← Book details Fatalwar Budurwar Mijina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 5

Sashe 2

Fatalwar Budurwar Mijina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gidane babba maikyau yasha shuke shuke manyan itatuwa da k'anana bayan gidan yanada nisa da yawa hakan yasa yazama kamar daji bayan ba shukar da babu wurin yayi kyau Sosai, shiga cikin gidan yayi Yanada d'akuna Sosai Kamar namai gida yara mata bak'i , manyan zanensa yacire ya lallak'a A gidan, masu gadi kuwa har 2 maza manya saidai d'ayan ba Musulmi ba ne Kusan shike kula da tsaftar gida d'ayan kuma gadi, saida yagana dasu sannan ya watsa ruwa already yayi sallah da guzurin Abinci, kwantawa yayi take kuma Aka fara Ruwan sama, kwance Yake Amma duka tinaninsa Yana kan Matar sa yasan yana tsananin sonta itama haka Amma Yana da tabbacin nashi son yafi Wanda yake mata, baisan meyasa batason nisa da Abuja kullum indai zasu samu matsala to bazai wuce inyace suyi tafiya tareba musamman wannan karon tasawa ranta tsanar garin jos da yawa,
Wayar sa d'auka daniyar kiranta Amma Tina fushi yake da ita saiya fasa Haka yayi kwana cike da mafalkan Matar sa,..

Washe gari yatashi late shiyasa baikira taba wayar ma gida ya manta da ita, Saida yaje office suka Gama meeting sannan ya wuce wani restaurant

Tinda ya shigo Restaurant d'in hankalinta yake kansa kasa jurewa tayi yana zama takoma inda yake,

Zama tayi kujerar da take kusa dashi Had'ida cewa"Barka kyakykyawa"

Ko d'agowa baiyiba kawai yaci gaba da cin Abincinsa

"Haba kanada kalar wayayyin maza Uwa uba ga kyau sannan daganin ka kwai kud'i to meye na share Wadda tazo maka da Alkairi,"?

Nanma baikula taba, Yana gamawa ya Mik'e yaje biyan kud'in Abin mamaki sai kawai Akace masa Abiya Masa,

Yasan Wannan mayyar ce Dan Haka baice k'ala ba saidai garin sauri yabar wurin Ashe ya jefar da k'aramin katinsa yawuce, Aikuwa ta d'auka ganin har number gidansa naciki Taji dad'i had'ida yin murmushi Wanda ita kad'ai tasan ma'anarshi

.........

"Falmata kuwa ganin har Daren yawuce baikira taba gashi duk fashinsa bazai iya shareta ba Saboda Yana sonta hakan yasata damuwa safiya nayi tafara kiransa saidai not respond, kukanta tayi Domin A tinanin ta da gangan yak'i d'auka,

Haka ta wuni Ranar sukuku saboda weekend ne Abbas yana gida tare da Matarsa,.

Sai Kusan dare sannan ya Tina da wayar koda ya d'auko yaga missed call My soulmate gabanshi ya buga yasan zata damu Yanzu haka kila tayi kuka Yana k'ok'arin saka Kiran kawai yaji motsi kunna wutar d'akin Akayi cikin mamaki yaga wannan yarinyar cikin d'akin sa na bacci gashi dashi sai gajeren wando...............

_BASEERATA ITACE ARZIKINA😍_

WhatsApp number 07064904617

Or

07068956952

*FATALWAR ☠️ BUDURWAR MIJINA*

_PAID BOOK #300 ONLY_

*MAY 5/2023*

_RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱..._

```MARUBUCIYAR... (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book, (6)Shagala Free book, (7) Silar d'a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9) Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12) Bak'in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d'aukar fansa free book. (14) ZAYYAN 💞 ZEEYAT PAID BOOK. (15) MAKARANTAR KWANA FREE BOOK. (16) SHAGALA FREE BOOK,, (17) SO SIRIRIN ZUCIYA..... And Other's BUT NOW (18) SAURAYINA.. (19)D.S.P ANNUR PAID BOOK....(20) SAKACINA PAID BOOK.... (21) SO!!! FREE BOOK... (22) FATALWAR ☠️ BUDURWAR MIJINA PAID BOOK..
loading..... Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱```

_Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah mad'aukakin sarki Mai bayarda baiwa gawanda yaso Kuma sanda yaso Ina godiya ga Allah Allah daya sake bani dama had'ida baseerar sake kawomuku sabon littafina maitaken *FATALWAR☠️ BUDURWAR MIJINA!!! PAID BOOK #300 ONLY* Ina fatan yabada darussuka ga kowacce macce Kai hardama mazan baki d'aya Allah ka k'ara shiryamu dukanmu_

*INAYIN LITTAFAINA DOMUN BADA DARASI DA FAD'AKAR DA AL'UMMA BAKI D'AYA....... AKODA YAUSHE ALK'ALAMIN MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱 BAYA RUBUTA SHIRME KO BATSA KO LALATA RAYUWAR AL'UMMA SAIDAI INA K'OKARIN WAYAR DA KAN AL'UMMA DAMA DAWO DAMU KAN HANYA MADAIDAICIYA ALLAH KA TSAREMU DA AIKATA AIKIN DANA SANI.. INASONKU MASOYANA ADIK INDA KUKE NID'IN CE DAI TAKU HAR KULLUM MAISON GANIN FARIN CIKINKU MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱*

*Free 🅿️ 11 to 15*

........Jan blanket d'in gadon yayi Cikin tsawa Yace" are you a mad? Bakida natsuwa ko kunya ne Zaki shigomin har bedroom d'ina saikace wata matata? Wai ba magana nake miki ba, waima ubanwa yabaki damar shigomin gida Inasu Joseph da sani ne," Ya k'arasa maganar cikin d'aga murya Yana k'are b'oye tsiraicinsa,

Itakuwa murmushi kawai take tana cire kayan jikinta daganan ta Afka masa wasan ya sauya....

*Nidai waje nayi Ina Allah waddaran mata masu irin wannan muguwar Rayuwar, Allah ka k'ara shiryamu shiri na Addinin musulunci Ameen*

Abunda baisani ba sani yau bai kwana gidan Nan ba Saboda Rashin lafiyar mahaifinsa Joseph ne kawai kuma yasha giyar sa tatil ya manta k'ofar bud'e, Kuma koda bai shawuba tsaf zata iya siyansa da kud'i,..

Mike'wa tayi zaune zuciyar ta nabugawa da sauri da sauri wani mugun mafalki tayi Amma tarasa me mafalkin yake nufi kawai taga fuskar Wani Yana kiranta Kan ta taimakesa Yana Mik'a Mata hannu amma sakamakon sunada nisa Bata samu taimakonsa ba saiya rufta cikin wani tsohon gini,

"Innalillahi wa'inna ilaihin Raju'unn Wai to me wannan mafalkin yake nufi? Kodai Mustapha ne cikin wani hali,? Tajefawa kanta tanbayar

Mike'wa tsaye tayi tana fad'in "inaaaaa in Sha Allah He is safe, Bari nasake kiranshi yanzu,"

Kiran number shi tashiga Yi Amma tana rings but no response

"Oh ni Falmata mijina yayi fushi dani Sosai Abunda baitab'a yiba, Amma naso ka fahimce Ni kawai bana son garin Jos gaba d'aya wllh,"

_(Ni kuwa nace koma meye ai ke kika janyo Amma hakan nufin Allah ne Domin faruwar wata matsala wani dalilin yakan giftama d'an Adam sai gagarumar matsala ta fad'omasa, tabbas Nan bada jimawa ba Falmata Zaki fad'a gagarumar matsala da kinsani da kinbi mijinki tinfarko...........(( SHAWARA GAREMU DUKANMU MATA, kada ki kasance Mai kafiya idan mijinki yaso tank'waraki indai Abun baisab'awa Addini ba to Kada ki kafe dama kahuwa Bata haifarda Alkhairy, sannan idan so samune duk tafiyar da mijinki zaiyi ku kasance tare Koda baiso zuwa dake ba Idan dahali kiyi dabaru kibi mijinki Y'ar Uwa hakan zaifi zama Alk'awari gareki, Allah yasa mudace Allah ka tsaremu da Aikin Dana sani Ameen, Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱 SHAWARA kawai nake Baku Koda yaushe....))_

Ganin wannan damuwar ba shine solution ba tafad'a toilet ta d'auro Alwala tazo tafara sallah tana Addu'a wa mijinta, Dama Falmata Akwai Ibada Bata Wasa da Azkhar Had'ida ibada ko kad'an, inda take makara gu d'aya ne intasha wannan tablets d'in.,

Tajima tana kaiwa Allah kukanta kafin takwanta.

Mustapha Komai kasa Aikatawa yayi Wannan Daren bayan komai ya wakana gaba d'aya kansa wani iri yake masa Karo na farko daya Fara sab'awa Ubangijinsa,

Washe gari ita ta had'a musu breakfast dakanta koda ya fito palourn ya ganta tana had'a kayan Abuncin ko kallanta baiyi ba ya nufe hanyar fita,

Da saurin Tasha gabansa tace"yanzu komai yagama wakana Mustapha Ishaq so ka sake ranka zaifi kawai muzama d'aya, Sunana Zeeza Kuma Tinda naganka nakamu da sonka zanso ka Aureni Dan Allah saboda na Aure ka yasa nabi wannan hanyar Amma ni ba Y'ar iska bace wallhi,"

Tsabar takaici baice mata komai ba ya zaga yata zai wuce, Caraf ta rik'e k'afarsa tana kuka tace"ka yarda Dani Wllhi bantab'a zina ba kuma yarda kasameni zaka gane kawai saboda Ina tsananin sonka ne shiyasa na Aikata hakan Wllhi idan baka Amince wa soyayya taba saina fad'awa Duniya kaine Wanda kaneman Kuma kamin fyade ta k'arfin tsiya"

Chakkkk ya tsaya, Abu d'aya ya fad'o ransa Falmata Akwai Randa suna fira take fad'a masa"Natsane mazinacin namiji mustapha kasancewarka kamili Wannan kawai zantuna na godewa Allah, da Ace kana zina Randa zan kamaka da wata wallhi daga Ranar zamu rabu Koda ba inda zani saidai nabi duniya Amma bazan iya Zama da fasik'i namiji ba"
Yana kawowa Nan ya zame ya zauna k'asan tiles d'in duk da sanyin Ac da itatuwan gidan baihana shi zubar gumi ba sosai.

Zeeza kuwa ganin ta Ambace B'ata Masa suna yayi sanyi saitayi murmushi A ranta tace nasamu lagonsa,

"Kazo muci Abinci ko Honey"

Baida zab'i dole yabiye mata,

Koda yaje Aiki ma ganin k'arin missed call na Falmata jikinsa k'ara mutuwa yayi baison mata k'arya kuma baisan mezaice mata ba Amma koma yayane tanada laifi data biyosa da hakan Bata faru ba ai, Haushi yaji Sosai saiya Kashe wayar duka,

Ahankali Zeeza Saida tagama siyen Mustapha ya koma kwartonta dama can tabar gidansu tashiga duniya ne, Saidai har yanzu takasa yin nasarar ya Amince da Aurenta,

Mustapha kuwa ya sauya Saidai yasa photon Falmata gaba wasu lokuta yayi kuka Amma baisan dalili ba haushi take bashi tinda tak'i binsa, yanzu ba kasafai yake kiranta ba wani lokacin saita kirashi idan kuma Yana tare da Zeeza bazai d'aga ba, Wani lokacin har Abbas yake kiransa ya Masa fad'a Kan yadawo saidai yace zaidawo Ahaka har Akayi Shekara,..

Wannan shine silar Falmata tasoma Shan magunguna na rage damuwa da saka bacci saidai inba Zahra ba Wanda yasan tana Sha, Yanzu sun zame mata jiki batama Jin dad'i saitasha,..

_MUNDAWO CIKIN LABARIN_

Zaune suke A Gardiner d'in gidan nashi kasancewar yau weekend bai fita office ba tana kwance kan cinyarshi suna fira wayar sa tafara ringing tana hannun Zeeza sunan da tagani ne yasa ta mik'e A razane tana rawar Baki "My soulmate wifey"

"Da..da...da....dama kanada Aure ne,"?..............................

_BASEEERATA ITACE ARZIKINA😍_

WhatsApp number

07064904617

Or

07068956952

*FATALWAR ☠️ BUDURWAR MIJINA*

_PAID BOOK #300 ONLY_

*MAY 5/2023*

_RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱..._
Chapter 2 · 0% Book details