← Book details El Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 39

Sashe 32

El Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai wajen 12:45pm sannan ya shigo gaida Ummi bedroom ɗin nata ya shiga suka gaisa yana shirin
fitowa ta ƙara tuna masa maganar fitar da zasuyi dasu Seeyamah anjima to ya ya iya? dolenshi ya amsa
dan shi harya manta ma, falon ya dawo yayi breakfast ya ƙara ficewa zuwa nashi part ɗin, fita yayi ma
daga gidan gaba ɗaya zuwa inda ake ginin kamfaninsu yaga yadda aikin yake tafiya sannan ya ƙara
dawowa gida.
Layin Mujaheed ya kira ya faɗa masa anjima da yamma zai masa rakiya dan shikam bazai tafi daga shi
saisu ba kamar wani direbansu sam ya manta ma wai fushi yake da Mujaheed ɗin, kira biyu yayi amma
duk ba'ayi picking ba sai ana ukun sannan aka ɗaga cikin jin haushi yace

"ALLAH MJ idan ina kiranka baka picking akan lokaci saina dinga cin ubanka dan iskanci sai ayita kiranka
bazakayi picking ba sai kaga dama".

"To mara mutunci kasan uzurin dayake hanani ɗauka ne zakamin tijara".

"Wani uzuri gareka daya wuce iskanci? ka shirya anjima after Asr zaka rakani shopping mall".

"Shopping Mall kuma? babynka zakayiwa siyayya ne?".

"Nabi babyn da gudu dalla malam ka shirya da wuri". bai jira cewar Mujaheed ba ya yanke kiran yana
cije baki ALLAH ya tsareshi da wannan ɓata lokacin shikam shi har yanada time ɗin wata mace bare har
ya zauna yana wannan shirmen.

Sosai Mujaheed ya ƙyalƙyale da dariya jin abinda Gashua ya faɗa wai yabi baby da gudu wllhy wasa
wasa Gashua ɗan air ne a bakinshi ma yaji wannan kalmar fa shine harya riƙe ta haka shi sam baiyi zaton
ma zai sauko haka da wuri ba a yadda ya san shi da shegiyar zuciya da riƙon bala'i, girgiza kai kawai yayi
yana ƙara sakin wata dariyar......

Maryam Ibraheem Aleeyu

Mrs Salees Mu'az 💝

09139964697

*EL HABEEB*💥

©️Oum Hanan.

Writer of DR SAIF.

*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡

(Home of expert & perfect writer's).
No 30.

Ya daɗe zaune bayan sun gama waya da Mujaheed kafin ya tashi ya wuce bedroom, kayan jikinsa ya
cire ya rage daga shi sai boxer da singlet farare tas ya shiga bathroom yayi wanka. bayan fitowar shi ya
shirya cikin ƙananan kaya baƙin jeans ne da riga peach color mai gajeren hannu ya ɗaura baƙin agogon
fata sai P. Cap kalar rigar daya ɗora a kanshi ya sanya baƙin takalmi sawu ciki yana cikin fesa turare
wayarshi ta fara ringing bai kulata ba sai daya gama fesa turaren sannan ya isa inda take lokacin harta
katse wani kiran ya ƙara shigowa yasan dai bazai wuce Mujaheed ba picking yayi yakai kunnenshi batare
dayace komai ba ya ƙara komawa gaban mirror'n ya tsaya ya ɗauki wani turaren yana fesawa daga can
ɓangaren Mujaheed yace

"Gashua ka gama shiryawa ne?". Da ƙyar ya buɗe baki yace

"Yes".

"Okay nima na shirya gani nan zuwa".

"Ok". yace tareda katse wayar ya ajiye kwalbar turaren ya fito falo, zama yayi ya shiga latse latsen
waya.

Daga Seeyamahn har Neehlah ba wadda taso Ummi ta haɗasu tafiya da Habeeb Seeyamah dai batace
komai ba to me zatace? itafa jinta take tamkar ƴar aiki a gidan Neehlah kam fuska ta shagwaɓe tana
faɗin

"Kai Ummi ALLAH da baki haɗamu da Yah Habeeb ba takuramu kawai zaiyi bazai bari ma ayi siyayyar
cikin kwanciyar hankali da nutsuwa ba".

Harararta Ummin tayi tace

"Sha zamanki tunda bazaki ba".

"Zanje fa Ummi kawai dai Yah Habeeb ɗin ne akwai matsawa wllhy ni banson tafiya tana haɗani dashi".

"Kin tashi kinje kin shirya kokuwa dai surutu zaki tsaya yi?". Tashi Neehlah tayi ta fita tana tura baki ko
yaya tafiya ta haɗasu ya dinga hantarar mutum kenan yana masa tsawa ina dalili.

Yanzun ma dai da sukayi wanka Neehlah cewa tayi Seeyamah ta zaɓi duk kayan da sukayi mata tasa,
wata doguwar riga ta ɗauka ta material multi color tasa ba yadda Neehlah batayi da itaba kan tasa
mayafi tace a'a ta bata hijab tasaka tafi sabawa dashi, hijabin ta ɗauko mata pink kalar datafi yawa a jikin
material ɗin ta bata ta saka iya gwiwa ne mai hannu tayi kyau sosai sai ƙamshi take.

Neehlah kam mayyar dogayen riguna ce dan haka yanzun ma cikin doguwar rigar ta shirya light brown
tayi rolling da mayafin rigar suka zauna zaman jira.
Ba'a daɗe ba sosai Mujaheed ya ƙaraso gidan shigar manyan kaya yayi dayake ma'abocinsu sosai
shadda milk color harda hula kalar shaddar kamar wani ango nan compound ma ya tsaya ya kira Habeeb
ɗin yace ya fito ya ƙaraso, sai daya kira Ummi yace su Neehlah su fito sannan ya fito daga part ɗin nashi
ya rufe ya fito cikin compound ɗin.

A bedroom Ummi ta samesu tace su fita yana jiransu a waje tashi sukayi sukayiwa Ummi sallama
sannan suka fito.

Ba ƙaramin daɗi Neehlah da Seeyamah sukaji ba lokacin da suka fito suka hango Mujaheed da alamu
dashi zasu fita, suna ƙarasowa suka haɗa baki wajen gaishesu cikin sakin fuska Mujaheed yake amsa
musu Gashua kam a cukule ya amsa musu da

"Lafiya". Tamkar wanda akayiwa dole ya buɗe front seat ya shiga ya hakimce bayan ya cillawa MJ key
ɗin motar, Mujaheed da kanshi ya buɗewa su Seeyamah back seat suka shiga ya maida murfin ya rufe
sannan ya shiga driver seat ya zauna yana kallon Habeeb da hankalinsa ke kan waya yace

"Wai Gashua ni zanyi driving ɗin ne?". banza yayi masa baiyi magana ba bai kuma ɗago ya kalleshi ba.

"Kaji?". Mujaheed ya ƙara faɗa duk cikin neman tsokana da son saiya sashi dai magana.

"A'a ni zanyi". yace yana juyawa tareda sakar masa harara, dariya Mujaheed yayi yace

"Yaro yaji hausa har dasu baƙar magana haka Gashua". ya ƙarasa maganar yana ƙoƙarin tayar da motar,
ƙaramin tsaki Habeeb yaja tareda maida kanshi kan wayarshi ya cigaba da abinda yake.

Maigadi ne ya buɗe musu gate suka fice daga gidan, saida suka hau kan titi sannan Mujaheed yace

"Ina muka nufa ne Mr. Man?".

Kamar yadda baiyi magana ba haka ma bai ɗago kai ya kalleshi ba, Mujaheed ya ƙara faɗin

"Wai Gashua bakaji abinda nace bane?". Nan ma banza yayi masa hakan ya hasala Mujaheed ya juyo
yana harararshi da faɗin

"Matsala ta dakai wulaƙanci wllhy kanaji ana maka magana ka ƙyale mutane banza mara mutunci".
Sosai Habeeb ya shaƙa saboda yadda Mujaheed yake kunyata shi da tsinkashi a gaban ƙananan yara su
kansu su Seeyamah mamaki ne ya cikasu jin yadda Mujaheed ɗin yake zaginshi musamman Neehlah
datafi sanin ko waye yayanta lallai idan ba Mujaheed ɗin ba bataga wanda zaiyi masa haka ya ƙyale ba.

"Autar Ummi ina muka nufa ne? siyayyar me za'ayi?". Mujaheed ya maida tambayar kan Neehlah, a
ɗarare tace

"Kaya ne za'a siyawa Seeyamah".

"Okay yayi kyau bari mu duba babban shago saimu shiga ko?".

"Toh Yah Mujaheed". Neehlah tace taja bakinta tayi shiru.
Mujaheed bai ƙara saurarar Habeeb ba ya maida hankalinsa kan tuƙi sai jefi jefi dayake jan su Neehlah
da hira waɗanda sam basu biye masa ba kuma duk yasan ganin wannan uban ƴan baƙin ran ne ya hana
Neehlah biye masa a yadda take da ɗan banzan surutun nan, sai yaja bakinshi yayi shiru aka shiga yin
tafiyar kurame ba mai magana titin Nassarawa ya hau yana ɗan dudduba kan hanya inda zaiga gurin
saida kaya, ganin motar ta ɗauki shiru yasa Mujaheed yayi connecting da wayarshi yasa waƙa ya fara
saurara yana bin waƙar.

Ido Habeeb ya ɗan runtse yanajin kiɗan har cikin ƙwaƙwalwar kanshi kamar a tsakiyar kanshi akeyi
ALLAHn da yayi shi ya tsani hayaniya koya take.

"Please MJ ka kashe banaso". yace cikin cool voice yana ɓata fuska.

"Why?". cewar Mujaheed yana wani kaɗa kai alamun waƙar ba ƙaramin daɗi take masa ba, a ɗan
fusace Habeeb yace

"Saboda motata ce inada iko da ita".

Murmushi Mujaheed yayi tareda ɗan taɓe baki yace

"Gori zakamin Gashua? daɗin abin nima dai inada motar nan kuma ina zamana ka kirani in maka rakiya
haba saikace wanda ya ɗauko gawa a mota kai ba za'ayi hira dakai ba Neehlah saboda tsoron ka itama
taƙi sakin jiki na kunna waƙa kace ba haka ba to ya kakeso ayi Gashua? kai bazakayi nishaɗi ba bazaka
bar wani yayi ba".

"Kawai ka kashe banason hayaniya banda ɗan iska ne kai meye abin saurara a waƙoƙin nan ba ma'ana
ba komai".

"Eh a ƙyaleni ni inaso a haka tafiya dakai matsala ne wllhy Gashua naji ka ƙara nemana rakiya wani
wajen ba inda zanje".

"ALLAH kayi wasa zan saukeka a tsakiyar hanyar nan".

"Ka daɗe baka saukeni ba Gashua". Mujaheed ya faɗa yana dariya, ƙwafa kawai Habeeb ya saki ya
maida kanshi kan wayarshi, su dai su Seeyamah suna baya sunajin irin dramar dasu Mujaheed suke
tafkawa dama ai abokan wasa ne Neehlah ta ayyana cikin ranta.

"Bari dai in ɗan rage volume badan halinka ba karka tadamin iska yanzu". yayi maganar yana ƙara sakin
wata dariyar tareda kai hannu ya rage ƙarar, dariya ce sosai ta kama Neehlah jin abinda Yah Mujaheed
ya faɗa wai karya tada masa iska amma ba damar yi dole ta haɗiye abarta ta sunkuyar da kai tana
murmushi, Mujaheed yana kallonta ta mirror'n motar dai dai lokacin ta ƙara ɗago kai suka haɗa ido ya
ɗage mata gira haɗi da kashe mata ido tayi saurin ƙara maida kanta ƙasa tana murmushi.

Tun daga nesa ya hango wani ƙaton boutique a side ɗinsu na dama dan haka yayi U town yadawo
ɓangaren dama har zuwa daidai boutique ɗin yayi parking tareda kashe motar.

"Gashua munzo fa ka fito muje".
"Waye zaije ɗin? kuje dasu kawai malam ga ATM nan a biyasu". ya ida maganar yana karkacewa ya zaro
ATM ɗin ya miƙawa Mujaheed

"No ka barshi kawai zan biya kasan kyautatawa maraya ba ƙaramin lada ne dashi ba". cewar Mujaheed,
baki kawai Habeeb ya taɓe tareda ɗage kafaɗu ya maida ATM ɗin aljihu, fita Mujaheed yayi ya buɗewa
su Seeyamah da har lokacin basu fita daga motar ba

"Bismillah ƴanmata". yace yana murmushi idanunsa akan Neehlah yana jifanta da wani irin kallo wanda
duk kunya ta kamata, fita sukayi ya rufe ƙofar sannan suka jera a tare zuwa cikin boutique ɗin.
Chapter 32 · 0% Book details