← Book details Laifin Waye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 6

Sashe 3

Laifin Waye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta turo baki tana matse ido kamar me shirin kuka.

"Dama baki k'arasa bani labarinta ba ya kamata kizo muje office ki k'arasa bani labari".

yana gama fad'a ya fice daga cikin d'akin cikin sauri.

Baba sa'a ta amsa masa to gani nan zuwa tafara kici-kicin gyara hijabinta.

"Nifa yunwa nake ji amma shine kike k'ok'arin fita ki barnini kadai' koh" .

Hauwa'u ke fad'ar haka.

Ko kallonta bata yiba balle ta bata amsa.

Acan office kuma Dr Nasir yana zaune akan kujerarsa yana sa hannu a farar takardar dake gabansa, yaji an murd'a k'ofar office ana k'ok'arin shigowa ciki d'aga kansa yayi yana duban me shigowa.

Baba Sa'a ce ta shigo ta rabe jikinta a bangon office d'in.

Dr Nasir yai mata nuni da hannu data zauna akan kujera, nan-da nan ta zauna dama jira take.

Likita ya dakata da aikinsa ya numfasa ya fuskanci Baba Sa'a kafin yace uffan sannan yayi gyaran murya yace.

"Ina fatan dai kinzo da shirin zama saboda kici gaba da bani labarin marar lafiyarki".

Baba Sa'a ta gyara zama tace.

"To Likita ai labarin Hauwa'u yana da tsawo nasan ko kwana zamuyi ina baka baze kare ba, amma kaima ka k'ara bud'e kunnenka kaji sannan ka shirya shirin kuka nasan kafin na k'are sai ka zubar da hawaye sannan kuma zaka tsaneni".

Numfasawa tayi sannan taci gaba da cewa.

"zaka kaso nabar wannan asibitin dan nasan zai iya zama rana ta k'arshe wadda zaka kyamaceni, bazaka so ka k'ara jin muryata ba saboda irin gudunmawar dana bayar wajen haddasa ciwon Hauwa'u" .

Dr Nasir ya dafe kirji idanuwansa suka fiffito ya mike tsaye yana goge gumin dake tsatstsafowa a fuskarsa.

"Yace...........

*Aisha Yahya Tanko* ✍️.
*LAIFIN WAYE*

*AMAZING WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
®️🪄

_(Burinmu mu Fad'akar mu wa'azantar tare da Nishadantar da Al'Ummah)._

*🗻A•W•A🗻*
*KUNGIYA MAI ABUN MAMAKI🇳🇬*

~Idan Rana ta fito tafin hannu bai iya kareta🌞🌄.~

*NA MARUBUCIYA AISHA YAHYA TANKO ✍🏻*

*PAGE 7*

*__________📖 cikin Mamaki yake dubanta yace "kina tsammanin abinda kunnuwana suka ji gaskiya ne ko yaya?, amma idan haka zanso kiyi saurin k'arasa min labarin nan".

inji Dr.

Baba Sa'a idanuwanta suka kawo kwalla tasa hannu tana matsewa.

"idan zaka tuna tun farko nace ma bani na haifeta ba,yarinyar k'anwatace sannan ba'a san ranta ba na aura mata Umar a haka dai rayuwarta ta kasance cikin bak'in ciki da k'unci a gidan mijinta
Kowa yana bak'anta ran d'an uwansa gaba d'ayan su idan ka gansu a wannan lokacin zaka tabbatar suna cikin matsala, amma ba wanda yasan meye matsalar tunda sunk'i bayyanawa lokaci-lokaci nakan lekabsu don naga lafiyarsu haka zan tai mata dabarun mu na manya ko da zanji ta sanar dani halin da take ciki amma ina bata iya furtan komai haka zan futo daga gidan ina wasi-wasi".

Baba Sa'a ta d'anyi shiru na lokaci kad'an kafin ta kara magana.

Dr ya koma ya zauna akan kujerarsa yana ci gaba da sauraronta.

Acan d'aki kuma Hauwa'u ce kwance kan gado ta daga kai sama tana cije baki sakamakon rad'ad'in daya taso mata.

Likitace ta shigo cikin d'akin ta tsaya a kanta tare dayin magana.

"Lafiya Hauwa'u na ganki haka ko har yanzu tunanin gidan kike, ki tausayawa kanki irin halin da kika shiga kinsan fa dole sai anbi a hankali sannan za'a cimma buried, ina Maman taki take?".

cikin karfin hali ta d'an yunkura maganar ta bata iya fita saboda ciwo tace.

" tana wajen Dr wallahi yau wajen zafi yake min ji nake kamar ana barkono ake zuba min".

Subhanallahi inji Likita me ya kawo haka ko kin sosa ne kinsan ba'a san tab'a wajen.

"Aa kawai dai yanzu naji yana min zafi.

A can office kuwa Likita ne yaci gaba da sauraron Baba Sa'a, wayarsa tai k'ara yasa hannu ya dauka ya kara a kunnensa yace.

" eh gata tana office d'ina to bari muzo yanzu".

ya mike a gigice yana laluben glas dinsa.

itama ta mike tsaye tana dubansa me ya faru lafiya naga duk ka rud'e ?inji Baba Sa'a.

*AISHA YAHYA TANKO*✍️

*TSANANIN RAYUWA*

*PAGE 8*

*By AISHA YAHAYA TANKO ✍️👭😨*

*INA ƘARA MIƘA TA'AZIYYATA GA IYALAN AMINU S BONO DA RASHINSA DA MUKAI LALLAI MUN YI BABBAN RASHI ACIKIN WANNAN MASANA'ANTAR TAMU😭😭*

"Abban Walida ina ka samo waɗannan mutanen me zasu yi a gidan nan kuma?".

Inji Amina.

Dakatar da ita yayi tare da daka mata tsawa yace.

"Ki iya bakinki, ki kuma sani nan gidana ne dan haka zan iya kawo kowa kar na sake jin bakinki ya furta wata magana game da su inaso ki bamu wajen zama ki kuma basu abincin da zasu ci su koshi nan zasu ci gaba da zama har sai ranar da Allah ya kawo tafiyarsu baki san irin ladan da zamu samo a wajen Allah ba, shi yasa kike haka ko kin manta *WANNAN TSANANIN RAYUWAR* da ake ciki a yanzu".

Inji Yusuf.

Tunda ake wannan maganganu Hama ta rakube ajikin mahaifiyarta tana tsoro.

Nan dai Amina tayi dukkan abinda ya buƙata saboda ba yan da zata iya ta gyara musu sashen baƙi ta kaisu ta kuma dawo wajen Yusuf ta iske shi yana wasa dasu Walida tace aranta.
``` ko wannan mutumin kamar ba shine ɗazu yake ta faman yi mata faɗa kamar zai cinyeta```

Yusuf ya dubeta yace.

"Sannu da ƙoƙari har kin kammala da baƙin kenan".
Nan ya kwashe labarin ƙarya da gaskiya ya faɗa mata har sai da Amina ta fidda kwalla dan tausayi.

A can ɓangaren Musa kuwa tun shigar sa cikin gida tunani ya addabeshi ya kasa zaune ya kasa tsaye ina tunanin irin badakalar da Abokinsa yake yi,Khadija ce ta iske shi a wannan halin ta tsaya tana dubansa kafin tace uffan,sannan tayi gyaran murya ta ƙaraso inda yake hannu tasa ta dafa shi tace.

"Haba me gida na lura tunda kuka rabu da abokinka ka shiga cikin tunani shin meye? matsalarka,inaso ka sanar dani ko akwai shawarar da zan iya taimaka maka da ita amma rashin sanar dani baze zamar maka mafita ba sai dai ma ya ƙara maka, karuwa ni dai ina me rokonka daka sanar dani pls me gidana".

Musa yaji daɗin kalamanta ya saki ransa ya zauna akan kujerar nan ya bata labarin duk abinda ya haɗu da Yusuf ya ƙara da cewa.

" Nikam bazan iya zama inuwa ɗaya dashi ba, tunda baya jin shawara ko banyo tunani duk abinda yayi zai iya faruwa akan Walida tunda itama mace ce".

"Hakane amma dai rabuwa dashi baze zamar maka mafita ba, ka daure kaci gaba da zama dashi har lokacin da Allah zai ganar dashi kasan fa irin su Yusuf basa jin kira tunda sunyi nisa addu'a kawai itace mafita dakuma ƙara tunatar dasu amma saurin fishi ba naka bane, tunda kowa ya sanka dashi haƙuri kawai zaka ci gaba da yi bari na kawo maka abinci kaci kayi wanka ko zuciyarka zatai sanyi".

Inji Khadija.

Nan ta mike tsaye ta nufi kitchen ta fara kici-kicin haɗawa Me gidan ta abinci da abin sha.

A can ɓangaren su Sadiya kuwa sun ƙara shiga *TSANANIN RAYUWA* gaba ɗaya rigar ba me shiga harkar su balle a taimaka musu haka suke tafi da rayuwarsu cikin yunwa da talauci ba damar su leƙo sai kaji anai musu dan kira ana cewa.

Talaucine ya sa Kawunsu guduwa ya barsu tunda ya gane su da Innarsu masu ƙashin tsiya ce haka suke jin irin wannan maganganun amma basa tankawa Sadiya ce take iya tanka musu.

Inna ce zaune a bakin rigarsu bacci ya ɗauke ta saboda tsananin ciwon cikin daya turnuketa Fatima tana kwance kusa da ita basu aune ba suka ji saukar ruwa a jikinsu tamkar ruwan sama.

*Taku har kullum A'ISHA YAHAYA TANKO ✍️*

*LAIFIN WAYE*

*AMAZING WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
®️🪄

_(Burinmu mu Fad'akar mu wa'azantar tare da Nishadantar da Al'Ummah)._

*🗻A•W•A🗻*
*KUNGIYA MAI ABUN MAMAKI🇳🇬*

~Idan Rana ta fito tafin hannu bai iya kareta🌞🌄.~

*NA MARUBUCIYA✍🏻* *AISHA YAHYA TANKO*

*PAGE 9

*__________📖 Dr ya jima Akan Hauwa'u Yana dube-dubensa daga bisani ya umarci Baba sa'a data kirawo ɗaya daga cikin Likitocin Mata.

Acan kuwa Likitocin Suna tsaye sunyi cirko-cirko a bakin ƙofar Suna sauraro.

Baba sa'a ta iskesu a haka ta isar da saƙon Dr.

ta biyo bayanta suka rankayo cikin ɗakin gaba ɗaya Suka tarar Dr Nasir Zaune gefe guda Yana girgiza kai fuskarsa cike da damuwa Mikewa tsaye yai Yana duban Hauwa'u "a gaskiya aikin nan ya dawo Baya Sakamakon Sosa wajen dan haka inaso Yanzu a gaggauta shiga da ita dakin tiyata nan da mintuna goma saboda gujewa matsala zanje na shirya kayan aiki kafin ku kawota". Yana gama fada ya ficewarsa daga cikin ɗakin.

Baba sa'a ta kurma ihu wanda ya karaɗe Asibitin baki Ɗaya.

Likita tai saurin rufe bakinta tace "idan baza kiyi shiru ba ki fita So kike yarinyarki ta ƙara samun matsala to ki kiyaye".

"Shikenan nayi shiru Amma dan Allah karku kashe min ita wallahi ina kaunarta kuma ita kaɗai ce ya'ta" inji Baba sa'a.

" Ai dama kashe mutane Muke yi da bakinki fa mukaji kince kinci Amanarta" inji Likita.

Wayarta ce tai ƙara tasa hannunta acikin Aljihun rigarta ta zaro wayar ta kara a kunnenta "ok tohm gamu nan zuwa" inji Likita ta Fara kici-kicin daga Hauwa'u da taimakon Baba sa'a suka ɗagata.

Acan ɗakin tiyata kuwa Dr Nasir ne sanye da kayan aiki Yana ta gyare-gyare yaji an turo ƙofa da ƙarfi tsayawa yai Yana kallon ikon Allah ganin yadda Hauwa'u ce kwance Akan doguwar kujera duk kamanninta sun sauya tausayin ta ya kama shi.

*AISHA YAHYA TANKO✍️*

*LAIFIN WAYE*

*AMAZING WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
®️🪄

_(Burinmu mu Fad'akar mu wa'azantar tare da Nishadantar da Al'Ummah)._

*🗻A•W•A🗻*
*KUNGIYA MAI ABUN MAMAKI🇳🇬*

~Idan Rana ta fito tafin hannu bai iya kareta🌞🌄.~

*NA MARUBUCIYA✍🏻* *AISHA YAHYA TANKO*

PAGE 10

__________📖 Nan da nan Dr. ya Fara kici-kicin yiwa Hauwa'u tiyata.

Acan harabar Asibiti kuwa Baba sa'a ce take kai da kawo ta zama kamar tababbiya Saboda irin surutan data keyi yasa Mutane hankulansu ya dawo wajenta.

Kafin kace kwabo Dr.ya kammala da Hauwa'u ya koma gefe guda Yana kallonta ya lalubi wayarsa ya daddana numbobi ya kara akunnensa ya kirawo Dr zahra.
Chapter 3 · 0% Book details