Part din nawa yayi masi karami don haka Altine ta mayar masu da zama can babban falon gidan inda gidan baya tsinkewa da kafar yan barka.
Mijin Buzuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 149 min read
Abokan karatuna sun zo min barka lokaci daya suka hada kafa akazo don akwai hadin kai sosai a tsakanin mu lokacin Nafisa suna zaune a falon su ma.
Har falon gidan daya sha gyara kwana biyu da haihuwa an canza har labulayan falon da kujeru duk da ba a dade da suraj yasa aka gyara ba amma AA yace dole su sake wasu don bakin da ke shigowa barka.
Bayan sun ga yaran na fito muka gaisa dasu suna min barka da ba,a suna kirana da maman twin's.
Maryam ta dauko drinks ta kawo masu da zasu tafi suka bada gift din da suka zo min dashi matan sunce sai sun dawo suna su nace ko wanan ma na gode.
Tana zaune daga barin part din ta da yan uwan ta ganin yadda muke harkan da course mate dina ta tabe baki har suka fice ana wasa da dariya bayan sun dauki babies din.
Nan na dan tsaya muna hira da Altine sai naji tace idan da mutum bai haihu bane zai ga takaici saukin abin dai nabaya aka samu.
Murmushi nayi na girgiza kaina tare da fadin banda lokacin ki don ba finane yanzu a gabana ba abin arzikine a gabana.
Nasani ai tunda kin shiga kin fita kinyi musaya diyan da ba naki bane kowa ya duba ya sani ban san lokacin da Altine ta shigo ba tace kai amma ke katuwar jahilan inace haka.
Ke a tarihi kin taba jin wanan zancen naki na masu tabin hankali kinje gun tsafe tsafen kin sun fada maki karya tunda yaran ki ne ta juya zuwa nata sai kiyi yadda zakiyi ga yaran nan a gabanki ai.
Ke wai wa kike ne a cikin wanan zancen yar kalan dangi kawai na fada ko kun dauka bamu san komai bane tace a,a kin sani don naga alama tai mata alaman mara hankali da hannu.
Wasa wasa fadan su da nafisa yayi tsawo ranan Nafisa taga tujara taga zari agurin Altine yar duniyar mata don da wanda tayi da kazafi duk ta hada mata sai ga Nafisa na kuka da hawayen ta wai yan uwan Samad basu kaunar ta basu kaunar diyan ta.
Tunda ga Altine ta sheganta mata yaran da ta haifa dashi yau ya dawo ya fada mata matsayin ta a gidan dana diyan ta.
Da kyat dai su momy da yan uwanta suka samu suka rabasu ni dai har na gaji na shige ciki na bar gurin don ban iya tsayawa sauraren su.
AA ya dawo ya samu sun lafa Nafisa ta same shi yace ke ki barni da wanan haukan inji da abinda ya samay ina fama da abinda ke gaba.
Yana ce ta fice mai daki bai son kananan magana diya dai diyanane ba na wani ba tace ai baka damu da yaran ba wa yan da ka damu da zuwan su gashi kana rawan kafa an haifa ma yan gwal.
Ke may yasa baki haifa min ba in rawa kafa kan su kamar wa yan nan din yace ya kara hasalata nayi rawan kafa don an haifa min abinda ke kika kasa samar min a gidana.
May na kasa samu kana nufin namiji ai duk rawan kan da kuke nasan don shi ne kukeyi haka yace yan gwal din dai da kikace an haifa min.
Kinga rashin kyau gori ba abinda baki fada ma yarinyar nan ba a gidan nan kan haihuwa tana hakkuri da Allah ya tashi nuna maki abunki sai gashi ya bata biyu a lokaci daya kuma kyawawa har sun saki hauka.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: As usual na tashi tun da safe nayi wanka na shirya tsab dani kafin in fito laraba ta shigo min da abin karyawa ta aje sai dana gama shiri na zauna don shan kunun kanwar da yanzu na saba sha don nafi son shi da tea.
Altine ne ta shigo dakin zata dauki kayan yara ta kaiwa momy da tai masu wanka take fada min ga yar uwar Nafisa a falo tana magana dani.
Nace tace ta shigo daga ciki can sao gata ta shigo da sallaman ta fuskanta dauke da fara,a tace maijego sai kunun kanwa ina aje cup din nace Anty Fatiha kece ashe tace eh.
Ban samu shigowa ba ranan da aka kai muna kayan buki don jama,a sunyi yawa a lokacin nace kai haba ba komai ai muka gaisa ta tambayi yara nace ana masu wanka ne a dayan dakin.
Tace to idan sun fito ki shafa min kansu Allah yai masu albarka nace amin na gode sai naga ta gyara tsayu nace bissimila zauna mana tace ba sai na zauna sai dai magana nake son muyi dake dama.
Nace to ai gani tace don Allah ina fatan zaki fahince ni ki fahinci zuciyana kuma nace insha Allahu.
Tace kin san zama da mai ilimi da wanda baida sai anyi hakuri don zaka ga wanda bai da ilimi yana abu wani lokaci kamar zararre nace gaskiya.
Tace kiwa Allah kiyi hakkuri da yar uwata uwar mu daya uban mu daya amma mu kan mu mun sani abinda take bata yin sa a kan gaskiya.
Duk wanda ya yarda da Allah kuma yai imani dashi ina tabbatar maki baya taba tabewa a duniya Dija nasan kina da ilimin zamani dana addini gwargwado kima bazamu ce duk ba don kowa dan koyo ne.
Nace gaskiya ne tace a gaskiya ga abinda dan zama na ya hango min a gidan nan dan zuwan danayi na zauna daku din nan.
Na fahinci dukkan ku kuna da rauni sosai kina sani fa ba mai iya maka wani abu a rayuwan ka bayan Allah in ma har wani abu ya samay ka tabbatar wanan abin kaddararene a gare ka dama kuma bamu iya kauce wa kaddaran mu.
Zaman gidan nan yana bukatan gyara daga gare ku ko in ce daga gareki ki tuna abinda ya kawo yar uwana gidan nan shiya kawo ki ke ma ta yaya zaku zauna kuna kona kanku saboda son zuciyar mutum daya tak.
Ta girgiza kai tace gaba dayan ku gidan kuna tsoron ta har mijin naku an san akwai asiri tabbas yaci annabawa Allah balle mu da ba kowan Allah ba face bayin sa.
Kina da makami a tare dake kin iya karanta shi don may ba zaki bi dare kibi rana ba wurin kwatoku har ita daga halaka.
Ki dage ki bata duk wani lokacin ki kina da dama yanzu ba sai kin dauki Alkur,ani maigirma ba a hannun ki yanzun ne lokacin da kike hutawa ki dinga aikwa ubangini kina fada mashi matsalolin ku sai ki ga sauki ta inda baki zata ba.
Amma duk kun biye mata ana wai asiri asiri da ita dake zuwa da wanda ke mata wakeyi in ba Allah ba ba wani abinda zata iya maki muddin kin koma ga Allah .
Ita kanta wallahi tasan kinfi karfin ta ga komai yanzu don ta fada na sani kuma haka ne mutumin da kullun kake binshi da sheri munana yana tsalkewa ai kasan yafi karfin ka.
Kada kiji ina wanan magana ki fassara min magana da wani manufa ina yin shi a matsayin ku na yan uwana musulmai har maigidan na zauna dashi jiya na fada mai inda yake da kuskure da rauni ya kuma fahince ni .
Da fatan ke ma zaki fahince ni na barki da saura a zuciyar ki sai ki nemo mafita amma ku gyara gidan ku don Allah inda kake fa shine wurin ka ba nawani ba.
Tana fadin haka tace nagode da kika bani lokacin ki kuma kika aurare ni da fatan zaki kula da abinda nace ma,assalam.
Tana fadin haka ta juya tafita daga dakin ajiyan zuciya na sauke tare da fadawa tunanen abinda tace min din.
Ya Amina ne ta shigo nake fada mata yadda mukayi da yar uwar Nafisa din tace ikon Allah Allah daya gari bambam ke nan.
Gasu uwa daya uba daya amma yanayin su ya bbambamta wurin hali ai gaskiya ta fada maki ba karya a ciki kjadija wallahi kija mijin ki a jiki yanzu ki nuna mai so.
Ba dai inda zaki yanzu kibar wa yan nan yaran wa wata ta rainar maki su da wani tarbiya na daban don haka wallahi khadija ki sa tsoron Allah ga alamarin ki ki bar wanan wautar da kike ki rugumi mijin ki da yayan ki kin dai ji abinda mama Tani ta fada maki ai.
Ga yara kamar diyan larabawa kyawawa dasu kamar mutum ya sace uban sai rawan kai yake yana alfahari da abinsa ko da kike cewa wai bai damu da yara ba wallahi nikan naga ya damu da wayan nan sosai.
Idan ya shigo ko hannun wa suke sai ya taba su kafin ya fito don yaran akwai su da shiga ido shiyasa mama tani tace a dan saka masu zuben azurfa don bakin mutane naji maryam tace zata nema masu sai ki tuna mata.
Hmmm nace nama rasa abinda zance sai na juya da fadin ya Amina ki duba kayan a fitar da wanda zasuyi amfani dashi yanzu zannuwa kuma sai ki cire min wanda kika ga ya dace saura a fitarwa laraba da Altine da mommy sai a cirewa hajiya mama ita ma.
Tace wanan aiki bari har maryam tazo don ba zan iya ba ni kadai wallahi kayan ne gasu nan kamar shago za a bude.
Gaskiya mijin ku yana son ki wanan buzuwan ne dai kawai da tai maku shamaki tsakanin ku da ba karamin abu zakuyi a gidan nan ba.
Wayana dake ruri ya dakatar damu na duba sai da na kalli ya Amina nace hajiya mamace fa ke kirana.
Na daga kiran da sallama muka gaisa tace kun tashi lafiya khadija ya su takwara na dasu momy ku da sauran su nace suna lafiya mama.
Tace dama na kiraki ne in tambaye ki may ke faruwa a gidan ku don Nafisa ta kirani ta kuma kira Alhaji a karo na farko ta kawo karan ku wurin mu.
Murmushi nayi nace mama may tace kuma mun yi tace eh to ke dai lafin ki shine wai kince zaki karbi girki yanzu shi kuma mijin naku wai yai maki abinda bai mata ba idan ta haihu.
Alhajin ya nemi layin shi a gabana ya kirashi yai mashi bayani yadda abin yake wai idan zata haihu jinga sukeyi ashe ya bata kudin komai da komai daya shafi haihuwa.
Yanzu kuma da taga a girin ki ba haka abin yake ba shi yayi komai bugun gaban shi shine take kiran shi da azzalumi da macuci.
Sai naki matsalan yace itace ta fara yin hakana yanzu kuma kema kika ce zaki rama nace hakana ne mama tace to kinga aikin gagawa inda yake kai mutum ai.
A lokacin ita gani take dama ne ta samu na yin duk abinda ta ga dama bata tunanen abin da zai je ya dawo gare ta yanzu gashi tayi a lokacin taji dadi yanzun kuma na wani yazo tana yin korafi.
Abinda nake so daga gare ki shine ki natsu don Allah ki dubi yaran ki kada ki biyewa shirmay ta ku koma daya da ita ki dauke idon ki ga komai da takeyi a gidan kinji ko nace naji mama na gode.
Mun gama wayan na kalli yaya Amina tace wanan bata da hankali wallahi yaya zaki kira sarakanki da wanan magana bayan baki da gaskiya ta ko ina.
Nace ya Amina wuyan sha,ani ke gareta ga wanda bai gane halinta ba idan tayi tana jin dadi yanzu ramawa ai sai taji zafi lokacin da ta karbe kudin ta wa ya sani.
Tace wanan ko yadda yai maki din nan yafi zafi ba don ko kudin daya bata masu yawa ne dole taji zafin ganin abinda ya sai maku don zaku dade kuna amfana dashi .
Ita karshe ma kila kudin a banza zai tafi gun bokaye da malamai nace tun yaushe wallahi ni abinta ma yanzu ya daina bani mamaki sam.
Ita fa yanzun na fahince ta gaba dayan mu bata son kowa ya rabe shi ne sai ita kadai ko uwar da ta haife shi tana kokarin nisanta shi dasu ne dan kowa bata son ya raba shi.
Yanzu ai sai dai ta mutu don karshen rabuwa har da rabo biyu a tsakani ai kinga dole ta ganku tare munyi hiran sosai karshe muka koma hiran maryam tana yaba kirkinta gare ni.
AA ne ya shigo dakin ya Amina ta fice wurin su momy yanayin shi ya nuna daga barci ya taso lokacin nace ina kwana daga inda nake bai amsa ba sai da yazo kusa dani ya lakutan min hanci yace .
Shine kika shayani jiya ina jiran amaryan jego tazo tayani kwana in sha karni murmushi nayi nace wane ni in ka ganin dakin ka mun yi arba,una ne.
Yace kai mata nace ai itace ta fara don haka kar kaga laifi na yace banga laifin ki ba ga hakan tunda bashi kike biyan .
Dan kallon shi nayi nace haka ka dauka ko yace tunda anci gashi zaki karba kuwa tunda kin iya daru ke ma.
Nace ni har wani daru gare ni ka san dai inda daru yake yace darun ki a cikin ruwan sanyi kike abinki babu fada balle hayani don haka yanzu nake tsoron fadawa tarkon ki.
Murmushi nayi nace sunan da na samu yanzu ke nan kuma aina gode tunda shedan mai sauki akai min.
Ya dan jima a dakkin muna magana akan sunan da taron da akayi muna kafin ya fice a gurina a falo ya samu Nafisa da yan uwanta zaune suna duban waya.
Jin motsin shi ya fito yasa su daga kai suna kallon shi Ihisan ne ta mike zuwa wurin shi uwar ta daka mata wani irin uban tsawa sai da yarinyar ta kado.
Da mamaki ya kalleta yace don may zaki hanata zuwa wurina tace don ni ke da yata ba wani ba yace ok ashe yar taki ce ke kadai kin san inda kika samo ta ke nan ?
Yau ka fada min abinda dana dade ina jiran ji daga bakin ka kamar yadda yan uwanka suke fada min game da yarana a gidan nan.
Fatiya ce tayi gyaran murya ta katse lazumin da take yi tace wanan wani irin abu kuke haka gabsn yara ko da yau kuke na kulluyaumin gidan ku babu zaman lafiya sai anyi fitina kamar kananan yara.
Yanzu ina amfanin wanan abin kece fa kika fara jan maganan nan ya baki amsa kince ina yafito kima kanki fada don Allah yaran ku girma sukeyi suna ganin abinda kuke yi.
Tace oya Ihisan jeki gurin Abban ki kinji yarinyar tana kallon uwar su don tsoro yace ta zauna abinta fita zanyi ya kalli nafisa yace kin kaini bango yanzu kan ya fita.
Tace ba laifin ka bane laifina ne dana yarda na nuna maka son kwarai har cikin zuciyata yanzun kam ya kare ai.
Kai Fatiya ta girgiza mata ta hau yar uwan da fada a cikin yare don laraba dake falon tana gyaran bangaren mu.
Zama tayi tana tunane a ranta bayan fitan shi wai itace kuwa Nafisa ita nafisan da suke rayuwa kamar ba gobe da mijin ta tana juya abinta yadda take so.
Ya gwada ma yar da tazo dashi gata har zuwa Ihisan dinta yanzun tana kokarin zama dodo a gare shi akan wata wai ita ake wa haka akan kishiya da take ma kallon bata kai mace ba.
Yau tana kallo ba dan ta rasa kudin yin sihiri a gareta tana ba kuma rashin masu mata aikin ba sai dai gani take abin baya tasiri a kan su ne yanzu gaba dayan su har samad din.
Maganar da zatai mashi da ya bata hakkuri akan shi yanzu kafin ta gama fadi ya bata amsa gaskiya dole ne ta kara danmara a gidan ta ta gasa masu kwakwa a hannun su.
Ya zama dole ta dauki mataki akan wanan yarinyar data shigo jiya jiya gidan nan tana kokarin ta taushe ta da karfi da yaji a gidan.
Kwana biyu ya Amina ta tafi sai momy da Altine momy ma sati biyu kacal Abba ya bata da kyat ya yarda tai muna satin biyun ta dawo.
Tafiyan ya Amina ya saukar min da kadaici sosai don kwana biyun da mukayi a tare ba karamin dadi nake ji a raina ba.
Wucewan ta yasa momy ta dawo dakin ita da Altine muna zama Laraba ko ance ta shigo bata sake jiki a cikin mu sosai tafi gane ma zaman falo ko tana wani aikin.
Gashi idan tayi wankin yara bata shigowa sai kayan sun sha iska take dawowa part din don dai kawai tsaron lafiyan su da take yi.
Na samu hutu sosai don idan suna falo barci nake samu inyi sosai sukan kyale ni har lokacin dana tashi ko yaran suna neman nono.
Maryam ko cewa nayi ta bude kayan ta dauki duk abinda ranta ke so ba wani kaya ta dauka ba sai turmin zani guda daya wai shine ya bata sha,awa a cikin kayan.
Madam kafa ya kiya har lokacin tana kwance a asibiti tana jinyar kafan basu sani ba ashe daurin da akai mata bai dauru ba da kyau dole aka samce aka gyara wani sabon dauri din iya wuya ta ci shi.
Ga rashin ganin kulawan da take Nafisa batai mata da takan shigo sau daya ta dubata har ta koma bayan kwana daya take shigowa gidan.
Ya kai yanzu sai ta share kwanaki bata leko ta ba sun dinki da sabuwa aminiyar madam din na baya da sukai fada tana kwance labari yazo mata.
Ta kudurta a ranta zatai wa Nafisa magana akan hakan duk ranan da tazo dubata din sai bayan kwana uku tazo a gurguje tana sauri tana wani sham kamshi.
Bayan sun gaisa take fadin akwai ida zata sauri take yi madam tace dama ina son magana dake don naji wani maganan da tsamace shi ba a gare ki Nafisa.
Tana wani taunan chewing gun tace ins jinki ai yanzu nafisa ki rasa wanda zaki hurda dashi sai sabuwa makiya na zaki dinki da ita.
Nace tace may ye a ciki madam business ne fa dama tsakanin mu ba wai haka kawai kike min ba yanzun kuma kina kwance kina jiyan zama kike son inyi kar in nemi wanda zai haska min hanya ko may ?
Ita ma sabuwa abinda kike min take min a yanzu kema idan Allah ya baki lafiya sai mu dora a inda muka tsaya ko ba shike nan ba.
Matsalan ku da sabuwa ku ya shafa bai shafeni ba kowa kudi nake bashi yadda ya bukata yaje min guri ko ya rakani inje.
Madam ta ce haka kikace tace ai haka maganan yake madam sai idan kin so juya shine a wani tsigar kuma wanan kam.
Tana fadin haka ta aje mata dubu biyar a gefen filon ta tace sai anjima don ni akwai inda zan tafi daga nan kallo madam ta bita dashi tana kallon takon ta tare da kutawa .
Ta raya a ranta sai ta dauki famsa in har ta mike akan Sabuwa da Nafisa kan abinda sukai mata din tace ai in kun san wata baku san wata ba dani kuke wasan.
Tana fita ta samu sabuwa a mota suka dauki hanyan zuwa jos ranan suke son zuwa su dawo a ranan kuma a gida dai ta bar yan uwanta da yara tace dasu zata dan je wani wuri ta dawo.
Bayan fitan da kamar awa daya sadiya ta fara kuka sunyi lalashi taki yin shiru tun suna lalashinta da girma da arziki har abu yafi karfin su.
Sai ga Fatiha dauke da ita ta nufo ni ina falona lokacin ina cin abinci tace Dija ko zaki duba muna yarinyar nan uwarta ta fita yau dai sai kuka take muna mun rasa gane kanta.
Karbar yarinyar nayi daga hannun ta ina lalashi ta muka samu ta dan yi shiru nace ina abincin ta tace bari ta dauko.
Ta dawo dauke da feeder ta ta miko min a na dan bata taja kadan sai kuma taci gaba da kuka nace yau halima lafiya kike kuwa na fara dan taba mata jiki zuwa kai naji kan yai zafi sosai.
Na dago nace mata ina ganin yarinyar nan bata da lafiya ne yau ina maganin ta yake a bata tace sai ta tambayi Yanyala.
Ta fita da yarinyar kasa cin abinci nayi na wanke hannu na samay su a falon suna tambaban wanda zasu bata daga ciki.
Karba nayi na karanta na mika masu paracetamol si bata ina tsaye ina kallon yadda suke bata maganin sai kuka yarinyar ke yi.
Su goyata nace ko zata yi barci Yanyala ta fara fadin ko sun goya ta kanta ba tsayawa yake yi ba ai nace haba dai sai kusa abu ku tare kan ta baya mana.
Fatiha ce ta goya ta na nuna mata yadda zata tare kan sai kan nata ya tsaya tana dan jijigata har tayi shiru barci ya dan dauke ta nace Allah ya sauwaka.
Na koma part dina na shige bayan kamar rabin awa ta falka kuma kukan ta muna ji har part dina muka fito dasu momy falon muka samay su.
Nan ma munyi munyi taki shiru momy tace su kira uwan mana wai sun kirata wayan baya shiga sai momy ta kira layin AA take fada mai abinda ke faru yace gashi tafe.
Kafin yazo yayi ta gwada layin ta ana fadin not reachable sai ya kashe ya iso gidan ya samay mu a kanta ya tambaya may ke samun ta ne ?
Suka ce haka kawai suka ga ta fara kuka momy tace jikin nata ai ya gashe ma ya dago yana tambayan Yanyala ina Nafisa taje ne tace tace masu zata nan ta dawo ta fita.
Momy a shirya mu kaita asibiti yace a dubata momy ta shiga ta fito tare da yanyala suka tafi likita yace zazzabi ne da kuma karancin jini ke damun ta.
Take aka bada gado ranshi idan yai dubu ya baci sai gwada layin ta yake faman yi baya zuwa shi ya dawo gida daukan abinda zasu bukata asibitin.
Yana shigo yace wa Fatiya bata dawo ba tace ,a,a har lokacin bata dawo yake fada masu an ba yarinyar gado wai bata da jini a jikin ta.
Tace duk kwanan tun da suka dawo gida yarinyar bata cika lafiya ba sosai ga uwar bata zama koma ta zauna ba nono take bata a kan lokaci sai taga dama.
Ya shigo wurina yana fada muna an aba yarinyar gado mukai mashi Allah ya sauwaka ya dauki abinda zai dauka ya bar gidan ranshi a bace.
Tara ya shigo gidan ya kara tambaya still bata dawo ba ya fita ya kira wayan ts yafi a kirga bai samu layin nata ba har wanan lokacin.
Altine dasu Fatiya suka shirya zuwa asibitin don kaiwa su momy abinci tunda har wanan lokacin basu dawo gida ba shir shiru har guraren sha daya da rabi suka shigo har lokacin ba Nafisa ba labarin ta ba a san inda ta tafi ba.
Tun yana jin haushi har ya koma fargaba idan ba wani abin bane ya samay ta can wurin bakin yawon ta don bai dauki wanan abin na kai sake ne ba.
Inda momy tayi sallah ta kira hajiya mama tana fada mata halinda ake ciki ranta ya baci sosai ta kirashi a waya tayi mashi tas ranan .
Sai ga su Altine sun dawo muna da labarin har yanzu ba a ga Nafisa kuma wayan ta baya shiga idan an kirata nan muka zauna jigun jigun damu a falona.
Nafisa sun samu layi a gurin boka haka yasa suka bi sahun masu jiran su gana dashi din sai biyar suka samu ganin bokan shirgegen mushiriki dashi yana zaune daga shi sai lagen bakin zanin daya yafa a jikin shi.
Ta fara bayani ya dakatar da ita ya kora masu abinda ke tafe dasu Nafisa irin su take so dama tace hakane boka shine mukazo wurin ka idan da taimakon da za a bani kanta.
Boka naki jinin in bude ido in ganta a gidan nan yace kada ki damu tunda kinzo nan zamu diba mu gani a cikin karfin tsafin mu.
Yadan yi surukullen shi ya dago yana dubanta tare da fadin kai haba dai gaskiyane kina aiki kamar bakiyi don wanan yarinyar itama hatsabibiyar kanta ne sosai.
Nafisa tace haba nikan na sani idan ka ganta kamar ta Allah da ita ni dama nasan ba banza ta barni ba ya kada kai yace a, a ba yadda kike nufi bane.
Ita irin masu baiwa din nan ne asiri baya saurin kamata gaskiya ga kuma tana da rikon addinin ta da wuya a aika mata ya samay ta gaskiya.
Sai dai idan munce zamu mata aiki kema akwai aiki a gaban ki gaskiya don sai kin bar komai daya shafi naki addinin zamu samu aiki ya kai gare ta.
Kallon juna sukayi da Sabuwa sai sabuwa ta kada mata kai Nafisa ta juya gurin boka tana fadin boka na amince da ko may ne zaka fada min zanyi.
Don na tsani wanan yarinyar naki jinin in bude ido in ganta a gidan nan wallahi ya ki kwantar da hankalin ki tunda kin zo nan.
Zakiga aiki maikyau sosai tace boka ko nawane indai bukata zai biya zan baka sabuwa tace ko akashe muna ita har yaran nata ko kuma a haukata ta tabi daji a manta da ita gaba daya.
Boka yace irin su na fada maki ba,a zuwa masu yadda kuke nufi din nan domin Aljanin da zamu tura ba zai samu aiwatar da aikin shi ba sai ya samu bata cikin ibada.
Ko bata sallah gata nan nagani tana yawan ambatan abin bautar ku koda yaushe a bakin ta gatanan anan gurin ina kallonta yace.
Ya mika mata wani ruwa a dan wani roba fari na yought yana fadi wanan kiyi kokari yau din nan ki yayafa ida kika san zata bi daga ita har mijin idan kin samu washe gari sun taka.
Yayi wani iri da hannuwan shi alaman mun raba hanya ke nan da AA yace ba sauran zaman lafiya a gare su karshe auren zai watse babu wanda zai tuhumay ki.
Sai wanan ya mika mata wani dan kuli yace zaki gina rami daidai bayan dakin ta ki binne a cikin ramin ki kawo babban dutse ki taushe gurin zata dinga jin gidan gaba daya ya fita ranta ga baki daya sai ta barshi ba shiri.
Wanan kuma a inda ake girki zaki saka da zaran zafin wuta yana dukan shi bata da kwanciyan hankali a zuciyanta tsana da ganin bakin mijin zata ji.
Idan kinyi haka yau ba tare da samun akasiba ina mai tabbatar maki bata kai wata daya a gidan nan komai tsananin ibadan ta.
Boka mun gode zakaji dasin aiki damu sosai nan gaba dama ai rashin sanin wurine yasa baka ganmu ba da tuni munzo ai.
Sai dai ya matsalan mijin nata ne kai ya kada yace wanan gaskiya samun shi shima yanzu ba abune mai sauki gare mu ba don uwar shi tsaye take akan dan ta.
Kai har uban ma yana tsaye sosai akan diyan shi amma da zaki iya samo muna dan kwalin kan uwar shi da kasan kafanta akwai aikin da zan hada maki zai ci sosai kuwa.
Sabuwa tace boka mun gode in Allah yaso zakaji nan bada dadewa Nafisa ta balle jakka ta fito da kudi masu yawa don jin dadin abinda yai masu alkawari ta bashi tare da fadin sai sun juyo.
Sai lokacin da suka fitone suka dubi lokaci hankalin Nafisa ya dan tashi don bata san gurin yana da nisa haka ba da ta dauko yanyala da yar Aljannan ta sun taho ta raya a ranta don haka take kiran sadiya dashi.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/2/21, 10:23 AM - Xxxxx: Garin Allah ya waye hankalin kowa a gidan a tashe yake tun shida da wani abu ya bargidan zuwa asibiti ya dubasu inda ya samu jikin yarinyar ya danyi sauki.
Za a kara sa mata wani jinin na biyu ya dan dade tsaye yana kallon ta yana mai jin wani iri har cikin ranshi sosai.
Yusuf ne ya iso ya samay shi a asibitin inda ya dan duba yarinyar kafin su fita zuwa police station su sanar da bacewan Nafisa din.
Dawowan su asibitin yayi daidai da isowa tare da Altine da Fatiha munzo masu da abin karyawa ida nake jan motar da aka ban gift gidan SJJ .
Tsayawa yayi da mamaki yana kallon mu yadda nake tuka motar cikin gwanan cewa da iya tukin bai taba kawowa a ranshi ina driveing ba da farko don ban taba nuna mashi iyawana ba.
Sai da muka firfito daga motar na rufe muka nufo inda suke tsaye a cikin jimamay tare da gaida su inda muke hada baki gurin tambayan anko gano inda nafisa din take.
Yusuf ne ya bamu amsa cewa wallahi har yanzun shiru ba a ji komai ba gamay da ita har na fara tafiya nace wai ba za a gwada tambayan wanan matar madan aji ko tasan idan taje .
AA yace wanan dabaran bai fado min ba sam wallahi don shawara ne babba yace ma Yusuf suje su tambaye tana cikin asibitin ai.
Suka nufi dakin da madam din take kwance sun fara gaida ita da tambayan ya jikin tace da sauki sosai sai tayi shiru.
Yusuf yace munzo mu tambaye ki ne ko kina da masaniyar inda Nafisa ta shiga tun jiya da safe da ta fita ba a ganta ba har wanan lokacin.
Tace cikin farga tun jiya fa yace kwarai sai tayi dan shiru ido suka kafe ta dashi yadda take nazarin wani abu a danta ke tunane a ranta sai can tace .
A bunkici Sabuwa idan basu tare don jiya tazo nan da safe dubani tace suna sauri zasu tafi wani guri tare da Sabuwa bata tsaya ba tafita duk ko da nuna matan danayi yin haka kuskure na.
Wacece Sabuwa AA ya katse madam da ta fara zuba cikin tsana tace wata aminiyar tane datayi sabuwa tana zama uguwar Nyanya ne.
Ki muna kwantace idan kina da layin ta kuma ki bamu cikin rawan jiki tace ina da layin ta sosai kuwa bari in duba maku mu gani.
Ta kira masu layin yasa a waya tare da danna ma layin kira sai dai amsa dayane kamar na wayan Nafisa din dai har itama.
Kallon juna sukayi da Yusuf yace itama not rechable ke nan wani abu dai yana faruwa dasu duk yadda akayi.
Kara kwatacen gidan Sabuwa tayi masu suka juya suka wuce batare da mata godiya ba sai AA ne da ya juyo yace idan a nason karin bayani zamu kara dawowa gurin ki kuma.
Wani irin takaici da bakin ciki mai tatare da Nadama ne ya rufe madam a lokaci daya har kwallan takaici suka zubo mata tana kiyas ta wani a cikin ranta.
Mun duba yarinyar shigowan likita yasa bamu wani dade a gurin ba ko da muka fito daga dakin motar su AA baya gurin nake cewa da su Altine ai anan ne madam din take ko ?
Fatiya tace eh don ranan sun zo da dare sun gaida ita da yar uwarta muka sa kai zuwa dakin don mu dubata.
Tana zaune da ganin idanuwan ta tayi kuka lokacin mukai mata sallama tare da gaida ita da mata ya jikin tace da sauki tana mamaki a ranta mai ya kawo mu asibitin wanan lokacin.
Nace ya kafan da sauki dai ko tace da sauki ta gode na bude jakka na na ciro mata kudi na bata dubu goma sai ta fashe da kuka.
Fatiya ce tace ba kuka zakiyi ba kiyi tawakkali ga Allah da kaddaran da ya jarabce ki dashi ai tace dole ne in kuka yar nan kuka dole ne gare ni ai.
Wanan yar tai min abinda ban zata ba gashi duk da abinda nake mata tazo dubani da zuciya daya har da alherin ta gare ni haka.
Ba komai nace da zuciya daya nake tare dakowan ku ni na juya tace yanzu maigidan ku ya barnan yana fada min Nafisa ta bata tun jiya ba a san ida take ba.
Ni dai jiya tazo nan a gurguje to ba abin alheri bane inda zasu koda bata fada min ba nasan wani kawai zasu da sabuwa don yanzu itace sabuwar amiyar ta.
May yuyuwa basu kasan nan ko kuma wani abu ya samay su a hanyar zuwa bamu dai fatan hakan amma ba a raba daya biyu daga cikin wanan dai.
Fatiha tace kauye kuma suka tafi yin may tabar yarinyar ta jinjira a gida zata tafi kauye ta barta yar a gida.
Madam tace ke dai Allah ya yafe muna kawai ni yanzu nayi na dama wanan karayar yaza min kamar ishara ne a kan duniya.
Idan mutum bai nufe ka da share ba kace kai zaka nufa tun a nan duniya Allah ke nuna maka abinka yanzu ba sai anje can ba.
Yanzu kudin nan da yariyar nan ta bani ya kara sa rayuwana a cikin nadama sosai wallahi muna binki da sheri kina saka muna da alheri.
Murmushi nayi na juya na fara tafiya Altine ta biyo ni Fatiha muka tsaya jira a cikin mota ta fito muka dauki hanyar gida.
Cikin mu babu wanda ya iya magana tunda muka fara tafiya har tsawon wani lokaci kafin Altine ta kawar da shirun da fadin ita wanan matar taga aya ke nan ga rayuwan ta ?
Fatiha tace aini imanin su ya cika min zuciya mutane babu imani a tare dasu yanzu idan wani abu mumuna ya faru dasu a hanyar mai zasu fadawa Allah kan hakan.
Har suka gama maganan su ban samu bakin magana ba ni kadai nasan abinda nake kiyastawa a raina wanda godiya nake wa Allah da bai min wanan halin na yawon bin bokaye da malamai ba wanda karshen shi nadama ne ke tare da mai wanan halin.
A A kan zuwa ya samu gidan sabuwa a rufe ya kara tayar mai da hankali inda ya tambayi makwabta sukace tun jiya rabon su da ganin ta suma a garin.
Sun kuma tabbatar masu sunga fitan su tare da nafisa din a yadda akai masu kwantacen ta sukace tabbas tare suka fita daga gidan.
Bai shigo ba sai karfe hudu na yamma ya shigo gidan a gajiye don yai wanka part dina ya fara shiga ko da wani labarin ya sani.
Yadda ya shigo na kalle shi ina falo zaune ina shayar da yara nono ya shigo muna gaida shi muka fara tare da tambayan shi anganta da jikin yarinyar.
Yace har yanzu dai ba wani labarin su sai dai makwantan wanan dayan matan sun sheda masu sun gansu a safiyan jiya tare wai zasu tafi wani kauye ne yanzu dai an bamu layin wata mu kirata muji ko tasan inda sukaje.
Wayan ta yana ringin bata dauki waya ba har yanzu nace oh wanan abin tashin hankalin da mai yai kama haka ne ?
Zaki fita zuwa nesa ai sai ki fada wa mutane don gudun irin haka ko akalla dai an san inda ka tafi ai.
Altine tace ai yanzu wanan yarinyar ne abin tausayi wallahi an rabata da nono da karfi da yaji haka gashi bata isa yaye ba ma.
Wallahi nima abinda nake tunane ke nan nace Allah yasa dai duk inda take suna lafiya shine fatan mu dai yanzu.
Dariya mai kama da yake yayi yana dagawa daga inda yake zaune kusa dani yace bari indan watsa ma jikina ruwa inji dadi.
Nace abinci fa ina ganin ko karyawa bakayi ba tunda ka fita gidan nan yace lemo nasha dazun da naji yunwa barin watsa ruwan inci abinci dai ko zanji dama ya mike ya fice daga part din.
Wanan matar akwai tsinanna wallahi, ji yadda ta saka bawan Allah nan cikin wani hali tsakanin jiya da yau din nan har ya fada .
Nace dole hankalin shi ya tashi ko don wanan yarinyar karama dake kwance asibiti cikin wani hali tace dama ba son yarinyar take yi ba ai kin ga idan ta mutu an huta ai.
Amma ke khadija ni sai ina gani kamar gudu tayi yadda suke ma maza idan sun gama dashi sai dai kuma zata gudu ta bar yan uwanta da diyan ta haka ?
Don idan zasu gudu ai shammatar namiji suke yi sai sun gama yaye komai na mutum sai su gudu su barshi daga baya.
Nace Allah dai yasa duk inda take tana lafiya sai Altine tace kai wanan baki san takaici ba wallahi banga abin tausayi wurin wanan matar bani.
NAFISA
Sun kamo hanya da ga yamma yayi masu inda suka dauki mota shata zuwa Abuja tun basu kai ko ina ba dare yayi masu tafiya driver ke yi kamar ai aike shi.
Sai kwasan su yake da uban gudu a daji tun suna firan bokan da sukaje gurin shi har suka gaji sukai shiru da bakin su driver na ta faman tukin mota.
Sun dan wuce kaduna kadan suka hango haske a tsakiyan titi driver su ne ya fara fadin yaushe aka fara checking wurin nan sai ya rage gudu bai kai ga karasawa ba ya gane yan fashine a hanya.
Salatin da ya saka ne ya fargar dasu abinda ke faruwa a titin yan fashin sun tare wani mota suna operiton sai suka hango motar su nafisa tafe.
Driver yayi saurin yin kwana garin juyawa sai motar tashi ta leka da sauri yace dasu kowa ya ta kanshi ya fita ya zura daji da gudu suka mara mai baya suma a guje cikin dajin .
Nan yan fashin suka farwa motar da suka bari da bincike suka kwashe duk abinda suka sama a cikin motar sukai gaba suko wurin gudu sin fadi sun jirji ciwo a jikin da kyat suka samu wani dan kauyen da suka bari a baya suka kwana a tsaye don mutanen garin sun shige gidajen su ko.
Sai washe gari mutane suka fito suka samay su a gurin ga mutanen da yan Fashin suka tare hanya motaci an taru a gurin wasu an kashe wasu kuma sun jirgita.
Basu suka samu isa wurin motar su ba sai da wani ya taimake su suna zuwa suka samu an masu dadaya da kaya duk an watsar da komai a daji.
Tsananin firgicin da ta kwana ciki yasa ta fita yacin ta ga gurin gudu ta gwauce a kafanta haka dai suka samu aka taimaka masu aka kwaso su garin kaduna akai dan bincike basu bar kaduna sai uku na rana koda suka iso Abuja lokacin yamma yayi sosai gidan Sabuwa suka fara zuwa.
Suka kitsa abinda Nafisa din zata fada a gida kafin ta wuce zuwa gida daidai AA ya fito yana magana da yusuf da security din gidan mota ya tsaya da ita.
Kallon mamaki suka fara mata yadda ta koma gaba daya ga jikin ta ko ina ya guje tana tangadi tun da ta dumfaro gidan gaban ta ke faduwa.
Ganin su cirko cirko a kofan gidan bai hanata kokarin shigewa ciki ba wani irin tsawa ya daga mata daga inda take sai da ta kadu.
Yace ke tsaya nan ina kika fito haka zaki shiga min gida ki koma can inda kika fito yawon tanbadan ki kada ki fara shiga min gida.
Yusuf yace ka barta ta karaso muji in da ta shiga aiko tace cikin dakewa kai wani irin mara tausayi ne Samad mutum ya dawo a wani irin yanayi baka bincike ni zaka fara min fada.
Yace na fada maki kada ki soma shiga min gida ya kalli security din yana fadin kada ku bari wanan matar ta shiga min gida daga yau.
Security suka ce angama oga yace yayi bai tsaya ba ya shiga mota suka wuce zuwa asibiti ganin ya wuce ta doshi gidan .
Security din suka taso mata nan gardama ya kaure a tsakanin su a gurin muna ciki laraba tazo tana fada muna abinda ke faru.
Muna fitowa falo Fatiya yadda ta gan mu ta zabura tana fadin lafiya dai ko Altine tace yar uwarkice akace ta dawo tana bakin get an hanata shiga gidan.
Gaba dayan mu muka fita zuwa waje a yadda muka samay ta a gurin munyi mamaki duk bata da dadin gani mun karasa ina tambayan security din suka ce umarni ne daga maigidan ya basu.
Jin haka nayi mata wani kallo nace yanzu sai kiyi hakkuri ki nemi maigidan ya basu izzini ki shiga nan muka bar su Fatiha a gurin ta muka juta zuwa ciki.
Fatiha ce ke tambayan ta ina ta shiga hankalin mutane ya baci ga rashin ganin ta tun safiyan jiya ga yarta tun jiyan bayan fitanta tana asibiti bata da lafiya.
Tace wace yar tawa ciki suka ce Sadiya yar jaririysn ta sai tayi wani iri a fuskanta na ko in kula da hakan tace kin san iya hankalin da aka shiga a gidan nan na batar ki kuwa ?
Sun dauki lokaci wurin har lokacin bai dawo ba nan dai cikin hikima suka lalashe ta take fada masu abinda ya faru da su a daji har suka kwana tace wayan ta da jakkarta duk yan Fashin sun kwashe acan haka ta dawo gidan.
Ga kafarta da tayi targade yana mata ciwo sosai don yayi tsami zuwa tanzu tambayan da fatiha ta jefo mata ya bata haushi.
Addah gurin bin bokayen da kika saba kukaje ke nan kuka hadu da wanan kadaran sai yaushe zaki ma kanki fada akan wanan abinda kike aikatawa ne.
Ke ko abinda ya samu matar nan a gidan nan ranan bai isheki kiwa kanki fada ba yanzun wanan abin da kikayi yaya kike son diyan ki da mijin ki su dauke.
Kin wuce kin watsar da diyan ki gashi kin rufe kitchen kin barmu da yunwa in badon wanan baiwar Allah dake gidan nan mun samu ta bamu kulawa da yaya kike son muyi.
Tsawa ta daka ma Fatiya tace wanan ya isheki haka na gane idan na barki a gidan nan watarana zan dawo in samu kun dinke da wanan matar a gidan nan.
Kai ta gyada mata tace ba zan taba cin amanan kowa ba sai dai daga ke har ita zan fada ma duk wanda yayi ba daidai ba gaskiya.
Kiwa kanki fada ga wanan halin da kike yi don zai kaiki a inda baki tsamani ba don daukan alhakin yayi yawa.
Abu wasa wasa har dare suna wajen ganin bai dawo bane yasa suka yanke shawaran zuwa asibiti su duba idan yana can ita da yar uwarta dayan Fatiha tana ciki tana sallah a lokacin.
A asibitin ma sin sha bambam a can basu samu ganin shi ba sun dai duba yarinyar suka juyo zuwa gida sai dai sun samu ya koma gida.
Yana zuwa gida ya shiga gida tare da bada umurnin su rufe maigidan shi bai kara fita ba sai safe don ranan yana da bukatan hutu a tare dashi.
Nashiga gurin shi na samu har ya kwanta a lokacin na karasa yana kwance ya kifa ciki shi kadai a dakin na shigo zuwa bakin gadon na zauna.
Juyowa yayi da fuskan shi yana kallo na nace sannu da dawowa ashe anka maman Ihisan din yace ta dawo dai tunda ta gaba abinda taje yi.
Kallon shi nayi cikin dan mamaki nace wani abin taje yi ashe ina tambaya ina kallon fuskan shi yace idan ba wani abu ina zata tafi tabar yarta mai shan nono.
Ajiyan zuciya na sauke don banda abinda zance cikin fadan mijin da mata nace abinci fa naga har ka kwanta ko yace bar abincin nan bana jin yunwa.
Nace kada ka dinga sa zancen mata a rai ka jawa kanka matsala kuma ki hado min tea kawai zansha na daga har na kai kofa nace ka bada umurini ta shigo ko.
Kallo na yayi ya kawar da kai saina dan tsargu da kallon da yai min din na fice daga dakin zuwa dafa ruwan zafin.
Ban dauki lokaci ba na kawo mai sai da ya sha na kawar da kayan na sauko ba tare da na kara mai maganan komai ba shima dai din bai mun ba.
Ina sauka na shige muka rufe Altine ce take tambayana ko Nafisa din ta shigo gidan daya dawo nace ban sani ba amma ina tsamanin ta shigo ai.
Mikewa nayi zuwa ciki na dan kewa ya ban daki na fito na gyara jikina ban fita falo ba na shirin kwanciya sai ga laraba ta shigo da mami na karbeta na shayar da ita.
Bayan mun kwanta ne har barci ya fara dauka na sai ga Altine a dakin tana fada min ashe Nafisa ba shigo gidan ba.
Karshe ma maigida yace a rufe mai gidan shi tunda ya dawo ta na waje tana hauka da yar uwarta nace badai Fatiha ba tace dayan ai Fatiha ce tazo tana fadi wai ai maki magana ko zakiwa maigida magana don ance yana gidan nace mata kin kwanta tun dazun kin yi barci.
Yau ma Altine yana nufin matar nan awaje zai barta ta kwana ke nan ko may tace wa yaja Khadija itafa tajawa kanta komai Allah ke tambayan ta.
Tun da safe ina karyawa sai gashi a dakin yace zai fita asibiti ya duba su nace adawo lafiya yakai kofa ya juyo yana fadin jiya ya akayi kika shiga motar nan , ?
Baki shiga wanda na baki ba sai wanda aka baki kyauta kikai amfani dashi kin nuna min kin fi bukatan wanan din ke nan ko ?
Kaina na dan girgiza nace wanda na gani a kasa ai dashi zanyi amfani ko don har yau banga wanda ka bani din ba a gidan nan.
May maganan ki ke nufi ke nan ban baki shi a kasa din ba ke nan ko nace bance ba tambayana kayi ai na baka amsa ko ?
Yaushe ma kika iya tuki haka ne ban sani ba nace ni tun ina kaduna nake driving motar ya Adam ai ko don bamu da mota gidan mu kake mamaki haka ?
Wanan kuma maganar kine don zance na bai kai can ba kuma yanzun na fahince ki ai daga zancen ki yana fadin haka ya fita nabi bayan shi da kallo.
Nace a fili tunda ina yar tallaka kana mamakin tukina ko ai samu yafi iyawa yanzu baga iyawan yai min dadi ba.
Matar ka daka wayar kamai da ita mutum a cikin mutane bakai mamakin iyawan ta ba sai nawa ai itace maganin ka a gidan nan.
Tayi yadda take so kuma a zauna lafiya yanzu ai zanga matakin da zaka dauka akan ta gidan nan don wallahi ba yarda zanyi ba.
Yana fita daga gidan asibiti ya nufa sai da ya duba yarinyar ya fito ya leka office bai dade da zuwa office din ba security din gidan ya kira shi.
Kan Nafisa tazo gidan da tashin hankali sai ta shiga gidan fita yayi zuwa gidan inda ya samay a cikin tashin hankali sosai da masu tsaron get din.
Yana bude kofa yace ke wata irin mace ce mara hankali zaki zo ki tara min jama,a a kofar gida na haka ne.
Tace don may zaka hanani shiga gida na don wani dalili naka can yace gidan ki fa kika ce tace idan nan ba gida bane ina kake son in tafi ?
Ida kika fito yace ke ni dai na auro ki ko to kije na sake ki saki daya yau ban son komai naki a gidan nan ki tatara ki kwashe awa daya na baki ki barmin gidana.
Ya juya gurin security din yace kada ku bari ta tafi min da diyana ko ina Nafisa da tayi mutuwar tsaye tun lokacin da ya furta ya sake ta sai da taji yace diya ta iya magana.
Tace diya kan nagama tafiya da abina bandaki wanan musakan zan iya barma ba yace mu zuba ni dake ki gani a garin nan.
Ya shiga motar shi ya tafi ya barta a gurin a cikin tashin hankali ina daki zaune naji hayani ashe itace ta kuma dora laifin a kaina.
Falo na fito na ce ma su Altine don Allah su kyale ta kada su tanka ta abokin mutuwa take nema sai lokacin Altine ke fada min wai ai ya sake tane a gaban kowa.
Da sauri nace subbahanallahi shiko yaya don may zai yi haka da hankalin shi kuma Altine tace ke kan ban san irin zuciyar ki ba wallahi.
Altine ba hakana bane nace wanan abin bashi ya dace da ita ba ai ba a yanke hukunci haka a cikin fushi sakin aure fa ba dadi ne gare shi ba.
Tace ke ai farin ciki yakamata ace kinyi nace saboda an sake ta din tace kwarai kuwa an huta da bakar daga a cikin mu.
Nace Altine ke fa mace ce bai dace ki farin ciki don aure ya mutu ba ko ta bar gidan nan bashi zai sa ta gyara halin ta ba sai ma ta nusa ga halinta mara kyau.
Kin ga kuma ga haihuwa a tsakanin su dole dai ko yaya ta koma a kira ta da uwar yayan shi a garin nan amma in yayi hakkuri ya ladabtata a cikin gidan shi kila idan tana da rabo sai ta gyara halin ta.
Amma saki baida wani alfanu ga namiji zuwa ga mace yanzu ma ko nayi murna ta tafi ai wata zai kara kwasowa gidan nan ko don haka banga abin farin ciki a wanan ba gaskiya.
Laraba tace gakiya ne uwar dakina na gamsu da maganar ki don baka san kalar da za a kwaso maka ba kuma don mazan nan da zaran sun dadana zama da mace fiye da daya a gida ba fasa aure zasuyi ba.
Gara wace ko ka santa kasan halin ta yafi ace a auro maka watacan daban sai dai ita din ce ba abin a tausaya mata ba ko kadan saboda halin tan nan duk da abinda ya faru da ita din.
Altine da magana na bai gamshe ta kitchen ta shige ta barmu a gurin muna magana da laraba ina gurin zaune ina jimamay sai ga Fatiha ta shigo part din.
Bayan mun gaisa take fadin nazo ne ki taimaka min da daysn layin mijin ku don wancen dana sani baya zuwa na ba wanda zata iya samun shi taimin godiya zata fita.
Saita juyo take ce min kin dai ji abin daya ke faru damu ko a gidan nan koda yake banga laifin mijin ku ba gaskiya.
Don yayi iya hakkurin da ake son namiji dashi don haka tsuntsun da yaja ruwa shi ruwa ka doka nace naji zaman jimamay nake a nan din kika samay ni yanzu.
Nayi iya kokari na tun jiya yai min iyaka da zancen su yasa kikaga na sa masu ido tana murshi tace ai ba komai don kinyi yadda duk akeyi don nasan da itace ba zataiwa naki yadda kikai muna ba.
Allah dai ya kyauta har abada ba zan taba goyon bayan karya ba nawa bai kona ni ba nawani kuma ba zai kona ni ba har ga Allah.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/4/21, 9:38 PM - Xxxxx: Ban san ya sukayi da shida Fatiha ba na dai gan su a gidan bayan wasu awowi gaba dayan su sai shige da fice sukeyi a gidan.
Ranan dai gidan ya koma na buzaye kowa ka gani fuska babu walwala a cikin su alamun bacin rai a tare dasu ba sai an tsaya fadi ba.
Shikuma tun da abin ya faru ya tafi bai dawo gidan ba har wanan lokacin magana nayi wa su Altine akan su fita batun su su daina zirga zirgan da suke a wajen gidan ma.
Don kada su dauka ko muna farin ciki da hakan ne gare su Altine tace kai ni kina ban mamaki akan wanan buzuwa ta dauka haka din ne mana.
Idan kece haka ya cika da ke tausaya maki zatayi akan hakan ba nan falon zata fito tana darawa ba murmushi nayi tare da fadin aimu ba ita bace sai mu nuna mata mu din masu tarbiya ne ko.
Baki ta tabe tamike zuwa ciki tana fadin ko dai duk tsoron nata ne haka daga ke har mijin ku shima tunda wanan abin ya faru ya bar gidan nan bai leko ba.
Nace ai kin fi kowa sanin ba matsoraci bane yanzu tunda ya nuna maki namiji yake dake da kawar ki buzuwa ta shige tana dariya ciki.
Mun yi saurin rufe part dina ranan don haka bamu san halin da suke ciki ba sai da safe ne naji ana buga kofan part dina da karfi ina zaune ina karyawa Altine ce taje ta bude kofan.
Shine a tsaye zata jashi da wasan ba,a tace ina khadija tana ciki ta bashi amsa ya wuce ta ya turo kofan ina kafa kai a cup din da nake shan kunun da Laraba ta dama min.
Ina kwana na fara mai yace Deedar waya balla min dayan dakin nan ya shiga nace tunda na haihu ban taba zuwa gyaran wanan dakin ba asalima ai bakaji na karbi key din ba da sunan zan gyara shi.
Wani iri yanayin fuskan shi yayi a lokaci guda ya furta Nafisa nafiki iskanci wallahi ya juya ya fita da sauri dakin.
Mikewa nayi na fito falo motsin da naji a kitchen na leka inga wace ke ciki Altine ce a kitchen din itama ganina ta juyo tana fadin mijin ki lafiya yake kuwa naga ya shigo a fusace yau ya kuma fita a hakan.
Nace shine nima abinda ya fito dani yanzu don ina ganin anmai barna a dakin shi da yake aje kayan sirin shi ne tace dan gado baya barin gado.
Wa zai mai inba wanan matar tashi ba suna fita a gida haka banza ne dama ai sai sun samu barnan da sukayiwa miji suke tafiya.
Tun jiya naso ince mu saka ido akan komai sai kuma maganan da kikaimuna ya sare min kafa da zancen nace yanzu ai ya fita.
Sanan may zaki iyayi akai Altine wanan tsakanin su ne don yafi kowan mu sanin halin matar shi ai .
Tunda ya fita da safen nan sai daya ya dawo yana shigowa muna falo zaune sai wayan shi yai kara ya daga kafin ya amsa muna gaisuwa.
Naji yana fadin OK ok yayi kyau an karbo yarinyar da kayan ko ya tsaya saurara sai yace No yarinyar dai da kayan zaku karbo min ku barsu su tafi su.
Ina ita Sadiya bakina ya subuce ya tambaya sai da ya gama sauraron mai wayan yace min tana asibiti dasu momy yau za a sallamota dai.
Wanan bata da imani tafiya tayi tabar maka yar jaririyan anan ?
Zama yayi a daya daga kujerun falon yana cewa kudina dake gidan nan dawasu abin amfani na ta kwashe zata tafi dasu.
Haka suke ai dama inji Altine sai sunyiwa gida tas suke tafiya su tsiyata mutum gaba daya Allah ne ya taimake ka ai.
Hannun shi yakai a goshi yana fadin bari Altine yadda matan nan tasan ina aje abu haka a gurin nan yake ban mamaki kuma ba ita kadai ta budeshi ba dole da taimakon maza ta iya bude gurin nan.
Wanka yayi ya fita ya dauko su momy daga asibiti sai yarinyar ta baka tausayi sai gashi ya shigo dauke da kwalayen madara wanda za a dinga bawa yarinyar tasha.
Zuwa dare su Ihisan suka shigo gidan tare da Samira munyi mamakin ganin samira tare dasu shima yana fitowa yace yarinya daya ya ba da umurnin a dauko sukai mai bayanin taki bin uwar ne anyi rigima sosai tace bazata bi uwae ba suka tafi suka barta nan shine dalilin dauko ta.
Ni dai tunda yaran suka shigo banyi magana ba sai ma Ihisan datazo gurina ta kwanta ita kuma samira ta kwanta saman dogon kujera.
Tunane nake na abubuwa da dama a raina har dare yayi ina son kwantawa ga yaran banji yace wani abu a kan su ba.
Momy ne ta ce sani ki shige abinki ki kwanta bar mu dasu a nan har safe muji abinda ya yanke a kan su din.
Cikin dare ma banyi barci ba sai tunane nake barkatai sai wani lokaci na samu barci ya dauke ni a gurin.
Kukan yaran ne ya falkar dani daga barci na tashi na samu momy na rarashin su na zauna ba karbi yarinyar momy dake zaune a gefe na tace ni wanan matar alamarin ta ya daure min kai yafi karfin mamaki.
Anya barin yarinyar nan datayi ba da biyu tayishi ba don shu,umancin ta yawa ke gare shi nace momy ni abin ne ma na kasa fasarashi wallahi.
Nan ta fara bani labarin a cikin dare yanyala ta gudu ta falka ta nemay ta bata ganta ba a asibitin sai da safe ne da yaje yake fada mata abinda ke faruwa.
Nace raina ya bani zata dawo gidan ai tace nima dai haka nake tunane a raina tun dazun don dawowan yarinyar nan da biyu ne gaskiya.
Mun dauki lokaci a dakin muna maganan da momy kafin in koma barci ita kuma ta mike zuwa sallah.
Da safe ya shigo gaida su momy ne yake fada mata zai bayar da Samira a ranan abi uwarta da ita koda ma bata je gida bane a je mata ita can garin su don bai dauka gida ta tafi ba.
Don a maiduguri aka kama su aka karbo mai kayan shi da yarshi ya ce wanan matar ta fita raina kwata kwata momy don bata da dadi tako ina.
A raina nace yanzu ko lokacin da ake fada ma ai baka ganin laifin ta sai na masu fada ma gaskiya ni ko a jikina kan wanan zancen.
Muryan shi naji yana tambaya na jikin Sadiya din nace tana barci har wanan lokacin a daki sai bai kara magana ba.
Kamar yadda yace haka ya fita da Samira a gidan ashe tafiyan ke nan bai dawo ba sai dare momy ke tambayan shi yar yace yaba da kudin jirgi an kaita Niger ai.
Allah ya kyauta momy tace mai ya fice zuwa part din shi sai dana dan jima a zaune na mike tare da daukan kayan abincin shi na samay shi a dakin.
Na shigo yana amsa call dan haka na samu wuri na zauna a gefen shi ya dan dauki lokaci yana amsa wayan.
Ya gama ya juyo yana ce min na san kina da hankali Deedar zaki fahinci halin da nake ciki a yanzu ki taimaka ma momy ku rike min yaran nan a dan zaman da momy zatayi kafin ta wuce wani sati.
Zuwa lokacin na gama yanke shara akan yaran na samu wace zata rainan min su a gidan nan don banson inyi nisa da yara nan ko kadan.
Nace yara ai na kowa ne sai dai ina gudun abinda kaje ya dawo ga zaman su a wurina a matsayin su na diyan kishiya na kishiyar kuma irin matar ka da bayarda da Allah tayi ba.
Cikin tsigar rarashi ya soma magana tana fadin kece hope dina yanzu kan yaran nan don nasan zasu samu kula yadda ya kamata a gurin ki.
Idan kin rike min su da zuciya daya Allah zai baki lada akan riko da kikai masu din darajan ki kuma agun yaran zai karu ne.
Nasan kina kokari akan iyalina khadija ina son ki kara duk da kalubalin da zaki samu duk da haka ina son ki daure ki rike min su amana.
Ni dai tunda ya fara magana ban yi magana ba sai sauraren shi nake yi na rasa may zance mai don yadda nake ji din a lokacin.
Wani nayi ya dauko ya kara dorawa a kaina har yaushe nakai munzalin daukan wanan nauyin ya dora min kuma akaina.
Shirun da nayi sai naji ya rungumoni ta baya ya zauna dab da ni ya kare matse ni a jikin shi da alama hakan yana rage mashi itin radadin da yake ji a zuciyar shi a lokacin.
Can dana ji shirun yai yawa na daure nace dashi ga abinci can na hada ma a dinning cikin karfin hali ya mike zuwa wajen abincin ya dan taba yace ya koshi.
Har na fita na barshi baida walwala a tare dashi nima dai haka nake sai dai na dan dake nabar abin a raina ne kawai in ga iya gudun zancen kafin in maganta kada in yi saurin fasa cikina yai min wani fassara na daban.
Don halin maza sai su laifi nasu ne amma sai su so su dulmiya mace a cikin shi su barta karshe da laifi.
Wanan tunanen ne yazo min na nuna mai kamar ba komai a raina kan maganan da mukayi din kafin in samu mafitawa kaina.
Har na mike zan wuce yace baki ce komai ba ga zancen yaran danayi maki dan murmushin yake na kakaro a fuskana nace
Allah ya taya mu duban su ai da na kowa ne ba a san mai kama wani ba cikin mu dasu nan gaba daga haka na juya na fita.
Daki na koma na kira maryam tazo da magana a gidan mu da safe tace zata idan ta fito school tace may ke faruwa ne dan fara fada min dai.
Nace sai dai idan kin zo din mayi maganan zai fi na kashe wayan falo na koma don kada damuwa ya isheni a daki ni kadai a ciki.
Ina zama Altine na fadin ita bata san yadda zata bawa Sadiya abinci ba ta karba nace ta miko min yarinyar in bata tana bani na fara gyara kan yarinyar yadda abincin zai zaunu mata da kyau bai dawo ba na fara bata tana karba.
Ina cikin bata ya shigo dakin cikin shirin barcin shi yana kallon yadda na ke ba yarinyar abinci tana hadiya ya dade a kan mu yana kallon mu kafin yai muna saida safe ya fita.
Zaune nake da maryam a dakina na gama fada mata yadda mukayi dashi tace cabdi jam akwai magana sosai a wurin nan.
Khadija ina zaki iya rika yaran wanan matar yadda yake nufi wani abu yaje can ya samay su ace kece kikai masu sheri don suna diyan kishiyan ki.
Shi kan shi uban ba yarda zaiyi ba idan kin masu wani abinda bai gamsheshi ba duk kokarin da kikeyi rana daya sai ya goge.
A mararaice nace maryam abinda nake tunane ke nan nima wallahi tace idan gaskiya ne don may ba zai kaisu gurin hajiyar shi ba ?
Nace maryam ni ban iya furta mai komai ba har ya kare naganar shi don ni abin ya daure min kai muna maganan sai ga momy ta shigo dakin.
Ganin mu shiru yasa zata juya muna hada baki gurin fadin momy shigo mana ai ba wani magana mukeyi ba.
Tana zama nace momy dama akan zancen yaran nan ne na buzuwa sai nake fada mata zancen da mukayi da AA din .
Katseni tayi tana fadin ai nasan ba zai fara ya dumfari hajiya da yaran nan ba tun jiya maganan da muke ke nan da ita karshe ma ta fada ma Alhaji ya datse zancen da ba a gidan shi ba.
Hakkuri zakiyi don inda tanice wallahi zan iya kama yaran nan may ye a cikin rika su din ai duk yiwa kai ne amma matsalan shine Alhaji.
Karshe dai ba mafita momy tace in bishi a sannu tunda yace zai samu wace zata kula mashi da yaran a gidan sai in daure in kama mashi na dan lokaci a gani.
Satin dana koma schools a satin momy ta barmu ta koma kamar yadda mijin ta ya umurce su data dawo gida ga babban sallah daya gabato saura yan kwanaki ayi sallah a lokacin.
Ban sa rai cewa zamu kaduna sallah ba shiyasa banyi wani yunkurin zuwa ba na dawo daga school ne na samu bakuwa a gidan.
Suna zaune a falo tare dasu Altine na shigo muka gaisa nadan dube ta cikin rashin gane ta ko daga ina take Altine ce tace min ai itace matar da zata kula dasu Ihisan itama yar uwar su daga can kaduna tazo.
Dan kallon ta na karayi ina mata sannu da zuwa ta amsa min tare da cewa mun samay ku lafiya ?
Nace lafiya kalau da fatan zamu samu kulawan ki yadda ya kamata tace insha Allahu zata kwatanta.
Sai yamma ya shigo gidan bayan ya dan huta ya fito kafin magariba ya shigo part din yana fadin Altine bazawarin ki ya bugo min waya wai na dauke mai bazawara shi.
Dariya tayi tace ai da ina dashi ba zaka rike ni a nan ba sun gama ba an su ya shigo dakin ya samay yace kin shigo ina wanka.
Nace eh naje in gaida kaine da dawowa yace ya gidan lafiya muke na bashi amsa yace kin ga matar da momy ta samo muna ko ita ma dai yar uwar mu ce kamar Altine sai dai ita a kauye take zaune mijin ta ya rasu ne a baya ta aurar da diyan ta.
Kinga ba yarinya bace itama don Allah ki daure kuyi zaman mutunci da ita kikuma sa ido ga irin kulawan da take ba yaran nan a gidan nan.
Yanzu a ina zata zauna sai lokacin na sauke ajiyan zuciya nace mai sai mu zauna a nan ba na dan lokaci ba ne har uwarsu ta dawo bai ban amsa ba ya fita.
Yana fita nace na shiga uku ni kan a gidan nan baka gama wanan ba ka fada a cikin wanan waini ko wace mace haka take rayuwa irin nawa ne a gidan ta.
Matar mai suna Shatu bata da yawan hayaniya sai dai kamar tana da zafin rai da yake ni ba zama nake ba ban san wani hali nata na boye ba.
Zaune muke a falo maryam ta sayo min abinda zamuyi amfani dashi na sallan ita da Altine suka fita zuwa kasuwan don ban yarda naje kasuwa ba banyi arba,in ba.
Laraba ce take kokarin kwashe kayan ta dauki kwandon tumatir take fadin shatu ta dan kama mata.
Ta cewa laraba ita ba aikin girki aka dauko ta tayi ba gidan don haka ta fitar da ita a cikin zancen aikin su a gidan nan.
Dukkan mu kallon mamaki mukai mata daga can laraba dake fitowa tace amma idan an girka kina ci ko ?
Dakatar dasu nayi da zancen nace haba mama Shatu bai kamata kuna haka ba da girman ku Laraba ki rage sai ki diba zuwa kitchen din.
Tun wanan dole na mayar da hankali ga takon shatu a gidan don yadda take nuna hasala da sauri zata iya cutawa yaran da take kulawa dasu.
Da safe ina shiri nake jin kukan ihisan har dakina na fito da sauri da ga daki ina tambayan may ya samay ta take fadin wai daga shirya tane take wanan kukan haka.
Dan tsayawa nayi ina nazarin yarinyar na kama hannun ta zuwa daki ina tambayan ta take fada min dukan ta tayi da zatai mata wanka yanzun kuma ta kara dukan ta din.
Dan shiru nayi a raina nace matsala ga wanan ga wancan yaya zan fito ma wanan matar don dai a haife ta haife ni kuma gata da rashin fahinta .
Sai da muka dawo da yamma ranan muka rufe don sallah da za a yi a gobe shi kuma zai tafi sallah gida nace mama Shatu dama ina son magana dake don Allah dai kinga yaran nan kanana ne sosai duka bai dace dasu ba a yanzu.
Don Ihisan ta fada min dazun kina dukan ta don Allah mama a bar dukan nan inda hali a tsawata mata dai yafi duka sauki ga yaro.
Yar nan kina tuhuma nane komay ko wani sheri kuma ake son a laka min don hadin ga wanan magana don nasan fada maki wanan zancen akayi.
Nan dai na lurar da ita na kota gane ban sani ba sai dai ina tune a raina idan ma nice ke rikon yaran haka dan abu kadan a kansu zai iya jawo min matsala tsakani da maigidan ke nan.
Washe gari ya tafi ya barmu a Abuja a nan zamuyi sallah mu tunda ba school a gida nake ban fita zuwa ko ina sai dai zaman su Altine ya debe min kewa a gidan sosai.
Sai shirin hada abinci muke yi muna kitchen gaba dayan mu in ka debe shatu dake daki gurin Sadiya da tai kashi tana canza mata pampers.
Sallama kayi aka shigo gidan laraba ce ta leka don ganin mai sallama sai gata ta dawo da sauri tana fadin uwar dakina yau fa muna da baki a gidan.
Su waye na tambaya tace wanan kawar Nafisa din nance tazo tana falo a zaune hannu na na dauraye na fita ina zuwa naga wanan Sabuwa din ne tazo ashe.
Mun gaisa take fadin gurin yara tazo ta duba nace to bari a kawo su ku gaisa na shiga nace Shatu ta fito da yaran.
Tana ganin su tace Ihisan ke ce kika ramay haka kika lalace kamar bake ba daga inda nake zaune ina kallon ta ina dan karkada kafa na.
Wanan ai basai an fada ba yaran nan a cikin kunci hajiya duban yaran ki kazo ko kin zo ne ki fada muna magana a kan yaran nan.
Tace gaskiya nake fada kin san dai yaran nan sun lalace ba haka uwarsu ta barsu ba nace da baku son su lalace ai sai ku tsaya ku duba abin ku ko.
Ta mike tana wani tafiys tare da fadin ita zata tafi dama Nafisa ne tace ta shigo ta duba mata yaran taga lafiyan su.
Sai ki je ki fada mata abinda idon ki ya ganan maki a kan yaran nace mama Shatu shaga da yaran ciki Allah ya baki ladan riko .
Taja tsuki ta fita tana zage zage har kofa na fita na kira security na nuna masu ita kan kada su kara barin ta shigo muna gida don Allah don ba alheri ke kawo ta gidan ba ta buga motar ta ta fita.
Altine tace mai yasa ba a kira ta ba ta yi daidai da yar iska nace ko makiyin Allah yasan yaran nan suna samun kulawa a gidan nan yanzu.
Aikin mu muka karasa maryam ta shigo min da dinkunan na fitar ma kowa nasa na bashi ranan sallah mukayi abin ci da sha iya mu sai security a gidan.
Zaune muke muna hira sai faman ciye ciye suke yi duk abinda ran mutum ke so ba wani sha maki ga kowa dama kuma haka muke ban saka masu ido ga abinda sukeyi.
Yana can bayan sun fito sallah wayan shi yai kara ya dauka ba sallama sai masifa data fara mai ya hada kai dani ana zaluntar diyanta duk yara sun lalace sun fige.
Kashe wayan yayi yana kashewa ya kirani yana tambayan wacece tazo gidan nan bayan shi nace kawar Nafisa ce .
Ina fadin haka ya hauni da fada inda yake shiga ba nan yake fita ba nayi shiru ina sauraren shi ba tare da nayi magana ba na kashe wayan.
Komay ya tuna kuma sai gashi ya sake kira ban daga ba har kiran ya katse yai kira uku ban dauka ba ina zaune ina ba Sadiya abinci ina gani naki dagawa.
Na gama na dauki yarana muka koma daki ban dade da shiga ba sau ga Altine ta shigo tana mika min waya tare da fadin mijin ki yace yana kiran layin ki baki daga ba.
Ta miko min wayan na karba ina karba yana fadin ina kike waya na ringing baki daga ba nace ina zaune a daki ne yace ok.
Kin gane daga yau ban son a kara barin kowa ya shigo min gida da sunan duban yaran nan ban dai tanka mai ba kawai ina sauraren shi.
Naji yace ana magana sai ki kyale mutu kamar bakyajin shi nakai iya wuya dashi nace wanan ba matsala na bane kuma na kashe wayan.
A gaban hajiyan shi yake suna gaisawa tace ma dama ina son ganin ka don may zaka hada yar mutane tana fama da kanta ka dauko wani wahala ka dora mata.
Hajiya banda yadda zanyi ne shiyasa na barwa deedar su a gida amma kasan itama tana da nata diyan ko so kake a tauye ta don kawai tana da hakkuri ?
Nan dai yayi mata bayanin an dauko mai kula da yaran Shatu nacan gurin su tana duba su ai tace duk da haka ai a karkashin ta suke su duka.
Kada kace zaka sa ido da son diya arai har ka kasa ganin kyautatawan da yarinyar nan ke maka
Yace hajiya don haka ne na dauko wace zata kula dasu na musanman a gidan
Tace ka dai ji hukuncin da Alhaji ya yanke akan yaran nan don haka kasa yadda zaka bi da gidan ka a samu zaman lafiya.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/6/21, 8:09 AM - Xxxxx: Zaune dai nake ina washe baki a cikin su amma ta ciki na ciki ina tunanen wayan mu dashi ga sadiya kamar mai wayau idan bani ba bata yarda wani yai mata wani abin.
Ni har na fara tsorata da lamarinta a raina yadda yarinyar tasan dimin jikina da hannu na ko guri nake idan ana gurin da ita zata fara kokarin juya kanta gare ni.
Sai na shiga tsarguwa a raina kodai maganan Nafisa gaskiya ne ita ya tace aka sauya mata to ta yaya na kawar da wanan jahilcin a raina irin nata.
Ga dai su yan biyu zakace bani na haife su ba don kyau da kwarjin yara kara fita yake a idon mutane kulan da suke samu ya saka suna komawa kamar diyan larabawa dasu don shegen kyau.
Fari dai nasan ba nawa bane kadai haka girman jiki sun dauko shi duka biyu don AA da yan uwan shi jajir suke suma haka hajitan su take.
Duk da manyata ya kama ta amma haka bai sa farin ta ya gushe ba sai dai idan ya tsaya a cikin mu ne farin shi ke gushewa.
Tunda nayi sallah ban fito ba don na fara sallah ina dakina zaune anan Altine ta samay ni mun dan taba hira da Altine din ta sako zancen Nafisa ina kaucewa.
Don ni yanzu ban ma son zancen a tare dani da naji ta matsa ne nace Altine ni fa gara ta dawo ta dubi yaran ta yafi mun don ko ban samu matsala akan komai da magidan nan ba akan yaran nan nasan zamu samu saboda yadda yake ganin bamu basu kulawa da ya dace dasu.
Tace kafin in kai ayya kai yana soma shi kulan da kike basu ko yaran ki kin tsaya kin basu shi yaushe shi ko uwar yaran da take nan ta kula dasu hakane.
Ke harfa laifin ki nake gani akan haka wallahi yaushe zan tsaya kula wasu diyan kishiya in bar nawa can su girma suce nice makiyar su nina kore masu uwa gida.
Nan nake fada mata laifina da ya gani tace amma mijin kan buzuwan wanan ta gama dashi ta ko ina wallahi.
Ke nifa tun kan yaran can biyu da bai damu dasu ba kamar ba diyan shi ba wallahi idan kana da matsala da uwar su yaran ba naka bane da zai dinga kin kula su yadda ya dace.
Laraba ce ta shigo muka maida kallon mu gare ta tana dauke da Alamin a jikinta tace uwar dakina yau fa kamar yaron nan baijin dadin jikin shi.
Nace mama nima na kula da hakan tunda yamma yana kuka na bashi nono yaki kamawa sai kuka yakeyi cshine kikaga na goya shi yayi barci dazun.
Tun dare baiyi ba mu kaishi asibiti a duba shi Altine ta fada nace yanzu kan ai dare yayi ina zamu fita da wanan sanyin haka ?
Laraba tace ko in daka albasa mu shafe mai jiki kila mura ke damun shi zai dan sa ya sake zuwa safe mu gani falon muka fito dukan mu muka zauna.
Ina kallon yadda take murzawa yaron albasa a jikin shi da kyau tace insha Allah zai samu sauki don ciwon yara bai wuce mura da ciwon ciki ba wani lokacin.
Sai da ta gama shafe shi tare da shaka mashi hannun ta a hannci ya shaki gafin albasan sosai ta mayar mai da tufafin a jikin shi ta bashi magani.
Shatu ne ta fito daga dakin da take dauke da Sadiya tana fadin yar nan taki barci hajiya tun dazun nake lalashin ta taki shiru.
Tana kokarin miko min ita na rasa yadda zanyi da raina a loacin karban yar nayi daga hannun ta Altine tace a shafa albasan mata ita ma mu gani ai.
Nace Anty lamarin Sadiya ne akwai wuya kin san ita komai nata dan ka,ida ne jikinta ma har yanzu bai tsaya daidai irin na yara ba.
Tace ban ita nan a shafa mata tafi dan uwanta ne da aka shafa mai ta karbi yarinyar daga hannu na tace laraba ta dako mata wani albasan ta shafa mata.
Shine muka samu yaran sukayi barci bayan an masu na gargajiya a gida ko da gari ya waye laraba tayiwa su yan biyu wanka ta kara shafa masu albasan a jiki dukan su aka goya su.
Ya kira wayana har sau biyu ban samu dagawa ba don ban kusa da wayan a lokacin na shigo na samu miscall din.
Wanka nayi na shirya tsab na fita mai falo din gidan dake a gyara tsab sai kamshi yake saboda gyaran dayake samu yanzu.
Nan suka fito suka samay ni muka zauna gaba dayan mu sai laraba dake girkin rana wanda zamu ci take dan tashi lokaci lokaci.
Hira dasu yana dan rage min damuwan dake raina wani lokacin sai dai hiran tasu ce kamar gugan juna don kowa a hasale yake da dan uwa.
Dan gara laraba da Altine akwai dan shiri a tsakanin su sosai daya da wani abu mukaji dirin motoci a hara ban gidan ban kawo shi bane sai da ya shigo.
Da mamaki muke kallon shi ba wanda ya tsamaci dawowan shi a ranan don mun dauka zai dan jima a can ne sannu mukai mai sai dai duk da yana amsa muna hankalin shi yana gun sadiya dake kwance tana kuka.
Ya nufi wurin yarinyar yana fadin yaya kuka barta tana kuka haka yana kokarin dauko ta zuwa jikin shi.
Altine tace yanzu uwar ta aje ta tayi sallah shine ta fara kuka ashe tayi kashi Shatu taje hada ruwa ta wanke mata ne.
Yace shine za a kyale ta tana kuka haka kuma ba wanda ya dauke ta ya juya inda nake yana fadin shiyasa na dawo don hankali bai kwanta ba kan yarinyar nan.
Yanzu ai sai ka kula da ita tunda ka dawo din don hankalinka ya kwanta ko yace wani irin magana kike fada min haka shiru nayi ban bashi amsa ba ya dan kura min ido zuwa dan wani lokaci sai ya kawar.
Ya aje yarinyar ya fara tafiya yace ina twins ban bashi amsa ba Altine ce tace suna lafiya jiya dai ne Al,amin baiji dadin jikin shi ba.
Yace yaya akayi yanzu yana kallona Altine ce tace mai jiyan dai an bashi magani sai kuma Laraba ta shafa mai magani sai jikin yai sanyi.
Baice zai ga yadon ba ya wuce zuwa sama yayin da ake shigo da kayan shi ciki nidai ina zaune a inda nake imani ya cika ni.
Altine tace lalai tsohon nan nasu bai nemi zaman lafiya da iyalin shi ba irin wanan halin daya dauko yana sa mutum sanyi ga abinda yai niya akan yaran.
Ban samu tofa komai a zancen da takeyi sai sauke ajiyan danayi ina mikewa daga inda nake daki na na shige ina shiga Laraba ta kawo min Al,amin wai jikin shi ya fara zafi.
Maryam na kira ina fada mata tace tunda an fada mai bari muga abinda zaiyi idan bai dauki mataki ba sai mu kai yaron asibiti.
Sai wani lokaci ya fito ya fice daga gidan dama nasa Laraba ta kula min da hakan yana ko fita ta sanar min na kira maryam din tace in shirya mu je asibiti da yaron.
Mun kai yaron asibiti sun duba shi suka rubuta maganin da za a bawa yaron sai da na sayo na dawo gida ina hanya naji ya kirani na dauka.
Kina ina ne nace hanya sai naji ya kashe wayan ba tare da yayi magana ba yana kashe wayan nabi wayan da harara na aje gefe na.
Na dawo gida dauke da yaron a kafada na nashigo gidan hannu daya dauke da ledan maganin da na sayo part dina na shiga don babu kowa a falon babba.
Ban jima da dawowa ba ta shigo dakin yana fadin ina kika fito na shigo na samu kin fita ina kokarin dago yaron dake kuka saman gado nace na kaishi asibiti ne.
Duban yaron yayi ya karaso yana taba yaron yace may ke damun shi ne wani haushin shi nake ji a raina ban iya bashi amsa ba sai kokarin dura ma yaron magani da nake shirin yi.
Wani tsawa ya daka min yana fadin bake nake tambaya ba kinyi shiru dago kai nayi nace ni ba likita bace don haka bansan abinda ke damun shi ba.
Naci gaba da bawa yaron maganin da nakeyi din ba tare da na kula shiba yace ok wani zance kike so ke nan kuma.
Har ya kai kofa nace zancen iyakar ka kace in tafi gidan mu nima tunda ban ba diyan ka kulawa yadda kake so ba ko ?
Juyowa yayi yace shi kike shawa wanan kamahin dama don kawai na tambaya akan sadiya nace bazaka tambaye ni ba ai tunda bani ce kaba kula da ita ba.
Duk abinda zaki fada ki fadi nasan haliku na mata duk halin ku dayane a wurin kishi ko kuma don kawai na tambaya shine abin wani zance can ?
Ya fita sai da nagama dura ma yaron maganin nayi tunane idan banyi da gaske ba akwai abinda ke shirin faruwa akaina da yaran nan.
Don yanzu hankalin shi na gurin yaran Nafisa kawai kamar su kadai ne yara a gidan yanzu dayake jini ya dawo min sai ban daga ba don jin lokacin sallah da yayi.
Ina ciki ina hada abinci a dinnng din shi ya shigo gidan na gama na dauka ya shige ashe yana tsaye yana kallo na.
Ina gamawa na juya zan sauka kasa naji yace ina kuma zaki yanzu nace part dina zan koma sai naga ya matso inda nake yace Deedar may yasa kike son bani matsala ne yanzu ?
Dagowa nayi na kalle shi ido cikin ido nace wani abin na sake ma yanzu kuma, ko da yake kasan duk halin mu daya wurin rashin kirki ai.
Murmshi yayi yace kin canza min gaba daya yanzu na rasa may ke damun zuciyar ki a gidan nan gaba daya kin canza dabiun ki gare ni.
Nace dama haka nake ai ko ka manta ne jawoni yayi zuwa jikin shi yace muje ki bani abinci kamar yadda kika saba bani a baya.
Da ke nan yanzu ka san ina da yaran da nake kulawa ma,ana yarana dana haifa don suna bukatana a kusa dasu.
Saboda yaran ne ba zan samu kulawanki ba yanzu nace koya min akayi hakan yasa na iya don kowa nasa ya sani murmushi yayi yace ki ban abinci dai yanzu don yunwa nake ji .
Table din na nufa na fara zuba mai abincin kamar yadda ya bukata yaja kujera ya zauna yana kallon yadda nake zuba mai abincin.
Nagama zan wuce yace ki zauna in gama mana kamar zanyi magana sai kuma naja na zauna a daya daga kujerun wurin.
Kura ma kofa ido nayi hankalina ya tafi ga tunane yace gaya min mai ye matsalan ki danine yanzu da ya kamata ace na samu jin dadi a wurin ki.
Maimakon in magana sai na fara kuka wiwi nace nagaji da wanan zaman haka nagaji nima ka sauwaka min tun yanzu yafi min alheri da zaman ukubar da nake yi a nan.
Shiru yayi baice komai ba sai abincin shi yaci gaba da ci hankali yana sauraren kukan da nakeyi.
Sai atukar mamaki maganar dana yi yake a zuciyar shi jin baiyi magana ba yasa na mike zan wuce sai lokacin na ji yace ki fada min laifin da nake maki har kika iya furta hakan a gare ni gabana kuma.
Baka san halin da ka jefa rayuwana a cikin gidan ba a yan kwanakin nan saboda fitinar gidan nan bankai lokacin daukan wanan kwaram din a lokacin nan ba.
Kasan girman nauyin da ka dauka ka dora min duk kokarin da nake a gaban kowa kake nuna mani rashin godiyan ka baka damu da damuwana dana yara na ba ina tsoron abinda nake gudu tun farko ya faru dani a gidan nan.
Mutum ya tara yara dashi dasu su koma banza a gurin ka gara tun wuri a rabu don ba zan iya daukan wanan wullakancin ba da kurciyana haka.
Ajiyan zuciya naji ya sauke yace yanzu na fahinci kina nufin ban ganin kokarin ki wurin kyautatawa su Ihisan da sadiya.
May zai sa inga rashin kyautatawan ki gare su bayan uwar da ta haifesu ta tsalka ta barsu iyayyena sun kasa rika min ke da kika zauna min dasu ba tare da gardaman komai ba ince baki kyauta min ba kuma.
Ko kinga na nuna bambaci akan yara nane da kike fadin ba zaki dauki wullakaci ba akan diyan ki kasa magana nayi ban iya furta wani abuba.
Yaci gaba da fadin wace tayi min haka ta yaya zan kuntata maki idan ban gode maki ba kin san yara nan kanana ne suna bukatan kulawa don su manta da uwar su a ran su.
Hawayen dake zubamin nake kokarin gogewa da bayan hannu na ina nazarin magananganun da yake min na dadin baki irin ta maza.
Karshe naji yace kiyi hakuri ke uwace yanzu a gare mu kada ki yarda wani yaga sarewan ki tun yanzu a kan gidan nan har a raina maki wayo kan hakan.
Kada ki dauki abinda nakewa yaran da wani manufa na daban kulawa ne kawai wanda ya dace su samu daga uwar su da basu samu ba yasa nake hakan.
Runtse idanuwa na nayi na sauke ajiyan zuciya ina mikewa zan bar wurin naji yace ki zauna mu gama maganar mu kada ki fita haka a fahunci kinyi kuka anan su dauka wani abin ne ya faru tsakanin mu.
Komawa nayi na zauna inda na tashi banji yai magana ba har wani lokaci na dauko na dan kalleshi naga ya mayar da kanshi a saman masangalin kujera yana tunane.
Jikin shi yai sanyi da maganan da na fada farko yasan kawai na kyaleshi ne da kamay kamay da yake min din amma a gaskiya yasan ko waye dole yaji zafin abinda ya nuna min kan yarana
Bai taba kawowa a ranshi nima yanzu na haihu a gidan kuma rashin ba yarana kulawan da ya daina zai iya haddasa wani a zuciyana ba kan yaran balle yai tunanen da yake bai dace ba a fili har kowa ya fahince shi.
Sai yanzu da nayi wanan maganan yake nazarin wanan abin zai iya jawo matsala sosai a tsakanin mu har abin ya shafi yara a gaba.
Gashi tun yanzu shakuwan da muka fara samu a tsakanin mu ya fara raguwa don yadda nake nuna mai din.
Wasu hawaye ne na bakin ciki naji sun kara zuwa min lokaci guda ina kokarin mayar dasu a idona.
Naji ya sauke ajiyan zuciya yace kukan nan da kike haka yana daga min hankalina idan hakkurin dana baki bai gamshe ki bane ki fada min in akwai wani matsala ne sai in sani.
Na dago na dan kalle shi nace rayuwan gidan nan gaba daya ba tsari a cikin sa nike nan a haka zan zaune a cikin kuncin miji dana kishiyoyi ko ina ba dadi.
Mace bata ganin fuskan miji a farin ciki taji dadi ko miji ya zauna da iyalin shi yaji damuwar matar shi kullun sai a dan kuraren lokaci za a zowa mutum sai nayi shiru.
Murmushi yayi yana fadin ina sauraren shi wanan ne kawai damuwar taki a gidan nan ko da saura don ina son in sani ida nake da gyara in gyara nan gaba kamar yadda kike so.
Don wanan kalamin naki naji shi har cikin raina da kika iya budan baki kina ikirarin ke ba zaki iya zama ki reni yaran ki a gidan nan ba.
Ban taba tunanen jin wanan maganan a gareki ba khadija bana jin dadin ganin ki a cikin takura hakan sai inga ban maki adalci ba ban kuma yiwa iyayyen ki ba suma.
Don Allah ki fada min duk damuwan ki dani a gidan nan a shirye nake da in gyara matukar bai saba ma addini ba a gidan nan.
Khadija abinda baki sani ba shine zama dake ya fadakar dani abubuwa na rayuwana da dama da na rasasu abaya a matsayi na namijin mace fiye da daya a gidana.
Ki yarda dani deedar bazan taba cutar ki ko wani naki ba balle diyan dana haifa da zufana don haka ki fada min komay ye damuwar ki kikuma bani second chance da zamu gyara matsalolin gidan nan da kike ganin tauyewa ne a gare ku.
Ajiyan zuciya na sauke don jin yadda yake kalaman shi a gare ni a cikin tausasawa ina jin zuciya ta tana min sayin radadin da nake ji nasa din da farko.
Tunane nake a raina may zan fada mai kuma wanda yai wanan maganan gare ni haka may yasaura in fada mai wanda shi bai san shi akan iyalin shi.
Kallona yake ban sani ba ganin na zurfafa ga tunane nima ya dan hura min iskan bakin sa na bude idona na sauke a kanshi.
Saurin kawar da fuskana nayi gare shi ina sauke ajiyan zuciya yace ke nake saurare deedar nace a hankali ba komai indai zamu samu kulawan ka a matsayin iyalin ka ya wadatar min ga komai.
In dai wanan ne kawai damuwar ki a gidan nan kisa kin samu dama don karatun kine da lalurar ciki yakawo hakan amma kuma nima fa an rageni a gurare da dama kin kuma sani.
Kallon shi nayi da saurin don jin abinda ya fada din yace yes nima indai wanan ne sai ince ni aka kuntatawa don ba a bani kulawan daya dace sai an fara ai min rowa kuma daga baya.
Murmushin karfin hali nayi nace da wanan bataliyan buzayen na gidan ka kake son a baka kulawa komai mutum ke yi idon su akan shi yake.
Murmushi yayi yana mikewa zuwa inda nake yana fadin yanzu ai bataliyan ki suka rage a gidan nan kadai ko su yaya zakiyi dasu kuma ?
Shiru nayi na dan harare shi yace kinyi shiru bakice komai ba nace wanan ai ba su saka ido irin wa yan cen.
Dukawa yayi daidai inda nake zaune yace wani iri naji har cikin raina kamar mai rada yace kin san may kai kawai na girgiza mai khadija ke kadai ce matar da zan zauna da ita muyi magana ta fahinta har mu fahinci juna a natse babu wani hayaniya a gidan nan.
Kalamin ki na yanzu sun sakani jin kunya kaina da nauyin ki a idona ki gafarce ni deedar nasan ban kyauta maki ba har ga Allah kin fada min yaro baida lafiya ban kula ban duba shi ba ni kaina ban san abinda ya dauke min hankali gayin hakan ba.
Ya kara dukowa gab dani yana fadin kiyi hakkuri ki tayani da addua duk da nasan kina min amma ki kara kwanan duk abinda nake Nafisa sai yaran ta nake gani a idona.
Wani iri naji gabana ya fadi sai dai na dake hakan a cikin raina yace na san kowa cece Nafisa nasan ba zata barni in zauna lafiya wanan tafiyan nasan tana can tana shiri akaina sosai fiye dana farko.
Cikin karfin halina nace mai idan sihiri kake tunanen tanayi shi din ma takeyi don duk wanda ke hada wanin Allah da Allah ya zama mushirki.
Kai may zai hana ka dage kana da sani gwargwado na addini yaya idan ka dage komai zata dauko maka akan ta zai koma.
Maganar gaskiya kana da rauni a gurin tsayawa kayi addinin ka kafi bada karfi a girin neman duniya wanda duk abinda ka samu iyakarshi a nan duniya.
Sai nake ganin harda sakacin ka gurin bata dama tana wasu abubuwan da takeyi a gidan nan kiriri zaka kama ta da laifin da ya shafi haka amma babu wani matakin da ka taba dauka kwakwara a kanta don may kuwa baxata ji dadin ta mai da kaimi ga sherin da takeyi ba tunda ta dauka shine mafita a gare ta.
Ka kafa mata tsauraran matakai ka dage gurin ganin addini ya wanzu a gidan ka dole ko batawa Allah ta rage wasu abubuwan da take yi din.
Ka duba yadda Alhajin ku yake tsaye a gudan sa bai ba ko wace mace dama da zata raina shi a matsayin shi na maigida ba garesu.
Kaiko duk wanan abin kayi watsi dasu ka kama akidar turawa da wanda ba naka ba don kawai so da ya rufe ma ido.
Yatsun hannu na ya ja da karfi ina fadin wanan maganan sai da na dan sake kara dan zafin da naji a lokacin.
Yace kika kara fadin haka sai na maki fiye da hakan yace akwai wata wace nake so da har son ta zai rufe min idona bayan ke.
Ko kin mata kece maganin Nafisa a gidan nan kin fada tun kan ki shigo gidan nan kuma na sheda hakan a gare tunda gashi yau kin koreta.
Dan dagowa nayi na kalleshi nace nine ma na koreta ke nan ba kai ba yace akan wa ta bar gidan nan to akan kine ke Deedar dama tace yar matsafa kike kinga kuwa tsafin ki yafi nata ke nan yanzu.
Murmushi nayi don jin abinda ya fada din nace wata sabuwa ke nan yace ai sinan ki yakai har inda baki tsamani ba.
Ni din nace yace yes yana dagawa daga dukawan da yayi a kaina yace yanzu dai jeki shirya don naga kin fara sallah kinga dama kin mata bukulu kin karbi girkin ki tun farko.
Nace ni ban fara sallah ba don ko yanzu wallahi banda tsarki a tare dani yace har da fadin wallahi nace ba karya nakeyi ba ai gaskiya na fada ma.
Mikewa nayi ina fadin ni zan tafi kada yaran su tashi a nemay ni kasa sai dai idan maganan da nayi dazun ya bata ma rai kayi hakkuri don Allah ka gafarce ni.
Haba dai zuciyar ki kika fada min fa kuma gaskiya kika fada idan kin bar abin a dunkule ai ba zan farga haka da saurin in gyara muna kuskuren mu ba.
Baki taba yimin musu ba iyakar ki bakar magana wanda na saba da wanan tun waje baki tsalake umurnina akan wanan maganan ba zan taba ganin laifin ki ba.
Nace Allah ya sauka don Allah a kula da ibada wanda zai zama garkuwa a gare mu da yayan mu nan gaba yace in sha Allah.
Ina kokarin hada kayan wurin yace barin in biki in duba Al,amin da yani nace mun hutar dakai ka bari har da safe idan Allah ya kaimu kaganshi.
Yace rowan dan nawa zaki min nace ban maka rowa ba sai ka dawo a tare muka sauka zuwa kasan don ya duba yaron sai dai mun samu sunyi barci da laraba a daki na ko yasa yai muna saida safe ya koma.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/8/21, 8:34 AM - Xxxxx: Tun dana dawo part dina na kasa barci saboda maganan daya fada min na Nafisa dake mai gizo a ido ke nan Nafisa bata bar bibiyan shi ba ko a can.
Tunanen samun mafita ga wanan alamarin nakeyi a raina har nakai wani lokaci dare ya raba sosai san nan na tsaya ga shawaran dana yanke a raina.
Ya zama dole in tsaya tsayin daka in koma ga mahallicin mu Allah in dukufa dakai kuka na gare shi in dukufa da fada mai damuwan mu gaba daya don samun mafita a gare shi.
Da farko dai na yanke shawaran zan kula da maigidan in mayar da hankali akan aure na sai kuma in kaifafa katfin ibada na dare da rana in yawaita karatin kur,ani da sadaka da taimakon wanda nafi mabukaci.
Da ire iren wanan shawaran ne nakai karshe har barci yazo ya dauke ni ban sani ba a gurin.
Kamar yadda nasa a raina haka na mike gabanin asuba da yake ba sallah nake ba na zauna na dinga tasbihi har zuwa bayan sallah asuba.
Wanka nayi ban kwanta ba, sai dana gama shirina na fito zuwa hada breakfast koda Laraba ta fito ta samu har na kusa hasawa dan wanke wanke da goge wuri ta tayani.
Part din shi na nufa nakai abin karyawa na jera mai kofan dakin shi yana rufe har lokacin don haka na sauko kada in tayar dashi tunda ba aiki zai fita ba ranan.
Na dawo na samu laraba ta gama shirya yaran nan na zauna falo gurin ta muna hira sai gashi ya sauko yana saye da dogon jalabiya baka a jikin shi mai taushi.
Sallaman shi muka karba tare da gaida shi ya karasa inda nake zaune ya karbi yaron a hannu na yana tambayan yaya jikin nasa ?
Nace jiya yayi barci sosai baiyi wani fitina ba yau kuma koda ya tashi babu alaman zazzabin a tare dashi kuma.
Dan wasa yayi mai kafin ya ajeshi ya dauki mami a hannun Laraba yana fadin Laraba wanan yarinyar kamar tana fin babana girma fa.
Tace ai ya dan fada ne saboda dan zazzabin nan dayayi kwana biyu amma ba wani finshi tayi ba gasunan kamar su kadai ake kiwo a gidan nonon uwar tasu yana da kyau sosai sai kace madara ake basu.
Daga inda nake nace mama kamar kin san nakusa fara basu madara tundai tsotson daren nan da suke yana damuna sosai wallahi.
Juyowa yayi inda nake zaune yana fadin idan kin hana su abincin su saidawa zaki yi komay ba wani madara da za a basu tunda suna jin dadin wanda Allah ya wadatar dasu din.
Nace don bakai ake wa wanan tsotson bane yace ki dai daure ki barsu su sha abinsu don Allah ban faye son wanan madaran ba da akeba yara yanzu.
Altine ce daga bayan shi data fito take fadin ina kwana tsohon su yace a, a manyan mata sai yanzu aka tashi ke nan.
Tace na dan koma na kwanta yau matar ka ce ta girka muna abin karyawa da kanta ta fara kyarkyaran mijin ta ke nan .
Nace kai haba Anty daga na taimaka maku kuma kudan huta bagashi shiga kitchen dina yasa kin dan samu runtsawan safe ba yau.
Sadiya basu tashi bane ya tambaya nace da safe dai ta falka an bata abinci ta koma barci Ihisan ko sai zuwa goma don ba school tana hutawa.
Ya juya dauke da yarinyar a hannun shi ya fita daga part din sai dan wani lokaci kiran shi ya shigo min na daga yace breakfast zaki bani nace ok gani nan zuwa.
A zaune suke a dinning din suke zaune yana ma yarinyar wasa na karaso ya tsura min ido har na iso gare su ina fadin yau kuma abincin sai nazo za a ci.
Yace ba haka kika saba min ba da sanyayyar murmushi na sauke a fuska na don jin may yace din yace koba gaskiya na fada ba.
Murmushi na sake yi na bude warmer din na fara zuba mai abincin ido ya kura min yayin da hannun shi ke ma yarinyar wasa nazarin nayake sosai yadda ban nuna abu a cikin wasan dadi sai abin yai mugun damuna.
Daren jiya shima ya dade yana tunanen magana na yayi nazari yagano rashin kyatawan shi sosai don yasan ida Nafisa ce yaiwa hakan da wani ya jisu a gidan tuni.
Sai yaji ba dadi a ranshi irin yadda yake min abubuwa ina hadewa ba tare da nuna damuwa ba sai dai indan yaba baka in bar maganan.
Dagowa nayi da niyar in tambaye shi idan abincin ya isa hakana sai naga ni yake kallo cikin wani irin yanayi na damuwa murmushi muka sauke wa juna nace wani abin nayi kuma ko kake min wanan kallo ?
Yace har yanzu hakkuri nake son kara baki Deedar kiyi hakkuri da abubuwan da suka faru tsakanin mu in Allah ya yarda hakan ba zai kara faruwa ba.
Kallon shi nayi ido cikin ido na nufe inda yake na mika hannu zan karbi yarinyar nace wanan ya wuce ai tun jiya ni ban rikon magana dama kasani tunda mun fahinci juna.
Sai dai wani bukata daya danake dashi akan Anty Fati don Allah idan da hali may zai hana itama ta dawo nan da zama yanzu mu zauna tare tunda can din ba ko yaushe kake samun zuwa ba akai akai.
Kina son kawo wanin zance ke nan a tsakanin mu yanzu kuma nace ba haka bane yaya kawai dai naga kamar shima wani nauyi ne a kan ka.
Sai dai naga kamar dawowan nasu nan zai sai kuma nayi shiru don irin kallon da yake min din yasa na kasa karasa abinda zan fadi din.
Ki bar wanan zancen don baki gama sanin ko waye Fati har yanzu nace koma may ye dai iyalinka ne itama diyan ka ake cutawa don sune har yanzu ba shakuwa a tsakanin ku.
To yanzu may kike son inyi ita fa ta zabi zaman kaduna bani na mayar da ita dole ba can so ki bar wanan zancen don Allah nace Allah ya kyauta.
Ya juya ya fara cin abincin shi hankali kwance ba tare da ya kara magana ba na mike da yarinyar a hannu na na nufi inda yake na kai mai kiss nace hucewan ka lafiya yayan mu.
Murmushi ya sauke yana fadin kin kuru wanan ya fanshe ki gare ni don dana bata maki rai kan wanan maganan nace a dai yi hakuri damu dan Allah.
Na fice ina fadin barin sauka kafin Altine ta fara min sherin data iya don bai mata wuya yanzu gashi ta fara fadi ko.
Yace kina tsoron ta ke nan indai Altine ce sai kin gaji kin fara bata amsa ai a gidan nan na fice ina dariya na barshi zai shige daki shima.
Na samu maryam tazo duba jikin Al,amin a falon gidan na samay su nan muka zauna muna hira dasu sai gashi ya fito cikin wani shadda Gezenah mai kyau ruwan sky color kalan yayi matukar karban jikin shi sosai.
Gaida shi maryam tayi ya amsa tare da fadin yana gyaran hulan shi yace zan fita zamu dan je wani guri da abokina nace na dauka ai gurin budurwa zaka wanan shigar haka ?
Altine ta cabe da cewa da baki fadi ba ai ke dai kice shigar tayi maki kyau sosai ko nace kamar kin sani anty don bai faye saka kayan gargajiya haka ba sai irin wanan lokacin na sallah .
Murmushi yayi ya fice mukai mashi sai ya dawo sai da ya fita maryam tace ai laufin ki ne da baki tsayawa ya shirya a gaban ki idan kin zabo mai yasa mai zai hana ya saka tunda kina sonsu.
Nace kina ganin idan na shiga dakin nakai dan wani lokaci ban fito ba yanzu Nafisa zata kutsa ciki taga may muke yi kedai maryam Allah ya kyauta kawai.
Don ko yanzu ban debe rai da zata dawo gidan nan ba nan dai nake fada mata abinda yace a gamay da ita din tace dama na sani khadija wanan matar ba kyale shi zatayi ba.
Ya zama dole yanzu gare ki kafinta dawo in ma dawowa zatayi gidan nan din kin kafa gwaunatin ki a zuciyar mijin ku ya zama kin mamaye ko ina a gidan nan ta yadda zata rasa gane kan gidan da komai.
Maryam ina kokarta hakan sai dai kin san shi da bahagon hali shima maryam amma zan kokarta in gani don aikine ja a gabana na yin hakan.
Don gaba daya sun sukurkuta mashi lissafin rayuwan shi maryam yana bukatan sai saiti sai dai na fahinci yana da saukin kai a wurin fahinta idan an sashi a hanya.
Sai yamma ya shigo gidan tunda ya fita daidai lokacin naci kwaliya ina zaune a falon gidan ya shigo idon shi a kaina na kada manyan idanuwa na ina mashi sannu da dawowa ya amsa.
Sadiya dake gefe na ya nufa yana mata wasa tare da dan daukan ta ya dan yi mata wasa ya aje ta tare da tambayan ina su mami na ?
Nace suna ciki ana masu wanka yace kinyi kyau sosai da wanan shigar nace na gode tunda ka yaba min dama don kai nayi shi ai.
Yace idan zan samu haka kullun zan yi godiya a kullun duk da dama kina yi amma shigan kananan kaya kamar sun fi karban ki ai.
Sai bayan sallah isha,i na shirya cikin wani arabian gown daga cikin kayan lefena rigar baka ce sai aikin da akai mata a gaba har kasa ya dane jikina dakyau har zaka iya ganin suran jikina dakyau.
Na shiga wurin shi yana zaune yana aiki a dakin shi ya dago yana amsa min sallama na nace barka da yamma ya gajiya ina zaunawa a gefen shi.
Yace ya kuke nace lafiyan mu kalau yaya dan murmushi yayi yace ba zaki daina kirana da yayan nan ba ko sallon ki yaudare ni da wanan kalman yayan naki.
Nace to yaya zance cikin dan marairaicewa yace wanda ya dace dani mana nace baban twince ko yace kamar wani tsoho can nace a dan shagwabe to nikan yaya zance ma don Allah bayan wanan.
Ke kika sani duk maganan da yake kanshi yana a duke bai dago ba sai murmushin da yake a baiyane a fuskan shi jin yadda nai magana ya dago kai yana kallo na.
Sai naji yai murmushi yace oya ki fadi ina sauraren ki nace sai nayi shawara zan fada ma juyowa yayi ya harare ni da sauri na kawar da kaina ina dariyan kasa kasa.
Mikewa nayi da zumar barin shi ya karasa aikin shi sai naji ya jawo ni da hannun shi guda yana fadin yarinya ni zakiwa wayo.
Juyowa yayi da kyau gare ni yabar abinda yakr yace ki tausaya min hakana khadija ina cikin matsuwa don Allah idan kin san kin fara sallah ki fada min please?
Ya kara matso da fuskan shi ya tokare gadon dani a tsakiyan shi har hancin mu yana gogan na juna magana kamar mai rada ya kara fadin in matse dake wallahi.
Nace wallahi yaya bana sallah dadi yakai ma bakina yace waye yayan naki sai kuma yaci gaba da fadin kamar in kara dokan Allah in badon tsoron shi ba da nake ji.
Nace tunda ya fara daukewa mai zaisa ka kara dokan ubangijin nasan nan da kamar sati biyu ko uku zai dauke gaba daya ne.
Ya goga fuskan shi saman nawa yace baki da tausayi wlh kin ma rainani har tsawon sati biyu kice jiya kika haihu ma.
Dariya nayi ya sake matso dani a jikin shi yace Allah bakiga yadda kika koma bane jegon nan yai maki kyau kamar in hadiye ki nake ji.
Nace kai ka taba ganin inda aka hade mutum da ransa yace da wuya in ba a fara kaina ba yanzu nace da ka amayar dani ba shiri idan matan ka suka gane hakan.
Juyawa yayi ya mike zaune ya koma inda yake yaci gaba da aikin shi na mike zaune naji yace yaushe ne zaku samu hutu.
Nace kasan bamu wani dade da komawa ba ai ina ga sai nan da wata da wata biyu mai zuwa yace ok na dauka ai ba zaifi wata daya mai zuwa ba don ina son mu fita da kune waje.
Nace da yaran nan kanana haka gara dai a bari idan sun kara wayau ko yace yara zasu hanamu jin dadi ne a can sai dai idan baki son zuwa ne kawai.
Zanso fita mana tunda ban taba fita wajen kasan nan ba ai nakai wani lokaci a gurin shi muna hira kafin na mike na bar dakin .
Rayuwa jin dadi da so da kauna muke nuna ma juna a gidan yana nuna muna matukar kulawa ni kuma ina kokari wurin kyautata mashi.
Har na yi wanka na fara sallah ranan da na fara zuwa gare shi yayi murna sosai da hakan ranan ya tabbatar da kewan da yake fadi na gaske ne har cikin ranshi.
Sai dai banje da yara dakin ba nan na barsu da gwagon su Altine da laraba suka kwana a wirin su sai ma mami ne ta danyi kuka ana bata ruwa ta koma barci.
Muna kwance bayan mun gama azzakar yake fada min zuwa next week zaiyi tafiya kasan waje zai dan dauki lokaci a can bai dawo ba sai dai kuma idan bai samu yadda yake so ba.
Nace idan alheri ne Allah ya tabbatar da tafiyan yace amin yace ina son kiyi min list din abinda zaku bukata a gidan nan.
Nace gaskiya ban tsanmani akwai abinda bamu dashi ba dai a yanzu amma ya bari zan duba in ga abinda za a kara muna.
Yace kina ban mamaki deedar ke wai baki san kice bari ki karba irin na wasu matan nace may ye riba na a cikin yin haka tunda nasan wata rana za,a tambaye ni kan hakan.
Ban taba tsamanin hakan daga gare ki ba idan mutum ya ganki ganin farko sai ya dauka idon ki a bude yake kan komai.
Dan murmushi nayi nace saboda may za ai min kallon hakan yace da anganki anga wayyan yar boko sai dai idan anzo magana mutum zai sha baka sai ya gane halin ki zai fahinci wanan a jinin ki yake.
Na dauki lokaci a dakin muna hira dashi ina sauraren sai jefi nakan dan amsa mashi sai naga ina fahintar wani abin da ban sani ba a gamay dashi.
Ta yadda zan warware matsalolin dake gaba a gidan sai bakwai da rabi na fito inda na samu Altine tana soya muna Irish da kwai na karyawa.
Dakina na shiga nayi wanka na shirya na fito bayan na gama kimtsa jikina na nufi falo anan na zauna na shayar da yara nono nan Altine ta gama hada komai ta samay ni a zaune.
Yau kan amaryan jego sai kyali haka Allah naga dare daya kin sake min ga komai gaba dayan ki murmushi na sauke a fuskana nace kai Anty Altine akwai ki da zolaya sosai yau yau da shiga turaka har kin hango wani canji a tare dani hakan.
Magana take yayin da na shiga tunanen a raina na san dai na gwada amfani da abinda anty Salbiya ta bani abaya ciki ya hanani amfani dashi a lokacin.
Duk da ban son in kasance macen da bata dogara da baiwan da Allah yai mata ba daga ni,imomin mu na mata da muke dashi a jikin mu don ko wace na da nata baiwan da Allah yai mata wanda zata gamsar da mijin ta dashi.
Ina son in fahinci ina ne nake da rauni a cikin halittana bai ko da yaushe in dogara da amfani da abubuwan da ban san abinda aka hada dashi ba.
Idanuwa na nalumshe a hankali ina tuna irin yadda muka kasance dashi a daren jiya din duk da ban yarda cewa abinda nayi amfani dashi din bane ya gigita min AA ba kawai.
Har da gudun mawan dana cire kunya na zake nayi yadda namiji ke bukatan jin mace na bayar da gudunmawa a gurin saduwan su.
Abunda na yarda dashi shine ruwan dumin dana ba amana wurin kula da kaina a lokacin da nake jego ya taimakamin matuka wurin kara hade ni kamar yadda ake bukatan mace ta kasance din.
Sai dai duk da hakan na yarda da kayan Anty salbiya din dari bisa dari don zama babu caji yana kara durkusa da mace a gurin mijin ta sai dai yana da kyau mace tasan may zatai amfani dashi wanda ba zai cutar da ita ba a jikin ta.
Shine ya shigo dakin ya katse min tunanen da nakeyi a lokacin yana saye da kananan kaya a jikin shi da suke kara fitar mai da suran shi na cikakken namiji a fili.
Ihisan tana jikina tana wasa da mami dake shan nono sai sadiya dake wasanta ita kadai a gefe na Altine dake kasa saman carpet ta fara gaida shi.
Ya kallin kayan karin dake gaban ta yace duk wanan ke kadai Altine shiyasa kike wanan kibar kamar wata curi dake tace dan wanan dana zubu har wani kama min ciki zai yi .
So nake in gama dashi in koma ciki in dumama sauran tuwo in dora a kai sai in kara jin dama yace kice in kara yawan abincin da nake kawo muku ke nan a gidan nan tunda na aje acici a gidana yanzu.
Dariya tayi tace ka dauka kowa irin wanan matar taka ne da take wasa da ci ni ina zan iya zama da ciki da yunwa ai sai in zubu rana guda.
Ya juyo gare ni yana fadin ki ban abin kari na tun kan wanan acicin ta hada da nawa robon ta cinye baki sani ba dariya na danyi nace ai tasan dole ta zuba ma naka yana aje wa yan nan diyan nata da suka kwaso ta da ci natsaya ba nono su sha.
Yace ai gara dai suci ko su kara kumari don ina son in gansu ko yaushe bulbul dasu kamar kajin agric a gidan nan ihisan ce ta dago tana fadin Abbi kalli yadda waban ke zukar nono ba kamar sadiya ba.
Ya dan lakuci kumatun ihisan yace itama sadiya ai ta iya tsotson samun nonon dai ne bata yi a bata ya duka yana ma Sadiyan wasa kafin ya dago yace wai ina Shatu ne ?
Altine ce ta tabe baki tace bata tashi ba ke nan tunda kaga ta turo yaran wurin uwar su da safen nan wanan kan bata san may ya kawo ta gidan nan ba ai.
Fita yayi nabi bayan shi da abincin inda na samay shi zaune yana waya na hada mai abincin har na gama bai daina wayan ba.
Dan gwauta shi nayi zan wuce ya jawo ni zuwa jikin shi yace deear kin sakani a wani yanayi jiya zuwa yau nace kana son dawo da abinda ya wuce baya ke nan.
Jayoni ya kara yi zuwa jikin shi yana sunsunan wuyana yace kamshin ki daban ne yanzu deedar wanan kamshin ina son shi wallahi.
Dan murmushi na sake nace kaci abinci kada yayi sanyi please yace ba abinci ne a gaba na ba yanzu deeder juyowa nayi na kalle shi tare da fadin may ye a gaban ka din ba yanzu kace in kawo ma abincin ba kaci.
Sake ni yayi ya dangana da kujera yana kallo na alama nayi masa da ido yaci abin cin ya sauke ajiyan zuciya ya jawo plate din zuwa gaban shi ya fara ci.
Ina zaune na kura mai ido yana cin abincin hankali kwance sai da ya ishe shi yajawo abin goge baki yana goge wa yace abincin nan nadai shine bai min dadi ba yadda nake jin test din naki girkin.
Kai yaya AA har da girkin na Altine zakai wa sheri yace tunda kika fada min ita ta girka naji abincin ya fice min a rai baki san ina gane girkin ki bane a gidan nan.
Sai idan kin so muna sheri sai ki bar wasu su girka abincin da mutum bai iya ci nace yanzu ai shike nan sai in dinga girkawan dama taimakona ai tayi tunda taga ka wahal dani daren jiya din.
Murmyshi ya sauke kawai yana sauke ajiyan zuciya yace tafiyan dana fada maki zanyi sun mai dashi nan kusa ina ganin gobe da dare zan bar gaein nan zuwa lagos don yanzu dole ta can zan tashi.
Nace kusa haka kuma yace ko in fasa ne mu zauna da sauri nace haba dai idan baka fita nemo muna na kan mu ai za mu durkushe ne kuma.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/11/21, 8:35 AM - Xxxxx: Washe gari da karfe uku ya dawo gida ya dade zaune a part dina yana hira da Altine da shatu sai mama dani dake gafe ina dan saka masu baki a hiran su.
Yaran shi na saman jikin shi duka hudun yana wasa dasu sai dai yakai wani lokaci a wurin mu ya dan dube agogon hannun shi ya mike yana fadin Altine bari na shirya lokaci na gaba towa na tafiya na.
Sai lokacin Altine tace au tafiya zakayi yau ashe yace eh tare da dan kallo inda nake yace kuma zan dan jima acan idan na tafi din.
Fatan aje lafiya a dawo lafiya sukai mai dukkan su ukun ya mike yana aje Al,amin da lakuto kumatun Sadiya a gefen shi.
Murmushin jin dadi nayi a baiyyane wanda ya nuna farin cikina a lokacin ya daga min gira ya fita sauke ajitan zuciya nayi bayan fitar nashi a din nawa na dan dade zaune na mike don tuno da signal din da yaimin kafin ya fita par din
Mikewa nayi na binshi nayi dakin bayan ya dan dade da fita daga dakinawa na yafe gyalen kayan dake jikina tare da murza humra a part din jikina na nufi part din nasa.
Ya na tsaye wurin wardrobe din shi yana ciro wasu kaya nayi sallama a kofan dakin nasa hankalina yana wurin abinda yake yi din na karaso wurin da yake tsaye din .
Bayan shi da bani na rungmay ta baya na kwantar da kaina ina fadin wanan dai kasan ba aikin bane nawa ne don may zaka wahal da kanka gayi ?
Ajiyan zuciya ya sauke don jin jikin mu daya hade a guri daya yace ina son ki huta haka nane nima nasan ba aikina bane ai.
Dan pick kiss nakai ma bayan tare da fadin nace ma nagaji da bautar ubangijina kai dai kaimin wayo don kar in samu wanan ladan na yau dai.
Na raba jikin mu ina karban kayan kala biyu daya dauko nace wanan kawai zaka tafi dasu kai da kace zaka dade a can ?
Ban son tafiya da kaya masu yawa idan zanyi tafiya don kin san ina fita nakan sawo kayan sawana a can nafi gane ma hakan.
Yana magana yana tsure ni da ido nace hakan na da kyau ai don rage wahala tare da fadin na hada ma ruwan wanka kaji dadin tafiyan ke nan ko ?
Jinshi nayi a baya na ya rike min weast dina yana fadin kin san dai ba zanyi wankan bazan ba haka kawai a wanan lokacin ina dariyan maganan shi na dago ina fadin akwai wankan banza ne kuma ni ban sani ba ai don, , , .
Kasa karasa maganan nayi don jin jikin mu daya hade wuri daya yana kokarin sunsunar wuya na yace kema kin sani ai wankan da baida dalili ai ba wanka bane ko ?
Bakina yake kokarin lalaba ina kokarin zulewa tare da yar dariya ina fadin kai yaya so kake kabi hanya kana jin gajiya a jikin ka kuma ?
Sai da yai nasaran cabka mun dade tsaye muna farautawa juna rai inda na debe nauyi da kunya da girman kai na yi mashi abinda ya kamata ta yadda ba zai manta dani ba idan ya tafi.
Mun dade a tare kowa na nuna ma dan uwa kaunan a fili da kyat ya barni ya jaye jikin shi daga nawa yana sauke ajiyan zuciya na gamauwa da abinda nayi mashi din.
Yace kin biyani bashina da ke kanki deedar nace ai ban san da bashin ka a kaina ba dana dade da biya in huta da nauyin shi a kaina.
Yace ko wanan din da kika fara bani ai na gode nace da saura ke nan dai ban sani ba na fada ina kokarin tsure shi da ido yace dayawa ma tunda an barni maraye a baya sai uwa ta mai sona momy.
Murmushi na sauke ina kokarin dagowa daga inda naya da kaina nace ke nan ka kashe Abba da hajiyan mu damu kannen ka yace kuna raye amma baku damu da damuwa na ba ai.
Mikewa nayi daga gadon kafin ya fadi wani abu na nufi bandakin saida nayi tsarki da ruwan dumi sosai na wanke gurin na hada mai ruwan wanka.
Yana a kwance nace ga ruwan can na hada ma kada ka makara yace sai biyar da rabi zan bar gidan fa don haka ki bari in gama abinda nake tukun don in tafi da dadin rai.
Na nufe shi ina kokarin daga shi don yaje yai wanka ya kara jawo ni saman jikin shi na fada sai tsawon wani lokaci ya kyale ni yana mikewa tare da dariyan mugunta ya nufi bandakin har yakai kofa.
Sai ya juyo yana fafin tasowa zakiyi fa ki min wankan nan tunda ke kika tara min wani gajiyan kuma yanzu duk nacin shi akan hakan ban yarda naje din ba don wankar sarkin da zaiyi din a lokacin yana bukatan natsuwa.
Ya fito na shiga na tsarkake jikina na shirya a nan dakin ban yarda na sauka ba a lokacin zaka dauka banyi komai ba don kaina dana tsane na rufe abinda gyale na saboda manyan matan da nake zaune dasu kada su fahinci komai ga hakan.
Yana zaune a bakin gado koda na gama na juyo gare shi kudi na samu yana faman lissafawa saman gadon na karaso inda yake din zaune.
Ba tare da ya dago ba yace min bissimilah zauna in maki bayanin su kudin na kalla daga inda nake yace wanan Altine zaki ba dubu talatin ne ta rike sai wanan laraba da Shatu su rike ashirin da biyar kan na dawo suma a hannun su.
Godiya na ari bakin su na fara yi yana murmushi yana gidaya ya hada bandur din kudin wuri daya yace wanan ki rike don lalurar ki dana yara kema.
Kallon kudin nayi ba tare dana karba ba nace sai dai kamar sunyi yawa mana yace cikin girgiza kai ba wasu kudi bane masu yawa ki karba ku aje don amfanin ku na fada maki zan dan jima a can din.
Don wurin kasa uku zan ziyar ta zuwa hudu mika hannu nayi ina godiya na karbi kudin daga hannun shi ina mashi godiya ya buge min baki.
Wanan godiyan yai yawa haka nifa zaki taimaka dashi kaina na tsune a saman kirjin shi nace yabawa ga alheri shine yin godiya don haka kabari in gode ma don ka sani na sani wanan kudin yafi karfin aiwatar da wani hidiman gida gare ni ai.
Murmushi ya sauke wayan daya karba yasa na samu silalewa a dakin na nufi wurin yara na in duba su na samu Al,amin yana kuka sai gani karban shi nayi na bashi nono inda na karbi mami ita ma na bata nonon.
Ina gama bata sai sadiya dana daga ina bata abincin ta tasha sosai duk da wahalan da bata abincin yake dashi nakan daure in bata lokaci na wurin bata abinci sai ta koshi.
Nan ya samay ni ina goge mata baki da jikin ta ya dan dade tsaye yana kallon mu kafin yace wani abu akai yace wanan dai dake ta bude ido a gidan nan.
Laraba tace kasan yaro kamar dabba yake mai kula shi yake sabawa dashi tun dai idan yana karami da mai bashi abinci yake bude ido ai.
Yace wanan ai gaba daya ma bata san uwar ta ba sai wanan don ba kulawa take bata ba ko da take nan din, idan ba don Deedar ba da bansan yadda zanyi da wanan yarinyar ba mama ya karasa fadi a cikin yanayin damuwa da tausayawa yarinyar yanayin ta.
Bai samu maganan da ya kawo shi ba Yusuf ya shigo gidan yasa shi fita wurin shi sai bayan fitan shi ne na basu Altine da tafito sakon shi nan suka shiga washe baki suna farin ciki.
Shatu na daki nasa laraba ta mika mata nata a dakin da take bata son fitowa a zauna da ita don irin mutanen nan ne masu saurin fushi ga dan magana kadan sai tayi yar zukut da mutane.
Kai mata kudin yasa ta fitowa dakin tazo inda nake tana fadin munga sako hadiza Allah ya saka da alherin sa ya umfana arziki nace amin mama.
Daga nan bata furta komai ba ko kallon yar renon nata dake wasa a gefena bata yi ba ta mike ta koma dakin su laraba ne ta bita da kallon takaici nayi kamar ban ganta ba ban kuma san may take nufi ba.
Shida saura suka bar gidan inda muka raka shi har bakin mota muna mashi a Allah ya tsare a dawo lafiya.
Yace Amin ya daga yana muna sai ya dawo idanuwa na na lumshe bayan na gama kallon motar tasu data wuce muka juyo zuwa ciki.
Sadiya ce ke dan kuka nake fadin ina shatu ta dauraye yarinyar nan dare na yi kada sanyi ya kama ta shatun na kira sai dai bata karba ba.
Sai can gata ta fito cikin daure fuska tana fadin gata tazo ta tsaya akaina nace lafiya Shatu zaki zo ki tsaya min a kai haka kamar mai shirin fada.
Tace kiran raki ne naji shi kamar da manufa a gare ni yasa na fito jin ba, asin hakan cikin mamaki na girgiza kai tare da fadin dama ba komai nake kiran ki dashi ba so nake ki daureye wanan yarinyar a saka mata kayan sanyin a jikin ta don dare.
Tace duk kokarin da nake a kan yaran nan ba,a gani a gidan nan dazin ma ina jin maigidan nan ke yake yabo a kan su ai.
Bani ba har su Altine dake falon a zaune sai da suka bude baki sona mamakin kalamin ta nace Shatu ban ko iya kiranta da mama din da nake saya masu a gaban su ita da laraba ba lokacin.
Nace kishi kike akan abinda ke wakana tsakanina da mijina a gidan nan komay kuma don wanan maganan naki ya na da manufa.
Tace konayi kishi ai gidan dan uwana ne ko nace idan kuma nace yau ba zan zauna dake gidan dan uwan naki ba ya zaunu a hakan ko.
Tace waban kuma fadi ne don ba yau ba nasan baki da ra, ayina a gidan nan don irin banbacin da kike nunawa tsakani na dasu Altine nasan komai ko sako aka bayar ki bani sai ya fito a hannun su.
Altine tace dani ke nan kike jayayya a gidan nan ni da kika sama a gidan kike bakin ciki da kasancewa na a gidan tunda kika zo kika samay ni a gidan nan kike wanan bakin ciki dama na san ku da bakin hassada.
Nan dai fada ya kaure a tsakanin su waya na daga na kira layin momy bai jima yana ringing ba ta daga kiran na fara gaida ita bata gama amsawa ba nace.
Momy akan shatu na kiraki a gidan nan don gaskiya na fahinci namu dai bai zo daya da ita ba a gidan nan.
Subbahanallahi tace tare da fadin mai yai zafi khadija ban san ki da korafi ba dole akwai abinda ke faruwa ke nan tsakanin ku.
Momy kawai dai ba zan iya zama da ita bane don kauce wa matsala murmushi naji tayi yayin da sukai shiru suna sauraren wayan nawa.
Nace momy ba zamu jittu da ita ba a hakkura kawai indon yara ne a barsu a tsakanin mu zamu rike su insha Allahu.
Tace bani Shatu din idan tana kusa zan mata magana nace momy ba sai anyi ba don na riga na yanke a raina ba zan zauna ana fitina har abin ya kai akaina ba wata rana nake ma gudu momy.
Tace zanyi magana da ita bata kusane nace eh don ban son bata wayana ma yadda nake jin zafinta a raina na kashe wayan tare da mike na nufi daki na har nakai kofa na juyo nace mama laraba kiwa Sadiya wanka don jikin ta ya baci.
Na shiga daki ya Amina na kira na fada mata halin da ake ciki tare da fadin matar nan ba abokiyar zama bane ya don za,a iya hada kai da ita gaba a cuta min tace kwarai kuwa zan samu momy in fada mata abinda ke faruwa don ta sani.
Bayan min gama wayan na jima a dakin sai da zan kwanta na fito nace Altine ku dauki yaran nan ki kwana dasu a wurin ki don Allah.
Tace angama hajiyan mu na daiyi murmushi na ce laraba ta shige min da yara daki muka kwanta ita ko tana dauka da wasa sai can dare ta fito daukan yaran basu falon duk mun shige mun rufe dakunan mu.
Don haka bata san wani daki yaran suke ciki ba da safe ban kulata ba dana shirya muka fice zuwa school bayan na yi wa laraba magana kada ta kulata don Allah idan tana fitina.
Sai yamma muka shigo gidan ihisan ma bata jima da dawowa ba gidan ina shigowa Laraba tana Sadiya wanka na leka su nafito daga dakin dakina na fada na fara kwabe kayan jikina da tare da watsa ruwa a jikina.
Sallah nayi na fito falon ban jima da zama ba sai ga Shatu ta fito tace nazo ne in baki hakkuri kan abinda ya faru jiya don hajiya Binta ta kirani.
Ni arziki nazo ci ba zuwa nayi nan don wani abubu naga kuna son hada min kai ai min bakin ciki ga samun da nake yi gidan nan.
Ikon Allah Altine dake zaune tana lazumi ta fadi nace Altine ya isa don Allah ban son fitinan nan haka na daga haka ban kara cewa komai ba.
Ta juya zata tafi tana maganganu nace shatu ki shirya da safe za a kaiki gida tace wanan kuma sai idan dan uwana ya dawo daga tafiya yace in barmai gida zan bari nace yayi.
Ta dauka wasa nakeyi da safe sai ga kiran wayan shi yace ta shirya a kaita gida zata fara magana ta kashe wayan sai da nagama shirina na fito falona na zauna ina karyawa.
Kudi da abu a leda na mikawa laraba ta ba shatu nace driver zaizo ya dauke ta zuwa kaduna har gida za a kaita daga haka na dauki hand bag dina dake gefe na rataya tare da daukan mami zuwa waje Altine ta dauki Al,amin muka fice.
Da Laraba taga mun fita an kule ko ina ta rufe kitchen ta shige dakin ta ta fito tayi cin mutunci a tsakar falon ta fice driver ya dauke ta zuwa kaduna.
Mun dawo da yamma na samu ta wuce hankalina ya kwanta dan zama da ita ba alheri bane ga yadda na hango abubuwa da dama a gareta.
A kulun muna waya dashi lafiya zai kira ya tambayi lafiyan mu mudan taba hira maganan shatu ne ya saka na kirashi kawai ranan don banson damuwan shi bansan halin da yake ciki ba.
Yau tun daya tashi hankalin shi ke wurin nafisa ya kasa zaune ya kasa tsaye duk yinin ranan ji yake yana son kawai yayi arba da Nafisa a idanun shi haka yasa washe gari ya katse duk wani abindake gaban shi ya juyo zuwa gida.
Ba wanda yasan da zuwan shi don ranan yana da kwana takwas da tafiya muna hira da dare sai ganin shi mukayi kwatsan ya dawo daga tafiyan.
Kallo daya nayi mai na fahinci akwai damuwa a tare dashi sai na dauka gajiya ne ya kwaso mun tare shi da zuwa ba wani walwala a tare dashi ya juya ya nufi part din shi.
Wanka ya fito mun gama hada mai abinda zaici na nufi gurin shi da abincin sai da nagama jera mai na nufi dakin yana tsaye yana fida riga a wardrobe din shi.
Sallama na yasa ya dan juyo gare ni nasha kwalliya a jikina na nufo shi ina murmushi ta baya na dan rugumay shi ina mashi sannu da zuwa.
Bai wani nuna jin dadin gani na ba a lokacin sai cewan da yayi kuna lafiya yana kokarin kwacewa a inda muke tsayen.
Da mamaki na bishi da kallo tare da fadin lafiya ko kake yaya yace may kika gani yana kokarin saka riga a jikin shi.
Tsaye nayi sororo ina kallon shi cikin mamaki hakan bai sa na dadara ba na bishi bakin gadon na zauna tare da fadin sai naga kamar kana cikin damuwa ?
Yace khadija ban son damuwa nan haka da yawa ki barni in huta don ina bukatan hutu ne na dan dade a zaune ba tare da nayi magana ba sai can na mike nace abinci na a dininng na shirya ma.
Yace bazan ci ba a koshe nake jin abinda yace na dago na kalleshi don duk halinda yake ciki idan nayi mai tayin abinci zai dan tsaya yaci.
Sai dai yau naga akasin hakan gare shi gashi ba fuska balle in matsa da tambayan shi na juya zan fita nace ubangiji Allah yai muna saukin koma may nene ke damuwan ka.
Nakai kofa naji yace bar abincin indan ci kamar wanda dama ya matsu in bar dakin nashi dan kallon shi nayi na juya na fita daga dakin.
Ina fita yaji ba dadi kuma a ransa sai dai yadda yake ji din fitan nawa dakin ne alheri a gare shi don wani irin haushi da takaicina yake ji a ranshi lokacin.
Dakina na koma a cikin damuwa sai dai ban iyajin zan koma wurin shi kuma idan ba shine ya nemay ni ba a lokacin cikin dare ma dana kasa barci tashi nayi na dauro alwala nazo zan tayar da sallah.
Ina kallon Labara dake barci da yaran makale a jikin ta na tayar da sallah na laraba sai barcin su suke hankali kwance a raina nace kin huta da jidalin duniya na mazan yanzu.
Salatu tasbihi nayi Allah ya ban sa, a daga laraba har yaran babu wanda ya tashi a lokacin a raka,an karshe ne da nayi sujada na dade duke ina rokon Allah bukatuna daga ciki ko har da sherin kishiya da makiya na duniya a kaina da yayana.
Ina idar da sallah na mike zaune ina ma Allah kirari da sunayen shi tsarkakkaku na dade a wurin kafin in ji kukan mami dama itace mai kwakwan shan nonon dare.
Kukan ta yasa laraba falkawa daga barcin tana dan bubugata nace ta miko min ita a inda nake zaune ga kamashin turare ya karade gurin yana tashi.
Nakai wani lokaci kafin mu koma saman gado da yarinyar mu kwanta da gari ya waye ba school zan shiga ba don weekend ne na kwanta ina ramuwar barcin da ban samu ba da dare.
Sai dai ina jin zuciyana wasai don ba kunci a tare da ni ko kadan a lokacin da ko har jin wani iri nake tun abinda yai min a dakin na fito idan natuna kamar nice bai son gani lokacin.
Gashi ban san abinda ke faruwa dashi ba sai dai hango tsanana karara a fuskan shi da kwayan idon shi a lokacin can cikin barcin dana samu mai dadi nake jin ana dan ja min kafana.
Zubur na bude idona na sauke a kanshi inda yake tsaye yayi kwaliya da gani wuri mai muhinmaci zai tafi lokacin .
Gyara kwanciya na nayi ina fuskantar ya dube fuska a daure yace tashi magana nazo muyi dake jin haka yasa na tashi kaina babu dan kwali ko hulla sai gashina dana daure a baya da ribon sai wanda yadan zubo min daga gaba kadan ina gyarawa.
Ganin na natsu ina sauraren shi don jin abinda zai fada min din nasan abune mai muhinmaci daya shafe mu nidashi.
Ganin na dago ina kallon shi yace Niger zan tafi yanzu in dawo da Nafisa don zata dawo dakin ta wurin yaran ta dani.
Allah ya tsare hanya nace mai ban kara tanka mai ba yace ban son ki dauki dawowan ta da wani fahinta don dama kin san komai.
Nasa kuwa sosai Allah yasa aje lafiya a dawo lafiya na kara bashi amsa tsaye yake a kaina komay yake tunane ban sani ba yaga ina kokarin tashi saman gadon daga zaune.
Sai da na mike da kyau nace mai ko wani abin ne kuma don zan shiga ban daki in watsa ruwa ajiyan zuciya naji ya sauke yace zan kara rokon ki idan Nafisa ta dawo gidan nan ban son tashin hankali don Allah ku barni in huta please.
Ka san ni da tashin hankali ne yaya AA inda dai zaka ya kamata ka tsawata tun a can amma ni may ye nawa na wani tashin hankali kuma.
Tare fa na shigo na samay ku a gidan nan idan naga abin da bai min ba ba matsala bane sai in tatara nawa i nawa in kara gaba inda nafi wayau a zauna lafiya idan dai nice matsalan ku dama.
Wanan kuma wani zance kike son ki dauka kuma ni dai kinji abinda na fadi yanzu na tafi a sauka lafiya na bashi amsa dashi ban iya shiga wankan ba na zauna a bakin gadon.
Tunane nake wanan abin ko na kai sake ne ko kirane dabara ya fado min na jawo wayana dake gefe na kira kakana Bado bayan mun gaisa nake fada mai matsalana.
Yace duk da dai kina kirana akaikai nasan wanan kiran na yau ba banza bane nace kamar ka sani tsoho don wallahi abokin nan dai naka ke son ya dauko min wani fitina kuma.
Yace na sani dama kuma na fada maki zai dawo da matar shi kada ki tayar da hankalin ki ko kadan halinki nagari gare su ba zai barsu su samu nasara a kanki ba da yardan Allah.
Ki bari ta dawo din mu ga abinda zata dawo dashi idan zai yi tasiri a kan ki ke dai ki dage da rokon Allah zan sa ai maki saukan alkurani anan da sadakoki yadda ya dace ayi.
Godiya nayi mai mukai sallama bayan yan nasihohi da yai min akan zaman aure da hakkuri tare da kawar da ido ga komai don aikin asiri bamai dorewa bane yace ko anga nasara akan shi na dan lokaci ne kadan.
Idan da hali yace kwana nawa nake zaton zaiyi a can nace bai wuce kwana biyu Bado yace barin gani idan zai yuyu zan shigo gaein naku yau din nan insha Allahu.
Haka yasa naji dadi muna kashe wayan na ji kamar na kara samun warakan da kunan da zuciyana ke min a lokacin
Mikewa nayi nashiga wanka na fito falo wurin su Altine muna hira tana tsokana na wai taga mijina ya dawo yana daure fuska yau ko ba an da take mai yaki karba mata.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/12/21, 6:57 AM - Xxxxx: Murmushi na sauke a fuskana ina sauraren maganar Altine yayin da cikin zuciyana nake dauke da tarin damuwa ina ji wani iri a raina sai dai ban baiyana hakan a fili ba ta yadda zasu fahince ni.
Nace Altine dan uwan ki ba hushi yake yi da mu ba, damuwa ce tayi mai yawa yana da tarin damuwa yana cikin wani hali da yake bukatan adduan ku a yanzu.
Da sauri ta dago daga ita har laraba dake ba Alamin ruwa tace cikin nuna damuwa ga magana na tace may ke faruwa dashi ne haka wallahi nima naga alaman hakan a tare dashi ai.
Nace buzuwa tayi kiran shi tun daga Canada ya juyo ba shiri zuwa Niger yana can ya tafi ya dawo da ita zuwa jibi nasan zasu iso nan din insha Allahu.
Sai naga Altine har laraba sun wani dafe kirji a cikin damuwa da firgici suna hada baki wurin fadin zata dawo fa kika ce hajiya ?
Nace kwarai kuwa don ko har ya tafi can din don yazo da ita din sai dai idan wani akasi aka samu ne zai sa ba zai dawo da ita din ba.
Nan dai suka shiga fadin albarkacin bakin su akan zancen ni dai ina zaune ina sauraren su ina nazarin maganan su ban yarda na nuna masu damuwa na ba a fili.
Don su din duka dangin miji ne a gare ni watarana nakewa gudu akan su don abu na iya juyewa a tsakanin mu kamar yadda shatu tayi min zuwanta.
Don dangin miji ba abin yarda ba ga matar dan uwan su idan mace nada hankali don duk yadda suke sonta suna da kyashi a kanta a zuciyar su sai dai abar na ciki a ciki.
Ban yarda su san sitin na daya shafi rayuwana sai dai abinda ya shafi cikin gida da sauran su na zahirine zamu zauna muyi hiran shi dasu.
Don kada in shiga daki zuciya ta ta hana ni barci yasa na daure na zauna a falon dasu suna debe min kewa akan damuwan nawa.
Mun kai wani lokaci a falon muna zaune can waya na yayi kara na dauka tsoho Bado ne a layin yana fada min suna hanya zuwa wurina yau yana son min kafi a gidan.
Nace Allah ya kawo su lafiya yace amin muka kashe wayan fita nayi na zuwa bakin get na samu Sanusi security don shi namu yazo daya dashi sosai a gidan.
Nayi mai bayanin komai yace kada in damu idan yazo zai san yadda zai kula da sauran kada su fahinci wani abu akai nayi mai godiya na dawo ciki.
Shi da kansa ya gyara inda kaka Bado zai zauna idan yazo din ya fada masu oga yace bako zai zo su kula dashi idan yazo.
Wurin uku na rana Bado ya iso tare da Al,kassim dayai mashi jagora zuwa gidan namu don shi yasan gidan sun samu taro sosai a wurin mu tunda Bado ya shiga part din naje na gaida shi bai fito ba yana ciki yana aikin da ya kawo shi sai faman fadin yake ayyah kai kasa haba haka da yawa abin yai yawa a gidan nan.
Nidai ba sanin abinda yake nufi nayi ba sai dai binshi da idanu kawai da nake yi.
NIGER REPULIC
Ta gama shiga da fice tana sauraren zuwan shi kamar yadda Yalliya mai magani ya gama tsara mata zuwan shi a duk inda yake a cikin satin.
Ta fito daga cikin dan bukkan gidan su ta zo bakin layin su ta sai dan abinda zata karya dashi don tun safe bata kai komai a cikin ta ba don babu abinda zata ci.
Tafiya take a hankali wasu mata biyu da suka santa suka dan gwauta juna suna gulmanta tunda suka hangota tafe da yar leda a hannun ta.
Taji abunda suke fadi duk da bata ji sosai ba tasan gulman ne akan yadda ta lalace ta zabge kamar ba ita ba ce ke zuwa da motoci tana yadda taga dama a dan kauyen nasu.
Wuce su tayi ba tare da sun gaisa ba duk da tasan su dariya suka saka ta juyo tana kallon su rai bace kamar zatai masu magana sai dai ta kyale su.
Don fada yanzu ba nata bane abinda ke gabanta ya ishe ta a lokhaka ta koma ta dan samu dan kwano ta zauna a tsakar gidan nasu tana cin dan abincin su na kauye data saye.
Fatiha ce ta fito ta kalli yar uwan nata tace dama daga kin gaskiya sai bata kina cikin rufin asirin ki babu ne baki samu a gidan ki.
Kin dauki son duniya kin dorawa zuciyar ki yanzun da haka ta cika dake wa ya kwana a ciki ke kin rasa muda muke ci a inwar ki mun rasa.
Babu takaici kamar yadda kika debo mai kaya kika sa aka tozarta mu a kasan da ba namu ba yanzu ban san da idon da zan kalli mijin ki dashi ba.
Nafisa da sai abincin ta take ci bata kula yar uwan nata ba sai can dai tace Saboda wanan abinda ya amshe ban tsira da komai ba nake son komawa in debi rabona sai nayi mashi tas zan barsu da takaici.
Kallon ta fatiha tayi tace har yanzun dai baki dadara da bin bokaye da malamai ba Adda duk kin sai da dan abinda kika samu kin koma kamar wata almajira dake.
Na tabbatar da zaki dogara da abinda kika samo acan zai isheki rayuwa mai inganci har na bayan ki su samu amma duk kin bi komai kin sayar kin mika ma malamai kudi suna maki karyan sihiri.
Tace idan bakin fata kike zaki koyi kunya Fatiha don gidan Samad dai sai na koma Fatiha tace idan ba komawan Allah da Annabi zakiyi mai ba ko yanzu idan kin koma gidan jiya zaki samu.
Don wanan da kike yi kanta tafi karfin ki saboda ta fiki rike makami a hannun ta na tabbatar da in har ta dogara ga Allah ba zaki taba cin galaba a kanta ba.
Maganan yai matukar bata wa Nafisa rai sosai haka yasa ta harzuka ta hau fada ma Fatiha magana cikin bacin rai ita ma.
Har take fadin ta gane da ita makiya ke mata dariya dama ta fahinci tana tare dani ai nan dai sukayi kaca kaca da junan su sai da kyar uwarsu ta samu ta raba su.
Bayan kamar awa hudu da fadan su kowa ya kama gaban shi tana zaune saman wani matacen tabarma wani yaron dan makwabatan su ya fara shigo da kayan abincin da AA ya tsaya ya sai masu a hanya da ya shigo kasan Niger din.
Ido ta zubawa yaron dake sintirin shigo da kayan Fatiha ce tayi karfin halin tambayan yaron wa ke da wanan kayan haka yaron yace bako sukayi a gidan.
Nafisa ko sai tunanen maganan malaminta yalliya take yi a ranta sai zuba ma kofan dan gidan nasu wanda ba wani gida bane ido.
Sallaman da yayi ne ya shigo gidan yasa gaban ta faduwa don sai take ganin kamar mafalki take yi bashi bane ya shigo gidan ba.
Fatiha dake tsaye a gaban kayan ne ta iya taron shi tana fadin sannu da zuwa ashe kana hanya maraba da babban bakon mu.
Kallon Nafisa yake yadda ta ramay tayi baki duk ta jemay ka wani kwano a gabanta da bussashe tuwo a cikin shi da akaci wanda alama ya nuna itace taci abincin ta kasa kawar da kwanon a wurin don kiuya.
Kawar da kai yayi daga kallon ta ya mayar ga mahaifiyar ta data fito daga dan bukkan ta tana son itama ta ganewa idon ta.
Dakin iyayyen su Fatiha tayi mai shimfidan ta barma mahaifin su dake kwance a gefe yana jinya ya dago da kyat shima yana masu sannu da zuwa.
A gurin da akai mai shimfidan ya zauna tare da gaida dan tsohon da yunwa ke barazanar aikwa dashi lahira ga kuma ciwon dake damun shi.
Nafisa na ganin ya shiga daki ta mike da sauri ta fada dakin su tare da saurin canza kayan da ya samay ta dasu don ita kanta taji kunyan a yadda ya samayta ya samu gidan nasu kuma.
Don zuwan karshe da sukayi duba jikin uban ya bata kudi da za ai masu gina a canza gidan amma ta hada ta dunkule ta koma Nigeria da kudin ta halakasu wurin bokaye da malamanta.
Tana shiyawa a cikin sauri wanan zancen ya fado mata a zuciya bata san yadda zai dauki wanan abin ba tunda bata sa zai dawo zuwa yanzu ya gane ma idon shi bata aikata abunda yace tayi ma iyayyenta din ba.
Nan dai ta zauna a dakin don matukar kunya da nauyin samad din ne ya kamata yadda ya samay ta da kuma gidan nasu da iyayyen nasu.
Fatiha ce ta shigo dakin tace lalai bokayen ki sun iya aiki don aiki ya biya sai dai bamu san irin kamun da zakiyi ba a yanzu kuma.
Nan dai fada ya kaure kuma dole taja bakin ta don kada AA din yaji hayaniyan su ya kara raina mata hankali kamar yadda yasha yi mata.
Fatiha tace yazo da maganan maida auren ku ne duk da dama a shiye kike da hakan don da sanin ki hakan zai faru.
Sai dai ina mai baki shawara ki bi a sannu wanan karon ki rike darajan auren ki ku zauna lafiya da kowa a gidan.
Fatiha taci gaba da fadin ba komai da kake so kake samu ba kai tsaye ki dogara ga Allah daya umurce shi da tara mata iya adadin yadda yake so a gidan shi.
Ko ba a fada maki ba wanan da kike tayar da hankali a kanta tafiki da komai wallahi kece dai ba ki yarda da hakan ba a zuciyar ki.
Kinyi saa idon da zuciyar mijin ku ya makance a kan ki nafisa har bai iya hango illar ki a gidan shi don abinda yasa nace ta fiki ilimi da sanin kai shine agaba ke makin sani.
Don haka ne nake cewa tafi ki ga komai wallahi don tana da ilimin da take amfani dashi gare ki da mijin naku a cikin hikima da basira wanda ni na dade da hango haka a gare ku.
Tace zaki uya zuwa ku gaisa yana dakin soro yana jiran ki idan kin dawo zamu karasa magana da muka fara tace da yar uwan nata.
Ta mike jiki a sanyayye ta fita dakin zuwa dan dakin da yake din ta shiga da sallaman ta dakin yana zaune yana kallon ta ta shigo.
A daidai lokacin kuma tsoho bado na can yana aikin cire kafi da sihirin da bokayen ta suka tura a gidan don bai zauna ba tunda ya shigo.
Take gaban shi ya fadi ya rasa may ma ya kawo shi nan yanzu shida ya rabu da kaya a baya hankalin shi a kwance yanzu a gidan shi yazo ya jajibar wa kansa wani wahalan nafisa kuma again.
Sai ya tuna don yaran ta ne kuma shi din ba wai baya son ta bane a ranshi kallon da yai mata ne ya dan razana ta don ba haka yalliya ya fada mata zai faru ba a tsakanin su idan yazo.
Cewa yayi zaiyi kuka ya gurfana mata yaji duniya babu sauran mace sai ita kodai hakan bai faru ba ita dai idan ya dawo da ita din zai fi mata sauki.
Cikin sanyin murya take mai sannu da zuwa tare da gaida shi da hanya cikin sanyin jiki.
Ya dago ya kalleta yace yanzu ke kin ga wanan zaman yafi maki a nan haka dukar da kanta tayi kasa don nauyin shi da kunya da take ji yanzu baki ya mutu murus bana fadi kuma.
Tace nasan nayi ba daidai ba a baya abinda nayi na nuna son kai da bin shawaran kawayen bariki a kasan ku wanda ashe abin ba haka yake ba.
Nai ma alkawari idan na koma yanzu zaka ga canji a gidan ka a tare dani idan Allah ya yarda cikin nadama da zai iya yarda da tuban ta.
Yace idan kin yi hakan kin kyautawa kanki na baki yau zuwa gobe ki gama shirin ki mu koma tare dake.
Wani irin ajiyan zuciya ta sauke don jin abinda ya fada ya mike ba tare daya tsaya sauraren abinda zata ce ba don yana son yaje yayi sallah a lokacin.
Yana fita ta bishi da kallo don ya cika mata ido a gurin ta sauke ajiyan zuciya taga ya koma fari ya zama wani kato har dan tunbi ya aje tace a ranta dan barin ta gidan ashe bai damu da ita ba ke nan tunda had ya samu kwanciyan hankali a tare dashi haka.
Wai shi samad wani irin muyum ne malamin ta ya tabbatar mata cewa ga abunda zaiyi idan yazo sai bata ko digon girgiza da nadaman rabuwa da ita ba a tare dashi banda shan kamshin da yake mata.
Tace ba komai a ranta ta samu din ta koma tunda har yazo din zata dasa a inda ta tsaya sai taga bayan wanan yar iskan da harda yar uwan ta ke ikirarin ta fita wai da munafukan iyayyen sa masu daure mata gindi a gidan.
Don ba karamin shiri tayi akan komawan nata ba don ga haske ta fara gani tunda har yazo din wurin ta.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
Kuyi hakkuri yau ba yawa kun san ranan yau ina gajiya sosai .
1/13/21, 7:23 AM - Fatima Amarya: Ranan Bado bai kwanta ba sai da yayi duk wani abinda yake son yi a gidan zuwa safe ya gama hada komai koda na shiga gaida shi bayan sun karya yake ce min su zasu koma.
Da mamaki na kalleshi tare da fadin tun yau kaka Bado yace to may zan tsaya yi na gama maki abinda ya kawo mu ai sai dai gaskiya duk wanda yai wanan aikin dana cire a gidan nan yana da karfin zuciya sosai.
Ki gode ma Allah dake baki kariya akan hakan don da wanan asirin dana gani a gidan yana aiki a kanki da yanzu sai buzun ki.
Nan dai ya fada min maganganu masu firgitawa yace harda wanda aka tura ai muna a yanzu duk ya karya su insha Allahu.
Ya kuma dasa nasa don neman kariya a gare mu a gidan ya kara da ce min kada kiji komai akan duk wani abinda zatayi akan ku akan ta zai koma komai ta dauko maku.
Ke dai ki kara dagewa da neman tsari a wurin Allah da gafaran sa shine babban mafita a gare ku nayi mai godiya sosai na koma ciki na hado mai tsaraban da zan basu na kawo mai yace a, a ko kufin motar ki ni ba zan karba ba mu dai fatan mu ku zauna lafiya da mazajen ku ku tara muna iyali masu albarka.
Murmushi nayi tare da masa godiya nace da Alkasim zan bashi sako na muka fita nace ya dauka idan sun isa ya bashi a can ya kara min godiya.
Suka tafi suka barni da kewan su a gidan tun tafiyan su na fara aiwatar da abinda ya bamu a kaina da yara na a cikin da bara nake aiwatar wa.
Ya dade a tsaye yana jiran ta don ance tun safe ta bar gidan zuwa wani guri da ba,a sani ba a lokacin ne Fatiha ta samu kebewa dashi.
Tace ka ga farce ni ga abinda ya faru a bayan wallahi bada sani na haka ya faru ba sai da wa yan nan mutanen suka tsayar damu ne na san abinda ke faruwa.
Yace ba komai Fatiha tace duk da haka sai ka kara hakkuri da Adda don bawai ta canza hali bane sai ma abinda ya karu mata daga halin ta daka sani a baya.
Murmushi ya sauke a fuskan shi yace Fatiha na saba da halin Nafisa banga wani abu da zatai min yanzu wanda ban sani ba daga halin ta kuma.
Allah ya kyauta tace don tasan ba yin hankalin shi bane bai a cikin hankalin shi don koda ganin yadda Nafisa ta koma ba zai kalle ta ba ai.
Tunda ta tun karo gidan gidan ta hango motar shi a kofan gidan gabanta ya fadi tsayawa tayi nisa da gidan tana tunanen abinda zata fada masu don tun asuba tabar gidan zuwa wurin malam boka Yalliya don da nisa sosai da kauyen su zuwa wurun shi.
Hango AA ya fito daga gidan ya kara fadar mata da gaba ta karaso don babu yadda ta iya tana ganin kamar tafiya zaiyi ya barta kuma.
Simi simi ta karaso tana kokatin boye ledan data dawo dashi cikin jikin ta da ganin ta kasan bata da gaskiya a yanayin da take tafe.
Daga ina kike haka ya fada fuska a daure yana kallon ta ta dago kai ta dan kalle shi tace daga gidan yan uwa na nake can cikin gari naje in ban kwana dasu ne.
Yadda take in,inaya yasa ya fahinci bata da gaskiya yace shine baki danar da kowa inda zaki ba da zaki fita tace koda na fita babu kowa a kusa lokacin.
Yace ke dai kika sani tunda ba zaki daina wanan halin da kika sawa ranki ba na biye biyen bokaye da malamai sai dai ki sani indan ni kike wanan shirmay babu abinda zan fasa.
Tace wanda yace ma na fito wanan wurin bai fada ma daidai ba ni sada zumunci na tafi yi a gari yace ki shirya don kin san da asuba zamu wuce ban son inzo in samau baki shirya ba kuma.
Tace Allah ya kai mu ta shige gida tana ta kokarin boye galon din ruwan rubutun da ta dauko a hannun ta.
Tana shiga ta nemi wuri ta aje kayan hannun ta tace wa fatiha ina kika fada ma Samad naje ?
Fatiha tace ina maki hani da kiran mijin ki da sunan nan na Samad don Allah kadai takai can a kirashi da hakan don zunubi kike daukarwa kan ki.
Idan na kirasa da haka ki hana shi ya amsa min yar sa ido duk sherin da zaki kulla min an rigaki ko don bakin ciki kinga zan komawa mijina zaki kulla min sheri cewa naje gidan bokaye.
Kai Fatiha ta kada tace ai hannun ka bai rubewa ka yanke ka yar sai dai kaita kayan shi hakana a jikin ka.
Ni ban fada mai komai ba tunda ba hauka nake yi ba da zan bata maki auren ki nassn abinda nake kece dai ke dauka na makiyar ki don fadin gaskiya na gare ki.
Nasan a yau zasu dawo don haka tun tashin mu nasa laraba ta gyara muna falo da ko ina na gidan inda naje dakin shi na gyara da kaina.
Mun gama na saka kamshi a ko ina na gidan tare da abinda tsoho bado ya ban in hayake gidan dashi gaba daya.
Daga nan muka dawo part dina muka gyara komai a ranan na canza komai na part din aikin maryam ne wanan komai sai kyali yake kamar ranan aka kawo ni gidan.
Sai zuwa hudu da wani abu muka rage aikin komai ya kammalu karmar yadda nake son shi wanan karon launin purple da fari ne a part din nawa.
Komai ya canza gaba daya sai mutum ya dauka sabon wuri ne muka koma ga kayan da ta karbo min wurin dinki data kai express akwana biyu aka gama min su.
Sai turare dan arab iri iri data kwaso min da kayan make,up abinci lafiyayye Altine ta girka da abin sha zuwa biyar duk mun hada komai mun kara gyara gidan da part fina duk da baiyi wani datti ba.
Shida da rabi suka diro gidan tare da yanyala da samiha sai samira da tai wani baki sai hakora da dogon gashi ya rage a jikin ta.
Suna zuwa part dina ta nufa da murnan ta sai kuma taja ta tsaya tana bin ko ina da kallo ta sauke ajiyan zuciya.
Na tare ta sosai tare da murnan ganin ta ta dan dade zaune a wurina nake tambayan ta ko tayi ciwo ne tace batai ciwo ba yunwa daine don ba abinci kamar nan ba kulawa da sauran su.
Tausayi ta bani sosai da take min bayanin sai gata tana kuka tana fadin ita ba zata kara komawa can ba.
Hakkuri na bata tare da fadin taje tayi wanka tazo taci abinci tace zataci kafin tayi wanka haka nasa a debo mata abinci ta zauna ta fara ci.
Sai da ta kusan gamawa ne sai ga samiha ta shigo kiran samira din da wanan halin nata na rashin sallama idan zata shigo wuri cikin tsawa na dakatar da ita da fadin ke idan ba zaki sallama ba maza ki fice min a part din nan.
Sai da ta dan kadu tace Sallamu Alaikum na amsa a hasale tare da fadin wanan dabi,an baida kyau don Allah mutum kamar ba musulmi ba shiga wuri ba sallama.
Tace a cikin yaresu uwar samira na kiran ta sai yarinyar ta bata rai nace jeki kiji kiran da ake maki sai ki dawo ta mike zuwa amsa kiran da uwar take mata.
Shiru shiru banji ya shigo ba na daure na mike zuwa part din shi in mai sannu da zuwa dauke da Al,amin a kafada na.
Na shiga da sallama na samu ya fito daga wanka yana saka riga a jikin shi ya amsa muna sallaman tare dan juyowa ya kalle ni ya mayar da kan shi ga abinda yake yi din.
A hankali na tako na karasa shiga dakin na tsaya daga bayan shi ina fadin sannun ku da zuwa an dawo lafiya ya mutanen can ?
Lafiya ya amsa lokacin da yake karasa saka rigar a wuyan shi yace ba tare da ya kallo ni ba fuska ba yabo ba fallasa yace waye kika dauko nace Al,amin ne yace ina mami sai lokacin ya juyo yana fuskanta na.
Nace tana barci bayan Laraba bai sake magana ba sai ya dauki turare yana fesawa jikin shi tsarguwa da mamakin shi ne ya kama ni a lokacin.
Shiru dakin ya dauka na dan wani lokaci juyawa nayi zan fice daga dakin don jin shirun yayi yawa akwai abinda zanci ya fada a takaice.
Akwaishi idan zakaci na girka maku dama don ina sa ran dawowan ku yau au har kirga kwanaki kika tsaya yi ke nan ?
Ban gane ba idan nayi hakan kuma laifi ne komay nace dashi a dan hasale don wani irin mamakin shi nake ji lokacin.
Dan kallona yayi kamar zaiyi magana sai kuma ya basar yace bashi na tambaye ki ba abinci nace ki kawo min dan Allah.
Nace ba laifin ka bane kuma banyi mamaki da ganin haka ko jin haka a gare ka ba yanzu don nasan inda ka fito ai.
Ina fadin haka na sa kai na fita daga dakin jikin shi ne yayi sanyi don yasan ban nuna kishi ba ga dawowan nasu tunda har nazo na tare shi da dawowa.
Amma shi bai san dalilin daya sa tun kan ya tafi baya kaunar gani na ba yanzu yasan ina iya kokarina amma shiya rasa laifin da nai mashi din yake jin haka akaina.
Ina komawa ina jin zuciyana yana min kuna na aje yaron na hada mai abincin nakai na aje mai nafito don yana daki har lokacin bai fito ba.
Na dawo part dina ban zauna falo ba na shige daki na da yasha gyara na alfarma wani iri nake ji kamar zuciyana zai fashe duk karfin halin da naso yi in dake a lokacin na kasa.
Zuciyana ta kasa daina tuna irin kallon tsanar da yake min tun kan yayi tafiya har zuwa yanzu da naje gaida shi din ya na min wanan kallon na rainin hankali.
Tambayan kaina nakeyi may nayi masa wanda ban sani ba may yasa bai min adalci ne idan halin shi na wulakanci ya tashi akaina ya kamata yai min uzuri ko don wani abu.
Hawaye naji yana silalo min a fuskana nace a hankali a fili may nayi ma AA yake son ya tsiro da abinda zai kawo fitina a tsakanin mu .
Why why duk hakkuri na da dauriya baka gani a idon ka ne share hawayen nayi da sauri na jawo waya ina neman layin tsoho bado in fada mai.
Sai da ya gama sauraro na yace kasa hadizatu kada ki damu da wanan don ba haka aka so ba a tsakanin ku kibi komai a sannu da yarda Allah duk wanan abinda yake ji a kanki zai daina jin shi.
Bafa karamin aiki akayi maku a gidan nan ba don har jaki baki da bakar akuya masu rai aka birne don ku aka hada fatar kura dana kare dana bakin maciji akai asiri dashi duk akan ku.
Ni kaina da nayi aikin cire kafin nan ba karanin wahala nasha ba a jikina don bakin Aljannin da aka turo yana maku aiki a gida.
Komai ya wuce da yardan Allah don ba karamin kwaran muka kwasa dasu ba a cikin daren nan danayi aikin a gidan naku.
Ki saki ranki ga kowa kada ki bari kowa ya fahinci kariyan ki har mijin naku da sauran wa yanda ke gidan kafin aikin mu ya shiga kansa.
Jin shiru ga almuru ya yayi sosai a lokacin ya fito a dininng din ya samu na jera mashi komai yadda ya kamata ya bude yaga sakwara ne a ciki.
Sai kulan miyan da ke dauke da dan ganye akushi yafi yawa sai nama dake ciki manyan yanka dasu sai kamshi ke tashi daya buda zama yayi ya fara diba yana zubawa a plate.
Ya fara ci a hankali yaji dadin girkin har cikin ranshi ya lumshe ido a hankali yaci gaba da ci ya kusa gamawa ne sai ga Nafisa ta shigo part din batayi wanka ba har lokacin balle ta canza suturan jikinta daya sha hanya.
Samad kai ka samu abinda kaci mu har yanzu bamu samu komai munci a cikin mu ba yunwa muke ji sosai wallahi.
Kallon ta yayi yace ba abin dafawa a shiyan ki ne yanzu tace da wanan gajiyan hanyar da muka kwaso zamu tsaya dafa abinci yanzu ?
Yanzu kai baga shi ka samu abinda kaci ba har don bamu da gata mu an barmu a zube hakana ni da tan uwa na.
Ya isa dan Allah ban son tsiro da fitina tun yanzu don Allah idan da tasan kina ci may zai hana ta baku tunda ta dafa abincin.
Yana fadin haka ya mike ya shige dakinshi ya barta a gurin abincin ta bude don yunwan da take ji gashi abincin yana daukan hankalin ta andade ba a gamu ba ta zauna ta cinye sauran daya raga tas har miyar bata bar komai ba.
Ta na isa dakin ta ta samu na aiko masu da nasu tace su samiha suci su kwaso mata naman ciki su saka guda guda a nasu suci ta zauna ta kara azawa a wanda taci din a wurin shi.
Sai da ta koshi nak tasha ruwa ta getse tace koma da ta zuba muna wani abu ba zai taba kama mu ba don don mun fi karfinta wallahi.
Yar wahala ina jira in huta ne in karbe yarinya na a gurin ta munafukar banza da wofi kawai wai ita uwar kinibibi da kissa itace gwanar rike mashi yara idan an barsu.
Yanyala tace ai Ihisan ta ban mamaki ji yadda ta nuna kamar ma bata san mu ba a gidan nan hankalin ta duk yana can gurin ta.
Ran Nafisa yai mugun baci tace ashe kuma kun lura da hakan nasan wani sheri tayi ma yaran ta raba ni dasu don ta gaje min su .
Idan da wanan Aljannar ce sadiya kawai ko kallon ta ba zanyi ba taje taita kayan wahala dama ni ban sata a jerin diyana ba can, don taulalin wahala ne kawai.
Yana zaune dakin bayan ya gama salolin shi ya dan duba laptop din shi ya koma saman gadon shi ya kwanta a rigingine yana kallon agogo.
Ba wanda ya shigo dakin a cikin mu har wanan lokacin wani zafi yaji a ranshi ita Deedar tunda ta fice bata shigo ba haka kuma Nafisa bata zo ba har lokacin.
May ye na fushi ga dan maganan nan yace to shima may yasa ya fada min wanan maganan ne don bai kamata ya nuna min hakan ba don ai kulawa dashi na nuna a fili.
Ya dan juya tare da jan tsuki yana ci gaba da tunanen shi sai ga Nagisa ta shigo dakin yana cikin yanayin jin komai bai mashi dadi.
Ya dan juyo ya kalle ta har lokacin ba wani wankan da tayi a jikin ta don yanayin ta kawai ya isa mutum ya gane hakan.
Zama tayi a bakin gadon tana fadin na dauka gajiya yasa ka barci ai ya katseta da fafin may ya hanaki wanka tun dazun da muka dawo har wanan lokacin ?
Ta kai hannun ta saman jikin shi da zuman taba shi ya gwauce yace cikin dakewa tashi ki shiga ki watsa ruwa tace bazan iya wanka yanzu ba don gudun daukan mura.
Kyaleta yayi dole suka kwanta haka na badon yaso ba sai dan tsamin daudan da takeyi sama sama don yanzu ya saba da shakan kamshi ga jikin mace.
Nikan tunda na koma part dina mukayi magana da tsoho bado naji wani kwarin gwiwa yazo min na fito nace akai masu abinci don nasan dare yayi ba zasu girka ba.
Tunda laraba takai mata abincin ta dawo nasa ta rufe part din namu bankara fitowa ba sai washe gari na shirya tsab na nufi part din nafisa na samay su kaca kaca a zaune.
Sai hira suke zubawa a cikin yare suna dariya nayi sallama na shiga gaban Nafisa ne ya fadi don gaba daya na sauya mata na koma mata wata hamshakiya dani a idon ta.
Sannun ku da zuwa nace mata tare da tambayan mutanen gida magana nake tana kallona a cikin mamakin sauyi na da yanayin magana na.
Na juya cikin wani tako da take ganin yanga da sallo nake mata na fice abina ta dade a zaune kafin ta sake wani irin ajiyan zuciya.
Tace duniya ku tabani idan ba mafalki nake yi ba don Allah yaushe nayi sake yarinyar nan ta zama haka a dan lokaci kadan a dan watan nin da nayi bana gidan nan.
Yanyala tace ashe bake kadai kikaga hakan ba nima mamakin sauyawan ta nake a raina gaba daya ta koma wata babban mace da ita.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/15/21, 8:23 AM - Fatima Amarya: Yayi mamaki da yafito ya samu breakfast din shi a dininng na aje mai komai na tafi koda ya sauko zuwa part dina ya samu duk mun fice a gidan kofa a rufe.
Ya tsaya yana mamaki inda mukaje haka ya kira waya bai shiga ba ya kira na Altine ya shiga yace Altine ina kuka ke kuka rufe gidan.
Tace muna nan makarantar su khadija suna wani taro ya kashe wayan tare da kutawa a fili ya koma part din Nafisa a falo inda laraba ta aje Sadiya tana gurin tana ta tsala ihu har zuwa wanan lokacin.
Daukan yarinyar yayi ya nufi cikin dakin nafisa dake kwance tana ramuwar barcin ta hankali kwance ya bita da kallon takaici tare da bugun ta yayi a hasale ta falka a gigice tana kallon shi.
Yace yanzu kin kyauta ke nan kina nan kina barci kin bar Sadiya ita kadai a falo tana ta faman tsala kuka baki damu da damuwanta ba.
Tace Sadiya may ye hadina da ita a yanzu ai na riga na mayar da ita hannun uwarta na ainihi ke nan idan ba diyar ta bace ta yaya zata rike min ita haka kawai.
Wa kallo yai mata na takaici yace Nafisa kina da hankali kuwa wai wanan haukan da kike yi a ina kika taba jin anyi haka ko duk jahilcin ne wannan ina laifin yarinyar nan khadija da ta sa hannu ta rungumay maki diya abayan ki tsakani da Allah.
Wani dariya ne ta sake tare da fadin kai may ka sani ta dai rike yar ta amma wanan mai zubin yan ruwan kan na yafe mata ita harga Allah.
Yace idan kin ce haka zaki yi kuwa ba sadiya ba har ihisan din duk a wurin khadija zasu zauna su biyu tunda ke baki da hankali nagane yana fadin haka ya fita dauke da yarinyar a kafadan shi yana lalashin ta zuwa part din shi.
Bamu dawo gidan ba sai after two ina saye da rigan mu na lauyoyi a jikina na tsayar da mota yana tsaye suna magana da Yusuf su Altine suka fito suna dauke da yarana.
Fuskan shi a kaina har na fito daga motar gaida su nima nayi kamar yadda su Altine suka gaida su sai dai ban tsaya ba Yusuf ne yace yau kin fara fitowa lauyan ki na ainihi ke nan nace wallahi kasan muna gab da gamawa yanzu ba hutu a gare mu.
Daga haka na shige abina Yusuf ya karbi mami hannun Altine mun shiga da gajiya a falo muka ya da zango dukkan mu.
Abinci muke ci ya shigo part din dauke da Sadiya ban dago na kalle shi ba yace tun dazun yar nan tana gurina da kyat na samu ta dan ja fida kadan.
Altine ku karbe ta ku bata wani abu taci don nasan yunwa take ji ga bata abinci da wahala Altine tace ba uwarta ta dawo ba ai an kaita da safe da zamu fita.
Fuska ya bata tare da fadin Altine ku barta a nan gurin ku don Allah fadin hakan da yayi yasa na dago kai da sauri ina kallon shi tare da fadin ta zauna a nan kuma bayan uwarta ta dawo.
Ina don uwar bata nan ne muka rike ta anan din yace kin ji magana na ai nan nake bukatan su zauna dukan su su biyun yanzu yana fadin haka ya juya ya fita daga dakin.
Bin bayan shi da kallon mamaki nayi tare da sauke ajiyan zuciya sai laraba ne tayi magana take fadin ina ganin dai wani abin ne ya faru akan yaran kun san ba kirki ne da ita ba.
To amma mama an taba yin haka don Allah ina don uwar bata nan ne na rike su a nan wurina yanzu kuma zai zo da wanan maganan haka.
Altine tace maganan Laraba ne dai dole akwai abin da ya faru nace ni gaskiya Anty matsalan gidan nan ya isheni haka wallahi.
Hakkuri suka shiga bani tare da fadin don yaga kina rika masa ne a gurin ki ne kadai yake ganin yaran zasu ji dadi kuma su samu tarbiya ni dai shi nake gani kamar hakan ne.
Shiru nayi na kasa ci gaba da cin anincin dake gaba na duk da yunwar da na kwaso a lokacin na mike zuwa dakina wanka na shiga na fito na gyara jikina tare da saka bubu a jikina redmade mai laushi daidai zaman gida.
Falon na fito don kada damuwa ya damay ni ni kadai ban dade da zama ba sai ga text ya shigo min shine ya turo min wai in mashi list din abinda muke bukata a gidan.
Share zancen nayi naci gaba da abinda nake yi nace Anty yau naga kun wahala ina ga zan bar fita yanzu da yaran nan a gida zan dinga barin ku tunda sunyi wayo ko ?
Altine tace wa yan nan diyan nawa dake da yawan tsotso haka zasu yarda su zauna a gida nace idan sun samu madara zasu zauna sai mu gwada a satin nan mu gani.
Tacevto shike nan idai mahaifin su ba zai yi fada akan haka ba nace satin nan ba zamu zauna a cikin makaranta ba don zamu shiga kotu muyi aiki ne a can kin ga ko fita dasu ba zai yuyu gare ni ba ai ke nan.
Laraba ne da gulma yaci ta shigo take fadin ina ganin da mutum biyu kawai aka dawo Altine tace ni tun da suka dawo ban ga ko dayan su ba har ita uwar gayyan tasu.
Ihisan ce ta shigo part din namu da kukan ta sai ga uban ya shigo shima yana zare mata ido yace idan na sake ganin kafan ki gurin su saina balbala ki a gidan nan.
Yana fita sai ga Nafisa a part din nawa ta shigo da zuman masifa sai kuma taja tayi tsaye tana bin part din da kallon mamaki can sai ta basar tace Ihisan fito muje.
Ba zaki zauna gurin wanan matsafiyar ba ya dai bar wanan data sauya ta karasata a nan idan ta iya tayi gunduwa gunduwa da namar ta kafin gobe.
Sai yarinyar ta make hannu taki zuwa tana matsowa da zumar janta ta yanka wani ihu ta nufo gurina tana kuka tsayawa tayi tana kallon mu nace Ihisan jeki gun uwar ki kin ji.
Aiko baki fada ba zata zo ne tunda bake kika haifar min ita ba nace ina yanzu gorin haihuwan nan ya wuce a gurin ki tunda kin tabbatar ni din ba juya bace.
Ina magana kamar banbson yi tare da ahafan kan yarinyar dake kwance a jikina tana kuka au don wa yan nan diyan da kike ganin kin haifa mai masu zubin diyan ke tare wa ya sani ko wani bayahuden kika je yai maki cikin su.
Nayi murmushi nace ba wani baya hude yai min cikin su ba wanan dai da kike hauka a kansa ne yai min.
Wata kila baki iya kwancin bane yasa kika haifo naki a haka don haka ki fice min daga shiya kafin ranki ya baci yanzu a gidan nan don zan maki abinda sai kinyi jinyar jikin ki.
Ya dai ba taki bace tawa ce kuma dole ki bani abina nace diyan ki dai don naji kina magana akan Ihisan kadai kwashi tarkacilen diyan ki ku tafi don Allah banson yawan hayaniyar nan naki a nan kina daman min yara dake barci.
Haushi da takaicin magana na ya kamata a wurin tace don wayan nan diyan da kike ganin kin haifa kibar daga kai a kansu kibari kiga girman su.
Ta Allah ba taki ba in sha Allah idan da rai da lafiya kamar gobe ne kin gani sha kurumin yadda kowa ya girma su ma girman zasuyi da yan uwan su gidan nan.
Ta rasa may zatace ta fice daga part din Altine tace dama na fada maki akwai wata a kasa kyalesu muga iya gudun su gidan nan.
Ko yanzu ki gode ma Allah don ta wullakanta ai ga saki ga yaranta kiri kiri miji ya hanasu zama a gurin ta ko haka ai ci gaba ne a gare ki don ya yaba da ke ke nan.
Wanan yabon kan ai da wahala Anty ace an dauki taulalin yara an dora ma sai sun girma su kama uwar su.
Tace ke dai din ce ba mai son hayaniya ba amma sai naga ko sanan riba ce a gare ki ai tunda duk wani kudin lalurar su yana a hannun su.
Murmushin takaici na sauke nace wanan bai a gaba na sam don ni ga Allah na dogara da lamarina idan rabona ya koka a wurin shi ko bai da niyar bani sai ya bani.
Shiru falon yayi na dan wani lokaci na mike ina fadin bari na dan huta a daki idan nayi sallah.
Na mike suka bini da kallo sai dana shiga ne laraba tace mace mai hakkuri komai tana gani a gidan auren ta don kin san dai wanan maganan ba gaskiya a cikin sa fada ne ba halin ayi kawai.
Altine tace hakkurin yarinyar nan yai yawa wallahi ba zakace zaka samu yaran yanzu da wanan halin ba.
Nan dai suka zauna suna zancen ina ciki bayan na idar na jawo wayana ina fada ma maryam abinda ke faruwa don bamu samu kebewa ba a school.
Ina gama wayan daidai lokacin ya dakin ba sallama balle inji shigowan shi sai muryan shi naji yana fadin baki ga sako na bane dazun.
Nagani nacea takaice tare da juyar da kaina gefe daya na bar kallon shi yace dake nake magana ai .
Nace don banda bukatan komai yasa ban amsa ba idan ma ina da bukata ai kasan duk abinda ya dace a saya a gidan ko ?
Bai iya furta komai ba don yadda yake jin zuciyar shi a lokacin kamar zai tafi yace ba haka na saba ba don haka ki fada min abinda kuke da bukata nace.
Shiru nayi mai ban bashi amsa ba na matsu ya fice min daga dakin ya sake fadin bakiji bane ina magana dake ya fada a hasale.
Nace ka sayo muna abinda ka sai muna last time kafin ka yi tafiya shike nan ko sai madaran yara da za a saya masu kuma.
Barin fada maki ban daukan wanan tsiwan naki yanzu bai kai karshe ba nace ai ba sai ka fada ba don alama ya nuna kansa.
Don ko ganina baka kaunar yi a kusa dakai don haka nima na kama kaina da kai tunda ba dole dama zaman biyayya nake a gidan nan ai.
Kana ja min tashin hankali na ba gaira ba dalili a cikin gidan nan ina zaune ban shiga shirgin ku ba duk da hakan ban tsira a gare ku ba.
Duk hakkuri da dauriya da biyayyan da nake maku kai kan ka baka ganin hakan sai ka cisguna min ka wullakanta ni yadda kake so.
Menene laifina may nayi maka da zaka dauki karan tsina ka dora a kaina don kawai ka cusa min bakin ciki da tashin hankali a zuciyana.
Ya isa haka kin fadi abinda kike son fadi kin gaji dani yasa kike fadan haka sai dai ki sani zama a gidan nan kamar yanzun kika fara don gida ba fita a cikin shi kin shigo cikin shi ke nan.
Murmushin takaici nayi nace tunda kaine autar maza kake ganin idan an shigo ba fita ka sani ni ba irin tarkacen matan ka bane dake tsayawa yin asiri ko wani abu a kan ka.
Yace nasa don nasan ko wacece ke har da halin da baki san kina dashi ba nasani kaita sani mana wanan kai ta shafa kamar yadda kace baza ka dauki halina ba a yanzu nima haka ba zan dauki naku ba a yanzu daidai zamuyi da kowa a cikin ku.
Khadija wuyan ki ya isa yanka nace har datsa ma ya isa ba yanka ba sai ka shirya ka datse shi din ki shirya min abinci irin na jiya don banda lokacin wanan a yanzu.
Kaje matar ka ta shirya ma ita da kake ganin idon ta da kwali a gare ka yanzu dama ku maza haka kuke kun fi son macen da ke latsaku a zauna lafiya.
Yakai kofa ya juyo yace ashe shiyasa kema kike son ki gwada latsa ni din to bari kiji idan kinyi haka ke wuya zaki ji a gurina wallahi.
Haka kace yace ai kin ji na fadi yanzu sanan may ye dalilin ki na kin shiga motar dana saya maki nace don bada zuciya daya ka saya min ba ai ba don ni ka saya ba may ye mutum bai sani ba.
Kallon mamaki yai min yace haka kika ce to in kara ganin kin shiga wanan motar dake ci mun rai idan ran ki bai baci ba a gidan nan.
Wanan din dai da aka bani da zuciya daya zan shiga tunda bakai ka saya min shi ba OK zamu gani dani dake a gidan nan kuwa.
Ya tura kofan ya fita a hasale nace mijin tace kawai matar ka ta bata ma rai kazo nan zaka fashe a kaina don nice marainiyar ka .
Da safe na fito zan fita sai wayau don babu motar a gurin na juya a hasale na shiga gidan zuwa part din shi banyi mamakin ganin kofan a bude ba lokacin don kila haka ya kwana yana jirana.
Yana kwance yana waya na banko kofar dakin wani kallo yai min ya ci gaba da maganar shi na koma gefe na tsaya cikin fushi ina jiran ya gama.
Ina jin ya gama nace ina motana yake don na fito yanzu ban gan shi ba yace nasa an fitar min dashi a gida don nace bazaki kara shigar shi ba ai.
Wani kake son in shiga ina wanda na saya maki din bazan shige shi ba na fada ma baki son fita ke nan gidan nan key din babbar motar shi dake aje na dauka na fita.
Dashi na fita zuwa school din in da zamu kotu yin wani gwaji sai dana biya school na ga maryam na wuce zuwa kotun.
Ranan sai five muka dawo gida Nafisa na samu tana magana a waje da wasu bakin ta yun shigowa na kallon su ya dawo gare ni na fito a gajiye ina rataye da jakana da rigan mu na lauyoyi a dayan hannu na na wuce su.
Uhuumm naji wata tace tace kin ga illar barwa kishiya gida ke nan Nafisa tace ai ni wanan shegiyar yarinyar ban san yadda zanyi da ita ba.
Yaya ko zakiyi da ita banda ki kawar da shegiya ai taki kawowa ne wata tace kafin nan ai shi mijin naku zaki tun kara da yaba ta wanan daman haka kina may har haka yake faruwa ga matar da tazo ta samay ki a daga baya.
AA ya shigo ke nan yana kokarin shiga wanka sai gata ta shigo a hasale tace samad abin naku har yakai can kaba wanan yar iskan motar ka tana shiga don an mai dani banza ko may ?
Amma dai kin san ita din mata tace don haka tana da iko da abina kamar yadda kema kika matsa sai da kika dauki wanda nake amfani dashi a baya.
Tace ke nan don taga na dauka yasa ta dauka yace a ganin ki ba mota dai nawace don haka banga dalilin zuwan ki nan kisani a gaba ba haka.
Yana fadin haka ya shige bandaki ya barta a wurin ina sam wallahi ba zai yuyu ba ta shiga motar dani ban shiga ba yana jin ta tana haukan ta ya kyale ta.
Part dina ta nufa sai ganin ta ta fado muna lokacin ina rungumay da yar ta sadiya ina bata abinci tace ke bani key din motar da kika fita dashi.
Ke kina da hankali kuwa zaki fado min daki haka kamar mara hankali idan kina da karfin kwata kizo ki kwata an ki baki din mota kuma ta zama mallakina daga yau.
Na gane kina jayayya danine a gidan nan nace ashe sai yanzu kika gane hakan ke jayayya ai ya kare tunda na mallaki abinda ke kika kasa mallaka din.
Tace kina nufin don kin haifi na miji gidan nan har zaki min gori a kan hakan nace kaji jahila haihuwan namijin kuma shine abin tsone maki ido ni ban kai can ba.
Bani shige ma Allah a gaba idan kina da karfin kwatan key din kizo ki diba na karfi ne a hannuna kaji min mata ko kin ki ko kin son abin miji na kowa ne a gidan nan.
Barin fada maki tace duk yadda kike gani kin kai ga shige shige a gidan nan na damaki na wuce gurin nace may shige shigen naki ya haifar maki ban da saki.
Ni ga Allah na dogara da alamarina ke da kike ganin wani zai baki abinda Allah bai tashi baki ba sai kije kitayi mota dai ce sai dai ki mutu a kan shi.
Tayi zage zagen ta ba wanda ya kula ta Altine ce taso kula ta tunda na daga mata hannu tayi shiru bata kara tanka taba har taci tagaji ta fita kowa yai banza da ita.
Yana zaune sai gata ta dawo cikin tsawa ya kore ta a dakin yace tasan shi tasan halin shi zai saba mata yanzu akan maganan nan idan ta damay shi.
Da mamaki take kallon shi tare da tunanen irin kudin data kashe a kan shi gashi komai sai kara lalace mata take ganin yana yi a gidan tun daaowan nata.
Fitinan yau daban na gobe daban duk dako malam yace zata ga canji sosai a gidan idan ta koma ba abinda ta gani daga cikin aikin malamin sai sa, an dawowa gidan kawai data gani.
Daki ta koma ta kira malam Yalliyan tana fada mai halin da take ciki yace har yaushe ta koma gidan idan da bai mata aikin kwarai ba har yaushe zata koma gidan.
Hakkuri ta shiga bashi akan gajin hakkurin da ta gani a gidan ta kashe wayan tana sauke ajiyan zuciya tare da tunanen wani mataki zata dauka kafin maganin ya fara mata aiki kan wanan yar iskan Banufar.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/16/21, 5:48 AM - Xxxxx: Har sati biyu ina amfani da motar AA bai taba tambaya na don may ba nima kuma da yake ba zama nake ba ban kula da lamarin kowa a gidan.
Yau na dawo a gajiye ba abinda nake so sai in yi wanka in dan kwanta shigana ke da wuya waka na fara yi ina saka riga sai gashi ya fado dakin.
A cikin yanayin daure fuska nagaida shi ya amsa tare da fadin may ye hujjan ki na fita kibar yaran nan a gida.
Naga ai sunyi wayo yanzu yasa na barsu tunda ina da masu kama min su a nan din don wahala nake dasu idan na fita gashi satin nan duk bamu zauna a cikin sulchool ba tun wancan satin muke shiga kotu.
Ban dai son hakan may yaran zasu hanaki yi idan kin je dasu din tunda ba ciki zaki shiga dasu ba ya fada cikin daure fuska shima.
Nace don ba kai suke tsotso ba amma barin su gida aiko su saukin su ne hakan nagani zaki fasa fita ke nan muddin kika ce ba zaki fita dasu ba kuwa.
In fasa karatu fa kace yace haka nace don naga kin dauki karatun fiye da komai a zuciyar ki yara kan a gida zan barsu don shine sauki a gare ni yace ki barsu din idan kin isa.
Washe gari na fice ba tare da yaran ba kira uku nagani nasa ban daga ba sai da aka gama wani sharia da muke saurare na fita na kira shi.
Yace may na fada maki jiya khadija nace may kafa da min fa yace ban ce kada ki fita gidan nan kibar yaran nan a gida ba.
Nace ka fada min to don may kika ketare doka na tunda kin nuna ban da muhinmanci daga yau ba zaki kara fita ba wayan na kalla ba tare da nayi magana ba sai na kashe wayan.
Mamaki ne ya kamani don naga dai karatin nan da abina ya ganni ciki don may yanzu yake son tsiro min da wata fitina kuma.
Duk abinda akeyi sai faman tunane nake a raina karshe dai na yanke shawara da zai fitar dani ba tare dana fada ma kowa ba layin Alkasim na kira.
Don tunda ya kare COE mina yake zaune gida ba aikin yi shi nakan kira idan ina da bukatan wani abu nace kada ka fada ma kowa zaka zo wurina ina son yau ka shigo Abuja akwai inda zaka kai ni.
Mun fito ban tsaya ba na nufo gida direct tsab na shiga shiri ba tare da kowa ya gane mai nake shiryawa ba komai da zan bukata na saka a mota da sunan zan kai wanki.
Alkasim ya iso ya sanar dani nace ya samu hotel ya kama da asuba zan fito mu hadu hanya na koma kamar ba komai naci gaba da mu,amula na da mutane.
Ya dawo yazo part din ina zaune ina ba yara nono ya su Altine suka shiga gaida shi da dawowa ya kalloni tare da fadin kin mai da magana na zancen banza ko?
Na dago kai na kalle shi tare da mayar da kaina ga yarinyar dake shan nono bance dashi ufan ba ganin haka su Altine suka mike suka bar wurin.
Kara matsowa yayi inda nake tare da rage tsawon shi kadan ya fara zazaga masifan shi tare da kara nanata min ba inda zan kara fita in bar mai yara da wahala.
Ido rufe nace kai nagaji da wanan auren wahalan nagaji wallahi don ina gidan ka sai ai ta min abinda aka ga dama don kawai an ga ban magana .
Allah dai yasa kasan ni ba yar iska bace balle ka dauka yawon banza nake zuwa ina barin yara a gida kasan inda ka dauko ni ka kawo ni nan don ku taru ku cuta min.
Kullun kai ke nan mutum bai maka daidai a rayuwan sa na gaji wallahi da karatuna ka ganni ka ce kaji ka gani yanzun na kusa kamala abina zakace wai ba zan sake fita ba.
Shiru yayi yana kallona da mamaki na yadda na buda mai wuta, don ban taba mashi irin na yau ba sai can yace idan makaranta ne na fada daga yau kin daina ke nan a gidan nan.
Tunda banga amfanin karatun da kike yi ba karatu kika zo yi ko zaman aure a gida don haka na kashe wanan karatun
Na share shi ba tare da na kula shi ba ya gaji ya fita daga part din wani irin hawaye ne ke silalowa daga idona .
Altine ce ta fito ta samay ni a haka tace asha khadija halin namiji kike ma kuka tunda ya fada maki kin fada mashi sai abarshi haka.
Har ta kare maganganun ta ban tanka mata ba da wuri na kwanta don nasan abinda na shirya a raina sai sakawa nake ina kwancewa har barci ya dan sace ni asuban farko na tashi na kamala komai da zanyi.
Zuwa karfe bakwai nace laraba ta biyo ni da Alamin na dauki mami takai min su wurin mota tana fadin ko tazo muje don babu mai kama min yaron nace yanzu zamu dawo ki jira ni ba dadewa zamuyi ba ai.
Tace Allah ya tsare nace amin ta aje min yaran a jiki na bar gidan karan bude get din gidan yaji sai dai yana mamaki wanda ya fita da safe haka don yasan yasa muna dokan talala a gidan.
Ita Nafisa ya hanata fita ko ina tunda ta dawo haka kuma ni ya kashe min fita makaranta wanda nasan yayi haka ne don kawai ya gyarawa matar sa rai a kaina.
Don haka ne ban yarda ba da wanan dokan da ya kafa min zai min salalan tsiya da karatuna gashi muna gab da gamawa yanzu.
A inda nace Alkasim ya jirani na samay shi tsaye yana jirana na fito na bashi key muka dauki hanya sai jahar kebbi jahar da dagani har shi bamu taba zuwa ba labari kawai muke ji.
Sai da yagama shiri ya nufi wurin nafisa suka gaisa yayi sallama da ita ya fito zuwa part dina sun gaisa da su Altine ya nufi kofana dake rufe Altine tace dashi na fita tun da safe ai.
Ya tsaya yana kallon ta da mamaki tare da tambayan yaran fa tace dasu ta fita yakai kofa ya juyo tare da fadin wa zai kama mata yaran a can da bataje da ko gudan ku ba ?
Altine tace zancen da muke ke nan yanzu ka shigo kila dai ba makarantar ta shiga ba sai dai in wani wurin ta tafi kai ya girgiza yace yayi kyau ya fita.
Yana jin zafi a ranshi wayan shi ya dauko yana neman layina akace a kashe wayan yake bai kawo komai a ranshi ba ya wuce zuwa office.
Tun muna tafiyan dadi har kowa ya ja bakin shi yai shiru a motar mun shiga jahar kebbi a nan muka fara tambayan garin KA,OJE.
Ana muna kwatance muna bi har dai Allah ya kawo mu garin lafiya da karfe biyar na yamma muka shiga garin.
Gidan Liman Hamza tsoho muka tambaya akai muna kwatance har gidan a kofan gidan muka tsaya da motar mu.
Ganin basu san mu ba aka tsaya tambayan daga ina muke wasun su ko hausa basu ji sosai sai yaren filace suke yi.
Dan gajeren bayani mukai masu suka gane nan take aka shiga muna sannu da zuwa wuri ya kaure da murnan yar wurin dan uwan su dake Niger state ce tazo gida.