← Book details Majnoon Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 27

Sashe 20

Majnoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tafiya suke suna Magana ammashi bayajin abinda suke fada, tun daga nesa Faisal ya nunawa kabir, gurin da adnan yake yace " ga abokinan ce sunansa adnan"
Da karfi kabir ya dago kansa ya dube gurin da faisal ke nuna masa ,

Tunda edon kabir suka fada kan adnan, yaji wani irin zirr kwakwalwarsa ta dauka; daga hannu yayi yadafe kansa saboda mummunan cewon dayake masa, yana kokarin nuna adnan, jiri yasoma dibarsa saboda zafin da kwakwalwarsa take masa, kad'an yayi ihu, a hanakali yake sulalewa kasa yafadi wanwar,

Daddy dake zaune acikin taro, yana kallon duk abinda suke, amma shi bai lura da adnan ba,sulalewar Kabir kawai yagani, da karfi yace " innalillahi wa inna ilaihin raju un" nanfa kaga kallon kowa yadawo kansa ana tambayarsa lafiya, dasauri yamike yanufi gurin su kabir, mutane suka bishi da kallo, kabir yana kwance a kasa a some, faisal ya durkusa kusa dashi, yana girgiza shi, duk ya tsorata, yarasa meke faruwa,
Daddy ya karasa kusa da faisal,
Ganin halin da ake ciki yasa mutane suka yo kansu, sai salati ake, hakalin kowa yatashi,

Cike da firgita adnan ya juya da gudu yafita yabar gidan, domin yasan dacewa yanzu kam komai yachabe, duk ya fita hayyacinsa, yana fita yayi daidai da wani mai napep yashigo layin da sauri yataresa , tare da umurtarsa daya kaisa airport, ba musu mai napep din ya tada napep suka wuce airport
□□□□ □□□□ □□□□
Koda faisal yajuyo gefe adnan yaga wayam, babu adnan babu labarin, abin yakara daure masa kai, waishin meke faruwane, kodai hakan yana nufin cewa wannan shine yayan adnan, kansa yake tambaya,

Daddy yasa aka kwashi Kabir akayi asibiti dashi, □□□□ □□□□ □□□□
Rumaisa tana cikin daki ita dasu leemart, suna tsokanarta, umma tazo tasanar da ita mummunan labari, bakaramar firgita tayiba, taso taje asibitin amma umma ta hanata domin tasan idan taje bayan kuka babu abinda zata musu, haka ta hakura tazauna gida...
□□□□ □□□□ □□□□
Bayan ankarasa dashi asibiti likitoci suka karbesa suka bashi taimakon gaggawa,

Cikin kakkanen lokaci suka gano matsalarsa, sun gano cewa babu abinda ke damunsa, sock ne kawai yadibesa, nan bada jimawaba insha Allah zai farka...
□□□□ □□□□ □□□□
Yana karasa airport cike da firgita ya sallami mai napep ko chanji bai tsaya karb'a ba, yakara shiga jirgi, yakoman kogi, tun suna cikin jirgin yake kuka duk ya tsorata,

Yau kam asirinsa ya tono, ya matsu bai karasa kogi ba yasanar da ummansa cewa tabbas Mubarak yana raye

bada jimawaba kuwa suka karasa kogi....

Waya ganemun edon umma taji lbrn Mubarak yana raye😜

https://free.facebook.com/Abdul-Mr-Smiles-Novels-220980808286357/?v=feed&_rdr
[10/20, 10:52 PM] ‪+234 905 395 7618‬: _Title:-_ *MAJNOON*😴
_The mad man_

_Author_:- *MR, SMILES*😃

105 and 106
Via *OHW*
_A love story_💝

Ana ajiyesa filin jirgi, Bai tsaya akazo daukar saba, taxi yashiga yakaraso gidan da shigowarsa cikin gidan yanufi sashen haj zainab cike da tashin hankali,

Tun bai karasaba yake kiran sunanta, dasauri tafito daga dakinta tana murna a tunaninta sunyi nasarane akan Mubarak,

Sunacin karo dashi taga yana kuka cike da firgita tace "adnan lafiya kuwa"

Adnan yakara fashewa da kuka, yana fadan "umma yau zamu mutu, wlh yaya Mubarak yana raye kuma yana ganina yaganeni"

Haj zainab ta toshe baki nta tana kokarin yin kuka tace "nashiga ukku" taja hannun adnan suka karasa cikin daki, tazaunar dashi kan gado, "kafadamun meke faruwane, garin yaya hakan tafaru" haj zainab tafada, takarasa maganar cikin hargowa

Adnan yana kuka yafara labarta mata komai akan abinda yafaruwa,

Cike da tashin hankali ta mike tsaye "karyane wlh bai isa ya hakana abinda kajima tana hasasheba, shidin banzaci uwarsama bazata iya daniba, matukar bokana yana raye, ai kamar yadda yabar gidan nan harna tsayon shekara biyu, haka zaibarka kayi mulkin wannan sa sarauta, ta juyo ta kalli adnan sannan tace " jirani naje yanzu nasanar da boka abnda ke faruwa, kazauna a daki karka fita saina dawo"
Tana gama fada sannan ta juya ta janyo mayafinta tayafa, tafita, tabar adnan nan zaune cike daki yana kuka,

Da sauri sauri take tafiya kamar ta had'a da gudu, daidai kofar falo fita sukaci karo da mai martaba saida gabanta yafadi damm, Sannan tadan daidai kanta tana ta gaidashi, ya amsa mata ya dube yace "ina zakije"

Nan take jikinta yadau rawa, cike da inda-inda tace "zanje, amm...amm...."

Mai martaba ya dakatar da ita dacewa "komadai inane, bazaki jeba domin yau inaji a jikina, kamar akwai wani abun da zai faru a gidan nan, don haka yau kowa bazai fitaba, tundaga kan 'yan aikin gidan nan harzuwa 'yan gidan nan, babu wanda zaije ko ina"

Dasauri haj zainab tace "amma ...."

Mai martaba yadaga mata hannu "banason gardama kikoma kawai bazaki jeba, yayi shiru yana kallon yadda jikin ke rawa, kamar zai tafi sai kuma yafasa yajuyo ya kalleta yace "ina adnan"

Cike da rashin gaskiya ta share gumin dake karyo mata sannan tace "yana cikin dakina" tana gama fada mai martaba yafice yabar gurin,

Tsaye tayi cike da tashin hankali, duk edonta sunfinfito, yaudai ko dubun suce tacika, take tambayar kanta,

Juyawa tayi takoma dakinta, adnan yana zaune yana kuka ya mike da saurin " harkin dawone"

Cikin sanyin jiki takai zaune kan gado " mai martaba ya hanani fita, yanzu bansan ya zanyiba, nashiga ukku" tadafe kanta tana kuka, adnan ya zauna kusa da ita shima kukan yakee...
□□□□ □□□□ □□□□
*Abuja*
_Bayan awa biyu_

Duk taron daurin aure kowa ya watse tsirarun mutane suka raka su daddy asibiti, suma basu jimaba suka wuce basu jira yafarkaba,

_Bayan wasu yan mintuna_

Abban rumaisa, daddy, dakuma Faisal, sune kadai a cikin dakin da Kabir yake kwance,

A hankali yasoma bude edonsa, yana nishi, hakan yasa su daddy suka karaso gurinsa, edonsa suka bude wanwar, dakarfi yazabura yana fadan "innalillahi wa'inna ilaihin raju'un" zai mike, daddy yamayar dashi zaune,

Cike dajin dadi abban rumaisa yace "bari naje nakira likita" yana gama fada yafita yabar dakin,

Kabir yadubesu duk bai sansuba, a hankali yake kallon jikinsa kafin yadago kansa ya kalli daddy yace "menakeyi anan"

Daddy yayi murmushi yace "bakada lafiya ne, ana daf da daura maka aure mukaga kazube akasa"

Gaban kabir yafadi, cike da mamaki yace "aure kuma ni, bayan wanda nakeda, yaushe nayi auren na fari, dahar za'a ace za'amun nabiyu"

Daddy yadubesa da mamaki, yaji kalamansa na masu hankaline kodau yasamu hankaline, yana murmushi yace "kabir kodai kasamu lafiya ne" yafada yana kallonsa,

Maimaita sunan yayi cike da rashin fahimta, waye kuma kabir, sai kuma yadube daddy yace " waye kuma kabir anan, ni sunan Mubarak"

Gaban faisal yayi mummunan faduwa, tabbas hasashensa yayi gaskiya, to meyasa akace ya mutu, tabbas akwai wani mummunan alamari akasa, a hankali ya furta sunan a bakinsa kamar yadda yaji adnan yana fada "yaya Mubarak"

Faisal yayi saurin cewa "kaine yarima Mubarak koh? Kanada kani adnan, sannan kuma mahaifinka mata biyune dashi, kadai sarkine"

Da sauri Mubarak yace "eh nine, suna inane"

Daddy yana mamaki ya dube faisal yace "ina kasan wannan"

Faisal yayi ajiyar zuciya yace "zuwana kogi duk nasan wannan, ko a tarihin hikaya bantaba ganin lamari irin wannan ba, acen garin kogi kowa yadauka Mubarak ya mutu, a tarihinsa dana samu cewa akayi mota ta konesa kurmus tayadda ko gawarsa ba'a samuba, saka makon hakan yasa mahaifiyarsa takamu da wani ciwo na rashinsa, saidai ni abinda yadaure mun kai shine, a labarinsa dana samu, banji ance yanada aureba, wai meke faruwa ne haka"

Kuka sosai Mubarak keyi akan wannan labarin dayaji, cikin tashin hankali yake cewa "meya faru da mahaifiyata"

Faisal yana hawaye yace "nima bansaniba, kawaidai adnan yacemun mutuwarkace ta maidata yadda take a yanzu"
yace " ina adnan?"
Faisal yace "tunda yaga kazube kasa, ya gudu, bansan inda yajeba"

A daidai lokacin abban rumaisa da likiti suka shigo dakin, jikin abba yayi sanyi sosai domin tun daga cen likita yasanar dashi cewa kabir yanasamu lafiya, likita nashigowa yakarasa gurin kabir ya dubesa yace "alhamdulillah tabbas lafiya tasamu"

Dubansa yayi cike da mamaki yace "likita wai meke faruwane nifa bangane kuba"

Likita yai ajiyar zuciya sannna yace "kayi mahaukane a shekarun baya amm..."
Dasauri Mubarak yace "hauka kuma likita? garin yaya"

Nan likita ya labarta masa komai akan abinda yasani, akan haukarsa da kuma losing memory kansa dayayi harda aurensa da Rumaisa,

Hawaye Mubarak yakeyi yana fadan "innalillahi wa inna ilaihin raju un"

Duk jikinsa yayi sanyi, jinyadda labarinsa yakasance, ya tausawa kansa,

Likita yadube Mubarak yace " kai dan wane garine, kuma meye labarinka"

Mubarak yana kuka yatsayar da kukan yace "sunana Mubarak nidan kogi state ne, inada aure mata daya dakuma yaro daya mai suna Khalid, ni bansan meye faru daniba, sai yanzu dana farka daga mummunan bacci danayi"

Abba yayi saurin cewa "yanzu kai kanada aure"

Mubarak yace "tabbas inada aure harda yaro daya"

Abba yayi ajiyar zuciya yace "tabbas nayi babban kuskure, dana hada aurenka da 'yata Rumaisa"

Mubarak yadube abbq da mamaki yace "wacece kuka Rumaisa"...

https://free.facebook.com/Abdul-Mr-Smiles-Novels-220980808286357/?v=feed&_rdr
[10/20, 10:53 PM] ‪+234 905 395 7618‬: _Title:-_ *MAJNOON*😴
_The mad man_

_Author_:- *MR, SMILES*😃

107 and 108
Via *OHW*
_A love story_💝

Dakin kowa yayi shiru, faisal mamakin yake to meyasa baiji labari a gurin kowaba cewa yarima Mubarak yanada mata, hard yaro, kuma meyasa adnan ya gudu, kansa yake tambaya,

Jin kowa yayi shiru yasa Mubarak yayi yunkurin tashi yana fadan "yanzu gida zankoma, zanje naga mahaifiyata da matata"

Gaban Abba yafadi, sai yanzu yatuna da maganar da haj luba take fada masa, kar wata rana yaron nan yasamu lafiya yazo ya gujemu, yan idan yatafi wane hali 'yarsa rumaisa zata kasance, Abba yana hawaye yace " dan Allah karka tafi wlh idan katafi zan iya rasa 'yata, 'yata tafada sonka so marar misaltuwa, dan Allah kataima kamun ka aureta, karna rasata ita kadai nakeda"

Dakin kowa saida yaji tausayin abba,

Mubarak yadube abba yace "bazan iya auren kowace macce ba a yanzu, nidai dan Allah kubarni na naje gida"

Faisal yayi saurin cewa "tare zamu tafi, domin inason nasan gaskiya labarinka, kuma nizan maka jagora harzuwa gurin mahaifiyarka"

Mubarak yamike tsaye yana gyara tufafin dake jikinsa yace "yanzu zamu tafi, bazan iya kara awa daya a garin nanba"
Chapter 20 · 0% Book details