Sashe 3
Idan Rana Ta Fito Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
ta leken hanyar da zan bullo sai gamu, ina gaba Ado yana biye dani har kasa ya tsugunna ya gaida Babana, ni kuma ina tsaye kusa da Baban, ya ce Ado gidanku taje? Nan Ado ya koro mishi bayanin yanda ya ganni Baba ya ce na gode Ado ni kuma na nuna ma Baba kudin tare da cewa gashi ma ya ce in kai mata kudin kunun. Nan baba ya sake yin godiya ga Ado, shi kuwa Ado cewa ya yi Baba don Allah .. ..! Baba don Allah kasa ido sosai akanta in za a ci gaba da matsa mata irin na wata rana za a yi da na sani, ko dai ta bar garin ko kuma ta hadu da bata gari wadanda zasu bata kudi su cutar da ita, ba a fata. Baba ya ce, toh zan kokarta lamarin ne wato sai dai Allah. Ado ya ce toh ni zan tafi, ga kudin nan don Allah kada su dake ta. Baba ya ce toh na gode na gode. Shi ne ya kai ni har dakin Baba Gaje, dama tun kafin mu iso ya ce in mun shiga in bata hakuri muna shiga ta kalle mu dama kai ne ka boye ta ko?? Ya ce haba Gaje ya ya zan boye ta bayan nasan duk tsiya dole ta dawo nan ta kwana,ni kuwa sai na mika mata kudin tare da cewa Baba ga kudin. Cikin sauri ta amsa tare da cewa Baba ga kudin. Cikin sauri ta amsa tare da kirgawa sannan ta ce in sha. Gobe ma in halinki ne ki kara. Baba ya ce Amma Gaje ai kya tambayi in da ta samo kudin nan ko? Ta kalle shi ta watsar, sannan ta ce kana yi kamar baka san wacece ni ba, to ina ruwana da inda ta samo kudi? Nasan dai ba zai wuce mazanta ta kula suka bata ba. 8----Baba ya ce gaskia Gaje ya dace ki dinga yiwa yarinyar nan adalci ita da Hinde dukansu ya yanki ne ta mike tsaye gara ka dake ni ko ka huce, ya ce batun duk bai kai nan Ba, kiyi hakuri ta ce ka ishe ni da batun wani adalci, adalci ban san shi ba,kuma kuluwa da Hinde suna da bambanci don ko kai ma ka nuna, ko ba kuluwanka zaba ba??? Ya ce ba zabenta na yi ba, ina dai tausaya mata ne, ni duk daya na dauke su, tunda ni na haife su. Ta ce ni na bambanta, me ake yi da kuluwa watsattsiya ya dube ta da dai na kowa ne kuma fa ta nagari lamiri ne ya sa kai ya fice ya barta tana cewa, toh ba sai ka sake ni ka zauna da kuluwan ba ta juyo ta zubamin don kwashi a tsakiyar kai koma daddiyar banza tashi mun a kai ni har cikin ya tsana naji rankwashin tamkar in saki fitsari, ...OHHH NI HAANAT NAGA MASIFEFFIYAR MATA. Na koma can gurin kwanciyata na rabe kan yan tsummokaran kayana. Shi ko Ado dakin haja ya koma wato kakarshi mahaifiyar babanshi Dattijuwa mai shekaru taga jiya tana ganin yau, gobe sai Allah haja ta haifi yaya da dama suna rasuwa da mijinta marigayi malam shehu maigari na yanzu Alhaji sallau, sai kanin shi maigari kawo kenan Alhaji sidi sai ko kanwarsu kuma yar auta mai suna Mairo ta yi aure an kai ta Garko mijinta Alhaji Dahiru dagabisani suka koma! Cikin kano,dan shi ma'aikaci ne na gwamnati domin yana daya daga cikin wadanda suka ya boko zamanin ana gudun bokon, gwammaja suka zauna daga bisani ya samu matsayin sakataran gwamnati suka koma nasarawa cikin jerin gidajan masu kudi. Mairo ta rasu gurin haihuwar ta ta biyu, bayan gama zaman makoki haja ta koma kauye tare da jikanta Muhammadu Bello, gurinta ya zauna har shekaru shida sannan mahaifinshi yazo ya dauke shi don saka shi a makaranta. Duki hutu ana kawo shi kauye gurin haja kafin a kai shi kasar waje. Ado ya zauna bakin gadonta ya ce tsohuwa mai dan koko, Allah kashe ki musha gunba. Ta ce raggon namiji daga ina kuma?? Ko gurin budurwarka ka je?? Ya ce Ai kin san dai ni bani da wata budurwa a kauyannan. Ta ce, ka zauna karatun shirme har ka tsufa. Ya ce haja don bakya zuwa birni ne shi yasa da kin ga maza manya ba su yi aure ba suna karatu. Ai ni insha Allah zan kafa tarihi a kauyannan. Haja ta ce burinka kenan kullum tadinka kenan. Ya ce ki taya ni da addu'a. Ta ce, ina yi amma na fita [18/09 9:00 am] Inna👬👫: IDAN RANA TA FITO 5.. Jikina yana rawa na shiga kuka ina cewa sai naje gidanku an biya ni na kwashe kwanukan na nufi gida, koda na shaida ma Baba Gaje ta ce ita fa ba sunanta sarai ba, don haka in je gidan su yaron in amso mata kudin ta ai dama ta kula ba da son Raina na dauki kunun ba, in ko ba haka ba tasha alwashin yau sai ta sumar dani. Cikin kuka na nufi gidan malam bawa da yake nasan yaron,Lanto ta ce bata maganin sisi bare naira talatin, in je in yi hakuri na ce za a dake ni ne ta ce ai shima din zata dake shi. Tun daga nan ban koma gida ba in bi wannan layin in bi wannan soron har dare. Lokacin da na hango yaya Auwalu da musa nasan ni za su kama, don haka da na killa da god sai zauran gidan Maigari. (soro) zaure biyar ne a gidan kafin ka shiga ainihin cikin gidan, zauran farko da dakin baki ciki zaure na biyu har zuwa na karshe duk na samarin gidan ne wato dakunan su na cikin zaurukan, zauran da ke tsakiya wato na uku kenan shine ake cewa zauran duhu. Ko da rana ne dindim yake nan na labe. Tun dana ga yau har da cocilar ta taba su musa don su nemo ni hakika tana nufin aikata abinda ta furta. Ina nan tsugunne sai kawai na ji an yi karo dani sannan aka ce wanene? Ban yi magana ba na kuma lafewa. Ya dallaro ni da yar cocilarshi tare da zuba min idanu, ke daga ina? 6...."Na yi shuru tashi mana, ya doka min tsawa jikinah na bari na mike. Me ya kawo ki nan? Cikin dashasshiyar murya Da ta disashe da kuka na ce za'a dake ni ne ya ce wa zai da ke ki? Na ce Baba Gaje ta ce sai ta sumar dani kuma wallahy zata iya. Ya tuno kwanaki ita ce yarinyar da suka yi karo tayi bari, ya tuna kalaman da take furtawa tana kuka. Ya ji muryar wasu a zauran farko sai ya kashe cocilar ni kuma sai na lafe jikin bango su musa ne ya tare sua zaure na biyu yana tambayar su, wasu ke nema? Suka ce wata yarinya ce kanwarsu ta yi laifi ta gudu ya ce to an ce muka tana nan ne? Suka ce a'a za dai su duba ne ya ce musu to babu kowa su fita, nan suka yi waje ya dawo gurina zo nan,na bishi zuwa wani daki nan cikin zauran duhu, yar katifa ce da filo tasha shinfida kasan kuwa wata leda ce mai santsi sannan bangon dakin yasha ado da farin fenti an yarfa baki a jiki sai wata adaka wato akwati tana dore kan wani dan tebur gaskiya dakin ya tsaru ya zauna kan kujerar katako ita kadai ce cikin dakin sannan ya yi min umarni da in zauna gefen katifar. Ado ya ce min ya sunanki? Na ce sunana kuluwa, amma babana yana kirana jidda, ya ce wanene baban naki? Malam kasim ya dan yi jim, sannan ya ce nan gidan wanzamai? Na ce eh, to ina mahaifiyarki? [18/09 9:00 am] Inna👬👫: Idan rana tafito