Chapter 70
Kufan Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 29 min read
Shafi na sittin da tara
69
Tun daga dogon corridor da zai sadaka da babban parlor din gidan zaka fahimci akwai wadanda sukazo,saboda tarin robobi da gwangwanaye na lemo har zuwa cikin ainihin falon,baiyi mamaki ba,saboda sanin yadda samhan keda jama'a da tarin qawaye....yasan hakan zata faru,shi yasa tun safe yabar musu gidan,saidai abinda ya bashi mamaki yadda aka gaza tsaftace wajen,duk da falon a yanzun babu kowa,shaidar sun tafi.
Sallama ya sakeyi karo na uku,shuru babu amsa,saiya nufi hanyar sashenta da dan hanzarinsa,saboda so yake ya qarasa dakinsa yayi wanka ya sake kwanciya,don sam jikinsa babu wani kuzari,kamar ya baroshi ga iman ne.
Mamakinsa ya ninku sanda ya shiga parlor dinta,kamar sautin kuka ya dinga ji daga bedroom dinta,abinda ya daga hankalinsa qwarai,ya qaran saurin da yake zuwa bedroom din.
Zaune take saman gadon,ta bawa qofa baya,bai tsaya rufe qofan ba ya qarasa gareta da sauri
"Dakata" ta fada da sauri sanda yake niyyar riqoni,sai ta daga kanta tana dubansa,mamakin dai still bai barshi ba,meye haka yake damun samhar daya sanyata irim wannan kukan?,har idanunta sukayi luhu luhu haka,ta fita hayyacinta?,uwa uba ma kayan dake jikinta sune dai bata sauya su tun safe daya fita ya barta,sai yayi calming kansa ya jawo kujeran madubi ya aza a gabanta,yahau kai ya zauna,cikin kulawa ya fara tambayarta abunda ke faruwa
"dama iman ta taba aure?" Ta jefa masa tambayar kai tsaye tana duban idanunsa
Ga mamakinta murmushi ya saki
"Eh....me ya faru?" Yadda ya dauki maganar ba da wani muhimmanci ba ya tunzurata matuqa,cikin tsananin fushi da fusata ta fara magana
"Oh.....kana sane kenan zaka auri matar da ciwon qanjamau yayi sanadin mutuwar mijinta?,ka kwaso mana masifa,mu taru mu mutu gaba daya ayiwa iyayena asarata?" Ko darr baiji ba game da abinda samhan ke fada,wanda ita awajenta maganar dai dai take da tashin duniya,yayin da a wajensa maganar bata kama koda matsayin tudu na slippers dinsa ba,ya riga daya samu dukkan wani bayani daya dace game da iman
"Ke waye ya gaya miki?"
"Masoyana wadanda basason halakata"
"Duk wanda ya kawo miki labarin to ba shakka cikin biyu daya ne,kodai ya kawo miki shine saboda ya tarwatsa farincikinki da zaman lafiyarki,ko kuma ya samu labarin ne daga muhallin da qarya da sharri da yarfe ta gurbatashi ko kuma shi ya zauna ya yiwa maganar ado.....tabbas iman ta taba aure kuma sun rabu da mijin,wannan kuma ba hurumin da lallai saina gaya miki bane,abune daya shafeni ni kadai,amma maganar tana da HIV wannan bata taso ba,so please ki kwantar da hankalinki mu shimfida kyakkyawan zama a tsakaninmu"
Cikin kukan dake cakude da masifa da tashin hankali tace
"Wallahi bazata sabu ba,ta yaya inaji ina gani za'a cuceni,mutuwa ta shigo jikina nasa hannu na tarbeta?,dama ku maza idan idanunku suka rufe kunason mace ko wanne aibu ke gareta bakwa gani,to ni bazan yarda ba,muddin kana sona kana son zama dani....dole ka haqura da auren iman,domin kuwa ni ban shirya mutuwa ba" idanu kawai ya zuba mata yana kallonta,saboda yadda ta juye masa daga samhar daya sani zuwa wata ta daban,a nutse yake karantarta,yadda wutar kishi ke huruwa cikin rai da zuciyarta,tun ba yau ba yasan wace samha wajen kishi,irin matan nan da suke daukan kishi kamar ibada,basa ji nasa gani akan wanda sukeso,ya dauka duka zata hankalta,kuma komai zai ragu,sai gashi a yau yatabbatar da cewa babu wani abu da ya sauya.
Tsam ya miqe saboda yadda ta fara fadin maganganu kan iman din,bayaso ya shigarwa iman din konya rama mata,saidai yana tsoron kada samhar ta shiga mutuncinsu malam.....tabbas a nan yasan bazai iyayi mata kaara ba
"Dukkaninku ina sonku,keda iman baby wadda ta isa ta sanyani na rabu da 'yar uwarta bisa bin son rai da zuciyar 'yar uwarta,ni nasan me na aura....hakanan nasan nasan wace iman,na kuma bibiye waye bassam" daga haka ya juya yana barin dakin,tayi kukan kura ta tare masa hanya
"Wallahi wallahi bazai yiwu ba" abinda ta dinga fada kenan,ganin da gaske ba zata bashi hanya ba sai ya dauketa cak ya.maidata dakin gadonta yaja mata qofa,cikin hanzari ya wuce nasa dakin ya murza key yana fesar da iska me zafi daga bakinsa,wannan wacce irin masifa ce haka?,wannan shine auren dama ko kuwa ya yake?,har yanzu ko hutun awa daya bai samu ba cikin gidanshi,banda ya fita kenan haka zai wuni suna irin wannan abun?.
Baiko gama sauke wannan tunanin ba bugun samha da muryarta ya riskeshi har dakin,bugu take da gaske kan ya bude mata qofa,lallai ba shakka ya tabbatar ta haukace tuburan samhar,wai anya ma kuwa bamai motsuwar kwanya ko lalurar aljanu ya dauko ba kuwa?.
Barinta yayi taci gaba da bugun iya qarfinta,ya shiga bandaki ya hada ruwa yayi wanka,sanda ya fito shuru babu bugun,da alama tayi wanda zata iya ta gaji,saiya haye saman gadonsa,idanunsa a lumshe ya fada nazari,wacce irin mace ya daukowa kansa?,anya bai tafka kuskure ba?,kodai wannan shine abinda yaa baraka ta hango masa tun yanzu ya fara riskarsa?,da ya rasa iman da wanne suna ya kamata a kirashi?.
Bai sake jin motsin samha ba,bai kuma tashi a wajen ba sai da aka kirayi magriba,ya daura alwala ya sanya slipper dinsa da carbinsa counter ya fito.
Shuru falon yake dai,hakanan yana nan da shararsa,yaji motsi daga sashen samhan,don haka ya sanya kansa ya wuce masallaci,bayan yiwa daya daga cikin yara guda biyun daya aje a gidan saboda aike da bude masa qofa kan ya shiga ya gyara iya hanya da babban falon kadai.
Ya jima zaune a masallacin,tunani iri daban daban na sauko masa,bai taba tunanin riskar matsala irin wannan ba kwata kwata da samha,ya zaci koda.mata uku ya qara bayan ita ba zatayi haukar datakai wanan ba,sai gashi ta bashi mamaki,ta kuma kwance masa kai gaba daya.
Bai bar masallacin ba sai da akayi sallar isha'i dashi,yaga maqotansa sosai suka gaisa,yaji dadin ganin karamci da mutunci daga garesu,daga nan bayan ya fito ya yanke shawarar samar musu abinda zasuci,daji da gani ma basai ya batawa kansa lokaci ba,babu wani abinci da zaici a gidan,bayason batawa kansa lokaci wajen komawa gida dauko mota,don haka ya tari napep drop zuwa da dawowa ya wuce dashi.
Da tafiyarsa da dawowarsa gaba daya bai wuce awa guda ba,mai napep din ya direshi qofar gida,ya biyashi kudinsa harda qari,ya dinga zabga godiya kuwa cikin jin dadi,hannunsa dauke da leda ya juya zuwa gate din gidan nasa,saidai mamaki sosai ya kamashi,ganin sabbin baqin motoci har guda hudu.
Layin nasu yabi da kallo,yana son tantance qofar gidan ne kawai keda sararun yin parking?,sai yaha ba haka bane,ko inama kawai space,jikinsa da zuciyarsa suka bashi wani abu,sai yaci gaba da takawa zuwa cikin gidan yana nazarinsa,har zuwa sanda yake gab da falo,inda ya fara jin tashin muryoyi.
Bai gaza ba bai kuma sareba yaci gaba da kutsawa,bai tsaya ba sai daya dangana da falon bakinsa dauke da sallama,dukka hankulan mutanen dake cikin falon suka dawo kansa,alamu masu qarfi na nuna cewa zancansa akeyi.
Mamaki sosai ya cikashi sanda sukayi idanu biyu da mahaifin samha,qanin mahaifinta dana mahaifiyarta,sai ita kanta mahaifiyar tata,amma duka sai ya shanye wanna,ya ajjiye ledojin saman daya daga cikin kujerun,ya qarasa falon yana gaidasu cikin matuqar girmamawa,suka amsa dukkaninsu,saidai da qyar mahaifiyar samha daketa shafa bayan samhan cikin salon lallashi ta amsa masa,bai damu da wannan ba,koma meye macace yayi mata uzuri,saiya maida kanshi zuwa ga mazan.
"Malam ameen,nasan zakayi matuqar mamakin ganinmu cikin gidanka ko?" Kai ya gyada,so yake kawai yaji qarshen zancan,duk da zuciyarsa tagama ayyana masa komai
"To ba abun mamaki bane duba da yadda diyarmu wadda ke da kwana guda tal cikin gidanka ta kiramu tana gursheqen kuka gami da neman agajinmu,sanda muka iso kuma mun iske mummunan labari mara dadi,wanda mu bashi ka bamu ba,meye abinda yake faruwa" mamaki ya kama ameen din,wannan wacce irin haukace samha ta aikata?,tana nufin dukka abinda ya gaya matan bata yarda da gaskiyarsa ba?.
A nutse yayi musu bayani kamar yadda yayi mata,saidai yana direwa ummanta ta cafe
"Dukka wadan nan bayanan baki ne ai babu wata gamsashiya hujja....ni banga laifin samha ba data nemi ka sake yarinyar nan ba,don ko nice abinda xan aikata kenan,bazan yarda ina zaman zamana a laqamin cutar da bata da magani ba" a nutse lamin ya daga kai ya kalleta kana ya sauke,yanzu ya gano daga inda kowanne hali ya fito daga samha,maida dubansa yayi ga qanin mahaifinta
"Yanzu kai banda abinka ameenu,da jininka a jika,da rufin asirinka,me zakayi da wata bazawara,bayan Allah ya maka baiwa da yarinya budurwa kamae samha?" Wani abune yazo ya tsaye masa cak a wuya,ya hadiye yawu da qyar yana jin yadda zuciyarsa ke masa zafi kan yadda ya aibata iman din,aibu mai muni kuwa,yadda ransa ya motsu da bacin rai yasa ya kasa bashi amsa,har sanda qanin mahaifinta shima ya tofa tashi
"Kuma ni nakega akwai qamshin gaskiya cikin al'amarin,tunda gashi ta bayyana har mijin nata ya rasu,kuma mun tambaya an tabbatar mana lallai HIV dince fa kasheshi tun kafin muzo wannan zaman,saboda haka nima dai gaskiya ina goyon bayan samha"
Gaba daya kansa ga qarasa daurewa da mamakinsu,daga mazan har macen duka babu mai hankali ashe?,zuwa sukayi su tursasashi zama da 'yarsu kenan ita kadai?.......da idanu shima ya kalleshi har zuwa sanda samha wadda ke gursheqen kuka jikin mamarta tayi magana
"Wallahi kawu dama ba sharri bane,kowa fa ya sani,shine kawai idanunsa suka rufe"
"Ni inaga aje kawai ayi gwaji" mamanta ta fada kanta tsaye tana dubansu
"Shikenan,magana ta qare" baban samhan ya fada yana kallon lamin.
Wani kallo lamin din yayi musu,wanne irin cin fuska ne wannan sukazo dash?,iman din tasa za'a dauka saboda cin fuska a tafi da ita gwajin cutar qanjamau?,kawai saboda kishiyarta daya tabbatar da gangan take wannan haukar ta buqaci tozartata?.
"Duk duniya banajin akwai wanda ya isa ya fiddamin matata zuwa layin gwajin cutar qanjamau,bayan ina da dukka yaqini da kuma hujjar lafiya lau take,tunda ta dawo mana gida bata taba wata nummunar cuta ba.....idan dai kuma shakka kan gaskiya da amanata kuma kuka dauki auren diyarku kuka bani to kun tafka kuskure,kuje ku sake bincike akan waye lameen yaron malam khalilu" tsam ga miqe yana jin wani irin zafi tun daga fuskarsa zuciyarsa zuwa gangar jikinsa,bai sauraresu ko waiwayesu ba ya soma haurawa zuwa dakunansa,yana jin yadda cecekuce ya barke a tsakaninsu,yana iya jin muryar maman samha na sake kafa hujja da cewa bashi da gaskiya shi yasa ya bijire,kuma babu makawa zancan samha gaskiya ne,ba wanda ya waiwaya a cikinsu har zuwa sanda ya kammala hayewa,kaifin muryarsu ya ragu,ya tura dakinsa ya shige.
Ya jima zaune yatsunsa cikin sumar kansa,kanshi yayi matuqar daukar zafi,wata qauna ta samha datayi saura a zuciyarsa ta fice fit,bashi da sauran wani buri a kanta,irin wannan tozarci datayi masa gangami har cikin gidansa,yayi mamakin yadda akayi ya debo 'yar gidan qananun mutane,ya dauka 'yar dattijai ce,ya jima zaune a haka ransa a matuqar bace,har zuwa sanda wayarsa tayi ringing,ya waiwaya yana duban fuskar wayar dake aje gefansa.
Sunan malam da ya gani ya sanyashi tashi ya zauna sosai kana ya janyo wayar,cikin girmamawa ya daga ya kara a kunnensa,a nutse malam yayi masa sallama,ya amsa sannan ya fara gaidashi kamar basu hadu ba dazun
"Me yake faruwa ne cikin gidanka lameen?" Kansa ya daure,ya akayi malam yasan da wani abu?
"Yanzu matarka da iyayenta suka bar nan wajena,karka boyen komai ka gayamin" kamar yadda ya buqata hakanan ya zayyane masa komai din,bai kuma boye masa ba,malam ya jinjina kai,yana boye razani da damuwa tare da sosuwar da ransa yayi
"To ai duka wannan ba abun bacin rai bane ko damuwa,qaramin abune da maganinsa bashi da matsala,yanzu abinda za'ayi shine,gobe da safe ka shirya ka dauki ita hajar da samhan,ku wucw asibitin a yiwa hajar din gwajin data buqata din a gabanta"
"Amma malam......." Karon farko a kafatanin rayuwasa daya kwatanta musu wa malam din
"A'ah lamin,kada kace komai,ni dakai da sauran makusantanta ne kadai mukasan lafiya lau take,amma su da basu sani ba akwai buqatar kankare musu shakku,kayi yadda nace din saboda a samu kwanciyar hankali da kuma nutsuwa"
"To malam,in sha Allah" daga haka suka katse wayar,yana jinjina halin girma da dattako irin na dattijon,saidai kuma abinda ya sake qona masa rai yadda suka dauki samha har tasa qafa tabar gidan ba tare da sani ko neman yardarsa ba,baya koda son ganinta a yanzu,don haka baima nufaci zuwa yaja mata kunne ba,saiya koma da baya ya kwanta idanunsa a rufe,zuciyarsa na masa suya,yana son kiran iman,don yana da tabbacin muryarta kadai zata shafe bacin ran dake ransa,ta kuma wanzar da farinciki cikin zuciyarsa,saidai kuma bayason ya qara mata damuwa da tasa damuwar,ya tabbatar duk wadda taji wannan batun a kanta dole hankalinta ya tashi.
Hasashensa kuwa haka yake,kuka sosai iman din ta dinga yi sanda taji case din,duka wannan sakamakon bijirewa iyaye ne,tana fatan kuma wannan shine sakamako na qarshe da zata amsa cikin punishment na laifinta,tausayin iman din ya cika inna qwarai,wannan karon da kanta ta zauna sukayi magana da iman din,irin magana ta 'yar da uwa
"Ki daina kuka iman,ina mai yaqini da tabbatar miki ba zaki tozarta ba in sha Allah,babu wata rana data fito ta fadi ba tare da nayi addu'a a gareki ta samun dacewa da kariya ba,kamar yadda babu wata rana guda daya dana yarda na wuce minti biyu ina fushi dake.....komai munin laifin da kika aikatamin kuwa,ciki harda auren bassam" idanunta dake cike taf da hawaye ta daga ta kalli inna,saita sakar mata murmushi gamida jinjina mata kai tana bata tabbaci
"Duka abubuwan da suka farun ba shakka naji babu dadi,saidai tashin hankali yafi fushi yawa a ciki,saboda na riga dana sani kin tafka babbar asarar rasa miji na gari,wanda nayi imanin bassam bai kama koda yatsar lamin ba wajen nagarta,wannan shine tashin hankalina,bawai fushi da zaben bassam ba,ko a lokacin kina ganin fushi saman fuskata ne kawai saboda ina fatan hakan zai canza ra'ayinki,to amma da yake rubutacciyar qaddararki ne babu abinda ya canza,tunda kika tafi ban zauna da fushinki ba ko qanqani,na maida kaina ga yimiki addu'a kan kubuta daga dukkan wani sharri da wahalar gidan aure.....ko sau daya jikina da bakina basu huta ba,inajin zafi.....ina kuma kasa barci duk sanda kikazo gidan nan kika tafi,saboda na karanci akwai matsala tare dake,nayita zuba idanu ki furta min amma baki fada ba,na zabi na barki ki gayan da kanki ne,saboda kada irin soyayyar da kike ma bassam tasa kiyi tunanin ina tambayarki ne don na na samu hanyar rabaki dashi kiyimin kallo na zalunci,saidai da yake Allah Allah ne,kuma baya bacci,yana tare da dukkan bawansa daya roqeshi da kyakkyawar zuciya da kyakkyawan nufi sai gashi ya kawo komai cikin sauqi,dukkan wata matsala ta warware.....ubangijin da yayi miki dukka wadan nan baiwarwarkin?.....kina tunanin zai saki hannunki akan wannan qaramar matsalar?,kuma matsala ta qarshe da yardar Allah?" Kai iman ta girgiza,tana jin nutsuwa na saukar mata,imani da kuma gamsuwa da hukuncin ubangiji na bijirar mata,qaunar inna tana sake ratsata,sai kawai ta rungume innan tana sake sakin kuka
"Na gode.....na gode inna,ba shakka uwa wata halittace ta musamman,kuma baiwa ce ga dan adam,kyauta daga Allah wadda babu kamarta" murmushi inna tayi tana sake kwantar mata da hankali.
**********Washegari malam ya fiddo sadiqu daga gidansa,ya kuma wakiltashi ya dauki iman ya kaiwa ameen ita,sannan yayi musu rakiya zuwa asibitin da zasuje.
Tsaf ya shirya cikin kyakkyawar shaddar wa gambari mai asalin kyau da tsadar ruwan sararin samaniya,sanda yake saukowa daga bene yayi tsammanin ganin samha,saidai waya babu ita,kai tsaye ya zarce zuwa harabar gidan,inda acan yaga abun mamaki,tuni iyayen samha da kawun nanta na jiya sun halasto wajen,suna ma cikin motocinsu,hatta da samhan tana gaban motar babanta,kansa a daure amma ya qarasa ya basu girmansu ta hanyar gaidasu,suka amsa masa ba yabo ba fallasa
"Saimu wuce ko?" Agogonsa ya kalla
"Iman din bata qaraso ba tukunna,so xamu jirata ne" ya amsa musu yana yin gaba,ya bude tashi motar yayi zamansa,duk duniya banda malam babu wanda ya isa ya sashi aikata wannan abun me kama da tozarci da wulaqanci,koda yaa baraka bayajin zataiys tan qwarashi.
Sau biyu qanin mahaifiyar samha na masa magana kan jiran da sukeyi
"Ina cewa dole jininta ake buqata ko?,idan kun qosa kuna iya yin gaba,na biyoku daga baya" amsar da ya bashi kenan ya maida idanunsa ya rufesu yadda suke. Jin jina kai yayi ya juya yabar wajen bai sake cewa komai ba shima,saboda ya fuskanci lallai lameen din ba kanwar lasa bane shima,da alama ma maganar da sukayi da malam din ta tilastashi aikata abunda suka buqata din.
End of book

Leave a comment

Post
Comments

112201018644657456668
Me ake jira da ita tunda tafice a zuciyarsa. Waje road please taje gatan datake gani tanada shi ya aureta
9 minutes ago

deejerh27
Allah yasa takara wani chapter din dai
37 minutes ago

deejerh27
Ai wallahi ko bai saketa ba bazai taba son sontaba kuma, abun haushi 🙄
38 minutes ago

ummueamn01
Kai wannan samha anyi daqiqiya🤦 Allah yada daga can ya baki red card.well done huguma, amma aqara muna more pages plsssss
an hour ago
Load More

Contact Us
Arewa Books Publishers
WhatsApp: 09031774742
Email: [email protected]
Navigation
Home
About
FAQ's
Legal
Privacy Policy
Terms of Service
Social
Facebook
Instagram

Copyright 2021, Arewa Books | ALL RIGHTS RESERVED | Powered by thinkcrypt.io
"
https://arewabooks.com/chapter?id=62d667a17fc1109aa61070e1#:~:text=Chapter%2070-,Shafi%20na%20sittin%20da%20tara,da%20malam%20din%20ta%20tilastashi%20aikata%20abunda%20suka%20buqata%20din.,-End%20of%20book
[7/19, 10:04 PM] Mummyn Yara: 70
Ba'a qara minti biyar ba suka shigo gidan,take kallo ya koma kanta,cikin shiga take ta alfarma wadda tayi matuqar dacewa da farar fatarta da kuma kwarjini da ajin da Allah ya bata,samha dake cikin mota ta tsurata da idanu,take ta raina kanta,wani kishin iman din na sake turnuqeta,alwashinta da burinta suka qaru,ta yaya ma zata yarda ta hada miji da iman din?,itakam ta godewa bassa daya bar mata makamin da zata yaqi iman din cikin ruwan sanyi ba tare da kowa ya zargeta ba.
Ta cikin madubi ya hangesu,saiya tada motar a hankali ya nufi bakin qofa,saitinsu ya tsaya ya bude motar ya fito,dukka idanunsa naga iman din,akwai damuwa mabayyaniya sama fuskarta,duk da yadda tayita qoqarin dannewa,ya tako a hankali zuwa gabanta,kwalliyarta na fusgarshi,daso samune ya sanyata cikin qirjinta ya shaqi ni'imtaccen qamshin da take fitarwa,ya kuma rabauta da dumin jikintan nan na musamman wanda yake gasgata cewa qalilan cikin mata keda shi.
Dab da ita ya tsaya,taqin dake tsakaninsu kadanne,kowa idanunsa cikin na dan uwansa,wani abu na ratsa jikinansu game da kowannensu,sai ya janye idanunsa a hankali ya maida kan sadiqu dake tsaye a gefe yana waya da matarsa
"Dalla malami dama a motar haya ka daukomin mata?,wannan cin amana ne wlh,ka siya mota ka tsaya kana batawa kanka lokaci" da alama akwai wani zafi qasan ransa,duk da yasan da wasa ya fadi maganar amma tabbas tana bayyana jin zafinsa cikin maganar,yayi masa uzuri mai tarin yawa sabida yafi kowa sanin waye lamin,jin zafinsa yana da alaqa da situation din da ake ciki a yanzu,don haka ya maida.masa da sassauqar amsa cikin rama wasan
"Idan mutum yaji zafi ya saka kaina gabas ya yanka mana.....zuwa dai a nepep an riga anyi,mota kuma bazan siya ba,a siyamin" sai ya kanga wayarsa a kunne yaci gaba da soyewarsa
"Allah ya sakamin" lamin din ya amsa masa yana janye idanunsa daga kan sadiqun zuwa ga iman,sake matsawa yayi daf da ita,wannan karon har suna musayar numfashin juna,ya sanya lallausan tafin hannunsa ya sanya nata a ciki yana dan murzawa kadan
"Kuka kikayi ko jiya saboda wannan wasan kwaijwayon?" Tambayarsa taso karya dukka wani qwarin gwiwa nata,sai qwalla ta nemi taruwa cikin idanun nata,kansa ga girgiza da sauri
"Noooo,wannan kwalliyar amarci ce zuwa ga sabon angon da babu irinsa.....don Allah na roqeki kada ki batamin abata,i like it queen,kuma nayi alqawarin bada tukuici me yawa,ki zaba,goyaki kikeso nayi mu tafi tun daga nan har asibitin a qafa a gadon bayana,ko kuma so kike na daga murya na shelantawa jama'ar unguwar nan ina sonki,ina kuma maraba da shigowar hasken gidan nan zuwa cikin gida?" Wani abu mai sanyi ya ratsa zuciyarta,kamar yadda kalamansa masu dauke da sanyayyar soyayya suka yi mata ba zata,bata shirya ba saiga murmushi ya kubce mata,abinda ya sakashi shima sakin murmushin kenan
"Babu ko daya a ciki"
"Saifa kin zaba"
"Jiranmu suke yaa lamin,kanaji sun fara hon" girarsa dukka biyun ya dage mata idanunsa tsakiyar nata qwayar idon
"Really?,ni ai banji bama,kinsan kurma ne ni kuma makaho ne a duk sanda nake tare dake,komai baya tasiri a wajen komai girma da qarfinsa,so ki manta mu qarasa uzurinmu.....zabi daya sarauniyata"
"Kayi haquri.... next time zan gaya maka"
"Promise?" Ya tambayeta yana murmushi gami da dage girarsa,martanin murmushin ta maida masa tana jinjina kai
"Ok,muje to" ya fada yana tasata a gaba,ta gabansu suka wuce,wanda kusan kowa yayi suman zaun acikinsu,kadama samha taji labari,wadda dayqar mamanta ta riqeta
"Mama ki barni na koma motarsu" ta fada sanda taga ya bude mata gidan gaba da kansa ta shiga ya maida murfin ya rufe
"Kiyi haquri ki zauna a inda kika fara zama,komai ya kusa zuwa qarshe fa,gaggawar me kikeyi?" Da qyar ta tausheta,tuni ameen tashi motar ta fara yin gaba,suka tashi tasu suka biyo bayansa.
Ya sadiqu da tunda yaga tsiyar da suke tsulawa sun manta ma dashi ya zare jikinsa ya yiwa kansa mazauni a bayan motar ya fidda wayarsa yaci gaba dayi,a hankali taji ya lalubo hannunta ya hade tafukan hannayensu waje daya,daya hanun kuma nakan sitiyarin motar,ya matse hannun gam cikin nasa,kana ya fara magana da tattausar muryarsa
"Kina tunani ko tsammanin akwai abinda yake da qarfi ko tasirin da zai iya rabani dake?,duk duniya babu shi,ban ganshi ba,idan ma kina ganin akwai kiyi gaggawar shafe wannan tunanin daga ranki" lumshe idanunta tayi ranta na sake yin sanyi,lallai taso tafka babbar hasara,yadda lameen yake na daban haka soyayyarsa take ta daban,tana tafe da wani irin sanyi da nutsuwa,bai sake mata magana ba amma yadda yake sarrafa hannunta cikin nashi dukka wani saqo da baki bai furta ba yana isa kai tsaye zuwa zuciyarta.
Wayarsa tayi ringing ,ya kalli wayar ya bawa iman din umarnin dagawa,don bayason cire hannunsa daga nata,ta daga ta saka handsfree
"Malam lamin,ka sauka daga hanya fa,akwai asibitin da zamuje wanda suka qware sosai wajen yin wannan test din...." Da ido yayi mata alamar ta kashe,saiya gangara gefan titi ya faka motar,ya kuma kasheta gaba daya.
Kashe wayar da sadiqu yakeyi yayi yana zare earpiece din kunnensa
"lafiya?,me ya samu motar?" Dukan sitiyarin motar lamin din yayi,fushinsa ya bayyana sosai,wanda hatta sadiqu ba iman ba basu taba ganin irinsa a fuskarsa ba
"Wai ni yaron mutanen nan ne?,kawai don na auri 'yarsu zasu dinga yin dukka yadda sukaga dama dani?,asibitin ma sai wanda suka zabarmana zamuje?"
"To sai me?, please kada ka bata ranka,minti nawane anyi an gama shikenan.....kaga,abinda za'ayi ku koma back seat ka bani driving din" haka kuwa akayi,suka koma bayan shida iman,abinda ya sake bashi damar sake kusanta kansa da ita kenan,cikin qirjinta ya kifa fuskarsa,kunya ta kamata,tanason ta tayashi sauke masa temper din daya dauka kamar yadda yaagaa ta koya mata amma kuma tana kunyar idanun ya sadiqun,duk da hankalinsa sam ba'a kansu yake ba.
Tsaiwar da sukayi ya sanya su samha suka rigasu isa asibitin,suna zuwa aka buqaci daukar jinin iman din,lamin ne ya rakata aka dauka a gabansa sannan suka dawo zaman jiran sakamako.
Ko sau daya lamin di n bai zauna ba,yanata kai kawo a area din da iman din take kamar mai bata tsaro,yayin da samha da tawagarta ke zaune daga gefe,baisan me suke tattaunawa ba amma hankalin samha a tashe yake,hakanan dukka hankalinta naga iman din,wadda suke zaune benci daya ita da ya sadiqu,yanata sako mata hirarki duka don ya dauke hankalinta daga tunane tunane.
Jira na wasu mintuna masu yawa kafin likitan da ya tafi gwajin ya dawo,dan gajere baqi,yaci farar labcoat,hannunsa sanye da safa irin ta likitoci
"Ku sameni a office" ya fada yana yin gaba cikin hanzari,dakatawa sukayi saida iyalan samha sukayi gaba sannan sukabi bayansu,kowa a zaune amma lamin na a tsaye,ya zubawa mutumin da aka kira da likita idanu yana nazarinsa,banda ma rainin hankali da wayo irin nasu duka manyan asibitocin gwamnati su rasa wanne asibiti zasu kawosu sai private?.
"Bayan sakamakon gwajin da mukayi ya bayyana cewa....." Sai ya danyi jim yana rarraba idanu ta cikin gilashin da lameen ya fahimci kamar ma yayi masa yawa,yanata saukowa yana turashi da hannu ne tun farkon ganinsa dashi sanda yake tsaye wata nurse na daukan jinin iman din,gyaran murya yayi sannan yaci gaba
"Jinin wadda muka dauka yana dauke da cutar cuta mai karya garkuwar jiki,wato HIV a taqaice" wani mugun samha da mamanta suka ja,wanda ya cika dakin,yayin da wani tashun hankali ya saukarwa iman,salatin dasu samha ke maimaitawa tare da maganganun dama sunsan za'a rina wai an saci zanin mahaukaciya ya sake ruda iman din.
Duk wannan rudun lamin din a nutsensa yake,shi ya kama iman ya zaunar da ita dai dai sanda samha ke fadin
"Daina tabata,saboda a yanzu aure ya haramta a tsakaninku" tsawar daya dakawa samhan ta haifar da wanzuwar shuru cikin dakin,ta kuma tafi da kowanne hayaniya data soma tashi,ya maida dubansa ga likitan da yayi dafafa saman kujerarsa yana qoqarin maida gilashinsa daya zamo sanadiyyar tsawar lamin din,sai ya miqa hannu ya dauki takardar dake gabansa wadda yake karantowa ta result din,ya cukuikuyeta ya cusa a aljihu,sannan ya waiwaya ga samha data miqe tsaye tana kallonsa.
"Yadda iman keda qanjamau nima itace dani,na boye miki ne saboda inason kema ki samu rabonki,amma tunda gaskiya ta bayyana,kije na sakeki saki biyu" salati suka dauka gaba dayansu,wannan karon harda mazan,tashin hankali wanda ba'a saka masa rana,tuni.mamar samha ta miqe kamar zata kife tana ambatar sunan lamin din,tama rasa me zata ce masa,bata taba tunani ko kawo abin zai juye haka ba,saidai bai saurari kiranta ba ya juya ga likitan
"Kai kuma,ka saurari kira daga kotu kan abinda ka aikata,ko dukka kudina zasu qare saina tabbatar an rufe asibitin nan" yana qarasa fadi ya damqi hannun iman,bai saurari dangin samha daketa kakkabi da fadin maganganu,ko ita samha data zube jikin mamanta tana rusa kuka ba,ko kuma sadiqu dake qoqarin dakatar dashi da nuna masa aikata babban laifi na rashin dacewar sakin samha,idanunsa jazur ya dubi sadiq
"Ta yaya masu cutar qanjamau zasu zauna da lafiyayya su shafa mata?na godewa Allah da banyi tarayya da ita ba bare na shafa mata kona zalunceta ba" daga haka yaja hannun iman suka fara fita daga office din,saidai tun kan yakai ga ida ficewa saiga likita a gabansa,yayi zaman 'yan bori,babu glass babu labcoat,duka sunyi nasu waje,ainihin kayan dake jikinsa suka bayyan,wanda wani wajenma a kode yake,ya fashe da kuka wurjajan
"Kayimin rai kayimin afuwa,wallahi wallahi indai abundanka fada zaka aikata dr dawood saiya daureni dauri na har abada,ka taimakeni kamar yadda Allah ya taimakeka,wannan aikin dashi nake ci nakesha nake kuma kula da mahaifiyata da bata da lafiya,nidin ba kowa bane face masinja,aikina aike aike da sharewa dr dawood wannan office din da kake gani,ina zaman zamana suka na nayi musu wannan aikin,wallahi ba halina bane" maganar dafa sandarar da duk wanda baisan shiryayyar da aka shirya ba,saidai lamin ya dake ya dubeshi
"Ai gwara aje kotun,kaga nan dawood din zai gane baragurbi irinku dake bata sunan asibitinsa" daga haka ya tsallakeshi yanata faman magiya da ban baki,suna zuwa ya budewa iman mota ta shiga,shima ya shiga,ya tayar da ita a zafafe ko sadiq bai tsaya jira ba ya fice abinsa da wani irin gudu dake nuna tafasar da zuciyarsa keyi.[7/19, 10:04 PM] Mummyn Yara: 71
Wani irin gudu yake,yayin da ita kuma ke kuka,gaba daya zuciyarta ta karye,duk da kuka take amma ta fuskanci ba hanya gida ya nufa da ita ba,hakanan ba hanyar gidansa ya nufa da ita ba.
Tana jinsa yana wayar cewa a rufe gidan,yaran kuma dake nan su tafi,tafiyar gaggawace ta sameshi,idan ya dawo zai nemesu,ya ajjiye wayar dai dai sanda sukakaraso qofar wani katafaren hotel,yana horn aka wangale masa babba gate din hotel din,ya gangara a hankali xuwa parking lot ya daidaita tsaiwar motar tasa sannan ya kasheta,maimakon ya fita a motar sai ya juyo gaba daya yana fuskantar iman wadda ke cure waje daya tana shesheqa,idanu ya zuba mata sosai yana dubanta duk da baya iya ganin fuskarta,qoqarin yake ya rage kaifin fushinsa kafin yayi magana da ita,tsahon mintuna sannan ya sauke qaqqarfar ajiyar zuciya,a tausashe ya kamo hannun iman din yakaishi saman qirjinsa saitin zuciyarsa,kana ya kwantar da kansa jikin kujerar,sosai take jin yadda zuciyarsa ke bugawa a tsakiyar tafin hannunta,koda baice komai ba tasan fushine sosai cikin ransa
"Iman......so kike zuciyata ta buga gaba daya?" Yayi maganar muryarsa can qasa yana dubanta
"Tun ba yau ba kinsan fushinki tarwatsa min nutsuwa yakeyi,bana qaunar sautin kukanki ko kadan......ya kamata zuwa yanzu kiyi shuru hakanan" a hankali ta daga kanta,idanunta a kansa,cikin muryar kuka ta fara magana
"Me yasa zaka aikata haka?,saki ya ameen a kwanakin da ko bakwai basu kai ba?,ya kake tsammanin ni zan dauka kenan?,wanne kallo kakeso duniya tayi mana musamman ni?" Ajiyar zuciya ya sauke,ya lunshe idanunsa yana budesu duka lokaci guda ya zubesu a kanta
"Iman.....ta zagi malam da inna....ta kirasu mayaudara maha'inta macuta.....ta fadi munanan kalmomi a kansu ba tare da tasan kunnuwana duka sun jiyemin ba lokacin da nake zirga zirga kuna zaune ke da sadiq,zuciyata ba zata iya jurar zama da duk wadda ta tabasu ko ta zagesu ba,bata taba zaton naji ba,Duk wanda ya zagi inna ko malam......kamar ya zagi wadanda suka kawoni duniya ne,su suka raineni har na zama mutum data kalla tace tana so,tana kuma muradin aurensa,koda iyayena sun kawoni duniya ne.....amma inna da malam sune sukayi raising dina up har na kawo matakin da nake kai a yanzu,bazan iya yiwa duk wanda ya nema wulaqantasu uzuri ba....koda haka bata kasance ba dama babu lallai na iya zama da samha,ba yabon kaina nake ba.....amma ni mutum ne da baya qaunar qarya ha'inci da kuma yaudara,dukka samha ta hada wadan nan,tunda ta iya shirya wannan ita da mahaifiyarta.....me kike tunanin zai faru nan gaba?kina zaton za samu nutsuwa da kwanciyar hankali a rayuwata da ita?,meye abun sha'awa ko jan hankalin bata dama ta zama uwar 'ya'yan da zasu fito ta tsatsona,na musu adalci ida na bari ta zama uwa a garesu?" Ya qarashe maganar yana zuba mata idanu,tabbas maganganunsa akan hanya suke,saidai ga tabbatar basu da wata mafita ko excuse da zasu bawa malam,dukkansu zasu tashi a matsayin masu laifi ne
"Nasan abinda kike gudu ko kuma tunani,kada ki damu da mutanen duniya,ba zaki taba gamsar dasu akan kowanne abu da zaka aikata ba,kaidai ka damu da aikata dai dai da kuma abinda mutanen qwarai zasu yaba dashi,komai zaizo ya wuce kamar bai faru ba,malam kuma nasan yadda zanyi da batunsa,kin gamsu?" Kai ta gyada masa a hankali,sai ya sakar mata murmushi yana saje matsowa kusa da ita
"Komai ya wuce?" Kai ta sake gyada masa
"Oya.... give me a kiss" daga kanta tayi da sauri cikin yanayi na kunya ta dubeshi,saiya dage mata girarsa yana sakar mata murmushi
"Eh,ko kiyimin koni nayi miki,amma nawa zai zama deeper than yours......don haka ki zaba" ta tabbatar da gaske yake,kuma daga yanayin kallon da yake mata ta tabbatar idan ya fara zataji a jikinta,saita kauda kanta
"Ya lameen...."
"Noooo.....wannan ba yayanki bane,mijinki ne"
"Kunya fa....."
"Ban santa ba.....bafa takura,the choice is yours.....ki bani dama kiga yadda zata kasance" sai ya fara qoqarin sake matsowa,abinda ya sata ta waiwayo da sauri da nufin yi masa abinda ga buqata din,saidai ya goce bata sameshi ba,sannan ya fara nuna mata bakinsa
"Right here nakesonshi" idanu ta fidda,saita runtse idanunta
"Let me help you" kafin ta gama tantance abinda zai fada din tuni ya riqe fuskarta tsakanin tafin hannunta,kamar yadda ta fada mata dinne kuwa, kisses ya bata masu dogon zango da kuma tsananin zafi,wanda da qyar ta samu ya saketa,kowa ya koma da baya yana maida numfashi,sai daya daidaita nutsuwarsa sannan ya miqa mata hannunsa
"Wayarki please"batayi musu ba ta miqa masa wayar,tana kallonshi ya bude wayar,ya cire layinta ya karya gida biyu ya watsa ta window,ya daga sexy eyes dinsa ya kalleta
"Am sorry......bana buqatar kowa ya nememu ne a yanzun haka,zan musanya miki da wani layin,xan kuma saka miki number duk wanda kike da buqata" kai ta gyada masa kawai,don a yanzu bata da wani abu da yayi saura face bin umarninsa da kuma yin duk yadda yakeso,hannunsa yasa ya zaro tashi wayar,ya laluba wata number yakira.
Batasan wa ya kira ba,amma taji yana maganar flight from kano to Lagos,ya buqaci a yanka masa ticket guda biyu.
Yana gama wayar ya kasheta gaba daya shima,sannan ya fita ya zagaya ya bude mata seat dinta kamar yadda ya saba ta fito,ya kulle motar suka taka zuwa ciki.
Batasan lokacin da ya karba musu daki ba,tunda suna zuwa key kawai ya karba na dakin,tana gaba yana take mata baya,kamar sarauniya da yaran gidanta,yadda yake matan kawai yana sanyawa taji kanta ya kumbura da yawa,wata kulawace da bata saba ganin irinta ba,kulawa ta musamman mai tsayawa a rai,wadda ke ratsa jiki da bargon masoyi.
Suna shiga abinci ya iskosu da wata leda ta daban da batasan meye a ciki ba,sallah suka fara yi saboda quracewar lokacin azahar din,sanna suka zauna zaman cin abincin,wanda cikin plate daya ya zuba musu,suka kuma yi sharing one spoon kamar yadda ya fara koya mata tun daga sanda suka zama ma'aurata.
"Uku ta kusa,jirgin qarfe hudu kuma zamu bi zuwa lagos,kiyi wanka ki shirya,akwai kaya cikin ledar can ki zaba ki saka kafin na dawo" bayanin nasa yazo mata a bazata,idanunsa yana kanta har ya ja qofar,abunda ya zama shamaki tsakaninsa da ita kenan.
Yana fita din ta shiga toilet ta soma shiryawa kamar yadda ya umarceta,duk motsinta ba abinda ke yawo a ranta sai abunda ya auku yau,komai tana ganinsa kamar a mafarki,addu'a ba wasa bace,hakanan duk wanda ya riqe Allah....yakuma yi abu ko ya bar abu saboda girman zatin Allah to ba shakka Allah bazai wofantar dashi ba,kalaman inna suka dawo mata,ta fadi gaskiya,duk da itama bata taba kawo lameen din zai aikata danyen aiki irin wannan ba,shiri tayi sosai,ta tadda komai cikin ledar,kana ta fidda wani dinkakken lace na alfarma,wanda koda idanu ka kalleshi kasan yaci kudinsa,akwai takarda a maqale a jiki wadda ke dauke da tambarin kamfanin IB COUTURE,kenan dinkakke ne daga masarrafar suttura ta lameen din.
Ta tabbatarwa kanta shi ya zabar mata kayan,saboda yadda yayi mata cif a jikinta,dinkin kuma ya zauna mata matuqa,kamar don saboda ita aka qirqiri kayan,turare ta fesa baya ta daura dankwalinta daya zauna mata das da salon dauri zamani na gaban goshi,wanda haka ya qarawa kwalliyar tata armashi.
Tana gamawa yana shigowa janye da qaramar jakar matafiya mai azabar kyau,idanunsa a kanta,tayi masa kyau fiye da yadda ya zata,ya kasa dauke idanunsa daga kanta har ya qaraso dakin bakinsa dauke da sallama can qasan maqoshinsa.
Bata ankara ba har ya cimmata,saiji tayi ya dagata sama cak ya dire saman madubin,ya kuma zagaye qugunta da hannayensa yana kallon cikin idanunta da wani narkakken kallo mai cike da soyayya,cikin wani low tune yace
"Fatabarakallahu ahasanul khaliqin,ma sha Allah,ma sha Allah,tsarki ya tabbata ga sarkin da ya tsaga wanna halittar..... queen,kinyi kyau kinyi kyau fiye da yadda zan fada miki.....inason wanna kwalliyar queen.....inason kici gaba da kasancewa a haka" a kunyace ta amsa masa
"Consider it done sir" da sassanyar muryarta,murmushi ya kubce musu duka su biyu,yaja da baya yana cewa
"Tsaf zamu iya rasa jirgi idan naci gaba da kallonki" sai ya taka da baya da baya a hankali
"Banason nayi missing kallon fuskarki kona second ne....ki jirani" ya fadi yana juyawa da sauri ya fada toilet din,yabar iman daskare a wajen cike da shauqi,qirjinta cike da soyayyar lameen din,zuciyarta ta cika da hamadala ga ubangiji da bai haramta mata ni'imar samunsa a matsayin miji ba.
Duk da yadda take tajin kunya tana doddojewa tun daga fitowarsa daga wanka shiryawarsa zuwa ficewarsu filin jirgi bai damu da wannan ba,yana maqale da ita yana karanta mata wani karatu na musamman,karatun da shi daya ya sanshi,ya kuma gama tsarashi a kwanyarsa da zummar zai dora rayuwar auratayyarsa akai,yanason ya morewa rayuwarsa qwarai da matarsa ta sunna,irin rayuwar da zata kasance abar sha'awa da kwatance ga dukka ma'auratan da suka sansu.
"Wannan sissinqewar da kikeyi baby ba inda zata kaiki.....inda xamuje sabon shafin rayuwa zamu bude,inda bau takura ko matsi,zamu tafi inda babu wanda ya sanmu bare mu samu naqasu" ajiyar zuciya ta sauke,da gaske dai lamin yake,ta gaji da yadda yake sanyata jin kunya,idanun mutane nata kaiwa kansu,don tun a daki kafin su fito sanda ya rungumeta ta baya a gaban madubi bayan ya gama shiryawa ya musu hoto ita kanta ta tabbatar duk wanda ya kallesu sai ya sake dubansu,sabida wani iri match da bata taba kula dashi ba taga sunyi,uwa uba dressing dinsu,tun kafin ma subar hotel din receptionist din dake wajen ta soma fada musu,yare ce,hakanan tana da barkwanci da haba haba da jama'a.
Kafin su tashi taga ya kunna wayarsa ya turawa sadiqu texs,tasan kuma bazai wuce shaida masa ya gayawa su malam sun wuce ba tare da neman afuwa da addu'ar su malam ba,itama hakan ya qara kwantar mata da hankali,tasan at least hankalinsu zai kwanta tunda a qalla sunsan suna lafiya kuma ga garin da suke.
_sai muce a sauka lafiya LAMIM_
[7/19, 10:04 PM] Mummyn Yara: "

Menu
Dashboard
My Library
Create Story
Home
About us
FAQ's
Privacy Policy
Terms of service
Logout

KUFAN WUTA