← Book details Majnoon Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 27

Sashe 10

Majnoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rumaisa ta karba tayi masa godiya, sannan yace "toni zan wuce "
Rumaisa ta kada masa kai cikin yanayin tausayi, sannan ta sauko daga cikin motar, shikuwa ya rufe motar yafice yabar gurin, yabarta tsaye a gurin Zuciyarta tashiga harbawa 9-9, nan tafara zancen zuci yanzu gata cikin garin sokoto saidai kuma btasan inda zata jeba, daman duk zuwan dasuke a motar abba suke zuwa, kuma idan sukazo basa wuce wuni daya, sai kuma sukoma, hakan yasa ko sunan unguwar da kakar tata take bata saniba, shiru tayi tana kallon garejin, sai taga kowa harkar gabansa yake babu wanda yadamu dawani, a hankali tafara taku ta sami wani gefen acikin garejin ta rakube tana cizon labba duk ciwo takeji a jikinta,

*** **

Wata babbar motace bus irin wadda tasauke rumaisa yanzu taja birki a cikin garejin, mutane sai fitowa suke,

Yafito daga cikin motar zuciyarsa fal da farin ciki, a hankali bakinsa yake furta " alhamdulilla"

Kallon daya nayiwa mutum daya fito daga cikin motar yanzu, naga kamar nasansa,

tsaye yayi yana kallon garejin gefe da gefe,

Caraf edonsa yafada kan rumaisa datake rakube a gefen gereji, zare edo yayi cike da mamaki, yakara furta " alhamdulilla" cikin sanda yake tafiya, kamar barawo yazo sata, ta yadda bazataji hayaniyar zuwan saba har ya karasa gurinta, da zuwansa ya cafki hannunta, cike da tsoro da firgita rumaisa ta daga kanta ta kallesa, gabanta yayi mummmunar faduwa, taje zatayi ihu ya toshe mata baki.....

Facebook page:- Abdul-mr, smiles novel's

Website:_www.abduljega.blogspot.com
[10/20, 10:45 PM] ‪+234 905 395 7618‬: _Title:-_ *MAJNOON*😴
_The mad man_

_Author_:- *MR, SMILES*😃

59 and 60
Via *OHW*
_A love story_💝

Tsorata sosai abban fahad yayi a lokacin da aka sanar dashi cewa fahad yana asibiti, Bayama 9ja suna American shida umman fahad amma a ranar suka hawo jirgi suka shigo 9ja,

Karfe 10:30 na safe jirginsu yasauka a airport dake garin abuja, tun a cikin jirgin mahaifiyar fahad take kuka, abban fahad sai lallashinta yake, da kyardai yasamu ta saurara,

Suna saukowa cikin jirgi motoci suka dira a airport din, daman abban fahad yasa a kawo musu moter, nan suka shiga motar suka suka wuce asibiti,

Suna karasawa bakin asibitin abban fahad ya dubi asibitin ya tsuke fuska "wht anan aka kawomin yaro" yafada a sanyaye, ransa a bace ya shiga asibitin a wulakance yake kallon mutane, yakarasa dakin da fahad yake, a kwance suka samesa duk ansaka masa bandej a jiki, umman fahad takarasa gurin fahad tana kuka, tarike masa hannu,

Abban fahad kuwa ma'aikatan yahau da masifa, fada sosai yayi musu ransa ya bace daga karshe yake cewa "wannan wane irin kauyancine da gigadanci, zaku kawomin yarona wannan karamar asibitin me suka sani, asibitin da kowane talaka zai iya kawo d'ansa, abban fahad yayi huci ya dube ma'aikatan, duk sunkuyar da kansu kasa, sannan yace "duk na koreku daka aikin tsaron yarona, domin naga bazaku iyaba" ma'ai katan suka shiga bashi hkr, amma sam yaki hkr, mahaifiyar fahad itama fada tamusu sosai itama ta goyi bayan maganar mijinta, sannan abba yafita yaje yasami likita yace yanaso ya bashi transfer zai dauke yaronsa daga asibitin zuwa wani babban asibiti, ba musu likitan ya yanka masa, yakarba suka dauki fahad suka bar asibitin dashi, wata babbar asibiti suka kaisa, saboda har a lokacin bai farka ba.
Duk glass yayanke masa jiki,

Likitoci sukayi masa aiki sosai sannan suka bada yakinin cewa insha Allah daga nan zuwa gobe zai farka,

Abban fahad yace "toh shikenan" anan suka wuni asibiti suna jinyarsa, mahaifiyar fahad ta tambayi abban fahad "waishin meya faru da fahad ne" abban fahad yace " nikuwa ta ina zan sani, bayan nidake duka bama kasarnar, mudai jira yafarka sai ya gaya mana da kansa"

Haka suka zauna ko wannesu cike da bacin rai da kuma jimamamin rashin lafiyar yaronsu, basason komai yasami fahad...

***** ***** *****
Wani irin katon falone, yasha ado da kamshin turare, wata dattijuwar mata mai kimanin shekaru 45 ce zaune tana kallon tv cikin nishadi da kwanciyar hankali,

Zarah tafito daga cikin dakinta tayi shirinta nafita tana kamshin, fuskar nan tasha make-up tayi kyau abinta sai murmushi take, takarasa bakin kujerar da matar take zaune ta zauna kusa a ita tana murmushi, ummana kallo kike"
Matar data kira da umma ta dubeta tana murmushi " ey, ina zuwa kuma haka aka chaba wannan adon haka"

Zarah ta sunkuyar dakai, tana sosar kanta, kamar marar gaskiya "umma gidan su maryam zance kinsan yau ake bikin antyn ta "
Umma tace " haka nefa, toh shikenan amma dai kirki dade a gidan domin kinsan halin mahaifinki baya son fitar nan dakike, idan yadawo bak'ya nan babu ruwana"

Zarah tayi murmushi tace " insha Allah bazaima dawo ba yatarar bana nan, da wuri zan dawo, nidai zan tafi saina dawo"

Harta mike zata tafi umma tace "zarah naga kwana biyunan kindaina fita aiki lafiya kuwa"

Zarah tadan langwabe kai tana kallon umma tace "ummana banga ribar fita aikin nan ba domin kona fita bana samun natsuwar zuci, ummana kawai kitayani da adu'a Allah yasa na iya jure bakin cikin dazan shiga nan gaba"

Umma ta dube tadan zare ido da mamaki " wane irin bakin ciki kuma 'yarnan, meke damun kine a gurin aikin"

Zarah tayi murmushi a lokacin duk kwalla sun cika mata edo, tana sauri tabar gurin kar umma ta gane kuka take shirinyi tana fadan " saina dawo zan fada miki umma " dasauri ta fice daga falon tafita harabar gidan,

Umma ta tabe baki "toh" sai kuma tayi shiru tana kallon kofar da zarah tafita, sannan tace " Allah yakauta, ina jiran dawowarki" ita kadai take maganar sai kuma tajuya taci gaba da kallonta,

Zarah na fita hawaye suka sauko mata, dasauri tashige motar ta,ta daura kanta kansitari, tana hawaye, zuciyarta har wani zafi take mata, rashin faisal a gareta ba karamin tashin hankali bane, a duk lokacin da suka hada edo dashi wani irin sonsa yake kara shiga zuciyarta, saboda ta sami salamar zuci yasa tadaina zuwa gurin aikin domin tagaji da irin wulakanci da faisal kemata, amma duk da haka haryanzu zuciyarta cike take da kaunarsa,

Sitarin motar ta daka tana hawaye sannan tadaki kirjinta daidai gurin zuciyarta tana fadan "laifin kine zuciyata, kece kika sakani komai, kece kika ingizani inda ake wulakantani, inda aka daukeni marar zuciya mai nacin soyayya... kuka takeyi cike da tausayi, cikin kukan take fadan "meyasa kika kamu dason maso wani, tabbas kuwa kin sakani a koshin walaha,..." kuka ya kubuce mata, takasa karasa maganar ta saukar dakai kan sitiri, ta jima a hakan kafin ta dago kanta, tatsayar da kukanta sannan tashare hawayenta, ta sai-sai ta kanta, ta kunna motar tayiwa mai gadi hoh ya wangele mata kofa sannan tafice tabar gidan...

*Wacece zarah...*

Facebook page:- Abdul-mr, smiles novel's

Website:_www.abduljega.blogspot.com
[10/20, 10:45 PM] ‪+234 905 395 7618‬: _Title:-_ *MAJNOON*😴
_The mad man_

_Author_:- *MR, SMILES*😃

61 and 62
Via *OHW*
_A love story_💝

*Wacece zarah*

Zarah heesham shine asalin sunananta, black beauty ce ga diri ga k'ira sonkowa kin wadda yarasa,

Zarah ta kammala karatunta na degree yanzu haka tana aikine a wani company, a company ne suka hadu da faisal, tun farkon haduwarsu da ita tafara nuna masa so amma shi saiya rika basarwa,

Hakan yasa tanace harsaida takai data furta masa, tun da ta furta masa cewa tana sonsa kuwa a take a gurin ya yi watsi da maganar tare da dayima wulakanci, ko da gargadin cewa karta kara bijiro masa da irin wannan maganar,

Amma duk da haka zarah bata daina binsa ba tanayi masa magiya akan yakarbi soyayyarta amma faisal yaki, kullum wulakancinsa kara karuwa yakee. Zarah tayi masa kuka har ba iyaka amma kwata2 yakiji tausayinta, shi ace warsa baya kaunarta, shi bata yimasa baki daya, duk wulakanci na duniya faisal yayiwa zarah akan yaga yacire mata sonsa a cikin zuciyarta amma ina yakasa...hakadai zarah taketa hakuri dashi, tana kara lallashin zuciyarta akan ta dage wata rana zatayi nasara akansa, ( wace rana ce wannan ) oho

Iyayen zarah ma'aikatan kwainatine, mahaifinta da mahaifiyar duk aiki suke, mamarta doc ce, mahaifinta kuwa librarian ne a wata university,

Su biyune a gurin iyayensu daga ita sai kanwanta Nafisat wacca suke kira da feena...

_Wannan kenan_

***** ***** ******

Haj lubace zaune a daki tasaka rumaisa gaba tana tambayarta akan tagaya mata yadda wannan abin yafaru kuma ta sanar da itada meye silar faruwarsa, rumaisa kuwa bayan kuka babu abinda take, hajja luba tace "to nidai nagaji da wannan kukan naki, tunda bazaki fadamunba, ni zan koma waje idan kingama kukanki saiki kirani kisanar dani" tana gama fada ta mike tsaye,

Rumaisa tayi saurin riko hannunta, tana shanshekar kuka tace "zan fada, dan Allah kizauna wlh zanfada "

Haj luba tayi ajiyar zuciya sannna ta zaune tace "fadamun ina jinki, meye silal faruwar komai" ta fada ta kallon rumaisa edo cikin edo,

Muryar rumaisa na rawa tafara fadawa hajja luba, komai daya faru, harda dukan da abbanta yamata akan saita aure faisal, tun bata karasa gayawa hajja luba,

Hajja luba ta dakatar da ita, zuciyarta tadau zafi zanta yabace sosai cike da masifa take fadan "shi Usman (abban rumaisa) shine zai miki auren dole, harda duka, wato kenan badan Allah yasa kinzo nanba , dasaidai kawai naji auranki daga sama, to wlh bai isaba, yadda yake nuna ikonsa akanki nima haka inada iko akansan domin nice na haifesa, hajja luba tayi shiru tana huci, sannan ta kara kallon rumaisa tace "kikace kinada wadda kikeso koh" Rumaisa tace "eh inada"
Haj luba tace "ya sunansa kuma d'an gidan waye" gab rumaisa ya tsinke yafadi, domin acikin labarin data bawa hajja luba bata sanar da ita cewa mahaukaci take soba, rumaisa tayi shiru tana kallon hajja luba, batasan sunan majnoon ba ballema hartasan sunan iyayensa, a wane gari yake oho, itama bata saniba, tsoro takeji karta fadawa hajja luba cewa wadda yakeso mahaukacine ne, domin tasan dacewa, zata dauki maganar tata ashirmen banza,

Tayi shiru hajja luba ta tsureta da edo, bakinta na rawa ta soma furta " bansan..."
Chapter 10 · 0% Book details