← Book details Idan Rana Ta Fito Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 8

Sashe 7

Idan Rana Ta Fito Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

22.......Su kam karkashin wata bishiya suka
zauna suna hangen ruwan daga in
da suke. M.B yana jefa 'yan kananan
dutsuna cikin ruwa, ya kalli Ado ya
ce Adamu yarinyar can da ta wuce kamar itama 'yar gidan ku ce. Ado
ya ce da ba ka santa ba? M.B ya ce
ba duka kannanka na sani ba,
'yanmata da Bintu da Asma'u na
sani." Ado ya ce, to ai sune
'yammatan, ita wannan da ka gani da ita zan aura, sai wasu matsaloli suka shigo, kuma ni na yi niyyar
auranta ne don na taimaka mata
bawai don so ba. Cikin ikon Allah da
na sama zuciyata auranta a 'yan
kwanakin da muka yi sai na samu kaina da soma sonta nan ya kwashe komai har da tarihin Jidda ya ba wa
M.B
Nan ya ji ya kara tausayin yarinyar
sosai, ya kuma bawa Ado labarin
turetan da ya yi dazun na. Bayan sun dawo cikin gari suka sake
hangen ta dauke da tiren goro.
M.B ya ce wai shin Ado yarinyar can
bata da aikin da ya wuce talla ne?"
"Kwarai kuwa. "In ji Ado,"Tana talla
ne sau 4 a kowacce rana, safe, rana, yamma da kuma dare."
Tausayinta ya kuma cika zuciyar M.B
kazalika sai gata da daren dauke da
tire. Ado ya ce, "In na jin takaicin
halin da yarinyar take ciki, lokacin
da na yi nufin taimaka mata sai na kara mata damuwa." Ya dubi M.B Muhammad tana zaman zamanta na
jawo ta, na kimsa mata sona cikin
zuciya, a karshe a ka raba mu don
Allah ban zalince ta ba?"
M.B ya ce "Ba ka zalince ta ba, kayi nufin taimakonta ne. Zan yi nazari nima na gani wane irin taimako zan
mata?"
*************23.....
Komai na bikin M.B suna tafiya dai-
dai, yanda Hjy ke rawar kai da ji da Ango tare da fidda kudi daga cikin jakarta take kashe su yana ba wa
M.B mamaki, ban da yasan komai
game da makarkashiyar da suke
kulla mishi, to da zai karyata duk
wanda ya zo mishi da batun cewa da wata manufa suke son auran shi
da Basma. Don haka ya bi ya lika
security a guraran da bai saka ba,
domin kara samun cikakken
rahoyan sirrin duk wata
makakarkashiya. Akwai fatitiikan da za a yi kafin
daurin auren, da kuma bayan
daurin auran tun saura kwana 2 biki
dangin mahaifiyar M.B da Kakarsa
Haja suka bayyana birni cikin su har
da Binto da kuma Ado, haka nan dangin Mahaifinshi daga Garko,
Binyo kam ta tsinke da lamarin
bikin 'yan birni, fadi take ina ma da
Kulawa muka zo bikin nan ta sha
kallon duniya,
, Allah Sarki Haja ta ce wa zai barta? Binto ta ce ai zan kai mata wadannan hotunna ta gani ki ko kai
mata in ji Haja, Allah yasa ina son
yarinyar na so kwarai Ado ya aure
ta, domin yanda yarinyar ke sha
wuya nasan Ado zaya rike ta da amana zai kula da rayuwarta, Binto
ta ce Baba ya yi saurin yanke
hukunci koda yake ya ce shekaru da
dama da suka gabata suka kulla
alkawarin auran Yaya Ado da Aina,
haka ne in ji Haja, amma ban gushe ba ina mata addu'a Allah ya bata wanda ya fini, amin in ji Binto. Hjy ta jawo aminiyarta cikin dai
wato Kilishi ta maida kofa ta rufe
tare da cewa kin san sirri dukkansu
suka zauna bakin gado. Hjy Shuwa
ta kalli Kilshi ta ce, "Kawata kinga
dai yanda komai ke tafiya min daidai ko?",
Kilishi dafa ta tare da cewa "Kawata
na ta6a ki da alheri na kula sai dai
menene shirinki na gaba?"
Shuwa ta ce, "Shirina na gaba kuma
na karshe shi ne kashe Bello, ta hanyar sa mishi gabu cikin abinci." Kilishi ta zuba mata idanu. "ZUWA yaushe za ki aikata haka?"
Kilishi ta tambaye ta.
"Da zaran anyi biki." In ji Shuwa.
"Ba ki tsoron a zarge ta in abin ya yi
wuri? Sannan Likitoci za su gano cewa ya
ci guba wacce amsa a ki bada
lokacin da kanwarki ta ji tuhuma ta
yi yawa? Ta ce ke ce ki ka bata?"
In ji Kilishi.
Shuwa ta yi dan jim sannan ta ce,"Haka ne.
Na so in yi wauta, zan bari sai sun
dan kwana 2.
Kilishi ta girgiza kai tare da yin
murmushi.
"Ya ya za ki yi da cikin da kanwar taki zata samu, musamman in an
samu irin natattun cikin nan an yi
an yi ya fita ya ki fita? Ina nufin
dadewarsu za su kusanci juna kuma
ciki zai iya shiga, kinga dan in ya zo
duniya in bai gaji Kakanshi ba dole ne ya gaji dinbin dukiyar da ubansa ke da ita wadda ki ke burin
kanwarki ta gada daga b.aya ki
mallake." Shuwa baya"Haka ne kuma fa, lallai
Kilshi kina da baiwa. To yazamuyi
[19/09 9:15 am] Inna👬👫: Idan rana tafito

24.....
Nan da nan Jami'an tsaro suka nufi
gurin da mutumin ya fado, shi kuwa
Ango tuni dangi suka zagaye shi
don jin me ke faruwa? Lokacin da su
Hjy Shuwa suka fahimci M.B ne ya yi harbin ba shi aka harba ba, sai suka cika da mamaki gami da tsoron me
zai biyo baya?
Lokacin da suka isa guri inda
mutane suka yi cincirndo don ganin
kowane ne Hjy Shuwa ta riko hannu M.B tana cewa
me yake faru ne Bello? Ya ce,"
An turo shi ne don ya kashe ni?"
Ta ce,"Su waye za su mana wannan
dayan hukunci?",
Ya ce "Sai Allah, shi ne kawai ya sani.
Sai dai kada ki damu ko su wanene
burinsu bai cika ba, kuma na sani
zamu hadu dasu karo na 2.
Jikinta na rawa "To bari in kira Dady
in sanar dashi. "M.B ya ce "Hjy ki bar shi kawai, wannan Jami'an tsaro za su yi gaba dashi in yana da sauran
rai ne ya musu bayanin dalilin sa na
son kashe ni, in kuma ya mutu shi
kenan sai in mun tsaya a gabn
Ubangiji." Hjy Kilishi ta matso,"To ai dama
karsa shi kayi domin barin irin
wadannan a bayan kasa fitina ne."
M.B ya yi murmushi ya kalli
mutumin lkcn da Jami'an suke saka
shi a mota, sannan ya dubi Hjy Kilishi"Da ina da wata dabara da zan iya yi lkcn da na hango shi wacce
zan kama shi kon kare kaina bayan
harbin to da ban harbe shi ba. Tilas ke sa mu harbi don mun fi son
mu ji bayani daga bakin me laifi,
kila ba shi kadai ba ne ta yiwu wasu
suka sa shi da makamancin haka kin
ga duk zamu ji'."
Ya zuba hannuwanshi cikin aljihu "Hjy ku koma ciki lkcn tashi ya kusa, kada wannan ya dame ku, domin
IDAN RANA TA FITO TAFIN HANNU BA
YA KARE TA.
HAKAN NAN ZAKARAN DA ALLAH YA
NUFA DA CARA KO ANA RUWA MUZURAI SAI FA YA YI."
Mar 7, 2015
Aisha Ummu Shureim Sa'eed
45..
Cikin sanyi jiki tare da tunaninko ya
gano sune? Suka ce "Haka ne."
25.....Amarya dai tana can gurin kawaye
suna lallashi ta don ita kuka ta kama
riris, sannan ta kasa zuwa gurin suna dawowa gurin ta rugo ta
rungume mijinta shi ko ya shiga
lallashinta.
Hjy Suwa ta kira mai abun magana
ta ce ya sanar da kowa an gode za a
tashi haka saboda wannan farmaki da aka kawo. Maimakon gidansu za
su wuce kamar yanda a ka tsara
daga gurin party ango da Amarya
za a yi musu rakiya zuwa gidansu
sai kawai a ka koma gida gaba daya
in da suka iske mutanan gidan cirko-criko. Haja sai kuka take lkcn da su Ado suka zo mata da labarin dukkan su
suna falo ne suna jiran zuwan su M.B
bayan an gama jajantawa yana
rungume da kafadun Haja yana
lallashinta ya dubi Hjyr "Ina su Basma su zo mu tafi dare na kara
yi." Nan take Hjy Tasa kuka,"
Gaskiya ba za kuje ba, ka sani ko ba
shi kadai ba ne me nemn ran naka? Haka kawai kuma sai ku je can ku kadai su kashe mana kai a banza."
Husna da Safina suka gurin Mahaifin
su da ke tsaye yana saurarn kowa,
Dady kada ka bar Bros ya tafi fa." Ya
dubi Hjy." Kada wannan farmakin ya dame ku,
don ba zai zama barazana ko
tsoratarwa a gurin dan Sanda
kamar ni ba, zamana ni kadai ko
zamana cikin mutane ba shi ne zai
kare ni daga mutuwa ba, ku fahimci wanna ni ba zan canza da komai ba kuma ba zan kasa walwa ba don
wannan.
Chapter 7 · 0% Book details