Sashe 2
Idan Rana Ta Fito Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
3... Sai da na tafi na duba naga rogo ne da kuli, a fiki na ce Allah Sarki Baba, Ina tafe ina ci sam ban ankara ba sai ji na yi na ci karo da mu2m, tuni tiren goron ya yi baya ya fadu na fara kallon da wa na ci karo gabana ya fadi ganin Ado. Yana tsaye yana kallona. na duka na soma tsince goron ina fadin nashiga 3 na yau zan sha jibga in ban gansu duka ba... Ado ya tsugunna tare da hasko cocila 'yar karama duk da cewa akwai hasken farin wata musamman yau watan yana 14 ya ce duba a hankali na kalli cocilar 'yar mai kyau ba kalar ta Babana ba da ya ta6a sautu birni a ka siyo mishi, sai na ji muryarshi yaba cewa ki duba mana me ki ke kallo haka? Ban ce komai ba na ci gaba da duddubawa banga wani ba ya ce kirga ki gani ki ya cika, na ce ban san ko na nawa ta zuba ba, ita ce ta kirga da kanta, ya ciro naira 10 nawa nawa ne goron? Na ce"Da na ficika ne da na kwandala." Ya mika min 10n "To rike wannan ki cika." Ya yi tafiyarshi na bishi da kallo, ko cikin mafarki bn ta6a zaton Ado zaya iya yi min magana ba, saboda Ado Saurayi ne mai girman kai game da jan aji, in ji 'yanmatan kauyenmu sannan shi kadai ne ya yi boki duk wata wasika in za a rubuta ko za a karanta sai annemi Ado, duk cikin kauyan shi ne babban yaron Maigari kuma duk kauyan babu wanda ya kai Magari dukiya, dabbobi da gonaki sannan su kadai ne ke zuwa birni. Jin an dauke tiren goron daga kaina sai na dawo cikin hayyacina yare da yin firgigit don ganin ko waye.......Bint o ce kanwar Ado, ta ce Kuluwa garin kallo wata rana sai an sace ki, nayi 'yar dariya na ce "Binto ina za ki?" Ta ce, "Dandali can za ki kai goron? Na ce, "Eh." Ta ce "hu'um, ke dai gaskiya ba kya hutawa gashi kin daina zuwa Mkrnt, na ce kema Binto kin sani in ban ke ba duka zan ci Mkrnt kuwa saboda kudin Laraba, ta ce in daina zuwa da Baba ya bani kuma ta kwace ta ce bani ba Mkrnta. Binto ta ce, shi yasa na daina zuwa gidanku ce min take yi in daina kula ki kai ke kula Maza ne da ke su Hinde sune dai-dai ni ni ko kin san ko a dandali rana daidai ce ba ma kwasar ta da su akanki....ko kin zo ko ba ki ba, a haka muka isa dandali na zauna kusa da mai gyada don ta kunna aci balbal, wato fitlar gwangwani Mar 6, 2015 Aisha Ummu Shureim Sa'eed 4..Binto ma gurina ta zauna muna ta hira ina bata labarin karon damu ka yi da Yayanta, lokacin da muka dawo gida ba wanda ya sai goron,don haka sai na mika mata naira goman a zuwan cinikin da nayi, ta zauna ta kirga goronta sannan ta dube ni "Siyan goron aka yi?" Na ce "Wani ne ya zubar min bai sani ba shi ne ya bani."Ta daga zaninta ta saka cikin lalitar ta tare da cewa "Irinsu ake so, shi ko wannan wanene? Na ce "Ado ne na gidan Maigaro."Hinde ta mike tab karya ki ke yi, Adi ne zai saurare ki? Sai dai in Mazan ki ki ka kula kalmar na bakanta min rai suna nufin ni 'yar isla ce. Cikin Muryar kuka na ce kai Hinde da yaushe na kula Maza? Baba Gaje ta ce to sarkin ruwan ido ke da ba kya raina abn kuka, in ma Mazan ki ke kulawa ina ruwana ni dai kudi na sani. Mikewa na hi naje nayo alwala don yin sallah dama kullum ba a barina yin sallah sai dai in na zo kwanciya in hada gashi an ce hada sallah babu kyau, su Baba Gaje ma sallar ba damun su ta yi ba, koda zata yin ma sai dai ta yi ta dokota ba tare da tasan hukunce- hukunce nta ba. Na dawo a gajiye ga yunwa, murnata daya shinkafa da waken sun kare, na shigo da kwarin gwiwata. Baba Gaje tana suyar kuli ba mika mata kudin ta kirga sannan ta kalmashe ta zuba cikin lalita ga sauran tuwi can dauki kici ki zo ki fita da wancan kunun, na dube ta Baba bana Hinde ba ne? Cike da masifa ta hayyako min, eh nata ne ta gaji don haka maza ki fita da shi kuma kada ki dawo min da ko kwano daya ne hakan na fita da kunun tsamiyar, ina Hawaye tsautsayi na fito ta lungun gidan Liman zan bi layin gidan Maigari domin in kai ma wasu masu faskare icen gidan Maigari kawai sai ga wani yaro ya shigo da gudu ya bangaje ni kafin na yi wani kokari tuni tiren ya fado, kunun ya zube........... Jikina yana rawa na shiga kuka ina cewa sai naje gidanku an biya ni n [18/09 9:00 am] Inna👬👫: IDAN RANA TA FITO ( 7)..! Na ce ta rasu, nan na soma kuka domin tunowa da na yi da mahaifiyata, ya ce daina kuka kada wani ya zo wucewa ya ji ya zargi wani abu daban, Allah ya jikanta. Cikin kuka na ce Ameen. Na dube shi. Mahaifiyata yar kauyen Rimi ce a can sumaila, shi ko Babana dan asalin nan kauyanne, wato farau ta nan Garko. An ce ya auro ta ne sanadin wani abokinshi, wanda ya kasance dan Rimin mahaifanta sun rasu sai wanta gurin shi take zaune kuma shi ne ya aurar da ita ga mahaifinmu, kamar yanda ka sani gidanmu gida ne da ya tara yan uwa wato gidan gado. Babanmu shi ne babba yana da kanne hudu kowanne da matarshi sai ko autarsu Baba Dije tana aure a sekahu, mahaifiyata ladidi ta samu Gaje uwargida da ya yanta shida. Sani da Awwalu da Musa, isa da kuma Hamisu sai cikin Hinde masifaffiya ce sosai, kaf gidan kowa tsoronta yake ji haka nan shima Babanmu yana shakkarta yanda Babana yake bani labari tun da aka kawo mahaifiyata gidan sam bata huta ba duk ayyuka da na gidan da na saidawa mahaifiyata ce ke yinsu, ko lokacin da take da cikina ba sauki rai da take mata,ya ce min ....! Wasu ma suna zargin cewa ita ce ajalin mahaifiyata domin ita ce a kanta lokacin da zata haihu, ta hana kowa shiga har ta haihu sannan ta fito ta sanar da haihuwar tare da rasuwa, a nan ne kowa ya zarge ta sai dai babu mai hujjar fadin hakan. Da wuya tana kisa kila da na mutu tun ina jaririya, madarar shanu nasha na girma ko yaushe ina gurin babana saboda Baba Gaje bata da lokacina kuma ta hana wasu su dauke ni in nayi kashi kuwa zagi da tsinawa haka take min uma sai dai mahaifinah ya wanke min, lokacin da na soma zama zuwa rarrafe idan nayi mata yarban nata yara dukana take yi iyaka karfinta hakanata so, babanah ya ce ba zai manta lokacin da na yi kyanda ba ya cire rai da ni danta yi min mugun ka mu gashi babu kulawa shi ne ya ke jinyata, ya ce a duk sanda ya fita neman dan na cefane ko yaje masallaci ko a ka kira shi yin aski baya sa ran cewa zai dawo ya same ni da rai in ma kashi nayi ko amai ko dai wani abu haka sai sanda ya dawn zaya gyara ni shi ne ya koya min sallah da kuma karatu, kai duk wata tarbiya da ya dace uwata ko ya ma yarta shi ne ya koya min sai da na soma zuwa makarantar allo sannan Baba Gaje ta maido dani dakinta ashe da! Ashe da manufa tayi hakan, nan ta kara sana'o'i talla kuwa tun daga lokacin na duka yinta ina siyar na tsira in ban saida ba duka, sannan Hinde in ta dawo da nata ni ce zan hada duka. Ado ya yi ajiyar zuciya cikin tausayi ya ce toh sauran mazan gidan dukh babu wanda zaya iya daukan wani mataki kanta??? Na ce babu saboda gurinta suke rancan kudi randa basu samu ba ka gako ba za su so su bata da ita bai ni fa gidan bani da wani gata sai mahaifina haka kuma ya yansu su hadu ne kanmu daya dasu amma ban isa ko magana in suna yi in saka baki ba, sai su shiga zagina ya ce yau fa wane laifin ki ka yi?? Na sanar dashi komai, ya mike ya nufi gurin akwatin shi ya bude ya ciro kudi. Kunun na nawa ne?? Na ce na talatin ne ya bani sannan ya ce ina zuwa. Cikin gida ya shiga kai tsaye dakin mahaifiyarshi ya ce Baba bani tuwan ta ce shigo ka dauka mana, ka kuma canza shawara ne za ka ci?? Abokiyar zamanta da ke zaune a kofar dakin tana gyaran waken kosan safe na karyawa ta ce Ado yau kaine za ka ci tuwon dawa? Ya ce Baba ya ya zan yi na nemi wani abun ban samu ba. Kakarshi da ke can kwance ta ce gara Ta ce gara dai ka ci ko kayi karfi kana dan karkara ka ce ba za ka ci dawa ba? Haja za ki sa in fasa. Ta ce toh fasa mana, yau ka kwana da yunwa. Ya fita yana dariya. Ya dire min abincin a gaba tare da cewa kici sai in raka ki gida. Na ce zata iya kala maka sharri fa, ya ce gurin mahaifinki zan kai ki na ce, toh ya shiga ya kawo min ruwa kallon mamaki ya bini dashi nasan mamakin ganin yanda nake cin tuwon tamkar nama yake yi ban taba cin tuwon ma dadinshi ba kuma har da rama, na side kwanukan tas na sha ruwa sannan na jingina da bango ina ajiyar zuciya ya kalle ni cike da tausayi kila na jima banci abinci ba, ya ce ina zuwa dubawa ya yi ko har yanxu masu neman din suna nan? Ganin sun tafi ya shige ya ce min taso muje. Babana yana tsaye kofar gidanmu yana