← Book details Majnoon Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 27

Sashe 17

Majnoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haj zainab tace " kullum kazo gurin photon nan saikayi hawaye, yakama murika manta abunda yawuce, tunda wannna yaron ya mutu adu'a itace kadai abinda yake bukata"

Mai martaba yashare hawayensa sannna yace "nima naso nayi hakan amma bazan iya mantawa da Mubarak ba, yatafi yabarni a lokacin da nake bukatarsa, Allah yajikansa da rahama"

Duk falon kaji an kwashi sautin ameen,

Shikam faisal jukum yayi yana mamaki, to idan wannan ya mutu, toshifa wancen daya baro abuja waye shi, kuma shin taya akayi wannan ya mutu, kuma a ina" duk a zuci yake wadan nan tambayoyin, yana so yasan amsar wadannan tambayoyi kafin yabar gidan nan,

A duk lokacin dataga mai martaba yana yiwa photon Mubarak kuka, jitakeyi kamar ta mutu saboda bakin ciki, amma bata nunawa mai martaba hakan, kullum cikin lallashinsa take,

hannun prince adnan taja sukabar falon suka wuce sashensu,

Bayan haj zainab tabar gurin mai martaba yasa aka kai faisal masaukinsa...
***** **** ****

Suna karasawa sashensu, dasauri haj zainab tasa makulli ta kulle kofar dakin ta zaunar da faisal kan gado tana dubansa tace "jiya kana gayamun magana saikuma wayarka ta tsinke, meke faruwane"

Cike da tashin hankali, a lokacin datayi masa tambayar a lokacin ya tuna da yadda yaga fuskar majnoon cikin jini, saida gabansa yafadi sannna yace " umma Mubarak nagani a grin abuja"

Mummunan tashin hankali ya ziyarci zuciyarta, tuni gumi yafara karyo mata, muryarta na rawa tace " Mubarak fa kace, daman bai mutuba "

Prince Adnan ya fashe da kuka cike da tashin hankali yace "ina gudu a mota zan dawo gida, akan titi wani mahaukaci ya hauro titin da karfi,ni kuwa ban anakaraba saina kad'esa, bayan nakadesa nafito domin na dubasa, shine naga Mubarak kwance cikin jini ga dukkan alamu yanzu yamutu, yadan yi shiru yana shanshekar kuka kafin yaci gaba dacewa " tashin hankali dana shiga yasa nabar gurin, tsoro da firgita suka kamani, bayan na shiga mota nakara gudu sosai domin nayi saurin isowa gida ina cikin gudu kuma wata dabba takara karamun akan titi, nayi yunkurin na kauce mata amma nakasa, kukan dukan danayi mata kawai naji amma dagashi bankara jin komaiba, bansan meya faru daniba farkawa kwai nayi naga kaina a cikin ciyawa, da kyar na iya fitar dakaina nasamu nahauro titi , ina haurowa kuma sai jiri yafara dibana naga duniya tafara juyamun nan nazube kasa, tun a lokacin bansan meya sake faruwa daniba sai kawai farka nayi nagakaina a asibiti" yaja majinar data cika masa hanci, yana kuka yashare hawayensa, haj zainab duk tafita hayyacinta, tsintsar fargaba ce karara akan fuskarta, tama rasa mezatace, duk jinin jikinta ya tsaya,

Prince adnan yana kuka yace " yanzu umma idan yaya Mubarak yadawo shikenan nayi asarar sarautar nan, saida komai yazo karshe yanzu kuma kOmai na neman jagulewa..."

Haj zainab tatoshe masa baki ta hanashi karasa maganar, tana girgiza masa kai itama hawaye take "bazamu rasa sarautaba adnan, kaine sarki a wannan masarauta, ai ta yadda muka kawar dashi tsawon shekaru biyu hakan kuma zamu kara karashi lahira, mudin bokana yana raye to insha Allah babu kai babu asarar masarauta, gobe zanje nasami boka zamuyi magana dakai idan nadawo tashi kaje dakinka, karka nunawa kowa kana cikin damuwa"

Prince adnan ya mike jiki bakwari yafita yabar dakin, haj zainab tabishi da kallo harya fita sannan tayi ajiyar zuciya ta share hawayenta, a hankali bakinta ya furta " tabbas akwai lauje cikin nadi,

Faisal kuwa yana zaune yana tunanin lamarin majnoon yaji an turo kofar dakinsa, anshigo,

Wata ma'aikaciya tashigo da farantin abinci a hannunta tazo har gabansa ta jibge masa abincin, sannan ta juya tana kokarin fita, da sauri yace "kee"

Matar ta juyo tana kallonsa " yallabai kada matsalane "

Faisal yayi murmushi yace " a a bakomai"

"Toh shikenan" tafada sannna tajuya tana kokarin fita,

Yakara kwala mata kira tajuyi akaro nabiyu "yallabai kodai da matsalane"

Faisal yayi dariyar karfin hali, duk alamar rashin gaskiya ta bayya a fuskarshi yana inda2 yace "amm ammm daman tambayarki naso nayi"

Tajuyo tana kallosa tace "uhim ina jinka meye tambayar"

Faisal yace " wai dan Allah wane d'an sarkine ya mutu "

Matar tayi murmushi tace "yarima Mubarak kenan, yaron kirki maison jama'a Allah yajikansa da rahama" takarsa maganar tana hawaye,

Faisal yayi mamakin ganin hawaye a idonta, cike tasauyi yace " meya silar mutuwarsa"

Matar ta tashe hawayenta ta dube faisal tace "koda biyana kudi zakayi bazan iya fada maka abinda yafaru da yarima Mubarak ba dimin saurauniyar gidan nan tahana kowa yabada labarinsa, duk wadda zaka tambaya a gidan nan bazai gaya maka ba, dazakabi shawarata danace maka kadaina tambayar kowa labarin yarima mubarak, domin zaifi maka sauki, kaga tafiyata " tana gama fada tajuya tabar dakin, faisal ya tsahi kamar zai bita yana kiran ta amma taki juyowa,

Bayan tafita yasauke ajiyar zuciya a hankali ya furta "ya Allah" sai kuma yafara zancen zuci " yau naga ikon Allah mutum yana raye sannan za'a rika kiransa da margayi, kodai mafarki nakeyi ba photonsa nagani bane, to idanma majnoon ba yaronsu bane, to to to.... sai kuma yakasa karasa maganar,

Shidaikam zaiso yaji labarin nan, to inama zai samu labarin kuma a gurin wa,

Prince adnan yatuna, yace "yes gurinsa zanje nafada masa gaskiya akan cewa nasan yarima Mubarak kodan yafadamun labarinsa....

Facebook page:- Abdul-mr, smiles novel's

Website:_www.abduljega.blogspot.com
[10/20, 10:51 PM] ‪+234 905 395 7618‬: _Title:-_ *MAJNOON*😴
_The mad man_

_Author_:- *MR, SMILES*😃

95 and 96
Via *OHW*
_A love story_💝

Cikin sand'a yafita daga dakin, leke leke yake ta ina zaiga hanya fita, nan yaji an tabashi tabaya ya juyo da karfi cike da faduwa gaba,

Edo hudu sukayi da wanda yatabashi, faisal yayi yake yana sosar kai kamar marar gaskiya,

Ganin fuskar bodyguard din babu ko fara'a, yasa faisal yace " ina nen dakin prince adnan"

"Uhimmm" kawai bodyguard din yace masa tare da kida kansa, sannan yace "muje" yana gama fada yayi shiru,

Nan yafara tafiya faisal yabi bayansa, har suka karasa bakin kofar dakin prince adnan,

Bodyguard din ya dube faisal yace "nan ne dakin" yana gama fada yajuya yabar gurin,

Faisal yayi tsaye a gurin yakusan minti biyar kafin ya tura kofar dakin yashiga,

Zaune yasamesa akan gado ya hada kai da gwuiwa, jikinsa yayi wani suku-suku,

Dago edonsa yayi ya kalli Faisal, a daidai lokacin faisal yasakar masa murmishi tare da cewa "yallabai gurinka nazo" yana magana yana noke kai ganin yadda prince adnan ke kallonsa,

Kamar bazaiyi magana sai kuma yace "shigo zonan kazauna" ya nunawa faisal gefen gado kusa dashi,

Bayan faisal yazauna sai kuma yayi shiru, adnan ya dubesa yace " meke tafe dakai,

Faisal yayi ajiyar zuciya yanakallon adnan yace " magana cee akan dan uwanka da akace yamutu, ni ina ganin kamar yana raye"

Tsorata sosai adnan yayi, da sauri ya dube Faisal cike da firgita yace "yana ina, kasansane ?"

Faisal yace " indai har hasashena yazamo gaskiya , to tabbas nasansa, ina son insan taya akayi dan uwanka ya mutu"

Gaban adnan yayi mummunan faduwa, baya son tuna lamarin domin yana kara kunar masa da zuciya, edonsa sukayi ja sosai yadube faisal yace " kai dan wane garine"

Faisal yace "abuja"

Gaban adnan yakara faduwa, tabbas anan yayi karo da Mubarak, indai kuwa hakane to tabbas Mubarak yana raye, nan yafar zancen zuci,

Faisal ya katse masa tunani dacewa " taya akayi dan uwank ya mutu"

Cike da firgita adnan yace "hatsarin mota yayi akan hanyarsa tazuwa garin kaduna, labari kawai mukasamu nacewa ya mutu acikin motar kuma motar ta kone kumur ta yadda ko gawarsa baza a iya samuba"

Faisal yayi ajiyar zuciya yanzu kam shakkun zuciyarsa yakauyagane cewa ba majnoon bane Mubarak, domin yaji labarin cewa wannan a mota ya kone kurmus,

Kara duban adnan yayi wadda tun tuni yajima dakara tsundumawa cikin duniyar tunani, yana tunanin taya zai bullowa lamarin, ta yadda faisal bazai ganeba,

Faisal yace "to ita waccen matar fa da bata magana ta wajen falo"

Saida adnan ya zabura lokacin da faisal yayi masa wannan tambayar, bakinsa na rawa yace "mahaifiyarsa ce, tun lokacin da muka samu labarin ya kone a cikin mota, lamarin ya gigitata sosai, tun a lokaci batakara yin magana, yanzu kuwa kusan shekara byu,

Faisal ya girgiza kai matar tabashi tausayi, to mezai hana yatai maka mata, indai har ganin Mubarak zaisa tasamu lafiya, mezai hana yahadata majnoon ko Allah zaisa tasamu lafiya ta sanadiyarsa, tunda kaman nunsu daya da Mubarak dinta, duk azuci yake wannan zance a fili kuwa dago kansa ya dube faisal "ina dai taimakon dazamuyi mahaifiyar Mubarak amma fa saida tai makonka"

Dasauri Adnan yace "menene inajinka"

Faisal yace "mezai hana mudauko, mai kamannun Mubarak wanda yake abuja, mukawosa gidan nan a matsayin Yarima Mubarak"

Mamaki yayi sosai taya akayi faisal yasan kudirin daya yanke acikin zuciyarsa, shima hakan ne plan dinsa,

Jiyake yasamu hanya mafi sauki ta yadda zai kawar da majnoon,

Murmushi yayi yana kallon faisal "kamar kuwa kashiga zuciya nima hakan natsara a cikin tawa zuciyar domin muwarkar da umman Mubarak" adnan yayi shiru sai kuma ya mike tsaye yace "ina zuwa" yana gama fada yanufi hanyar fita,

Faisal yayi saurin cewa "akwai fa matsala daya"
Ko juyosa adnan baiba balle yatsaya yaji mezai fada, janyo kofar yayi da karfi yafita da gudu......

Ina kuma zaije..🙄

Facebook page:- Abdul-mr, smiles novel's

Website:_www.abduljega.blogspot.com
[10/20, 10:51 PM] ‪+234 905 395 7618‬: _Title:-_ *MAJNOON*😴
_The mad man_

_Author_:- *MR, SMILES*😃

97 and 98
Via *OHW*
_A love story_💝

Da gudu yashigo dakin haj zainab, tana zaune ta rafka uban tagumi, tana tunanin yadda zata bullowa lamarin,

Taji shigowarsa saida tatsora data ganshi, tun bai zaunaba yake fadan umma nasan inda yaya Mubarak yake" yana kokarin zaunawa

Cike da Firgita haj zainab ta riko hannusa tazaunar dashi tana kallonsa edo cikin edo "yana ina ne adnan"

Prince adnan yana hawaye farin ciki yace " umma bakon nan dayazo yasanar dani cewa yasan inda yaya Mubarak yake, amma ban nuna masa alamar akwai wani abu dayake faruwa tsakanina dashiba, yace yanason atai makawa umman Mubarak domin tafita daga halin datake ciki"
Chapter 17 · 0% Book details