← Book details Laifin Waye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 6

Sashe 4

Laifin Waye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dr zahra ta shigo cikin ɗakin hannunta riƙe file ahankali ta nufo wajen Dr ta miƙa masa file ɗin hannu yasa ya karɓa yana duddubawa.

"Tab nifa lamarin yarinyar nan ya Fara bani tsoro Muna murna munyi nasarar aiki Amma yanzu ta dawo Mana da aiki Baya inji Dr zahra.

ya numfasa ahankali ya gyara Zamansa, "Allah dai ya rufa asiri fatan mu Allah yasa daga wannan sai kuma sallama" inji Dr Nasir ya dubi Hauwa'u wadda take kwance kamar gawa.

"innalillahi wa'inna ilaiyun raju'un Dr" inji Dr zahra gaba daya suka nufi karasa gadon da Hauwa'u take kwance Dr kifa kansa yai Akan gadon.yana salati hannu yasa Yana goge kwallar.

A Nan na kawo karshen Labarin kashi na daya mai Suna LAIFI WAYE mu hadu a kashi na biyu ƙofa a buɗe take ga duk me san ƙarin Bayani ya tuntubemin Akan wannan number din 08173846034

*AISHA YAHYA TANKO*

*LAIFIN WAYE*

*© AMAZING WRITER'S ASSOCIATION✍🏽*

*BY AISHA YAHAYA TANKO*✍️

*PAGE 11*

Gaba ɗaya suka yo kan Hauwa'u a kiɗime suna ƙoƙarin lalubo ruwan dake gefanta.

Dr ne ya yayyafa mata ruwan ta ɗan motsa kadan ta buɗe idonta

" Allah na gode ma da kika farka ina ne yake Miki ciwo?".

Hannu Dr yasa ya dakatar da ita ya nai mata nuni data fita ta basu waje su ƙara duba jikin Hauwa'u Baba Sa'a ta fice daga ɗakin jiki a sanyaye tana waige-waige kamar mara gaskiya tayi jigum a bakin kofar ɗakin tana share hawayen da suke kwaranyowa ta ƙuncinta tasa hannun ta share .

A can ɗakin da Hauwa'u take kwance kuwa su Dr ne suke duba ta suna ƙoƙarin gano abinda yake damunta a wannan lokacin.

Dr Zahra ce take rubutu a cikin file ɗin dake hannun ta.
Dr Nasir ne ya dubi Hauwa'u yace.

"Yanzu me yake miki ciwo a jikinki?".

Ta ɗan numfasa cikin ƙarfin hali tace.

"jikina ne yake ciwo ji nake kamar ana sassara min shi".

tana maganar ne cikin ƙarfin hali.

Murmushi yayi ya dubeta yace.

"Sannu ga magani nai na rubuta miki za'a siyo miki shi yanzu kisha insha Allah zaki ji daɗin jikinki fatana dai ki kula da kanki ki ƙara hakuri har kiji sauki ki koma gida hankalinki ya kwanta idan mijinki yazo kice ina san ganinshi a office ɗina akwai tambayoyin da zan masa".

Yana gama faɗa ya juya ya fice daga cikin ɗakin Dr Zahra tana biye dashi fitar su ke da wuya Baba Sa'a ta nufo su fuskarta cikin damuwa tace.

"Dr ya jikin nata dan Allah ka fada min halin data ke ciki kar ka ɓoye min komai".

Dariya yayi me ɗauke da nuna farin ciki yace.

"ki kwantarki da hankalinki na gano abinda yake damunta kuma in sha Allah ba wata damuwa yanzu dai ga magani nan ki siyo yanzu ake san tai amfani da shi".

Miƙa mata takardar yayi nufi office ɗinshi

Dr Zahra ta juyo wajen Baba Sa'a tana cewa.

"Ya kamata kiyi sauri ki siyo mata magani tasha yanzu kuma ki taho mata da abincin da zata ci".

Tana gama magana tabi bayan Dr Nasir tana murmushi.

Shigarsa office keda wuya ya zare glass ɗin dake idonsa ya zauna akan kujera yana duba file ɗin dake gabansa yaji an turo ƙofar office ana ƙoƙarin shigowa.

Dr Zahra ce ta shigo office ɗin ta ƙaraso inda yake ta ɗan rusuna gabansa ta ajiye masa file ɗin tana murmushi kallon -kallo suka da Dr Nasir.

Ta sakar mata wani irin kallo me dauke da abubuwa.

*AISHA YAHYA TANKO*✍️

*LAIFIN WAYE*

*© AMAZING WRITER'S ASSOCIATION✍🏽*

*BY AISHA YAHAYA TANKO*

*PAGE 12*

_Ina Amare 'yan ƙwalisa ko masu sha'awar koyon kwalliya nazo muku da sabon albishir *Hafcy-beauty-kn*,07038455700 ta shirya tsaf don gyara Amare su fito tas ta tanadi kayan kwalliya kala -kala wanda ake kira mai da tsohuwa yarinya duk mai buƙata ya tuntuɓemu a wannan Number acikin farashi me rahusa Tana gyara Amare tana koyar da ɗalibai shima cikin farashi me rahusa._
*08173846034*

Dr Nasir ne yai ƙarfin hali yayi ajiyar zuciya yace.

" Dr ya akai ne ko akwai wani abu ne?".

Cikin kissa take magana.

" A'a Dr daman zuwa nayi muyi sallama kafin na wuce gida amma idan na ƙarasa zan nemeka a waya ina fatan wayar tana kusa dakai?".

Ɗaga kai yayi alamar Eh bakinsa ya gaza furta komai tun shigowar Dr Zahra ya rasa abinda yake yawo a tsakiyar kansa komai ya tsaya masa.

Dr Zahra cikin ɗaga sauti tace.

"Dr ko baka ji abinda nace ba naga ka tafi tunanin Hauwa'u".

A firgice ya ɗago kansa yana dubanta cikin inda_inda A'a Dr jinai kaina ya sarawa.

Ta ƙara matsowa daf da shi tanai masa sannu fuskarta cike da tausayi juyawa tayi a hankali ta nufi kofar fita taji ya kira sunanta cikin muryar ta bata taɓa jin wani ɗa'na miji ya kira ba,tsayawa tai cak saboda yadda taji tsikar jikinta ta tashi ƙafafuwanta sunyi mata nauyi yadda baza su iya ɗaukarta ba.

"Bazaki ki bari na ƙarasa wannan aikin ba na kaiki gida ba kinji".

"Na gode da kulawarka amma a halin yanzu har an zo ɗaukata".

Ficewa tai cikin sauri ba tare data jira amsar da zai bata ba.

Miƙewa yai tsaye yana kai da kawo acikin office ɗin ya rasa abinda yake damunshi shin ina zai jefa rayuwarsa ko ya ƙarbi tayi Dr Zahra.to shin ina zai kai soyayyar da yake wa Hauwa'u wadda yake jinta har cikin zuciyarsa a haka dai yai ta tunanina daga ƙarshe ya yanke shawarar duk yadda zai yi ya ceci lafiyar Hauwa'u ya haɗa files din dake tule akan tebur ɗinshi ya sa glass ɗin idonsa ya dai shirya tsaf ya nufo kofar fita ya murɗata yaji kamar ana ƙoƙarin shigowa cikin office dakatawa yai yana jiran me shigowa Umar ya shigo fuskarsa cike da damuwa sallama yai wa Dr cikin ladabi

Dr ya bashi wajen zama shima ya zauna suka fuskanci juna na 'yan daƙiƙai kafin suyi magana.

"Dama cewa akai kana san ganina shine nazo naji ko lafiya?".

"Ban fahimci abinda kake nufi ba ban shaidaka ba daga ina kake kuma waya turoka?".

Wajena lokaci guda ya jero masa wannan tambayoyin.

Ya ɗan ɗago kai yana shafa ƙeya gumi ya fara sallama a fuskarsa duk da sanyin Ac amma be hana gumi kwarara ajikinsa ba.

"Ni sunana Umar ni ne mijin Hauwa'u".

Ya zare glass ɗin dake manne a idonsa yana duban shi sannan yace.

"Dama kaine mijin nata to masha Allah dama wasu 'yan 'tambayoyine zan maka idan bazaka damu ba kwanaki inaiwa Baba amma taki sanar dani takamaiman abinda yake damun Hauwa'u saboda akwai sila mudai a iya bincikenmu na likitoci mun gano abinda ya haddasa mata ciwon sai dai ƙarin bayanin da muke san ji daga gare ka ina sauraronka".

Cikin kiɗima da fargabar ta ina zai soma yace a ransa ranar wanka ba'a boye cibi yau itace rana ta ƙarshe da zan bayyana maƙasudun ciwon Hauwa'u saboda aga *Laifin Waye* a ciki".

Inji Umar.

*AISHA YAHYA TANKO*

*LAIFIN WAYE*

*© AMAZING WRITER'S ASSOCIATION✍🏽*

*BY AISHA YAHAYA TANKO*

*PAGE 13*

_Ga masu buƙatar talla su tun tu ɓemu ta wannan Number kamar haka 08173846034_

Wani irin kallo yake masa me ɗauke da tuhuma gyaran murya kafin yace wani abu ya ɗan numfasa yace.

"To Malam Umar kai nake sauraro nasan kasan dalilin da yasa nake san ganinka amma ka gaza cewa komai".

Ya ɗago kansa yace.

"Ina maraba da duk tambayoyin da zakai min nima in sha Allah zan sanar dakai komai game da rayuwar mu da Hauwa'u".

Dr Yayi murmushi me ɗauke da nuna jin dadi.

Umar ya fara magana kamar haka.

"Ni dai tunda na buɗi ido naga Hauwa'u a gidan mu nasan nayi matar aure daga wannan lokacin na ɗau san duniya na ɗora mata duk da lokacin kowa zai ɗauka ƙauna ce kawai ta wa da ƙanwa nake mata saboda duk abinda take buƙata nina ke mata shi, ko take san ci ni zanyi ƙoƙari naga na siyo na bata a haka har tai girman da zata fahimci soyayyar gaskiya nake mata daga nan ta fara jan baya dani ta kuma guji duk abinda zai fito daga hannuna tun ina ganin abun wasa ne har ya zama gaskiya,ni kuma kullum ƙaunarta ƙara shiga raina take ga samari a waje suna tururuwa a kanta a duk lokacin dana ga Hauwa'u da wani ji nake kamar na fille kansa na huta, abokaina suka bani shawara ko tana so ko bata so nasan yadda zai ai na aureta da zarar anyi auren zata fara sona naji daɗin shawararsu nabi duk hanyar da zanbi don naga na mallaketa nasami goyan bayan Baba Sa'a tai ruwa tayi tsaki hatta Babana dan kallo ya zama bayan anyi bikin mu ne sai matsala ta ƙara kunno kai Hauwa'u kwatata taki bani haɗin kai ni kuma abin yana damuna narasa wanda zan faɗawa kawai sai na yanke shawarar sanar da Baba Sa'a nan take ita ta nuna ɓacin rai a fili ta zo gida ta iske Hauwa'u tai mata nasiha ta tafi bayan ta tafi ne Hauwa'u ta nuna ita wannan nasihar bata shiga zuciyarta ba, ni kuma gashi nasha magani ƙarfin dana ke jina kamar matashin doki da shigata dakin na iske baccin ya fara ɗaukarta banyi wata-wata ba na haikefa wanda tun tana motsin yadda zata ƙwaci kanta har ƙarfinta ya fara karewa ni kwa ji nake kamar ana ƙara min wani sabon ƙarfin ajikina nan take naga jini ya fara tsattuwa ajikinta daga nan hankalina ya dawo jikina gabana yai mummunan faduwar ganin bata motsi ga jini be dena zuba ba na ɗauketa a suma na kawo ta wannan Asibitin naku na komagida na sanar da Baba Sa'a halin da ake ciki, itama hankalinta yayi mutukar tashi".

Daga nan na tsorata na fara dana sanin abinda na akaita mata.

Dr Nasir yace.

"To ga irinta nan ka haddasa mata cutuka idan an sami sauki anan sai kuma wani abun ya ɓullo,har yanzu kana san zama da ita idan ta sami sauƙi?,ko yaya amma inaso ka gane itafa rayuwar aure sai anbi ahankali balle a wajen yara dudu shekarun Hauwa'u nawa da har zaka gwada mata karfi inaso ka sani cewa kaine sila ba kowa ba".
Chapter 4 · 0% Book details