Sashe 6
Laifin Waye Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
"Tun zuwa na baki ce komai ba kuma ina ji Baba tace wannan zuwan naki ne ko nayi laifi inaso ki sani tun lokacin da aka kawo miki asibitin mu naji kin kwanta min ta nan ne na fara neman inda kuke zaune kuma gashi ban sha wahalar da mun gidan ba".
Hauwa'u tace.
"Nagode sosai bisa ƙoƙarin da kai akaina Allah ya saka da Alkairi".
"Nazo da ƙoƙan barata ina fatan zaki bani dan Allah ina so ki bani dama idan kin gama idda muyi aure in sha Allah zan baki kulawar da baki samo ba".
Inji Dr Nasir.
"A'a ba zan taɓa amincewa dakai ba har abada na dauke ka Yayanah wanda zaka tsaya min a matsalata".
"Kin san kwa me kike fada Hauwa'u ni bazan cutar dake ba nine mijin daya dace ki aura inaso ki bani hadin kai ki karbi tayin da nai miki nasan zaki ji dadin zama dani yana gama faɗa ya Miƙe tsaye ya zaro kudi acikin Aljihunsa ya ajiye mata ya fita cikin sauri daga gidan ba tare da ya jira amsar ta ba.
ta zubawa kudin ido ganin yawansu BaBa Sa'a ta fito daga ɗakin tace.
"Wallahi ke sakarai ce mara wayo ae duk ina jin abinda kuke fada ki sani cewa Dr Nasir shine mijin daya dace ki aura da zartar kin kammala idda kinsan baxan iya zama dake muna goga kafada ba sai kace uwar gida da amarya ba".
_AISHA YAHYA TANKO_
*LAIFI N WAYE*
*© AMAZING WRITER'S ASSOCIATION✍🏽*
*BY AISHA YAHAYA TANKO*
*PAGE 18*
Ta gama balbalin faɗanta ta inda ta shiga ba ta nan take fita ba tace.
"kiwa kanki faɗa ki sani a yanzu bani da burin da ya wuce naga Allah yai miki sakayya daga wahalar da kika shiga abaya kullum addu'ar dana ke miki ita ce zaɓin Allah ada na tursasaki akan abinda bakyaso kuma kin bi amma yanzu na gane kurena naga faɗan dana ke miki ba shine mafita ba, na biki a hankali shine kawai dan Allah Hauwa'u ki karbin tayin Dr Nasir kinji".
inji Baba Sa'a.
Hauwa tace.
"Baba kar ki damu zanyi dogon tunanin akan Dr Nasir in sha Allah zan sanar dake nan da kwana biyu".
To shikenan ƴar albarka Allah ya shiga lamarin mu Baba Sa'a tace yawwa dama ina so ki shirya kayanki jibi gobe zamu kauye wajen su Inna Hama saboda suga jikin naki su tabbatar kin ji sauki kuma kinsan Mahaifiyarka tana fama da ciwon ƙafa ko tashi bata iya yi.
Inji Baba Sa'a.
Hauwa cikin zullumi ta miƙe tsaye bakinta
yaƙi rufuwa dan murna tace to Baba bari naje na fara shirya kayan.
"Haba ƴar nan kya dai bari kici abinci kar yai sanyi irin wannan murna haka kamar wadda akai mata albishir da zuwa Makka".
Inji Baba Sa'a.
"Tab Baba ai zuwana ƙauye dole nai murna yaushe rabon da naje yau kusan shekara uku fa ai kinga dole naji daɗi sosai ki bar abincin bana jin yunwa".
A can asibiti kuwa mutane sun cika a kofar office ɗin Dr suna jiran zuwan sa isar sa ke da wuya yayi parking ya fito daga motar fuskarsa babu walwala yana ta saƙe-saƙen acikin zuciyarsa game da Hauwa'u har ya isa bakin office ɗin mamaki ya kama shi ganin yadda aka cika bakin office ɗin ya saki fuska yai musu sallama suka amsa duk suka miƙe tsaye tare da yi masa sannu da zuwa ya Amsa toh aka buɗe masa office ɗin ya shiga ya ganshi tsaf yayi addu'a sannan ya zauna akan kujerar sa ya fara ganin mutanen da suke zaman jiransa a haka duk ya gama da kowa ya ɗan kashingiɗe yaji wani ƙamshi ya bugi hancinsa ɗago yai yaga waye Dr Zahra ce tsaye bakin kofar ta kasa ƙarasowa inda yake yace.
"ki shigo mana Dr ya kika tsaya Anan ko nayi laifi ne.
Inji Dr Nasir.
Dr Zahra tayi murmushi tace "ai kai baka laifi nice dai me laifi da har yanzu na kasa rabuwa dakai zuciyarka bata wajena tana wajen Hauwa'u amma duk da haka nake bibiyarka inaso ka sani duk halin dana shiga kaine silla".
tana gama faɗa ta juya tana tafiya.
Dr Nasir ya mike tsaye yana buga hannu yace "a fili wannan wace irin ƙaddara ce take nufin tunkaroni Allah yai min magani ya dawo ya zauna ya ci gaba da duba files din dake gabansa.
Washe gari da sassafe tuni Hauwa',u tai wanka ta shirya tsaf ta zauna a kan wata tsohuwar kujerar ƙarfe tana jiran fitowar Baba Sa'a tasha kyau kamar bata taɓa aure ba idan ka ganta.
Jim kaɗan Baba tta fito daga cikin dakinta itama ta shirya tsaf ta dubi Hauwa'u tace Allah yasa dai kin gasa jikinki kinsan dai likitoci sunce aci gaba da gasawa har sai kin dena jin ciwon ko yaya kar kilu ta jawo bau kina jina koh".
Hauwa 'u tace haba Baba Sa'a ta ina zanyi wasa da lafiyata ai ban manta wahalar dana sha ba kullum sai na gasa wajen.
Suka yi sallama da Malam suka fito suna hira har suka isa bakin titi inda zasu hau motar da zata kai su Ƙauye suka ga mota ta tsaya agabansu.
_Aisha Yahya Tanko_✍️
Alhmdllh abin da na rubuta dai-dai Allah ya bani lada wanda nayi kuskure
Ya Allah ka yafe min
Mu haɗu a littafi na na gaba.......