← Book details Idan Rana Ta Fito Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 8

Sashe 6

Idan Rana Ta Fito Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

amma na kasa kallonsu, ya ce kin saida ne? Na ce saura kwano 2, ya ce muje na bi su zuwa cikin gonar, ya kira daya daga cikin mutanan da suke aiki ya ce su dauki abinci karkashin wata bishiya muka zauna, ya ce nasan an dake ki ranar ko? Na ce eh, ta dake ni. Ya ce shi yasa ki ke ta 6oye min har kwanaki 4 ko? Nayi shiru, ya ce kin fasa auran nawa kenan? Na kalle shi sannan na kalli Sama'ila na sunkuyar da kai, na za ci kayi fushi ne game da abinda ta yi maka ka fasa. Sama'ila ya ce, "Allah Sarki, Abokina samun kansa ya yi da kara muradin auranki, kuma insha Allahu ba fashi, sai dai wani iko na Allah, Ado ya ce matsalar daya ce, Jidda na kalle shi gabana na faduwa zuciyata cike da son jin wace matsala ce wannan?" Ya ci gaba zan tafi birni karatu, kuma zan dauki kimanin shekara 3 ya ya ki ke ga za ayi? Nayi shiru ina nazari sannan cikin karaya wato cikin amincewa raina na rasa Ado na ce Allah ya bada sa'a Sama'ila ya ce abinda za ki iya cewa kenan? Na ce to me zan ce? Ado ya ce Jidda shawararki nake son ji game da mokamar auranmu? Na ce Yaya Ado haka kurum na ji a jikina auranmu ba zaya yiwu ba, saboda zai iya kasancewa in ka tafi birni ka manta dani, sannan ga matsalar Baba Gaje in ta gan mu ta ji labari kamar yanda ta ce kai kara gurin mahaifin ka ba ka jin akwai matsala? Ya ce don Allah bar zancan wannan Babar taki, zan fa ci gaba da zuwa zancena tunda Babanki ya yarje min kuma kada ki damu kinji na ce to. [18/09 6:15 pm] Inna👬👫: Idan rana tafito 20 Ban damu da su ba na ci gaba da aikina, sai da zan fita muka ci karo da Babana ya dawo zai yi shirin Masallaci, cikin murna ya ce,a'a wa nake gani haka? Kulun majadan, kai amma fa kinyi kyau cancadi." Dadi ya rufe ne, kun san mu2m yana son ya yi gayu a kuranta shi, kuma ban ta6a sa rai wata rana za ta zo da zan ji irin wannan kalmar ba. Na ce "Baba ba ta nan shi ne na saka wannan." Babana ya ce,"Ai ko kin yi kyau, na jima ina son in sai miki kaya in ganki haka tamkar sauran yara, amma hakan ya faskara. Allah ya sakawa Ado da alkhairi, na fita cikin farin ciki, duk wanda ya sanni in ya kalle ni sai ya sake kallona, saboda mamakin kwalliyar da na yi, wasu kuma su ce iyen ba, an ci gayu cikin zuciyata kuwa ba wanda nake so daga ni irin Ado, yau dai ya ganni cikin gayu. Wasu Dattijai suna cikin siyan goro sai na ji muryar Sama'ila yana cewa, "Yammata muna son goro." Na kalle su cikin kunya, bayan an gama sayan goron na rusuna na gaishe su cikin ladabi. Ado ya ce a"a Sama'ila kaga mutuniyar taka ko? Yau kam duk kauyannan kin cinye 'yammata a kyawun kwalliya." Sama'ila ya ce,"Na yarda da kai.' Dadi ne ya rufe ni, na ce "ko dai kuna tsokana ta ne?" Ado ya ce, tunda ki ka fito tsakanin ki da Allah mu kadai ne muka yaba adon naki? Na yi dan murmushi sannan na ce, a'a Baba ma..........21......."S auran kalmar ta ki fitowa lokacin da na hango Baba Gaje ita da kawarta Dija suna dawowa daga biki, tuni su Ado suka gano ina cike da fargaba, sannan suka kalli inda nake kallo, ba su san Baba Gaje ba, amma duk sun yanke hukunci cewa ita ce, musamman Ado wanda ya ganta da dare, tana furta kalmar Kuluwa ina ki ka samo wadannan kayan? Cikin mamaki take magana, Ado ya shaidata a muryarta, don haka sai ya ce "Sannu Baba." Ya tsugunna shima Sama'ila sai ya tsugunna bata kalle su ba ni krum ta zuba wa idanu cike da masifa, tana karkada kai. Dija kuma tana fadin "Tabdijam, lallai yarinya ta rika." Ni kuwa tuni tsoro ya cika ni na soma kuka domin ban ta6a ganin fushinta irin na yau ba, don jikinta har 6ari yake, ta ce shin kai Ado ka ke ko wa? Ban ce ka fita hanyar ta ba?" Sama'ila ya ce, "Baba da aure muke sonta don Allah kiyi hakuri." Ta zaburo baki na kumfa "Ban hakura ba, na ce ban hakura ba iskanciin banza da wofi, na ce da ku aure zan mata? Tsinannu kun gama lalata 'yar uban wa zai aure ta?" Ado ya fusata ya kalle ta ya ce, Ni ne zan aureta." Ta kara kusanto shi"kai mara kunya ka fita daga inadunan in rufe ka kiyaye ni bar ganin ubanka ke da gari. Ado ya ce,"Baba insha Allahu sai na aure ta, ki rubuta ki ajiye sai na tsame ta daga wahalar da ki ke bata." Dija ma ta matso "kai dan sara sa'arka ce! ku ji mu da tsagera," Suka mike tsaye, Ado na cewa, "Yi hakuri Jidda, ki daina kuka kukanki yana soya raina." Baba Gaje wani tukuki ta ji cikin zuciyarta , ta cije yatsa sannan ta yi gaba fuu. Dija ma ta bita tana cewa, "Gaje gidan su zamu ke kai kashedi." Gaban Maigari suka zube, Baba Gaje ta saki kuka tana fadi "Maigari kun ne masu hukunci ya ya zaka yi da danka Ado wanda ke lalata min yarinya?" Dija ta yi zaraf ta ce, "Har batun cikin da ya yi mata kwanakin baya ki sanar da shi." Nan da na kuwa ta dad rushewa da kuka. Dija dama baki tuno min da wannan ba, Ranka ya dadw kwanaki har ciki ya yi mata cikin zuaran nan naku mai duhu, sai da kyar asibitin Garko suka cire shi, na ji tsoron kawo kara ne don naga ku ne masu garin amma sai naga an ci gaba ni dai ranka ya dade a shiga tsakanin su." Wakilin Maigari ya nuna ta "Ke ba mu son zancan wofi, Ado za ki ma sharri?" Maigari ya daga mishi hannu tare da cewa,"Dakata Wakili." Ya kalle ta "To baiwar Allah, kiyi hakuri zamu yi bincike kuma zan dau mataki. Ta ce, "Na gode, na gode." Ta mike suka tafi. Cikin dakin Baba Gajen suka yada zango sai sheka dariya suke yi, Gaje tana ta zugawa Dija godiya da dabarar da ta kawo mata. Shi ko Maigari Sai ya dubi Wakili da Liman ya ce, Dan yau zaya iya aikata abin da ya fi haka, shi yasa na ce ba zai je karatun nan birni ba, Liman ya ce ni kuma sam ban yarda Ado za ya aikata haka [18/09 6:50 pm] Inna👬👫: Idan rana tafito
Chapter 6 · 0% Book details