Sashe 19
Majnoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Umma tace "tana cikin dakinta, ita da kabir, nashiga dazu nagansu suna karatu"
Murmushi abba yayi sannan yace "bari inje insame, zamuyi magana dasu" yana maganar yana kokarin tashi harya mike, sannan ya wuce dakin rumaisa,
Suna zaune rumaisa ce ke ja masa karatun shikuwa yana zaune kusa da ita yayi jugum,
Yafada duniyar tunani, idan suna tare da rumaisa, sai yarikajin yanason kamar ya iya tuna wani, amma sai kuma yakasa,
Abba yaturo kofar dakin yashigo, hakan yayi sanadiyar juyowarsu gabaki daya suna kallon kofar,
Murmushi abba yamusu, suma sukai masa, yakaraso kusa dasu yayi tsaye a kansa yace "karatu kawai kukuyi"
Rumaisa tace "wlh kuwa ai mumma kusa gamawa"
Abba yayi murmushi yace "yawwa hakan yanada kyau" sai kuma yadanyi shiru kafin yace "amm daman maganar auren kune gobene, kuma ni banason yawan taron jama'ar nan, nasa angayyatomin malamai sannan kuma abban faisal shizai wakilci kabir a gurin daurin auren, sannan kuma cikin harabar gidan nan nakeson adaura auren, dan haka idan kinadawa wasu kawaye dazaki gayyato saiki sanar dasu, amma fa bada yawaba"
Farin ciki gabaki daya ya lullube rumaisa, tana murmushi race "ni abba banida wasu kawaye da yawa, yan skull dinmune kadai, kuma bazasu wuce mutum biyarba, sannan kuma suduka nasanar dasu"
Abba yace "yawwa hakan ma yayi"
Kabir ya dube abba yace "abba ni ina nawa abokanai"
Murmushi abba yayi sannan yace "gamu! ! ai mune abokananka, kuma danginka, kakwantar da hankalinka, kaji?" Abba yakarasa maganar yana kallonsa yana dariya,
Kabir ya girgiza kai,
Sannan abba yafita yabar dakin, yabarsu sukaci gaba da karatunsu,
Rumaisa sai farin ciki takeji a cikin xuciyarta,
Burinta ya kusa cika, Majnoon zai zamo mijinta...
*Washe gari*
ranar aure,
Tunsa sassafe abba ya yasa aka share harabar gidan tasss,
sannan yadauko wayarsa yakira daddy faisal yasanar dashi cewa kafin 10:00 yakirawo malaman gabaki daya su hallara a harabar gidansa, zuwa karfe 11:00 a daura aure,
"Toh" kawai daddy yace sannan suka kashe wayar,
Suna kashe wayar daddy yakira faisal,
Yana kwance a cikin blanket yana bacci mai dadi, yaji wayarsa tadau kara, a hankali ya zuro hannunas yadauki wayar yakara a kunnesa, batare daya duba wayake kiraba,
Hello son" shine sautin daya daki kunnensa, sai lokacin yasan da cewa daddy ne kekira, cikin muryar bacci yace "daddy antashi lafiya"
Daddy yace "lafiya lau, amm daman tun jiya naso nakiraka nasanar dakai cewa yaune daurin auren rumaisa ita da wanna marar lafiyan"
Wani irin mummunan faduwar gata ya ziyarci faisal, da karfi yace " what! !!, da sauri yaye blanket dinda ke jikinsa, daddy yace " lafiya kuwa meke faruwane "
Cikin gaggawa faisal yace "daddy ina zuwa ..." da sauri ya tsinke wayar, yace "ohh shet"
Juyawa yayi gefen adnan, dake bacci sai kwasar minshari yake yasamesa yana bacci, da karfi faisal yake bubuga kafarshi yana kirana sunansa, "kai tashi akwai matsala"
A hankali yake bude edonsa ya dube faisal yace " lafiya kuwa ?"
Faisal yace " ina kuwa lafiya, yanzun nan daddy ya kirani wai yaune za'a daura auren, mutumen abuja mai kama da yayanka Mubarak,"
Da karfi adnan yamike cike da tashin hankali yace "ehhh, nashiga ukku" cikin gaggawa faisal yace " yadace ace mun isa garin abuja kafin a daura auren nan, domin kasan idan aka daura auren nan baza a barmu muzo dashiba"
Adnan yace "hakan za'ayi maza jeka dakinka kayi wanka nima yanzu zanshiga nayi wanka anan " dasauri adnan, yafada toilet,
Shima Faisal yakoma dakinsa yashiga wnka, bawani wankan kirki adnan yayiba domin duk ya tsorata, yana fitowa cikin gaggawa yasaka kayansa, yana gamawa yanfi dakin ummansa,
Yana shiga dakin yatarar da ita zaune akan sallaya, nan yashiga fada komai dake faruwa, bakaramar firgita tayiba, cike da tashin hankali tace " bazakuje a mota ba, jirgi zaku hau yanzu yasaukeku abuja, kushirya maza kuje airport kafin mai martaba yatashi daga bacci"
Haka kuwa akayi bayan sun gama shirya duk yadda abin zai kasance,
Atare suka fito shida umma,
Koda suka fita suka tarar da faisal tsaye a bakin kofar dakin adnan, shima haryazo bai gansa cikin dakinba shine yatsyawa waje yana jiransa,
Nan suka wuce zuwa harabar gidan, driver yadaukesu a moto ya lula dasu zuwa airport....
Aha muje zuwa....😃
https://free.facebook.com/Abdul-Mr-Smiles-Novels-220980808286357/?v=feed&_rdr
[10/20, 10:52 PM] +234 905 395 7618: _Title:-_ *MAJNOON*😴
_The mad man_
_Author_:- *MR, SMILES*😃
103 and 104
Via *OHW*
_A love story_💝
Suna karasawa airport sukayi sa'a kuwa jirgir safe bai tashiba, nan suka shiga.... suka lula zuwa abuja..
□□□□ □□□□ □□□□
Rumaisa tana zaune a daki, tare dawasu kawayenta su biyu, leemart da kuma maryam, suna fira, amma ita sam zuciyarta bata gurin, tunani takeyi ashe daman burinta zai cika akan MAJNOON, yau za'a daura mata aure tare da kabir (Majnoon) tazamo mallakinsa shima yazamo nata, daman hausawa sunce komai yayi farko zaiyi karshe
Maryam ta dafata, ta baya, saida ta zabura "waike tunanin me kike ne, tun dazu muke miki magana amma kinyi shiru"
Rumaisa ta sosa kanta, cike da jin kunya tace "amm bakomai, me kikace ?"
Maryam tace " cewa mukayi kitashi kije kiyi wanka kingafa lokaci yana tafiya"
Murmushi rumaisa tayi sannan tace "Tohm shikenan kujirani yanzu zanfito" tana gama fada tamike tafada toilet,
□□□□ □□□□ □□□□
Abba kuwa tuni yayi wankansa cikin farara shadda, sai fara,a yake, anata shirye-shirye fara daura aure,
umma ma tasha ado, ita da haj luba sunyi kyau abinsu, yau farin ciki ya yawaita a gidan abba,
□□□□ □□□□ □□□□
Kabir kuwa tunda yatashi a safiyar yau yakejin gabansa nafaduwa,
Duk yakasa sakin jikinsa, musan mamma dayaji labarin cewa yaune aurensa,
Tun jiya abba yakai masa nasa kayan dazai saka, yayi wanka yafito yazo yayi tsaye a tsakiyar daki, shifa yanzu komai yadaure masa kai, a duk lokacin dayaji anyi maganar auren nan sai gabansa yafadi, yarasa dalilin yin hakan,
Yayi tsaye a bakin mirror yana kallon kasan, bansan meya tunaba sai kuma naga yayi murmushi, sannan yafara shafa mai, bayana yagama,
Sannan ya shirya shima cikin farar shadda tasha aiki, tana kalli, yasaka hula baka, takalmi bakake, abinka da farin mutum saifa yafito tas dashi, yayi kyau sosai...
□□□□ □□□□ □□□□
9:30
Motoci sai parking sukeyi a kofar gidan abba, yafito waje yana tabar baki cike da fara'a, duk da auren na boyene amma saida mutane suka taru sosai, domin abba mutumen mutanene, harabar gidan abba tacika sosai, saura mintuna kadan a fara daura aure, koshi dan daddy baya nan ne yatafi airport dauko faisal ...
□□□□□ □□□□□ □□□□
*Airport*
Jirgi yadira a airport dake abuja, cikin gaggawa su faisal suka fito, daman daddy yakaraso shima su yake jira duk ya kagu suzo, domin yaga lokaci yana tafiya,
Tundaga nesa faisal ya hangi daddy, da sauri suka karaso gurinsa, faisal yayi hug dinsa cike da fara, "you're wll com my son" faisal yayi murmushi yace " thanks daddy, faisal ya nuna adnan dake tsaye a bayansa yace "daddy wannan aboki nane sunansa adnan"
Cikin gaggawa daddy yace " oya let's go, daga baya idan an gama dauren auren mayi magana a gida, kushiga muje lokaci na tafiya"
Nan suka shiga mota, daddy yajasu suka nufi gidan abba..
□□□□□ □□□□□ □□□□
Mutane sai kara taruwa suke, Abba yashiga cikin gida yafito da kabir ango, domin lokacin daure aure yakusa, Su daddy kawai ake jira,
Rumaisa kuwa bayan fitowarta daga wanka, kawayenta suka fara shiryata, suka tsara mata kwalliya mai kyaun gaske,
Sannan akaje ga sutura ananfa akasha rigima domin ko wacce aka dauko sai rumaisa tace ita bata yimata ba, itadai tafison a yau dinnan tafi kyau fiye da kowace rana,
Da kyar dai aka samu tazabo kala daya, sannan tasaka, tabbas tayi kyau sosai kamar ba itaba, leemart tayi dariya tace " amarya ansha kamshi, kinyi kyau abinki" murmushi kawai rumaisa tayi, suka kwashe dadari, maryam tace " nimadai baza'a barni a bayaba, saina tsokano magana, amarya bakya laifi kokin kashe dan masu gida" su duka suka kwashi dariya harda rumaisa, haka dai sukaci gaba da zolayarta ita kuwa sai faman murmushi take musu.. (amaryar Majnoon😜 )
□□□□ □□□□ □□□□
Motar daddy ta ja parking a bakin kofar gidan abba, tun a lokacin adnan yakejin gabansa na faduwa,
Daddy da faisal suka fito suka barshi a cikin motar yana tunani, harsun fara tafiya faisal yaduba yaga babu adnan da sauri yadawo bakin motar ya leka, yaganshi zaune yayi jugum, faisal yace "fito muje mana"
Saida adnan ya dan zabura yace "to...to" sannan yafito suka nufi kofar shiga gidan, a lokacin har daddy yashige ciki, gaban adnan sai faduwa yake,
Suka tura kofar gidan suka shigo, nan suka tarar da mutane zazzaune, sukayi tsaye suna kallonsu, faisal ya dube adnan yasauke murya yace "cab di jan, to yanzu taya za'ayi mufita da shi"
Adnan yayi ajiyar zuciya yace " hmm nima ina nasani, niko ganinsama banyiba"
Faisal yashiga leka taron yana fadin " bari na duboshi" nan ya d'aga yashiga neman Majnoon, yabar adnan tsaye a gurin, zuciyarsa sai saka masa take taya zai kashe majnoon batare da faisal yasaniba, haka dai yayita sake-sake.. yana neman mafita
□□□□ □□□□□ □□□□
Kabir yana zaune akan kujera, kwata- Kwata yau bayajin nishadi, baisan komeye dalilin hakan ba, jin anfara adu'ar daurin aurensa, yasa yaji kansa yafara sarawa, nan take edonsa suka chanza launi zuwa ja, duk jikinsa yadau gumi, tashi yayi dasaurin yana kokarin komawa cikin gida,
A daidai lokacin faisal ya hangesa, da sauri ya kad'a hannu yace " yes!! Nagansa" sannu yafada, sannan yakarasa gurinsa,
Assslamu alaikum" ya tsayar da kabir tare da mika masa hannu sukayi masubaha, sannan kabir ya amsa masa,
Yana murmushi yace " sunana faisal, amm munzo ne nida abokina domin mutayaka murnan aurenka, mubakine daga kogi state"
Da karfi kabir ya zare edo, kwakwalwarsa tarika juyawa kamar zai iya tuna sunan, kamar yasan sunan, amma sai kuma yakasa tuna komai,
Faisal yariko hannunsa yace" muje koh,
Kabir yabishi da kallo, suka nufi kofar fita,
Adnan dake tsaye a bakin kofa, tun daga nesa yake hangosu,
Kallo daya yamasa yazare edo, duk jikinsa yadau rawa tabbas yaya Mubarak yana raye, mummunan tashin hankali ya ziyarci zuciyarsa, duk ya fita hayyacinsa, gumi yasoma karyo masa,