Chapter 62
Kufan Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 39 min read
Shafi na sittin da daya
61
*****"To yadda shirye shirye ke kankama hakanan gadan gadan cikin gidan kawai ya isa gaya maka cewa gagarumin biki aka tarka,yadda suketa shirye shiryensu hakanan iman ke sabgarta,ganin komai take kamar bazai faru ba,kamar lokacin bazaizo ba,musamman da ya zaman yanzu ba waya suke da dr ahmad ba,saidai suyu exchanging tex massage ta sabuwan number dinsa,sai takejin komai kamar ba wani me muhimmanci ba.
Shaf tama manta saura kwanaki goma biki saida yaagana ta iso,a ranar ma tadawo daga makaranta kenan ta samu yaagana a parlor har ta watstsake gajiyarta
"Ke kuma daga ina kike?" Ta watso mata tambayar tana mata wani duba na sama da qasa,da mamaki a fuskarta ta kalli yaganan
"Makaranta mana yaagana"
"Hodijam" ta fada tana kama baki
"Ke a yawon boko zaki qare?,to daga yau koki sanar musu su baki hutu,koma kada ki shaida musu keda fita makaranta sai bayan biki,gyaran jiki alhmdlh gashi yayi kyau a ido amma kina maida ma mata aikinta baya?" Mamaki yacikata,ta koma ta zauna kawai tana sauraren ikon Allah,wai duka meye haka ake mata wani titsiye ne?,jiya jiya suka gama da bushira kan lefe,don tace ma dr a barsu sai ran daurin aure a kawo bushiran kamar ta cinyeta danya,yanzu kuma ga yaagana da nata tarin damuwar,sam itafa ba zata dauka ba.
Batasan da gaske yaganan take ba sai washegari data shirya zata fita makaranta,da sallama ta ratso ta parlor din,kamar kowanne lokaci matuqar yana a waje shi idanunta ke fara hasko mata,yana zaune qasan carpet ya tanqwashe dukka qafafunsa a gaban yaagana,yana sanye da wata jallabiyya ta maza mai gajeran hannu da wuta me dan fadi ba turtle neck da aka saba gani ba,kalarta ruwan hanta da yayi masifar haskashi,duk da safiya ce amma qamshinsa ya cika wajen.
A nutse ta qaraso,ta dan rusuna daf da yaaganan tana gaidata,ta amsa tana qare mata kallo,kallon da iman batason taga tanayi mata shi,saboda tasan indai taga irin hakan akwai magana bakin yaaganan
"Barka da asuba" ta furta a hankali tana gyara zamanta,sai a sannan ya daga kansa daga danne dannen da yake a waya,kallo daya yayi mata ya sauke kansa,kamar ma baisan da wanzuwarta a wajen ba,ya amsa mata da wata irin shariya data sanya ta sake kame kanta da kyau,gaba daya ta dauke kanta daga sashensa tana duban yaagana dake mata magana
"Wannan safkon fa?"
"Makaranta" wani duba yaagana tayi mata
"Au ashe jiya baki riqe abinda na gaya miki ba kenan?.....to nabi makarantar da gudu na tattaketa na kuma bubbugeta da sanda" a hankali ya maida wayarsa aljihu yana miqewa
"Inason fita yaagana.....zuwa yammaci amma zan dawo" ya fadi mata da tattausan muryarsa dake cike da nutsuwa da kuma kamun kai
"To ba laifi" daga haka ya taka a nutsensa ya fita a parlor din,abunda ya bawa yaagana maida hankalinta kan iman,ta inda take shiga ba ta nan take fita ba,tun iman na daukan abun da wasa har sai da ta sakewa yaagana kuka,wai me yasa babu wanda ya damu da damuwarta ne?,ko yaushe kawai sake jefata kawai suke cikin damuwa da kuma nuna halin ko in kula a kanta.
A hankali inna ta koma da baya,ta saki labulen tana sakin murmushi ba tare da wani cikin iman ko yaagana ya ganta ba,abinda take shirin yiwa iman din kenan yau yaagana ta aiwatar,ta tabbatar rashin dangin uwa ko na uba a kusa ne yasa wasu abubuwan da yawa suke faruwa,ita din tun asalinta me kara ce da alkunya,musamman akan 'ya'ya,sau tari tanason musu magana ire iren wadan nan abubuwan amma sai taga kamar rashin kunya ne,har yau har gobe akwai kunya tsakaninta da malam,shi yasa wani lokaci shike karbe ragamar fadan.
Luf inna tayi cikin dakinta kamar bata gidan,mufida ko dama bata tashi ba tana fa barcinta,sosai yaagana taci qaniyar iman,sannan ta sanyata ta dauko mata jakarta,ta dinga fidda rabobi masu dauke da magunguna,tsumammu na asalin kanuri,ba bata lokaci ta fara hada mata tana bata tana sha,duk da tasan cewa iman din babu wani abu data rasa na game da budurci,amma hausawa na cewa idan kana da kyau sai kuma ka qara da wanka,ita kadai tasan kudin data kashe wajen hado magungunan,saboda bana wasa bane,ko a can ba kowacce mace ke iya siyanshi ba.
Tun iman na kuka da hawaye har ta koma na zuci,saboda iya ranar magungunan da yaagana ta dirka mata kadai sun sanya ta saddaqar ta kuma tabbatar auren fa da gaske ne yazo,zuwa washegari kuwa tuni suka fara bin jikinta sosai yadda yaganan keso,ita kanta ta shaida haka,kawai saita saka kuka,lokacin bushira na dakin tana duba dinkuna iman din da aka kawo.
Da farko tsoro bushiran taji
"Tsakani da Allah wannan fa daukan haqqine,pants nawa na canza iya yau,haka kawai an maidaka kamar wata karuwa,wallahi ko ta sake bani zubdasu zanyi" dariya sosai Bushra ta saki
"To wallahi kin tona kanki,zan gayawa yagana kada ta bari ki matsa daga inda take saikin shanye koma menene,ina cewa gata akayi miki,shi dr ahmad din so kike ya rainamu?" Harara me zafi ta watsawa bushira,tana ganin ma kamar bata bakine ta tsaya ci gaba da magana da ita,kawai saita kewayeta ta fita a toilet din,yayin da bushiran ta rakata da dariya tana cewa
"Kamar wata baqauya wallahi,idan aka cewa wani nurse kike shirin zama qaryatawa zaiyi" itadai iman ta fice waje abinta,ranta fal qunci bacin rai da kuma jin haushin kowa ma.
**********Tun saura kwanaki shida a fara bikin gidan ya fara karbar baqi,dangi na kusa kusa da inna dana malam din gaba daya,abinda ya sake takura iman kenan tare da sake sanyayar mata da jiki,ta kuma tabbatar lallai da gaske auren nata za'ayi.
Yau tun safe take ta shiri,akwai guraren da bushira ta matsa mata zasuje,karbo dinkunanta da kuma siyayya da bushiran tace zatayi cikin kasuwa,batasan dai me zata siyo ba,amma yawan kudaden da ta bata ajiya ya bata mamaki,daga nan zasuje amaryar kb yau zata fara mata wani gyaran jiki na musamman da ake cikin satin da za'a fara biki,duka ba wannan ne a gabanta ba,tana so ta shiga makaranta tayi settling komai na kwanakin da bazata samu shiga ba.
Comb din da take taje dogon gashinta ta ajjiye sanda wayarta tayi ringing,tasa hannu ta dauka tana duba me kiran nata,wata abokiyar karatunta ce da suke mutunci sosai,duk da cewa ta girmeta,don matar aure ce yaranta biyu,saidai tasu tazo daya sosai da iman din saboda nutsuwar matar.
Gaisawa suka farayi da ita sai ta fara yiwa iman din qorafi
"Yanzu duk yadda muke hajar sai da biki ya rage saura sati daya zamu sani?,kuma har kizo ki dauki excuse ma ba wanda ya sani?" Mamaki ya kama iman sosai,tama rasa abun cewa
"Amma mun baki uzuri ai,tunda a qurarren lokaci komai yazo,Allah ya sanya alkhairi,ranar yaushe ne waliman?" Ajiyar zuciya ta sauke a boye tunda ta samu mafita,batasan ranae yaushe zatace mata ba,saboda ita kanta batasan yadda komai ke wakana ba,bushira ce uwa kuma makarbiya ta komai
"Ran juma'a,amma kiyi haquri maman sauda,zan sake kiranki,ayimin afuwa"
"Babu komai" daga haka sukayi sallama da ita ta sauke wayar,mamaki fal zuciyarta,komai nata a sakwarkwace,banda tallafawar bushira ta tabbatar babu abinda zai yiwu,idama ya yiwun to zaizo ne a mugun baude.
Amma kuma wa ya shiga makaranta ya daukar mata excuse?,waye ya sanar musu da auren nata?,tunda dai ita tasan babu wanda ta gayawa,bushira itace amsar data zo ranta,saita girgiza kai kawai,ta wani fannin bushira na sake samun kima da daraja a ranta.
Har zata ajjiye wayar sai wani abu yaja hankalinta,ta sauke daukar wayar tana lalubar number dr ahamd,ba zata iya tuna rabon da suyi waya dashi ba,saidai musayar text lokaci lokaci.
Kamar ko yaushe yauma data kira dai qin shiga tayi,ita ba'a kashe ba kuma ita bata shiga ba,mamaki ya kamata ta sauke wayar tana kallon number,dai dai sanda bushira ta shigo dakin,abinda ya dauke hankalinta kenan bata kuma bi ta kan wayar ba,har suka fice daga gidan.
Cikin damuwa iman ke kallon bushira
"Na rasa wanne irin zumudi akewa bikin nan,ina tunanin fa ki gyaramin wajen kwanciya,don bazan iya ci gaba da zama cikin gidan nan ba"
"Bismillah,ina miki maraba,amma dai biki kam bakiga komai ba,bikin mutum uku fa za'ayi" harara ta watsa mata
"Duk jirgi daya ya deboku daman,ke kika kaiwa 'yan class dinmu gayyata ko?,kika kuma settling abubuwan da zan shiga yau nayi"
"Abun kuma harda sharri saboda an tsaneni?,nakai musu card tabbas,saboda akwai qawata a cikinsu,so bazan bata ita kadai na tsallakesu ba tunda nasan kuna mutunci,amma duka sauran abunda kika fada bansan anyi ba" tasan bushiran,qarya ba halayyarta bace,tunda ta fada hakanne,to amma waye?,ko dr ahmad ne?,amma kuma bushira kadai tasan zata shiga yau makaranta,ko inna bata gayawa ba saboda yaa gana.
Kusan wuni sukayi a waje kafin su gama komai,abu daya ne ya tsaidasu neman wani turare,ba inda basu duba ba babu,qarshe a wani store akace zasu samu,iman tayi mitar tayi mitar kan a abarshi su wuce gida saboda gajiyar datayi,tace ta yafe tunda dai ita zaa nemowa shi amma bushira ta kafe
"Kinsan Allah tunda har angonki nason qamshinsa saina nemoshi ko qarfe dayan dare zamukai"
"Yaushe kukayi doguwar magana da dr da har zakisan haka?"
"Oho miki" ta fada tana shiga napep,dole itama ta bita tana ta mita amma bushiran tayi banza da ita.
K'in shiga ciki iman din tayi,tace tana daga bakin qofa,ta shiga ta fito,ta samu daya daga cikin kujerun dake wajen ta zauna,ta fidda wayarta tanata replying saqonnin fatan alkhairi da abokan karatunta ke mata.
Bata jima ba sai gata ta fito,ta fidda turaren ta fesawa iman din tana cewa
"Don Allah jimin qamshinsa" Idanunta ta lumshe,sosai qamshin yayi mata,zata iya cewa wannan shine qamshi na biyu data taba ji me dadi da kwantar da zuciya
"Hajaratul iman ibrahim khalil" sunan da aka kirata dashi kenan,wanda ya sanyata bude idanunta dake lumshe da gaggawa tana duban sashen da sautin kiran sunan nata ya fito.
End of book

Leave a comment

Post
Comments
No Comments posted yet

Contact Us
Arewa Books Publishers
WhatsApp: 09031774742
Email: [email protected]
Navigation
Home
About
FAQ's
Legal
Privacy Policy
Terms of Service
Social
Facebook
Instagram

Copyright 2021, Arewa Books | ALL RIGHTS RESERVED | Powered by thinkcrypt.io
"
https://arewabooks.com/chapter?id=62cecd8e0ba46f15b711502c#:~:text=Chapter%2062,nata%20ya%20fito.
[7/19, 10:03 PM] Mummyn Yara: "Chapter 63
Shafi na sittin da biyu
Afuwa dai,ayi haquri dani,anata samun mistake,al'amuranne sai a hankali,sabgogi sunyi yawa
62
Sauka idanuwanta sukayi aka muneera,itama nata idanun nakan iman din,tana kowa inda take cikin fara'a da walwala,tsam iman din ta miqe,ta dauki jakarta tana saqalata a kafadarta,har yanzu idanunta nakan muneera,a duk sanda taga muneeran sai wasu abubuwa da suka shude marasa dadi sun dinga dawo mata,wannan na daya daga cikin abubuwan da ya sanya bata qaunar ganin muneera ko kadan
"Anya duniya da amana kuwa?,kin bacemin bat iman?" Muneera ta fada tana qare mata kallo sanda ta iso inda take tsaye,murmushi ta qaqalo wanda baije ko ina ba,tana duban muneeran
"Dama rayuwa ai ta gaji haka muneera,wataran za'a hadu kamar yadda dole wataran arabu" kai ta jinjina
"Gaskiya ne" ta furta tana qarewa iman din kallo
"Kinga yadda kika canza iman?,kin zama wata big madam,meke faruwa ne?,wannan gayun da kyan ya zarta wanda na sani a baya"
"Ke bakiga yadda kika koma ba?" Itama iman din ta fada tana dubanta da murmushin yaqe,da gasken take muneera ta canza,shekaru ba wasa bane,sun jima ita da ita basu hadu ba,ba zata iya tuna yaushe rabon data sanya muneeran a idonta
"Bansan me nayi miki kika tsaneni ba iman,bayan duk abinda nayi nayi ne da niyyar alkhairi,naje gidanku na tarar kun tashi,ance an qera muku gida,saidai ba address babu phone number" kai iman din ta girgiza tana jin qosawa sa tsaiwar
"Bakimin komai ba,kawai Alla ne ya kaw lokacin rabuwarmu,idan babu damuwa zan wuce don Allah ana jirana"
"Ba damuwa,ki bani address ko number waya,inason na sameki a gida muyi magana,aurena ya kusa,kuma ya kamata ace kedin kinje....amma idan bazaki damu ba,ga invitation din,a jiki akwai number wayata,idan kin kirani nayi saving "a gaggauce iman din ta karba katin,ba tare data tsaya dubawa ta cusa a jakarta,tayiwa muneeran sallama suka wuce.
A napep bushira ke tambayar iman din wace wannan,kai tsaye ta gaya mata muneera ce,saboda basu taba haduwa ba,bata santa a fuska ba,tunda suka dauki hanya iman din bata tanka komai ba,sai ta samu kanta da tuna rayuwarta ta baya,daki daki,guraben da tayi kuskure da a lokacin take kallonsa ba'a matsayin kuskure ba suna fito mata daya bayan daya,kafin su isa gida zuciyarya da qirjinta sun mata wani irin nauyi,suka hade da gajiyar da suka kwaso,don haka suna sallama da bushira dakinta ta kulle,ta watsa ruwa ta samu waje ta kwanta tana qoqarin calming down kanta.
*_Biki Bidiri_*
A hankali ta lumshe idanunta tana jin yadda kanta yake sara mata gefe guda,wani irin ciwon kai ne da tun a jiya take fama da shi,rashin isashen barci,hayaniyar gidansu gami da fargaba ne duka suka taru suke hade mata.
Hannunta ta saka ta shafi fuskarta dasu,rangadeden lallen da aka bata wasu awanni ana zana shi ya bayyana tarwai saman farar fatarta data tsumu da gyara ta kuma karbi gyaran yadda ya kamata,duba daya zaka yiwa lallen kasan lallai sunzo qarshen inda akasan ma'anar qunshi da gasken gaske.
"Bushira.....i have to go......na gaji" bushira da ake zanawa nata lallen tace
"Ba zaki iya tafiya ba ke kadai iman,ki qaran minti biyar yanzu za'a zo a daukeki don Allah,ki daure kisha magani kafin jibi ki warware,amarya da jinya ai ba kanta" ta qarashe maganar tana tsokanarta,murmushin da yafi kama da yaqe tayi mata kawai ta kifa fuskarta saman cinyoyinta,ita kadai tasan abinda takeji,wani abune cure a qijrinta,inda kuka zaizo mata data fi kowa jin dadi,amma babu shi babu alamarsa,sai dunqulallen qunci da ya barwa jikinta.
"Yauwa,muje iman na rakaki ki wuce gida,idan maryam ta dawo aka mata nata lallen ma taho tare,tunda tace na jirata kinga babu dadi na tafi na barta" bushira ta fada tana miqewa,sai ta daga kanta a hankali sannan ta miqe,ba tare data ce koma ba ta janyo mayafinta dake samun kujerar dake wajen ta yafashi saman kanta dake cike da sassalkan gashin da yasha gyara,babu abinda yake fitarwa sai wani irin qamshi ke tafiyar da zuciya,cikin set na kayan gyaran amaryar kb global enterprises.
A hannu ta riqe dankwalinta hade da wayarta,me qunshin na mata sannu bushira biye da ita suka fito.
A hankali take takawa,sam hankalinta baikai wajen ba sai da suka tsaya gaban motar,hannun bushira dake dauke da danyen lalle ta saka cikin dabara ta bude mata seat din gaba,qamshi da ya bugi hancinta gauraye da sanyin acn ya ankarar da ita motar waye,cikin mamaki idanunta fal tarin tambayoyi ta kalli bushira,tafinkowa sanin yanayi da kuma halin da zuciyarta ke ciki,me yasa zatayi mata haka?,qasa qasa tace da ita
"Karki zargeni,na rasa wanda zan kirane wallahi,kinsan saurayina baida mota bare na kirashi,kona kira ma bai kamata nabar matar mutane ta shiga motar wani ba,sai akayi dace ina kiran yaa ameen din yana kusa da nan" ta yarsa da bushira,kuma tana iya bakin qoqarinta,bai kamata kuma ga gwale qoqarin nata ba,zamane na mintuna sun isa gida ita dashi kowa ya kama gabansa,saita dauke idaunta ta shiga motar cikin sanyi,bushira ta maida murfin ga rufe,sannan ta juya zuwa cikin wajen,daidai lokacin da ya fara tada motar.
Tana jin sanda motar ta fara hawa kwalta,idanunta a runtse tana sauraren bugun zuciyarta da take dokawa da wani irin qarfi,so take tayi controlling kanta kafin ta buda baki ta gaidashi,saidai sunata kokawa da zuciyarta,ita a karan kanta bata da muradin kallonsa amma zuciyarta na qarfafa mata gwiwar aikata hakan,ba zata iya tuna kwanakin data diba bata sashi a idanunta ba,daga qarshe tadan juya kadan ta dubeshin,duban da bai wuce na Sakan biyar ba,amma ya bar mata miki me tarin yawa cikin zuciyarta,wani kyau daya sanya zuciyarta bugawa taga yayi,askinsa na musamman dake qara qawata masa fuska yayi,an rage sumar kansa,bata kai yadda ta saba ganinta yawa ba,gashin dake fuskarsa kuwa,wani gyara akayi masa na musamman.
"Ina yini" ta furta tana rufe idanunta
"Lafiya lau" ya amsa mata a taqaice ba tare daya juyo ba,yana jin yadda shima tashi bugun zuciyar ke canzawa,turaren ta ke fushar hankalinsa,wani mayen qamshi da baisan a inda ta sameshi ba,saita maida kanta saman qafafunta kawai,can qasan zuciyarta tana ambatar sunan Allah.
Idanunta na a rufen taji yana gangarawa gefan titi,sannan yayi parking
"One minute please" ya fada da muryarsa data qara wani irin taushi,tamkar wanda ke jin barci,ya buda motar a tausashe ya fita,abinda ya bata damar bude idanunwan nata a hankali,ta zuba masa idanu ta cikin gilashin motar,ta tabbatar bazai iya ganinta ba,yana takawa da wani irin taku cikin ginshira da kamala,ta dade da sanin cewa an canza ya ameen tun da dadewa,komai nasa ba irin wanda ta sani bane,bata janye idanunta ba har sai daya shige katafaren ginin IB COUTURE da yake mallakarsa,wajen da yayi wata irin shahara taban mamaki cikin lokaci qalilan,yake kuma samar masa da kudaden dashi kansa bai aza samunsu anan kusa ba.
Idanunta ta janye,tana sauke ajiyar zuciya,dukka gaba daya yau ya fama mata wani tafkeken tabo da kuma miki da take qoqarin rage radadinsa zuwa matakin waraka kar ta shiga gidan wani dashi,sanda take qoqarin janye idanun nata.....a daidai nan suka sauka kan wasu katina dake kife kusa da gear na motar,ta zubawa bayan baqaqen katinan da aka yiwa kwalliya da gold idanu,zuciyarta bugawa das das das haka nan ba tare data san dalili ba,a hankali ta miqa hannuwanta ta daga daya daga cikin katinan.......cikin sakanin da basu gaza hudu ba ta karanto abinda yabi ragowar kuzari da kuma walwalarta yayi rugu rugu dashi a take,yasa taji kamar kujerar da take kai ba zata iya daukarta ba,dukka wani qunci fargaba da damuwa data nannade ta wurgasu bayan zuciyarta suka dawo fil,a hankali ta runtse idanunta tana qoqarin maida katin cikin 'yan uwansa,nadama da dana sanin daga katin na saukar mata,sunan SAMHA da MUHAMMAD AMEEN dake rubuce jikin katin na wulgawa ta cikin duhun idanunta.
Sake bude idanunta tayi tana fatar daina ganin sunayen da suka kasa bace mata,saidai tana budesu basu sauka ako ina ba sai akan fuskarsa,yana takowa zuwa bakin motar,shi da wasu ma'aikata dake sanye da rigar dake dauke da suna da tambarin kamfanin a gaba da bayanta,tsura masa idanu tayi tana tuhumar zuciyarta,shin meye dashi ne haka da zuciyarta takasa masa a dalcin tsige duk wata soyayyarsa datayi saura ta wurgar da ita ta huta?,me ya mallaka daya banbamta da tarin masoyan dake karakaina a kanta?,kudi?,Kyau?,ko dukiya?,akwai wasu da dama cikin masoyanta da suka zarta lamin din,amma me yasa lallai lallai saishi?,me yasa?. Tajefawa kanta tambayar tana maida idanunta ta kulle sanda taga ya sallami ma'aikatan yana tunkaro motar,kanta na sake tsananta ciwo.
Tanajin sanda ya buda murfin motar ya shigo,yayi bismillah sanda yake zama,yana shirin tada motar muryar wani ma'aikaci ta riskesu
"Yallabai,dukka kayanka fa sun kammala"
"Harda gugar?"
"Eh harda ita,amma guda talatin ne suka samu,sauran biyar din suna hannun inusa,amma yace yau zai kammala su"
"Okay,ka bawa lawan kace idan kun tashi a company yakaimin gida"
"To yallabai,a sauka lafiya" ya fadi yana ja da baya,shi kuma ya tada motar suka wuce.
Wayoyinsa yaketa amsawa sanda suke tafiyar,wanda dukkansu kusan sun danganci dauren auren da zaa gabatar jibi,tayi Allah wadai da ganin baiken kanta na shiga motarsa yafi sau dubu,ta tabbata da ita din tana da fiffike da tuni ta jima da sulalewa daga motar takai kanta gida,saidai ba wannan damar,haka ta haqura tana Allah Allah sukai gida,sam gani take ma tuqin baya sauri,kamar wanda babu laka a jikinsa.
"Me yake damunki?" Taji ya jefa mata tambayar sanda suka gangarowa cikin layinsu,cikin mamaki tayi shuru tana maimaita tambayar cikin kanta ba tare data bude idanunta ba
"Babu komai" itace amsar data zabi ta bashi,bai sake cewa komai ba kamar yadda itama bata sake koda motsi ba,har zuwa sanda suka qaraso qofar gidan,ya kashe motar yana kallon qofar gidan nasu wanda ke a bude da dan tashin maganganun mutane daga ciki.
"Wait" ya fadi sanda ta sanya hannu tana yunqurin bude qofar ta fice,wayarsa ya cire daga charge,ya laluba wata number ya kira
"Fito,ina qofar gida" yafada a taqaice yana cire wayar daga kunnensa,baa cika mintu guda ba gate din ya bude,badi'a ta fito,ta qaraso bakin window dinsa cikin fara'a tana masa sannu da zuwa
"Ki rakata daki,ki tabbatar tasha magani" ya bata umarni kai tsaye,sai a sannan ta kula da iman,ta zagayo fuskarta cike fal da damuwa tana mata sannu,murmushi tayi qoqarin sakar mata ganin yadda duk ta damu
"Karki damu,dan qaramin ciwon kaine,ina hutawa zai warware" ta fada tana fita a motar cikin bawa kanta qwarin gwiwa.
Ajiyar zuciya ya sauke mai qarfi sanda suka shige gidan,baisan me yasa ya tsaya kallonsu ba.....baisan me yasa yakejin damuwa ba,baisan me yasa yakejin farga ba,duka ya rasa dalilin hakan,bashi da wani cikakken qwarin gwiwa,wayarsa data dauki qara yasa ya maida kansa gareta,ya daga da sauri ya maqala a kunne yana fadin
"Am on my way sorry bello" ajjiye wayar yayi yadan qara mata speed,sam ya mance yabar baqinsa suna jiransa zai daukosu.
Koda suka shiga gidan gani tayi kamar baqin ma qara daduwa sukayi,bata da walwala ko qwarin gwiwar fuskantarsu,hakan ya sanya ta kama hannun badi'a suka wuce dakinta kai tsaye
"Kijamin qofa idan kin fita,zan sha magani na kwanta,duk wanda zai bugan qofa ko kikaga yana nemana kice barci nake"
"To yaa iman,Allah ya sawwaqe,kisha maganin don Allah,don nasan idan kawu ya dawo saiya tambayeni kinsha" kai ta gyada mata cikin dauriya tana sakin mata murmushi,saidai cikin ranta tana fadin,ba kawunki nada da kika sani bane,a yanzun bata iman yake ba,duk wata kulawa da zaki gani fake ce,yana yinta ne kawai saboda inna da malam,yana musu kaara ne.
Bayan badi'a tabi ta murzawa qofar key,sannan ta jingina da qofar,a hankali sai abinda ya tsaya mata a wuya tun ganin katinan da tayi ya soma narkewa izuwa wani kuka mai nauyi da cin zukata,dukka jikinta ya fara shaking hawayen suka cika idanunta suka fara gudu saman fuskarta,sai tsaiwar ta gagareta,ta sulale a hankali zuwa qasa tana qanqame jikinga waje daya kamar maijin sanyi,bata wani option a yanzu banda tayi kukan,shi kadai ya rage mata,ta tabbatar ta gama rasa ameen rashi na har abada,tayi kuskure guda daya tak daya ruguza mata dukka rayuwarta, maybe rugujewar ta bibiyeta har zuwa qarshen rayuwarta,taqi shi a sanda gaba daya duniya ke mata sha'awar kasancewa dashi,sai ta tuna wata magana da inna ta gaya mata sanda take shirin barin gidan zuwa gidan kawu muntari inda acan ta zauna har zuwa sanda aka miqata dakin bassam
*_dama sau daya taj take zuwa maka a rayuwa,sai mai matuqar sa'a ne take waiwayarsa a karo na biyu,kada kiyiwa kanki hukuncin da zai zame miki qarfen qafa a rayuwarki_*
A sannan gani take innar bata fahimci komai ba,gani take inna ta daina sonta ameen akwai takeso data damu tabar wanda zuciyarta takeso ta auri ameen din,tabbas maganar inna gaskiya ce,qila tana cikin mutane marasa sa'a a rayuwarsu,wadanda damarsu bata saje waiwayarsu,ta tafi kenan har abada.
Dama ta bawa kanta sosai tayi kuka ta qoshi,wanda ya rage mata nauyi me yawa a zuciyarta,ta kusa awa biyu kafin ta tashu,ta laluba maganinta tasha,sannan ta qarasa izuwa bandaki.
Ruwa mai zafi ta hada tayi wanka,tanajin yadda ruwan bai zama saman fatarta saboda yadda tayi sulbi da yawa da kuma laushi,ta nade jikinta da babban towel dinta ta dawo daki.
Sau daya ta kalli fuskarta a madubu bata qara ba,tayi jajur saboda kukan da tasha,abunka da farar fata,undies ta saka ta zura dogywar riga kawai ba tare data shafa komai ba banda turare ta haye gadonta a hankali,ta runtse idanunta dake mata radadi a hankali tana fatan Allah ya aiko mata da barci,saidai amaimakon haka,wasu hawayen ne masu dumi suka zuraro mata har cikin kunnenta,ta bude idanun nata a hankali,ta jawo wayarta dake saman kanta,ta bude bayan wayar,ta ciro sabon layin mtn data siyo tun wancan satin zatayi amfani dashi,ta dora kan wayar ta sake kunnata,sannan ta tafi kai tsaye tana laluben number ameen din, number da bata taba kiranta ba tsahon rayuwata,ta zubawa number idanu tana kallonta, number da tayi saving da MA.
Tanaso ko yaya kafin shudewar wannan dama da take da ita ta aje masa wani saqo,koda basu da yawa,koda bazai fahimta ba, at least karin farko ta rage nauyin dake saman zuciyarta,ta kuma fitar d wani abu daga cikinta komai qanqantarsa,saita shiga ma'adanar saqonni wajen da zai bata damar aika saqo,ta saka number dinsa ta fara rubuta masa saqo ta sabuwar number dinsa kamar haka......
"
https://arewabooks.com/chapter?id=62ced7ea0ba46f15b711fc31#:~:text=Chapter%2063,dinsa%20kamar%20haka......
[7/19, 10:03 PM] Mummyn Yara: 63
_Rasa abinda muke so na nuni ne da cewa rabonmu yana ta can wani wajen yana nemanmu, dan mun fad'i a soyayyar wani ba wai mun rasa soyayya ta har abada bane, Ba asara bane danka rasa wanda kake so, asar shine ka rasa kanka wajen kaunar wanda kai a wajensa ba komai bane, sauk'i yana tare da tsanani, mai hak'uri yana cimma dad'i, mai kyauta baya rasawa, kowa yaji tsoron Allah, Ubangiji zayyi masa mafita, manta da damuwa ka fuskanci rayuwa, kowa ka gani a duniya akwai abinda ya dame shi,fatan nasara sa kuma fatan dacewa ga sabuwar rayuwar da zata fuskanci kowanne bawa_
Dai dai sanda saqon ya isa dai dai lokacin ga lumshe idanunta,hawaye suka gangaro,sai ta danna wayar ta kasheta gaba daya,ta yadda bazai sameta ba,koda ace zaiyi yunqurin kira don bin ba'asin wanda ya tura saqon,a hankali ta tunda da ita din mahaddaciya ce,ta kama farkon suratul a'araf can qasan ranta tana karantata,a hakali idanunta suka fara nauyi,baccin da bata zaci zuwansa ba ya rarrafo ya rufe mata idanuwa ruf.
_sai muce a tashi lafiya amaryar dr_😊
Sanda saqon ya rikeshi yana zaune tsakiyar baqinsa suna duba kayan da zasu sanya ranar daurin aure,wanda dukka abokan angon akayi musu dinki iri daya,ya karanta saqon ya sake maimaitawa ya kusa sau biyar,baisan number din ba,sai yayi yunqurin bi ya kira don yaji waye kamar yadda ta zata,saidai ya tadda layin a kashe,ya sake gwadawa suka sake bashi amsa guda daya dai,dole ya maida wayar ya ajiye yana tattara hankalinsa ga abinda sukeyi,saidai abun mamaki saqon ya tsaye masa cak a zuciyarsa,ya kuma barshi da tunane tunane,hakanan ya samu kansa da yawaita duba wayar lokaci zuwa lokaci,kamar me neman wani abu.
Sanda samha ta kirashi ya duba wayar da wani zato daban a ransa,bai daga ba yasa wayar ne a silent,saboda yasan maganar da zatayi masa
"Anata kiranka fa" daya daga cikin abokansa me suna abdus sabur ya fada,sai ya dauki wayar yadan matsa daga dakin zuwa farfajiyar hotel din yana kara wayar a kunnensa.
Lumshe idanunsa yayi bayan yayi sauraro na wasu mintuna kana ya budesu
"Samha......na gaya miki am not interested....
Albarkan aure nake nema,kuma albarkan yafi dukka wani abu da za'ayi,am ready to pay ko nawa ne indai walima ne,so karki sake sako maganar wani dinner ko something else please" daga haka ya datse wayarsa,ya furzar da iska daga bakinsa,baisan me yasa samhan ke matuqar son bidi'a a biki ba harda wadda ta wuce gona da iri ba,ya shirya musu walima a waje mai tsada ya kuma kashe kudi sosai,hakanan shima ya shirya reception na musamman shi da abokansa immediately ana gama daurin aure,shi wannan yafi burgeshi tun asali dama,ma'adanar saqonninsa ya bude yana sake karanta saqon dazu,sai ya samu kansa da sake trying kiran wayar,amma dai amsar iri daya ce switch off,haka ya juya zuwa ciki,zuciyarsa cike fal da tunani iri daban daban,yana jin samha na kira amma ya shareta ya sanya wayar don't disturb yaci gaba da sabgarsa.
**********Sosai gidan ya sake hautsine da jama'a da kuma baqi iri daban daban,lallai bikin mutum uku ba wasa bane,tuni iman ta aro dukka wata juriya da dauriya ta azama kanta,tunda kowa ya sani bikin dake hade dana maza da kuma mace,macen kusan itace take zama madadin sauram angwayen,kowa yazo ita yake nema,irin tarin kayan da taga inna da malam sunyi mata yayi matuqar bata mamaki qwarai da gaske,kaya ne na gani na fada,kaya na 'yar gata wanda ba kowacce mace ke samun irinsu,ko ba'a gaya mata ba ta tabbatar da cewa sun kashe iyayen kudi masu yawan gaske,hakanan ta fannin cimar abincin biki babu abinda ba'a tanada ba cikin gidan,tun daga ranar yau din da take gobe daurin aure gidan ya kaure da hada hada,tuni su yaagana aka shiga hidima,yaa baraka ce bata qaraso ba sai a gobe,saboda daga can wajen ma a jigawan tana da baqi,kuma zatayi nata bikin.
Sanye take da wata doguwar rigar atamfa exclusive,dinkin free gown wanda yayi matuqar zauna mata a jikinta,tun daga nesa idan ka hangeta zakaga yadda take zuba qyalli tako ina,irin qyallin nan da ake kira na amarci,nata na musamman ne tafe da wani irin kyau da kwarjini data yi,a hankali take ratsa mutane,fuskarta a sake tana magana da wasunsu idan sukaci karo,innarta take nema tun dazun,saidai innar tayi mata baton dabo cikin gidan,daga qarshe mufida ta gano mata innar cikin kitchen,saboda haka ta nufi can din kai tsaye.
A tsaye ta hangi innar ita da wasu 'yan uwanta guda biyu,sai wani a tsaye wanda ya baiwa qofa baya,kuma tun kafin ta qarasa zuciyarta da gangar jikinta suka bata lamin ne,sabida tsaiwarsa ba baquwa bace a wajenta,yana tsayen hannayensa zube a aljihun rigarsa.
A hankali ya waiwaya sanda tayi sallama,sai kuma ya dauke kansa ya maida ga inna sautin matan na amsa sallamar tata yana karade kitchen din
"Yauwa to shikenan,jeka ma ga iman nan sai ta kawo maka,ka kira sadiqun ku zauna da Allah kuci abincin,itama ka turke min ita,gaba daya ku ukun kun sauya kun zama wasu iri,kullum da abincina kuke barina,sai tafiya kuke da yunwa a cikinku,kada ma kai kaji labari,mutumin da baya wasa da cikinsa amma yau ya zama haka?" Daya daga cikin matan dake aikin abinci a wajen ta saki dariya tana cewa
"Aure kenan,ai aure ba wasa bane" dan qaramin murmushin gefan baki ya saki,shi bama abinci ba,komai jinsa yake wani iri,wai a goben ne zai zama magidanci kamar kowa?,hatta da gangar jikinsa bayajinta yadda ya saba ji,yana matuqar jin dadin nuna kulawa da damuwa da al'amarinsa da inna keyi,ya rasa dame zaya saka mata a rayuwa?,kome zuciyarsa tace ya yiwa innar sai yaga yayi kadan a tsaya dai dai da matsayin abinda tayi masa a rayuwa
"To na gode,a fito lafiya" ya fada cikin girmamawa yana juyawa,sannan yabar kitchen din.
Ko tsayawa jin abinda ya kawota innar batayi ba yasa lami wata cikin matan ta hada abincin tace ta dauka taje can suci,sai tafi sakewa saboda can sashen nasu ne babu mutane sosai,kamar ta aza hannu aka haka ta dauki kayan abincin,saidai duk wanda ya kalli fuskarta yasan akwai abinda ya sosa zuciyarta.
Zaune yake saman kujerar falon,ya jingina bayansa da kujerar yayin da yayi crossing qafafunsa,hannunsa riqe da wayarsa yana taba a hankali,yana fuskantar qofa ne,ta yadda duk wanda ya shigo shi xai fara gani.
A nutse ya daga kanshi yana amsa sallamarta,sallamar data yita ciki ciki,ya zube idanunsa fes saman fuskarta yana nazartarta,fuskarta ta sake zama cute and adorable,komai nata ya canza,saidai sauyin mode dinta ya tsaya masa a rai,ba haka fuskarta take ba sanda ta shigo kitchen din ba,ya kafeta da idanunsa da taji sun mata nauyi suna shirin kayar da ita harta iso ta ajjiye abincin,ta kuma tashi da niyyar tafiya
"Zo nan....dawo ki zauna" ya bata umarni kai tsaye,yadda umarnin ya fita da sautin muryarsa datai kauri da kuma nauyi yasa ta kasa bijirewa abinda yace din,saita dawo ta kuma zauna nesa dashi.
"Ba cewa inna tayi kici ba?....oya,maza zuba" ya fada nuna abincin da hannu,batason maganar tayi tsaho,don haka ta fara zubawa a plate.
Ci gaba yayi da duban fuskarta,a hankali yace
"Me ya bata ranki?" Tambayar data sanyata tadan daburce kadan,batayi tunani zaiyi noticing hakan har ya tambaya ba,sai ta miqe da kwanon tana cewa
"Babu komai,zan wuce da abincin ciki zanci a can,ana jirana" kamar ba zaya amsa ba,sai kuma ya gyada kansa,baiga muhallin takura mata ko matsa mata ba,ya bita da rakiyar idanu sanda take takawa,duk da cewa cikin mayafi take,amma yana iya hangen yadda sassan jikinta suke juya kansu da kansu
"Ya Allah" ya fada yana lumshe idanunsa,yafi kowa sanin akwai wannan tattare da iman,shi yasa ya zama telanta yake kuma tattalin duk wata sutura ko dinki da zata sanya a wancan lokacin,kafin ta wargaza komai da hannunta.
Number badi'a ya laluba ya kirata,ya kuma gaya mata ta tabbatar iman din taci abincin data fita dashi saboda ya idar da saqon da inna ta danqa a hannunsa,babu jimawa badi:an tayi masa text kan taci,sai ya jawo abinci ya buda ya fara zuba nashi yana kiran sadiqu yaji a ina suke shima.
*_RANA BATA K'ARYA saidai uwar diya taji kunya inji 'yan magana_*
Yau take juma'a,kuma dai dai da ranar da dukka bangarori waliyyai da kuma wakilan angwaye da amarensu suka tsayar a matsayin ranar daurin auren yaran nasu,ta kowanne sashe idan ka kalli gidan cike yake da al'umma,kowa cikin ado da mabanbantan shiga da zata nuna zallar farincikin da mutanen ke ciki,hayaniya ke tashi tako ina,ga abinci nan da aketa hada hadarsa tun daga tashinsu har zuwa yanzu da zugar maza mai yawa tayi gaba zuwa gidajen amaren don dauro auren angwayen guda biyu,kafin a dawo a daura na iman wanda shine na qarshe dama a yadda aka tsara.
Daga can ciki quryar dakin iman,iman dince tare da qawayenta,wanda kusan a cikinsu zata iya cewa babu wanda ta bawa card din gayyata da hannunta,kusan dukka bushira ce tayi wannan aikin.
Tayi kyau iya kyau,kai kace diyar sarkin aljanu ce cikin shigar fari da gold,tun daga suturar ciki zuwa ta waje,komai nata fari da gold ne,shigar da tayi masifar hawa da fatarta,bawai kwalliya tayi ba,aah,hasalima banda hoda babu komai saman fuskarta,saidai wani glowing da take zaka dauka canza iman din akayi ko kuma wankan inji akayi mata,jikinta wani irin mayataccen qamshi yake fitarwa,wanda duk wanda ta gifta sai yace
"Kai masha Allah,lallai amarya da gaske kinsha qamshi" tuntuni kafatanin ilahirin kayanta bushira ta zauna tasa kabbasa ta turare mata su,qamshin ya cakuda dana jikinta ya bada wani ni'imtaccen qamshi,sahihin hadin turare daga AMARYAR KB GLOBAL ENTERPRISES da kuma hadi na musamman daga wajen yagana tun daga maiduguri.
Dukka maganganu hira da kuma tsiyar da suke mata bin kowa da idanu kawai take,wayarta na hannunta tana jujjuya wayar,shigowar wani saqo mintuna talatin da suka shude shi ya sake jefata duniyar tunani,saqone daga dr Ahmad,dr din data manta rabon da taji muryarsa direct ta waya,saidai musayar saqonni kawai,ta gaza gane ko fahimtar dukka kalmomin da saqonsa ke dauke dashi,kanta ya daure tam,don haka taci gaba da juya wayar kawai,tana tunanin dimuwa da yadda zuciyarta ayau din ke wani irin bugu da sauri ya haifar mata da dodewar tunani ta kasa kowanne irin tunani akan saqon.
A hankali a hankali hayaniya ta sake qara qarfi cikin gidan,har iman din taji kamar wani abu yana hawa kanta
"Mun dawo,ai an daura,saura na iman.....eh suna waje" muryar halifa wani jikan yaagana ta iso har inda iman din ke zaune.
Yadda zuciyarta ta buga ya sanyata furta
"La haula wala quwwata illa billah" hadi da rintse idanunta,shikenan.....shikenan ta faru ta qare fa furta can qasan ranta,ta maida bayanta sosai jilin kujerar da take kai ta runtse idanunta,kunnuwata nata debo mata hayaniyar jama'a mabanbanta a cakude da surutai iri daban daban.
"Lafiya dai ko?" Taji muryar bushira daga gefanta,ta bude blue eyes dinta da suke wani sheqi ta zubesu fuskar bushira
"Kun cika surutu wallahi"
"To a gidan makoki muke da za'a hanamu magana?" Bushira ta fada tana harararta,tadan zubawa bushiran idanu cikin mamakin yadda take ta sabgarta itama,kamar batasan komai kan sha'aninta ba.
Wayarta ta miqawa bushiran bayan ta bude saqon
"Karanta" tace da ita a taqaice,saita sanya hannu ta amshi wayar,ta kuma duba saqon kamar yadda ta umarta,tabe baki tayi ta miqa mata wayar
"Ungo,ni ban fahimci komai ba" idanu tadan zuba mata,sai kuma ta amsa wayar kawai ta maida idanun nata ta rufesu ba tare data sake cewa komai ba.
Daga inda take tana iyajin yadda aketa bada umarnin shirya abinci,saboda yanzu yanzu za'a gama daurin aurenta,ana gamawa kuma ance a fiddashi sanoda mutane suci su samu tafiya da wuri,tsam ta miqe qafafunta na rawa,wani irin fargaba da tashin hankali ma cika qirjinta,saita kawai fa nufi toilet ta tura qofar ta shige,bushira wadda ita daya ke ankare da ita ta bita da kallo har zuwa sanda ta shige din,sai taci gaba da sabgarta ba tare data ce mata komai ba.
[7/19, 10:03 PM] Mummyn Yara: 64
Sosai ta dafe sink tana duba fuskarta a madubi tana son bawa kanta qwarin gwiwa,tana son gayawa kanta da kanta kalmomin da zau qarfafeta,saidai duk yadda takai ga wannan dakiyar abun ya faskara,wasu irin hawaye masu zafi ne suka kubce mata,saita sadda kanta tana kallon yadda suke diga dis dis dis,duk da haka bata sare ba tana qarfafawa kanta gwiwa.
A qalla ta shafe mituna kusan ashirin cikin bayin,saita yagi tissue ta gyara fuskarta,ta kalli kanta kana ta fara takawa zuwa bakin bandakin,ta sanya hannu ta bude qofar,kalmar farko data shiga kunneta cakude da guda ta haifar da wata irin tsawa tsakiyar kanta,tsawar da ta sanya kanta a take ya sara,ciwon kai kuma ya saukar mata,ilahirin jikinta ya dauki rawa,ta zubawa ya baraka dake dakin tana sakin guda idanu
"Allah na gode maka,ko yau na mutu burina ya cika,iman ta zama ta lameen lameen ya zama na iman,alqawarin Alla ya cika" bakin yaa baraka takebi kawai da kallo,ta tabbatar da cewa yaa barakan ba zata taba yin wasa makamancin wannan ba,saboda baby wasa a tsakaninsu,tamkar wata doluwa ta tsaya kawai tana kallon ya baraka,bushira data fara hangota ta qaraso bakinta kamar zai bare
"Kizo ki bani tukuicina na wahalar banza dana dinga yi na rarrashi kan dr ahmad din bogi......harda tafiya toilet za'ayi kukan gulma,anaso ana kaiwa kasuwa" ta qarashe fada qasa qasa tana dariya.
Lokaci daya taji zuciyarta na gaya mata cikin duniyar mafarki take,ta runtse idanunta da qarfin gaske tanason tabbatarwa kanta mafarki ne ko kuwa gaske?,gudar da wata cikin qawarsu ta sakar mata a tsakiyar ka ya sanya kanta ya sake sarawa,sai gwiwoyinta sukayi sanyi,maimakon hawaye a wannan karon gabbanta ne suka gaza daukarta,numfashinta ya fara kakkatsewa,batasan me yake faruwa ba,ta daiji qafafunta sun kasa daukar gangar jikinta,a hankali taji tana sulalewa,takai qasa bata kai qasa ba dukka bata da wannan amsar.
Sama sama kamar kuma cikin duniyar mafarki take jin hayaniya cikin kanta
"Bata farka ba likita" wata murya data kasa tantance ta wace tayi maganar cikin sanyi
"Kada ku damu,zata farka,ba wani abu bane babba ya sameta ba,razana ce ko kuma taga wani abu da yayi matuqar bata tsoro ko firgitata,zata farka nan da kowanne lokaci,anyi mata allurorin bacci ne don qwaqwalwarta ta huta" muryoyi iri daban daban suka hau masa godiya.
Wadan nan maganganun suka tabbatar mata a duniya take,kana kuma ba mafarki takeyi ba,don haka ta fara qoqarin buda idanunta da takejin kamar an watsa mata tsakuwa,sun bude din saidai hasken daya cika dakin taji ya yiwa idanun nata yawa,wala'alla hakan yana nufin idanun nata sun jima arufe
"Hasbiyallahu la'ilaha illa anta" tayi qoqarin furtawa,abinda yaja hankalin dukka wanda yake kusa dasu
"Ta farka likita.....ta tashi" muryar yaagana cikin zumudi ta fada,abinda yasa likitan tsayawa sannan ya juyo zuwa inda iman din ke kwance,zuwa sannan idanun nata sun samu damar budewa,dukka jama'ar dake dakin ta bisu da kallo tana amsa sannun da suke mata daya bayan daya,yaa baraka,badi'a,bushira yaa gana da anty lami qanwar inna.
"Sannu ya jikin?" Likitan ya tambaya yana buda file dinta dake nuni da sabone
"Da sauqi" ta amsa masa da dasashiyar muryarta
"Ma sha Allah,me yake damunki yanzu?" Ya sake tambayarta yana gyara gilashin fuskarsa
"Babu komai,sai kaina da nakejin yamin nauyi kadan"
"Babu komai zai daina" ya sake fada yana duba zubar qarin ruwan,magunguna ya rubuta ya bada file din
"Zuwa anjima kadan zan sake round na dubata,da yiwuwar basai ta kwana a asibiti ba"
"To likita,sannu da qoqari" cewar yaa baraka,juyawa yayi ya fice,abinda ya basu damar sake matsowa suna dubata,kowa na nuna kulawarsa a kanta,binsu take da kallo kawai,zuciyarta na mata tariyar abubuwan da suka shude a baya
"Ya kamata tasa wani abu a cikinta kafij tasha magungunan nan" anty lami dake saman kujerar dake dakin ta fadi sanda usama dan yaa baraka ya shigo da magungunan
"Gaskiya dai,don na tabbatar babu komai a cikinta,don ko da safe bushira tace bataci komai ba" sai a sannan ta daga kanta tana duban window din dakin,duhu ya ratso sosai,da alama an jima da yin sallar magariba,to duka tsahon awannin suma tayi ko barci take?,yaagana tacewa zata shiga bandaki,bushira ta qaraso zata kamata
"Barshi zan iya zuwa da kaina" duk da hakan bushira bata barta ba,saita taka mata har qofar bandaki sannan ta jirata ta fito,alwala ta daura ta nema abun sallah bayan ta tambayi qarfe nawa?,badi'a tace mata qarfe tara na dare,ta jinjina abun cikin ranta,a yau ta rasa dukka sallolinta na ranar,a zaune tandinga ramasu gaba daya guda hudun saboda rashin cikakken qwarin jiki,bayan ta idar ta miqe a hankali tahau saman gadon sosai ta zauna,yaagana ta saka mata pillow daga bayanta yadda zataji dadin zaman,daidai lokacin da usman qanin usama ya shigo dauke da manyan ledoji
"Ina ka shiga tun dazun?,anata neman dan aike da zaije gida ya karbo mata wani abun tasa a cikinta?"
"Kawu ne ya kirani,gashi yace na kawo" yamatso kusa dasu ya ajjiye,badi'a ce ta tsugunna tana fidda kayan abincin,kana gani basai an gaya maka ba takeaway ne,amma bisa tsari da tsafta,faten dankalin turawa ne me kayan lambu da wadatacciyar hanta da qoda mai yawa,zazzafan ruwan zafi da yaji kayan qamshi,sai kuma wasu plates dake nannade wanda aka shirya fried rice da coleslaw sai gasashiyar kaza.
"Matso bushira ki zuba mata wanda zata iya ci" yaa gana ta fada,saita matso ta zuba komai a plate,da kanta taja kujera ta zauna gaban iman din,ta kalleta fuskarta dauke da murmushi,kamar ma qunshe dariya take,ta ajjiye plate saman cinyar iman din
"Oya mrs lameen,ga abinci"dubanta iman kawai tayi ba tare data ce komai ba,don har yanzu qwaqwalwarta da zuciyarta sun kasa yarda da abinda ya farun,garin yaya?,waye ya qulla ko ya shirya?,tallanta aka yiwa lamin?,ko.haquri aka bashi?,ya akayi dr ahmad ya barta katsam ba tare da sanin ko yardarta ba?,wanne laifi ta yi masa data cancani ya barta haka kamar wani abu ne mai sauqi aikata hakan?,wadan nan tambayoyin ta dinga yiwa kanta sanda take kai cokalin abincin bakinta,kaiwa kawai take ba tare data lura da abinda take diba ba
"Kici abinci da kyau mana iman,wanne irin ci kike masa ne?,sai diban ruwan kike kin bar abubuwan amfanin" duban tsanaki tayi ma plate din,sai ta fara hadawa da dankalin tana ci a hankali,cusashi kawai takeyi,amma bakinta sam babu dando.
Tana tsaka da tsakura aka turo qofar dakin,sallamarsa ta karade cikin husky voice dinsa ta ratsa dakin tun kafin takai ga daga idanunta taga wanda ke shigowar,idanunshi bisa saman fuskarta,itace ta farko a dukka dakin da idanunsa suka fara sauka akanta,yayin da ita kuma ta gaza daga qwayar idanunta ta kalleshi,kamar yadda ta gaza ci gaba da cin dankalin da bushira keta mitar ba wani ci take ba,ta fara motsa cokalin cikin plate din.
Dukka dakin suka fara masa maraba da shigowa,ya janye idanunsa a hankali daga kanta ya maida ga jama'ar dakin,ya fito shar cikin shadda gezner mai asalin kyau da tsadar army green me haske,dinkin babban riga da 'yar ciki da dogon wando,takalmin qafarsa rufaffe ne baqi,duk da darene hasken fitilun da suka wadaci dakin sun fidda kyau da walwali da shigarsa takeyi,tun daga hularsa takalmi zuwa shaddar dake jikinsa,kai da gani basai an gaya maka ba zakasan cewa ango ne.
Yadda takun takalminsa ke bada sauti haka bugun zuciyarta ke daduwa,qamshinsa ya mamaye ilahirin dakin,kamar shi daya ne ke amfani da turare a duniya,qamshi mai sanyi da tafi da tunani,ba me qarfi da saka damuwa ba.
Miqewa bushira tayi daga inda take zaune itama tana masa sannu da zuwa
"Yauwa sannunku" ya amsa mata yana isa gaban kujerar bayan sun gama gaisawa da mutanen dakin,dafe makarin kujerar yayi kawai da hannuwansa ba tare da ya zauna ba
"Sannu,ya jikin naki?" Ya tambayeta idanunsa na bin hannayenta daya tsaru da lallen amarci tana wasa da spoon cikin abincin
" Da sauqi" ta amsa masa tana jin kaifin idanunsa a kanta,wani irin kwarjininsa ne na musamman ya saukar mata,gefe daya kuma wani tsoro da cika ido nasa suka mamayeta
"Tunda Allah ya kawoka kai ka gwada ko zataci abincin,mu munyi iya yinmu taqi cin abin arziqi,ga magunguna agabanta suna jiranta" yaagana ta fada tana saba jakarta tare da miqewa tsaye tayi qofar waje,da daya da daya sai gasu suna ficewa daga dakin,kafin kace wani abu dakin ya koma wayan,daga ita sai shi.
Shuru ne ya ratsa dakin,kamar babu sauran wata halitta a cikinsa,kurrrr yaja kujerar baya kadan,sannan yayi taku biyu,ya isa gaban kujerar ya zauna,qiris ya rage gwiwoyinsu su hade waje daya saboda irin kusancin dake tsakaninsu,qirjinta ya tsananta faduwa lokacin da taji hannunsa saman nata hannun,ba musu ta sakar masa plate din da yake niyyar karba din,ya daukeshi daga saman cinyarta zuwa tasa cinyar.
Sosai ya nannade babbar rigarsa,yayi bismillah ya debo abincin yakai bakinsa,sai kuma taji yace
"Oya,take it" tare da kafeta da idanu,yana tauna dankalin a hankali cikin bakinsa.
"Open your mouth mana,ko sai na tashi?" Ya fada a dan kausashe wannan karon,jin ya motsa ya sanyata daga idanunta da sauri tare da bude dan qaramin bakinta hadi da daga idanunta zuwa fuskarshi,ta tsammaci zai taso inda take ne.
Shigarsa ta fara keta tunaninta,kyansa ya bayyana baro baro saboda kusancin da ke a tsakaninsu,saita runtse idanunta sanda yakai cokalin bakinta,yayin da shi kuma yabi qaramin bakin nata da kallo wanda yadan sake yin jaa,tsigar jikinsa ta zuba,karon farko daya sake yiwa fuskarta kallon qurilla daya wuce kima,saboda yana da tabbacin a yanzun bai wuce kimar ba,bai kuma taja sharia ba.
Saman cinyarta ya maida abincin,yaja kujerarsa gaba sosai ya cike sauran gap din da yayi saira a tsakaninsu,a hankali ya kama qafafunta dake lillo ya dora saman cinyarsa,qanqame jikinta tayi waje daya tana jin tsigar jikinta na zubawa,mamaki sosai ya cikata,bayajin komai ne?,baya gudun ta bata masa wannan shaddar tasa me dan karen tsada?,dama ya bata kan taci da kanta,gaba daga a takure take,wani kunya da nauyinsa ya cikata,ga kuma dumin tafin hannunsa dake saman qafafunta yana ratsa kowacce gaba da sashe na jikinta.
Tanayin spoon daya taga ya dauke cokalin shima ya sake diba yakai bakinsa,ya sake miqa mata taci ya kuma karba,da alama karba karba yakeso suyi da cokali daya,abinda ya sake daure mata kai,ya kuma jefata a tunani,har ta kasa daurewa ta daga idanunta ta saci kallonsa,sai gashi karaf ya kamata.
Girarsa ya dage mata kana ya langabar da kansa
"Karki damu,bazan cinye miki ba,banci abinci bane tun safe....." Qas tayi da kanta saboda yadda lumsassun idanunsa ke saukar mata da gajiya,haka sukaci gaba da karba karba,idan tayi spoon daya shima shima zai karba yayi,wani lokaci kuma har spoon biyu yakeyi,da haka ta tabbatar da gaske lallai yunwar yakeji sosai kuwa.
Wasa wasa sai gashi sun tashi da dukka dankalin dake wajen,ya miqe da kansa ya dauke plate din,ya ajjiyeshi,ya dauko tissue da kuma magungunan nata ya dawo ya zauna kamar yadda yake daxu,ya miqa mata tissue da ruwan,magungunan kuma ya balla da kansa,ya buda tafin hannunsa ta miqa mata yana kafeta da idanu,yana tuna yadda take gudun magani.
Sauke idanunta tayi kan lallausan jan tafin hannunsa me dauke da zara zaran yatsun hannu,ta kalli magungunan,ta miqa hannu da daya da daya tana dauka tana kuma runtse idanunta tana korasu da ruwa,guda dayan data rage ta miqa hannu zata dauka,sai ya maida hannun ya rufe harda yatsunta da suka shiga ciki,tsigar jikinta ya zuba,tayi nufin janyewa amma yayi mata riqo irin na maza,duk da cewa babu zafi a riqon amma tana jinsa har cikin qashinta
"You better stop it iman......me yasa koda yaushe kike kai kanki asibiti?,rayuwarki nada tsada.....kuma yi miki auren dole bashi yake nufin rayuwarki tazo qarshe ba,kada ki damu, there is a way.......akwai chance da zan baki,ni bazan takuraki tauyeki ba" mamaki daurewar kai da rudani suka kamata lokaci daya,dole ta sake dubansa don tabbatar da abinda ke saman fuskarsa,ya tsareta da sexy eyes dinsa da suka sake lumshewa kamar mejin barci,dai dai lokacin aka tura qofar tare da yin sallama.
Fauzan ne daya daga cikin abokansa na kusa kusa,tunda dama shi bashi da wani amini sama da sadiqu,tare suka taso tare suke sharing matsalolinsu,kunya ta cika iman,ta soma qoqarin zame hannunta amma yaqi bata wanna damar
"Sir lokaci yana tafiya fa" ya fada cikin salo na tsokana,ameen din bai damu ba sai ya duba agogon hannunsa yana cewa
"Ta nan dinma wani aiki nakeyi.....da Allah taimaka ka duban likitan nan yazo ya sallamemu....inajin zata iya kwana a gida ai" ya qarashe maganar yana aza mata idanunsa daa kasa jurewa daukarsu,yanata dora mata nauyinsa ga kuma nauyin fauzan
"Ba matsala,madam ya jiki?"
"Da sauqi" ta fada cikin wani irin sanyi
"To Allah ya bada lafiya" yayi maganar yana juyawa ya fice abinsa ba tare daya tsaya jin amsarta ba,saboda ya lura nauyinsa takeji,uwa uba lamin din harara yake maka masa a fakaice,don dankwali ne kawai saman kan iman din.
A hankali ya sakar mata hannu,ya tura kujerar baya ya miqe,ya fara tattara magungunan yana maidasu leda,ya gama yayi musu waje,ya dawo gabanta ya zuba hannayensa cikin aljihun wandonsa yana ci gaba da kallonta,kamar zata nutse haka takeji,kamae gadon bazai dauketa ba,gefe guda kuma kalamansa na mata yawo aka,tana son fahimtar abinda yake cewa.
Turo qofar da akayi ya maida hankalinsa ga qofar,likitanne ya shigi,ya bawa lamin hannu sukayi musabaha sannan ya dudduba abinda ya kamata ya duba din,ya maida hankalinsa ga lamin ya masa dukkan bayanin daya dace yayi,kai yake gyadawa cike da gamsuwa har ya gama sannan ya bashi amsa
"Inajin kamar wannan file din daga yau ya gama aiki,indai wannan damuwar ce ba zata sake kawota asibitin nan ba,saidai wani ciwon kuma daban idan Allah ya kawoshi,in sha Allah" murmushi likitan ya saki,kalamansa sun burgeshi,ya miqa masa hannu sukayi musabaha yana cewa
"Well-done,Allah yasa" ya bashi file din yace zaiji balance na abinda zasu cika a reception,duk da cewa baya tunanin zasu cika din saboda kudin da suka ajjiye kafin ayi admitting nata,qilan ma ciko za'ayi musu.
[7/19, 10:03 PM] Mummyn Yara: "

Menu
Dashboard
My Library
Create Story
Home
About us
FAQ's
Privacy Policy
Terms of service
Logout

KUFAN WUTA