← Book details Kufan Wuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 3 OF 6

Chapter 66

Kufan Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 31 min read

Shafi na sittin da biyar

65


Waya yayi daha waje ta 'yan sakanni zaiga usama ya shigo,ya miqa masa file din


"Kaje kuyi settling komai,idan ka gama ka samemu a waje"


Qarasowa inda take bushira tayi,murya qasa qasa take tsokanarta


"Irin wannan luf da kukayi a daki?,ahhh.....sai naga kuma kwanin abincin babu komai,a ina kuka zubashi?" Bashi da nisan gazara tsakaninsa dasu,yana tsaye tana magana da yaa baraka,don haka ta watsawa bushira harara da sauri,dariya bushira ta bushe da ita,koda bata buda bakinta tace komai ba,kana kallon fuskarta zaka tabbatar akwai salaama mai yawa daga zuciya da ruhinta,wanda ya bayyana har saman fuskarta.


Dukka gaba sukayi suna kwashe kayansu,ya tako a hankali gabanta ya miqa mata hannunsa,ta sanya nata a ciki a hankali,saiya hade tafukan hannayensu waje daya,yana sarqafe yatsunsu cikin na juna,ta zamo daga saman gadon a hankali ta sauko,bai saketa ba yana cu gaba da riqon hannunta,suka fara takawa suna fita daga dakin,tanason zame hannunta saboda idanun mutane amma ta kasa,abinda ta lura dashi shine....shi sam bai damu ba,ita kadai tasan wannan connection din me yake haifar mata ga gangar jiki da kuma zuciyarta,haka taci gaba da binsa sannu a hankali har suka iso farfajiyar asibitin,sai a sannan ta lura motocine kusan guda huduna fake a wajen,bisa dukkan alamu suna kan hanyar yi masa rakiya ne kenan zuwa gidansa,sai a sannan ta tuna da samha,zuciyarta ta buga,ranta yana neman jagulewa,amma data ambaci sunan Allah sai taji kamar cirar qaya abun cikin ranta.


Da kansa ya bude mata gaban motar ta shiga ya mayar ya rufe,ganin komai takek kamar almara,kaffa kaffan da yake da ita wNi sabon al'amarine a wajenta da bata saba gani ba,musamman idan ta aunashi da rayuwarta da bassam,kudi kawai sune a gaba da komai a wajensu.


Qamshinsa ya sake cika motar sanda ya shigo ya maida murfin ya rufe ya gauraya da ac ya bada wani yanayi na musamman da zai iya narka da dukka wanda zuciyarsa ke cikin ganiyar soyayya,ya juya ya kalleta kadan ya janye idanunsa,su kadai ne a cikin motar saboda akwai wadatar abun hawa,yana shirin tada motar fauzan ya qaraso


"Yaaa?"

"Ku jirani mu dawo saimu wuce"

"Muje tare din kawai,ya za'ayi sarki guda yabi kwalta shi kadai?" Ya fada yana dariya da alama wani yaren ne nasu,murmushi kawai yayi,zai tada motar yaagana ta qaraso itama


"Ameenu.....me xai hana kayi tafiyarka kawai ku wuce gida,mu idan yaso ma fita titi mu samu abun hawa?" Zuciyar iman ta buga,kamar tayi magana amma ta hana kanta,Allah ya sani sam bata shirya ba itakam,da wanne zataji?ba zatar sata kwantar da ita,ko kuma tafiya gidan miji shima babu shiri?,abun ai sai yayi mata yawa wai shege da hauka.


Duban iman din yayi na tsahon minti daya sannan ya maida kallonsa ga yaagana


"Babu matsala yaagana,ku shiga mota fauzan zamu kaiku gida,har yanzu da sauran lokaci ai daren bai gama yi ba"


"To ai shikenan" ta fada tana qarawa gaba,dai dai nan iman ta saki ajiyar zuciya a boye gana godewa Allah da bai aminta da shawararta ba,tana buqatar lokaci da kuma nutsuwar da zata tattara dukkan wasu tunanuka da suka cika kwanyarta,ta zubda na zubdawa ta dauki na dauka,idanun taci gaba da bari a lumshe,tana jin sanda motar ke fita a asibitin har suka hau titi.


Shurune ya wanzu a motar,daga bisani ya maye gurbinsa da sautin karatun qur'ani da muryar sheik shuraim da qaramin volume,abinda ya sake haifar mata da tarin nutsuwa qwarai har suka shigo layinsu.


Tun daga nesa zaka fahinci akwai sauran jama'a baqi a gidan,a hankali yaci gaba da jan motar har suka qaraso qofar gidan,ya kashe motar kawai ba tare daya fito ba,tana kallon sh yaagana da aka sauke suna shigewa ciki abinsu,sai ya sauke glass dinsa ya kira badi'a,ta qaraso cikin girmamawa,ya bata umari ta karbo key wajen inna,sannan ta buda motar ya fita,ya zagaya inda take itama ya bude mata.


A gaba ya sanyata kamar wani bodyguard,suna shiga ciki jamaar dake wajen suna mata sannu,batasan ya akayi ba sai taga ya saita mata hanya zuwa sashen da dakunansu shida ya sadiqu suke a maimakon cikin gida,gab da zasu qarasa badi'a ta qaraso miqa masa keys din ya karba ita kuma ta juya.


Daga bayanta ya taka a hankali ya tsaya,har tana jin hucin saukar numfashinsa,inda zatayi wani kyakyawan motsin ba shakka zata tsinci kanta a jikinsa ne,ta gefen qugunta ya miqa hannunsa ya zura key din ya bude qofar ya kuna turata.


Kyakkyawan parlor din nan nasu daya tsumu da qamshinsa ya bayyana,yana nan a killace komai neat,kamar ba cikin gidan sashen yake ba,don ko alama bai nuna yasan ana biki ba saboda yadda yake fes,ci gaba yayi da directing nata har zuwa bedroom dinsa,komai na ciki yana nan,babbar katifarsa da tasha zanin gado fes kamar wani zai kwana a ciki,harda ragowar kayan amfaninsa wasu duka bai kwashe ba,zuba hannayensa yayi a aljihunsa yana tsareta da ido,kallon qurillar da yau ya koyoshi,ita kuma yayi mata zafi da nauyi da yawa,tanajin kamar ba zata iya jurar ci gaba da daukarsa ba


"Akwai abinda kike buqata kuma?" Ya tambayeta da lallausar muryarsa,saita zame ta zauna gefan katifar kanta a qasa tana girgiza masa kai alamun


"A'ah" hannunsa ya fiddo daga aljihun nasa tare sa wayarsa dake ringing yana murmushi


"Meye ne ya kashe bakin iman yau din?" Ya yiwa kansa tambayar ba tare da ya furta mata ba,ya daga wayar ya kara a kunnensa


"Suna iya tafiya ai,basai sun jiramu munzo ba.....ai yafi dai,gani nan" iya abinda ya fada kenan,ya fara takawa zuwa qofa


"Bacci yana da kyau a lafiya da qwaqwalwa,akan dauki jibgin kayan tunani a ajesu gefe duk yayin da kazo kwanciya,saboda bawa qwaqwalwa da ruhi hutu,da kuma samun lafiyayyen barci,ki kwanta kiyi barci sosai,asuba ta gari" kalamansa na qarshe kenan sanda yake fita a bedroom din,tabi hanyar daya wuce da idanu kafin ta janye idanun nata tana dawo dasu cikin dakin,qaqarfar ajiyar zuciya ta saki,wani abu nason tsaya mata a wuya,wajen wata yanzun zai tafi ko?,shine tambayar data tsaya mata,amma data zuqi numfashi da kyau....kwanyarta ta dawo mata da dimbin kulawar data samu daga wajensa na taqaitattun awanni sai taji komai yana wankewa daga ranta data kirayi sunan Allah,kafin ta bude idanun nata ma taji an turo qofar an shigo,bushira ce,ta bita da kallo


"Ina zaman zamana ya tasoni,nida ya qyaleni,keda zakiyi kwanan dakin love" abun bushira zuwa yanzu dariya yake bata,ita din qawace ta musamman kuma ta gari,wadda samun irinta a wannan zamanin sai an tona,ta qaraso tsakiyar dakin tana dire kayayyakin data riqo,duk abubuwan amfanine da zata iya buqata,harda kayan sawarta


"Gashinan inji inna,tace tana gaisheki" rau rau tayi da idanunta,tun a sannan kewar inna da kuma qaunarta suka sake dirar mata,a yau da burin inna ya cika ko yaya zuciyarta?,ko yaya matakin farincikin dake shimfide saman fuskarta?


"Ba zatazo ta dubani ba?"

"A'ah wallahi tace bada ita ba shiga dakin suruki,nima nan da kika ganni dakin nan yafi qarfina,a parlor zan kwanta na rage zafi a waya nida sahibina,Allah muma ya aurar damu ya bamu me tattalinmu irin haka" dariya bushira taso bawa iman,ba yadda batayi da ita su kwana kan tafifar tare ba amma taqi,tace to ko qasan carpet dinne ta kwanta nan ma taqi,ta dire mata komai ta juya zuwa parlor din tana cewa


"Nidai Allah barci xanyi,a gajiye nake tubus,Allah ya bamu alkhairi" bin bushira tayi da kallo harta fice taja mota qofar sannan ta dawo da dubanta still dai cikin dakin.


Komai nashi a killace a kuma tsare,hatta da saman madubinsa da bai kwashe kayan shafawarsa ba sunanan a jere,ta dauke idanunta ta mayar kan katifar dake dame da farin zanin gado gefe kuma ga lallauan bargonsa ruwan madara,sai tarin fulalluka manya da qanana cikin wankakkun pillow cases,ko meye yakeyi da fulalluka haka da yawa oho.


Ita kanta sai a yanzu takejin gajiya na sauko mata,amma ba zata iya kwanciya ba sai ta watsa ruwa,ta miqe tana duba ledar,kayanta ne a ciki na sawa da undies,sai su cake da qananun lemo da kuma qunshin kaza a ciki,wanda wannan ta tabbatar ya lameen ne ya hadosu,saboda duka favourite dinta ne a ciki.


Saman madubi daga gefe ta hangi farin towel a ninke,ta fidda kayan jikinta ta daura towel din daya saukar mata har cinyoyinta,ta lumshe ido tana shaqar iska sosai,qamshin daya tsumu a jikin towel din na cika hancinta,qamshin turarukansa daya hade da na sabulun wankansa,ta waiga kadan tana jin kamar yana labe a wani wajen yana kallonta,baby kowa itama ta sani,kawai zuciyarta na raya mata ne,ta qarasa gaban bandakin ta zura slipper dinsa,saiga qafarta ta tashi qarama a cikinsu,sabida tazarar size na takalmi dake tsakaninsu,ta tura bandakin ta shiga.


Karamin bandaki ne,amma kuma komai nashi fes yake,sai ragowar dan damshi da yake ciki,da alama ba'a jima can can da yin amfani dashi ba,komai nashi dashi tayi amfani,sai gashi ta dosani kadan daga cikin qamshinsa,yasan sirrin turare da kuma ya zabarsa,tayi wanka sosai da ruwa me dumi a qaramar heater dake bandakin,sannan ta fito ta tsaya gaban mudubi.


Mayukansa ta tatsa ta shafa,nan qamshinsa ya sake qaruwa,saita dinga ji kamar suna tare dashi,ta gama tsaf ta shirya cikin wata lallausar rigar barci pink mai gajeran hannu,iya tsahon rigar cinya ne,wandon kuma iya saman idon sawunta ya tsaya,ta gyara kanta ta matseshi waje daya,batayi amfani da sauran turarensa ba saboda gudun wani abu,saita dauki nata ta fesa,zuwa sannan gajiya ta sauka a gabbanta sosai,burinta kawai ta kwanta,ta isa karifar ta haye,ta ware duvet dinsa ta lulluba tana sauke numfashi me qarfi,gaba daya qamshinsa ne tako ina,yama kashe nata turaren,take taji yana haifar mata da wani yanayi cikin zuciyarta.


Idanunta ta rufe a hankali,fuskarsa ta ta daxun ta dawo mata tarwai,kyansa ya fita ainun,yadda yake mata magana da dukka wani body contact da suka samu adan qaramin lokacin,wani qaqqarfan so da batasan da zamansa a zuciyarta ba ya taso ya mamayeta,take kewarsa ta saukar mata,wata irin soyayyarsa ta motsa mata,saita qanqame daya daga cikin filallukan dake saman gadon cikin jikinta da kyau,take ta fahimci amfanin tarin fulallukan dake kan katifar.


Sake jawo guda daya tayi ta kifa fuskarta a kansa,qamshinsa daya ratsa filon yaci gaba da shiga hancinta,ya dinga haifar mata da wani yanayi,shauqi qauna da bege zuwa ga masoyin da ya yiwa zuciya wawan kamu,sai take jin inama ace yana kusa da ita?.


Kara ta fara ji qasa qasa kamar alarm tsakanin filallukan,ta miqa hannunta a kasalance ta laluba sai ga qaramar waya,kira akeyi,kuma sunan LAMIN ne a rubuce baro baro,mamaki ya cikata,daita daga wayar don jin waye.


Sassayar muryarsa dake dauke da wani abu me nauyi ce tayi mata sallama,muryar data sauke wasu abubuwa masu nayi a zuciyarta,da qyar ta motsa labbanta ta furta kalaman amsa sallama


"Kin kwanta ne?"

"Eh" ta amsa masa a taqaice,shuru ya ratsa na wasu sakanni,sannan ya sake cewa


"Good night, sleep tight,karki makara sallan asuba" lafuzzan suka fita a bakinsa can qasa kamar bayason yin magana,abinda ya qaraaa saukar mata da gajiya kenan


"Okay"ta iya cewa,ta zame wayar daga kunnenta a hakali idanunta a lumshe ta maidata inda ta dauko.


A haka tabar idanun nata suna ci gaba da hasko matashi,wasa wasa wani irin bacci ya rarrafo ya lullubeta,dukka jikinta ya saki,wata nutsuwa ta fara zuwar mata,ta lula duniyar bacci me dadi


_sai nace asuba ta gari amaryar muhammad al'ameen_


SAI KUMA MONDAY IDAN ALLAH YA KAIMU,BISSALAM.


End of book


Leave a comment

Post

Comments

nasrahsadiq
Masha Allah,naji Dadi sosai a wa'yannan shafukan ,Allah ya kara basira da hazaka.Amin

13 hours ago


112201018644657456668
Da saura mudai dan Allah iman ta riqe ajinnan yadda ya kamata tunda ya riga yashigo hannu

14 hours ago


rukeebuwangal
Monday yayi Nisa please sister love 😘🥺💕

14 hours ago


jidderh4212
Nima dai har Monday Ina laifin gobe ki bamu Sai weekend aje hutun pls ataimaka Monday. Yayi nisa😭😭😭😭😭

14 hours ago


Load More

Contact Us
Arewa Books Publishers

WhatsApp: 09031774742

Email: [email protected]

Navigation
Home
About
FAQ's
Legal
Privacy Policy
Terms of Service
Social
Facebook
Instagram


Copyright 2021, Arewa Books | ALL RIGHTS RESERVED | Powered by thinkcrypt.io

Shafi na sittin da biyar"
https://arewabooks.com/chapter?id=62d0173df9d9563d0156afa0#:~:text=Report-,KUFAN%20WUTA,SAI%20KUMA%20MONDAY%20IDAN%20ALLAH%20YA%20KAIMU%2CBISSALAM.,-End%20of%20book[7/19, 10:03 PM] Mummyn Yara: 66

Daga can nashi bangaren wayar shima ya sauke,ajiyar zuciya mai nauyi ta kufce masa harda sheshsheqa,tamkar yaron da yasha kuka ya gaji,kowacce gaba ta jikinsa a mace take,cikin ransa yake addu'a da fatan ubangiji ya jarabci iman koda da rabin soyayyarta dake cike a qirjinsa,ya fara takawa a kasalance yana tunkarar ainihin ginin gidan nasa hannunsa riqe da ledoji guda biyu.

"Alhamdulillahil lazi bini'imatihi tatimmus salihat" ya furta a bayyane sanda ya shiga riski parlorn nashi,shuru yake kamar yadda gidan yake,saika zaci babu kowa cikin gidan,ya juya a hankali da direction dinsa zuwa inda dakunan samhan suke.

Da sallama a bakinsa ya tura qofar bedroom din ya shiga,bata amsa ba kamar yadda bata motsa ba hakanan bata amsa ba,sai ya saki qofar ya tako zuwa cikin dakin.

Saman bedside table ya ajiiye ledojin hannunsa yana sake maimaita sallamarsa,still dai bata amsa ba,kanta na lullube da tsadajjen mayafi kalar lace din jikinta.

Baya kadan yaja,yana zuba hannayensa cikin aljihu,ya kuma sake maimaita sallamar,burinsa shine kawai ta amsa,saboda tarin lada alfanu da kuma albarka dake cikin hakan,kodon kasancewar wannan rana da kuma lokaci na farko na tarayyarsu a rayuwa

"Samha" ya kirayeta a tausashe,kamar jira dama takeyi ta yaye lullubin dake kanta,ta dubeshi da idanunta da suka kumbura sukayi kuma jajur dasu

"Me kakeso kacemin ne ameen?,akwai abinda ya rage da baka fada ba"

"Ya salam" ya fada yana fidda hannayensa daga aljihun,sannan ya tako zuwa gabanta ya sake tsaiwa

"Yanzu dukka bayanan da na miki da wanda akayi miki daga gida baki gamsu ba?"

"Wanne bayanai?,na yaudara da cin amana?", Maganar tata ta masa zafi,amma a yanzun dole shine a qasa,kuma hankali da tunaninsu ba daya bane,sai ya sake matsawa gabanta ya tsugunna,ya kama hannayenta ya riqe

"Samha,kada ki bari hankalinki ya gushe daga jikinki,ki tsaya ki nutsu ki fahinci ki kuma kalli komai ta fuskar daya dace...." Zame hannuwan nata tayi ta kuma ja da baya a razane

"Bazan fahimci komai ba,bazan kuma gane ba,abu daya na gane shine ka yaudareni ka kuma ci amanata,a rasa yarinyar da za'a baka sai iman?,yarinyar da nakewa kallon qanwa?,kuma ban san da hakan ba sai bayan an daura auren?,wannan wanne irin munafurci ne?"

"Ya Allah" ya fadi saboda yadda yaji kalmar tayi nauyi da yawa

"Ka fita ka barmin dakina koni na fita" ta fada cikin daga murya hawaye na sauka daga idanunta.

Cikin zuciyarsa yaji tana buqatar space,idan yaci gaba da pushing dinta kan lallai su samu sulhu zata iya fadin maganganun da dukkaninsu ba zasuji da dadi ba,don haka ya miqe tsam,ya cire leda daya daga cikin ledojin ya taka zai fice,yana jinta tana cewa yazo ya dauke ledojinsa tana turosu cikin daga murya,saidai ko juyowa baiyi ba bare ya kulata,ya fita yaja mata qofar ya haura sama zuwa dakinsa.

A nutse ya buda dakinsa zuciyarsa qunshe da tunani da kuma saqe saqe iri iri,baisan wanne irin kishi haka samhan ke dashi ba,koma dai meye shi bazai dauki irin wadan nan sabbin dabi'un da tun daren farko ta fara tsiro masa dasu ba,baiga wani cin amana ko haramci da ya aikata ba,wala'alla tun asali don batasan wace iman a wajensa bane,da batayi abinda tayi a yanzun ba,bayason kuma fayyace mata komai,don ya tabbatar idan hakan ta faru sai taji ita din ba komai bace a wajensa.

Kayan jikinsa ya cire gaba daya,ya shiga toilet yayi wanka,yazo ya shirya kansa cikin wasu pyjamas ruwan sararin samaniya,sunyi matuqar amsarsa,gargasar qirjinsa gaba daya a waje take,ya sanya takalmin dake hade dasu ya dauki wayarsa ya sake fitowa.

Yadda ya barta haka ya sameta,kai tsaye ya nufeta bakinsa dauke da sallama,sai ta miqe tana kallonsa,yana isa gareta baiyi wata wata ba ya dagata cak ya rabata da qasa,take ta fara wutsil wutsil gami da tattata dukka qarfinta tana son qwacewa daga hannunsa,saidai ina,ya nuna mata banbamcin,bai tsaya ba ya jefata saman gado,ya kuma matseta yadda ba zata iya tashi ba.

Kokarin qwace hannayenta daya riqe gam takeyi tana fadi cikin kuka

"Ka sakarmin hannuna,ni ka qyaleni"

"To dama waye yace miki wani abu zanyi miki?" Ya fada a nutse tsaf,idanunsa cikin nata,kunya ta kamata saita ci gaba da borin kunyarta

"Indai kinason na fitar miki a daki to saikin tsaya kin saurareni" ta tabbatar idan bata tsaya din ba qaramin aikine wajen ameen din suyita zama a haka,dole ta rage turje turjenta,ya fara mata magana a nutse

"Zan gaya miki gaskiya ne samha,ni mutum ne da tun asali bame boyon gaskiya ba,komai dacinta ina fadinta,zata yiwa mutum dadi ko bazatayi masa ba.......ima itace mace ta farko dana fara so a rayuwata,kuma wasu dalilai a baya da kuma qaddara Allah ya nufi ba zamuyi aure ba,saidai dai dai da rana daya ban taba cire sonta daga zuciyata ba......a yanzu qaddarar aurenmu ta tabbata,wanda bazan iya wofantar da hakan ba,uwa uba inna da malam....mutane ne masu kima da daraja a idanuna,baya ga iyaye na sune mutane nafarko masu daraja ta farko a rayuwata da zuciyata,sunmin komai,sune suka maidani wannan lameen din da kike kalla a yanzu,jininsu yafi warfin wulaqanci,dake da iman duka matana ne,kuma na aureku saboda kowacce akwai soyayyar da nake mata,kada ki tashi hankalinki akan lamarin iman,kema matata ce kuma abar sona kamar ita...." Kalamai masu dadi gami da kwantar da hankali yayi mata,irin kalaman da suka sauke zuciyarta sosai,saidai kuma tana buqatar tayi shawara kan yadda zata bullowa abun,akwai babbar matsala ace ya auri wadda ya fara so suka rayu gida daya ya hadata da ita,soyayyar farko ba wasa bace,da yawa yawan mutane basa iya daina son wanda suka fara so a rayuwarsu,saidai wani dalili ya dusasheta

"Naji,ka tafi zan kwanta"
"Naji nima zan tafi,amma tashi kije ki wanka ki cire wadan nan kayan na jikinki ki sauya wasu" ya fada yana tsareta da idanunsa dake mata kwarjini da yawa,abu na farko da ya fara jan hankalinta kenan tun farkon haduwarsu.

Ganun da gaske yake bazai tashin ba yasa ta shiga bandaki tayi yadda yace din,ta fito a shirye cikin kayan bacci masu kauri tana dubansa,sai a sannan ya sauko daga saman gadon cikin kasala da mutuwar jiki,ya Sanya slipper dinsa,har yayi taku biyu ya tsaya ya waiwayo

"Da gaske na tafin?" Ya furta yana dubanta,hade rai tayi

"Eh mana" don har cikin zuciyarta bataji ta huce ba,batajin zata iya bashi komai a yanzu,sai abinda ta tattara ta kuma yanke shawara a kai,bata hangi kawo iman yanzu ba,saboda ance mata bata da lafiya,sannan auren ba zata ne,so saboda haka saita jaa zarenta da kyau ta kuma wajigashi sannan,ta yarda da maganganun nan na wasu mata dake alfahari da mutuntakarsu wajen jan ran miji,bata yarda ta sakar masa jikinta ba bare ya moreta da yawa har raini ya shigo tsakani.

Murmushi ya saki yana ci gaba da takawa tare da fadin
"Allah ya bamu alkhairi" abinda take qiyastawa sam shi ba shine a ransa ba,bashi da wani shauqi kwata kwata a yanxun haka,gaba daya ruhi da gangar jikinsa nat wani gun,ya tabbatar da a bigire ko muhallin da zuciyarsa tafi karkata ne,zaiyi wuya ya iya sanya qafarsa ya fita,ya sake tambayarta ne wai koda tana da tsoron kwana a sabon waje.

*****WASHEGARI da cikakkiyar nutsuwa ta farka tayi sallar asuba,wani irin kwanciyar hankali da nutsuwa data jima bataji kamarta ba yana saukar mata,har yanxu dakin dai qamshinsa yake,wanda shi ya tayata kwana yake kuma debe mata kewa.

Ko addu'o'inta bata gama ba ta leqa bushira a falo,sai ta sameta ta gama tata sallar tana a tsaye,ta qarasa suka gaisa bushiran nadan tsokanarta

"Ya kwanan dakin soyayya?" Harararta tayi

"Ke kika sanshi,don Allah muje ki rakani naga innata"

"Daga nan nima gida zan wuce naga tawa innar ba" fuska iman tadan bata

"Haba bushira,ya zaki tafi ki barni don Allah a wannan situation din?" Idanu ta fiddo tana dariya

"Kijimin mata,ki kama mijinki a hannu abun sonki,ga innarki ga malam dinki,ga ya sadiqu amma kicemin haka?,ciwo dai kin warke wallahi me kuma yayi saura?,duk sanda aka tashi kaiki zan dawo qafarki qafata" shuru tayi,ita kanta tasan bushiran tayi namijin qoqari,don a yanzu ta zarta qawa ko aminiya,saidai a bata matsayin 'yar uwa,sannan tabbas ya kamata taje ta huta.

Tare suka jero zuwa cikin gidan,sun tadda baqi sun buga sammako sun kammala shirin tafiya,cikin mutunta juna suka dinga gaisawa,ragowar dangin lamin da suka rage sunata yi mata fatan alkhairi,sai da suka kebe da yaa baraka sukayi magana ita da ita

"Don Allah hajar ki kula da lameen,bashi da kamarki,kuma duk duniya babu matar da zai aura sama dake,mun godewa Allah da wannan damar bata kubce masa ba damu gaba daya,ba ruwanki da lamarin kishiyarki mijinki shine a gabanki,in sha Allah zan dawo nan kusa na hadaku keda lamin din muyi magana sosai,kiyi haquri da kutsen da mukayi miki aka kasa dr naki.....ni dama nasan bazaikai labari ba tunda yace zai kara da dan qanina....ba yabon kai ba" ta qarashe tana dariya,maganar data sanya iman murmusawa,ta sadda kanta qasa tana jin kunyar yaa baraka.

Sai da suka fice duka su da 'yan maiduguri,yaa gana ce kawai ta rage,sai dangin inna daga nijer su biyar,suma sun gama shirinsu,driver dinsu suke jira ya iso.

Cikin bedroom ta cimma inna tana kintsashi mufida na tayata,waiwayowa tayi tana amsa sallamarta,duba daya zaka yiwa fuskar inna kasan cikin farinciki take,wata kyakkyawar fara'a ta sakarwa iman din,hakan yahaifar da farinciki a zuciyarta mai yawa,ta tako cikin dakin tana duban mahaifiyartata,me yafi bin xabin iyaye dadi matuqar babu son rai ko kaucewa addini a ciki?,ina zata kwatanta kallon da take mata a yanzu da kallon data samu sanda ta zabi bin son ranta.

Gaida innar tayi,ta amsa mata cike da kulawa tana tambayarta jikinta

"Da sauqi sosai inna" mufida ta matso tana gaidata,saita saki murmushi

"Yammatan inna kinyi wuyar gani,ni ban ganki ba sam tunda aka fara hidindimun nan"

"Ina zaki ganta tana maqale dani,mutan nijer dai sunce lallai kam mufida ta zama tawa,wai ta juye yanayinmu yanzu" murmushi Iman tayi
"Gaskiya ne mana inna" tana duban mufidan,tanajin dadin xaman yarinyar wajensu,ko babu komai inna tana dame debe mata kewa,hira suka dan taba da inna,ta tambayi malam tace tunda yayi sallah ya fita,maybe shima yana sallamar baqinsa ne,sai iman din ta shiga ciki neman yaagana don su gaisa,saboda bata ganta ba.

A dakin da aka saukesu ta sameta,ita da bushira data gama shirinta tsaf,ta zauna daga gefanta tana gaidata,ta amsa mata cikin kulawa tare da tambayarta jikinta,ta amsa mata da sauqi,itama dai hirar suka dan taba,sakayau take jinta a yau din,bushira ta yowa inna sallama,innar ta cikata da abubuwan alkhairi masu yawa,tayi kamar ba zata karba ba amma inna ta dage saita amsa

"Bari na dauko wayata na rakaki" iman ta fadi tana miqewa,dakinta dake rufe ta buda tashiga,ta laluba wayartata inda ta ajjiyeta sannan ta fito

"Idan kin rakata ki koma can sashen kiyi wanka ki kimtsa tukunna,amarya kike,bai kamaci ki dinga yawo a haka ba" yaagana ta fada tana duban iman din,dole ta amsa da to,amma bataga aibun nan din ba da baza'a barta tayi wankanta a nan ba.
[7/19, 10:03 PM] Mummyn Yara: 67

Duk da cewa ba datti dakin yayi ba,amma saita samu kanta da tsaiwa ta sake kintsa dakin da kyau,ta kunna wayarta saidai ta nuna low battery,ta duba inda taga charger a dakin ta jona ta sannan ta miqe tana duba agogo,har tara saura tayi,sai ta fidda kayan jikinta ta daura towel din jiya a jikinta ta shige bandakin.

Ruwa zafi me yawa ta tara,ta jima cikin bandakin tana wanke jikinta,ita da kanta ma take mamakin dadewar data yin,daga qarshe ta daura towel din ta soma nemam brush dinta,babu cikin kayan,dole wanda ta gani a toilet din ta dauka tayi amfani dashi,ta hada da alwala sanna ta maida komai a muhallinsa ta nufi qofa.

Wani yanayi me dadi ne yake sake ratsata,iskar dake kadawa cikin dakin tana fifita jikinta dake dauke da damshin ruwa,ba shakka babu abunda yafi nutsuwar ruhi dadi,haqiqa babu Abinda yafi kwanciyar hankali dadi,ta taka a hankali xuwa gaban madubin,tana sake qarewa mayuka da turarukan dake saman madubin kallo wanda a daren jiya bata yi ba,da daya da daya take dauka tana dubasu,dukkansu designers ne masu matuqar tsada,ta ajjiye tana sakin murmushi sannan ta zabi mai daya da niyyar shafawa,saidai turo qofar da akayi ya dakatar da ita.

Ta cikin madubi ta hangeshi,yayi tsaye daga bakin qofar,idanunsa suka sauka saman farar fatar bayanta wadda keta qyalli,ta kuma bayyanar da kyawun surar mamallakin jikin.

Tsorota tayi,sosai zuciyarta ta buga,saidai kafin tayi kowanne motsi yaja qofar ya rufe mata,hakan ya sanya ta fasa shafa man,ta isa inda ta ajjiye kayanta ta dauka ta fara zurawa,lallausar atamfar england light green mai adon dark green da fari,dinkin half bubu da yayi matuqar yi mata kyau da fidda shape dinta,sai data gama saka kayan sannan ta koma fa shafa manta,tabi jikinta da turare,tana tsaka da fesawar aka sake turo qofar,shi dinne dai,sanye da wata danyar shadda dark ash da aka yiwa aiki da baqin zare,rigar iyakarta gwiwarsa,sai gajeran hannu daya fidda farin yalwataccen hannunsa dake da albarka gargasa,takalminsa half cover ne baqi mai asalin tsada,sai sheqi yakeyi kamar ba'a taka qasa dashi,hannunsa dauke da wani madaukin kayan abinci dake dauke da tambarin wani mai tsada kuma shahararren gidan abinci,qamshinsa ya fara gauraye dakin,wani irin qamshi data saba ji daga gareshi kadai.

Da tattausar muryarsa da ta sake zama so cool yayi sallama,fitar sautin furucinsa ya shiga har cikin qashi da bargonta,uwa uba adonsa daya tafi da dukka hankali da tunaninta.

A nutse ya tako,ya jawo wani table ya dora abincin a kai,daidai lokacin data furta
"Sannu da zuwa....."
"Yauwa sannu" ya amsa mata yana sanya hannunsa tsakanin madubinsa,ya fiddo wata lallausar darduma mai kyau ya shimfida,zare takalman qafarsa yayi ya hau kai ya zauna

"Qaraso da kayan abincin can" ya fadi yana duban fuskarta da tayi wani fayau,dankwalin atamfar data masa Vshape ta yafashi saman kanta yanaga zamewa,lallausan gashinta daya fara daga gaban goshinta yanata fitowa tana sake gyara dankwalin.

A nutse ta fidda komai ta budeshi

"Ina kwana"ta gaidashi tana niyyar miqewa,fuskarta na kallon wani waje daban

"Zauna kici abinci" ya bata umarni kai tsaye,sai ta koma ta zauna din sosai kamar yadda ya buqata.

Plate daya ya zara ya zuba abincin,sai ya qara cokali daya,ya kuma sakashi a tsakiyarsu

"Bismillah" ya fada yana fara cin abincin a nutse abinsa,sai ta basar dashi kamar ba da ita yake ba,,bata ko motsa ba,illa wasa da take da yatsun hannunta,tabtasa sukuni da sakewa gaba daya,yadda yake jefa mata kallonsa da yanayin kusancin zaman nasu gaba daya ya takurata yanayinta,mamakin abinda ya fiddoshi daga gidansa da wurwuri haka takeyi,a matsayinsa na sabon angon da jiya jiya ya shiga dakinsa,uwa uba kuma yazo ya buge da cin abincin safe a waje,yaa sadiq kam ko motsinsa babu,don ko dazun data shiga cikin gida tanajin ana kiran wayarsa ya fadi inda ya aje key din setting room din malam amma wayar tasa a kashe.

Sai da yayi loma kusan biyar sannan ya sake motsa bakinsa a nutse

"Bismillah,me mike jira?" Ya fadi yana kafeta da idanunsa dake dauke da wani magnet mai matuqar qarfi da kuma tasiri,saita motsa a hankali ta dauki spoon din ta fafa juya abincin.

Duk bayan wasu sakanni sai ya jefa idanunsa a kanta,wani abu na motsa zuciyarsa yana kuma tabata ta kowanne sashe,ita ta fara janyewa,ya bita da kallo sannan ya tsiyaya mata tea mai zafi ya miqa gabanta,ya dauki cokalinsa yana ci gaba da cin abincin.

Bai wani jima ba shima ya kammala,ya miqe ya dauki tissue yana goge gefe da gefan bakinta,takawa yayi a hankali zuwa inda ta ajjiye magungunanta,hannayensa ya zuba cikin aljihunsa yana qare musu kallo,ta motsa kadan itama tana kai kallonta ga inda yake,nauyi da kunya suka kamata,tayi ajiyar pants nata a wajen wanda ta cire,ya riga yaga koma meye bata da abinyi illa qas da kanta da tayi

"Idan kin tashi ki daukeshi ki wanke" taji ya fada sanda yasa hannunsa yana matsar dashi gefe a nutse,kamar qasa zafa tsage ta shige haka taji,duka yaagana ce ta jawo mata wannan aika aikar.

Takowa ya sakeyi zuwa inda take bayan ya balli dukka magungunan,yadda yayi mata jiya a asibiti yanzunma hakan yayi mata,ya shinfide mata tafin hannunsa,ta dinga daukan magungunan da daya da daya tana sha,har zuwa sanda ta dauki na qarshe,dai dai lokacin da akayi knocking.

Kamar dazu yanzun ma baiyi magana ba,ya bude qofar ya karba abinda zai karba,maida qofar yayi a hankali ya rufeta,wannan karon harda murza key,abinda yaja hankalin iman kenan,ta daga idanunta tana duban qofar,sannan ta sake maida duban nata ga lamin din sanda yake dawowa ciki.

Da mamaki tabi hannunsa dake dauke da wuqa da kallo,table din daya dora abinci a dazu ya janyo zuwa gabanta,ya dora wuqar daketa qyalli akai,yayi taku biyu zuwa baya,yasa hannayensa ya fara balle maballan rigarsa,sannan ya zareta ya jefar,farar singlet dinsa ta bayyana,a hankali itama ya zareta ya jefar da ita daya bangaren,take faffadan qirjinsa mayalwaci mai cike da albarkar gargasa ya bayyana,gami da damtsensa dake nuni da alamun qarfi da yadda motsa jiki ya zaunar masa.

Tsoro fargaba da kuma daurewar kai suka kama iman din sanda yake takowa gabanta,idanun nan nasa akanta,wani abu mai nauyi da qarfi yana gilmawa ta cikinsu Gwiwoyinsa ya sanya a qasa kamar wanda zaiyi kneel down,ya dauki wuqar ya buda tafin hannunta dake cikin hannunsa ya sanyata still idanunsa nakan iman wadda tsoronta da fargabarta suka ninka na baya,saita kalli wuqar kana ta kalleshi

"A wancan karon,kin furta cewa zaki kasheni muddin aka aura miki ni,sai gashi a wannan karon ma bata sauya zani ba.....irin wancan auren akayi miki....bansan wanne alwashi ne a ranki ba wannan karon,idan irin na baya ne,gani nazo da kaina ki cika burinki!,saboda na sani qiyayya bata gushewa daga zuciyar wanda ya furta qiyayya haka ta sauri.....,ki aikata abunda yake ranki iman!!!" Ya fada da wata kakkausar murya mai madaukakin sauti,idanunsa na sauya kala,da alamu tun daga zuciyarsa abun yake motsa masa.

Sosai ta rude ta kuma diririce, take idanunta suka hada qwalla wadda bata iya tsaiwa ga iya ramin idanunta ba sai da suka gangaro saman fuskarta,wacce magana ce haka me muni lamin din yakeyi?,shi baisani ba?,baisan shine farincikinta ba?,baisan shine burinta dama mafarkinta gaba daya ba?,baisan shine duk wani motsi tashinta da kwanciyarta ba?,waye xai tayata tayi masa wannan bayanin?,waye zai tayata fahimtar dashi?,baya ganin komai rubuce saman fuskarta ne?.

"Na baki dama ki aiwatar da nufinki!!,ki cika burinki!!" Ya fada a tsawace yana matsa hannayenta,furucin daya ida rudata,ta fusge hannunta da sari takuma yi wurginda wuqar,
"Bazan iya ba" Ta fadi itama da madaukakin sauti gami da runtse idanunta gaba daya kamar wadda taga wani abun tsoro,kuka mai matuqar qarfi yana qwace mata

"Saidai idan har ni din na maka kutse cikin rayuwarka.....na datse maka dukkan wani tanadi da kuka yiwa kanku samakon tallata da aka yi maka aka maqala maka ni,kana kallona kuma a matsayin matsala.....a yau na baka dama ka kawar dani nima....hannuwana ba zasu taba iya dauke numfashin wani dan adam ba,dan adam dinma dake da girma da kima da kuma soyayya daga zuciyata" ta fada da qarfi tana sauke kanta qasa,sabbin qwalla masu zafi suna keta idanunta suka fara gudu suna sauka saman cinyarta,ba shakka furuci masifa ne,shine abu guda dayan da yake da qarfin gina ko ruguza komai.....komai girmansa,idan ya fita ya riga daya fita,ta tabbatar kalmace mafi ciwo data furtawa lamin,kalmar da da alama ta tsaye masa a rai matuqa,kuma kalma mafi girma da zaka nunawa maqiyinka girman qiyayyar da kake masa,kalmar kisa.....idan ta tuna tana jin kanta kamar ba ita bace a wancan lokacin.

Kamar me sauraren bugun zuciyarsa haka ya runtse idanunda yayi shuru....kalmominta na qarshe sun dagargaza gami da narkar da wani abu daya tsaye masa a wuya tsahon shekaru,yana jin yadda abun ke narkewa yana wucewa,yana da yaqini yana kuma da kokwanto dukka akan iman din,saidai a yanzu ya samu zallar yaqinin da babu shakka,soyayya yake buqata daga gareta,kalaman da zasu sake tabbatar da kuma jaddada matsayinsa kai tsaye....bawai nuni ko ishara ba.

A tausashe taji an kama dukka kafadunta guda biyun an miqar da ita tsaye,sai a sannan ta bude idanunta da suka jiqe da hawaye suka rage kaifi da tsahon zara zaran eye lashes dinta,haduwar idanuwansu waje guda ya haifarwa da kowannensu wani babban al'amari cikin zuciyarsa,saqon da kowanne ya sakarwa dan uwansa ba tare daya sani ba ta hanyar idanunsa ya isa ga qirji yakuma zarce cikin zuciyoyinsu kai tsaye,tsaiwarsu a hakan ya mata wani irin kwarjini mai yawan gaske,ya lameen tsaye a gabanta,dukka surarsa a bude,abinda bata taba gani ba kenan daga gareshi tunda ta mallaki hankalin kanta

"Ita zumar asali har abada tana nan a matsayin zumarta,har kullum binta ake a nemota....bata buqatar a tallatata,ba maɗi bace da sai yasha talla kafin ya samu masu so da kuma masu buqatan saye,abace mai darajar da har kwanan gobe saidai abita anemota,koka tashi neman nata....wuyar samu take,duk duniya nafi kowa sanin darajarki hajar....cikakken namijin da ya amsa sunansa,yana amfani da qwanjinsa da kuma fikirarsa wajen samawa kansa abindan yakeso,abinda kuma ya dace da muradinsa da mafarkinsa,baya jira azo ace masa gashi,koda yaushe farauta yake yaga ya samu,muddin wannan abun nada kima da daraja a wajensa" wasu irin kalamai masu cike da tarin hikima,gefe daya kuma suna fidda zallar kima da darajar da take dashi a zuciyarsa,ta wani fannin kuma yanason bayyana mata shine ya nema aurenta kenan da kanshi?.

Bata gama wannan tunanin ba taji ya sauko da hannuwansa daga kafadarta zuwa nata hannayen,ya kamasu ya riqesu a tausashe cikin nasa hannun yana murxawa a hankali,idanunsa cikin nata yana saukar mata da wasu abubuwa masu nauyi da girma,wanda take taji qafafunta sun soma laushi,kamar ya fahimci hakan,sai ya hade gap din dake tsakaninsu,ya jawota zuwa cikin jikinsa,yayi mata kyakkyawan masauki a qarjinsa,kana ya sanya hannayensa yayi mata qawanta,al'amarin da yaso wucewa da numfashinta,dumin jikinsa ya fara ratsa fatar fuskarta tare da wani qamshi na musamman da bata ta jinsa daga jikinsa ba,da alama gashin dake qirjinsa turare na daban yake masa amfani dashi ba wanda yake sanyawa a jikinsa gaba daya bane, tsigar jikinta ta zuba,ta lumshe idanunta,tanajin wata nutsuwa da rahama daga zuciyarta,yayin da a nashi bangaren tudun jikinta ya sanyashi dauke wuta na wasu sakanni,saidai dole su qarasa maganar da suka dauko,saitin kunnenta ya fara magana qasa qasa

"Da qyar na rayu iman....da qyar na kawo yau,saboda maganganunki sun zubamin dafin da ya dinga cin jiki da zuciyata kullum,nabar qasar nan amma na tafi da tafkeken tabo da kuma memory na dukka abinda ya faru,naci wuya a makaranta.....na gaza fahimtar karatun da najeyi,har sai dana fara fuskantar barazanar na rasa damata sannan na farga,ko sau daya ban taba warkewa daga ciwon da yake zuciyata ba,ban warke ba iman sai ayau din nan,duk da haka na tabbatar an barmin tabon da bazan manta dashi ba,nayita tuhumar kaina.....me yasa bazan cireki daga raina ba bayan a yanzu kedain matar wani ce?,na gaza gano amsa,darare da yawa sunxo sun wuce ta gaban idanuna sanda nake zaune ina tuna tashinmu zuwa rabuwarmu dake,barci ya qauracewa idanuna,nayi kuka nayi kuka har bansan adadi ba,na zana na binciki kaina laifina da kika gaza karbata amma na rasa,sai wasu uzururruka da zuciyata keta baki,ta kasa gano laifinki ko daya,ina can labarin mutuwar aurenki ya ruskeni,nayi matuqar baqinciki bazan boye miki ba....saboda inda ace nike da ikon rubuta qaddararki.....zaki tsallake kalmar zama bazawara har qarshen rayuwarki,bai kyautu nayi murna ba,saboda mutuwar aure ba wasa bane,sannan uwa uba a sannan gaba daya duk wani burina dake kanki ya mutu murus,zuciyata taci gaba da kallonki a matsayin qanwata,kamar dai matsayinki na daa can can,wani sashe na zuciyata na qaryatani,ni kuma ina sake gasgatawa kaina hakan,komawarki makaranta ni na tsaya akai,na tursasa sadiq wanda ke fadin shi har yanzu bai sauko ba,ko.meye ya faru dake ke kika jawa kanki,nayi masa gori sosai na kuma fada masa ganganu,har yaso yaji haushina,daga qarshe dole yatsaya akai kamar yadda na buqata.

Sanda na dawo na tadda komai na tafiya yadda ya kamata naji dadi sosai,na karanci kunya da nauyin haduwa kikeji dani,abinda yasa a wancan lokacin nakiraki nayi magana dake kenan,nayita karantarki a fakaice ba tare da kin sani ba,zuciyata na gaya min akwai soyayyata a zuciyarki,Allah ya sani naso na fara jin daga gareki koa jirwaye ne kiyimin amman banga wannan ba,katsam kuma saina fahimci akwai dr ahmad cikin rayuwarki,kina kima bashi girma da kima qwarai da gaske,na shiga damuwa da dimuwa sosai amma nayi qoqarin cinye abata,saboda wani sashen na zuciyata ya sake shiga shakkun har yanzu da gasken baki sona,wannan yasa nayi shawarar jayewa na sake baki damarki.

Ban qara shiga rudani ba sai randa malam ya taramu,a ranar nazo da qwarin gwiwata na gabatar masa dake saboda sauyin yanayi dana fuskanta daga saman fuskarki,ga mamakina sanda tambayar tazo kanki sai kika gabatar da dr ahmad a matsayin zabinki,wannan ya qarasa kashe dukka wani buri nawa da fatana....ko ranar da muke magana da yaa baraka a bayan gida naga tahowarki,daga ke har ita ba wanda yasan na ganki,amsar dana bata sanda take nunamin asararki da zanyi.....ina sane na bada ita,na zaci daga bisani zan sake ji daga gareki,ga mamakina sai naga kin sake janyemin gaba daya......iman" ya kirata qasan maqoshinsa,yatsunsa na tsakiyar nata yatsun,muryarta na rawa ta amsa masa

"Ba girman kai ko wani abu yasa nayita baki wannan damar ba,dalilina.....na yiwa kaina alqawarin bazan taba tilasta wata mace ko a tilasta mata zama dani ba,saboda zaman aure anyishi ne saboda farinciki da jin dadi mai dorewa,dakuma samar da tsaftatacciyar zuri'a....nayi qoqarin mantawa dake amma yaa barakata fitittike,tayi tattaki har maiduguri takai qarata wajen yaagana,yaagana ta nemoni,takuma ce zata yi magana da malam,koda iman bata sona a wannan karon bata isa tsallakewa aurena ba.......ban yarda na zauna anema min soyayya ba iman....idan nayi haka na zama lusari,ban kuma yarda da kaina ba,don haka na nemi su barmin komai na daidaita al'amuran bisa tsari,kaina tsaye na nema dr ahamd,yaso ya qi,amma daga bisani daya fahimci lallai zai auri gangar jikinki ne kawai.....zarrarata tafi tashi,....kuma ninafi cancanta dole ya sallamamin.

Ko yaushe rana da zata fito ya fadi dani kike musayar text da sabuwar number da a wajenki dr ahmad ne" a sannan daga kanta tayi tana dubansa,kamar dama ya shiryawa hakan,idanunsa na cikin nata ya dage girarsa

"Yes,na samu nutsuwa sosai,saboda na samu kalaman masu tsada daga gareki,duk da ke a wajenki ahmad ne" kunya ta kamata,ta maida kanta tana son tunano dame dame ta taba rubuta masa?,tabbas a lokacin ta shiga mamaki matuqa na yadda ta dinga ji da ganin sauyin kalamai daga wajensa,wasu irin kalamai dake nuna zallar qauna zuwa ga abokin soyayyarka,kalamai masu tsada da bata taba jinsu a wani waje ba,ashe yaa lamin ne?,amma fa tafka abun kunya

"Karki damu,a yanzu ina da buqatar ninki wadan nan,abinda yasa nace aboye komai a je a zuwan ahmad ne,saboda zuciyata na ganin kamar zan sake rasaki,a wannan karon kuma inajin idan na sake rasakin bazan iya daukar hakan ba,me yiwuwa duka makusantana nima su rasani" dagata yayi daga jikinsa,ya soma durqusawa a gabanta,saita kasa ci gaba da tsaiwa itama ta sulale ta bishi,fuskarta ya kama ya sanya a tsakiyar tafukan hannayensa

"Koda baki sona iman.....nayi alqawarin dasa miki soyayyarki a zuciyata,soyayyar da zata hanaki sukuni...."
"......barema ina maka son da ban taba jin koda labarin irinsa ba" bai shirya ba yaji saukar kalaman,idanunsa ya lumshe yaja numfashi kamar zai shide,kunyar barin zancen da tayi yasa ta kama tafin hannunsa ta boye fuskarta a cikin murmushi yana qwace mata,a hankali ya cusa daya hannun nasa saman sassalkan gashinta da yake tsone masa idanu shekara da shekaru ya fara motsashi,yanajin laushin daya jima yana hasashen yana dashi a idanunsa yau a hannunsa.......
[7/19, 10:03 PM] Mummyn Yara: "




Menu
Dashboard
My Library
Create Story
Home
About us
FAQ's
Privacy Policy
Terms of service
Logout

KUFAN WUTA
Chapter 3 · 0% Book details