← Book details Mijin Buzuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 4 OF 6

Part dina muka shiga ba abinda muke sai labarin muna dariya mukaji anyi nocking din kofa.

Mijin Buzuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 115 min read

Laraba ta mike tana dubawa shine tsaye a kofan yake tambaya ina ina tace gani a ciki yace kice mata zan shigo.
Ta juya ta fada min da sauri muka gyara ya shigo da sallaman shi waban karon ya canza kayan jikin shi zuwa jallabiya.
Wuri ya samu ya zauna tun ban mai iso ba yace madam gurin ki nazo sai dai naga kamar kina da bakuwa yanzu din nace kawatace ba bakuwa bace ai yaya.
Yace good zan so in tambaye ki wani abu gamay da gidan nan dafatan zaki ban amsa yadda nake so ba tare da kin boye min komai ba.
Nace insha Allahu yaya idan na sani zan fada ma yace good buzayen su nawane a gidan nan nace gaskiya ban san adadin su ba yaya kai ya gyada ya sake fadin kina ganin sun kai how long a nan nace ban sani ba don nima anan na samay su gaskiya.
Yace kina nufin duk dadewan nan suna gidan nan tare daku nace eh yace wanan wani irin rayuwa ne haka ina mutum zaiji dasin rayuwan sa a haka ?
AA wani irin mutum ya zama da baida lissafi wallahi dan zama nan mutanen nan suna takura min sosai ba dama mutum ya dawo da gajiya ya huta sai sun damay shi.
Kada ki damu zanyi maganin abin insha Allahu maryam tace mun gode yaya wallahi da abin yai dadi gidan sam babu kwanciyar hankali ko kadan .
Yace kada ku damu ku dan bani time mu gani har ya dawo ya mike ya fita yanufi kofan fita wajen gidan kiran wani buzu yayi yace ya kidaya mashi su nawa ne a gidan nan.
Na fito rakiyar maryam yana zaune saman motar shi muka gaida shi yake fadin zata koma ke nan nace eh yace barin sauke ta don nima gari zan shiga nayi mata sallama na fita.
Gidan ya koma shiru kamar ba taron nan a cikin sa nace wuta soja ga wuta ga halbi don dole yau kowa ya natsu badon Allah ba.
Ashe bayan sun fita ya bugi ciki maryam yaji komai na gidan tunda ya fahinci na boye mai wani abu ba gidan dake faruwa.
Washe gari nayi bakin course mate dina tun da nai aure zuwan su na fako ke nan gurina mun dade dasu sun fito na rakasu zasu tafi lokacin motar AA ya shigo gidan ban ko kalli inda motar take ba balle sannu da zuwa.
Shima kallon mamaki yake aika min daga inda nake muka gama magana suka ja motar su muna dariya suka tafi ni kuma na juya na shiga ciki ban kara bi ta kan sa ba kuma.
Wai ashe hakan da nai mai yaji zafi kodana shiga ban fada ma mama ya dawo ba na shige ciki don yin sallah la,asar.
Ina sallah ya shigo dakin bai ko sauya kayan jikin shi ba muryan shi naji suna gaisawa da laraba a falo tana mai sannu da zuwa ya leko dakin ina sallah tsaye yai min dakin ni kuma danaga haka ban yi saurin katse sallah ba.
Sai dana gama addua na shafa na mike ina ninke sallaya na gurin muryan shi naji yana fadin ke baki san nayi tafiya bane da baki iya yiwa mutum sannu da dawowa ba ?
Da zaka tafi ka fada min nai maka Allah ya tsare hanya ne da zaka zo ka tsare ni yanzu Allah dai na ganin ka duk abinda kuyi a gidan shine gata na.
Na fadi ina nufar side drower dina don aje carpet din sallah yace kina nufin sai na biyo ki nan na fada maki zanyi tafiya kin min wullakancin da kika saba yi min zaki gaida ni da dawowa komay ?
Zama nayi a bakin gadon batare da nace mai komai ba yace kina ganin wanan rayuwan da kika dauko shine zai fisheki a gurina komay ?
Ni dai ban mashi magana ba ya buga tsuki ya fita a hasale na bishi da harara tare da fadin karfin hali wai barawo da sallama ke nan.
Yanzun kuma wai laifina mutumin nan zai gani yanzu ban masan kan girkin gidan ba yanzu tunda na daina bin komai.
Falo na fito na samu laraba tana ganina tace injin dai ba wani abu tace kinyi ba kuma naga mai gidan ya fita a hasale mama rabu dashi rainin wayo yake son yi min wai ni ban mai sannu da zuwa ba.
Lokacin da zaiyi tafiyan shi ya sallamay ni balle yanzu in tare shi da dawowa tace ai da kin tare sa din ba komai bane Aljannan ki kikaiwa hakan.
Mama har zancen wani Aljanna ake a gidan nan da babu tsari dole in masa haka mama ai idan na gaida shi gobe ma fiya da haka zangani garesa .
Yaba nufin zan zaman bisa ne yana min wullakanci ina bishi shi yana bin umurnin wata saboda ya gyara mata raine yaki sallama na ai yasan dani a gidan.
Watau yanzu hankalin shi ya fara dawowa gare shi idon shi ya bude zai zo ya lalashi banza ko ban cikin matan da zasu dinga bin namiji yana cusguna masu cikin nan ne kawai ya kawo min cikas a gidan nan.
Ki dai yi hakkuri tunda ya sauko yanzu ba gashi har ya biyo ki dakin ki ba inda yana tsoron ta ne ai ba zaizo nan din ba ko yanzu.
Allah ne ya karba muna adduan mu ya kawo saukin lamarin nan kurkusa har ya gane hakan nace bai gane komai ba wallahi mama ki barni dasu kawai a gidan nan.
Dana haihu sai an nemay ni don ba zan zauna ina cin wanan kashin ba da kurciyana su bata min lokaci na a banza.
Sai dai iyayyena da nasa suyi hakkuri tunda basu ke zama min ba nice nasan abinda ake min don haka ni zan wa kaina mafita a gidan nan.
Abincin dare muka gama na dauka bayan nayi sallah na kaiwa Suraj tare na samay su zaune a falon sama din dagani dukkan su rayukan su a bace yake.
Muryan nafisa naji tana fadin akan may zaki kawo mai abinci a gurin ki yake ne ko may kayya ke zaman shi gurin ki ya dama a rayuwan ki ni yaya Suraj na kawowa abinci.
Ke waya kiraki gurin nan ko an fada maki sa,annin ki ne zaune girin nan suraj ya fadi a hasale yana kallon ta.
Tace amma dai kasan a gidan mijina kake ko ina da daman shiga ko ina naga dama a gidan nan ba wanda zai min shamaki.
Ai na dauka gidan ubanki ne nan din ba ita ba harni saida na waro ido waje ya nuna mata kofa yace fice nan tun ranki bai baci ba ko yanzu in tatakaki a gaban mijin naki yana kallo.
Don shi ya daure maki gindin iya shegen da kikeyi gidan nan saboda samun wuri yayi maki yawa har kishiya kike son juyawa ko ?
Kallon AA tayi don yai magana yace Nafisa ki fita kin san halin suraj tunda kikaji ya fadi zai iya aikata maki abinda yace yanzu.
Ta juya yace dawo da sauri ta tsaya yace waye da girki ranan da ya tafi a cikin ku kallona nayi na dukar da kaina kasa ya sake maimaita maganan shi.
Nace itace don nima ban san yayi tafiya ba ya dago yana kallon dan uwan nasa tare da fadin why brother why kabari haka na faruwa a gidan ka.
Kan wanan mara mutuncin zaka watsar da matan ka na kirki ka kama banza can wanan da kake gani cin kasuwa ne ya kawota wurin ku munsan irin case din su da dama.
And kuma gobe goben nan ina son duk taron buzayen nan subar gidan nan tun suna sheda kansu ko in turo a kwashe min su kaf wallahi.
Ke kuma kin zauna wanan banza tana juya ku kamar ta samu waina daga yau ni suraj nace ki mike da tai maki tsiya kikirani ina garin nan yanzu .
Dama nasan zuwa ka nan ba alheri bane an turo kane ka koreni ko ta halin kaka a gidan nan ba inda zan tafi yan uwa na kuma ba zasu tafi ko ina ba tunda ina gidan nan.
Ai bakai nake aure ba dan uwanka nake aure yace zaki gane baki da wayo ranan ma kyale ki nayi don mijin naki baya kusa yanzu ya dawo a gaban shi zan lalatsaki son raina.
Ganin yana magana AA baiko dago kai ya kalle mu ba sai wayar shi yake latsawa a binsa kamar hankalin shi bai gurin draman da akeyi.
Har na bar gurin ina cike da mamakin wai shi AA wani irin mutum ne haka wanda bai iya yin katabus a gidan sa kanin ka yazo yana shimfida doka a gidan ka kana zaune kana sauraro batare da ka furta wani magana ba.
Har na kasa boyewa na fada ma laraba abinda ke faruwa tayi dariya tace bazaki shiga tsakan su ba tun suna yara ance haka suka taso su uku da Yusuf da yanzu ya zama dan gida shima garesu.
Idan ma da ta matsa a kanta zaimai da haushin rashin mutuncin idan tayiwa dan uwan nasa sai kunji mamakin shi.
Allah ne ya karba adduan mu ya jefo aikin shi nan kuma har ya zabi zama daku mutumin da baida sauki ko kadan kowa yasan shi da rashin mutunci ai.
Washe gari ina daki kwance naji kururuwa yana tashi muka fito ciki da sauri ashe nafisa ne shiko yana tsaye murtuk da fuska yasa bakin glass cikin kakin su na sojoji.
Sai umurni yake bayarwa nafisa na Fadin sai dai ta bisu yace tafi nono fari amma yau babu buzun da zai kwana a gidan nan.
Kaf mazan su da matan su aka kwashe a gidan karo na biyu ina fatan daga wanan tafiya kada Allah ya dawo muna dasu gidan kuma.
Ranan laraba taita aiki a falon yasa duk a kwashe kujerun falon aka saka wani su tv da komai na nu,ora aka canza na gidan nafisa tunda ta fita banji duriyan ta ba haka shima mai gidan ashe wuri suka nema masu can wani unguwa da zasu zauna.
Sai dare bayan goma ya shigo lokacin ni har na kwanta mun rufe part din mu yazo yana kwankwasawa don waya a kashe take tunda zan kwanta.
Laraba dake falo ne ta taso ta bude mashi part din ya shigo yana fadin tana ina tace tana daki a nan ya samay ni kwance saidai na falka daga barcin dana fara.
Har kun kwanta yace eh kawai na iya bashi amsa don haushin shi da takaici da nake ji a raina yasa ban ganin dan sauran girman shi da nake gani dama.
Ashe abinda ni ban sani ba shine waya suraj sukayi da hajiya yana tambayan AA zai zo abuja yana son sauka gidan shi shine kafin ya samu wuri.
Hajiya tayi murmushi tace anya zaka iya zama a gidan dan uwanka yanzu yace saboda may hajiya tace gidan ya koma kamar tashan buzaye kowa yaje bai marmarin komawa kuma.
Nan dai ta kora mai duk halin da dan uwan ki ciki yace kada ta damu zai ma abin magani in sha Allahu shine mafarin wanan turjin da yazo yi a gidan ya watsa kowa don bai barta da kowa ba yace idan tana son mai aiki a nema mata yar kasan nan.
Ranan kan sun sha zagi su da dangin su kaf a gurin su da abikan ta inda suka tasa AA a gaba saida ya basu wani gida nashi suka tare a cikin sa wai kafin su gama shiri su koma gida.
1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Yanzu gidan AA tankar babu kowa a cikin sa ne don shirun da gidan ya koma wani lokaci muna fitowa falo anan zamu zauna muyi hira da mama sai yaran Nafisa da in ta fita ta barsu a gidan.
Da farko dasu take fita zuwa unguwa daga baya kuma ban ya akayi ba take barin su gidan ta fita haka zasu wuni da yunwa sai idan ni na basu abinci.
Babu wani dogon shiri tsakanina da maigidan tun wanan Clash din ya faru Yusuf ma yanzu ya dauke kafan sa a gidan.
Gida nake son zuwa nakai sati ina binshi da zancen yana ja min rai akan zuwa na gida wai sai na haihu zan tafi na dage akan maganan bai dai ban amsa ba kan tafiya.
Sai yau da ya dawo ya same mu a babban falon gidan muna hira Samira ne ke bamu labari ina rike da yar gurin Nafisa a jikina abinci nake bata.
Ya shigo kamar yadda ya saba idan ya dawo gurin aiki a kasalance muna gaida shi ya samu guri ya zauna Ihisan ya tambaya maman su tace ta fita tunda safe.
Kai ya girgiza yana fadin ina son ranan Friday din nan zan yi tafiya sai ki shirya kuje gida ki dubasu kwana uku ai is ok ya fada yana kallon fuskana.
Kwana uku wanan dadewan da nayi banje gida ba haka one week dai dan dama ke nan yace idan zaki wuce kwana ukun ki fasa ki bari sai idan kin haihu.
Tun ranan na fara shiri na shiga kasuwa da maryam muka sai tsaraban da zamu kai gida tare da mama laraba zan tafi don barin ta gidan ba zai yuyu gare ni ba.
Nafisa bata san da zancen tafiya na ba sai ranan da zamu wuce naje sallaman ta har dakin ta na samay ta nace mu zamu tafi ai muna gafara.
Tace na aikeki ne da zaki sallamay ni dariya nayi nace akwai rai akwai mutuwa don haka ba don ki na zo ba nazo sauke nauyin hakkin makwabtakane gare ki.
Daga haka na fito abina na samu mama a kofa tana jirana a waje muna fita na samu AA a gurin motar .
Motar shigan shi ce ya bamu zamu tafi dashi nan dai ya kara jaddawa driver da yaja mu a sannu kada yai gudu damu.
A raina nace kaji kitihin maza kamar wata wace ya damu da ita a gidan abin mamaki harda hilux na biye damu a bayan mu dauke da kayan tsaraban da ya saya muna .
Ban san da wanan sayayyan ba sai yanzu da motar mu zai tashi yace tsaraban ki na dayan motar.
Ban samu godiya ba muka daga daga wurin ina mamakin shi wa zai ganni da tarin arzikin nan yace wai ba zaman lafiya a gidan shi.
Shike nan ya gama daure ni ta wanan fannin kai maza sun sa takon sheri nace dole in ja bakina in tsuke kan wani matsala nawa ke nan don babu wanda zai yarda da wanan.
Duk da fadan da yai ma driver bai hana shi sharara gudu ba dan kankanin lokaci sai gamu garin minna wani dadi naji a raina daya sakani lumshe idanuwa.
Ina mai jin dadi a raina gidan mu ba bakon wuri bane ga driver nayi mamaki ba tare da kwatance ba ya kaimu har kofan gidan.
Sai dai nayi mamakin ganin sauyin da gaban gidan ya samu sosai an rushe ginan dana sani anyi na zamani a yanzu.
Da mamaki na fito daga ciki motar sai kallon tsarin da akaiwa gidan nake yi gaisuwa nake samu daga wurin samarin dake zama opposite din gidan mu suna zaman kashe wando.
Wa yan nan samarin da suka taso ne suka yi kokarin shiga muna da kayan mu cikin gida sai ga yaran gidan mu a guje sun fito taron mu.
Nan dai muka rungumay juna dasu muna murnan gani junan mu na yaushe rabo ciki muka shiga laraba tana biye damu a baya.
Maman mu tana tsaye ta kasa boye farin cikin ta gare mu sai fara,a take a fuskan ta da dan gudu na karaso na rungumay ta cikin farin ciki.
Ke da hankalin ki kuwa kike wanan gudun da tsohon cikin ki nace mama don Allah bari mana ina cikin yake ina kallon kaina na sake rungumay ta ina jin wani irin abu har cikin raina.
Mun shiga ciki inda samarin ke ta faman jibga kayan a tsakar gidan mu kallon dakin mama nayi nace mama nifa na kasa fahinta wanan sauyin da na gani a gidan nan yanzu.
Tace bari ki huta mana ai zakiji komai dake gudana ko a bakin baban ku idan ya shigo nima haka naga wanan aikin.
Allah sarki dan uwa mai dadi sai ga kanina Nasir da gudu ya sawo min banbara da ta waska wai abin tarban shi ya kawo min.
Nan na baje falon mama na ci bambarana sosai na kora ruwa sama iskan fanka na buguna sai barci ya dauke ni a gurin.
Barci nayi sosai a gurin sai da mama ta tayar dani in sallah na tuna da driver da muka zo dashi nace mama ankaiwa driver ruwa kuwa ?
Tace yanzun kika tuna dashi ankai mai har abinci sun ci suna can da Alhassan ya kai su su samu inda zasu sauka.
Laraba fa na tambaya tace tana can dakin tana sallah na mike nima don zuwa sallah amma cikin nan naki ya girma da yawa anya ba batan wata kikayi ba kuwa baku kidaya da kyau ba.
Ai ina zuwa awo mama su suka fada min cikin yayi girma kamar ba cikin fari ba ne na gani kai mama bar wanan magana kina sa ina jin kunya sosai wallahi.
Tace ikon Allah shi zancen cikin ne abin kunya kamar bamai uba ba ciki ciki da gatan shi zaki wani kama noke noke haka.
Bayan nayi sallah ne daddy mu ya shigo gidan da murna na taso na tare shi shima yaji dadin gani na da yayi yace that is my girl khadija ke ce haka kika zama wata big mama.
O lord daddy har dakai cikin min sheri yace common zo nan in kara ganin ki nayi dariya naje gab dashi na zauna sai kallona yake yana jin dadin ganina.
Mun dauki lokaci dashi muna hira anan yake fada min irin alherin da AA yake masu a raina nace munafuki yar ku nacan yana gana mata tasko yazo nan yana wani kyautata maku.
Yanzu ni zan fara kawo korafin zanan da muke a gidan nan a gaban su dole in ja baki na in shiru ko kuma in kebe da mama da take ita mace ce ta taimaka min da shawara..
Sai washe gari aka fara raba tsara na nesa ni na shirya zuwa gidajen su kai masu don ba lokacin da zan ja dole na shirya ban hutaba na fita.
Gidan ya suwaiba ne karshen zuwa acan muke har karfe takwas muka dawo gida ranan na samu kebewa da mamana itace ta fara kawo min maganan tana fadin.
Naji dadin ganin ki a haka khadija kullun ina kwana da zancen ki a raina dashi kuma nake tashi nasha mafalki da farko mara dadi a kan ki.
Sai da naje gida maikunkele na karasa har beji naga baba nacan ya ban addua da zandinga yi akan ku yace idan kin zo a sanar mashi tun jiya da kuka iso na tayar da Alkassim ya tafi ya sanar mashi da zuwan ku.
Shine yaba da sako a kawo maki kinga sakon nan ta mike tana daukowa tace rubutu ne da hayaki yace kiyi shi tun nan gida dama ina Allah kizo ba sai kin kaiga haihuwa kamar yadda yace ba.
Nace mama nasan kin damu da rashin zuwa na ai sai dai ai kin san ba laifina bane tsoron daddy nake ji kan umurnin daya bani da za a kaini.
Dadin ku haka yake ai ni ban san halin shi ba idan na matsa da magana sai yace ina son kashe maku aure ne komay ?
Mama zuwan nan da nayi akan haihuwa na ne na matsa in zo don irin abinda za a aiwatar idan na haihu din na ce nazo da kudi da zan bar maku ai lalurar haihuwan dashi in Allah ya sauke ni lafiya.
Maganin da ta dauko ta fara min bayanin su tare da fadin yanzu idan kin gama sai in debo maki garwashi ki hayakin yace idan kin kwanta zaki mafalki da wani abu duk abinda ya tsaya maki a rai to kiyi taka tsatsan da abin nan.
Ruwan rubutu ta miko min tace wanan idan kin gama wanka kiyi hayakin sai ki shanye gaba daya ki shafa sauran a jikin ki sai ki dora da hayakin.
Ga ruwa can ki watsa kafin dare yayi sosai ta fadi tana mikewa na tashi na wanka kamar yadda mama tace ina fitowa na samu tana zaune tana jirana da garwashi a gaban ta.
Rubutun ta miko min nasha na shafe jikina da saura na shiga yin hayakin sai da yabi jikina da kyau na cire rufin danayi mun dan taba hira nan cikin daren naba kudin nace ta boye su zan ba daddy nasa da wani don kada ya fahinci wani abu.
Albarka tai ta saka min tare da kara min nasiha kan hakkuri da juriya a gidan miji har barci ya dauke ni ban sani ba ta fito ta barni don in samu barcin.
Washe gari tunda na tashi nake baki masu shigo taro na don an kai masu tsaraban da nazo dashi suna tambayan yaushe zan koma sai ace masu gobe.
Duk wanan bai sa zancen mafalkin da nayi da madam da yanyala ya fita raina ba da wata mace da ban sani ba mama ta lura da damuwan da nake ciki sai da muka kebe nake fada mata abinda na gani a cikin mafalkin nawa.
Da farko dai ana taro ne a dakina sai gasu sun shigo fuskan madam ya canza ta karbi wata yarinya ta barin wurin yarinyar ta koma wani kala kamar abin tsoro.
Yanyala kuma ganin ta nayi tare da nafisa suna bina da gudu ina kama yara sai ga AA yazo ya tare mu sai suka juya da sauri..
Ajiyan zuciya mama ta sauke tace ke nan akwai wani fitina a boye da zai taso nan gaba ki yabada lambar wayan shi mu kirashi mu fada mai abinda kika gani din.
Nace nima zan so na samu lambar inje dashi don ko wani abu ka taso mun a can sai in kirashi in mai bayani.
Mama ta kirashi sun gaisa yace a bani waya bayan dan wasan jika da kaka da muka taba dashi ya fara tamnayana ko nayi mafalkin nace eh tare da mashi bayanin komai dala,dala ya sauke ajiyan zuciya tare da fadin ikon Allah.
To Allah ya kyauta ya tsare ya kare kuma mafalkin farko yana nufin suna da mugun manufa akan abida zaki haifa nan gaba sai kiyi taka tsatsan da su sosai lokacin haihuwar naki don akwai wani sheri da suka kula.
Sai nabiyu dake da zurian dkine suke bi da sherri wanan daya tare ku shine zai taimaka maki a nan gaba akan sherin nasu.
Yaushe ne tafiyan ku nace gobe yace da wuri haka nace kwanakin da akan bake nan inyi yace ba damuwa tunda bada safe kwarai zaku tafi ba ai nace eh malam.
Yace to goben zan ba yarda abu akawo maki kafin ku wuce sai ki kirani a waya zan maki bayanin komai Allah ya kara tsarewa nace amin nagode muka kashe wayan.
Shikan daddy ba abinda ya damay shi sai harkan shi yake dani da mamane muke kashewa muke binnewa mu kadai ba tare da yasan komai ba sai kuma ya Amina da wayanta ke kai yana kawowa akan mu.
Sai da mukai waya da tsohon na danji sanyi a raina yadda ya kwantar min da hankali sai shirin ake min yayin da nake jin raina ba dadi na komawan nawa.
Don bansan kuma damay zasu tare ni kuma don yanzu tsoron su nake ji sosai abin yayi yawa sosai kullun babu sasauci ga alamarin nafisa din.
Abuja tun ranan da muka bar gidan ta fita ta bar yaran sun kadai a gidan har mijin ya dawo basu dawo ba ashe sunje wani kauyen kefi ne dare yai masu acan.
Ranan yai mata masifs sosai yakuma sa mata kulle ance mai kishiya bata mutuwar Allah ni da ban gari amma laifina Nafisa ta gani.
Wai na kai AA wurin tsafi an tsafe shi tun kan in dawo gidan dole ta mike don tasan ina can gida ina sabon shiri a kan ta da mijin ta.
Da rarashi da komai taciyo kanshi ya yarda yanyala ta dawo ita kadai ta zauna dasu don kula da yara nan suka hade sukai ta binne binnen su a gidan yadda suke so.
Saboda sakon da za a kawo min muka dan bata lokaci gashi sai kira yake muna ina bamu taso ba har yanzu muna may a minna har wanan lokacin.
Banbi ta nasa ba sai dana karbi sakona muka kama hanyar Abuja uku da wani abu muka shigo garin da shirina na dunfari kofan ina adduoi a bakina banji fargaban komai ba na shiga gidan ba kowa a falo sai tv dake aiki shi kadai.
Part dina na bude ana samun kayan da akai min tsaraba daga gida ciki Ihisan ce ta fito taga laraba ta shigo da wasu kaya ta sake ihun ganin mu shiya hankaltar da iyayyen suka san mun dawo.
Dakin ta nufo tana jikina tana zuba surutu sai ga Yanyala ta shigo tana kiranta nayi mamaki kwarai da gani yanyala ta dawo gidan sai dai ban tankata ba taja yar suka fita.
Mikewa nayi zuwa uwar dakina na fara tube kayan jikina sai ga Laraba ta leko tana fadin uwar dakina maza a barsu kawai kinga matar nan ashe sun dawo gidan nan kuma.
Nace mayu ne basu da zuciya wace Suraj yaiwa koran wullakanci irin haka ko kofan gidan nan in nine ai ba zan kara kallo ba.
Tace kin san su da bakin nacin tsiya ai in sun samu guri kamar gidan gado suka samu ta fita na mede baki ina fadin shi dai ya sani mina fuki.
Kansu zai kare shida ya dauko jaraba gidan shi ya sani ana wani labewa ga asiri yanzun dai ban kara yarda da cin kashin kowa daga cikin su.
Wanka nayi nayi sallah ban fito ba sai da nayi la,asar nafito falo bambarana na diba naci mai isata na saka saura a cikin fridge.
Biyar daidai ya shigo part din mu da mama suka fara gaisawa yana tambagan ta ya hanya da mutanen gida.
Ya juyo inda nake dan cin sauran bambaran dana rage yana fadin kun iso ashe nace eh yaya mutanen gida sunce suna gaishe ka sun gode.
Bai yi magana ba sai kallo na dayake yi sai kuma ya tuntsure da dariya yace haka kika je masu da katon cikin nan kowa na kallon ki dashi.
Nace ai sin san ba laifina bane don bada shi nazo nan ba da farko yana kallon abinda nake ci tare da fadin maye wanan haka kuma kike ci nace cimar mu ne na yan Niger.
Ko zakaci ne in dibama na tambaye shi ina kallon shi tare da fadin ga doya can daddy yasa muzo ma dashi nace ya barshi muna dashi yace a, a.
Yace nako gode ai doyan ku daban take da namu na nan tana sakwara mai kyau sosai akace nace in diba ma bambaran ne ya bata fuska tare da fadin ci abinki na gode.
Ya fita naso ranan in huta amna hakan bai samu ba sai da ya saka ni in mashi sakwara da miyar egushi yace yana so dole muka daka mai shi.
Zan kai mai abinci na hadu da nafisa tana saukowa saman harara ne ya raba mu yadda naga ranta a bace nasan sunyi tsiyane ta fito.
Shima a haka na samay shi ban kula ba ban kuma tambaya ba shine naji yana tambayana da cewa idan mace ta dawo tafiya kafin yamma ba ita bace da girki sai idan yamma yayine lokacin amsan girki ya wuce ta iso bazatai girki ba.
Nace eh haka naga anayi sai lokacin na fahinci may sukewa rigima nakuma fahinci dalilin shi na matsa muna mu taso da wurin da yake yi tun muna minna.
Nace idan girkin take son yi ka barta mana tayi ba shike nan ba nasan dai ina gidan zuwan ta gida sau biyu kuma bantaba cewa zan karbi girki a ranan da ta dawo ba.
Don haka na kulle a raina nasan abinda zan mata nan gaba idan tayi tafiya ai abin ba tsoro bane don taga ina daga mata kafa ne ta dauka duk asiri ne ke cina.
Ranan wani munafukin soyyaya gwada min in da na dabe komai a raina nima na gwada mai nayi missing din shi.
Washe gari ban fito ba har goma muna dakin muna barci wanan abin shi ya bakanta wa Nafisa rai sosai don tana falo tun bakwai tana dakon fitowan nawa.
Bayan na fito ne na samay su zaune a falon na shige ina jin tana buga wani uban tsuki nace sai dai shi kan yanzu.
Dakin ta nufa ta samay shi ya fito wanka gadon ta kalla na gyara shi fes kamar bamu kwanta ba tace dan dadin abu kazan mace.
Anje gida an tsuma anzo maka dashi ka rude harda kaiwa karfe goma da mace cikin daki baka fito ba may kake nufi da hakan ko tafi kowa dadi ne wai.
Yace baki ganewa ke wanan sirina ne kuma nakai karfe goma din kema kije ki tsuma naki idan kina son in sha daya dake.
Yana magana yana nuna mata lokaci da hannun tace Samad ni kake fada ma haka akan wanan yar duniyar matar taka yace na fada maki ke may ye na shigowa ki mun wanan maganan haka.
Ko ke ba a kwana dake ne wani yahanaki kai wanan lokacin ne a dakin nan kullun ke ke nan amaki ba daidai ba cikin korafi.
Na dauki hakkin kine na kai mata ko ita ta saka ido akan abinda mukeyi dake ne a gidan nan barin fada maki nagaji da wanan halin naki wallahi.
May na rage ki dashi na rayuwa akan wanan yarinyar ne a gidan nan kina da abinda bata dashi tayi hakuri dani ta zauna dani duk da tasan ina tauye ta din akanki.
Ko finta kikayi a gurinanr wai tace tana gyada kai lalai Samad shike nan an kaika wurin dodon Nufawa sun asirice ka tunda har ka iya fada min wanan magana ko duk zaki kazane yasaka sake wanan santin.
Yace ashe kin gane nasha dasin da ban taba shan irin sa ba jiya kuma ki bace min da gani dakin nan kafin ranki ya baci sororo tayi tana kallon shi yau.
Don tana da tabbacin aikin da taimay ba zai iya taba daga ido ya musaya mata maganan ta ba sai gashi jiya jiya da dawowa na gida taga sauyi mai yawa a tatare dashi din.
Bata iya kara magana ba juyawa tayi tafita a hasale shikuma yaci gaba da shirin sa hankali kwance tana zuwa daki ta rarumi waya tare da danna wa madam kira.
Tana dauka tace ayyah madam na shiga uku wanan yarinyar ibilishiya ce ta gama min da miji kin san wai sai yanzu suka fito tun jiya da suka shiga barci nayi mai magana baki ji irin santin kaza da Samad ke min ba yau.
Madam tace waya aikeki wayasa ki ki masa magana Nafisa nafa fara gajiya da wanan halin naki kema kin san idan mace tayi dan tafiya bata gida namiji dokin ta yake yi kamar tayi tafiyan shekara ne.
Tace madam abin ne da ban haushi wallahi yun jiya fa sai yanzun suka sako kasa ji irin kudin da muka kai kefin nan fa duk akan shegiya ta dawo mai makon inga sauyi sai bacin rai.
A bangare na na shirya mai abin karyawa wanan duk yana daga ciki huduban dana samu wurin mama Tani harda dadewa ban fito badanayi daga gurin shi din.
Sai da ya gama shiri ya sauko ganin ban kawo mai abin karyawan ba yasa ya biyo part dina nan na zaunar dashi muka karya ina jan shi da dan hira ya bata lokacin shi a gurina.
Yana fitowa ta wani kafe shi da ido sai gani na fito dakin dauke da case din shi a hannuna tare muka jera zuwa waje sai da motar shi ya bar gurin na juya na shiga ciki.
Barci nayi sosai sai bayan sallah na fito falon gidan na zauna tare da kuna tv bayan nasa laraba ta gyara min falon don wurin kamar tunda mukai tafiya ba a gyara shi ba.
Suna daya gefen zaune nace Samira ta miko min remote na canza canal nakai muna mbc 2 muna kallon fin can na rage sautin tv na danna kiran layin shi ya dauka.
Hira mukayi sosai dashi duk hankalin ta na gurin mu tana ji kamar ta taso ta shake ni a furin takeji a ranta.
Da gangan nayi mata haka karshe kasa zama tayi a falon ta shige ciki tare da kiran yaran ta suka barmu a gurin bamu tashi ba sai yamma muka shige part dina .

ZAINAB IDRIS MAKAWA
1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Ni kaina canzawan da nayi a gidan cikin dan kwana biyun danayi da dawowa yana buurgeni don a sannu ina samun kulawa daga maigidan ta yadda ban zata ba.
Ashe gaskiyar maryam da take fada min ciki bai saka rage komai gun miji sai dai ma ya kara maku farin ciki .
Don ni a wautana na dauka cikin da nayi saurin samu ba zai barni inyi yadda raina zai so ba ko samun kulawan maigidan a kaina ashe abin ba haka yake ba sai yanzu da nayi amfani da nasihar mama tani dake fadin indan baan dadage ba zasu daga min nono a cikin wasa.
Ba miji kulawa yana kawo shakuwa da yarda a tsakanin ku sai yanzu na kara yarda da wanan maganan don na gani a kaina.
San kulawan da nake nuna mai da yawan manne mai idan muna tare yasa na fara zama kamar wata abokiyar shawaran sa.
Koda ban je gurin shi ba shi da kansa zai zo part dina mu dade muna hira dashi wanda haka nasha kama su da Nafisa suna fitin akan hakan.
Duk da har yanzu bawai power ta ya kare a gidan bane akwai dan shakkunta a tare dashi ban damuwa da hakan kokarin kafa kaina nake a gare shi.
Yanzu ma na dawo daga rakiyar shine zai tafi office nan muka wuce su a falo zaune kamar kullun idan ina da girki hakan take miin wanda nasan ba zaman banza take a gurin ba zaman saka idone akan mu.
Ina shigowa tace karuwanciin banza indai na miji ne can muka fito muma talkaman ya tsunke baan yarda na kyale ta ba najuyo nace ashe takalman naku dama tsoho ne kuka saka harda ya tsunke din.
May kike nufi da maganar ki nace amsar maganar kice na baki ai dama tsohon gindn kika kawo mai wanda mazan buzaye suka gama dashi ashe shiyasa kikai saurin daukewa.
Wa, iyazu billah nan naga tijara iyayyena sun sha zagi ranan a haukace ta tashi kamar zata dukeni sai tazo kusa dani kuma komay take tunawa sai ta dan ja baya.
Nace kiyi naki kibar na Allah wanan kan an hade mutu ka raba takalmin kaza ba abinda zai sashi tsunkewa da kike tunane yanzu muka fara wasa dake a gidan nan.
Idan kin fada min biyar sai na fada maki goma don haka shege ka fasa dani dake na shige dakina ma barta tana masifa.
Karshe na fito wanka sai ga kiran shi ya shigo min yana tambayana wai may kuma ya hada mu da Nafisa ne bayan fitar shi yanzun ta kirashi tana tashin hankali.
Murmushi nayi nace yaya kadai san halin matar ka magana ta fada min na bata amsa shine ya zama tashin hankali nina fita batun ta ai tunda na bata amsa ai.
Deedar bakya dai ji baki fita zancen ta wai nace ai na fita nikan tunda ban tsaya kulata ba yadan gama babatin shi ya kashe wayan na kali wayan nace Waire inji yarbawa.
Da yake ba abincin rana yake dawowa ci ba don haka na samu issashe barci na dakyau da rana sai bayan sallah la,asar na fito falo da laraba muka zauna.
Babu kowa a falon sai baby ita kadai a kwance falon tana tsala kuka kamar in share yarinya na dai daure nace laraba ta dauko min ita.
Allah sarki yarinyar tana kara girma kanta ma yana kara wani yin gingiringin dashi ga wani dan molo dayayi a gaba idan ka kalle ta sau daya bakaa son ka kara kallon ta karo na biyu.
Na duba tayi kashi da amai nace laraba ta duba yanyala ta bata yarinyar ta duba babu kowa a part din yana a rufe gashi tana kuka da alama abinci take so a bata.
Dole laraba ce nasa ta wanke mata kashin ta kawo min ita shiru shiru basu dawo ba nan kira AA ya shigo min muna waya yana jin kukan yarinyar.
Yace sadiya ce a gurin ki nace eh yanzu na fito falo na samay ta ita kadai a kwance tana kuka mun duba part din babu kowa da alama ma yunwa take ji.
Tayi kashi an wanke mata sai dai ba abincin ta a kusa yace gashi nan zuwa yanzu AA yana kokarin kula da yarinyar sosai don yafi uwar kula da ita gaskiya in dai yana gida zai dauke ta su tafi part din shi.
Amma uwar da wuya kaga ta dauki sadiya a jikin ta ba a dade baa sai gashi ya shigo dauke da madaran da ake mata amfani yana zaune aka bata tasha sai barci ya dauke ta.
Ajiyan zuciya ya sauke tare da kada kai yace wanan wani irin rashin imani ne haka ga Nafisa na lura sam bata son yarinyar nan tunda aka haife ta hakan nan.
Take kyamkyamin ta sai wani maganan banza wai an hurhura mata yarta ne donn likita yace mata namiji zata haifa sai gashi ra haifi mace macen wai musaka acewar ta.
Laraba dake gyarawa yarinyar kwanciya tace da Allah take jayaiya ke nan kuma irin yaran nan in suyi lafiya ai su ke zama wani abu wata rana.
Ya mike yana fadin ina hankalin ta zaisa ta gane hakan yanzu tana can wurin bakin yawon ta mara dalili daga haka ya haura sama.
Sai da ya dan jima da shiga na mike na samay shi a dakin yana kwance rigingine na karaso na zauna a gaban shi ajiyan zuciya naji ya sauke.
Dan kwantawa nayi saman jikin shi tare da kokarin kawar mashi da tunanen shi wanda nasan akan Nafisa din yake yin shi nace.
Bazaka koma wurin aikin ke nan ba ya sake sauke ajiyan zuciya yana dora hannun shi a saman ciki na yace banjin komawa na gama na yau sai dai gobe.
Zan zauna inga dawowan wanan mara mutuncin ne nace haba zakuyi halin kuma ke nan ka kyale ta tunda kun saba da hakan.
Yawon nan na fisa yakai min ko ina ko aikin gwaunati take iyakar ta ke nan kai ko aiki take ai ba zata kai haka ba dai.
Ta saba ne tun farko babu hanawa a gurin ta amma da tun farko akwai dokan hakan a gidan ka bazata yi ba ai yanzu ko abin wuyan tankwarawa zai yi a furin ka.
Zan ko baki mama idan ba zata iya zama gida ba sai dai mu rabu wallahi dagawa nayi daga jikin shi don jin kalamin shi da yayi nace.
Haba yaya kada kai fatan rabuwa da uwar yayan ka don abin ba zai damay ka ba sai gaba idan yara sun tasa babu uwar su a cikin gidan ka nan fitinan haka ke taso wa.
Ka saba hakkuri da abinka kayi hakkuri da abin ka sai dai ka zama na miji akan hakan ka nuna mata kai ke auren mu bamu ke auren ka ba ka nuna kaine maigida a gidan ka shine nake gani solution din haka.
Samad amma kasan yau ba ranan girkin wanan bace da kuka shige daki da ita haka da sauri na dago saman jikin shi sai dai shi hannun shi na saman ciki na din har lokacin.
Kallon ta nayi daga gani ko daki bata shiga ba dawowan ta ke nan taga motar shi tasan yana gidan ta hawo sama.
Malama a koyi yin sallama idan za a shiga wuri gada kizo ki samu ba daidai ba tace gidan ku su koya min sallama din .
Zama na gyara tace tashi ki fice daga dakin nan nace koke ki fice min daga dakin nan na kalli agogo kiga lokaci idan kin iya karfe nawa yanzu ko kuma kwancen girkin da kika saba zaki min yanzu kuma.
Tace an ki a kalla din wai kokarin kike ki jaye mai hankali zuwa gare ki wai yarinya kin makara samad nawa ne don haka kije ki nemo mijin ki.
Ke bakiji kunyar fadann maganan nan ba wai yaya Abdulsamad namu duka ne da naki ne ke kadai da baki wanan haukan da kikeyi ba don Allah ki ficewa mutane daga daki na fadi a dake.
Muryan shi a dake ya daka muna tsaya yace ke kifice min nan tun ban bata maki rai ba gidan ubanwa kika fito yanzu kin bar yarinya a wullakace ita kadai a gida.
Wai Nafisa anya kina da burbushin imani a zuciyar ki kuwa tace sasai ka saman naka ina kake son in fita da wanan yar haka a nuna ni a gari.
Yace lalai yanzu na kara tabbatar da koke wacece na yarda baki da imani tunda har kina iya yayya da hukuncin Allah akan abinda yaso gare mu.
Inajin sun kaure na mike tsam da zumar in bar masu dakin suci kansu sai naji tace duk munafukin da ya fada ma na tafi na barta sai ya rungumay ta ai dama may yarage ba ai mata ba .
An riga da an shiga an fita tun tana ciki an hakakala ta sai ki karasa abinda ya rage gatanan na bar maki ita babu inda zan fita da ita a dinga nuna ni.
Kin san dai inda kika shiga aka hurhura maki yarki kaikayine ya koma kan mashekiyar sa ai kowa ya dai bo da zafi bakin sa.
Ki bari ki ga kema abin da zaki haifa ga cikin jikin kin ki da yardan Allah sai kin haifi wanda tafi wanan munu nace Allah ya bani sai in rugumi abina da hannu biyu watarana sai ya bani mai kyau.
Zaki gani dani kike wasa a gidan nan nace inga Alherin Allah a tare dani don bakiyi kamar Allah ba ai yace wai nafisa kina da hankali kuwa ?
Yar uwar zaman ki kikewa wanan fatan haka tace yar uwar zamana na ina yar uwar zaman ka ai da tai min sherin ai banga ka dauki wani mataki ba ga hakan.
Yace mai tayi maki da zan dauki mata ki a kanta ko itace mai bayarwa ba Allah ba har kina ikirarin sheri da bakin ki a gaba na kuma.
Wallahi duk abinda ya saman min jinina nan gaba ba zan barki akan hakan ba don ki sani tunda kiyi ikirarin haka da bakiin ki.
Oh ashe da yafi dane tun dan baizo duniya ba kana ikirarin daure ni ai ban san da yafi da dadi ba sai yanzu daka nuna nace ni ba abinda zaki iya min da yardan ubangiji na don ga Allah na dogara baga wani ba.
Ina fadar haka na fice na barsu a dakin nafito rai bace zuwa daki na laraba na gani na haka duk ta damu dan zama nayi da ita gurin na mikewa zuwa yin sallah ina idar da sallah ns kira mamana ina fada mata abinda tace min din.
Mama tace ds yardan ubangiji lafiya zaki haihu mai albarka wanda zamu aika ita batayii kamar Allah ba duk cika baki ne irin na wanda bai san Allah ba.
Kada kisa zancen ta arai ya damay ki lafiya lau zaki haihu cikin hukuncin ubangiji nace to mama tace kira kakan ki fada mai yadda kukayi kiji may zaice.
Muna gama waya ba kirashi don gaskiya na tsorata da zancen nafisa don nasan shuuma ce tunda har ta furta zata iya din.
Mun gaisa yana min wasan jika da kaka nace Bado akwai matsala fa yace na sani ai tunda naga kin kirani murmushi nayi nace ai da banda layin kane ban kiran ka.
Yace to yaya akwai sauki dakika koma din nan ko abin yana nan har yazu nace Bado akwai sauki sosai wallahi tsakani da miji ba wanan yawan fitinan yanzu sai dai ita abokiyar zaman nawa ne.
Nan dai na kora mashi halin da ake ciki naji yayi dariya tare da fadin hadizatu kin yarda Allah nace kwarai Bado yace to kisa yarda kika yarda da Allah kika kuma imani dashi ba abinda zata aiko maki ya kara galaba a kanki insha Allahu.
Ki kwantar da hankalin ki kidai ci gaba da yawaita addua da yawan sadaka da kyautatawa mabukata na kasa dake in sha Allah duk abinda ta dauko a kanta zai koma idan ta mata zata ga ba daidai ba a rayuwan ta.
Mukai sallama dashi na kashe wayana sai danayi isha,i na fito falo na samu laraba zaune ita kadai a cikin damuwa nace mama anan zaune ne ?
Tace to uwar dakina banda zaman bamu da wani aikin yi sai kallo ba kamar can da yan aiyukan wata rana har suka fi karfina bane.
Zama nayi nace an karbo kayan guga wuri mai wankin nan tace an karbo sai dai yazo min da wani zance wai an yagi zanin ki ta kasa jiya ba haka ya wanke shi ba.
Nace ikon Allah wata sabuwa ke nan kuma zani na may zasuyi dashi kuma tace sheri mana yar nan ai haka masu bakar bidan asiri suke da yawan surkulen su.
Yanzu wani katon mushirinkin bokan ne nasan ya bukaci a kawo mai yankin zanin ki nace wallahi mama haka aka taba min kafin ki zo garin nan ban fada ma kowa ba sai maryam dana nuna kayan.
Sai tace injin dai baki saka kayan ba nace wallahi na saka tace ashe idan har Allah ya nuna ma sheri ka gani ga idon ka ai sai kayi taka tsamtsam kinga kwanaki kafin muje garin nan naku.
Nace tace Yanyala na samu tana kakabe carpet din kofan nan tana tara kasan a zata zuba a cikin wani leda sai gani munyi rikici sosai da ita ban fada maki bane don gudun fitina bakiga na dauke carpet din a wurin ba.
Nace ikon Allah wai duk akan in bar gidan suke wanan abin haka tace ko ki nakasa ba ba sherin da yan bakar bida basu iyawa yar uwanzaman su ba ai Allah dai ya tsare ya kare nace Amin.
Mama dauko zanin da aka yanka din mu gani nace wa laraba ta mike taje daukowa sai ga AA ya shigo dakin yana fada min wai Abba ya daga bukin zainab sai gaba.
Da sauri nace mai subbahanallahi yace eh dalilin da ya bayar yana da kyau kin san ta kusa kara karatun yace idan ta karasa sai ayi ya wuto da ita nan gaba daya.
Nace Allah yasa haka yafi zama alheri ai ni abin zai mun dadi gashi an fara fadin dama ba zan tafi yanzu yai min daidai ke nan.
Ni dai ban san abinda yasa yayana Yusuf ya daina zuwa gidan nan ba yanzu na tambaye shi kallo na yayi zaiyi magana.
Laraba ce ta shigo dauke da kayan a hannun ta ina gani na manta yana gurin nace wanan sabon kayane fa mama sai ya juya yana kallo.
May ya faru yace nace nakai wanki ne yanzu mai wanki ya aiko min wai yazo guga ya samu an yankar min zani na da mamaki yace yankar zani kuma may za a yi dashi idan an yan ka din.
Laraba bata san sanda ta bashi amsa ba da fadin asiri mana Alhaji yace ta miko mai zanin tana mika mai tare da nuna mai gurin da aka yanka din.
Fita yayi da zanin a hannun shi laraba ta fice part din yana fita tana zaune falo yace Nafisa waya yankawa Deedar zanin ta gidan nan.
Tace wanan ai tambayan banza ne zaka zo ka sani a gaba kana tambayana wa ya yankawa matar ka zanin ta kafin yai magana Ihisan tace Ami ne Abbi tare da Yanyala muka je da Ami ta tsare yanyala ta yanka da suka aiki mai wanki.
Dawo da kallon shi yayi gurin Nafisa din yace kin gani yarki ta fadi gaskiya zaki lalata min ya da bakar bidan asirin ko har da ita kike zuwa.
Ihisan kamar mai wasa tace Abbi an kai wa wanan mutumin da baida riga har ya shafa min wani abu a jikina jikake dim dim uwar takai ma yarinyar duka sai da ta kife kasa daga saman kujeran.
Yana karasowa shima ya dauke ta da mari kauuu sai data duka ya tallabo yarinyar yana rarashin ta yaja hannun ta suka nufi part din shi.
A gaban laraba akai komai tana labarta min abinda ya faru nace Allah ke nan dayake ban da amanan ta ya fitar min da hakki na Allah ya gani ina matukar son kayan nan.
Ban ji duriya shi ba haka yasa na fahinci yana cikin bacin rai sai da safe ya shigo part dina yana fadin shi zai fita nawa zanin yake ya biyani nace ka barshi tunda ina da wasu dama cikin wanda ka saya min na lefe ne na dinka shi.
Kudi ya fito dashi koda ban kalla ba nasan kudin yana da yawa yace gashi in za a samu irin sa a nan sai ki saya a kara dinka maki kalarsa.
Nace daka barshi ai don ba yau suka fara min haka ba a gidan nan karo na biyu ke nan wallahi yace ga Ihisan ta fadi yadda sukayi wani gardama zatai min kuma.
Har fa da yata suka tafi gurin shirkan su aka shafa mata wani abu bayan bokan yai mata tsirara wai da ita da Samira duk jiya ihisan din ke fada min.
Allah ya kyauta shine kallama ga sherin ta ko yanzu din shina kara maimaitawa a bakina ya fice nace monday zamu koma school fa.
Ya juyo yana fadin monday din nan mai zuwa nace insha Allah sai yai dan shiru yaja tsuki tare da fadin Allah ya kaimu nace Amin komawan kakewa tsuki kuma ?
Yace No naso kafin ki koma motocin mu sunzo ne don akwai naki a ciki ban son wanan toiries din gare ki kwanaki naba da sako sai ba a samo wanda nake so ba.
Nace ai ba komai tunda ana kaini ba wani matsala bane duk lokacin da suka shigo sai a bani yace shike nan .
Sai ki min list din abinda ake bukata mu gani kafin monday din in baki daga haka yasa kai ya fita a dawo lafiya nayi masa daga gurin da nake zaune din.
Kudin da ya aje min na dauka na kirga sai da nayi mamaki tare da fadi a raina wanan kudin har da toshin baki dai kada naja zancen da nisa watau.
Ina adana kudin maryam na shigowa gidan sai da ta kalle ni ta tuntsire da dariya tace wanan ciki ya kara maidake wata babba mace haka.
Nace da ba babban nake ba may nake tace ai na manta tana kaiwa zaune tace yau banga buzuwar gidan ku falo ba don haka take zama kullun kamar mai gadi.
Yau Allah ya tona mata asirine ai nan dai na kwashe maganan na fada mata tace muguwa Allah yaki aniyar yar iska da Allah kadai yasan sherin da zasuyi dashi.
Nace wallahi shiya ban saka yaran nan a cikin zancen mu da ace ina masu mugun hali a rayuwan su bazasuga ana cuta min suyi magana ba tace wallahi da ba,a jin komai haka don koyo zasuyi suma yau da gobe bai bar komai ba ai.
Nace bata da kunya ai don wanan ba shine farko tsura ta ba kin manta zacen layun da aka gani cikin filo daya kirata cewa tayi sheri ake son mata dai.
Maryam tace shi wanan din ma sheri ne yar nata ta fada ai tayiwa kanta don idan tasan kunya taji shi muna cikin zancen laraba ta shigo tana fadin ga gugumanmun nan su shigo da sauri muke tambayan ta tace tace magajiya ko madam ake ce mata.
Dariya muka kwashe dashi nace kai mama kin iya sawa mutum suna wallahi maryam tace ai magajiyar ce kin sani ko har kauce hanya anayi wanan irin abu nasu haka.
Nice na kawar da zacen da jefo da maganan komawan mu makaranta tace wallahi na dauka kafin mu koma kin haihu nace haba dai yanzu fa nake a takwas.
Tace ni dai rokona kada ki haihu muna exam don wanan karon ba wani dadewa zamuyi ba sosai nace to gani nan dai ni san abin zaizo min ne a rikice wallahi.
Kana naka Allah na nasa ne ban taba daukan haka a gare ni ba wallahi maryam tace ai haka abin yake muna cikin hira mukaji ihun Ihisah kamar ancire mata rai.
Zan daga maryam taja tsuki tana fadin ina kuma zaki don baki da zuciya ta kashe ta mana ba ita ta haifi abinta ba ki kyalesu su kashe ta in sun isa sai can muka tsinkayi muryan namiji yana fada nace yadawo ne gidan.
Mama laraba tace kamar muryan Soja nake ji maryam tace shine ma don munyi waya yace min yana hanya zai shigo kallon ta nayi da mamaki nace maryam yaushe kuka dinke dashi kuma ban sani ba.
Tace kece zaune ai tun yaushe muke tare tun wannan ranan daya rage min hanya fa ai da badon Allah ya gyara ya kawo sojan ku da kila mun samu matsala dake don saura kiris kijini ana min guda.
Kallon ta nayi da mamaki nace wa ke din tace wallahi saboda ke nayi ta daga ma zancen kafa don ban san yadda zasu dauke ki ba idan zancen ya fasu anji.
Wa da zaki aure na tambaya cikin tsure ta da ido tace yayan ki mana Yusuf sai da naji gabana ya fadi nace ina zuwa daki na shiga na kewaya na fito.
Tana kwance saman digon kujeran falon nace maryam wai wani Yusuf dai kike nufi tace kina son kara kewayawan ke nan Yusuf dai da kika sani mana.
Na dafe kirji tare da fadin haba biri yayi kama da mutum ashe shiyasa zainab ke min hannun ka mai sanda tace ai bata san ko wacece ba don ko AA bai bari ya sani ba.
Maryam da kin daure ni wallahi dakin sakani tsaka mai wuya a tsakanin ku da barin gidan nan zanyi tace don may saboda kawai na auri mijin sister inlaw din ki zaki bar gida.
Nace ai idan nayi rantsuwa dubu bazan fita ba sai suce dani aka kulla zancen tace dasun dauki alhakin ki wallahi yanzun haka muna rikici dashi ne ai.
Wai wallahi nayi kadan na fada mai ai ko rikici suraj ya fishi shima kwakwan da yake kenan yasan ko waye aka saka muna rana a kd din.
Nace wallahi baki da kirki maryam harda saka rana ban sani ba tace yes don bamu son ki sani ki bata muna zance ba nace to Allah ya sani ai.
Tace yanzun haka yazo ne mu tsayar da magana a sa mai lokaci wai baison ya zauna nan ba mata nace zaki iya da yaran hajiya umma kuwa ?
Tace da ita zan zauna bafa gari daya zamu zauna ba waike baki murnan zamuyi aure a gida daya dake ne ina ruwa na da wata umma can.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Monday da muka shiga makaran ta da kyat na samu zuwa don yanayin da nake jin kaina ranan dai a dadafe nayi komai daya kaini.
Asibiti na wuce sun dubanu suka ce wai juyawa ne yasa nake jin haka ko wani month din zai juya sai mace ta dan ji jiki magani pain killer suka bani muka dawo maryam ce ta raka ni.
Two ina gida ruwa na watsa a jikina nayi sallah na kwanta can cikin barci nake jin laraba na kirana sama sama na bude idona.
Tace baki kike dasu a falo da kyat na tashi sai dana dan jima a zaune na mike zuwa falon mata ne da ban san su ba su biyu zaune.
Tun kan na zauna nace laraba kawo masu abin sha mana na juyo ina masu sannu da zuwa ina kaiwa zaune.
Gaida su na fara suna amsawa laraba ta kawo masu drinks din kwali da cups ta aje a gaban su matar tace sun gode.
Ai da kin barshi muzo maki godiya ne dama maigidana ne ya turo ni ai mai godiya a wurin ki nasan baki san mu ba ko ?
Nace wallahi ban sheda ku ba tace matar SJ jalingo ce da sauri na dago kai ina kallon ta nace ayya ban san ku bane na fara gaida ita tare da tambaya ya gida.
Tace yaso muzo tare dashi yai maki godiya kan alherin da kukai mai keda maigida shine ya fara turo mu.
Nace ai babu komai idan wanan ne ai don yaya Adam akayi tunda ba sanin ku nayi ba sai dai mun sha rigima yace a nan kuka biyo mai kuma.
Matar tace ya fada muna ranan da mukaje office din shi yace abinda mukai mai baiji dadin shi ba ai ko wurin Adam muka bi zai muna din.
Murmushi nayi nace haka yake shi nace hajiya baku sha ruwan ba tace no ki barshi a koshe muke nace haba ko kun raina ne da sauri tace haba dai.
Wallahi tun dazun muka so zuwa sai wanda yasan gidan zai kawo mu ya dan bata muna lokaci nace Allah sarki ba komai hajiya ai ba sai kunzo ba.
Don yanzu mun zama daya daku tace hakane ashe cikine dake haka nayi murmushi tace Allah ya raba lafiya wace suke tare ne ta karba da Amin.
A raina na amsa mata tace a, a kina kunya irin namu na fulani ne sai dayan da batai magana ba tace nima zubinta yai min na fulani tunda muka shigo.
Nace mu fulani ne asalin mu sai dai bama jin fulanci ne tace haba kinyi kama da fulani sosai wallahi suka mike tana fadin ana jiran mu a waje ga wanan maigida yace a kawo maki.
Da sauri na kada kai nace a, a wallahi hajiya bazan karbi ko kwandalan ku ba don Allah nayi maku Allah yasa a more .
Da mamaki ta tsaya tana kallo na tace haba dai kanwata idan kinyi haka ba zamuji dadi ba ai nace wallahi hajiya bazan karba ba tace to shike nan ban layin ki don in kin haihu muji muzo barka.
Na karanto mata layin nawa tasa a wayan ta har wajen gida na raka su motar shigan su kawai ma abin kallo ne daidai nan nafisa ta danno gidan da motar ta idon ta a kan baki na.
Ta fito ta shige da yaran ta ina tsaye matar tace wanan fa kardai ince kishiyar ki ce don mun taba hadewa a gurin wani buki da ita.
Murmushi nayi nace kishiyatace hajiya ta kada kai kawai tace bari zamuyi waya tunda ina da layin ki don kin min sosai wallahi.
Nace na gode suka ja motar su suka tafi na shigo cikin gidan Ihisan ta sheko ta rike ni nace ihisan kun dawo ya school tace cikin shirmay yara uncle din mu yace ban iya karatu ba zata fara zuba sai ga uwar ta fito.
Wani tsawa ta daka ma yar tace maza ta bar gurin ta shiga sake yare nan na fahinci tana koyawa yaran yaren su.
Ta juya da hausa tana fadin idan ba mutum ya haifar min yaraba ya barnmin abina mana wanan wani irin bakin naci ne haka.
Nace kinga kafana agun yar ki sai dai su biyo ni idan kuma sun zo bazan koresu ba don ni ba irin ki bace mara hankali don ni banda lokacin ki yanzu.
Na shige na barta awurin kalamin ta yasani tsayawa cak tace munga ciki sau ra muga haihuwan shi kuma in don shi kike taka kowa yarda kika ga dama.
Najuyo nace ke jahila ce ta karshe wallahi mai jayayya da ikon Allah ni bazan biye maki ba mu koma daidai don haukanki yafi karfi na na rufo kofan part dina na barta nan.
Maganganun ta suna matukar ci mun rai sosai wallahi wanan ko haihuwar nayi gidan nan yaya yaran nawa zasu taso a cikin wanan rayuwan gida kullun fitina haka.
Duk da anty hauwa tace in yi kokari in haihu a cikin gidan nan ammani ina jiyo ma kaina abinda kaje ya dawo ne idan na haihu a cikin wa yan nan kurayen dake farauta na haka.
Zan mai magana ya barni in koma gida ko kaduna da zaran month dina ya kama wata zuciya tace min karatun ki fa.
Ajiyan zuciya na sauke nace kuma dai dole fa inyi hakkuri da wanan karatun in sama ma kaina lafiya a gidan nan tukun zai fi in da hali ni kan ya canza min gida ma da yafi.
Ranan da nayi girki ina son mashi maganan kaini gida sai gashi ya rigani fadin gobe zamu Niger da Nafisa babanta baida lafiya.
Cak na tsaya ina fadin goben nan yaya yace eh in Allah ya kaimu sai dai a can zan barsu in dawo sai tayi kwanaki ta gama ganin su ita zata dawo.
Antan cikina ne ya kada sai da naji abincikina yana juya min lokaci guda don mamaki abinda ya fada min.
Dama haka maza suke munafukai ne wai ni naje gida bai kaini ba sai driver yasa ya kaini ya dauko ni.
Lalai na miji ba dan goyo bane ba a kuma bashi amana ni ke nan iyayyena basu kai yaje ya gaida su ba ke nan har ya kare bayanin shi ban kara fahintar may yake fada min ba .
Ya lura da sauyawa na amma sai ya dake kamar wanda bai fahinci wani abu ba daga gare ni a dadafe naga gari ya waye min na fice daga dakin.
Bai kulani ba ya gama shiri ina jin hayaniyar su ya gaure gidan na shige na dakina can sai gashi ya shigo ina kwance a kuryana.
Yasha wani shadda sai maiko take zubawa duk da shi ba gwanin saka kaya hausawa bane sai kayan sukai matukar karban jikin shi sosai .
Amma ni sai kyau di ya koma min duhu a idona ya karaso inda nake ya samu bakin gado ya zauna.
Mamaki yake yadda tunda yayi sallama ban karba mai ba gashi na nuna ma ban san shigowan shi ba dakin.
Muryan shi naji yana fadi bakyajin dadi ko yau ba zaki shiga school bane na ganki a kwance haka shiru nayi mai ya kara tambaya bakya jin dadi ne wai Deedar.
Nace lafiyata kalau yace ki fada min mana udan bakyajin dadin jikin ki ne a kaiki asibiti nace idan ma banjin dadi ne ai wanan ni ya shafa ko ba kai ba.
Yace may kuma yakawo wanan magana haka nace don Allah malam kaje kaji da abinda ke gaban ka ka barni in ji da nawa zancen matar ka shine a gaban ka ni da ban da galihu a gurin ka ai ban samu wanan gatan ba.
Ko asibiti sai idan nakai kaina don jin lafiya ta baka damu da ka san lalurana ba sam a gidan nan ajiyan zuciya ya sauke tare da fadin.
Duk akan tafiyan da zanyi da Nafisa ne kike fada min haka nace Allah dai yakai lafiya umma ta gaida assha na mike na shige ban daki na barshi a gurin.
Ya dade zaune gurin yana jijina magana a ranshi kafin ya mike ya nufi kofan ban daki ya murda yaji shi a rufe gam ina daga ciki ina jiyo muryan shi yana fadin.
Deedar ki fito muyi magana na fahinta dake shiru ban bude kofan ba har yagaji da jira ya fita danaji shiru na bude daki na fito gidan ms tsit a laman sun tafi ke nan.
Ina tsaye ina sa kaya a jikina kiran wayan shi ya shigo min ban daga ba har kiran ya katse ya sake kira karo na biyu hakana kyale wayan ya tsuke.
Nagama shiri na fito na samu driver a waje wai yana jirana nace ayya ka huta abinka zanbi kawata ne ta sauke mu sai ga maryam ta iso ta bude min na shiga.
Kallona take yi tare da kallon titi wai may ke damun ki ne khady yau na ganki kinyi wani so weak dake mana haka ina AA yake bai saukeki ba kuma ?
Ban kalle ta ba na bata amsa da fadin ya tafi Niger da Nafisa yau da safen nan da sauri ta juyo tace Ni may khady don Allah ki bar wanan wasan .
Nace wallahi maryam yau da safen nan suka tafi tace amma dai maza shegu ne wallahi yanzu shi baiji kunya yin hakan ba khady.
Nace kunyar may zaiji ba matar shi bace ni don yaje garin su ba shine damuwa ba banbancin da yake nunamin a filin Allah maryam shine ya fara isata wallahi.
Ki duba ni da naje gida maryam ba shi ya kaini ba bai kuma je dauko ni yanzun ma bai fada min zancen tafiyan ba sai jiya da daddare yake fada min.
Tace ya fada maki yasan bai shuka gaskiya ba ta yaya zai fito maki da zancen da wuri ki tayar mai da hankali ya fasa.
Koda yake itama baki san irin kwaram din da suka sha da ita ma kafin suyi tafiyan ki kyalesu su suka sani indai sune ko acan sai sun sayar da hali ai.
Nifa tafiyan bai damay ni ba maryam sai dai ni da yake nuna mata ba kowa bace a gare shi nan dai na kora mata yadda akayi muna shiga school tace kyale shi kada ki daga sai kin ja masa rai sosai.
Mun shiga lectures bacin rai bai barni nayi abin kwarai ba ranan da kyat naga mun taso ta dauko ni ta kawo gida.
Gidan naga yai min mu kadai dagani sai laraba kadai a gidan da dare ma na samu ya kira ni bandaga wayan ba karshe ma kashe wayan na kwanta abina.
Kwana uku ban bude waya ba ina amfani da waya ta tada da layin dabai sani ba maryam na sauke ni motar Yusuf tana shawo kwanan gidan.
Tsayawa mukayi muna dakon zuwan shi gaidashi mukayi ina fadin haba yayana ka manta da kanwan ka gaba daya.
Yace ba hakana bane khadija aiyuka ne sukai muna yawa ban kuma samun zama yanzu sosai nace Allah sarki maryam tayi min horn tace zata wuce nace sai gobe.
Hararan ta yayi yace kece mai daurewa karya gindi ko kin hanata bin umurnin mijin ta tana biye maki ko ?
Nace haba yayana maryam bata da laifi binta shine sauki a gare ni tunda wanda nake nan don shi baisan muhinmaci na ba.
Yace a, a kanwata kada kice haka don Allah don ba haka zancen yake ba gaskiya daga cikin mota maryam tace baku da gaskiya wallahi.
Ke rufa muna baki don Allah tsigar da yake magana da ita na fahinci wani abu yace yanzu khadija ya dace ace mijin ki yayi tafiya baki kirashi kinji saukarshi ba har wanan lokacin.
Ai ba tafiyana yayi ba yayana tafiyar matar sa yayi kuma suna tare kiran mai zan mai kumani yanzu Allah dai ya dawo dasu lafiya maryam tace shike nan kuwa.
Yace ki daina bin zancen wanan mara gaskiyan zata kaiki ta baro wallahi nace yayana maryam din ne kuma yau zatakaini ta baro ?
Yace kin ga mubar zancen nan muyi na gaskiya don wallahi baki kyauta ba khadija mahaifin Nafisa ne bai da lafiya suka je gaida shi.
Daga cikin motar ta kara fadin shikenan kuwa ke dan Allah barnan ai surikin kine zan fada mai kece mai zuga mai mata tace rufa min asiri tana kokarin jan motar ta ta bar gurin.
Yace tsaya ai magana ta fahinta ai abokin kuka ba a boye mai damuwa abinda kikayi ai ba daidai bane khadija dayakiraki ai sai ki dauki wayan kiji korafin shi ko.
Amma yana can kin saka shi a damuwa gashi kin ki daukan waya ga kuma kinki bari driver ya kaiki school gaki a cikin yanayi.
Nace ai yanayin nawa bai gaban shi nice da kaya ni ya dama ya kada kai yace ba hakana bane khadija ku na ma maza fahinta baibai wani lokaci.
Lalurar ciwo ya kawar da komai yanzun haka sai da yaje ne suka kai tsohon asibiti duk wanan ciwon ba wanda ya kaisa asibiti ashe.
Nace eh hakan yana da kyau sosai yanzu dai barin in kirashi kuyi magana yaji lafiyar ki don Allah ko hankali shi zai kwanta.
Nace akwance hankalin shi yake tunda yana tare da farin cikn shi ai basai yaji tawa ba baza ki min ba ke nan sai naja na tsaya daga cikin mota maryam tace ki saurare shi kiji may zaice din.
Bashi ke nan ba baidai wuce dadin bakin su na maza zai maki tunda kina sokuwa sai ki yarda Yusuf yace khadija ki saurare ni nan kiji may zan fada maki.
Wallahi wallahi duk mu nan musan AA yana son ki shuumancin matar shi kawai ke damun ku khadija kin yi hakuri a gidan nan kowa ya sani kuma kina kan yi .
Kinyi abinda bako wace mace zata daure mayin sa ba saura kiris ya rage khadija buzuwa takai karshen ta a gidan nan.
Yanzun dai ga wayan saura bayani zan maki idan kun gama wayan yana kira ya miko min na karba muryan shine yake sallama na amsa.
Yace kuna lafiya nace kalau yusuf ya zagaya gurin maryam ya barni a gurin muna wayan ba wani magana mai tsawo mukayi ba ya tambayi lafiya tace da dalilin da yasa na ki daukan waya nace ba komai sai anjima na kashe wayan nace wa Yusuf dake duke ga wayar shi ya karba yana fadin har kun gaisa nace eh nagode.
Yace ki kara hakkuri aimu ko hanzu bukatan mu ya biya khadija kin shigo gaki har da cikin a gidan nan.
Wanda ba wanda yai tsamanin hakan a gidan nan haihuwan ki gidan nan shine babban masifan dake addaban Nafisa a yanzu don nike jin irin wayan da sukeyi dashi idan muna tare.
Don haka don Allah ki kara daurewa khadija ansan abinda zafi nima na nuna mashi abinda yayi bai kyauta ba yakawo min uzurin rashin lafiyan tsohon na yarda.
Haka dai muka dan dauki lokaci dasu a gurin karshe mukai sallama suka tafi na shigo ciki na samu laraba a babban falon gidan gana kallo.
Nan na zube falin muna dan taba hira tace ta kawo min abinci ne nace ta kawo min amma kadan na mike ina fadin bari mu shiga ciki dayani in rage kayan jikina.
Sai da na watsa ruwa na fito falon na samu ta aje min kulan abinci na zauna naci muna gurin akai sallah a nan nayi sallah tara muka shige daki.
Cikin dare na falka da tunanen mafalkin da nayi a gidan maganan tsoho bado ne ya fado min a raina tashi nayi na gabatar da nafila ban kwanta ba sai da aka kira sallah bayan na sallamay na fito ina kiran laraba tafito a dan gigice tana fadin lafiya uwar dakina ko jikin ne.
Zama nayi ina fadin mama wani malki nayi a gidan nan jiya yau yakai kwana uku a gurin mugudanan ruwan dakin maigidan nan ko dai akwai wani abune da aka boye a gurin nan mama ?
Tace bazance a a ba don kin san wani lokaci mafalki na zama gaskiyane tunda idan mutum nada tsarin mutanen a kanshi zasu iya nuna mai haka ko kuma Allah da nasa ikon idan zai yake ma mutum wahala sai ta baiyana maka abu ta inda baka zata ba.
Nace yanzun yaya ke nan tace idan kina gane wurin muje mana zan ma mai gadi magana tunda muna shiri dasu sai mu tona mu gani tunda mu kadai ne a gidan.
Tunda safen nan muka fita zuwa baya tare da dayan maigadin dataiwa magana naga kokarin mutumin nan daya iya tona wurin baiji kazantaba sai gashi ya ciro wani kwallaba dake da layu da yawa a cikin sa.
Mamakine ya kama mu sosai jikina har rawa yakeyi yace zai tafi da kwalban a bincika masa ko na maye a ciki muna shiga falon akwai wani carpet wuri hawa step din saman AA nan ma nace wa laraba ban yarda da gurin ba.
Ta sake kiran maigadin ya shigo suka daga yace akwai rami bayan daken din ya tona saida naji tsoro nan ma wani abune an cacaka mai allurai sunfi a kirga aka bine.
Maigadin yace wanan matar takai shuuma wallahi sai ya cire abu har gurin kofan ta ya fita dashi gidan haka na wuni sukuku a gidan.
Sai AA ya kwashe kwana shidda a Niger bai dawo ba ya kama jumma tunda maryam ta sauke ni na shiga gida tace zata shigo da dare ta kawo min sako dana bata tazo mun dade muna hira ta wuce.
Washe gari har mun rufe gida akai ta bugawa muka bude AA ne ya dawo a cikin dare nidai ina dakin ban fito ba sai gashi ya shigo ba laifi nayi mai sannu da zuwa da tambayan mai jiki.
Yace da sauki tare da tambayana lafiya ta nace Alhamdullahi haka muke zaune a gidan ba wani sakin fuska a tare dani sai wani rawan kai da yake min ban kula ba don nasan don matar bata nan ne.
Sai da ta share sati biyu ta dawo da yamma ina jin hayaniyar su nasan ta dawo ke nan sai ga ihisan ta shigo min har part dina.
Ban fita taron ta ba tunda da zasu tafi bata sallamay ni ba ita ma na gama abinci na kai mai muna zaune sai gata ta shigo part din shi da kayan dake jikinta data dawo dashi wani shadda ne blue yasha aiki da zare yellow.
Abinci yake ci ina zaune a gefen shi ina game da waya na ta shigo ta samu wuri ta zauna can naji tace ke ban dago ba don kiran rainin da tayi min ta sake fadin dake nake magana fa.
Nace ki je gun yaysn da kika haifa ki magana dasu hakana ba dai ni khadija ba tace kin san abinda kika yi ai nace ko da ban sani ba na sani din don nasan ba alheri bane ya kawo ki nan yanzu.
Tace amma dai kin san na dawo yau ko may zaisa ki kawo masa abincin ki kuma nace kin duba lokacin da kika dawo ko ko tsoron ki zanji in canza lokaci in bar maki shi.
Table din ta buga da hannu ta saida kayan sama suka girgiza tace wallahi kinyi kadan ke baki isa ba wallahi nace isar ke nan kikaga haka ke wacece da za a ji tsoron ki wai.
Ya dago rai bace yace mata Nafisa bar nan tun kan na bata maki rai ina mun gama wana maganan tun dazu tace wallahi ba zata bari ba don ita zatai girki tunda ta dawo yau.
Yace sai kiyi mu gani tunda jidali kika dawo dashi ke wata irin mace ce da bata da godiyan Allah kwana nawa ina can tare dake bata bata ranta ba kan haka yanzun ma kin dawo din ba zaki bari a zauna lafiya ba .
Nidai ban sake kula ta ba nan suka gama sa insa din su har ta gaji ta fice tunda na kwanta ban motasa ba shima bai nemay ni ba nasan yana cike da bacin rai ne.
Tunda na koma part dina banjin dadi don haka na samu guri na kwanta can cikin barcin da na dan samu ya dauke ni naji mara na ya yanka min.
Tun ina ji kamar mafalki nake har yakai na bude idona na dan saurare sai ya dan lafa min na sake rufe idona sai kuma ya dan kara cunkula na na bude ido ciwo sosai yake min dabaran kiran maryam nayi a waya .
Sai dai wayan ta yana busy naja tsuki na wurgar da wayan ga maran yana addabata da ciwo irin wanda ban taba jin sa ba.
A hankali na mike zaune daidai lokacin da naji ya lafa min din na sauko na nufi falo in duba laraba na samu laraba din ta fita bata nan cikin part din kitchen na nufa don in duba kanwa na daiga kanwar najika na nufo falo sai naji kafata ya rike min lokacin laraba ta shigo dauke da kayan wanki a hannun ta .
Tana ganina tace subbahanallahi uwar dakina lafiya dai ko nace mama marata ke min ciwo yanzun kuma kafata ya rike min sosai ban iya dagawa.
Tace ubangiji ya sauke ki lafiya ko in fada ma Alhaji don na barshi a waje yanzu kaina girgiza mata na samu kafan ya sake min na karaso gurin kujera na zauna cikin karfin hali.
Na dauki kanwar nasha ina aje cup din yana shigowa falon kallon yanayina yayi ya fahinci banjin dadi yace lafiya kike kuwa Deedar ga AC kuma kina zufa haka.
Na goge zufan cikin karfin hali nace haka na yake min kwanan nan cikin ya kara murda min na nade wuri daya yace nace baki da lafiya ko muje asibitii ne na girgiza kai nace ba komai ai zai bari.
Yadan dade tsaye a kaina yana kallona ya juya fita daga dakin da kyar na samu na daga zuwa dakina laraba tana tsaye ta kallona har na shige maryam na samu tana kirana da kyar na daga wayan nace maryam kizo da saurin don Allah cikin wani irin murya mai ban tausyi.
Tace haihuwa ne ko may khady nace nima ban sani ba ki dai zo don Allah tace gata zuwa yanzu ta kashe wayan.
Ya lafa min ya taso ba a dauki lokaci ba sai ga maryam ta shigo ta samay ni ina yarfar da hannu ta iso gurin a rude tana fadin haihuwar ne khady ban sani ba maryam ko shine yazo wani irin ciwon mara dai nake ji maryam.
Can ya yanka min nace wayo maryam zan mutu wallahi ta rude tace barin in kira mama kila tasan haihuwa ita laraba na shigowa dakin tana kallon yanayina tace wanan kan haihuwa ne sai dai kila da sauran lokaci.
Waya maryam ta dauka tra kira anty Hauwa tai mata bayani tace bari ta turo sister Larai ta dubani ba ajima ba aka kira maryam ta dauki waya sai ta fita.
Tare suka shigo da matar da aka kira da sister larai din tana zuwa tace in kwanta ta dubani tana dubawa tace haihuwa ne yazo sosai a dan ban tea ko kunu in sha don ba a so nakuda da yunwa.
Da sauri laraba ta hado min tea mai zafi ta kawo na karba na sha da kyat do ni ba gwanan shan tea bace na sha na dire cup din kasa ina kallo sister din ta gyara guri a dakin leda ta shinfida sabo da ta bare shi a gaban mu.
Tace su dan fita daga falo su jira mu ta hada allurai tayi min cikin ikon Allah tana min alluran kamar ta jawo nakudan kusa ne na koma ba zama ba tsayi.
Maryam ta kira tana tambayan ta akwai leda a kusa yadda maryam taga ina cije baki itama ta fara kamar mai nakudan tace don Allah fita wanan rakin ki har yafi na mai nakudan gaskiya ai.
Da ya wani taso min tace kwanta kwata da sauri da taimakon ta na nisa da karfi tana kiran oya push pushi niko Allah nake kira a bakina.
AA yana shigowa falon don ya dubani a yarda ya barni kuka yaro yana gauraye falon yaja ya tsaya yana kallon maryam data rude sai kuma ya nufi kuryan dakin ya daga labulen dakin .
Don ya tabbatar maryam na fadin Alhamdullahi ta haihu ta hau murna laraba ma sai hamdala take zubawa a gurin da mamaki ya sake labulen dakin yana fadin dama haihuwa zatayi ne mama tace eh Alhaji.
Haihuwar ce tazo da sauki wallahi kiran ds ka kwala wa maryam daga ciki ta shigo da sauri dakin tace karbi yaron miko min wani zani again jikins rawq ta bude wardrobe dina ta dauko zani.
Tana mika wa ta fito yana tsaye ya kasa zama a dakin ta mikawa laraba yaron mai matukar kama da uban sa sai dai shi farine sol yafi uban fari.
Mikewa yayi da sauri ya karaso wurin laraba kamar zai karbi yaron Laraba tace bari a goge shi Alhaji.
Yace to to mama ikon Allah haka abin yazo da sauki kuma ikon Allah sai hamdala yake zubawa ban dauki lokaci ba macen ta fito sai kuka take zuba har yafi na namijin kamar yai tsuntsuwa ya fada dakin yace wani again ?
Kafin wani lokaci matar da yake aikin su ne ta saba ta ta gyara yarinyar ta aza saman gado ta kwala wa maryam kira ta shigo tace dauki baby girl din ki bamu wuri.
AA kan kasa hakkuri yayi sai da ya karbi yaran tun ba ai masu wanka ba yai masu addu a ya fito ya bari ana gyara muna jiki.
Direct wurin Nafisa ya nufa yana washe baki yace ki min murna mata na ta haihu yanzu tace may kace yace nace Khadija ta haihu yanzu ta zabura ta mike tsaye tare da fadin ina yace a dakin ta mana.
Kana gidan nan ta haihu Samad yace yanzun na shiga in dubata na samu ta haihu tace nashigs uku ya zaro ido yace haihuwan kika shiga uku ko may ?
Hannun ta yana saman kirjin ta tace ka barni don Allah da abinda ya samay ni a gidan nan can kuma tace may aka samu yace mace da namiji ta zube saman kujera kamar ba kashi a jikin ta jagwab

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Daga inda yake tsaye a gurin ya buga ma mommy waya yana sanar da ita zancen haihuwan sai yusuf da ya kira tare da kiran mahaifana ya sheda masu.
Tana zaune ta zuba mai ido tana sauraren abinda yake fadi a cikin murna tun tana sheda shi har ta dinga ganin ya koma mata wani abin,ki a zuciyar ta.
Jirin da take jine yasata dafe kanta da hannun ta daya sai rintse idanuwanta da tayi tana jin shi sama sama yana farin ciki.
Fitowan laraba part dina yasa ta bude ido ta sauke kanta tana fatan raba tace ai yaran sun mutu ko sai taji laraba na fadin Alhaji matar data karbi haihu tana bukatan ganin ka.
Yana cikin fara,a yake fadin to, to mama gani nan zuwa ya dakatar da wayan da yakeyi suna zaune tare da bakin da tazo dasu sai yanyala da itama hankalin ta a tashe yake wurin.
Yana barin gurin ta kalli yan uwan nata a cikin yare take magana rai bace tana fadin shike nan ta kara min asiraina dana binne a gidan nan .
Dayar tace asiri kika birni Addah tunawa da wace take maganar ko wacece ta ja tsuki tayi daki yanyala ta mike ta bi bayan ta zuwa dakin.
Samun ta tayi tana safa da marwa a tsakiyar dakin tare da dan bubuga dundun hannuta wani saman wani tana jin motsiyan yanyala ta juya da sauri tana kallon kofan.
Yanyala wanan yarinyar ta gama dani a gidan nan an fada min kada in yarda a zubar da jinin haihuwa a gidan don komai da nasha wahalan nema na girka kaina zai lalace yanzu ga wanan banzan tazo ta haihu min a cikin gida na shiga uku ban san ta ina zan fara ba kai na ya daure da yawa yanyala.
Yanyala tace madam ya kamata a kira tun lokacin bai kure ba muji shawaran ta don ba abinda za aiwa sanyin jiki bane.
Kira biyu madam ta dauki wayan ta fara mata kirari tana fadin sai ke manyan mata a gidan Abdulsamad ba wata bayan ke a gidan nan.
Madam yau ba wanan a gare ni madam kashina ya bushe a garin nan yarinyar nan ta gama dani a gidan nan.
Cikin tsoro madam ke tambayan may ya faru kuma wani abin tai maki daga dawowanki jiyan nan tace madam yarinyar na shu,umace ta haihu min a cikin gida madam ta kara min duk wani abu danake tunkaho dashi a gidan nan na kwarai.
Ta haihu madam tace hankali tashe tana tambayan Nafisan tace gashi na fada maki kinji wallahi ta haihu ko minti talatin ba a yiba.
Cikin rudewa madam tace gani nan zuwa yanzu ki jirani don Allah ki natsu Nafisa har in zo musan abinyi tace ina jiran ki ai ban iya komai saura kiris in fasa ihu Allah ya kare ni.
Koda ya shiga dakin ya samu na shiga wanka muna ciki da nurse din data karbi haihuwan nawa jin shigowan shi maryam tai mata magana gashi ya shigo sai ta fito daga bayin ta barni a ciki.
Takardan da ta rubuta magani ta dauka ta mika mai tana sharce zufan da tayi na wahala tare da fadin wanan nake son a sawo min zan mata ne ta dan samu saukin tsamin da jikin ta yayi sai dana gyara jikina na fito daga bayin ta shiga gyara yaran wankan farko tayi masu ta kawo zaitun ta goge jikin su dashi kafin ta kara masu wanka na biyu sai ihu suke calarawa.
Daga inda nake ina shafa mai ina mamaki a raina wai nice na haihu haka yau na dandani abinda ake fadi gamay da haihu.
Wai cikin suna fadin abin yazo min da sauki ke nan gaskiya nagaida mata a gaisheku iyayyen gida don dai kune gidan.
Komai ya kamala sai wani irin barci da nake ji yasa na kwanta nurse din nan ba karamin kokari tayi min ba sai data gyara ni ta gyara yara ta dawo kan daki laraba na fadin ta bari ta gyara tace aikin ta take yi ai.
Mahaifa ne suke muhawaran inda za a rufe maryam da laraba ke kuskus din rufewa inda buzuwa ba zata gani ba don tana iya wani sheri dashi.
Laraba ne tace bari taiwa sabo security magana taji nan ta fita gurin su ya tare ta yana washe baki tare da fadin ashe uwar dakin mu ta sauka yanzu maigida ke fada muna wanan abin farin cikin daya samay mu yau .
Ta gaya mai abinda take bukata dashi yace akwai ko yadda za ayi sosai ma nan ya nuna mata bayan gidan engine din wutan gida na stand by yace yasan yarda zaiyi ta fita tazo mai dashi ya faki idon mutane ya nufi gurin ya rufe ya mayar da kasa kamar ba a taba gurin ba da farko.
Madam ne tsaye tana rike haba tana tafa hannayen ta tace ai rudewa ya kasa barin in tambaya mai shegiya ta dire mai nasan itama bazai wuce mace ba tunda an fada muna sannan yaya halittan yarinyar yazo ?
Daga inda Yanyala take zaune take fadin biyu fa ta haifa madam data dafe kirji sai da takai zaune bata sani ba tace tagwaye matane zallah ko?
Mace da namiji naji yana bugawa iyayyen sa kaita fara girgizawa tana fadin shike nan ko a yanzun ta ci galaban mu gurin wanan.
Madam shine damuwa ji irin kudin dana narka wurin cikin yarinyar nan kan in haifi namiji kowa kuma na fada min namiji ne a ciki na ashe shegiyar yarinyar nan ta sa an musaya mata da dana.
Yanzu abinda nake son ki dashi ki kwantar da hankalin ki ina wanan abinda na dutse ya bayar tace yana nan tace gobe idan Allah ya kaimu zan shigo sai mu amfani dashi.
Bar yan iska ba suna murnan an haifi namiji da mace ba to sai mun lalata ruyuwan yaran su koma dolaye ko sakarkaru sai muga yadda za ayi kuma.
Ajiyan zuciya Nafisa ta sauke tana fadin sai yanzu hankali na ya kwanta don da har na mance da zancen maganin nan.
Yanzu ko har naji sanyi a raina shegiya sai ta kare rayuwanta wurin yawon neman magani wa yaran bata gane komai ba.
Don Allah madam kada ki wuce goben baki shigo ba don kin san ka,idan maganin an haihu gari ya waye ne kowa ya gama ganin lafiyayyen da sai aga ya sauya daga baya kuma.
Karki damu badon yau munyi da hornarable zai shigo ba ai da anan ma zan kwana wallahi tace ke dai da wanan hornor din naki mutu karaba ke nan.
Tana mikewa tace ya za, ayi da tsohon zuma ake magani abu tun muna da jajayen sawo idan da ban gama da dan baza ba da yanzu bai dade da gudu ba ya barni tunda yaci moriyar ganga ya samu rabon shi suka tafa.
Ina kwance barci nake ji saidai ban iya yiba a lokacin don yadda nake jin jikina wani kala inayi ina shafa cikina tare da tuno abinda ya wuce dan awanin da suka shige.
Muryan AA ne dakin yana fadin wanan ne maganin don yace akwai wanda babu sunan sa sai dai akwai irin shi kudin su daya da wancan din.
Ta karba ta duba tare da fadin sune inda nake kwance ya dan kalla yana fadin barci take ne ?
Sai lokacin na motsa tun shigowan shi dakin ya karaso bakin gadon yana mai kura min ido kaina na sada kasa don na kasa jure kallon da yake min din.
Deedar ya jikin ba dai inda kike ji yanzu ko ya tambaya yana kokarin taba min jiki nace lafiya nake nurse din dake dakin bai hanashi tabani ba yana fadin maman twin's ke nan ?
Murmushi nayi masa na turo baki nace ban san ya akayi na dauko wanan hannun ba ko ita dake da gadon abinta bata haifa sai ni.
Yace nowarder nikan ina mamaki ina kika dauko tagwaye kuma nace maman mu ce tagwayen itama namiji ne abokin tagwacin ta ai.
Amma mama ta kyauta min wallahi don nike da wanan baiwan data sam baku a zurianta gashi ita bata samu ba ni na samu ta sanadin ta.
Maryam ne ta shigo dauke da yaran a hannun ta da suka sha kayan sanyi da farin showel tace ga kyautar Allah ka rika dazu ka dauke su ba ai masu wanka ba.
Sai da ya karbi yaran ya dade yana masu kallon kwab dukkan su biyu ya dago yace wa maryam wanan sun dara uwar su ma fari nake gani tace shi muke fada da mama yanzu.
Wa yan nan gaskiya kamar diyan wasu halfcase dasu ya kara maimaitawa yana mikawa maryam su nace daga inda nake maryam dan ban ruwa in hade maganin nan.
Ta kwantar da yaran a gefe na yace ruwan zafi fa zaki bata tasha kada ki debo mata na sanyi shiyasa nace mommy ta taso yau din nan tazo.
Nace a wanan lokacin yace jirgin yamma zasu biyo ita da Altine zasu zo da sauri nace ashe baka manta da alkawrin da kai mata ba ke nan yace yana raina ai.
Don naso tazo tun kan a haihu don ban dauka tarbon wata zaki yi haka ba na dauka ko sai irin tsakiyan wata din nan ne haihuwan idan naje sai in zo da ita.
Har yakai kofa zai fita bayan ya tsare ni da ido nasha maganin sai ya juyo yana fadin Nafisa ko ta shigo dakin nan na tare da fadin kasan ba a kimtsa ba kila tana jiran a rarage ne ta shigo.
Kai ya girgiza ya fita maryam ce ta kalle ni tana fadin kai namiji ji mutumin nan yadda yake rawan kai da samun yaran nan yanzu.
Nace haka yake ai idan an mai haihuwa sai dai son yaran nasa a baki ne kawai ai baida jan diyan shi a jikin shi shi.
Tace to ke zaki yarda ne aikrce zaki koya ma yaran manne masa ko baiso kuwa don idan ma baki koya masu ba sai wata tazo kiga yana nan nan da diyan ta kina kallo.
Ajiyan zuciya na sauke tun yanzu zan fara fuskantar wani abu kuma akan yaran da basufi awa daya da fadowa duniya ta mu ba mai cike da rikici a cikin ta.
Sai lokacin nace maryam ta miko min yaran don in masu addua na karanta masu adduoin tsari tare da bude farinjin su na karanto masu adduan tsari daga zina.
Biyar laraba ta gama abinci har lokacin nurse din nan mai kirki tana gidan tana ta koya mun komai da zanyi akaina da babeis din.
Abincin suka debo min nurse din nan ta sani a gaba ina ci mommy suka iso gidan ina jin muryan su sai gasu dakin da murnan su suka shigo sai naga har da ya Aminana suka zo.
Ina ganin ta nayi narai narai da idanu kamar zanyi kuka saboda dadin ganin ta da nayi gaishe su na fara yi mommy ta karaso inda yaran suke tana fadin khadija aike ke da sannu yara manya haka dasu kamar ba tagwaye ba don Allah.
Nan dai ake anata hira sai ga Laraba tazo tana kirana dagani maganane da ita haka na mike mommy tace dawo ki saka hijjabin ki ko nan da falo zaki yanzu ki kula da hakan.
Na samu laraba take cewa muje kitchen naga abinda aka shigo dashi sai dana dan duba nace mommy za a kira ta san yadda za ayi dasu ai.
Nama ne mai yawan gaske sai kan shanu har biyu da kafafuwan su da sauran tarkace ya kwaso dakin na koma suna zaune nace mommy Laraba na magana dake da Anty Altine a falon.
Mikewa sukayi sun samay ta ta nuna masu kayan da abinda nace mommy ta duba tace dayake akwai frezer sai a saka zuwa gobe amma kayan cikin a dan diba ke Altine ai mata ferfusu da zata sha kafin ta kwanta yau.
Bayan sun gama adana komai yadda ya dace mommy na shigowa dakin tace ikon Allah ance naka sai naka yau mune a gidan babangida ake halarta muna komai a matsayin mu na manyan shi.
Ance ma hakurci mawadaci abinda muke mashi nuni dashi ke nan tuntuni ya kasa fahinta na tuna da mukazo zaman yar nan Ihisan irin taskun da Nafisa ta nuna muna a gidan nan lokacin.
Altine ce ta tambaya ina take ne mommy tace tana kasansu ai nace ta dawo jiya mommy tace jiya jiyan nan dai nace eh jiya suka dawo daga can.
Altine ta kara tambaya tashigo taga tagwaye ko laraba ne ta basu amsa da ko leke ba wanda ya shigo daga sashen ta tana fadi ta fita.
Lokacin na bata rai nace ban ma son su shigo din mommy don mafalkin danayi kafin in haihu nan dai na koro masu abinda nake tajiwa akan yaran nace mafalkin hakan nayi da Nafisa din.
Da sauri Altine tace indai ina gidan nan kuwa ba zasu ga yaran nan ba har su dauka don wallahi kemaymay zan masu idan sun shigo .
Mommy tace dole muyi taka tsantsan kan haka don hajiya mama saida ta fada min haka dana shiga muyi sallama da ita wallahi tace don Allah musa ido kan shu,umar matar shi ashe kinga da batu ke nan a gidan nan.
Ya Amina da ba gwanar magana ba sai fadi take Allah to ya kare yanzu mommy kina ganin zamu iya hana mata su ta dauke su din nace in dai har anyi suna basu sanu taba su shike nan ai.
Anty Altine kamar yadda nake kiranta tace har bayan suna indai ina gidan nan bazata dauke su ba may ye amfanin boye mata an san manufar ta ne.
Ai gara a nuna mata tunda itama haka take wa mutune idan ta haihu har yanzu wayasan diyan ta a cikin dangi.
Nan dai suka sha hira akan nafisa din har wani lokaci sai kafin in kwanta nace ma mommy yaya zasu kwanciya.
Tace bari taje dakin da ba kowa su sauka a ciki nace ya Amina tace a a mommy ke ce dai zaki zauna dasu nan mana ni da Altine sai muje can dakin ko dakin laraba.
Mommy tace dake dai Amina zamu tsaya nan din don dare da sauran lalura don bamu san yaran ko suna fitinan dare ba.
Ni barci ya cika min ido koda AA ya shigo masu da ledan kaji gassasu ya dan duba yaran suka gaisa da baki yadan yi hira da Altine tana tambayan shi ina tarin buzayen gidan shi .
Dariya yayi yana nuna ta ya fita ya Amina ce ta tayar dani wai in tashi in kewaya kafin a kwanta don inji dadin barci da dadi ruwa ta surka min na shiga na fito take fada min wai ga kajinan in ci na gyada kai nace bazan iya ci ba anty mommy ta hauni da fada tana fadin zaki yi jagon wasa khadija jego fa baison hakana daure kici ko kadan ne da dan ruwan tea sai ki kwanta.
Badon naso ba haka na daure na sha tea din na kwanta can cikin dare nake jin muryan su wai namijin ya hana su barci yana kuka.
Ruwa suka bashi sai ya dan fara barci kuma yasa kuka ya falka sai da mommy ta goya shi suka dan samu barci tana fadin yunwa yake ji yasa bai runtsa ba.
Washegari koda bakwai yayi har nayi wanka na shirya ko suna ta hada hadan wanka da hada abin karyawa zuwa tara duk mun karya muna zaune sai ga Nafisa da madam sun shigo dakin .
Sai da naji gabana ya fadi Altine dake kitchen ne ta shigo dakin da saurin ta taja ta tsaye a bakin gado.
Bayan sun gaisa dasu mommy tace ga kawayen ta sunzo suga babies su gaida mai jego tana wani fara an dole ta nufi bakin gadon da yaran ke kwace suna barci.
Altine tace dakata kada ki taba su don Allah barci suke yi ta riga nafisa dukawa gurin da yaran su wani kallo Nafisa tayi mata tace nice zaki hana daukan yaran ?
Tace ban hanaki ba amma aladan mune ba a taba yaro idan baiyi sati da haihuwa ba don haka barsu nan har zuwa gaba madam tace amma ai itama uwace a gurin su ko ko baki sheda ta bace.
Haka umurnin yake daga kakanin yaran komu nan ai kin ga daukan su mukeyi ba dai ko zargina kike son yi komay nafisa ta fada.
Babu zancen zargi anan amma ki barsu nan ikon Allah yaran ma rowan su akeyi ke nan nidai kaina na duke ina cin ferfesun da aka aje min yaji kayan yaji na gargajiya sai kamshi yake yi.
Kiri kiri sukai wa juna sai da Altine tayi masu na mahaukata ta nuna masu ita tsohuwar yar barikice itama suka fice baram baram a part din .
Mommy tace yau Altine kin cece mu da muna kadai a dakin nan ai kyale su zamuyi su dauki yaran ajiyan zuciya na sauke baya fitar su.
Mommy tace falo zamu koma duk wanda yazo muce suna ciki don zasu iya biyo muna ta wani hanya kuma tunda sun fahinci an gane su.
Laraba ce ta shigo tana fadin abin mamaki yau naga bakuwa a gidan nan cikin buzayen da suka zo tana sallah har sallah walha take yi.
Jiya ma tunda tai magariba take zaune tana karatun kur,ani wurin har aka kira sallah isha,i tanayi mommy ne ta bata amsa da fadin ke ance maki duka suka taru suka zama daya akwai na Allah a cikin su ai sosai ma yanzu wayewan kai na addini ina ne bai ratsaba.
Kukan da babyn mace tayi ne yasa hankalin su ya koma kanta mommy ke fadin yaran nan yunwa suke ji ya kamata su fara kama nono haka na Amina kara gyara nonon nan a basu su sha .
Fuska na tabe shigowan maryam dakin na mayar da hankalina gare ta gaisawa tayi dasu mommy ta mike ta nufo ni da yarinyar.
Falo suka koma naji dadin hakan nan suka barni da ya Amina da maryam ina koya min yadda zan rika yaran.
Haka dai na daure yarinyar tana kamawa tana sakewa sai barci ta koma kuma na samu saida.
Ya Amina ne tacewa maryam kin makara maryam baki samu rikicin buzuwan ku da Altine ba kan daukan yaran nan da sauri maryam tace sun dauke su ne ?
Tace ai Altine ta hana su yau munga hauka badon Altine ba kan da mukan ai bamu iya tijaran su don yadda suka hakikance sai sun dauki yaran.
Nan dai ta bata labarin abinda ya faru tace mun dai gode Altinen na nan nace yar mijin ki ne fa sai ta harare ni kallon mu ya Amina tayi tace ta ina tazama yar mijin ta kuma ?
Maryam tace tambaye ta dai yaya nace ta sojan gidan su mommy da sauri tace Suraj nace shifa in Allah ya yarda tace ko shine naji ana rikici da uwar ya samu mata Abuja tace bata yarda ba yar yar uwanta zata hada shi da ita.
Wata sabuwa ke nan dama nasan sai an kwasa da Umma don da ganin ta irin matan nan ne dake mulkin diyan su sosai.
Muna cikin maganan mommy ta shigo dakin sai mukai shiru tace in fita kuna siri ne ya Amina tace a, a mommy ashe maryam din khadija ne Suraj ke so nan Abuja.
Da sauri mommy tace wace maryam nace wanan maryam dai tawa mommy ta sake fara a tana fadin dako yayi dacen mata wallahi dama shi irin ku yake so ai wayyyayu mata kamar shi.
Duk wace uwar ta kawo yace batai mai ba ita kuma taki bari ya kawo wace yake so idan mijin kine ubangiji Allah ya ingata tsakanin ku.
Suraj yana da kirki wallahi bai biyo halin sauran yaran dakin ba da nuna banbanci uwar ce dai matsala yanzu yana nan kan ya dage.
Ko zuwan nan dayayi last naga sun zauna wurin Alhaji nasan ko zancen ne ya Amina tace ita bata ganin yadda ya girma baiyi aure ba mommy tace wa yaya Allah dai ya kyauta.
Shine ai take ganin laifin hajiya mama wai ita ke sakewa diyan ta itakan ai bata da wasa ga yaro ko auren yayi ko yana under control din ta ne.
Suraj din daine ma bai faye bin dokan ta ba sani lokaci nace Allah dai ya shawo muna kan ta da abin baiyi dadi bako gaskiya.
Shiru maryam tayi na fahinci ta dan shiga damuwa mommy tace idan kina son abinki yana son ki in Allah yayi ai dole ta hakkura saukin abin daya ne idan taji ace ke din yar masu hali ne zata iya yarda daga baya.
Fita tayi tana rufo kofa muka kwashe da dariya nace mun zama yan kurkuku ke nan kofan ma sai an rufe mu a ciki ya Amina tace dole ni yanzu ma yadda in an watse zaku kwashe da ita nake ji ai.
Nace idan mommy bazasu zauna ba wallahi saidai in koma gida ban iya masifan wanan matar gaskiya yanzun dai sai yadda shawara ya tsaya ai don ban tsamani baban maigidan zai yarda ta zauna har arbain ba saboda gudun yadda akayi wancan karon.
AA ne ya budo dakin ya shigo gaisawa sukayi da ya Amina sai maryam data gaida shi ya amsa ya Amina ta mike zata fita yace zauna fita zanyi ai maryam kira min mommy falo.
Maryam ta mike zuwa kiran mommy din daga can bata dawo dakin ba momy ta shigo tana fadin kai Altine akwai tsiya wallahi.
Yana duke yana duba yaran yana kare masu kallo yace nurse din nan ne data karbi haihuwan yaran ta bugo min wai za a kaisu su amshi riga kafi yanzu can asibitin su.
Dama ashe kiranta wai yar maryam tayi makwabtane tayi kokari sosai wallahi matar kuma na tambaye ta mai za a bata tace wai ai gida ne tunda yar maryam ta turo ta sai ku fadi abinda za a bata mommy.
And kuma mommy ya akayi ina office yanzu nafisa ta kirani tana kuka wai tazo ganin yaran an hanata daukan su ita da kawayen ta.
Kafin mommy tayi magana sai ga Altine kamar an turo ta dakin momy nacewa ba hanata daukan su ai mukayi ba kasan ai haka ba zai yuyu ba babangida.
Altine ta cabe da fadin haka tace ma an hanata dauka idan bata da wani manufa may ye don ance suna barci a barsu sai bayan suna zata matsa sai sun dauke su.
Yace ke mahaukaciya da uwata nake magana tace ni kuma yarana nake karewa ba wallahi tsohon su yanzun an daina hakana irin hakane sai abu ya zo ya samu yaro a haife shi lafiya sai daga baya a rasa gane kan yaro .
Amma idan anyi suna yaro yasha addua duk wanda zai dauka ya dauka ana ta fadakarwa akan hakan yanzun duniya ya lalace wallahi ba a gane mugu a fuska barci suke akace su barsu don jiya basu bari anyi barci ba da dadi dan namijin yanata kuka da dare.
Yanzun dai na fahinci kece mai rashin mutuncin wa mata na ke nan ke kika sakata kuka ko wai harda kuka tayi don an ce su bari su tashi kila tana da wani manufa kenan akan su.
Taga yara bulbul gwanin ban sha,awa ta kwaso wani gaiyan buzayen ta suzo lashe min diya kai ya girgiza yace ke mahaukaciya ce tace naji dai ita wake daukan nata idan ta haifa ai ta sani sherin matane kawai irin namu.
Muko nan mun san komai wallahi sai anyi suna zamu bari kowa ya dauke su yace ke kada ki aibanta min mata fa an fada maki matana muguwa ce .
Bansan lokacin da na saka masu baki ga zancen su ba nace may ye na naci idan bata san sherin data kulla ba tun jiya ai na haihu bata shigo sai yau zata kwaso munafukan ta su zo min.
Wurina ya juya yana nuna ni yace mommy ki ji a gaban ku take fada kan yaranta ya juya zai fita yana fadin Altine ji mana ta bishi baya suka fita daga dakin.
Momy tace aini na gode da zuwan Altine dako Alhaji bai so a zo da ita ba sai da akace babangidan ne yace tazo ya yarda tazo.
Irin su ne daidai dasu ai momy don ta nuna masu ita ma ta iya ya fita sun dade sai ga Altine ta dawo dakin tana fadin ikon Allah.
Ina kawar buzuwa da suka shigo dazun bakar matar nan mai zubin yan duniya yanzun suna fitowa wallahi muna tsaye da tsohon su kawai mu kaga ta yanke jiki ta fadi.
Adaga ta wai tayi kariya a kafan ta daga faduwa fa a gaban gidan nan su momy suka mike suna fadin subbahanallahi yanzu tace gata can za a kwashe ta ai duk sun tada hankalin su a waje.
Gurin nace aniya mako miya wallahi kinga mugun abinda suka riko ne ya koma masu nan suka barmu zaune suka fita sai ya Amina ne bata fita ba dakin ta zauna dani a dakin da yara.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: Yadda naga maryam tana ta faman shirya ma sunan yasani tambayar ta wai har suwa zasu zo ne take wanan shirin haka ne ?
Tace idan ke baki da mutane yaran da mutanen su suka zo duniya don haka ki barni in shiryawa bakin su ke baki san abinda kika haifa ba ina gani.
Ga mijin ki shi sai faman shiri yake keko kin zauna sai kumshe kai a cikin daki gobe dai ki shirya mai sallon na tafe gidan nan suyi maki gyaran kai.
Murmushi nayi mata nace to maman biyu Allah ya kaimu goben lafiya saura kwana biyu suna babu zama don abubuwa sun yiwa kowa yawa don an gyara ko ina na gidan.
Yusuf ne ke gabatar da komai shikan AA nasa bayar da kudine kawai washegari yan kaduna suna isowa basu dade da zuwa ba mutanen minna suka iso mota daya doguwar motar maikatan lafiya nasu mama tani aka basu.
Duk gidan ya cika da jama,a hotel AA ya kama ma bakin namu mai kyau da tsada sai yabawa suke yi yara sunyi goshi inji momy tunda har hajiya umma tazo Abuja suna hajiya mama kawai aka bari a gida.
Naji mamakin rashin zuwan Anty Fati da batayi ba sai dai sakon da ta bayar a kawo min yaran dai sun zo da wasu yan uwanta mata biyu nasan su don suna zuwa gidan idan naje kaduna.
Duk wani abinda za a gabatar sune masu gabatar dshi su Fauziya basu samu zuwa ba don suna tsamanin kira binta da zainab dai sun zo sun hade da maryam da wasu kawayen mu biyu da muke zaman mutunci a hostel.
Baiyi shawaran komai dani ba da iyayyen shi da yan uwanshi yake shawaran shi nima kuma hakan bai damay ni ba.
Ban baku labarin sunan yar gurin Nafisa da sukai shagali ba bayan dawowan mu inda mata yan duniya suka barje gumin su ranan akai ta muna iya shege agida dasu haibaici da gori.
Sai ga Nafisa yanzu fitowa waje yana son ya gagareta don nuna tan da akeyi tana gani ana cin arzikin mijinta babu dama tai magana.
Muna nan da daren nan muka samu labarin hajjata mata an hanasu tafiya don a shekaran akai doka saudiya sai mace taje da muharamin ta zata shiga saudiya.
Wanan abu ya tayar muna da hankali sosai don muna ganin bazasu samu dagawa ba zuwa makka sai da yusuf ya shigo yana muna bayanin wai AA ya biyawa Ahmed shine zai tafi tare dasu da yar wurin umma daya su hudu ke nan.
Washe gari aka tashi da hidimar buki a gidan inda ake ta shigowa da kulolin abinci gida yana waje sai ganin Nafisa yayi ta fito da yaran ta da yan uwanta wai zasu bar gidan har taro ya watse yace babu inda zata tafi mai da yara inda zata tafi ita daya bai hanata ba.
Dole ta juya ciki dasu bata dade ba ta fito ita kadai ta fita ta barsu da yan uwan ta su Fatiya a gidan.
Sai abin arziki nake samu daga matan da ban sani ba wai matan abokan shi da yan gurin aikin su ne ke zuwa muna murna.
AA ya yanka ma yara raguna biyu na suna sai shanayen da aka yanka don aukin nama Umma da momy ne suka zo kiran su mama Tani su fito falo ga kayan suna za a gabatar masu.
Duk wanda yazo ina bashi kulawa da tallaka da mai arziki don abu daya ne ya tara su a gurin don haka nake ba kowa kulawan daya dace don kada wani yace na fifita wani.
Ihun dana a falo ne yass mu yin shiru ashe cikin kayan sunan ya saka min makulin motana sabuwa dal baka kal da ita wata jeep dirkekiya na mata new desgn.
Maryam ta shigo dakin da murnan ta tana rawa tace kin kai ga mota khady AA ya bada ki kyautar mota albarkacin su yan biyu.
Baki na tabe nace in dai don su zai ban mota ya bari ban so suka shiga min shakiyanci a gurin amma kasan raina nace may wanan mutumin ke nufi danine dama daya kasa saya min mota kullun yana min wake.
Nafisa ne suka shigo da kawayen ta gidan kallo ya koma wurin su don shigar su sun nuna hali da gadara sosai a jikin su.
Sai zuwa rana Anty hauwa ta danno da tawaganta sai motoci ake fakawa a gidan bata dade da zuwa ba hajiya laila SJJ ta iso itama wuri ya dauki manyan mata don su shidda ne ita ma .
Kyautar da suka kawo ne ya girgiza kowa a gurin motace Parado fara na mata mai kyau dashi sai da jikina ya mutu na kasa magana a gurin.
Tace yayan ku ne yace a kawo maki ita albarkamcin su yan biyu ki karba don Allah don yasan halin ki su momy da Umma aka kira don karban wanan kyautar sai manya.
Anty hauwa ta karba tace ai godiya wurin maigida su yan biyu sun gode nikan na rasa may zance don nasan akwai rigima gurin AA idan yaji.
Walima aka shirya zuwz hudu aka hallara babban falon gidan Nafisa suna ciki ana cacakan AA dani da yaran sai mugun baki suke muna.
Labarin kyautar wata motar ya kai gare su ranan da kyat su Badosa suka shawo kan nafisa ta haukace wai an nuna mata banbamci annuna mata ita ba yar kasa bace.
Da kyat aka samu ta fito wirin walima suka zauna sai wani sallo suke suna ganin su anty hauwa da mutanen ta sai kuma ga matar Sjj sun fito sunga karyan naira inda take aiki a gurin.
Sai suka koma kuskus ina na samu mutane ne haka irin kudin da ake ba malamar da gudun mawan da tace ana nema marayu wurin ya firgita Nafisa ta fara mikewa zuwa dakin sauran ma suka bita.
Malam ta gama sai Fatiya tace a dan bata lokaci akwai kiran da zatayi mata yan mintuna kadan don Allah.
Tunda ta karbi abin magana ta fara wurin yayi tsit inda tai nasiha kan hakkin yaya zuwa iyayyen su kafin su girma da inda illoli ke fitowa daga iyayye mata wurin tarbiyan yara yanzu.
Kowa ya yaba da hankalinta sosai kudin data samu tace a hada a bawa malaman batayi don karban komai ba sai ta rufe akan jin tsoron Allah a zukata saboda mata sun shagala da yawa.
Coure mate dina sunyi kokari sosai don ku san musulmai da Christian duk sun halarta harda wa yanda ba course din mu daya dasu ba sunzo.
Anci an sha araba jakkuna dake dauke da kayan buki a ciki mai hoton yaran su biyu taro dai ya watse lafiya ana sam barka.
Can kuwa kawai Nafisa ne ke kara zugata har yaushe na shigo gidan da zan bunkasa haka a cikin dan kankanin lokaci kai mutane akwai munafunci dasu.
Don neman fada ne a gurin mijin ki yasa suka tara mata wanan abin arzikin haka mai yawa wata tace ni ba shiba kun ko ga sarkan wuyan ta a wirin waliman nan zai tasan ma milayan kusan biyu ko uku fa.
Kai kai ina wanan yar talakawan ta gama min yakar kauna a gidan nan yaushe nasa sarka makamancin haka a wuyana wata tace kece baki so lokaci daya sai ya mallaka maki wanda ma yafi wanan kudi.
Banda abinda zancewa Anty hauwa da maryam sai godiya don itace ta hada kan sarkunan ta canzo min wanan a Dubai a matsayin kaddara ana gama taro ta rada min a kunne in adana sarkan nan don ya tsone ma kowa ido a gurin sosai.
Yara sunci suna don na Mijin an saka mai muhammadu Aminu-lah kanin Abban su daya rasu, sai mace da aka radawa sunan hajiyan su Aisha humaira tun haihuwan Ihisan yaso sawa tace bata yarda ba don ba wani ya haifa mata diyar ba.
Ko zuwa dare ban samu kaina ba duk da ciwon da kaina ke min don bakin kaduna dana Minna dake gidan zakace ba a watse ba.
Yana shigowa get din gidan idon shi akan motar da aka kawo min kyauta ya yaba da motar sai dai ya dauka mai shi na cikin gidan ne tazo buki.
Yana shiga Nafisa dake dakon shigowan shi tana mara mai baya kusan a tare suka shiga dakin lokacin.
Ganin yanayin ta yasan tana da magana a bakin ta don haka ya sashi daure fuska jin muryan ta yayi tana fadin macuci azzalumi ya juyo da zauri
yana kallon ta tare da fadin may nayi maki kuma daga shigowa na yanzu.
Tace azzalumi zakace baka san cutar da kaimin ba wai kai zaka nuna ma duniya niba kowa bace yace to wa kike nafisa shugaban kasa kike ko matar shugaban kasan ?
Tace ban ko daya yace to ki tsaya a matsayin ki na matar Abdulsamad yafi maki cutan da kike cewa nayi sai ki fada min inda na cuce ki kuma ?
Tace wani cuta ne bakai min ba kuma na taba haihuwa ka sai min sarkan gwal ko na taba haihuwane ka bani mota a matsayin kyautar haihuwa.
Kai ya girgiza yace lalai Nafisa ke butuluce ta karshe sarka wani irin ne ban sawo maki ba duk naje turai shine tsaraban ki kina amfani dashi a gidan nan ne idan na saya maki ban ganin shi.
Mota kuma shigowan ki gidan nan mota uku na saya maki kina kadarwa wanan ma yanzu da kike shiga nawa ne kika dauka a matsayin dannan kirjin ki bayan kudi da kika saka in baki na fati ko ita khadijan ?
Tun suna fada su biyu a dakin har yakai sun fito falo a bainan jamma,a suna yi umma ta fito tare da gwagwanin shi suka kada kan shi ya fice ya barta.
Yace umma wanan matar kashe ni take son yi haihuwan nan da tana da halin murde yaran nan da uwar su da tuni ta murde su sun mutu kowa ya huta.
Akan ki ne kishiya ta fara haihu a zauna lafiya may wanan matar take nufi da nine kamar itace ta haife ni ko ta ajeni a gidan nan haka ?
Fitan su bai sa ta yi shiru sai tonawa kanta asiri da miji take a gurin yan uwan shi kowa na tirda halin ta.
Ban samu kebewa dashi ba sai washe gari don fada mai zancen motar tunda nayi wanka na shirya cikin wasu atamfan exclusive na sillace jiki zuwa wurin shi.
Yana kwance har lokacin sai dai ba barci yake yiba kuma yana kwance rai rai kamar wanda ke tunane a lokacin sallama nane yasa shi dan dagowa gare ni.
Tun ban kai zaune ba nace yaya lafiya ko ina zama a kusa dashi ya dan gyara min na zauna da kyau yace matsalan kune da baya kare wa nake tunane.
Nace mun kuma da mamaki ina kallon shi kafin in kara fadin, wani abin mukai maka kuma yace zaku fasa ne gaba dayan ku na rasa gane inda kuka dosa da rayuwana.
Allah ya kyauta nace don ban san may mukai mashi ba yai wanan jam,in haka gare mu nace godiya nazo in wa su yan biyu akan kokarin da akai muna mun gode Allah ya kara rufa asiri yasa a fi nan karfi.
Kamar ba zai karba min ba sai can yace amin ke kin iya godiya idan an maki alheri nace kowa ma ai ya iya tunda bamune muke nema ma arzikin naka ba sai yadan yi murmushin yake.
Yace ina yaran suke nace ana masu wanka sai dai naji umma na fadin kamar yau zasu koma fa yace yau din nan nace haka naji ta fadi jiya dai don wai Abba yace kada su wuce yau idan sun zo.
Komawan su ba zaiyi yau ba sai dai gobe har yan Minna din nace harsu yace eh haka nake so idan sin dan huta sai kowa ya kama hanya kisa Altine ta kirga min ko su nawa ne daga minna haka ma yan kaduna.
Nace nabarka lafiya har na daga na dawo nace ai na manta kaga bakuwar mota a waje gidan nan ko ?
Yace eh to akwai dai motoci a gurin gaskiya nace wata parado fara yace ok da wani flawer kamar gift ko nace eh ita yace naganta tun jiya a packer gurin.
Nac to ita ma wasu yan biyu aka kawo wa kyautan ta mikewa yayi da sauri yace wa ya kawo masu kyautar mota haka nace wanan dai matar mutumin nan dan uwan yaya Adam dakaiwa alheri sune suka zo dashi.
Nan dai na fada mai yadda akayi tun kawo kudin su da bankarba da kuma zuwan su jiya da mota da har anty hauwa ta karba.
Abinda nayi tsamani ne ya faru don lokaci daya idon shi ya canza min ya hauni da fada khadija jin ya ambaci sunana na asali yasa na fahinci maganan takai magana gurin shi.
Ban fada maki rayuwana ba haka yake ba cin hanci ke nan suka kawo maki komay yau idan badon nasan halin ki nasan ko ke waye ba da ba abinda zai hana in saba maki a gidan nan.
Nace yaya kada kaga laifina a hakan nayi duk iya kokari na in kaucewa hakan don gudun bacin ranka sai suka biyo min ta wanan tsigar kuma.
Banda yadda zanyi a cikin mutane ga maganan da ta fadi wai kanwa nake gare shi do haka su yan biyu yabawa mota bani ba yace ni zai gwada wa mota komay ?
Ko gidana bai gannin da motoci bane da zai dauko wanan motar ya kawo maki motar nawa na saya maki da kikaji nafisa na fada akan shi jiya.
Ke bari kiji idan kin shigo rayuwanane ki lalata min suna wallahi baki isa ba duk fadan da yake yi kaina na kasa ban san lokacin da hawaye yazo min ba cikin wani irin murya mai sanyi nace.
Ni yaya Abdulsamad nice na shigo rayuwan ka don in bata ma suna ni khadija Adamu danladi dini sai na mike hannun na naji ya riko min ta baya.
Na koma na zauna a inda nake yace ki fahince ni Deedar wanan ba rayuwana bane cin hanci da rashawa da ina wanan halin da yanzu nafi haka a garin nan.
Cikin kuka nace na sani yaya amma ni may ye laifina a ciki yanzu tunda ba rokon sa nayi ba sun nuna min wanda ya rigaka kwana ya rigaka tashi ne da ban karbi kudin su ba sai suka biyo min ta nan kuma.
Amma idan kaga laifina a cikin wanan maganan har kake ganin za a hada kai dani a cuce ka kayi hakkuri zan kirasu suzo su dauki abinsu tunda ni ban san gidan su ba ma.
Ki barni dashi zan kirashi inji dalilin yin haka a gareni don banga dalilin saka mata na ga maganar business din mu dashi ba.
Shiru nayi hawaye yana zuba min sai can danaji ya tsagaita fadan na mike na fice a dakin ina share hawayen fuskana da bayan hannu na.
Bayana yabi da kallo har na fice daga dakin ya sauke a jiyan zuciya tare da jan guntun tsuki ya mike a inda yake yaka ya shiga yanayi yana tunane abinda ya faru tsakan mu yanzu har na bar dakin.
Sai yaga rashin kyauta min da kalamin shi don a gaskiya bai ga laifina a cikin zancen ba don ko gidan su ma bawai na sani bane kamar yadda nace mai.
Ina shiga daki na samu a nata hada hadan wanka da shirya abin karyawa wa baki na samu ya Amina tayi wa su Affan wanka tana shirya su na shigo tace ga diyan ki nan wai ba zasu tafi ba yau suka ce.
Nace ina ganin ba yau bane tafiyan su duka ai ganin yanayi na yasa ta fadin wani abin ne ya faru kuma ?
Ina kuka nake fada mata abinda ya faru tace ikon Allah wanan mijin naku halin shi sai shi may ye a cikin haka ba karuwa ya samu aka kawo gudun mawa ba.
Ina share hawaye gajiye ta fado dakin itama tsayawa tayi tana tamnaya ya Amina tace uhmmm ita da mijin su ne akan motar da aka bata jiya ne suke jidali nan dai ta fada mata komai.
Tace shikan wanan shiya kwaso mai sunan nashi da komai wallahi to ba za a mayar ba wa ya taba wanan halin don Allah dai shifa wani irin bahagon mutum ne shiyasa yai daidai da kalar matan shi ai.
Fita tayi kafin wani lokaci sai fa momy ta shigo dakin tana fadin yanzu nake jin wani magana gurin Altine ya Amina ne ta fada mata komai.
Tace haba babangida yaushe kuma aka taba yin haka in bakai mai godiya ba ai sai ka kyalesu da wace aka ba din ko ?
Tace umma tace zatayi mashi magana ai idan ya shigo nace Allah yasa ma bai buga mai ba kamar yadda yace zai kirashi din.
Altine na kalla nace yace wai ki kirga mai mutanen da suka zo daga kaduna da minna ko mutum nawa ne suma yasan mutum nawa suka zo tace dan gidan momy ke nan ga dadi ga wuyan sha,ani.
Sai zuwa goma da wani abu ya sauko kasa koshi tare da Yusuf suka shigo part din su gaida mutane a can dakin dasu umma suke ne bayan ya gaida su tace babangida sai muke jin wani zance kuma mara dadi.
Idan baku samu karuwa ba kun ga wani ya kawo abin arzikin shi gidan nan a baya arzikin diyan ka ne ya jawo maku alheri don may zakace a mayar da kyautan motan da aka baku.
In ma kana ganin da wata manufa ya baka ai samun hanyar da zaka mayar mai dashi kaima zakayi ba wai a dauka kai tsaye ace amayar haka ba.
Kallon shi Yusuf yayi yana son karin bayani yace Umma ba wai hakana bane sun biyo ta wanan hanyar ne don suga sun bata min tsarina tace idan da haka ne ai ba zasu hada da matanka harda diya ba ko ?
Kayi hakkuri abinda ya wuce abarshi akan ya wuce sai a faki gaba kuma yace to shike nan umma ya wuce ai tunda kinyi magana.
Tace ta gode nan yace naji ance yau zaku koma wai munyi waya da Abba nace dashi gobe zan sallamo ku kudawo gida tace to shike nan Allah ya kaimu goben lafiya yau da gobe duk daya ne a gurin Allah ai.
Ya barin wurin su dakina ya shiga inda nake zaune da yan uwa suka gaisa dasu ya fada masu yana son su bar tafiyan su har gobe mama Tani tace bai zama dawainiya ba tunda angama abinda ya kawo mu.
Sai dai kuma dama muna son magana akan ita khadijan wai muna rokon ko za a bamu ita mu tafi da ita taje gida tasha ruwan zafi sai su dawo.
Dan murmushi yayi tare da fadin mama kuyi hakkuri a barta a dakin ta don mu gidan mu ba a hakana sai dai idan wata zata zo ta zauna da ita nan ne babu damuwa.
Mama Tani tace to shike nan zamuyi shawara mu gani abinda shawara ya yanke zakaji yace karatun ta ma sati biyu kawai suka bata leave.
Yana fita na turo baki nace ni gida zan koma gaskiya ban iya zama ni kadai anan inyi jego da yaran har biyu haka a gabana.
Yafi mu gaskiya mama Tani tace don kinga idan kinje gida yaya zakiyi da karatun ki kuma yace komawa gida ba aladan gidan su bane dole dai kiyi hakkuri sai a turo maki wace zata kula dake nan.
Ban so haka ba don ni na sama raina zuwa gida inyi wanka a can ban taba tunanen zai kawo min cikas ga zuwa gidan da na kwalfawa rai ba.
Wunin ranan dai haka nayi shi ba dadin rai sun shiga gari har yan kadunan yan tsiraru aka barmu dasu a gida da yamma ya dawo ya kirani falo na fita na samay shi zaune.
Yace wanan sallaman yan minna ne wanan kuma na yan kaduna ko akwai sauran wani abinda za a basu ne nace babu an gode.
Ina shirin mikewa yace min ya na ganki haka wani abin yana damun ki ne shiru nayi sai da ya kara maimaita maganar shi nace gida nake son zuwa in sha ruwan zafi.
Nan da kike ruwan sanyi kike sha kafin in magana sai fa Nafisa a gaban mu tace samad kasan yarinyar nan bata da girki tunda ta haihu ko ?
Yace wani abin kika ga munayi da ita anan tace ban yarda kana ke bewa da ita ba haka don hakkina ne yanzu.
Nace au hakane to tunda abin haka gobe zan karbi girki na a gidan nan ko ba za a ban ba inji tace wallahi baki isa ba don sai kinyi arbain.
Nace tunda ke ke iko dani sai mu gani idan ban insa ba din ko kin manta ke ma haka kikayi baki arbain din ba kika karbi girki ki ko kinfi wani ne a gidan nan.
Don haka nima zan karba kamar yadda kika karba kina nufin dani zaki takara a gidan nan nace da abin kwarai kikeyi da nayi koyi dashi sosai kuwa amma girki a gidan nan gobe kamar nayi shi na gama ne.
Ina fadin haka na dauki kudin tare da kiran laraba ta shigo min da kayan na barsu a gurin suna fafatawa da ita na shige ciki ban san yadda suka karata ba.
Nasha alwashin dama sai na rama hakan a raina idan ita tayi a kuraren lokaci wancan karon ni da wuri zan mata nawa iya shegen nima tunda da gangan take yin tsiyar ta don ta nuna tafi wani iya iskanci.
Momy na kira na danka ma kayan su na yan kaduna mutanen minna kuma na ba mama Tani nasu a hannun ta.
Washe gari baki sun watse sai su momy da Altine sai ya Amina muka saura a part din maryam ne ta shigo zuwa yamma muka shige daki muna hira damu uku.
Anan nake fada masu yadda mukayi da Nafisa da jiya maryam tace kwarai kuwa gwama da kika ce hakan ko ba zaki dakin shi ba nuna mata kowa ya iya iya shegen ai.
Girki nasa Altine su shirya dashi zuwa biyar ya shigo gidan ya dan jima zaune a falo gurin su kafin ya shigo wurina ciki.
Ganin shi maryam ta fita ya samu wuri ya zauna yace ya batun girkin naki yau nace yana nan kamar yadda nace yace cikin marairaicewa bazaki bari yaran nan su kara kwari ba.
Nace cewa nayi zasu hanani yin girki din dama haka zanyi tunda tace bata san nasiha ba muje zuwa ga haka.
Ya ga dai da gaske nake magana ba wasa a cikin harkan don ashe ita ce ta tayar mashi da hankali ya mike jiki ba karfi ya fice dakin.
Can ta samay shi ranan dai sunyi bala,i sosai yace ai ita ta fara tunda nace zan rama sai ta kyale ni da ta kyaleni bata fito da cin mutunci ba yasan da ban karbi girki a yanzu ba.
Dare yayi da kaina nakai mai abincin shi na zauna sai da ya gama na kwashe kayan yace ina yaran suna daki na bashi amsa fuska a daure murmushi kawai yayi yace a can zasu kwana ne ?
Nace tare da wa nima ai ba anan din zan kwana rashin mutunci tai min nima na rama in nuna mata ba tsoron ta ake ji ba nasan da gangan ta take iskancin ta.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
1/2/21, 7:38 AM - Xxxxx: An buga ma yan uwa da abokan arziki zancen haihuwana na kusa da na nesa sai kiran waya nake faman karbawa na mutane.
Sallama akayi a kofan falon za a shigo duk muka maryam da hankalin mu wurin mai shigowa da sallama da murya a natsune haka.
Wata bakuwar fuskane daga cikin buzayen mai sallaman tana gaba rike da hannun Ihisah sai wata daya dake bayan ta sai daga bana ya fadi don ganin kamar su da Nafisa da yaiwa take na daure fuskana don ganin su.
Bani kadai naga wanan kamar ba duk wanda ke falon ya san Nafisa yaga kamarsu da wanan buzuwan wani sallaman ta kara muna a karo na biyu muka sake karba masu.
Ihisan ce ta shiko gurina ganina rugumay da baby a hannuna tana fadin anty baby babyan mu ne nace eh Ihisan banganki ba tun da kuka dawo sai yau.
Wuri momy ta basu suka zauna mai kama da Nafisan bata zauna ba saida tayi bissimillah a tsigar kamala takai zaune.
Tare da fara gaida mutane da ta samu a gurin tace dani kece maijegon nace eh tace tubarkallah masha Allah Allah ya raya muna su akan tafarkin addinin musulinci.
Allah ya tsare mina suna daga duk wani aikin shedan daga mutun ko aljan da duk wani abinki masheranci muna fadin Amin.
Tace munzo mun samay ku lafiya don muna zuwa washe gari sai mukaji haihuwa nace bari mu barki ki huta sai mu shigo mugaida ke.
Nace na gode dan shiru ne ya biyo falon sai ihisan dake zuba surutu wai a bata baby ta dauka nace ina Samira sai matar tace tana kwance gajiyan hanya ya saukar mata da zazzabi jiya.
Allah sarki gaskiya dai banganta ba tace eh ai tana yawan ban labarin ki sosai tace kina basu abinci mai dadi kina dai kyautata masu sosai.
Yarinyar dake hannun maryam ne ta danyi kuka kamar irin mafalkin nan da yara kanyi tace idan sunyi haka ku karanta masu kalman sha hada a kunnen su kunnen hagu kuma ai masu auzu billahi mina shetanin rajjim.
Ki dinga shafa masu man zaitun sai da dare idan zaku kwanta ki shafa masu man habba da safe ma hakane don kariya daga duk wani abin sherin daga gare su.
Nagode nace tace ba damuwa Allah ya raya ya inganta cikin hausan su na ayan Niger take magana mai kama da kananci ko sakwatanci.
Mikewa tayi tana fadin mun gaishe ku dama nace bari mu shigo mu gaisa muyi barka kuma to na gode sai dai ban sanki ba gaskiya.
Tace tana dariya wanan ne karona na farko da nazo Nigeria a Niger nake aure mijina ya rasu shekara biyu ke nan yanzi na dan zo ganin ku ne in koma kwana biyu.
Nace munko gode wallahi tace ba komai nace baki dauki yaran ba don naji nauyin matar sosai ganin kamalanta ya cika min ido tace a, a barsu har gaba ai muna nan daku kwana biyu.
Dayan matar tace wa Ihisan tazo suje tace ki barta mana tana wurin uwarta ne ai sai dayan tayi yare sai ita ta juya da hausa tana fadin.
Za a rabata da yan uwanta ne wanan ai duk shirmay ne don sune dai nata din kinga don Allah mu tafi maryam tace baki dai fada muna sunan ki ba har yanzu.
Tace hakane sunana Fatiha wanan kuma Zakiya ita ubane muka hada da ita amma uwarta ta rasu ita ta kare karatun ta ne batayi aure ba niko nayi aure har ina da yara biyu sai dai basu tare dani suna gurin mahaifiyar uban su can Cameron don acan nayi aure.
Da fatan zamuji dadin kasancewa daku na dan lokaci a gidan nan nace insha Allahu mun gode kwarai tace sai mun kara shigowa ke nan.
Suka fice tare da rufo muna kofan a yadda yake kowa gulma ya cishi a falon marym ta fara magana tana fadin ikon Allah ashe akwai na Allah haka a cikin su ?
Momy tace haba maryam akwaisu ma sosai kuwa ai irin masu shigowan nan jahilan su ne da talauci yaiwa katutu suke shigowa nan.
Ko a cikin sun kuma akwai na kwarai sosai laraba tace itace mai ibandan nan dana fada maku ko yaushe ka wuce su suna sallah ko karatun kur,ani a falo suke zama abinsu har dare.
Ikon Allah gashi kuma abu daya suke da Nafisa ita ta fito daban inji ya Amina sai momy tace haka abin yake ai wani lokaci.
Mun kai wani lokaci muna hira a kansu kafin in mike zuwa cikin dakin in kewaya koda na fito ban koma falon ba wurin su na zauna a daki.
Ya Amina ne ta shigo dakin tana fadin in hada maki tea ki shane ko kunun zaki sha nace bani kunun don yai min dadi sosai.
Tace Adam ya bugo waya kin kewaya nace sai yanzun zai kirani ai nayi fushi wallahi tace ke ko ai ya kirani jiya da muka iso mana.
Muna zancen shi ne wanan matar SJJ ta fado min a rai nayi salati nace kinga na manta da matar mutumin nan tazo nan kafin in haihu kwanaki har taban layin ta tace idan na haihu in sheda mata kinga na manta ban fada mata ba ko.
Tace tazo gidan nan fa nace wallahi tazo har da kudi maigidan ya bayar a bani sai dai ban karbi kudin su ba nace don yaya Adam ne nayi masu hanya.
Tace amma dai Khadija nan don may baki karba ba su wayan nan ai ko nawa ne baki ragesu ba wallahi bacin ribar ma da sukaci dake ai da kin karbi abin ki wallahi.
Nace haba dai ya Amina sai kace ba training din ki ba da su daddy don may zan karbi kudin su haba dai tace kirata don Allah ko don in santa ma don ban santa ba Allah yasa tana kasan ma indai itace bata faye zama nan ba sosai kullun tana waje.
Kunun da ta zuba min nasha sai na dauko wayana na danna kiranta watace ta dauki wayan mun gaisa nake fadin nice sister din matar Adam.
Tace ok wacce muka zo gidan ta da anty ko nace eh anty na kuss ki fada mata na haihu jiya tace masha Allahu anty ko tayi tafiya amma zan kira ta in fada mata insha Allahu.
Mukai sallama bayan tayi min barka muka kashe wayan Altine ta shigo dauke da kwanan abinci ta dire min a gabana sai da naji gaba ya fadi sauko ki ci kada huce nace anty ba yanzu ba yanzun nan nagama shan kunu kinga kofin nan.
Tana kokarin bude kulan ta zuba min abincin tuwon farar shikafa da miyan shuwaka sukayi naga tazuba da yawa na bata raina nace haba anty ina zankai wanan abincin haka.
AA ne ya shigo dakin fuskan dana bata yake kallo Altine na fadin duka zaki cinye shi fa yace bazataci abincin bane ko may naga ta bata fuska ?
Nace haba yaya ya zanyi in cinye wanan abincin data zuba min yace haka kuwa zaki cinyesa duka sai kun kula don bata cin abinci sai kayan kwadai.
Cikin marairaicewa da yanayin shagwaba nace ni dai wallahi ana takura min mafarin a saka mutum yin babban tunbi ke nan.
Yace tunbi kan ai tunda diya biyu suka fito a cikin ki sai kin yi shi in zakici abinci ki sauka ki ci Altine tace kaima baban jegon in dauko ma filet ne a zuba ma yace Altine kamar kin san tun safe ban karya ba wallahi.
Tace kana may haka har wanan lokacin tsohon su bakaci abinci ba ina momy taji dan ta bai karya ba wai har wanan lokacin.
Yace wallahi muna can wurin kai wanan matar asibiti ne ashe a cinya ta kare fa da kuma kafa abindai ba a magana wallahi.
Nace wai garin ya ta fadi ne tayi wanan kariyan haka yace abinne ikon Allah tace wai taga kamar abu ya gitta a gaban ta sai taga duhu bata san lokacin da ta fadi ba.
Altine tace mugun abin su ne ya koma masu balle tagwaye da kofi yace nima dai abinda nayi tunane yanzu ke nan wallahi don yanzun na dawo security ke ban wani abu wai a jikin ta ya fado lokacin da za a dauke ta.
Altine tace kaga abinda nake fada ma jifa muna tsaye dakai kasan kamar an kifa ta a kasa ne yadda ta fadi kofin yaran ne ta gani ba wani abu ba.
A nan zakaci tare da matar ka ko a hada ma naka akawo ma karkuma buzuwan matar ka tace an mata shishigi yace indan ma tace bani zatayi yaushe ma ta zauna gidan balle ta dafa.
Tana can suna zancen wanan matar na barsu can nayi masu abinda zan masu tunda a gidana ta fadi na barsu can.
Yusuf yana tafe yanzu ya dawo zai karaso sai muci daga falo momy ta shigo dauke da yaron yafi fitina sosai tace khadija sai fa kin karawa yaron nan nono yasha don tun dazun yaki shiru.
Na tabe fuska nace momy a bashi ruwa don Allah yace saboda may za a bashi ruwa ko nono sayarwa zakiyi ne ?
Karban yaron yayi daga hannun momy ya dora min a cinya na yana fadin gyara ki bashi ya sha kinji.
Raina bata sosai ya Amina daga inda take zaune tun shigowan shi dakin batai magana ba tace dole sai kin daure kafin su saba don ita kamun nan take jiwa zafi.
Dukawa yayi bai damu da suna dakin ba yana kokarin bude min riga nayi saurin budewa shi ya gyarawa yaron kai ya tallabo shi ya sa mai nonon a baki yadda zai iya kamawa.
Shi kuwa yaron ya cabe ya kama ja ban san lokacin da nace wayyo Allah na ba don zafi cikin tsigar lalashi yace min daure zafin zai bari na dan lokaci ne kawai yana rike da kan yaron ya duka yana kallon yadda yaron ke shan nonon.
Ya samu ya zuka sosai ina faman runtse idanuwa na don zafi da nake ji har cikin raina yana ganin yaron ya kama da kyau ya mike tare da fadin barin dan shiga ciki in fito idan Yusuf ya karaso.
Ya fice daga dakin momy tayi murmushi tace ikon Allah komai nason kwanciyan hankali wallahi ji babangida kamar bashi bane ke wanan abin.
Altine tace gaskiya tsohon ku ya sauya gaba daya wallahi gashi yanzu har za a sake dashi ayi hira da komai dashi ya sauke wanan jin kan nashi na da can.
Momy tace yarinyar nan ai ba karamin kokari tayi a cikin ruwan sanyi take ganar dashi hanya ba a garaje ba indai mace zata iya bin namiji a saukake sannu sannu zasu kai ga manufan da ake nema.
Ya Amina tace yanzu idan mace na samun itin kulawan nan ga namiji mai zai dame ka kuma da zancen wani kishi can indai za a baka hakkin ka.
Hakkuri ai bai bar komai ba yanzu datayi hakkuri gashi Allah ya bata wa yan nan yara haka masu kyau dasu da sha,awan dauka.
Samira ne ta shigo dakin da sallama sai da nayi mamaki nace Samira ashe baki da lafiya ne ta zube a gabana tace anty wai kin haihu nazo in ga baby ne.
Yaron dake hannu na take dan tabawa tana mai wasa ta dago tace ance biyu kika haifa anty nace eh ga dayar can hannun maryam ta juya tana kallon ta daga inda take durkushe ta juyo tana fadin so cute .
Anty yaran nan nada masifan kyau sun fi baby Ami kyau sosai nace itama tana da nata kyau din ciwo daine ya mayar da ita hakana ai.
Tace hummm that mumu girl sai kuma ta bata fuska tana fadin zanci abinci anty nace tuwo ne fa kin ga kalar shi ta dan ya mutsa fuska sai can tace zanci a ban .
Nace baku dafa abinci bane tace wai Ami ta wuce da key din kitchen kin sai ance that madam ta fadi and she break her leg .
Allah sarki nace mata tana mikewa daga durkushen da take tace anty kina tausayin ta ne ke ni ban son ta muguwa ce sosai ita da Ami yau naji suna magana kan twins din nan fa zasu kashe su ni kuma ban yarda a kashe yaran nan masu kyau haka dasu su kashe momo din Amin dai amma ba wanan ba.
Bani ba duk wanda ke dakin sai da hankalin shi ya daga nace cikin karfin hali ke Samira kada ki masu shiri tace wallahi anty naji ne sai Amin mu ta kore ni dakin.
Nace ikon to Allah ya tsare laraba na kira nace a ba su abinci har da sauran dake part fin
Tin samira bata fita dakin ba Altine tace suyi a hankali don sun fara ganin kohin tagwaye a kan su tun yanzu in sunce sheri suka iya sun kai karshe ai.
Yarinyar dai ta kalle ta ta fita dauke da abincin da laraba ta mika mata momy tace wanan zancen ba na kyalewa bane fa babangida zanwa magana ya binkici yarinyar yaji komai wanan karon.
Don gaskiya ba maganan kyalewa bane wanan don mutum mugu ne tunda tayi niyar masu cuta tasan duk hanyar da zata bi ta cuta masu din
Nace anya ko an fada mai zai yarda don kirikiri yasha kamata da makamancin case din nan ni banga yana daukan wani mataki ba akanta sai ma abinda ya karu don agaban shi sai tayi ikirarin halaka mutum bai kuma daukan matakin komai wallahi.
Altine tace ko ba zai dauka ba wanan kan dole a fada mai komai don ya sani ya bincika yarinyar yaji da kunnen shi mana.
Momy tace kai abin ne da daure kai wallahi ya Amina tace momy kun san fa ba banza ta barshi ba wallahi aikin banza nayin haka ina sai dai asiri kan inji maryam.
Tare da Yusuf suka shigo part din falo na fito na samay su Yusuf yana min barka tare da yaba kyaun yaran sosai Altine ce tace dama kai muke jiran shigowan ka tun dazun.
Yace shi tace eh sai momy ta karbe tace dazun muke jin abin mamaki a gurin yar nan diyar Nafisa babban sai Altine tace yar agolan gidan ka dai.
Kai ya girgiza yace ke baki barin sheri dai momy ta kwashe abinda mukaji a wurin samira din ta fada masu bude bakin shi yace kai shine abin damuwa momy ?
Nafisa bata da hankali wallahi zafin kishin ta ne kawai amma may zata iya yiwa yaran nan don tasan ba kyale ta zanyi ba itama.
Yusuf ne yace a, a AA wanan ba karamin magana bane ya zama dole wanan karon ka nuna mata an fasan abinda take yi kafa san halin Nafisa sosai wallahi don may zaka tsaya yin gardama kan abinda ka sani kuma.
Shiru yayi yana sauraren maganan kowa yanzun zan bikici yarinyar inji komai kafin in mata magana sai lokacin na sauke ajiyan zuciya jin zai dauki mataki akan zancen.
Abinci aka fita masu dashi yaci sai da ya sallami Yusuf yazo ya kira Samira cikin dabara ya fito mata da zancen ya shiga jin har abinda bai tsamani ba daga gurin yaran yana recoding a wayar shi.
Ta dawo yawon gantalin ta a falo ta zube karfe takwas da wani abu tun safe da ta fita abin ya faru da madam suna can wurin jinyar ta.
Ya sauko daga sama fuskan shi a daure yace ina kika fito a wanan lokacin tace amma dai kasan abinda ya faru da madam gidan ko ?
Na sani sherin ku ne da kuka dauko ya fara fada maku ai tace ban gane sherin mu ba yace Fatiha ina son ku saurara kuji ya kuna oudio daya dauka na hiran shi da yaran ta.
Ba Nafisa ba har yan uwanta da yanyala kanwar uwarta sai da suka kadu dajin komai tiryan tiryan yadda ya fara tambayan yaran yace kuga sabbin kannin ku ko yaran suka ce mun gani Abbi har biyu suna ta shirmay su yana dariya.
Yace ai za a sace maku sune Ihisan tace in kashe wanda zai sace su in yanka shi sai Samira tace ko Ami ban yarda ta kashe su yace takashe su kuma samira tace eh Abbi naji suna magana da Madam din nan ai ta kwashe komai ta fada mai.
Oudio na karewa ya dago kai yace may zakice kan wanan yar uwarta ta hawaye yazo ma tace amma ke kan halin ki ya fita daban a cikin mu.
Ban san may kika dauki duniyan nan ba wallahi shiyasa nace wurin bakar bidan asirin ki kika dauko yar nan dakika tsana.
Tace Fatiya kada ki fada min maganan banza don bake ke min zaman aure ba zan shigo kasar su ina bare su kyale ni ne ?
Don wanan hiran yara da ya dauka har zaki dauka gaskiya ne in shirya masu akayi suce haka kafin a dauka fa baki tunanen haka ke ?
AA ya kaleta yace nine zan shirya maki sheri ko may yace bari kiji wanan recoding din zai kashe ga hukuma ne yanzu don su sani ko ciwon kai daya daga cikin diya na yayi wallahi ke ce.
Lokacin da kuke kulin sherin ku idon ki ya rufe da bakin kishi kin manta da yaran suna kusa dake bakin san abinda kike fadi ba.
Su yarane suna nan suna koyi daduk abinda kike yi a gaban su don haka ba zan lamunci wanan ba ga diya na ita Samira yar kice komai zaki koya mata banki ba don yarkice nai maki kara kuma a kanta.
Fatiya tace yanzu dai wanan kadai ai ya isheki ishara don babu abin kunyan dayafi wanan idan mutanen nan suji wanan zancen fa.
Yace yaushe kuma shiyasa suka hana mata yara an mayar dake mujiya maciya abin tsoro don sherin ki ta harzuka tace suji mana suma ba sherin suke min ba.
Ko ban san abinda take aikatawa a gare ni bane har canza min diya a ciki da tayi na sani amma baka dauki mataki ba sai wanan zancen yaran zakazo ka tsure ni da zancen banza haka.
Yace an cen za maki ya kamar yaya cikin tsure ta da idanuwan shi yace kowa yaga yaran nan ansan ba nata bane wallahi diya nane ta sa aka sauya mata zuwa nata.
Kana dauka zan yarda da hakane ko may yace Nafisa anya baki da tabin hankali kuwa kin san ko abinda kike fada nan dai kanwar tayi mata kaca kaca tace gobe zata koma Niger ina zata da wanan abin kunyar haka ?
Azo ana nuna su a tare kishi haukane ko may kin samu gidan da zaki huta mu huta rashin hankali ya hana ki kwantar da hankalin ki.
Cikin murje ido taciwa yar uwar nata mutunci tace ta tafi mana an tsare ta ne nan dama bata isa ta nuna mata ga abinda za tayi ba.
Don ba ita ke mata zaman auren ta ba ya mike yace zanyi maganin ki don haka ki shirya ki koma kasar ku don ba zan zauna da wace bata tsoron Allah ba a gidana.
Nan dai su fatiya suka shiga bani hakkuri da ban baki suka farar mata dole tayi shiru ya fice gidan gaba daya.
Duk abinda ya faru akan idon laraba itace ta shigo tana bada labari hankalin shi ya tashi sosai har yaji auren nafisan gaba daya ya fice mashi a rai.
Mun ci gaba da hada hadan shirin suna wanda maryam bata da hutu itace ke zirga zirga ka karatu AA da kan shi yace ya daukar min excuse a school inda suka ban sati biyu.
Yana jin dadin yadda yake shigowa gidan ya samu ana ta harkan arxiki da raha da dariya sai yake ganin gidan tankar ba nasa ba.
Chapter 4 · 0% Book details