Chapter 69
Kufan Wuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 11 min read
Shafi na sittin da takwas
68
Har cikin qashi da bargonta takejin yawon da hannun nasa yakeyi saman kanta,abunda ya sake iza wutar dake zuciyar kowannensu
"Kin shirya tafiya gidana,gidanki gidanmu?,na gayawa yaagana?" Qanqameshi tayi tana girgiza kanta alamun a'ah
"Pleaseeeeeee" yaja kalmar data sauka kai tsaye a qwalqwalwarta ta baza wani yanayi a sassan jikinta daya sanya ta sake qanqameshi,so yake ya rikita mata lissafinta gaba daya da alama,zatafi kowa son hakan a yanzu,amma dole ta kame kanta,uwa uba koda taje gidansa a yanzu sai tayi jira kwanakin samha sun qare sannan ya iso gareta
"Ina buqatar tozali dake kowacce rana cikin qarqashin inuwar gidana..... please queen,ki gaya musu kin warke" yayi maganar yana matseta sosai a jikinsa,bawai sha'awa kawai ba.....wata qaqqarfar qaunarta daya dade da sakayata a wani lungu me zurfi na zuciyarsa saboda tunanin zamantowarsa looser akan soyayyar iman din a yanzun take fidda kanta
"Bazan iya gaya musu ba"
"Ni kin bani dama na gaya musu?" Murmushi ta sake,gani take kamar bazai iya ba,don haka kanta tsaye tace masa eh,sai ya zame jikinsa a hankali daga gareta,ya fara takawa zuwa qofa.
Idanu ta zaro sosai ganin fita zaiyi da gaske,uwa uba kuma babu riga a jikinsa ya zubdasu a wajen
"Yaa lameen" waiwayowa yayi yana dubanta da idanunsa da suka sauka kala
"Riga fa" duban jikinsa yayi,har ga Allah ya manta ba riga a jikinsa,dumin jikinta ya ratsashi sosai har bayajin sanyin iskar dake kadawa,iska mai zafi ya furzar kana ya saki murmushi,da hannu yayi mata nuni kan ta kawo masa,saita maida masa martanin murmushin ta juya zuwa inda ya yasar da rigar,yabi qugunta da kallo yadda suke juyawa kamar tana yine da gangan,yafi kowa sanin bada gangan bane,haka halittarta take,ta qaraso inda yake ta miqa masa,sai ya hada da hannyenta ya riqe,ya sanya daya hannun a hankali ya kama qugun nata ya riqe yana dubanta
"Ranar dana fara ido hudu da wannan abun ban iya barci ba,nayi mafarki har babu adadi,inda na godewa Allah ranar sadiq ya tafi borno,ni kadai na karbi punishment dina,da lallai an tafka abun kunya,tun daga ranar na canza miki yanayin dinkinki zuwa dogayen riguna,amma duk da haka ban tsira ba,saida wani ya qyallomin ke,bazan taba yafe masa ba".
K'as tayi da kanta,karon farko tausayinsa ya kamata,ko meye ita ta jawo masa,saidai ta godewa Allah daya tsare mata abunda yafi komai tsada a rayuwar kowacce diya mace,ya barshi ga lamin din
"Kayi haquri ya lameen,ka yafemin don girman Allah"
"Shshshsh.....qaddararmu kenan,ba wanda kuma ya isa ya tsallakewa qaddararsa.....ya wuce,ni dae mu manta gaba daya kin taba kasancewa halalin wani,tunda dai na samu gundarin hajar dita shikenan.....Taimakamin na saka rigar please,kin tafi da duk wani kuzarina.....zan iya ci gaba da fita aiki kuwa nan gaba?" Ya fada yana langabe mata,qaramin kurmushi ta saki,ta qara matsowa dab dashi,sai ya riqeta sosai ya shimfida mata qafafunsanya jata ta takasu,abinda yadan qara mata tsaho kenan,ya saka hannayensa ya zagaye bayanta dasu,qamshinta na bugunsa duk sanda ta daga hannunta da niyyar gyara masa rigar,a haka ta taimaka masa ya gama sawa sannan taja da baya,sai a sannan ta maida masa amsar maganarsa ta dazu
"Kai dake da mata biyu kaga fita ya kamaka dole" agogon hannunsa ya kalla,sai a sannan ya tuna da samha har ga Allah,duk da cewa sanda zai fito basiyi rabuwar dadi ba amma dole ya dubata,a matsayinta na baquwa cikin gidan dama unguwar gaba daya,ya laluba aljihunsa ya ciro wayarsa,ya taras da miscals na mutane,har ya dinga mamaki ya akayi baiji shigowar kiraye kirayen nasu ba,da gaske iman ta musamman ce kamar yadda zuciyarsa tasha gaya masa.
Baibi takan kiraye kirayen ba ya fara neman number samha,sau uku yana kira bata daga ba,saiya maida wayar aljihunsa,iman bata ankara ba taji yayi sama da ita
"Bacci nakeji,muje ki tayani na rageshi,nafi samun qwarin gwiwar yiwa yaaganan bayani" facin din juna suke,ya zubawa fuskarta ido kamar yadda itama take kallonsa,kusanci da wani yanayi na musamman ya wanzu a tsakaninsu,kowa na sake kallon kyau da kyautar da Allah ya yiwa dan uwansa,wani shauqi na fusgar kowannensu,wata magana yake gayawa iman din can qasa,da alama wani sirri mai nauyi yake furta mata,wanda har yasa ta gaza ci gaba da kallonsa,ta sadda kanta qasa,fuskarta na fitar da qawataccen murmushi,baiyi qasa a gwiwa ba ya tattaro cikin jikinsa gaba daya kamar xai maidata cikinsa,ajiya zuciya da kuma hamdala na kubce masa lokaci daya.
A hankali bacci yayi awon gaba dasu gaba dayansu,wani irin bacci mai matuqar dadi da nutsuwa.....
Ya rigata farkawa,hakan ya bashi damar kallonta yadda ransa yakeso,indai zai yiwu da an bashi matarsa ya wuce da ita,motsawar da yayi da niyyar sauka ita ta sanyata farkawa,saidai ta kasa motsawa saboda kunyar yadda ta jita a jikinsa kane kane,waiwayawa yayi ya sake kallonta,yadda yaga fatar idanunta suna rawa ya tabbatar masa ta tashi,sai ya saki murmushi,ya duqa a hankali yayi kissing goshinta
"Time for salat,kada mu makara" ya qarasa fada yana sauka din,kana ya wuce toilet.
A hankali ta bude idanunta ta saukesu a gurbin daya tashi,ba iya wajen ba,hatta da jikinta yabar mata qamshinsa mai yawa,miqewa tayi taja dankwalinta ta rufe kanta,dai dai sanda ya fito fuska da hannuwansa suka akwai lemar alwalar da yayi,yana sauke hannun rigarsa da ya nannade saboda kada ya jiqe.
Da idanu ya bita tamkar wani tsohon maye,ta wuce ta gabansa ta qarasa toilet tana jin mugun nauyinsa,ya saki qaramin murmushi cikin zuciyarsa yana fadin
"Daga dan wannan abun?"bugun zuciyarsa gaba daya ya sauya daga sanda suka kwanta shida ita a shimfida daya,yadda dumin jikinsu yake ratsasu na junansu haka wata sabuwar soyayya ta dinga huda kowannensu,tsohuwar shaquwar dake tsakaninsu ta motsa kanta da kanta.
Gefan hannun damansa ta tsaya ya tayar musu da salla jam'i shi da ita,bai tsawaitata sosai ba kamar yadda bai gajartata ba,suka sallame,kowa yayi addu'o'insa na bayan sallah sannan ya miqe yana dubanta bayan ya saka takalminsa
"Muje ki rakani mu gaisa dasu,bamu gama gaisawa ba na shigo ta nan" kunya da nauyi suka kamata,batasan da wanne ido xata kallesu ba,amma dole ta laluba dan kunnenta data gani gefan pillow dinta wanda batasan ya akayi suka cire ba,tadai san dasu ta kwanta,ta fara sanyasu,saidai gaba daya a diririce take saboda yadda yake ritsata da kallonsa,ita dai tasan ba dabi'arsa bace kallon,amma ya zuwa yanzu ya canza.
Bataji tahowarsa sai saukar hannunaa data ji saman nata hannun,jikinsa yana gogarta kadan kadan,zame hanunta tayi ba shiri har dan kunnen nafaduwa,ya duqa a nutse ya debosu,ya kama kunnen nata yana saka mata,ya sanya ya bamesu,saiya tura bakinsa gefen kunnen yana ce mata
"Dama can tun asali nike saka miki dan kunne,lokacin kina mitsitsiyarki kin tuna?,eheennn,daga yanzu aikina ya dawo gareni" sai yaja da baya yana gyara zaman hular kansa,yayin da tayi mutuwar tsaye a wajen saboda yadda numfashinsa ya hade da kalaman ya shige mata kunne gaba daya,cikin jarunta dason nuna dakiyarta ta bude idanun nata saidai juya masa baya tayi da sauri ta kuma nufi qofa.
Bai dakatar da ita ba,a haka suka tafi,saidai tayi nadama,ta gwammace jerawa sukayi,saboda yadda takeji a jikinta yana qare mata kallo ne har zuwa sanda suka isa sashen.
A kofar kitchen ya samu inna,cikin matuqar girmamawa ya gaidata
"Ya lameen.....naga shigowarka fa,inata nemanka,naje sashenku inata bugawa baka buden ba" cewar mufida cike da quruciya,kunya ta kamasu su duka,har innar,da sauri iman tayi gaba zuwa dakin yaagana,yayin da lamin ya shafa kanshi yana son basar da zancan,itama innar gaba tayi,wani mayalwacin farinciki yana ratsata,irin farincikin da kowacce uwa keji sanda ta kalli diyarta a tare da ita da managarcin miji,tasan da shigowarsa,sabida baqin da tayi sun gaya mata,amma jin sashensu ya nufa kuma tatabbatar iman nacan yasa bata nemi kowana cikinsu ba,yaagana ce keta qorafin saita qwanqwashi kawunan ja'irai,daa anata fama da kowa a cikinsu ashe gulmace,data sani tabar 'yan banxa kowa yaji a jikinsa,taga inda kowa zaikai soyayyar tashi,itadai inna murmushi kawai takeyi,don bata da amsar data wuce murmushin,farincikin dake ranta Allah ne kadai yasan yawansa.
Batasan malam yana dakin suna magana da yaagana ba sai data shiga,cikin jin kunya ta zube tana gaidashi tun bata qarasa shiga ciki ba,tana addu'ar Allah yasa lamin ya wuce kada ya biyo bayanta,malam ya amsa yana tambayarta jikinta
" Da sauqi malam" ta amsa masa tana duban qasa
"To alhamdlh,dama abinda nake jira kenan,qaraso ciki hajar,dama inason magana dake" sum sum ta miqe zuwa cikin,yaagaba da farinciki itama ke ratsata ta bita da kallo
"Ja'ira,kamar wata ta Allah" ta fada tana jefa mata harara,gabanta ya fadi,Allah yasa kada ta titsiyeta gaban malam din,don ta fuskanci 'yar ba ruwana ce itama yaaganar,Allah ya taimaketa daga haka bata qara ba.
Tana zama lamin din ya shigo,kunya ta kamashi,shima ya samu waje ya zauna kamar yadda malam yasa iman din,maganganu yayi musu masu yawan gaske,wanda kusan sunfi karkata ga iman din
"Kada ki bamu kunya iman,ubangiji shine yasan manufarsa da ya juya al'amarin yazo ahaka" abinda tafuskanta shine har malam su yagana suka ninke,shi da ita ne basusan abinda ke faruwa ba sai data fashe.
Godiya sukayi masa gaba dayansu,musamman lamin wanda kamar zai shige qasa,malam din ya miqe yana duban yaagana
"Yaaya,inaga tunda ta warware ai zasu iya wucewa gida koda zuwa anjima ne" wani dadi ne ya kama lameen,kamar ya tashi yayita shiwa malam albarka saidai babu dama
"Ba matsala,idan ma tafiyar bata samu yau ba gobe ko jibi idan ta sake warwarewa saisu tafi,kafin nan an sake qarasa sauran kintse kintsen da ba'ayi ba"
"Yau din dai yafi dacewa.....ni xan fita,sai na dawo" dukkansu suka hada baki wajen yi masa a dawo lafiya,ya fice ha barsu,zuciyar lamin a dagule,me yasa yaagana zata hanashi iman dinsa alokacin da yafi dacewa ta kasance dashi,a yanzun da ya tabbatar sa samun iman din gundarinta,sai yakejin kamar bazai iya nisa da ita na awa guda bama.
Ficewar malam din yasa yaagana ta dawo da hankalinta kanshi
"Bana nufin hanaka iman....saboda gaba dayanmu a yanzu burinmu shine ta kasance cikin dakinta,akwai dalilin da yasa nakai abun zuwa jibi,kayi haquri Muhammad" murmushi ya sakewa yaagana din,bashi da yadda zaiyi bashi da kuma da zarrar yin jayayya da ita,yafi kowa sani baya ga yaa barka itace mutum ta farko datafi kowa son tarayyarsa da iman din.
Miqewa yayi yana cewa
"Zan wuce yaagana,sadiqu har yanzu bai shigo ba"
"Uhmmm,wannan,kada ma ka sanya ran ganinsa a yau,jiya sai daya gamamin iskanci sannan yatafi,bai tadda kakannin ba ni sai ya maidani kakar tasa" murmushi yayi mata ya sanya hannunsa a aljihu ya ciro rafas na 200 sababbi,ya jima yana ayyana irin alkhairin da zaiwa yaagana amma ya kasa ganin me yafi dacewa da ita,ya ajiye kudin a gabanta yana mata sallama
"Dawo nan ameenu ka dauki kudinka,meye haka?"
"Ayi mana addu'a yaagana" abinda ya fada kenan ya sanya kansa ya fice.
Ajiyar zuciya yaagana ta saki
"Tashi ki rakashi,idan kin dawo ki shigo inason ganinki" tsam ta miqe tabishi kamar yadda yaaganan ta umarceta,cikin zuciyarta take jin batason yin nesa dashi.
Kamar yasan da fitowarta kuwa ta sameshi zaune cikin motar,yadan kunnata tana warming kanta,duka qofofin gaban a bude suke,saita shiga seat din mai zaman banza a hankali,tana shiga yasa hannu da hanzari ya maida murfin motar ya rufe.
Ya kwanto jikinta sosai sanda zai rufe murfin,koda bayan ya rufe din bai dagata b,ya danne kusan rabin jikinta,idanunsa ya zuba cikin nata yana aika mata da kallo mai nauyi da ajjiye saqo a qwaqwalwa da zuciya wanda zaiyi mutum ya manta irin wannan yanayin.
Bai iya cewa komai ba sai morewa kallonta da yayi na kusan mintuna goma,sai da yaji ya gamsu don kansa sannan ya kama tafin hannunta yayi kissing dinsa,ya hada da goshinta,sannan ya nutsa hannunsa a hankali zuwa qugunta ya riqeta sosai
"Kiyi matuqar kularmin da kanki iman,kwanakin da yaagana ta dibamin sunyi yawa,amma tafi qarfin haka a wajena"kanta ta jijjiga tana murza tafin hannunta saitin inda yayiwa kiss din
"Ko bai isa ba na qara miki?" Dan zabura tayi,shi wai bayajin komai ne?,baisan nauyinsa takeji ba,ya lameen din da takewa kallon yaya a wajenta yau shine yaketa mata wadan nan abubuwan?,kamar ya karanci abinda ke ranta ya sakar mata wani tattausan murmushi,ya fidda hular kanshi ya ajjiye
"Ki tsammaci abubuwa masu yawa da suka fi wadan nan zafi.....na yadda bakisan komai a soyayya ba iman,banga abinda kika iya ba,dole na bata lokacina na baki horo na musamman" saiya buda murfin motar,ya zagayo side dinta ya bude mata ya matsa gefe ya bata daman fitowa.
Tamkar makaho da dan jagoransa haka ya sanya hannunsa cikin nata,bai saketa ba sai daya kaita qofar parlor sannan ya koma,kasa wucewa tayi,ta labe ta bayan labule tana hangensa,cikakken gentle man din da a yanzun ya zama mallakinta,bata bar wajen ba sai daya shiga motar ya tayar.
Tana juyowa wa zata gani?,inna ce a zaune,amma saita dauke kai kamar bataga komai ba,kamar zata fadi saboda sauri ta wuce dakin yaagana don taji kiran datake mata.
Kala kalan magungunanta ta ritsata dasu,dama wancan gutsuro wannan,inda tasan neman da yaaganar ke mata kenan ba zata dawo ba,hakanan tana bata rai ta karba ta shanye kowanne,yaa ganar kuma ta sanar mata zaman kwana biyun da zatayi a gida dalilin wannan ne,sai final gyaran jikin da takeso azo goben ko jibi ayi mata,daga nan ta zarce da bata wasu shawarwari da hikimomi gami da dabarun zaman aure wadanda zasu amfaneta.
*_LAMIN_*
Tunda ya dauki hanyar gidansa tunanin iman dinne fal zuciyarsa,duk wani moment da sukayi spending tare ya dinga dawo masa,shi kadai cikin motar ya dinga sakin murmushi,hannunsa yana tuqi,daya hannun kuma na dafe a qirjinsa,daidai sanda ya tsaida motar qofar baqin gate din gidansa ya sauke ajiyar zuciya,yabar samha cikin yanayi na rashin fahimtada daidaito a tsakaninsu,a yanzu kuma baisan me zai shiga gidan ya iske ba......
End of book

Leave a comment

Post
Comments

109346365637918680979
Allah ya biya ki da aljjana huguma kinyi duk yadda akeyi luv u so much
2 minutes ago

103039842410465448425
Muna godiya
2 hours ago

112699676368185333462
Nice one
3 hours ago

116654277997892434205
Wai wannan buk har banason ya qare godiya me tarin yawa
3 hours ago

Contact Us
Arewa Books Publishers
WhatsApp: 09031774742
Email: [email protected]
Navigation
Home
About
FAQ's
Legal
Privacy Policy
Terms of Service
Social
Facebook
Instagram

Copyright 2021, Arewa Books | ALL RIGHTS RESERVED | Powered by thinkcrypt.io
"
https://arewabooks.com/chapter?id=62d57954241eaa1ff3ba79b0#:~:text=Chapter%2069-,Shafi%20na%20sittin%20da%20takwas,yanzu%20kuma%20baisan%20me%20zai%20shiga%20gidan%20ya%20iske%20ba......,-End%20of%20book
[7/19, 10:04 PM] Mummyn Yara: "

Menu
Dashboard
My Library
Create Story
Home
About us
FAQ's
Privacy Policy
Terms of service
Logout

KUFAN WUTA