dashi zai daina yanzu ma fa dariya ya dinga yimin a waje.
Binta ne ta gaida ita yasa bata bani amsa ba suka tsaya gaisawa ta tambaye ta mutanen gida tace suna lafiya bata tsaya ba ta mike tana fadin madam ni zan tafi sai kin dawo ke nan.
Nace madam kan ai tana abuja suna bushasha wata kawar buzuwa ce uwar dakin su suke kira madam tace ko wata garmakar mace haka karfafa nace ita ashe kin santa ma ?
Tace na santa mana lokacin da mukaje sunan ihisan sukayi muna tsiya suka kulle abinci Allah yasa da mommy na gidan ta saka aka kawo muna a wani gida.
Dariya nayi nace kai Nafisa ai ta tsula tsiya gidan nan kuma har yanzu akan yi take don ku jiya sai da muka kwasa da ita ai bayan fitar ku.
Kai khadija wallahi kina kokari mun dawo gida muna maganan ki da hajiyan mu take cewa ai tunda batayi galaba a kan ki ba yanzu bazata taba yi ba da yardan Allah.
Ke dai adai yi sha,ani wai ancuci na kauye ni abin nata gani shi nake kamar mai motsi akai tace babu motsi wallahi inji ya Amina haukan kishine irin nasu kawai su haka suke kishin su a haukace.
Nan gaba idan taga abin ma bai mata ba taga ba ci kokari zatayi ta wawashe mijin naku ta gudu kasar su bai kuma samun labarin ta.
To Allah ya kyauta nace ina dora kafana saman kujeran da nake zaune akai Binta tace wai khadija wallahi ba don na sanki ba da sai in ce baki taka kasa wallahi.
Duk kin canza gaba daya komai naki yayi fresh nace tafi yar sheri wanki da ko mota ya kasa sai min don tsoron buzuwa wani kasa zakice ban takawa kuma.
In dai mota ne tafe yake ai ki dai haihu ki gani har abinda yafi mota zamu saya maki nace oh haka kuke ashe kowa yaci ladan kuturu yasha dungu ko ?
Ta fice tana dariya ya Amina ta zauna gefe na tana fadin abindai da sauki yanzu ko na mede baki nace wani sauki dukkan su biyu fa anty ba wani sauki don ko anty fati ba baya ba ashe.
Tace ita fatin nace dama mana nidai kawai ban bin ta nasu ne don kawai a zauna lafiya amma ko ita ba kanwar lasa bace.
Tace zata iya indai Fatice don ba wanda ke jin dadin ta a gidan nan ko kwanaki na iske suna rikici da na shiga wai motar ta ya baci ta sayar bata fada ma kowa ba kuma an nemay kudin an rasa su.
Wai to Ya Amina may take da kudine sai naga tayi dariya tace ke ma ai ba sai kin tambaya ba ni dai abinda nake so dake khady shine.
Kada ki yarda da cewa wani zai iya maki wani abu ki yarda da Allah shine maiyin komai a rayuwa ki idan rokon Allah ne ki tashi da kan ki Allah maji rokon bawan sa ne.
Ki dai dage da gyaran jikin ki kina kara ma kanki daraja a furin mijin ki wanan kan ban hanaki yin sa don yana taimaka wa mace a rayuwan auren ta.
Amma bin boka ko malam kin san ba dabiar gidan mu bane kullun da wanan zancen nake kwana ina tashi ina kuma maki rokon Allah kema kada kiga suna yi kice zaki kauce ma hanya yanzu da abinda yan uwan Fati suke mata korafi ke nan.
Sai dai kuma dole ne yasa Fatin yin haka don tana ganin shine kawai mafita a gareta ta manta da Allah shine mai yin komai.
Nace anty ni jiya na kara yarda da halin ta da ake fadi ai wai fa kin yin girki tayi don kawai na taimaka nayi mata girkin sallah ranan danaga suna rikici da miji.
Ashe ta kulle ni a rai ta aje shine jiya taki girkawa da yai magana tace wai ai nice mai girka mai may yasa ba zai tambaye ni ba.
Tace ai da kin sani ki kyale su a zauna hakana mana ba ita zata sha wuya ba ita dake da yara ke haka fa take bata dadi da kowa bata shiga mutane ta waye.
Ai mijin nan naku yana da mata wallahi ga mutum har mutum amma bai samu abokan rayuwa a gidan shi ba shiyasa yake kara yin abu a dabbale wallahi.
Don mace na kara gyara namiji ta hanyoyi daban daban sai idan ba ai dace ba zaki namiji bai kullawa yan uwan shi komai.
Nan nake fada mata hiran mu da hajiya tace matar tana a cikin damuwa ne khadija yau ba maison ace nashi baida kirki ai.
Mijin ku fa yadda nake ji ba karamin mai kudi ba ne a garin nan shi ma rigima ne dai kawai da baida shi amma kinga yan uwa sai korafi sukeyi akansa.
Waini ya Amina yanzun haka zan zauna ban leka mama ba idan shi Daddy bai son ganinna ita mama fa da ya tauye mu da ganin juna.
Tace kin manta haka halin daddy yake ne ko suwaiba dake cikin gari ai dai kinga yadda suke kwashe wa dashi idan ta jera sati uku tsakani tazo gida.
Halin su ne na filani ya dauko yake wanan akidar haka ko kuma tsabar izzala ce ta haushi haka ban sani ba kiyi hakkuri kwana nawa ya rage idan kin haihu zaki gan su.
Ya Amina har wanan lokacin ban je gida ba gaskiya nikan da mun koma din nan zan matsa mashi zani gida ne don banzama har wanan lokacin ban leka su ba.
Shigowan yaran da ihun sune ya dakatar damu da hiran sukayo kaina na rungumay su a jikina Allah ya dora min son yara a rayuwana tun kan yayan ya Amina din.
Karamar da bata saba dani bane taki zuwa wurina dole na yunkura ina fadin zo nan yar bura uba mai shege kiuya kawai wai ita nan bata san ni ba.
Uwar tace ke ko ina zata sanki tunda aka haifeta ba zuwa kike sosai ba kuma datai wayon na kinyi aure ba zuwa kike yi ba tana ganin ki.
Mijin tane ya shigo gida yana fadin matar manya ke nan gani na dawo nace wata matar manya can kodai matar wahala may ke gidan ban da tarin fitina kullun safe da kalar da za a tashi dashi.
Yace mijin ki fa last done ne wurin kudi khadija bazaki fadi haka ba ai mana nace ya Adam kudi ai basune farin ciki ba ko ?
Yace hakanane kuma kin fini gaskiya tanan har ina cewa zan kawo wani ogana da ya dade yana neman fili a wurin shi yasa mashi hannu yaki ki muna hanya asa.
Tsuki naja nace wanan idan yaki abu ai ya kishi ne sai dai mu gwada mu gani idan zamu ci sa, a kawai amma bansa zai yi ba wallahi.
Yace kai dako kin kyauta muna wallahi khadija bashi ba harni nan da na warke idan wanan abin ya yuyu ai aje aki gaba daya zanyi in fara business.
Nace kai yaya Adam wanan wani irin abune da zaisa harka aje aikin ka kanshi kuwa yace wallahi khadija muddin muka samu ya sa ma takardan nan hannu mur warke har abada.
Ina fada maki AA ba karamin mutum bane fa sa hannun shine kawai ya gagara wata kila kuma da rabon mune har abin ya biyo ta wurin mu yanzu.
Ogana wani dan jalingo amma lagos yake zaune yayi ritaya shine ke ta binshi shekara da shekaru yaki saka mai hannu a takardan nan.
Shiru nayi ina tunane har banjin may yake fadi sai can naji yana fadin ai kinsan da ina da sister wace ta rasu din nan a lagos farkon auren mu da yayan ki nace eh yace to ai mijin tane nake maki zance nace in Allah yaso zan masa magana sai dai nasan zamu kwasa dashi koda zai yarda din ma.
Ya Amina tace ki daibi a hankali kada wanan maganan ya hada ku nace insha Allahu ko maryam kawana ta taba min korafin nan yaki saka ma mijin yayan ta hannu.
Ya Amina tace ashe haka yake dai sai mijin ta yace aikin nasu ne akwai hatsari a cikin sa da yanzu yana saka hannu barkatai da sun yi waje dashi tuntuni.
Ko jiya da dare naga matasan masu kudi garin nan sun parke motocin su a kofar gidan shi nasan wani harkan business sukeyi kinsan shi fa dan kasuwa ne kuma yana wasanni da dama ta idan kudi ke zo mai ke nan ai sai dai akwashi da boyon kurwa ne sosai wallahi.
Ina gidan tare dasu har dare anan na wuni sai baya magariba ne ya kirani yace wai kina inane nace gidan yaya na amma yanzu mijin ta zai sauke ni gida idan ya dawo sallah.
Yace No ki jirani in zo akwai inda nake son muje daga nan nace dashi sai kazo ya kashe wayan yaran ya Amina na rabawa goron sallah.
Kudi ns girka masu yawa na aje mata a gefen inda take zaune tare da kara kirga wani na sake aje mata nace naki ne da yaya Adam kuyi hakkuri dashi baida yawa.
Ita ya Suwaiba nace ta bude account taki har yanzu kuma tana raina sosai don nasan irin wahalan da suke ciki idan ta bude ai kinga zan dan rika tura mata da wani abu lokaci lokaci.
Tace zan ma daddy magana a bude mata din kin san halinta nako in kula da abu ai gaskiya kan tana bukatan taimako nace aishine kullun zaka bata abu sai ta hannun daddy dole shi kuma ya dinga fada da mutum wai kana rikon mijin ka kudine.
Ni kuma wallahi anty ban iya cewa ya bani kudi idan bashi ya dauka karan kanshi ya bani ba tunda muna samu a gurin girki idan zakayi dubu goman nan sai ya zube ma shi kafin ya fita.
Tace yanzu wanan din da kika bamu baiyi yawa ba khadija nace idan ban baku ba wazan ba anty tunda kune dole na.
Bandai ba dangin shi kudi kai tsaye sai dai in saya masu wani abu in basu gudun yawan magana da zargi tace haka shine daidai ai.
Don wallahi zargin ki zasuyi akan yana sakar maki kudi su bai basu ba tace kina da dabara da yanzu an fara kusun kusun kin san gidan yawa.
Wayana ne yayi kara na duba shine a layin ina dauka yace fito mu tafi nace a, a bazaka shigo ku gaisa ba ke nan kuma sai naji ya kashe wayan.
Tare da yaya Adam suka shigo gidan har cikin falon ta suka shigo suka shiga gaisawa tana mai barka da sallah.
Yaran suka zo suka rusunna suna gaida shi ina ganin yaji dadin hakane naga ya shafa kan yar karamar yana tambayan ta sunan ta.
Kudi ya debo ya basu tare da ajewa ya Amina nata a gefe ya mike yana fadin zai mu tafi zamu unguwar dosa ne.
Yaya Adam sai wani haba haba yake mai abin ni sai mamaki nakeyi na mike ina cewa ya Amina sai na kara shigowa tace yaushe zaku koma ne nace muna nan tukun ba rana.
Tace tafiyan ku ai kamar na filani ne idan ya tashi ko ba shiri ranan tafiya zakuyi nace to ya muka iya sai bi har wajen dirkekiyar motar shi suka raka mu ita da yara mijin ta yana tsaye dashi a waje nayi masu sallama na shiga muka tafi.
Yace yau kin kawo mata dawainiya ko nace wani dawainiya kuma mutum da dan uwan shi ina dawainiya ina zamune wai haka ban ko zata ba.
Yace baki da shiri ne mu koma nace ban ce ba ina dai tsoron ka saida nine kawai dariya ya dan sake yace dasun sai mai baki kan.
Gidan gwagona zani kanwar Abba tayi ciwo ance tana ta magana na ko yaushe can nake son muje mu gaishe ta don yau nake da lokacin zuwa.
Allah sarki ashe dai daddy yana da yan uwane da yawa haka yace sosai kuwa suna da yawa fa sosai don ma wasun su sun rasu ko .
Mun isa gidan da ganin gidan ya dauki shekaru don ba wani gida bane can irin dai gidan tallakawan ne kamar mu.
Da haba haba dattijuwar ta karbe mu tana fadin maraba da babana yau kaine a gidan ashe da rabon zamu kara haduwa dakai yace yana shiga dakin gwago kiyi hakkuri wallahi ban faye zama kasan bane muka shiga dakin tana kokarin kawar da tsumakaran saman kuje ta gyara mai wuri tana fadin zauna zauna baba ubangiji yai maku albarka da ka tuna dani yau.
Ina tsaye daga kofa ta kawar da kayan saman gadon gefe tare da fadin karaso kinji yar albarka tana nuna min inda zan zauna.
Na kai kasa saman carpet din sallah ta tare da fadin babba nan ma yayi mun ai aka shiga gaisawa tana ta tambayan shi mutanen gidan su da iyalin shi.
Ta juyo tana kallo na nayi murmushi ina gaida ita ce itace buzuwar ko sabuwar ce ta garin nufawa yace sabuwar ce gwago.
Ta kamo min hannu tana fadin sannu kinji yar albarka ki rike min ubana da kyau kinji kinsa mata suke gyara gida ina murmushi nace to babba .
Nan sarakanta da yara ta suka fara shigowa gaida shi suna mashi sheri bai iya wasan tobashi ba sai kamay kamay yake masu yadda na lura dashi.
Matar tana da kirki a yadda na kula ga addini magana kadan ta kawo Allah tana nuni da rikon zumunci a gare su.
Yace Ahmed fa yana inane yanzu sai da ta dan bata rai tace yana nan gida kasan shanin aikin su na Nepa ashe basu da tabbas.
Yana cikin wa yanda aka kora daga aiki kwana ki ga iyali ya tara kamar ka shima mata uku gare shi sai dai yadara ka don yanzu diyan shi goma ga ba aikin yi kuma.
Yace wai ikon Allah yanzu Ahmed din ke da diya goma gwago tace ga na shadaya nan a ciki ana maganan shi sai gashi ya shigo tace kaga dan halas nan ya shigo.
Kallon juna sukayi sai suka dara yace wai mama yau kodai dan naki yayi batan kaine yau baban ku ne a gidan ki gaskiya ranan yau ta dabance.
Sun dade rike da hannun juna suna shammatar junan su sai daga karshe yake fadin yanzu nake ji wurin gwago abinda ya samay ka.
Yace wallahi ya za ayi da sha,anin kasarnan tamu sai hakkuri yace haba Ahmed shi ne baka leka ni ba yace kasan ganin irin ku idan baku kuka nemi mutum ba abu mai wuyane sosai.
Yanzu ai cikin hukuncin Allah gashi kai ka nemay mu ka kwashe ladan dazun naji Altine na maganan su hada kafa suje gaida kawu da sallah nace mata mu mun je tunda aka sauko idi.
AA yace haba ya bamu hadu ba daku yace wallahi ana saukowa mukaje muka gaida shi kasan mu bamu wasa da kawun mu yace ai na ga alama.
Gwagon tace Alhaji banda kamar Alhaji ga yan uwa duka kaf har gobe Alhaji duk da girma ga iyali yana tsaye ga alamarina garin nan sai ta fashe da kuka.
Wani iri naji a raina dukar da kaina nayi kasa ina kokarin maida hawayen da yazo min a lokacin gwago kiyi hakkuri haka rayuwa yake AA yace mata ya ciro kudi ya aje mata tare da fadin gwago mu zamu tafi zan maida wanan gida don yanzun bata dogon hira ta fara tsufa.
Hararan shi nayi sai lokacin Ahmed din ya juyo gare ni yace amaryan ne ko buzuwar yace amaryan ce yace ikon Allah aiko ita buxuwan ce sak.
Yana washe baki ya mike tare da fadin muje waje muyi magana ina Altine ne tazo in bata goron sallah kada ta cini da bakin nan nata gwago zakiji yadda zamuyi da Ahmed din insha Allah.
Sai lokacin na mike tare da fito da kudi cikin jakkana na mika mata nima tana ta saka muna albarka muka bar gidan.
Sun dan dade da Ahmed din a waje suna magana ni kuma muna tsaye da wace aka kira da Altine din da sauran yan uwanta muna hira sukace zasu shigo kafin mu koma Abuja sai kunzo nace na shiga mota suna ta janshi da ba a tace sai munzo Abuja suna idan matar ka ta haihu yace kada kiyi mamakin ma kije can ki zauna har ta haihu din.
Ahmed din yace dako abu yayi kyawo wallahi tunda ba aure takeyi ba yace ai shine taki aure ba sai ki koma zama da mu ba muka wuce suna daga muna hannu .
Ajiyan zuciya na sauke ya juyo yana fadin ya akayi ne nace ummm, umm gani nayi ashe dai kuna da yan uwa ne haka da yawa garin nan yace wanan da kike gani uwar su daya da Abban mu da ita da Iyan bawa ok baki santa bako lokacin haihuwan Ihisan ne ta zauna damu acan Abuja.
Nace ok wanan tsohuwar da suka zauna da mommy yace ita ok inji kin ji don su binta lokacin nace naje mana matarka tai muna hauka kai ya girgiza yace yanzun ma tana can ai na barta tana haukan ne .
Wai ita girki zata karba yau nace ai da kabarta ta karba din tunda ita taga zata iya yace in kaita ina idan ta karba din ko ta cika min daki da fitina.
Nace da ina kake kaita da kuke daki daya kefa baki da kunya nace I'm sorry big brother tuba nake yace hauka ta dai takeyi.
Allah da ka barta tayi ai tunda zata iya din ko ba wani matsala bane shiru yayi min bai bani amsa ba nima shirun nayi mai sai can nace yawwa don Allah ko kasan wani AS Hamza jalingo wai.
Sai da ya waigo ni yace cikin dakewa ina kika san shi ke nace mijin yayan Adam ne mijin anty Amina da ta rasu tabar mai yara biyar.
Yace nasan shi may ya faru shiru na danyi kafin in ce wai alfarma suke so a wurin ka don Allah badon mu ba sai dan yan maratun diyan nan ka saka masu hannu a takardan da yake so ka saka mai hannu.
Yace aikin da suka baki ke nan kuma nace a, a wallahi basu bani wani aiki ba magana daine ta taso har naji amma ni basu sani ma magana ba.
Shi AS jalingo din ne baida abin duban marayu ko shirmay ki din ne yasa kika fadi haka nace kai kullun ai banda wayo ne a giri ka yace abinda nake so dake daga yau kada wani hurda aikina ya kara hada ki da kowa kinji na fada maki.
Don ban daukan wanan shashanci abi ta matana ace ana neman wani abu a gurina haka don yaudara ko may ?
Don Allah kayi hakkuri bansan maganan zai bata maka rai haka ba da banyi mashi ba amma ban karawa da yardan Allah kayi hakkuri ka yafe min idan na bata ma raine.
Ni abinda yasa kaji nama maga hakane kawai zanyi in rama itin halarcin da yaya Adam din yai min a rayuwana wanda dashi nake tunkaho yanzu do badon shi da yai min tsaye a karatuna ba da iyakata secondry school don daddy baida halin kaini gaba.
Amma ya Adam shiyayi tsaye har sai da nayi aure ya daina sa hannu a zancen karatuna shine kawai yasa kaji nayi ma maganan nan.
Huci naji ya furzo dana gama maganan bai sake tanka min ba har aka wagale get din gidan muka shiga muna tsayawa ya bude motar nafita yace dauki ledan na daya ki shiga dashi wurin ki na juya baya na dauka kamar yadda yace nace Allah bamu alheri ban tsaya ba na wuce.
Ina shiga falon yaran nata wasa suka sheko suka rike ni suna mi oyoyo nace miss you guys ina ihisan na tambaya tana gurin uwar ta na karasa dasu a rike a hannu na na gaida Anty Fati da tayi kamar bata ganni ba.
Mama laraba ta fito daga inda take tana sannu da zuwa an dawo nace na dawo mama ya gida tace muna lafiya wajen antyn taki suna gaida ku nace tare da fadin barin dan watsa ruwa mama tace kudai baku da tada ko wani lokaci wanka kuke bamu gujewa wahala da cikin ki da tsohon daren nan zaki wanka.
Idan ban watsa ruwa bane banjin dadi mama nace mata ina dariya na wuce dauke da leda a hannu na har na fara hawa sama nace mama in akwai ruwa a flasks akawo min don ban iya saukowa kuma.
Tace barin in duba lokacin naji yaran na mashi sannu da zuwa na shige abina ban tsaya ba ina shiga na tube na shiga bandaki daidai fitowa na sai ga mama laraba dauke da ruwan zafi a cup tana fadin banga flasks din ba ina ganin mai abune ta dauke abinta nace tofa kuma wata sabuwa ashe ?


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Kallon yarinyar Abba yayi tare da dan jujuya ta ya dago yana fadin Allahu akbar ya mika wa hajiya umma yar yace yanzu da wanan yar haka babangida ya turaki waje a cikin daren nan ?
Bai tausayawa yar shi ba saboda saboda halin da zata iya shiga yana magana yana duban wayan shi bayan ya gama kafa glass din ido shi.
Umma tace ai fushin uwar ne ya shafi yar amma ai ba zaiki yar shi ba tunda ya iya kaita har waje cikin wata mai alfarma da kowa ke son ya natsu yayi ibada a cikin sa.
Murmushi tsohon yayi yana danna kira a wayan shi ya kafa a kunnen shi tare da alaman saurarawa.
Muna zaune falo bayan na gabatar mai da abinci yana shan ferfesun kajin danayi a matsayin abincin dare ihisan da daddy ne a gefen shi suna wasa.
Sai ni da anty Fati da Affan da muke hira daga can wurin kujerun da muke zaune mukaji yace hello Abba.
Duk muka dago muka kalle shi cikin kashe murya anty Fati tace yar iskan kila itace yanzu haka takai karanshi gurin Abba ai dai ta fara ganin sheri ga kaya ta.
Sauren wayan yake yi ba tare da yayi magana ba mukaji yace naji Abba nagode ya kashe wayan ya dan kallo mu yana mikewa yabar gurin tare da nufar hanyar fita waje.
Wallahi ban taba tausayin wanan matar a rayuwa na khadija don ban iya manta abubuwan da tai min a rayuwa na har in koma ga mahalici na kuwa.
Hakuri za a Anty ai ita bata bar kowa ba nidai ban mata sheri ba indan kuma ta nufe ni dashi ya koma saman kanta insha Allahu.
Tace kiri kiri mata ta hanani zama a dakina ta fito fili ta fada min kuma wai kadan na gani daga sherin ta shine yanzu zan tausaya mata ai mata ma yafi haka wallahi.
Allah ya kama su daga shi har ita abinda na gani akan wanan matar nawa sane kiri kiri zasu garin nan tare tace bazan yi girki ba har su gama kwanakin su su koma suna tare.
Ai wurin nan kan shagoce a wurin kwana da miji ko ni can shine yawan matsalan mu don ba shiga harkanta nake ba tun farko don haka ne abubuwa suka zo min da sauki.
Don bamu taba zama haka yadda muke dake din nan ba tunda na shiga gidan nan har rana ita yau kuwa don yar rainin wayo ce tana ganin ita tafi kowa ko shi kan shi gani take tafi shi bata san namiji ki sabo ne ba idan halin shi ya tashi dan abu kadan sai ya kaskanta ka akan shi.
Tace Allah ne fa ya kama su khadija ina fada maki koshi ba kanwar lasa bane wurin wullakanci bata kai karshe ba sai gashi a gaban mu don duk bamu farga da shigowan shi ba lokacin.
May kike fada ya tsure fati da ido ta kasa magana ya kara maimaita maganan shi tare da kallo inda nake nace bafa maganar ka ake ba da Affan take kutawa yayi ya wuce sama.
Nan yafi auki ai don nan zai iya zare idanu can ko ko mussu bai iya yi nace anty wa ya fada maki wallahi yana yi yar iskan matace dai ya hadu da ita.
Sallaman su mommy ne da Anty amarya yasa muka mayar da hankalin mu gurin taron su muna gaida su da shigo tare da masu barka da sallah.
Mommy suka kai kallo a gare mu yaran duk suna a kujeran da nake zaune two seater sai samira dake barci gajiya a dayan kujeran dake gefe na ta rankofo jikin ta wuri na.
Mommy tace don Allah duba saboda Allah may yafi wanan Nafisa kina can kina fada akan wanan yarinyar duba yaran ki a tare da ita.
Anty Amarya tace yaro ai dama fuska yake bi idan bata basu fuska ba ai ba zasu bita haka ba dukkan su.
Yanzu ba Fati da khadija muka samu a tare ba suna hiran su gwanin ban sha,awa amma ke kice da kowa ba za a zauna lafiya ba.
Muryan AA mukaji daga baya yana fadin mommy kun shigo tace eh babangida don Allah kai hakkuri don Alhaji da ya saka baki a cikin maganan nan kada wani abu kuma ya kara samun wanan yar.
Kallon Nafisa da take tsaye tun lokacin nayi mommy tana sance yarinyar a bayan ta tana kokarin mikawa Anty Fati da ta gane haka sai tayi saurin mikewa tare da fadin tana zuwa tayi hanyar kitchen duk muka bita da kallo don kowa ya dago ta.
Ni mommy ta mikowa yarinyar tana fadin karbar ta khadija nasa hannu bayan na jaye ihisan a jikina na karbi yarinyar tana ta barcin ta ba wasu kayan kirki a jikin ta duk da sanyin kaduna da akeyi din.
Zama sukayi tare da fadin Nafisa ki zauna mana ayi magana tana wani harare harare ta zauna tare da yanyala.
Mommy tace Alhaji ne yace idan munzo dama mu tara ku sai gashi Allah yasa mun samay ku a nan din baki dayan ku.
Tau Nafisa duk da Alhaji baiji ta bakin mijin ku ba yanzu dai wanan abin ya ishe ki ishara baka shigowa wuri kace kai kan ka kasani kai kadai.
Ihisan da ta kara hawa jikina anty amarya tace wai ku bakuga uwar taku cikin wani hali bane ku barta ta huta mana hakana.
Shiya karbe da fadin laifin tane ai anty ko yaushe yaran nan suna saman jikin ta hatta idan abinci zata ci sai dasu take ci nayi fada bai sa sun daina ba.
Tace kin zama uwar yara khadija mommy tace in dai khadija ce haka take ai tun gida da yara ita yaro baya isanta ai.
Fada mai kama da nasiha sukai muna a gurin tare da jawa kowa kunne a cikin mu sukai muna sallama suka tafi suna fita yanyala ta mika hannu ta karbi yar daga hannu na suka shige dakin su.
Don shi ya raka su mommy har bakin motar da sukazo dashi an daiji kunya idan an santa angama cika baki gashi tun ba,a je ko ina ba anfara gani.
Anty Fati ce ke wanan maganan bayan wucewar nafisa din ciki ta ce ni ai ba zan taba yarda da kishiya ba har dai irin nafisa mara imani.
A raina nace hardani ke nan dama ban ce sai kin yarda dani ba ai banda ma kowa sheri idan kun min kuma insha Allahu ya koma kan mace.
Bamu dade ba na tayar da Samira na kora ihisan zuwa dakin su nima na shige nawa na barta da yaran ta a gurin.
Washe gari na tashi da son zuwa gidan Ya Amina don can nake son wuni idan na shiga na gaida su hajiya da sallah daga can sai in wuce wurin ta.
Sai dai hakan bai samu ba don bakin dake shigo muna su Anty fauziya ne tare dasu binta suka shigo muna gaida dan uwan su da sallah basu samay shi gida ba.
Har lokacin ba duriyan Nafisa ko wani nata hatta ihisan banga ta fito ba yau abin karyawa ma yanyala ce ta fito ta karbi ruwan shayi ta koma.
A dakina muke zaune tare dasu bayan sun fito wurin Anty Fati nan suka zauna muna hira sosai da su wanda hiran na zancen auren zainab ne.
Sai gashi ya turo kofa suka shiga gaida shi ina dan tsaya a jikin mirrro sai dai duwawo na dake saman mirrow na zauna akai.
Gaidashi da dawowa nayi ya mayar da kallon shi gare ni yana fadin bazaki zauna da kyau ba wanan tsayin da kikayi fa haka ?
Gyara tsayawa nayi da kyau yace dani yau dakin nan nawa yana bukatan gyara don tunda nazo haka yake da kyakyami nake zama a cikin sa.
Nace zaka bar key ne a gyara maka yace eh ina ma gida ban fita sai anjima idan Yusuf ya shigo.
Ya fice Anty Fa,iza tace kai daga Yusuf dai sai yayan mu Allah ya hada amintaka a wurin nan nan suka shiga tuna labarin su na baya suna dariya.
Nace ai gaskiya zainab tayi dacen miji wallahi don idan ta iya zama dashi zata ji dadi wallahi Fa,iza tace ai kema kinyi dace don yayan shima yana da hali mai kyau.
Baki na mere masu nace kai anty kina dai son zance ne kawai wanan gidan gidan danger ko yaushe a cikin fitina ake.
Wallahi anty wani lokaci sai inji kamar in bude ido na in ganni gidan mu don fitinan yayi yawa wallahi tace ai dazun hajiya ke bamu labarin abinda ya faru jiya nace eh tana nan ta dawo zaku shiga ne.
Ina anty faiuziya ta fadi da sauri nace wurin ta anty ina dariya tace ban tashi jin bakar magana ba yau da farin ciki na fito gidana.
Dakin Nafisa kuwa har lokacin tana kwace a dunkule wuri daya sai kiyasta yadda zata dau fansa akan mu baki daya take a zuciyar ta.
Wai yau itace har iyayyen mijin da ta tsana sukai mata alfarman dawowa da ita gidan samad don albarkacin wanan yar data haifa a haka cikin wani yanayi.
Zuciyar ta ke mata soya tun safe gashi ta hana kowa fita sai da yaran suka damay tane ta tura yanyala gurina ta karbo masu abin karyawa.
Taba yaran sun sha amma har yanzu a takure suke a dakin tagane nufin su so suke ta barsu suje gun waccan yar isakan mayaudariyar yarinyar dija yar gidan malamai.
Waya sani ma ko duk ta asirce har da yaran nata ne bako daya irin wanan kulawa da shakuwa dake son shiga masu don ma tana tsaye a guri daya dasu da abinta tasan zaifi haka.
Madam ta kira a waya tana sheda mata duk yadda akayi tace dama ai malam ya fada muna zai karbe ki idan kin je tace kayya da kinga irin wullakantan danayi a gurin su madam sai kin tausaya min.
Wanan yarinyar na yarda ba a banza ta shigo gidan nan ba ga iya kissa kamar tsohuwar karuwa tasan kan sheri har ta gaji.
Yanzu so nake da komai ya daidai in shege kasar mu kafin yar iska ta haihu in yi waje da ita ta haihu can a gidan su ta dandana bacin ran data sani ciki ita ma taji idan da dadi.
Madam tace injin kin tuna da kai mata wanan yarinyar wurin ta shegiya muga karyan jan yara a jiki idan zata yarda ta mamay ta a haka yadda take.
Don nasan shegiya da wayon tsiya ba karbar yar zatayi ba zata samo wani abinda tace tana mata ta guje ma ganin ta kusa da ita.
Ai ko ta guje tura mata zanyi shegiya sai ta haifi irin ta itama ko wace ta fita idan tace sheri ta iya mu zuba dani da ita a gidan nan baki da dama wallahi nafisa madam tace.
Kofan ya turo tayi saurin kashe waya tana kallon shi yace dawa zaku zuba a gidan nan kina da aiki don ko yanzun kika kara gigin min iskanci ba kyale ki zanyi ba don nagaji da halinki nafisa.
Tace nasan ai ba yin kanka bane duk abinda zaka fada yanzu kana da daman fadi duk abinda kaga dama a kaina yanzu.
Yace ki bi sannu wallahi kin san zaman da kike a gidan nan don haka ki natsu kamar yadda kowa ta natsu don ba fin wata kikayi a gidan nan ba duk abu daya ya kawo ku gidana.
Idan akwai abinda ta tsani ji shine yace duk daya suke da sauran matan shi har da wanan da ta shigo kamar jiya a rayuwan shi dama fati abin banza da bata da wani kira na mata da ake so.
Juyawa yayi wurin su samira yacewa ihisan may takewa kuka samira ne ta bashi amsa da fadin wurin anty take son zuwa Ami ta hanata fita.
Common taso kije don may zaki tsare yarinya haka a daki ki hanata walwala tace don ya tace ita din yace yanzu kin daina fadin tayi zuciya ta haifi nata ne ?
Ya rike hannun Ihisan suka fita a cikin yare ta fadawa samira ta dauki baby takai min ita tare da feeder din ta ta mike dama itama fita take son yi ta sukuci yarinyar suka fito daga dakin.
Muna zaune dasu anty Faiza muna hira ya shigo rike da Ihisan yana fadi gata nan wai zata zo wurin ki uwarta ta hanata.
Fauziya ne tace ikon Allah har yara ma a cikin kishi wanan mace dai Allah mana tsari da irin su wallahi faiza tace ai abinda mutum keyi sai yaga kamar shi kowa ke yi.
Fauziya ta fada maki abinda ta roka maku kun tatauna da ita kuwa wani irin kallo nayi mai ina mamakin shi wani irin mutum ne haka da baya boyon magana kai tsaye yake fadin abinsa.
Kallo na sukayi tare da mayar da kallo a gare shi tana fadin bata fada muna baz yayan mu khadija alheri ne ya samay mu komay ?
Zanyi magana Samira ta shigo dauke da baby a hannun ta tana fadin anty ance in kawo maki ita nan na mika hannu ita fadin mama na Allah sarki na karbi yarinyar.
Nadan dubata tare da nufar anty Fauziya da ita na mika mata yarinyar tana ganin katon kai tace subbahanallahi haka take nace eh abin tausayi ne yarinyar yana tsaye a dakin har lokacin yana ma yar gurin Faiza wasa.
Nace ki duba cikin ta inda akai mata aiki da wurin a bude yake tayi saurin bude cikin yarinyar ta gani ta mayar da sauri don har yanzu akwai wani roba a jikin ta.
Da ta dago kai tana kallon yayan nata dake tsaye tace yaya haka aka haifeta ashe yace wallahi abin akwai tausayi sosai saura suka mike zuwa ganin yarinyar.
Yake cewa su Ikilima dai basu damu da zuwa wurin mutane ba Faiza da ta sauke ajiyan zuciya tace yayan mu kasan su ai da nuna akidar wariya dakin su har yanzu haka muke dasu ba abinda ya canza.
Yaran dakin mommy ne can zaka ga an kawo su suce sun zo ziyara ne kwana bibiyu suna zuwa wallahi yace shiyasa nake so mommy halin matar nan yana min wallahi.
Motsin da yarinyar tayi ne ta miko min ita da sauri yana kallon mu nace barin goya ta ko zata dade tana barcin yace likita ya fada mata haka daga ita har yan uwan nata raggaye ne.
Ina goyan yarinya Binta dake zaune fuskanta wani iri tace ke da cikin ki hakan nan zaki goya wanan yarinya don Allah ki bada ta amaida mata da abinta.
Dariya nayi nace may kike tsoro kada a kara haifo maki haka ko may ai mutum baya kaucewa kadaran shi ko ina yake.
Baiyi magana ba sai dan girgiza kai yayi ya fice daga dakin Faiza tace ai gaskiya ne khadija ko ita sheri yasa tabayar akawo maki don tasan kina da ciki.
Allah dai ya sauwa ka idan mada wani manufa tabada tayi wa kanta ai, ai itama Allah ya bata yar hakana da take kin ta a kusa da ita.
Khadija fada muna abin alherin don Allah don a kage nake tun dazun inji don yace kece zaki fada muna mu baki goron albishir.
Nace ina ganin bana zaku sauke farali ne don sharan dana bashi yace ko gyaran daki ko wanan nace dashi duka dai baidai ban amsa ba har yanzu.
Don mun dade dayin maganan tunda ya tayar da zancen yanzo nasan akwai maganar tafiyan ku ke nan tace ko shi yasa Yusuf ya amshi passphot din mu kwanaki nace shine.
Murna suka fara yi ba basu jima ba sukace gidan hajiyar su zasu tafi nace yau naso shiga mugaisa kuma gashi ban samu fita ba ko da zuwa dare ne zan shiga.
Bayan sun fita ne nayi waya da maryam ina fada mata zancen dawowan Nafisa gidan tai ta kunduma mata ashar nace kai maryam baki da kyau wallahi.
Dakin shi na nufa wanda wanan ne karo na buyu dana taba shiga dakin sai da na tsaya na kare wa dakin kallo tare da mamakin yadda akwai mace a gida dakin miji yake a haka.
Naga kokarin shi da ya iya zama haka a wanan dakin sai dai abinda na kula dashi shine iyaka a dan gyara fadon da za a kwanta akai.
Ga goyon yarinya haka na zage na gyaro ko ina na dakin har ban daki ina yi ina sauraren numfashin yar da ke bayana data take yin shiba wahalce.
Kacar nagama na fito daidai yarinyar ta falka nakai wa uwar itadaga kofa na tsaya ban shiga daga ciki ba na tsaya daga kofa.
Na sallamay sallah ya shigo dakin yana gaida ni da aiki tare da fadin yanzu hajiyan mu ta kirani a waya wai taji abin alherin da ya samu yayan ta sun koma mata da murna.
Yaya ka biya masu din ne na tambaye shi sai da yace nifa ba yayan ki bane nace inawa su Zainab kara ne ai nima nasan ba yayana kake ba yanzu.
Yace yana zama sun tsorata da ganin yar nan ai don naji binta na maki magana nace ita dama ai matsoraciyace .
Yanzu na maida ita nazo in yi sallah ya mike yana fadin ki girka abinci da dan dama don ina ganin su chezer zaso gidan nan don muna da meeting yau.
Nace anty ya kamata ka fadawa don itace mai gidan don ni ba girki nake yi ba yace amma kin san yadda mukayi dake tun Abuja ko.
Sanan idan ma ba kece da girki ba may zai sa in fada mata tunda ba kunya zata iya fitar dani ba nasu banda kayan haushi.
Haba yaya AA kaima fa kana da laifi akan anty gaskiya bai dace kuna haka ba ga yara girma suke suna ganin abinda kuke yi kuma.
Baice dani komai ba sai fitan da yayi daga dakin ganin banda lokaci yasa na mike lokacin kyautan da abokan shi sukai min jiya .
Wardrobe na bude na fito da kudin sai da na ware ido daga inda nake zaune don ganin yawan kudin har zuciyana tana zargin wace irin sana,a sukeyi hakane wai.
Da wanan tunanen a raina na fito zuwa kitchen din wanda banyi tsamanin an dafa wani abu ba a cikin sa da rana laraba tana zaune dan lungun kitchen din kamar marainiya nace mama kun koyi abinci da rana gidan nan tace to shine nake nan ai a cikin damuwa.
Na tambayi hajiya tace wai na tambaye ki aike ce mai mashi girki ba ita ba nace kuma da sauri tace tau haka dai tace min da naje gurin ta dazun.
Allah ya kyauta nace ko wani gauta ja sai dai in bai sha rana ba yadda take so zan bita mu tafi a haka tunda itama alamarin ta ba baya bane.
Aiki muka hau yi gadan gadan sai gashi yafito yana fadin wai ba ai abinci bane da rana ko may ?
Shiru nayi ban tanka mai ba tana zaune a falo yake sake tambaya tace ba,ayi ba don na dauka khadija zatayi ne yace itace mai girki ?
Ita naga tanayi ai da kuka zo OK kawai yace ya kira yara shi suka fice daga gidan Samira ne tazo ta samay ni a kitchen din tana fadin anty yunwa tana taba cikin ta.
Nace bari dafa maki indomie kusan a tare mukai aiki da ita don bata koma dakin su ba again.
Sai yamma lis suka dawo gida da yaran nan suke fadin wurin hajiya mama suka tafi ashe kafin magariba na gama hada masu komai abinci ne tuwon alkama da miyar yauki sai jar miya da na dafa na cow tail ya dafu sosai sai dafa duka da yaji cabeji da kayan hadi nayi amfani da zaukaken nama daban soya ba sai kayan ganishin dana yi a sama.
Bayan nan kuma na hada masu zobo da yaji kayan kamshi da kayan hadin shi dadai sauran tarkace na motsa baki na aje masu sai da na gama jerawa na haye sama na bar gurin bayan na mutanen gidan dana saka daban na nuna ma laraba wanda ke so ya diba.
Ina shigewa Nafisa na fitowa ta nufi abincin zata diba Laraba ta fada mata abindanace tace ita wanan din nasu zasu diba din don nasan sherin da nayi a ciki yasa nace hakan komay ?
Kamar an fada min sai gashi na manta wayana a kitchen na sauko in dauka na samu zata bude mama ihisan kada ki taba wanan din .
Muryana taji daga bayan ya yasa ta juyo tana fadin akan may ba zan debi wanan din ba nace saboda maigidan da bakin shi na girka ba don ke ba.
Tace kin dai san sherin da kikayi a cikin sa don haka sai na diba din sai dai ki mutu idan na diba na karasa wurin ina fadi bazaki diba ba tunda iri dayane da wancan dana aje din .
Kai may ye Nafisa wai kina da hankali kuwa tace sai ka koya min na gaji da wanan rashin hankalin da kake kira min a gidan ka ka wanan yarinyar.
Na kira maki don ko baki da alaman shi da baki tsaya kina wanan abin kunyar da kikeyi a gidan nan ba.
Bar wurin nan yanzu kafin ranki yakai ga baci anty Fati dake tsaye tana sauraro tace ikon Allah a ranta ashe Allah zai gwada min faduwan buzuwanan haka ingani da idona.
Samad an wanke an baka kasha diyar matsafa ta gama dakai ka fita hayacin ka baka cikin hankalin ka baka ganin kowa a gaban ka sai ita yanzu.
Yace ashe kema da don ban ganin kowa a gaba kikewa mutane yadda ranki yaso ke nan to yanzu itace a gaban nawa kamar yadda kika ce din.
Sunyi tsiya sosai dashi duk da haka na dauka bazata debi abincin ba sai gata tana diba abinci ta haye sama dashi tana sababi ita kadai don shi har ya shige ko ya barta a gurin.
Idan dane na tabbatar da sai anyi dayan biyu ko ta kifar da abincin ko kuma ta diba tunda tace shi din dai zata diba din.
Abin duniya ya taru yai mata yawa a rai gashi ganin da tayi muna mu biyu tsaye a falon ya kara tayar mata da hankali sosai wai ace duk biyun nan da Samad suke kai ina ba zai yuyu ba wallahi.
Bakin shi sunzo sai da ya fada ma kowa yana tare da abokan shi a falo sai dai bai leka wufin Nafisa don kofan ta a rufe yake.
Suna tsaka da tataunawa ne sai ganinta yayi gaban su bata damu da duk wanda ke gurin ba bata kuma gaida su ba sai jin ta kira sunan shi gatsal sukayi.
Tace Samad ina son ka sawo min magani yanzu kakuma sayo ma yarinyar nan permpers tare da magani itama don mura take yi.
Yace baki da hankali ne baki gani tare da mutane bane ko baki da hankali ne tace idan na ganka da duniya ne ni may ya damay ni dasu tunda wurin ka nazo.
Nafisa wai baki da hankali ne komay Yusuf dake rubutu ya dakatar yana fadin haka yace kin fi saura yan uwan ki ne da suka natsa kansu a dakunan su komai.
Dayan ya kalle ta yace ai dama tare kuka zo ne ashe yana tambayan AA din da yakai iya wuya da abinda tayi mashi din.
Bai bashi amsa ba sai mikewan da yayi ya nufi hanyar sama tabishi tana maganganu itama bai tsaya ba sai dakin ta.
Tana shigowa yakai hannun zai wanka mata mari ta gwauce mai tace akan dan wanan maganan da naje ma dashi zaka mare ni ?
Baki da hankali ne ko baki ganni da baki bane da ba zaki iya jirana su wuce ba ko sai kin zubar min da kims ta a ko ina zaki ji dadi ?
Daga yau idan ina da baki a gidan nan kada ki kara zuwa inda suke idan bani na bukaci kizo ba ke wata irin mace ce da baki da tunanen abinda ya kamata haka ?
Ai basai kai mun haka ba zan san ka auro diyar matsafa ta canza ma tsari da ai naga ko bakin may baka shayin in fito a gaban su.
Sai yanzu ne zaka tsiro min da wanan dokar naka mara amfani ko haka ta tsara maka yanzu kuma a gidan.
Yace eh haka ta tsara min don ta fiki hankali da tunane abinda ya kamata ne ga addini na ta tsara min hakan.
Wani dariya tayi tace wai abin mamaki bai karewa a duniya haushi yake ji cikin ranshi kamar ya shaketa yake ji a ransa.
Don bakin da ke gidan ne ya juya yafice daga dakin baice mata komai ya zauna gurin su rai bace dashi.
Yana zama dayan yace sai kai mijin buzaye wanan matar taka ashe halinta na nan yadda yake ada bata canza ba har yanzu.
Sai daya yace cool down my friend mun saba da halin irin matan nan na ketare ko salis gashi nan haka yasha wuya da nasa kafin ta yaye shi tayi gaba Allah yasa yana da karfi arziki da yanzu ta gama dashi yanzu kai muke jiwa dan uwa.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Zan iya cewa Alhamdullahi a zaman mu na dan wanan lokacin a kaduna don zaman ya kara haska min hanya sosai a gidan AA na fahinci wasu abubuwa daga halaiyyan mutan gidan daga mijin har matansa da ma yan uwan uwashi.
Yanzu na gama tanadar abinda nake son fahinta daga gare su sai dai wanda ya kara boye halin shi bai fitar a fili na gani ba kan shine ban samu nazarin sa ba.
Na fahinci zaman akwai rikici na son mallakan miji ta ko wani hanya musanman daga wirin buzuwa.
Ida ita kuma fati ta kasa daukan girman ta ne a gidan sabado abuwa kamar biyu zuwa uku dana fahinta.
Na farko akwaita da son jiki don ko kanta bata iya yiwa komai balle danta ko mijin ta amma kuma a hakan take son jin girman ta.
Sai abu na biyu dana fahinta gare ta shine tana da kishi irin na matan da da basu iya boye kishinsu a zuciya sai sun bari abokiyar zama ta fahinci hakan gare su.
Na uku tanada fadar magana kamar wace taci kashi bata tsayawa ta auna magana ga ko waye zata fada mai kai tsaye cikin halin ko in kula yai ma dadi ko kada yayi tadai fadi zuciyar ta.
Ga bason mutane a kusa da ita don zaka iya zama da ita wuri daya idan bataga dama ba taima magana sai ku wuni a hakana da ita atakaice akwai ta da nakasa ga kowa.
Irin matan nan ne da ba,a gane samun su don ko yaushe jiya i yau ce gare su bawani canji tare da ita haka yasa mutane ma basu damu da ita ba sosai don har yau da ake bukin sallah banga wani bako kodaga gidan su yazo.
Ita kuma buzuwa gaba daya har mijin na fahinci ba dadi a tsakanin su burin ta kawai ta ba kowa iko kowa iko a gidan mu koma sai bi sai yarda tayi da kowa.
Ba ta kaunar taga wata ta rabi shi ko magana yayi da wata anjima kadan zakaji su sun rikeci dashi suna jidali kan hakan.
Ga rashin yarda da kowa kowa ta dauke shi mai tsafi idan kayi sallama sai ta tura aga mai ka shigo gidan dashi idan kuma ba gurin ta kazo ba bata taba amsa ba sallama balle su gaisa da mutum.
Kai abindai gashi nan sai gyaran Allah bana mutum ba don haka ne idan nayi sallah nakan roki Allah ya haudani kan su ga baki daya don shine kawai mafita yanzu gare ni.
Tun dana fahinci gaba dayan su suna adawa dani na fara kama kaina ga kowa a gidan.
Yau ma da aka wayi gari haka yasa ban fito ba tun safe ina daki na don Fati ce tayi girki don haka na zauna daki.
Banji motsin kowan su ba haka kuma baisa na fito ba dana gaji da kwanci na gyara daki nayi wanka bayan na shirya na haye gado na jawo waya ina kiran yan uwa na muna gaisawa dasu.
Karshe maryam ce na kira tana min korafin na tafi na barta don su abuja sukayi sallah tace ba inda ta fita tana jin garin ba dadi.
Nace mu kan muna nan don banga ya saka ranan dawowa ba gare mu kamar da abinda yakeyi ne a garin don bai faye zama a gida ba kuma kullun cikin meeting suke.
Jin an turo kofa dakin yasa nakai kallo na ga kofan inda naga shine ya shigo dakin ido na zuba mai har lokacin da ya karaso inda nake kwance din.
Ina kwana na tare shi dashi ya amsa min yana zama tare da fadin lafiya kike kuwa nace lafiya ta kalau may ka gani halan ?
Ajiyan zuciya ya sauke tare da bin dakin da kallo yana fadin naga baki fita bane har yanzu ko yau baku abin karyawa ne a gidan ?
Bani ce da girki ba ai ko ka manta ne na bashi amsa yace ok yana mikewa maryam na gaida kai nace mashi yace a itace ta bugo waya nace eh tana min korafin yaushe zamu dawo na barta can ita kadai.
Yace ba yanzu ba gaskiya don ban gama abinda nakeyi ba a nan kofa sati daya ma bamu kaiba garin nan kike wanan zancen.
Yau Friday idan mun dawo daga mosque ina son zamu fita daku gaba dayan ku zaria zamu tafi mu gaida su.
Allah ya kaimu nace ina kwantawa ya juyo ya kalle ni yana fadin ba zaki tashi ki nemi abinda kikaciwa cikin ki ba kin san fa kina da ulcer ga kuma lalurar ciki a jikin ki yanzu.
Nace ina gudun in fita in jawa kaina wani magana ne kuma nima yunwar na fara ji yanzu yace you see maganan may zaki jawa kan ki don kin nemi abinda zaki ciwa cikin ki.
Common taso mu fita ki girkawa kan ki abinda kike so kici dole na mike na bi bayan shi muka fito babu kowa a falon suna ciki suna barci laraba kawai muka samu rakube a gefen kitchen din tayi tagumi.
Tana ganin mu ta dan zabura tana sauke ajiyan zuciya tare da fadin yau uwar dakina naji gidan shiru dama kece mai fitowa mu dora girki kuma sai naga baki fito ba kema yau.
Ganin shi a bayana ta fara gaida shi ya amsa tare muka shiga kitchen din dashi yana tambaya na abinda zanci nace orth zan dama don jiya da zan kwanta nasha tea idan nasha yau kuma zai damay ni ne.
Sai da yaga na dora ya fice kitchen din laraba ta shigo tana fadin yau har karfe takwas ya gwauta ba wanda ya fito daga cikin ku.
Nace kin san banice da girki ba don ba zan kara dora komai don yaran ta suci ko mijin ta ba ta dawo tana nuna min bacin ranta a kan hakan kuma.
Tace aishi Alhaji ya saba idan da sabo da halin matan shi girki fa ba wai ya damay su bane gidan nan a gurguje na karasa abinda nakeyi na wanke har tukunyar nace ma laraba ta kai min daki tajirani a can kuma.
A dakin na samay ta nace mama ki hada kisha iya yadda kike iyawa ki zauna a nan din har ki gama tace nagode tana murna.
Sai da tagama zubawa naja tire nima na hada nawa nan muka zauna tana sha muna hira har muka shanye zata fita da kayan nace ta dan dakata har yabi cikin ta.
Hira mukayi sosai tana debe min kewa sai gashi ya fito a cikin shirin shi zai fita yana fadin mama kina nan ne tace eh zata mike yace zauna a binki fita zanyi nace ka karya ne yace zan karya a gurin hajiya idan naje can.
Ido na runtse tare da fadin mutum da mata uku kuma bai daina cin abincin mama ba har yanzu yace kun bani ne nace idan zaka sha sai in baka ai don akwashi.
Zama yayi anan ya sha cup daya dana hada mai ya fice sai guraren goma mama ta fito tana fadin bari ta sauka kasa kada abar falon ba kowa.
Fitan ta bata dade ba naji karan bude kofan wani daki a cikin su ashe anty Fatine ta fito yaran sun damay ta suna jin yunwa ta fito ta duba idan an gama sai taga kitchen din ba komai.
Laraba ta kwalawa kira a dan hasale tana tambayan ta ba,a dafa komai bane a gidan ta ce yau hajiya bata sauko ba tun dazun.
Tsuki taja ta kalli Laraba din tana fadin yanzun ya take son muyi ke nan har wanan lokaci ace ba,a karya ba sai dai idan na rana zaku dora gaba daya ke nan .
Laraba tace hajiya yadda kikace haka za,ayi ai ko sai dai gaskiya ban tsammanin zata fito yanzu ba kila tunda takai wanan lokacin bata fito ba.
Ki kirata muji ko may ya hanata fitowa laraba ta nufi daki na lokacin har na kwanta in huta sai gata nace tace mata ba komai kawai ta juya zuwa fadin sakon.
Bayan ta fada mata ne ta bata rai batare da ta fadi komai ba ruwan tea ta dora masu suka karya dashi su kuma sauran part din bansan yadda suka karata ba.
Darana ma wai ta tsaya jirana ko zan fito sai da laraba tazo tambayanta may zata dafa tace ban fito bane tace hajiya ina ganin fa maganan da kikayi ne ya bata mata rai ta daina girkawa yanzun.
Don wanan dan maganan dana fada zatace tayi fushi ko may tace laraba ta su shiga kitchen din jeloup ta hada masu wanda a gurin dahuwa yai half done.
Ya bude zaci ya kasa ranan tasha fada ni dai ina sama ban fito ba har sukaci suka sude abin su ban san ma sunyi ba daga baya ne nake ji.
Karfe biyu mun shirya zuwa Zaria da ya sanar ma kowan mu kusan nice karshen fitowa inda na samu anty Fati da yaran a falo ban san abinda nake jira ba.
Na fito muka fita a tare Laraba da Yanyala kadai muka bari a gidan suna gadin gida Nafisa ce ta kamay a gaban mota inda muda yaran zamu zauna a baya.
Tunda muka hada ido sau daya na kawar da kai sai naji yace da ita bayan ya shiga motar ke ya haka ki koma baya mana wurin yan uwar ki.
Ki bar yaran nan gaba da Yusuf sai da tayi dan jim ta bude kofan motar ta fito maimakon ta shiga sai ta sa kai ta koma cikin gida a hasale.
Na dauka zai bita ne don ko ita haka ta zata sai yace mu shiga mu wuce kawai .
A kofan gidan su Yusuf ya tsaya ya dauke shi muka wuce sai zaria inda muka samu taro sosai a gurin su.
Sai yamma lis ana kiran sallah magariba mu ka shigo garin kaduna duk daurewa nake a yadda nake duk da ba wani tafiya mai nisa bane amma sai da na wahala.
Yana yi daga inda suke gaba shi da Yusuf yana juyowa yana min sannu har Yusuf din anty Fati da muke a guri daya batace min kala ba har muka shigo gida.
Nan kuma muka samu Nafisa ita ma ta hau ta cika dashi wai ya wullakantata a gaban iyalin shi ai da ba haka sukeyi ba a gaban mota take shiga tare dashi sai yanzu ne zai tsuro da wani munafunci ko dole ne sai yaje da Yusuf duk inda zai tafi da iyalin shi.
Already na yi miya kagin mu wuce nabarwa laraba tuwo ta tuka min ta kwashe a leda ta sa a cikin kula har mu dawo.
Mun dawo sallah nayi na fito hakana cikin yanayi na rashin jin dadi jikina na raba takaiwa kowa nasa sai na mai gidan dana shirya mai a falo saman d/table.
Falon kuma laraba ta gyara shi kwal kamar yadda muke gyara namu nacan Abuja sai kamshi ke tashi cikin shi.
Tun da na sauko ban koma sama ba ina zaune tare da shine yana cin abinci ta samay shi da wanan fitinar haka.
Sai data gama maganan ta yace akwai wanda kikafi ne daga cikin su ko may dasu basuyi min korafin rashin shiga gaban mota ba sai ke.
Ko wani abin zaki tsunta a gaban motar udan kin zauna din Yusuf kuma na sha fada maki baki isa ki raba ni da shi ba tun farko a tare kika samay mu ko iyayyena basu ce zasu raba ni da Yusuf ba balle ke.
Tace tunda yasan abinda yai ma ba aikai bazaka gane hakan ba ne yace kamar yadda kema kika san abinda kikai min Allah ya kubutar dani daga sherin ki ko ?
Ni dai ina zaune na harde hannaye saman kirji ina kallon su tare da kada kafana tace ai nasan duk bayin kan ka bane saboda an birkice ma kwakwalwa yanzu.
Ke kika birkita min kowa yace mata a zafafe yana kallon ta tace ai kafi kowa sanin amsan wanan din yace ban sani ba sai kin fada min tace nadai fada ma gobe ni zanyi girki a gidan nan din ku sani.
Yace bazakiyi ba don ba haka aladan mu yake ba sai lokacin nasa baki ga zancen su wanda nasan karfin zancen akaina take yin shi dama.
May zaisa kace bata yi tunda tana iyawa wanan ai dama al,adane kawai ba shari,a ba ko Allah ya kaimu goben nace ina mikewa.
Ko baki ce ba ai gobe zanyi din ne don haka ki kama min bakin ki a gurin nan don baki isheni ba ke ta fadi tana karsawa a hasale.
Maganar ta shafe ni ne yasa na saka baki don wanda bai shafeni ba ai bakiji na sa maku baki a ciki ba ko ?
Lalai wuyan ki ya isa yanka a gidan nan amma na baki dan lokaci kadan indai samad ne inda saniyar gaba tasha ruwa ko na baya intazo anan zata sha.
Ba dai ta kawar da kishin ruwan nata ba ko yadda shanun gaba ta kawar da nata tace sai dai ta kawar a burkutacen ruwa nace ruwa ruwa ne komai daudan shi dai ai ruwa ne don ba za a kira shi da wani suna ba can.
Kai ya fada cikin tsawa tare da fadin ya ishe ku hakana ban son kara jin bakin wani a gurin nan kuma.
Sai da na juya ne na ga ashe har anty Fati tana falon zaune ita ma tana sauraren mu nagama abinda nake na haye sama ita kuma tana zaune suna fafatawa dashi.
Wanka nayi na shirya na nufi part din dole sai da na tsaya gyaran part din don ban iya kwaci a hakan ina gamawa na kwanta ban jira shigowan shi dakin ba.
Har barci ya fara daukana can cikin barcin naji hannun shi saman cikina yana shafa a hankali dan gyara kwanciya nayi na shige a cikin jikin shi.
Yace ya naji jikin ki haka da zafi nace banjin dadin jikina na ne sosai na kwanta kin sha magani ya tambaya nace basai na sha magani ba zai bari.
Ina duban yarda zamu koma abuja a haka dake cikin wanan yanayin ina ga sai dai mubi jirgi daku sauran su biyo mota zaifi zan iya na bashi amsa ba tare da na bude idanuwa na ba.
No bazaki iya ba gaskiya ko bukin zainab bazaki zo ba don wanan wahalan da kikeyi idan kin shiga mota nace mama tace zai bari ai ko.
Bai mun magana ba sai can naji yace ki fada ma Adam gobe ina son ganin shi around ten kan maganan AS Jalingo din.
Da sauri na bude idanuwana na sauke a kan shi ya gyara kwanciya yana dan taba kaina tare da fadin wanan na fada maki ya zama na farko yazama na karshe a gare ki don ba haka nake aikina ba ko wanan ina da dalilin yinsa.
Nace koma may ye dalilin duk da ban sani ba dai na gode tunda na samu abinda na saka ma yaya Adam dashi a rayuwa na nima.
Eh hakan na daga cikin dalili na sai na biyu wanan ne karon ki na farko da kika taba rokona wani abu tun haduwa na dake nasha gwada ki ta hanya da dama kina cinye gwajin ki gare ni.
Sai kuma shi kanshi Adam din da nake son in taimakawa wanan ne dalilin da yasa nace ki masa magana yazo mu gana dashi.
Ya Ahmed fa da naji kayiwa alkawari don tunda naji laraban shi abin ya tsaya mun a raina wallahi wani Ahmed nace na unguwar Dosa da mukaji.
Kai Deedar kina da abin mamaki Ahmed kuma ai na gama da zancen shi tun jiya yazo mun yi magana kwagila na sama mashi wanda zai daga shi idan ya iya tanadi.
Mutum ya cika gida da iyali haka tun yanzu wani tanadi kike tsamanin zai iyawa kan sa nan gaba tunda akan haihuwa yake har gobe.
Nace hmmm nan ma kwana nawa ne zamu cika gidan nan yazamanto ko inda zaka zauna babu yace bissimillah udan zaku iya ai ina da bukatan hakan nima.
Ranan ina Allah Allah gari ya waye in bugama Ya Amina waya ya Adam yazo su gana bai bari na fito sashen nashi da wuri ba sai misalin tara na safe.
Ban san may ya kawo Nafisa falo ba ta zauna anan na samay ta har Yanyala da yaranta kitchen na shiga na hada abin karyawa wa kowa a gidan .
Sai dana gama na shiga nayi wanka na gyara jikina lace na saka duk da akwai ciki a jikina bai hana kayan su karbe ni ba.
Ruwan wanka na shiga na hada mai na fito na gyara dakin yadda ya dace mace idan zata fita girki tayi bata bar ma yar uwa daki don sheri tazo tana gyara rai bace ba.
Kamar yadda ni na samu anayi a gidan abin ba kyau don har unders sai ace an manta dashi sai dai kai idan kazo gyara ka kawar inda ya dace.
Wanan nafisa tafi yi min don ita Anty fati sau daya ta barshi na kawar mata Nafisa kuma dana gane abin nata kissa ne idan ta barshi a gurin idan nagama gyara nake bar mata abinta yanzu.
Gashi dai yau tace zata karbi girki a gidan inda kwanan ta ashirin da wani abu yanzu da haihu tana tasan ma yin arbain ke nan yanzu.
A tare muka fito falon dashi muna jere zuwa falon tun muna akan steps din take bin mu da kallo har zuwa saukowan mu kasan.
Wurin table muka nufa inda sai da ya ja min kujera na zauna shima ya ja ya zauna a guda daga inda take tace idan baka mutu ba dai zaka sha kallo.
Wanan bokan naki yaci biya wanan rawan kan da jiji da kulawan kan ai sai mota za akai biya gurin tsafi.
Gidan mu bama tsafi bama shirka idan dai kince ayar Allah na aiki na yarda da wanan kan don bamu wasa da karanta shi don neman tsari ga shedanu irin ku.
Tsiyan abindai mutum bai taba samun yadda yake so nace kamar yadda ke ma ba zaki kara samun irin na da ba a rayuwan ki har a bada kenan.
Yan kwana ki na deba maki a gidan nan gaba daya idan kin dauka wasa ne sai mu zuba na bude baki zanyi magana ya bugi table din da karfi tare da fadin enough.
Nafisa barnan tun raki bai baci ba ke ma kuma idan kika kara tanka ta haka a gabana kuna wanan shashancin ranki zai matukar baci.
Duk wace ta fasa daukana sukutun takai gidan boka ta raina Allah yanzun ma ku dauke ni ku kai iyakarta ke nan
Mata baki da aiki sai sa ido da jan maganagirkin nan ina ba hakkin ki bane yau kin zo nan kin kashe mu da ido kina ganin zaman ki a nan din zai sa mu fasa abinda zamuyi ne komay , ?
Idan naki yazo kin bukaci ai maki banyi ba shine zakiyi magana ba wanan takanar fadan ba haka na hauka zalla da kike yi ina jiyewa wanan bakin naki watarana.
Shiru nayi ban kara magana ba har ya gama fadan shi ya fara cin abincin shi masa na aika laraba ta sayo shina dan diba naci kwara biyu nasha ruwa don ya isheni.
Daki nakoma na barshi a gurin na kira yaya Amina na fada mata tace gashi ko zai fita barin fada mai wayan na a hannun ta naji tana fada mai sakon.
Ina ji yana hamdalla a wayan tare da zuka min addua har na gaji na kashe wayan sai gashi ya kira layina da kan shi.
Yana tambayana nace eh to ina ganin maganan ne sai dai kuma bashi bane kadai zakuyi sai dai idan kazo zakaji ko may nene daga bakin shi.
Yai min godiya ya kashe wayan na wurga wayan gefe na kwanta ina maijin kunan maganan Nafisa a kaina da tayi min a gaban shi duk da na bata amsa dai.
Amma sai lokacin nake dana sani ban bata amsar dayafi wanan ba zafi yadda itama zataji zafin da naji a ranta.
Amma nasan dai idan itace ko yau ma ba gobe ba karawa zatayi don haka na tanadar mata amsan da zan bata mai zafi daidai da maganan ta din gare ni.
Shigowan shi dakin ina kwance na dago ina kallon shi da fuskana dake nuna damuwa a cikin sa yace kin kira Adam din don ban son ya wuce lokacin dana bashi.
Nace na fada mai yana hanya tafe insha Allahu yace ai mai godiya kafin yazo ba wani matsala yace yana juyawa.
Sai kuma ya sake juyowa lokacin har na mayar da kaina saman filo yace may yasa kike son mayar da kanki daya da Nafisa ne a gidan nan ko yaushe ?
Nace amma kaji ai ita ta fara takala na da zancen ko sai taja mutum idan ya bada amsa kuma yayi laifi a gurin ka.
Tana dauka kowa yadda take yake idan bata daina kirana da diyan matsafa ba ni zan dauki mataki da kaina a gidan nan.
Tunda ta fada daya ta fada biyu taga ba wani mataki dana dauka akan hakan yasa take ci gaba da aibantani yadda take so idan kuma na rama ace ba haka ba.
Sai daya dan kada kai ya murmusa yace ke na kun zama daya yanzu da ita don may ba zaki fita batun ta yadda Fati take fita batun ta ba idan tanayi.
Ban yi magana ba sai runtse idona danayi ina jin kuna a cikin zuciya na naji yana fadin ban son irin wanan fitinar kinji na fada maki gaskiya.
Ido na bude nace ita ma ka fada mata ta daina shiga harkata tunda ban shiga nata ba ni kin shiga kan tunda kin auri mijin ta yace.
Nace ba sai in bar mata mijin ba indai shine zaman lafiyan ku tunda na fito na ganta a wurin nasan tsiya take ji yau a gidan nan.
Yace tunda har kin fahinci hakan mai zai sa ki biye mata ku zama daya da ita kuna saida hali a gaban yara suna kallon ku.
Juyawa nayi na kyale shi naji ya fita daga dakin can ya dan jima da fita wayana yai kara ya Adam ne na dauka yana fada min gashi a kofan gida mu.
Nace to yaya barin fada mai kazo yanzu namike zuwa fada mai dakin shi na samay shi yana duba abu a cikin computer shi jin na shigo ya dab dago yana kallo na nace ya Adam ne yazo yana waje wai yace kice ya shigo mana ki bashi wuri kafin in fito.
Har waje na leka na samay shi zaune a motar shi muka gaisa na fada mai ya shigo tare muka shigo gidan dashi dama kafin in fita na fada masu bako zai shigo falon.
Nan anty fati ta mike kafin in dawo tare da yaran ta sai nafisa muka shigo muka sama zaune lokacin shima yana saukowa ke nan.
Tun bai karaso ba yake fadin bata fada maku akwai bako zai shigo bane batai mai magana ba kuma bata tashi daga inda take zaune ba.
Ya sauko yana fadin baki jini bane tace gani nayi itama ai bata shige ba ko yace you're very stupid Nafisa ina magana kina yi.
Yadda ya hasala yasa ta mike kitchen na koma na hado kayan taron bako na kawo mai tare da dan zama muka kara gaisawa daga nan na shige ciki.
Sai lokacin ya kalli ya Adam yace bissimillah mana ga ruwa nan kasha yayi godiya tare da balle marfin drinks din ya dan tsiyayya yace kai hakkuri fa kasan matsalan mata yadda yake haka muke fama dasu.
Yace a, a ba matsala ko mu masu daya ma wani lokaci ai sai hakkuri su haka Allah yai halin su da karamin tunane.
Tsuki yaja yana fadin wanan nasu yafi na kowa ba a haduwa wuri daya bai jidali ba kowa na jirace da dan uwan shi.
Allah ya sauwaka yace yana gyara zama tare da fadin ta fada min abinda ke nan sai dai da farko zanso inji alakan ku da wanan mutumin dan shiru yaya Adam yayi yana aje cup din da ya kurba drink's a cikin shi.
Can Yace a gaskiya zan iya kiran shi da uban gidana da kuma mijin yar uwata da tarasu shekarun baya auren mu bai dade da ita yar khadija din ba a lokacin.
Ta rasu ta barshi da yaran su guda biyar a tsakanin shi da ita sai daga bayane ya auri wata yar kasar su yanzun haka ita ke gidan zaune dashi da yaran.
Kuma zan iya cewa yanzu dai shine jigon da muke dashi duk da ba yar uwana a gidan yana taimaka min sosai ta fannin aikina don shine ma ya samo min wanan aikin Nepa da nakeyi yanzu.
AA yace madalla na fahinci abinda nake son ji daga gare ka sai dai banji dadin ta yadda ka biyo min ta hanyar ita deedar din ba gaskiya.
Yanzu ai mun zama daya koma may ye zaka iya tunkara na gaba da gaba kai min magana don ni ban faye son abi ta gurin iyalina ba kamar yadda kukai min.
Ba zan boye ma ba ita Deedar ta cancanci in mata alfarma ko wani iri tazo dashi don tsawon zama na da ita bata taba rokona wani abu a duniya na rayuwan ta ba.
Idan na bata ta gode idan kuma ban bata ba koda tana da bukatan wanan abin bazata taba min magana da tana son abin ba.
Ya Adam yace alhamdullahi naji dadi kwarai da ta samu wanan shedan daga gare ta don kusan sai ince haka halin su yake daga ita har yan uwan ta .
Wanan halin ne yasa kaga ban kyashin in mata in ma yan uwanta daidai gwargwadin halina yanzu kuma kaima gashi ka shedi khadija da wanan halin wanda na san tarbiyan da suka samu ne daga iyayyen su haka.
AA Yace to yanzu dai maganan shi AS kamar an gama ne sai dai zan so in zauna dashi muyi magana tsakani na dashi kan fili.
Sai kuma kai naka da nake son ka bar aikin nan in da halin bari in sama ma kwangila wanda zai tallafa maka ka gina kan ka dashi da iyalin ka don nima ina son in rama alherin da kukai min dakai da iyalin ka wanda ban manta dashi ba kuma ina afahari dashi yanzu.
Godiya ya Adam yai mai inda bai tashi ba sai da suka aje lokaci a tsakanin su akan ya samay shi idan ya koma Abuja.
Suka rabu da farinciki da jin dasin juna ya adam ya koma gida yana sheda ma Ya Amina yadda zaman nasu ya kasan ce a tsakanin su

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: A dadafe mukai kwana goma sha daya kwatsam da yamma ya shigo yana fadin gobe jirgin bakwai na safe zamu bi zuwa Abuja.
Da mamaki na kalle shi nace gobe goben nan kuma yaya yace eh halama zaman kd din ya maki dadi haka nace wallahi.
Da dai kun tafi kun barni nan har hutuna ya kare sai in samay ku daga baya don nan din mutum yafi sakewa ga yan uwa kuma kana gani.
Baki da hankali Deedar kina ganin zan wuce in barki garin nan ne komai karfin tafiyan goben ma donki zanyi shi ai don ina son muje asibiti idan mun koma.
Baga asibiti masu kyau anan din ba ku tafi kawai zanje ni da ya Amina na cikin magana mai kamar fada yace tunda Amina ke auren min ke.
Har ya fara tafiya ya juyo yace wai may kike tsunta a garin nan da baki son komawa Abuja naga idan na biye maki garin nan zaki dawo dani baki daya da zama.
Nace a yadda muke full house din nan yana min dadi ne don ba wani zaman part ga mutum yana yadda yaso a cikin gida.
Yace can din wa yahana maki yin hakan nace kaima kasan inda matsala take ai don yanzu muna komawa angayan buzaye ka zasu cika muna gida ne.
Wani kallo yai min baiyi magana ba ya juya ya fita dakatar dashi nayi cikin dan gudu ina fadin yaya sai ya juyo nace don Allah zan shiga wurin ya Amina da cikin gida in masu sallama kada in girshe su kuma.
Ya kalli agogon hannun shi tare da fadin a wanan lokacin zaki fita nace please yace shirya in sauke ki idan kin gama ki kirani in dauko ki kuma.
Nidai na juya da sauri hijjab kawai na zura a kaina na jawo kofan dakina na rufe a falo na samu Nafisa zaune da wanan yar uwar tashi suna kus kus fitowa suka zuba min ido.
Ban tanka su ba na fice ina jin Nafisa na jan tsuki a waje Affan ya tare ni yana fadin anty zan biki nace gidan hajiya zan tafi affan yace eh zanje.
Na kama hannun shi muka nufi wurin mota shi ya dakatar damu da fadin ina kuma zaki dashi haka nace cewa yayi zai bini.
Common shige ciki ya dakawa yaron tsawa ya juya da sauri motar na bude na shiga ya tayar na dan kalle shi nace yaro ne fa kana masu haka basu jin dadin ka ai.
Yace kin sagarta yaran nan idan kin koma zasuji daban nace ba sai in koma dasu ba ko muje da maman su gaba dayan mu.
Da sauri ya juyo yana fuskantana tare da fadin ina nace can Abujan mana ko itama ba gidan mijin ta bane can.
Yace ke baki san komai ba da data dawo nan waya koro ta can ta zauna nan tunda haka taga yafi mata nace ai ba tanata za a bi ba yaran yakamata ka dubawa makomar su.
Yaro fa sai da tarbiyan uba a kusa sai dai idan ya rasa su ne ya dauki maraici hakana.
Kofan gidan ya Amina ya tsayar da mota yace idan kin fito ki kirani nace to na fita ya wuce.
Ina shiga yaran ta suka tare ni da murnan su mun gaisa na shiga dasu ciki tace daga ina haka da yamman nan da cikin ki tsoho nace daga gida zuwa gidan yar uwata mana.
Baki san ba a son mai ciki tana fitar yamma haka ba nace daurowa fitan nawa yayi nazo maki sallama ne na fadi ina zama.
Yaushe zaku koma nace wai fa yanzu yazo yana fadin gobe goben nan da bakwai na safe in Allah ya kaimu.
Shiko may yasa yake hakane nace haka yasaba dashi yanzu shirin da zan maki ina zan samu yinsa da yamma haka nace nidai idan na samu yaji ya wadatar dani kibar ssuran shirin ai ba zamu dade ba zamu dawo bukin zainab don kafin sallah babbane akace bukin.
Wayana yai kara na dauka maryam ne akan layin take fadin wai yaushe zaku dawo ne kin barni nan abubuwa na son cabe min nace kaji ki da wani zance kamar may shirin aure.
Tace don Allah yaushe zaku dawo wallahi ina bukatan ki khadija sosai nace ke gidan mijina fa nake dariya tayi sosai tace ana muna kuri da auren nan muma dai mun kusa bin layin ku ai muhuta gorin auren nan hakana.
Kiyi yau idan kinyi fushi mana tace banyi yau amma zan baki mamaki don sai kin sha mamaki na.
Dariya ta bani nace gobe idan Allah ya kaimu muna nan tafe korafi ya kare ni kina ban mamaki mace da mijin ta kuma a dinga damuwan ta wai ta dawo .
Ko kun hada baki ne da buzuwa wai tace shegiyar tana ina ne wai nace kd mana muna nan tare da ita.
What naji tace wai mijin nan naku wani irin sokon mijine shi maryam mijin nawa ne soko na katse ta tace hannu a kunne na madam kada a yankani .
Yau kuma AA ake shigar ma fada nace ya son ranki yar mata tace daina rage min aji kice KARAMAR BAZAWARA.
Dariya mukayi sosai da ita tace sai dai kinzo don akwai labari gaskiya nace kamar yau ne insha Allahu tara ina dakina da yardan Allah.
Mun gama waya da ita ya Amina ta kalle ni tace aure zatayi ne nace bar ta da shimay ta ba aure zatayi ba so take dai in koma mu shiririce can da ita.
Ina gidan ya Amina anan nayi sallah sai baya magariba na bar gidan nida ya Amina muka shiga cikin gida.
Mun gaida Anty amarya dake farko shigowa sai umma da ke kusa da part din Abba su hajiya mama da mommy sune daga ciki part din su yana kallon juna.
Wurin mommy muka shiga nan take jun zancen tafiyan mu tace waishi babangida wani irin bahagon mutum ne haka bai fadin abu sai a kuraren lokaci.
Ya Amina tace shi nake fada mata yanzu ai wai yaji take so ni kuma ban riga da na aika ba ai mata mai hadin nan.
Mommu tace in don yaji ne akwashi nan gurin a koba na sadiyan shehu ba tace shi take so wai taci shi ranan tace dandanon yai mata.
Mikewa nayi nace barin gaida mama tace yakamata kada taji kin shigo tun dazun baki lekata ba kuma.
Tana zaune tana lazumi na shiga dakin ganin tana lazimi na shige wurin su Binta a kwace na samu zainab gaisawa mukayi dasu Binta tace daga ina haka da daren nan nace gida nazo sallaman ku ne.
What don Allah har zaku koma ke nan nace wallahi haka yace dazun da yamman nan sai lokacin zainab tace yanzu nima yaya ya ke fada min amma yace ku jirgi zaku bi ai nace eh tafiya safe zamuyi shine nazo sallama don goben nasan a gurguje zamu shigo.
Zainab yakama ta fa ki koyi sakewa da mutane hakan wanan shirun baiyi maki a wanan zamanin don ni naga ranan bakina nace na juya ina kallon ta.
Murmushi tayi tace kaji ki da wani zance haka halina fa yake Binta tace tana sin komawa anty fati ne kila nace Allah rabaki da halin anty Fati .
Mutum bai iya maida hatsi sufe kullun jiya ayau ita kodan kiza kizan na fa batayi na mata hajiya mama ce ta bude labulen dakin take fadin.
Khadija kece da daren nan nace eh mama nazo in sallamaku ne yace gobe zamu koma wai tace ikon Allah gobe goben nan kuma nace haka yace mama kuma tafiyan safe zamuyi .
Nace aiko kuna nan har bukin zainab tunda ba nisa nace nima naso haka mama tunda muna hutu ne yanzu amma yace a, a.
Daga inda zainab take tace hajiyan ki tuna mata zancen set din kada ki manta Binta tace mara kunya zancen kayan ma ke ce mai tuni ashe ba a ko bari mu, mu tuna.
Nace kunyawa zata ji kan abinda take so kuma kece dai mara kunya ai da kika sa baki a zancen manya dariya ta kwashe dashi lokacin da taga na dafe baki tace ai kin gama.
Kunyar may zakiji dama in ina fadin kina da baki sai tace wai kazafi nake maki yanzu ai gaki kin gani hajiya da idon ki.
Murnushi hajiya tayi tana fita tace in kin gama ina falo nace to hajiya tana fita na mike Binta tace ina kuma zaki nace wurin hajiya mana ko so kike in zama mai zunubi kuma na fice.
Zama nayi kasa daga gefen ta na fara gaida ita bayan gama gausuwan mu ne tace dama akan kayan zainab ne wanda aka saya tace bata son irin sa .
Nace ta fadawa dan uwan ta wai ita kunya take ji nikuma magana irin haka baya hadamu dashi don zaiga kamar umurni ne nake bashi akan dole.
Shiyasa nake son kuyi magana dashi udan da hali sai ya kara mata wani su zama biyu dana alhaji din dayai mata.
Zanyi magana wayana yai kara na dauka shine a layin yace kina ina baya na dauka nace gani wurin hajiya yace ok ya kashe waya.
Nace mama ina ganin in anyi mai magana ai ba zai ki ba zai canza mata din tunda dai bata son wancan din da akai mata hajiya tace matsalan ai Abban ku yabawa kudin komai a hannun sa.
Sallaman dayayine ya katse mu ya shigo dakin yadda ya samay mu a zaune ya fahinci wani magana muke yace karana takawo ko ?
Yana zama yake fadin haka hajiyatace kai mata wani abin ke nan ko tana kallona nace shawara muke na uwa da yar ta kawai ka tsargu.
Yace ashe nazo daidai sai ai shawaran dani ke nan tunda nazo murmushi hajiya tayi irin na manya da yake baiyana jin dadi a gare su.
Dama kazo a daidai magana muke kan zancen kayan zainab sai gaka yace ina mun gama maganan da Abba ko na bada duk wani abinda za a bukata ta bagaren shi.
Ka gama hajiya tace sai dai ita zainab din take korafin kayan yanzu yace hajiya mu yarinyar nan ta samu wuri korafi kuma kan kayan da Abba yasai mata ko may ?
Nace yaya ba haka ake nufi ba ana magana ne kan abinda ake yayi kasan shi Abba din bawai yasan kan kayan bane yace ke kikasan kan su ke nan ko ?
Ya fadi yana harara na hajiya tace kada kaga laifin yar mutane itama yanzu ta san da zancen kasan hajiya umma zai sata zabo ita kuma kasan sai ta samu riban sai ta zabo mata mai karamin kudi.
Yace kai umma tana nan da halin nan hajiya tace may za a fasa kadai san halin bakina suke son ji kawai akan zancen har alhajin.
Tunda ina yar tane baiba kowa ita yake ba dai tawo masu abinda ransu ke so mu kima kaga namu iya bi.
Yanzun ya kuke son ayi tunda an riga da ansaye din tace shine ka samu muna magana anan yazon shawaran da muke ke nan ai.
Nace ni sai naga a bar wancan din a matsayin na Alhaji sai ka saya mata wani mai kyau a matsayin naka ko na hajiya din.
Hajiya tace a dai barshi a matsayin nasa din zaifi yace idan mun koma sai taje ta duba mata komai acan a bata list din duk wani abinda za a bukata daga can din yana magana yana sa hannu aljihun shi hakan yasa nace mun gode yayan mu ina mikewa.
Hajiya tayi murmshi tace kema dai yayan naki ke nan zama nidai na shige ina masu dariya a can muka zauna ina fada masu yadda mukayi zainab naji ta dungumay ni nace kamata yayi ki shigo mu zagaya dake ina ganin zaifi.
Ban dauki lokaci ba ya gama ganawa da mahaufiyar shi yace in fito mu tafi nayi masu sallama tare da zuwa dakin mommy na yima su anty Amina sallama suma muka tafi.
Duk wani shiri da zanyi nayisa a cikin daren nan mama laraba zata biyo motane zuwa abuja sai da safe na samu anty fati bayan nagama shirya nake cewa anty a gafarce mu idan munyi ba daidai mu zamu tafi ke nan tace yau ne tafiyan nace eh haka yace ai tace dukan ku kenan zaku tafi nace eh Affan najin haka ya mike da sauri yana fadin anty mu fa nace zan dawo in dauke ku ai yanzu zan tafi yin wani abu a can ne in dawo.
Karfe tara kamar yadda nace wa maryam muna cikin garin Abuja har na huta na gyara part dina ba kowa a gidan sai mu kadai.
Don shima muna isowa ya nufi office ya barmu ba kowa a gidan sai mu kadai abinci na girka da zanci don rashin karyawa da banyi ba can.
Ina zaune a falo sai ga Samira ta shigo tana tambaya na abinci nace ta jira ya dahu tana zaune sai ga uwar ta turo kofa tana fadin may samira tazo yi guri na yarinyar tace Ami yunwa nake ji ke kuma baki girka ba nazo gurin anty taban.
Idan ban girka ba ke ba zaki iyaba da zaki zo nan a tsafe min ke nace cikin wani murya mai kaushi ke ya ishe ki ya isa haka idan bakin ki ya kara kirana da matsafiya zaki gane kuren ki a gidan nan.
Da dasuke cin ban tsafe su sai yau ne zan tsafe maki su da sherin ki wanan kalman ya isa hakana daga bakin ki daga taimako zaki dinga aibanta ni haka ke wata irin mace ce da baki da lissafi.
Ke kina ganin budar idon ki a kaina zai razani ko may ko umurni kike ban karya na fada ke ba yar matsafa bane ko may duk tsafin da kuke dake da iyayyen ki a kune yake ai.
Nace kin dauka kowa irin kine jikan mayu masu yawo da maita suna sayarwa kuna yat ga ganye kuna kuma tallan kan ku.
Nafa san komai harda zuwa gidan dakike gun tsohon mijin ki da kika bari a gida sai shekara shekara zagayo shi.
Ni din ta fada a rude nace ke mun san komai fa da na dauka abin naki na wasa ne zaki gane ki dawo hanya amma yanzu nagane baki san ana maki ragowa ba.
Yunwa da kika saba zama cikin sa yasa ko girkin abinci bazaki iyawa yaran ki suci ba sai yawo bin boka da malamai saboda bakin yunwa har dangin kaf kika kwaso zuwa gidan mijin ki don baku gaji kunya ba.
Ina ma akasan shi balle a jishi uwa da uba duk a gidan suki zaune an fada maki ana bara ana karuwa kin dauka ban san yanyala uwar ki ce data haife ki tsohon dake bakin get kuma da kuke kira da Ruwa shine mahaifin ki.
Ban aune ba sai ganin ta nayi a gaba na wai zata doke ni ban san ina da wanan azaman ba a yadda nake jin jikina da nauyi sai ji kake kau kau kau na zuba mata maru biyu masu kyau ta yunkura Allah yaban sa, an ta nan na mata dukan banza a dakin.
Na turata waje ashe har yanzu samira na dakin muryan ta naji tana fadin idan kun gama ki bani abincin anty.
Kitchen na shiga nasamu abinci har ya tsane yana son kuna na zuba mata tafita a falo ta tsaya taci abinta inda uwar na daki tana fama da bugun waya wa miji da su madam.
Samad kazo gida yanzu daga magana matarka ta daga hannun ta mare ni yace what tace kazo tun kan ayi barna a gidan nan don ba yarda zanyi ba.
Ta kasheta kira madam tana fadin a turo mata yan uwanta yanzu gidan don babu lafiya wanan bakar banufan ta na son kashe ni.
A zabure madam da tasa yan uwanta a taso azo gidan sai dai sunzo bakin get masu gadi sun tare su waya madam ta buga mata tace gata fitowa.
Shafin hannu na kwance a kumcin ta magana tayiwa yan sandan kofar gidan suka ba shiga doka ne daga maigidan nan ta shiga dura masu ashar har bakin layin dayan yan sanda ya raka su da bindigan shi.
Abin sai ya taru ya zama mata biyu ga na cikin gida ga kuma namiji ya hana kowa nata shiga gidan .
Ciki ta koma a haukace tana tatara kayan ta wai ita ba zata zauna a kashe ta ba a gidan sai yasan yadda zai yi yau a gidan.
Nikan ina zaune bayan na dan cakula abinci don yunwar da nake ji ya bace min na daina jin shi kuma yanzu ina sauraren zuwan maigidan inji irin hukunci da zai dauka saboda irin haukan da take tana sababi.
Zuwan su laraba da Yanyala da kayan mu ne yasani fitowa waje tun lokacin sai dai na samu suna rikici a bakin get masu gadi sun hana yanyala shiga gidan.
Nace ma security din ya barta tashiga mama da harshe turanci muke magana dashi yace oga yace kada subar wani froriner ya shigo mai gida.
Ga Nafisa a tsaye sai surfa ma zagi take yi masu akan may zasu hana yanyala shiga gida zasu bar Laraba fa shigo.
Nace a cikin hausa ku bari wanan ta shiga don uwar matar oga ne ita ma daga kd take tafe sai yace ok ma tare da sarawa ya bude mata get din.
Tunda na fadi haka nacewa driver ha shiga muna da kayan mu cikin gida na barta a wurin tana masifa.
Saida ya fito ya shiga masu da kayan su ciki suma mun zauna da mama a falo muna fira abincin dana aje mata na dauko mata tana ci muna hira.
Sai four ya shigo gidan kai tsaye dakin shi ya nufa ya watsa ruwa dayake ranan muka dawo ban sawa raina wani yin girki ba duk danice zan karba.
Sai na kyaleta ita tayi don gudun jan wani fitina sai dai mun girka a part din mu don gudun ta taso a gaba.
Part din Nafisa ya fara shiga yanyala ce zaune a falon ta ya gaida ita da dawowa ya nufi cikin dakin inda ya samu yar tana kuka ga uwar a zaune bata kula mata ba.
Wurin yarinyar ya nufa ya dauke ta yana fadin sadiya ya akayine mai ke damun ta ne kin kyale ta tana kuka haka.
Idon ta da ya kade yai ja tace samad yau ina son ka raba muna gida da wanan yarinyar idan ba zaka dauki mataki ga abinda tai mun ba.
Haka kawai zatai min wanan aikin haka na kiraka kuma bakazo baka dauki wani mataki ba a kai sai yanzu ka ga daman shigowa gidan.
Kallon mamaki yake mata yace oh dama so kike da na dawo in shigo gida in rama maki dukan ko may ?
Ke may kike da har ta mare ki baki rama ba sai ni kike son inzo in tare maki fada komay yanzun haka ko ban tambaya ba nasan kece kika fara wanan fitinan.
Kamar kada taji haka daga bakin shi tace shike nan dama na sani ta wanke tabaka kashanye ta kaika gurin matsafan iyayyen ta an tsafe ka.
Ka sani yau ban zama a gidan nan da wanan gajar matar taka mai karfin doki ta illantani a banza tunda ita fadan mahaukata takeyi.
Yace kije duk inda zaki tafi kofa a bude take maki idan ke ba zaki tsaya ki rama ba sai ni ke son in zo in rama maki ko ?
Yana fadin haka ya aje yarinyar zai fita tace kazo ka dauki yar ka nagaji da wahala banza hakana yace ki barta ta mutu dama ba son ta kike yi ba ai.
Ya fita dakin sai samira ne ta shiga ta dauko yarinyar ta kawowa yanyala ita itako har kofa tabishi tana fitina bai juyo gare ta ba yaci gaba da tafiya .
Hiran daddy mukeyi muna dariya sai gashi ya shigo part dina daga unda nake zaune nayi mai sannu da zuwa ya amsa .
Labara na gaidashi yace laraba ku iso lafiya ta hanya tace da godiya Alhaji ya naku hanya da aiki kuma yace Alhamdullahi.
Daga haka bai kara magana ba ya fita nima kuma ban bi bayan shi ba don yadda na ganshi bai walwala yasa ban bishi ba don nasan yasan da batun fadan namu.
Sauraren shi nakeyi inji mai zace min akan zancen sai naga bai min magana ba ya fita har dare bai nemay ni ba nima ban je inda yake ba don ban kara jin duriyan shi ba ma.
Washe gari da safe da ya shigo har lokacin yana cikin tamke fuska gaisawa mukayi ya juya ya fita zuwa maryam yasa na manta da zancen a raina.
Har kwana uku banji yai min magana ba kuma babu wani sakin fuska a gare ni ga gidan ya koma muna tsit kamar ba gidan nashi ba.
Wani lokaci ashe mutum yana da rana ko shigowan da nake ina ganin su a falon ashe wani abune ga Laraba a yan kwanakin tana gyaran gidan sosai yai kyau da wani haske kamar dai ba gidan ba.
Zaman doya da manjan da yake damu ya ishi nafisa da kanta ta nemi shiri don taga haukan bazai fisheta ba dashi.
Na idar da sallah na fito falo na zauna wayana dake gefe yai kara na duba shine a layin na dauka da sallama ciki ciki yace ba tare da ya karba sallaman ba.
Bazaki kawo min abinci bane ko may nace dashi ban san ka shigo bane ya kashe wayan sai da na dan dauki lokaci namike na shiga kitchen na hada abincin shi na fita.
Bai gurin cin abincin bayan na jera ne na shiga dakin yana zaune nace na hada abincin gani tafe yace ba tare daya dago kan shi ba gare ni.
Komawa nayi saman kujeran dininng din ina jiran fitowan shi sai can ya fito har ya zauna bai yi magana ba na zuba na juya zan wuce yace ina zaki na dawo na zauna.
Abincin ya fara ci ba tare da ya kula dani a wurin ba sai da ya kusa karewa yace may ya hadaki da nafisa har yakai kuka hada jikin ku a wanan yanayin da kike ?
Shiru nayi ban bashi amsa ba ya dago yace ba tambayan ki nake nake yi bane nace ban san amsar da zan baka ba yanzu don ban san may ta fada ma ba kake fushi dani.
A hasale ya aje cibin yace ashe kin san ina fushi dake ke nan ko dana dauka kina da hankali ashe ban sani ba duk kanwar jace halin ku daya ga baki dayan ku.
Kina a wanan irin yanayin har zaki tsaya irin wanan fada kuna tijara wa junan ku nace dama nasan laifina zaka gani kan wanan maganan.
Fadan ku bai damay ni ba sai cikin dake jikin ki idan ke baki san zafin kan ki ba nina sani don idan har wani abu ya samay ki ni zaku daukowa magana.
Baki da hankali ne ko halin Nafisa ne ya zama maki bako kuma nace har part dina fa tabi ni zata dake ni bayan zagin da take min kuma.
Ta dake ki mana idan tayi hauka ne ta dake ki din idan rashin hankalin ta ya kai can tunda ita bata dake ki ba aike kin dake ta din.
Najirane inji kin ce wani gurin naki yana maki ciwo na shirya abin da zan maki kan haka sai Allah ya taimake ki banji kin min korafin komai ba.
Ranan dai naga bacin ranshi sosai a gare ni don yai min fadan da bai taba yi ba a gidan har sai da nayi kuka a wurin.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Laraba mace mai kwazo da sanin ya kamata ga kawar da kai ga abin mutum ga aiki a tsakani da Allah idan nace wani halinta wanda bai mun ba nayi karya illa da farko dana fara ja baya da ita.
Don yawan complain din Fati da takan mun don idan ta dauko zancen Fati shiru nakanyi in nuna mata banson zance.
Amma yanzu da muka dauki dan lokaci tare da ita saina fahinci wasu abubuwa a gamay da halinta, na farko dai tana korafinn akan zaman su da Fati.
Sai na biyu tana son ja na da maganan da ya shafi cikin family house din su AA sai daga baya na fahinci abida yasa take hakan.
Yau na fito da niyar zuwa gidan su maryam mu gaida anty hauwa dani da mama laraba zamu fita budan part din mu naci kararo da su Samiha sun dawo gidan.
Madam ta gargadoso don bazata iya ba sun isheta a gida shine mafarin ladabin shegun da Nafisa take ma AA akan yayi hakkuri idan anyi sunan yarta tayi arbain zata gida ta wuce dasu.
Ya amince mata da su dawo su zauna a gidan kafin lokacin data ce din dan hakan akace tsakanin mata da miji sai Allah don haka ta san kan abinta bata samu matsala wurin jawo hankalin shi ba.
A raina na hade mamakin ganin su zaune a falon har falon ya fara komawa yadda yake da da tarkace da shara komai akaci anan za a aje falon.
Ko kallon gefen su bamuyi ba muka fice daga gidan driver yana waje yana jiran mu ya kaimu unguwa.
Sai da motar ta fara tafiya laraba tace abin mamaki bai karewa a duniya mutanen nan dawowa sukayi kuma gidan nan again.
Murmushi na dan sake tare da fadin sun dawo mana mama tunda gasu nan har mazan su a gidan tace ikon Allah sai dai kuma ina ganin shigan dare sukai ma gidan don kafin mu kwanta ban gansu gidan nan ba danazo kwaso kayan da security sukaci abinci.
Dama haka suke kamar bakin sheri basu sauka gari da rana sai a cikin dare a wayi garin dasu ba mai cewa ya san saukan buzu a gari sai dai ka wayi gari ka gane shi.
Nace mama kin san su basu yarda da kan su ba balle wani don haka komai nasu a cikin munafunci sukeyin sa .
Munje gidan anty hauwa a can muka wuni gidan mun sha hira sai yamma lis muka dawo gida ba mu girka komai ba don mun ciko ciki a can gidan da muka fito.
Kamar gidan buki haka naga gidan ya koma min ga hasken kwayakwayan wuta ya haska falon sai hiran su ke tashi wasu kuma na waka har da tafin hannayen su.
Wani iri naji tankar a kaina suke wanan hayaniyar duk da naji kewan rashin su amma yanzu sai na tsunci kaina ina bakin ciki sake ganin su a gidan da nayi zamu zauna dasu kuma.
Bamu karasa shiga part din ba naji sun sake wani irin dariya har da guda irin shigen na matan larabawa.
Tirkashi nace raina ya baci sosai don nasan dani suke haka na daure ido rufe na bude part din muka shiga muryan laraba naji tana fadin oho wanan masifafun sin dawo ke nan kuma.
Ban iya bata amsa ba kai tsaye bed room na shiga na rage kayan dake jikina zuwa dogon riga na daura dankwalin shi a kaina na dawo falon na samu laraba.
Nace mama ko a dan dafa maki wani abu ne ki dora akai kada ki kwana da yunwa tace kai yan nan wanan koshi da nayi haka sai dai gobe idan Allah ya kai mu dai ko ?
Nace bari dai mu dora da dan ruwan tea a kai don kwanan nan mama sai dare yayi wani masifan yunwa yake damuna sosai.
Sai da tayi dariya tace yar nan banda abinki yunwa ai yana maki da sauki na gani mace mai ciki da ake so taci ta koshi amma ke har yanzu cakulan abinci naga kinayi.
Haba mama aiko yanzu ina ci da yawa fa a kwanakin nan har mamnakin kaina nake yi irin wana cin tace a hakan shine ci kada fa ki haifo min miji ko kishiya a ramay nace mama kishiyar dai don ku ji dadin kishi dakyau irin na gidan nan.
Laraba tace kedai bari yar nan ai har na sallamay sallah ina mamakin wana abin ke dai da gani kin san ba banza bane wanan abin haka.
Ace wai yadda aka rabu baram baram din nan wai Alhaji ya iya dawo da mutanen nan gidan nan haka kai da gani kasan ba abin kai sake bane wanan wanan.
Kai mama kai sake kuwa ya dawo da ita kin san bai iya saba mata a hakan yadda yake tsoron alamarin ta aiko hajiyan su baya shaku haka nan.
Tace yar na yanzu ma cikin abi yayi sauki ke nan ai idan dane ai bai isa yai mata hakan ba ma gaskiya kowa na ganin kokarin ki sosai da kike iya fuskantar matsalan wanan matar a zauna lafiya.
Ko can sai da hajiya Fati tai magana ranan ganin kun fita da shi tana zaune bata iya cewa komai ba a kai.
Nace mama ai abin nasa ne sai kaga kamar ya kubuta daga kaidin ta kwana buyu kuma sai kiga ya kara dulmiyewa a ciki sosai.
Ai bata barshi haka ba kullun irin su a cikin tushi aikin su suke yi suyi nan suyi can ko yaushe a cikin kauce hanya ake don dai kawai aga an kuntata ma abokiyar zama ta muzanta a gurin miji.
Aike bata samu yadda take so a kanki ba har yanzu nace Allah kuma ba zai taba bata sa, a akaina ba har ta mutu.
Shiru nayi ina tunane a raina yanzun haka zamuyi ta rayuwa a cikin wa yan nan mutane kai ke nan ba wani rayuwan jin dadi dakai da miji gaskiya nikan da ake cewa wai ka gani ka daure ba zan iya cin fuskan Nafisa ba wani lokacin har da miji.
Juyowa nayi nace mama ina ganin bread din nan tun na jiya ne ba zan iya cin sa ba gaskiya ko zamu fita in samu wani na aike sa ya sawo muna.
Tace bari dai ni in leka idan masu gadin nan su nanan sai in basu su sayo muna ko na mike na shiga na fito mata da kudin bread din.
Shiru shiru zanga laraba ban ganta ba gashi kuma ba wayane da ita ba dole na fito zuwa duba ta na samun har an datse get din gidan ta baya.
Karasawa nayi gurin get din ina tambaya buzanyen waya rufe get din gidan daga ciki ne karfe takwas da wani abu.
Don security din bakin get di basu nan su ma ina ta mamaki a raina babu wanda ya tanka min nasa hannu na bude get din .
Laraba da security din nan biyu ne a waje ina bude kofan motar shi na isowa gurin da mamaki ya shigo yana kallon mu ko kallon inda yake ban tsaya yi ba.
Na ba security din hakkuri muka shige da mama a ciki ina shiga ban tsaya jiran komai ba na jawo akwatuna na nafara hada kaya na da suke nawa sai da na shake akwatunana kaf ina jan zip ya shigo dakin .
Kallon akatunan dana dora a saman godo yake yi ya dago ya kalle ni tare da fadin wanan kayan fa na may ye kuma.
Ban bashi amsa ba na nufi gurin wardrobe na bude na tono handbag dina da nake dasu na fara saka kayan shafe na a ciki yana tsaye yana kallo na.
Yace bake nake tambaya ba ina zaki haka kike hada kaya saida na gama na sauke akwatunan kasa na dauki hijjab dina yace ina kike nufin zuwa bada izinina ba sai lokaci na dago nace gidan ubana zan tafi yau insha Allahu komai dare kuwa.
Murmushi yayi yace a wanan lokacin kin ko san karfe nawa muke yanzu da kike wanan haukan wai ma da izinin wa zaki tafiyan.
Wani kallo da ban taba mai ba cikin bacin rai nace izini izini zan nema a gurin wa gurin mutumin da aka hada kai dashi aga bayana zan nemi izini ko may ?
Cikin mamaki yace aka hada kai dani aga bayan ki akan may nace koma may ye ku kuka sani na fara jan jakkan zuwa falo rike ni yayi daga baya yace zaki bar wanan haukan da kikeyi kosai ranki ya baci.
Ki tsaha ki min magana yadda zan fahinta rashin kunya ya hanaki tsaya kina ganin wanan ne mafita ga komay nene kike shirin yi din.
Yanzu akan idon ka Allah ya nuna maka abinda sukai muna ni zaman su a nan tare daku bai damay ni ba kuma ba zai taba damu na ba din.
Lafiya ta da na boyar Allah dake zama don ni a gidan nan najawa nagaji wallahi nagaji da irin wanan zaman gara na tafi inda ake sona da kaunana ida kansan zafi na yafi min.
Malalacin Murmushi ya sake tare da fadin akan dawowan mutanen nan kike wanan haukan ashe idona ya ciko da hawaye nace dawowan su gidan nan bai tare min komai ba don a tare na samay ka dasu.
Lafiya ta na jawa don gaba ban san irin abinda zasu iya min ba ina cikin wanan hali gara na koma ida aka san zafi na da ciwo yafi mun sauke.
Kallon yadda nake zubar da hawaye yayi sai naga ya fita zuwa falon yace mama wani abu ya faru ne bayana.
Laraba dake zaune tayi tagumi a takure guri daya tace Alhaji mutanen nan dai ne da suka dawo sin saka mu a gaba da dariya yanzun kuma na fita zuwa sayo mata bread ina ba masu gadi sako suka rufe mu ta baya.
Yace rufewa fa yana fadin haka na fito ya kalle ni baice komai ba ya nufi kofan fita daga part din har ya fita ya dawo ya cire key di dake lake a jikin kofan ya rufe mu ta baya ya wuce.
Zama nayi a gurin ban iya magana ba sai kukan da nakeyi part din nafisa ya nufa suka hade da ita tana fitowa.
Nafisa wa yarufe kofan gidan nan da mama laraba a waje sai da taimai wani kallo tace nice nace su rufe don ko bazan yarda ana fita a wanan lokacin ba tana kebewa da wasu maza a dauka yan uwana ne dake gidan suke haka ?
Nafisa kin san yarda muke da laraba kuwa tace ko ya kuke ai aiki take a gidan nan kuma a karkashin ka take.
Kallon mamaki yake mata don yadda take maganan sai dai yana jin ba zai iya mata masifan daya shiryo yai mata ba suna hada ido yaji wani irin abu a tare dashi ya soki zuciyar shi.
Wanda yazo da fada sai gashi yana maganan lumana haba wanan ai kin san bai dace ba kamar laraba ce za ace ta fita yin zance a waje ko may ?
Samad kaga idan matar ka ta turo kane kai min cin mutunci in sani don bazaka zo nan ka tsare ni ba kana fada min wanan magana.
Zuwa tayi gidan nan ta samay mu bata isa ta ce zata juya kowa yadda take so ba dokane na bayar ko itace ta fita wanan lokacin zance a rufe gidan nan ne.
Ta fada tana wuce shi ya bita da kallo sai yaji bai iya musa mata da komai a lokacin suko yan uwanta sunyi tsit suna sauraron su.
Yaja kafan shi ya bar gurin zuwa part din shi bai iya aiwatar da komai ba don kwarjin da Nafisa tai mashi.
Yusuf na kira ina kuka ina fada mashi yai mashi magana ya bude muna kofa don ya rufe ni ta baya .
Hankali tashe Yusuf yake tambayana abinda ke faruwa nace Yusuf nagaji da auren mijin wata wallahi bazan iya zama a gidan nan ba gaskiya.
Yace yi hakkuri gani nan zuwa yanzu don Allah kanwata kada ki fita a cikin daren nan kin san halin da kike ciki fa yanzu.
Hali ba zai hanani kwatar inci na ba nagaji ne sai kaga abu kamar yai sauke gare ka sai kuma a bulo da wani abin ban iyawa wallahi yace zaki iya insha Allahu khadija ki kara daurewa dai please.
Maryam na kira muna gama waya nace tazo ta dauke ni jin ina kuka yasa taba anty waya tana tambayana ban boye mats komai ba abinda ke faruwa.
Tace wai shi wani irin mutum ne da bazai iya tashi tsaye ba akan gidan shi yanzu kiyi hakkuri khadija dare ya riga da yayi sosai .
Ki bari gobe idan Allah ya kaimu zamu shigo mu samay shi dole ne yasan tsarin da zaiwa gidan shi duk abinda take ji kowa ya iya sa ai.
Da kyar ta samu ta lalashe ni na bar kukan da nakeyi din taita bani magana akan inyi hakkuri in bari har suzo.
Yusuf ne ya iso gidan tun waje ya fara mamakin ganin buzayen sun dawo gidan don bai fada mai cewa sun dawo din ba sai da yazo ya gansu.
Nan ya fahinci inda matsalan take ciki ya shiga ya samu matan sai raha suke a tsakanin su bai tanka su ba ya nufi part din mai gidan kai tsaye.
Muryan Nafisa ne daga inda take zaune take fadin kai waye da zaka shigo min gida haka kai tsaye ka wuce sashen maigidan baka nemi iso ba.
Ya juyo da zuman ya fada mata bakar magana wani iri yaji a ransa da sauki ya ambato Lah, illah,ha illah muhammadan rasullilah sau uku yaji wasai a ranshi yace ke baki isa ba wallahi kuma sherin ki yayi kadan a kaina.
Yana fadin haka ya wuce part din azaune falon sama inda ya ke zama ya huta ko yaci abinci ya samay shi zaune.
Lafiya na ganka a wanan lokacin Yusuf yace ba dole in taso ba kanwa ta takirani hankali a tashe zata bar gidan ka.
Sai yanzu danazo kuma na fahinci abinda yake faruwa a gidan AA yaushe ka dawo da mutanen na gidan nan baka sanar dani ba.
Yusuf ashe abinda ake fadi gaskiya ne kakai kanka inda ka wuce iyakar ka matsalan na nida iyalina harshi dole sai ka sani ko may ?
Kallon mamaki Yusuf yake mashi yace gaskiyane na wuce iyakana a gare ka amma kayi hakkuri nayi kuskuren yin hakan.
In Allah ya yarda kuma hakan ba zai kara faruwa ba don nima na sani matsalan iyalin ka baidace in shiga ba.
Amma ka sani matsalan wanda ya shafi khadija ya zama dole in saka baki a cikin shi don matsalanta a gidan nan ya shafeni.
Yusuf ya fadi a kakausar harshe yace ban min gidana tun muna sheda juna dani dakai a gurin nan matsalan Deedar ya isheni nima.
Tunda na aureta ban zauna lafiya da matana ba kullun a cikin jidali muke a gidan nan ba wani kwanciyar hankali dana samu a cikin gidan nan.
Yace naji wanan kuma kai kajawa kan ka haka tunda baka iya tsayawa kayi adalci a gidan ka ka bar mace ta shige maka a gaba kan komai.
Ni ba zaka fada min wai khadija ta shigo ka rasa kwanciyar hankali a gidan ka ba don nafi kowa sanin gudun mawar da shigowan ta gidan nan ya baka.
Tun kan khadija ta shigo gida ka baku da kwanciyar hankali da matar ka haka ta shigo ta samay ku da tarin matsalan ku a gidan nan.
Yusuf ka tafi ka barni a yadda nake jin din nan idan ma zaka tafi da ita ne ga key can ka dauka ka kwashe ta ku tafi duk inda zaka kaita da daren nan sai kun dawo.
Inda ya nuna mashi key din ya dauka ya fice baiko kalle shi ba ya ja tsuki a kofan suka hade da Nafisa tana shigowa tace mu zuba dani dakai agani.
Yace ko mun zuba indai ni Yusuf ne baki kwashe komai wallahi don nafi karfin tsafin ki ko wani shirka daga inda AA yake zaune yace Yusuf ka fice min a gida nace maka.
Yusuf ya fice bai ce mai komai ba part dina ya nufa ya bude muna falo ba wanda ke magana a cikin mu inajin an bude kofan na mike a zatona shine ya shigo.
Sai naga Yusuf na zauna naji wasu hawaye suna zubo min na takaici da kunan rai yace khadija yi hakkuri ba sai kin fada min komai ba na fahinci duk abinda ke faruwa a gidan nan ko.
Daga wurin shi nake yanzu wanan shu,umar matar ta riga da ta asirice shi da sihirin ta yanzu maganar ta wuce yadda ma kike zato ga AA din.
Kuma dan dawowan nan da kukayi ne komai ya faru ina kuka nace ni ba zan zauna ba yayana dama can zaman hakkuri nake don ba sona yake ba har ga Allah.
Yace ki bar fadin haka khadija don so wallahi ni nasan AA yana son ki fin karfin shi da asiri ne kawai akayi yanzu kuma insha Allahu zamu kwatoshi daga halakan ta.
Sai dai abinda nake so dake yanzu don Allah ki jaye wanan maganan ficewa daga gidan nan da kike fadi idan kinyi haka kamar kin nunawa Nafisa nasaran ta a fili ne.
Kin ga kina dauke da tsohon ciki haka tare dake sai taji dadi dama nasan akan abinda akai wanan aikin ke nan yadda yai masu din nan nasan ba zasu kyale shi ba nasani .
AA mutum ne dake da yawan sakaci yasan halin matar shi amma shi bai damu da neman kubuta daga sherin ta ba zan kira hajiyan su yanzu insanar da ita abindake faru ta kara baki hakkuri takuma dage gurin yi masa addua itama don yadda na fahinci abin aikin gagawa aikai masa.
Nan kafin in magana ya fara neman layin hajiyan ta dauka suka gaisa bai boye mata komai ba ya sheda mata harda abinda ya faru yanzu a tsakanin su.
Hajiya sai innalillahi take maimaitawa yace ga khadijan hajiya kuyi magana tace kana gidan ke nan yace eh don ban fita ba ina gurin ita khadijan yanzu haka.
Miko min wayan yayi bayan tace ya bata hakkuri ta shiga bani ba abinda nake sai kuka sai fadin take don Allah in rufa mata asiri kada inje ko ina zasu san abinda sukayi tace in ba yusuf din wayan don kuka da yaci karfina na bashi ban san may tace mai ba naji yana fadin in Allah ya yarda hajiya zan shigo din.
Sai kuma ya mikawa laraba wayan ta karba itama sai fadin take insha Allahu hajiya ina tare da ita ko wani lokaci zan bata hakkuri in Allah ya yarda.
Ya dai dan kara min nasiha da nuna min kuskuren tafiyan da nake son yi din tare da ban shawaran in kara dagewa wurin mika lamarina a gurin Allah.
Karshe dai yai muna sallama ya fita muka rufe kofan part din nan laraba itama ta shiga bani baki tana lurar dani illan da fitar mace gidan mijin ta ke jawo mata a gurin kishi.
Da barin ta fahinci halin da muke ciki kamar nuna mata samun nasaranta ne a kaina kukan ma da nake ya daina zo min sai tunanen maganan da Yusuf ya fada ma hajiya sunyi a kaina nakeyi.
Ranan sai dai barci barawo ne ya sace ni ban dade ba na falka gajikin ba dadi abu gamai ciki haka na daure na gabatar da nafila na dade zaune ina mika kuka na a wurin Allah da fatan ya sauke ni lafiya.
Washe gari tunda na tashi nayi sallah na gaida laraba na koma na kwanta ban fito dakin ba barci da ya soma dauka na laraba ta shigo tana fada min ina da baki a falo.
Nafito na samu anty Hauwa da wata kawar tane da nake gani tare da ita ko yaushe ina fitowa tace khadija badai kuka kika tsaya yi akan wanan kishiryar taki ba.
Dayan matan tace ai kuka baima irin matan nan ki dake ki nuna mata duniyan ci in kin yi kuka har ta gane ai abinda take son gani ke nan dama daga gare ki.
Duk namijin da kikaga ya zauna da mace so ne yasa ya kawo ta gidan shi kinga zomu zauna zo mu saba idan ita tana asiri ke kuma ki nuna mata karfin Allah a kan ki.
Anty Hauwa tace bamun zo nan bane don mu hadaki da mijin ki muyi magana yin hakan yanzu gare mu kamar tonuwar asirin ki ne tsakanin ki dashi a gareta.
Shawara mukazo mu baki babu inda zaki kinji na gaya maki a gidan nan dai da bata son ganin ki zaki zauna ki haihu lafiya lau a dakin ki.
Idan kinji na kuda daure ki kirani ko ban gari akwai matar da zan turo tazo nan gida ta karbi haihuwan ki haihuwar ki a cikin gidan nan shi zai kawo nasaran cin galaban ki a gurin wanan matar.
Don matane basu gane ba sun dauka zuwa asibiti a haihu wani abin adone yanzu haihu yanzu ga saporters nan suna zuwa har gida su karbi haihuwa jinin nan da zaki zubar a cikin gidan nan shi zai karya duk wani asirin da ta binne a gidan nan.
Sai abu ya gagara ne ya kama aje asibiti da mata sun sani irin haka ko sau daya ne da sun daure sun haihu a dakunan su don samun sauki a rayuwan su.
Sun min magana mai tsawo wanda har naji na fahinta da zancen su nayi masu godiya anty hauwa ta mike tana fadin mu zamu tafi dama na zo ne don nayi maki alkawarin zuwa yau din.
Matar tace zauna ki gyagije adakin ki kamar ba ayi ba kuma kada ki biyewa ciki ki zama raguwa a gurin miji.
Ki nuna masa dashi da ita basu isheki ba ki fuskanci rayuwan dake gaban ki da kanshi zai dawo ya koma kunyar ki a gidan nan zaki ce na fada maki watarana.
Gani da komai da namiji ke so a gurin mace gyagije ki koya mata hillan mu na mata ki nuna mata ke ma kin iya fa.
Muka fito muna dariya suna zaune da su madam suna kwasan kanu labarai a gurin nafisa sai gamu mun fito madam tunda ta kyala ido taga anty Hauwa tasha jinin jikin ta muna fita daga falon tace.
Nafisa may ya kawo hauwa black din JJ gurin wanan yarinyar kuma Nafisa tace waye ita din sai da ta kalli kofan da muka bi tace ashe akwai shegiyar kuwa.
Indai wanan yarinyar da Hauwan JJ take hurda a garin nan idan baki mike tsaye da kyau ba watarana sunan ki sorry a gidan nan.
Nafisa ta dafe kirji tace kin barni a duhu sai zuba kike yi haka tace itace fa hajiya sabuwa ranan take bamu labarin ta wurin hatsabin banci ga kudi amma ba wanda ya isa ya rabi mijin ta yanzu har gida zata ci mashi mutunci.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Na dawo daga raka su anty a yadda na samay su falon ya nuna min suna wani magana mai muhinmanci ne.
Har na dan shige naji muryan Nafisa tana fadin ba wata hauwa zaki jira ba ko uwar hauwa ce bani shayin ta kamar in wuce sai na dawo baya.
Ke karamar shu,uma kin tsargune da ganin anty hauwa gidan nan gida kan dole ta shigo cikin sa tunda yar uwarta na cikin sa.
Ba a hana guzamay irin wa yan nan shigowa ba na nuna su madam da yan uwanta nace sai matan kirki irin su anty hauwa za a hana .
Ai in kin ga bakina sun daina shiga gidan nan tabbatar da nice bani gidan nan barin gidan nan kuma gare ku tankar hasaran ku ne kuma don a tare zamu fita daku.
Karya kike wallahi ai wanda ya riga kwana ya riga ka tashi na cabe da fadin ke nan zaki rigani fita kenan ko ?
Tunda kin rigani shiga ke mai gayyan tsiya ba ai magana ba sai ni dana tarkato baki alheri zaki magana.
Bakina yan yar arzikine irin alheri ko ruwan gidan AA bai ishesu kallo ba balle abinci gidan shi wanan sai yan yunwa irin ku masu gayar har dangin su da abikan bushasha a zo ataya su cin arziki banza ta fadi.
Ke yarinya kada kice zaki fada min magana inji madam to uwata kin tsargune ko kin sha ruwan gidan nan ne ke ma ?
Na wuce ina dariyan ke ta nan nafisa da yan uwanta suka shiga magana ina jin su ban tsaya bin ta kansu ba na shige part dina.
Ina shiga ban tsaya falo ba daki na shige na dauro alwala na fito na fara sallah nakai wani lokaci ina sallatus tasbihi ga ubangijina na gama na bude kur,anina na shiga tulawa a gurin.
Sai sha biyu da wani abu na daga wurin falo na shiga na samu laraba zaune tana kallo zama nayi ina fadin mama yunwa nake ji ban karya ba yau.
Tace na gama abinci naga kina son dafa duka mai ganye shina dafa muna uwar dakina naji dadin ganin ki haka kin maida komai ba komai ba yanzu ki barsu da halin su.
Allah bai barci bai gyangyadi yana kallon kowa da halin sa ne mai hakkuri shike da riba wata rana ai ta mike ta zubo min abincin ba laifi naji dadin abinvin sosai.
Nafisa ta kalli madam bata damu da wa yanda ke falon ba a lokacin tace ni na rasa jinin wanan shigiyar ko wani irine madam.
Jifa abinda arnen bokan na ya fada shekaran jiya nashikan naga fa,idar shi sosai don jiya sun kwasa da Yusuf amma wanan kamar abin bai haukan ta ba ita.
Madam tace irin su shegu basu shigowa ai sai sun shirya ba a banza suke shigowa duniya ba ki dai bi a sannu har ta haihu kinji boka yace sai ta haihu zata hudu .
Samira dake zaune tana ma baby wasa ta dan dago ta kalle su sai kuma taci gaba da yin wasa da hannun yarinyar.
Na idar da sallah a zahar ina zaune sai ga Samira da ihisan a dakin sun samay ni falo ihisan tace abinci anty.
Nace maman ki zatai fada ida kinci abinci nan Samira tace anan zamuci ban son abincin part din mu ba dadi kamar naki.
Laraba nace ra dibo masu sun zauna sun fara ci Samira tace anty haihuwan baby zakiyi irin na Ami din mu nace wa ya fada maki.
Tace Amin mu da madam naji suna magana dazun wai sai kin haihu zasu huda ki su huda baby anty kada ki haifi irin baby Ami don Allah.
Ami bata son baby nan nata tayi ta dukanta tana zagi wai jinin ki nada karfi ba a iya hudaki yanzu inji madam ta dago tana tambayana.
Eh Samira sai na haihu tare da Amin din ku za, a hudamu idan na haihu amma itace zataji ciwo ai idan an huda mu din fuska ta bata.
Tace shiyasa sukace ke boka yace baki huduwa da sauki sai Abbi din don shi tun shekarajiya an huda shi.
Duk da gabana yana faduwa da zance yarinyar amma sai na biyewa shirmay ta ina fahintar wani abu hartace wai a filon Abbi ansaka mai abu shiyasa ya hudu da sauri.
Shigowan maryam ya katse muna hiran yaran da muke sauraran abi boye daga shirmay su na fahinci iyayyan suna hira ne a gaban su.
Maryam ta bisu da harara nace ya haka kuma ta zauna tana aje jakka da gyalenta a gefe suna gamawa suka mike anan suka bar kayan da sukaci abincin suka fice.
Shegu suma sun iya kwadai irin iyayye su nace maryam ai zuwan ki ya katse muna jin laraba ne yau nan dai na kora mata abinda yarinyar tace.
Ido waje maryam tace mun shiga uku wanan matar dai a haka zata mutu ga bin bokaye da yan tsubbu yanzu ya za ayi nace shinake tunane.
Maryam ni na dade da sanin haka tun fadan mu da ita na rasa gane kan AA a gidan nan magana ma sama sama yake hada mu yauma karewa fita yayi bai shigo part din nan ba.
Yanzun kin gane ni sai naga ki bari sai idan yana gida kije dakin gyara mai ki bude filon a gaban shi ki nuna mai tare da tambayan shi wanan nasa ne idan kin gani amma kafin nan ki fara dubawa idan gaskiya ne.
Duk wanan sakacin ki ne da mijin ki khadija kallon ta nayi tare da fadin sakacina kamar ya fa tace wallahi sakacin ku ne khadija.
Khady ke malama ce kin iya karantawa ki rubuta da kanki yanzun bansan matsalanki ba khady duk kin yi laushi da yawa baki irin wanan kiza kizan naki.
Laraba tace ayyah ai abin ba hakana bane ke dai kada Allah ya hada ki da irin wa yan nan matan shu,umai barin ta banza akayi kike zato.
Jifa fa ba fasa yinsa ake ba a kullun jifanka ake amma ai uwar dakina tana kokari wuri ibada sosai wallahi.
Nan dai muke ana ta tataunawa kan matsalan har yamma ta tafi kamar yadda bai damu ta duba mu ba nima haka na dage mai kafa har ya gama borensa.
Ina daga daki wayana dake falo ya dauki ruri laraba ta kawo min dakin hajiya mamace kan layi mun gaisa ta tambaye ni jiki na ce alhamdullahi mama.
Tace to yaya ina akwai canji fa alamarin gidan naku ko yanzu nace akwai mama tace ban kirashi ba shima bai kira ba tun ranan.
Nace mama kiyi hakkuri abin sai a sannu da addua don kullun halinta kara baiyana yake na sheri.
Nagama waya na kashe falo na fito naji ana sallama laraba ce ta leka security din gidan ta gani a kofa na yace Alhaji na da boko waje yace a kira masa daya daga cikin matan gidan nan.
Nace bakon ya fadi haka yace eh sai dai naga suna da zubi da Alhajin gidan nan sosai sai dai na gidan nan yafi shi tsayi da haske sosai.
Daki na koma na dako hijjab na fita duk da ban san shi ba amma ganin shi da kakin soja yasa na fahinci shine.
Da fara,a a fuskana nace yaya Suraj kaine a gidan mu yau sannu da zuwa ya amsa min tare da fadin ko kece amaryan ta mu nadan yi murmushi nace bissimillah ka tsaya nan mana.
Yace nazo security din kun sunce maigidan yayi tafiya duk da ban sani ba nace eh yace ok yanzu muka sauka shine nazo nan in dan watsa ruwa kafin in samu masauki.
Ashe maigida ma baya nan nace ko bayanan aimu muna nan yaya shigo daga ciki na fara tafiya ya biyo ni zuwa ciki part din AA na nufa dashi na bude dayan dakin nace ya shiga tare da fadin barin je in hada ma abinci yaya.
Yace ya gode nafice a falo muka hade da Nafisa tana huci tare da fadin dama na sani har kwasan mazan naki yakai ki dauki kato ki kai sashen miji na.
Waye kato naji ya fada daga bayan mu ashe ya fito yaba da sakon a sawo mai katin waya ya samu muna magana.
Sai da naga kaduwa a tare da ita data ganshi ya nunata yana fadin har yanzu wanan halin tsiyar taki yana nan ashe yace to na dawo kasan zamu zuba dake a gidan nan don a nan zan zauna daku kwana biyu kafin in kama gida.
Naji dadin har cikin raina ya sake nuna ta yace ki natsu a dan zaman da zanyi a gidan nan tare da ku don ko mijin ki ya takani yasan halina ba raga mai zanyi ba balle ke.
Murmushi nayi na wuce part dina naje nace wa laraba mama yau muna da bako yaya Suraj ne ya dawo anan zai zauna tare damu kwana biyu.
Abinci lafiyayye muka hada mai takar wanda nake hada ma AA na kai mai a dinning na aje na kwankwasa kofan nace abinci na kan table.
Ya dan leko yana fadin ya gode na fita saida na koma nake fada ma laraba ashe wai maigidan yai tafiya ne tace ikon Allah kuma shine babu ko sanarwa haka ?
Nace ba komai mama ni dai Allah ya sauke ni lafiya shine addua na ko yaushe yanzun banda lokacin komai a rayuwana.
Nafisa ko a bangaren ta tun fafatawan ta da Suraj ta shige daki sukuku tana kiran madam ta dauka tace madam kina ina yanzu ?
Madam tace wani matsalane kuma ya faru yanzu tace wanan dan iskan ne yau yazo gidan mu bakiga yadda nake kaduwa ba don tsoron shegen mutumin nan nake a rayuwa na.
Madam tace ke ki debe wanan tsoron ki nuna masa shi din may har yaushe zaki tsaya wani kanin miji yana baki tsoro kamarki yanzu kuma.
Nan dai ta bata karfin gwiwa akan zaman da zaiyi a gidan kan kada ta sarara mai don tasan AA bazai yarda ba ai mata wullakaci.
Iyakata dashi in kai mai abin karyawa kafin ya fita idan ya dawo da dare kuma in kai may yau weekend bai fita ba yana dakin shi kwance.
Daga can yake jin dararakun su ya sauko ya samu wani buzu zaune yana sharara masu labari sai dariya suke kwasa saukowa yayi daga sama tun kan benen yake fadin kai may ye haka su waye hakan kuma.
Gaba daya suka maida kallon su gare shi har ya sauko kasa yace wa yan nan fa daga ina suke haka ne ?
Ya nuna namiji yace kai tashi ka fice cikin karfin hali tace ya fice gidan ka ne gidan dan uwana ne fa yace ok belt din jikin shi yake zarewa a hankali.
Kagin buzun yai azaman tashi har ya make shi a kasa ko ya nana kasa ya fara kai mai belt da shuri duk matan suka mike suka fara kururuwa.
Ihun su muka ji nida Labara muna rigen fitowa abinda muka gani yasa mu ja baya daga kofa na muka tsaya kallo abinda ke faruwa.
Sauran mazan dake waje suna dafa shayi suka shigo gidan nan ya hada dasu yai ta aika masu shuri da bugu da belt.
Hankalina ya tashi na fara rokon shi yayi hakkuri Nafisa ko wuri daya ta manne da yan uwan ta suna kyarma ya na huci ya nunata yace sai nayi maganin ki a gidan nan shegun karuwai kawai.
Wani dadi naji a raina yau ga mai maganin shegu yazo gidan juyawa yayi wurina yace duk wa yan nan a nan suke ne kai na gyada mai ya waro ido yace duk wanan taron a gun mutum daya yake mutum kusan ashirin da wani abu.
AA wani irin mutum ne shi da baida tunane yaya gidan ka zai zama happy family da wanan kwama calan haka zai dawo zamu hadu dashi gidan nan.
A daidai wanan lokacin ne maryam ta shigo ta samu an gama rikicin yana masu sababi duk sun shige daki sun boye.
Chapter 3 · 0% Book details