← Book details Fatalwar Budurwar Mijina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 5

Sashe 4

Fatalwar Budurwar Mijina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kaga kwantar da hankalin ka, Amma kafin Nan ya kamata nama fad'a gaskiya, A yarda bayanin d'an uwanka ya nuna Kai ba mazauni Nan bane kana tafiya kana barin matarka gaskiya hakan bai dace ba Sam in shout Dai Matar ka tana Shan magunguna ba bisa k'a'ida sun mata yawa sune suka bata Reaction tafad'i Kuma kad'an su tab'a k'wak'walwarta Had'ida neman yiwa mahaifarta illaha,"

"Innalillahi wa'inna ilaihin Raju'unn doctor magunguna kuma tona meye,"?

"Eh na kore damuwa, Wanda idan mutum Yana cikin damuwa ko tinanin wani Abu saiya Sha to daganan Komai zai shafe yasaka bacci Mai tsawo, nayi mamakin inda tasa mesu Gsky Domin konan Hospital ba k'aramin Issue yakesa mubawa mutum irin wannan maganin ba saboda had'arinsa,"

"Yanzu doctor meye mafita,"? Cewar Abbas Cikin damuwa shima

"Eh to mafitar d'aya ce dole tadaina Shan magunguna d'in gaskiya, kuma A kula da ita sosai sannan tana buk'atar miji kusa da ita"

"to doctor mungode, yanzu zamu iya ganinta muma ko,"?

"Eh data farka ma zaku iya Tafiya in Sha Allah,"

Zahra na Zaune kusa da ita ta rauka Uban tagumi tana kallanta,

Shigowa sukayi da sallama k'arasawa yayi kusa da ita Had'ida Kama hannunta yad'an murza

"Sannu da zuwa Ina wuni," Zahra tafad'a

"Lafiya qlu Alhmdllh nasaku wahala ba kuyi hak'uri Dan Allah, kuma Ina matik'ar godiya gareku, yanzu kutafi gida kawai ku huta kuma data farko muma zamu dawo,"

"A'a mudai jira kawai," Cewar Zahra"

"A'ah madam kema kina buk'atar ki huta kuma kin manta bada Husna kuka zoba? So tanada buk'atar ki kusa Dan Haka ku koma muma tana falkawa zamu zo, idan kukaje kinga sai ya fad'a miki me doctor Yace d'in,"

"Eh hakane to Allah yasawwak'e sai kun iso d'in,"

"Ameen"

Sallama sukayi suka wuce,

Basu jima Sosai da Tafiya ba tafarka,

Ware manyan idanuwanta tayi sai kansa suka fad'a, Rintse idanuwa tayi tasake bud'ewa still dai shine

Murmushi Yayi Had'ida Kama hannunta Yace"ki daina wahalar da idanuwanki nine dai mijinki mustapha nadawo kuma Yanzu in Sha Allah ba Abunda zai hana mu koma tare jos,"

Ya mutsa fuska tayi Had'ida kauda kanta daga kallonsa, ita fushi ma take dashi ai,

"Sannu wife yanzu me kike buk'ata,"?

Shuru ba Ansa,

K'aramar dariya yayi ganin yarda tawani Sha mur"To wifey ba laifi bane naso zuwa dake tinfarko kika k'i, Amma Yanzu komai ya k'are tare zamu koma, wifey," cikin serious tone ya Kira sunanta

Maida kallonta da saurarenta duka tayi kanshi

Yace"daga Yanzu kada kisake Amfani da wad'annan magunguna gashi sune silar zamanki Nan Kuma suna barazanar rabani dake,"

"Uhunmmmmm inda bada suba Taya zankawo yau? Inda badasu ba ai da bakazo Nan d'in ba, so ni duk buk'atar shansu ta motsa saina sha,"

"Shikenan Kisha nagani ai muna tare, kitashi muje gida Koda inda Yake miki ciwo ne,"?

"A'a bakomai Kuma fa Ni bazani Jos ba,"

"Au Baki sami darasi ba,"?

"Darasi name,"?

Ganin Yana Shirin Tona kansa sai yayi shuru

Saida yabiya gun doctor yak'ara Masa tini sannan suka wuce,

Cikin kwana biyun Sosai take samun kulawa daga gurinshi harsu Zahra ma,

Sati d'aya sukayi mustapha yace yau zasu wuce jos, taso gardama Amma Wannan lokacin sauya Mata Yayi b'acin Randa Batasan Yanada ba yanuna mata harda Zahra suka Mata fad'a dole tabishi suka nufe Jos...

Tinda suka sauka jirgin suka shiga mota gabanta ke fad'uwa zuciyar ta saiwani rawa take,

Suna shiga cikin gidan gabanta ya buga da k'arfi, Saida ita furta nashiga Uku A fili,

Kallonta yayi ganin duk tayi wani iri yasa ya kama hanunta suka fito motar

Joseph da sani suka iso wurin suna gaidasu,

Ansawa Yayi kafin ya gabatar musu da Matarsa,

Sosai su Joseph sukayi mamakin Wai Ashe yanada mata,

Cikin gidan suka nufa, duk tawani sukuku da ita tarasa meke damunta sannan bakinta ya Mata nauyi takasa Anbaton Allah tinda tashigo gidan,

Nuna mata komai yayi kafin yashiga da ita d'akin sa bayan yanuna Mata nata, zama tayi gefen gadon, shikuma ya rage kayan jikinsa yashiga ya watsa ruwa, inda ya barta Nan ya sameta,

"Haba Wifey Wai meke damunki ne kije kiyi wanka,"

Kwantawa tayi kawai Kan gadon tana Rintse Ido,"Inajin badad'i kamar wani Abu zai iya samuna"

"Haba mezai sameki bayan gani kawai kina damuwa ne tinda bakison garin Amma zansa kiso shi very soon, Bari nazo namiki wankan tinda najima banyima Y'ar matata wanka ba," Ya k'arasa maganar cikin zolaya Had'ida nufota,

Da saurin ta mik'e tana dariya tafice A d'akin tana fad'in"Banaso zanyi da kaina,"

Dariya shima yayi, Yaji dad'in ganin tasake shifa yanzu yama manta Sam da Maganar Zeeza Dan yanzu Anyi wata 2 ma,

D'akin nata yana jikin Gardiner d'in hatta window d'in nata tana cikin duka Gardiner yanzu haka bud'e take iska Mai sanyi nashiga kuma tana iya hangar Wannan iccen dama kabarin Zeeza Saidai inba Wanda yasani ba, bazaka tab'a cewa Anyi tonon k'asa wurin ba, Saida tafara waya dasu Zahra sannan tashiga toilet, tagama wankan duka tafito harta shirya taji Kamar Ana Kiran sunanta da wata irin murya cikin kuka,

"Falmata!!!! Kitaimake Ni,"?
Kalmar da taji tana fitowa Kenan ta window d'in,

Cikin k'arfin hali tanufe window d'in talek'a bakowa Amma wani irin duhu yagame wurin

Iska tasoma kad'awa da k'arfi take labulayen d'akin suka Soma fira sama kamar zasu cire, wutar d'akin ta d'auke take d'akin ya game da wani matsanancin duhu wanda ko hannunka baka iya gani, tsoro taji da sauri tajuya ganin meya kashe hasken, kawai taji Anshak'o wuyanta tabayan Anyi sama da ita Ana k'ok'arin fidda kanta cikin Wannan k'aramar window d'in.............................

_TO FANSSSS MUN FARA KABARIN KO MEZAI FARU DA FALMATA A YANZU??? MUJE NEXT PAGE ZAMU SANI KUMA K'ARSHEN FREE PAGE IN SHA ALLAH_

_BASEERATA ITACE ARZIKINA😍_

WhatsApp number 07064904617

Or

07068956952

*FATALWAR☠️ BUDURWAR MIJINA*
_PAID BOOK #300 ONLY_

*MAY 5/2023*

_RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱..._

```MARUBUCIYAR... (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book, (6)Shagala Free book, (7) Silar d'a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9) Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12) Bak'in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d'aukar fansa free book. (14) ZAYYAN 💞 ZEEYAT PAID BOOK. (15) MAKARANTAR KWANA FREE BOOK. (16) SHAGALA FREE BOOK,, (17) SO SIRIRIN ZUCIYA..... And Other's BUT NOW (18) SAURAYINA.. (19)D.S.P ANNUR PAID BOOK....(20) SAKACINA PAID BOOK.... (21) SO!!! FREE BOOK... (22) FATALWAR ☠️ BUDURWAR MIJINA PAID BOOK..
loading..... Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱```

_Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah mad'aukakin sarki Mai bayarda baiwa gawanda yaso Kuma sanda yaso Ina godiya ga Allah Allah daya sake bani dama had'ida baseerar sake kawomuku sabon littafina maitaken *FATALWAR☠️ BUDURWAR MIJINA!!! PAID BOOK #300 ONLY* Ina fatan yabada darussuka ga kowacce macce Kai hardama mazan baki d'aya Allah ka k'ara shiryamu dukanmu_

*INAYIN LITTAFAINA DOMUN BADA DARASI DA FAD'AKAR DA AL'UMMA BAKI D'AYA....... AKODA YAUSHE ALK'ALAMIN MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱 BAYA RUBUTA SHIRME KO BATSA KO LALATA RAYUWAR AL'UMMA SAIDAI INA K'OKARIN WAYAR DA KAN AL'UMMA DAMA DAWO DAMU KAN HANYA MADAIDAICIYA ALLAH KA TSAREMU DA AIKATA AIKIN DANA SANI.. INASONKU MASOYANA ADIK INDA KUKE NID'IN CE DAI TAKU HAR KULLUM MAISON GANIN FARIN CIKINKU MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱*

*FREE 🅿️26 to 30*

_Last free page in Sha Allah, Wannan shine k'arshen free page so idan kinason Ayi tafiyar dake kibiya 300 D'inki....._

.....gashi Anrufe mata baki Sam takasa ihu, neman k'wacewa take Amma kasa A Yanzu Sam batada ma wani saurin kuzarin kwantar Kanta idanuwan ta sunfito suna neman kafewa,

Jin shurun yayi yawa Bata dawowa ba yasa yamik'e ya nufe d'akin nata, rufe ya tarda k'ofar nocking yafara"Wifey yadai shurun Lafiya kuwa ki bud'emin k'ofar Mana kizo ga Abinci"

Nanma shuru sake murd'a handles d'in k'ofar Yayi kuma saiya bud'e, shiga yayi yanata magana

Kan gado ya hangeta kwance tarufa da blanket ga Alama dai bacci take,

"Bacci kuma soulmate bakici Abinci ba? Kuma ko sallah bakiyi ba," ya k'arasa in Yana Hawa Kan gadon yana tashin ta,

"Wayyo zan mutu wuya na," shine Abunda tafad'a tana falkawa

Rik'eta Yayi "kinga natsu Soulmate nine fa, waye zai kasheki kuma,"

Jin muryasa yasa tabud'e idanuwanta kalle kalle tafara Amma komai Yana normal wuyanta ta tab'a shima lafiya da sauri ta sauka Kan gadon tadube wuyanta cikin madubin Amma ba Alamar komai,

Cikin mamaki tace"Wllh my soul shak'emin wuya Akayi harda d'agani sama sannnan Ana k'ok'arin fita dakan nawa cikin Wannan window d'in,"? Nuna Masa tagar tayi

"Hahahaha Kai soulmate kina Neman zautar da kanki Yanzu Haka saboda wad'annan magunguna ne ke Neman haukatamin ke, wazai iya d'agaki sama ta hanyar shak'ar wuyanki? Saikace A film ko labari,? Hahaha wllh wifey kinada Abun dariya yanzu Haka mafalki ne kike ba kina bacci na tarar dake ba,"

Shuru tayi Alamar tinani itadai tasan Anshak'o wuyanta tabayan Anyi sama da ita har tana neman mutuwa amma Yanzu tana bacci kuma bawata Alama hakan na nuna gaskiya mustapha ya fad'a,.

"Kada kisawa kanki dogon tinani zo muje yanzu Haka harda yunwa nadamunki,"

Tagama gasgata Maganar sa Kan mafalki ne, Dan Haka tabishi kawai Saida sukayi sallah sannan sukaci Take Away d'in da ya tura sani ya siyomusu,

Kwantawa sukayi daganan suka Lula sabuwar duniya........

Washe gari Tinda safe suka tashi tare sukayi wanka kitchen d'in tashiga tasoma girka musu Abinci
Saidai tagama takirashi yaci yabawa su Sani sannan Yawuce gun Aiki,

Zaune take ita k'ad'ai sai TV data kunna wayar ta nagefenta Bata jima da Gama waya da Zahra ba,

Nocking k'ofa taji Anayi, "Waye," ta tanbaya?

Amma shuru ba ansa Saidai Anata buga k'ofar

Tsaki taja taje tabud'e saidai bakowa Anan cike da mamaki tarufe tadawo ta zauna sake buga k'ofar Akayi Wannan karon da k'arfi kamar za'a k'arya k'ofar irin Mai bugun yagaji ba'a bud'e masa ba,

Tsoro yasoma kamata dakuma Jin haushin waye Wannan

Cikin masifa taje tabud'e har tana shirin fad'a da kowaye Amma nanma bakowa fitowa tayi duka taduba bakowa can ta hange Joseph Yana Aikinsa kwada masa Kira tayi yazo Yana fad'in"Sannu madam"

"Da kwai Wanda yazo gidan Nan ne,? Ma'ana wani ya shigo bayan fitar maigidan,"?
Chapter 4 · 0% Book details