Sashe 31
El Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sosai Ummi ta nutsu tana jin wannan labarin mai cikeda al'ajabi idan ta fahimta yaran su uku ne kenan
kuma duk kamar su ɗaya kuma kowacce da inda take tsai tayi da ranta tana auna kan labarin lallai ko
waye dole ya rikice ko ita kanta abin ya matuƙar ɗaure mata kai da shiga ruɗani.
Nannauyan numfashi ta sauke kafin tace
"A ina ita yarinyar daka gani a gidan Hajiyan take?". A taƙaice yabata labarin Heedayah kamar yadda
Hajiya ta sanar dashi yaje kuma yaga har gidan ranar da Hajiya tasa ya maida ita gida.
Kai kawai Ummi take jinjinawa cikin zuciyarta tana ayyana wasu abubuwa masu tarin yawa idan har
hasashen ta zai zama gaskiya to yaran nan ƴan uku ne maybe wani abun ya tarwatsa su kuma ba wadda
tasan da zaman ɗaya a cikinsu danƙari akwai cakwakiya cikin al'amarin nan warware shi sai ALLAH.
"Ita waccan yarinyar da kake gani a shopping mall ɗin kasan inane gidansu?".
"No Ummi har yanzu bansan inane gidansu ba shine nakeso inyi bincike dan gano gaskiyar al'amarin".
Kai Ummi ta jinjina tana faɗin
"Hakan yayi tun farko ma da abinda kayi kenan ka tsaya shirme da sakarci tabbas lamarin yana buƙatar
bincike kuma na baka goyon baya hundred percent dan ta hakane za'a gano iyayen su na asali jikina
yana bani duk inda yaran nan suka fito daga babban ahali suke sanin abinda ya tarwatsa su kuma sai
ALLAH zanfi kowa farin ciki idan aka gano real parents ɗinsu ALLAH ya bada sa'a".
Cikin farin ciki yake kallon Ummin yana ƙara jin wani ƙwarin gwiwa na shigarshi ada bai bawa abin
muhimmanci ba kamar yadda yake jinshi yanzu cikin ranshi saboda mahaifiyarsa data shigo cikin
lamarin.
"Thank you so much Ummi". yace murmushi na suɓucewa kan fuskarsa, itama murmushin ta saki tana
faɗin
"Karka damu nidai fatana karka shiga cikin lokacin aikinka abi komai a sannu har zuwa lokacin da ALLAH
zai bayyana mana abinda ke ɓoye kar ayi gaggawa idan kana buƙatar wata shawara ka sameni".
"Insha ALLAH Ummi thank you very much".
Kanshi kawai ta shafa tana murmushi shikuma yayi kissing hannunta.
"Good night Ummi". ya faɗa yana miƙewa tsaye da niyyar barin bedroom ɗin Ummi ta dakatar dashi da
faɗin
"Ya kamata gobe idan ALLAH ya kaimu kuje da Seeyamah a samar mata kayan sawa". tuni yanayin
fuskarsa ya canza ya wani haɗe rai yace
"Ummi driver fa?".
"Ɗazu yake sanar dani anyi masa waya daga ƙauyensu mahaifiyarsa ba lafiya zaije ganota". Ummi ta
amsa masa tana tsareshi da ido, shiru kawai yayi yana murza fatar goshinsa daya tattareta shine ma zai
kaita siyan kayan sai kace wani ɗan aikinta?
"Bakaji abinda nace bane wai Abbuna?". Ummi ta katse masa tunanin dayake, sai daya zura hannu ɗaya
a aljihu ɗayan kuma ya shiga shafa sumar kanshi kafin yace
"Naji Ummi amma kawai sai a ganni nakai yara siyayya please Ummi suje kawai da Neehlah ko nawane
zan bayar ta ɗauki duk abinda takeso". ya ƙarasa maganar yana marairaice murya kar ma Ummin tace
zata takura masa shifa gani yake hakan kamar zubar da girma da ajinshi ne kawai a ganshi ya raka yara
siyayya.
"Kai ɗin kai zaka kaisu, meye a ciki dan ka rakasu? ba yayansu bane?". zaiyi magana Ummi ta dakatar
dashi ta hanyar ɗaga masa hannu dolenshi ya amsa mata da to sannan ya ƙara yimata sallama ya fice
daga bedroom ɗin ta bishi da kallo tana girgiza kai, gani yake wani uban aiki ne kaisu siyayyar da zaiyi.
Direct kitchen ya wuce bayan komawa part ɗinshi ya haɗa coffee yadawo falo ya zauna kan 1sitter ya
miƙe ƙafafunshi kan center table ya fara sha duk da yadda yake fitar da turirin zafi kuwa ya riga ya saba
sha da zafi haka. Bayan yagama sha ma sai daya ɗan jima zaune anan sannan ya shiga bedroom yayi
wanka ya ɗaura alwalah ya fito ya shirya cikin pyjamas dark purple masu kauri ya fesa turare sannan ya
tada sallah, raka'a biyu yayi, yayi addu'oe ya shafa sannan ya kwanta bayan ya karanto addu'ar kwanciya
barci ya shafe jikinsa.
Asubah ta gari Mr Habeeb Gashua 🤩.
★★★_________★★★
Duk bakin bed suka nema suka zauna bayan hawowar su upstairs Neehlah tace
"Sisi kinga Yah Habeeb ɗin ko?". murmushi kawai Seeyamah tayi ta gyaɗa mata kai batare datace komai
ba dan har yanzu bata wani gama dawowa daidai ba gabanta kuma bai daina faɗuwa ba, baki Neehlah ta
taɓe tace
"Kinga irin halin nashi ko? yanzu haka wani laifin ya yiwa Ummi shine zai huce a kanmu inajin da bamu
gudo ba da duka zai kai mana". ƴar dariya Seeyamah ta ƙaƙalo nan ɗinma dai bata tofa tata ba to itakam
me zatace a kansa? kuma alƙawari ta ɗaukarwa kanta insha ALLAHU ba zata dinga shiga sabgar shiba
dan ita harga ALLAH kallon mara mutunci take masa.
Ita ta fara shiga bathroom tayi wanka kafin ta fito har Neehlah ta fito mata da night dress doguwar riga
har ƙasa orange color da baƙar hula tana fitowa ta shirya itakuma Neehlah ta shiga bathroom ɗin dan yin
wankan.
Ko bayan da sukayi addu'a suka kwanta Neehlah tana ta jan Seeyamah da hira taƙi biye mata sosai ita
haka ALLAH yayi ta magana bata dameta ba da haka har barci ya ɗauke su.
Bayan sallahr asubah Neehlah barci ta koma Seeyamah kam kasa komawa tayi ta cigaba da zama bisa
dardumar tana karanto azkar can ƙasan zuciyar ta tana ƙara godewa ubangiji kan wannan ni'imar dayayi
mata bayan tsahon shekaru sha takwas data ɗauka zaune a gidan marayu yau rana ɗaya ubangiji ya turo
baiwar shi dan ta share mata hawayenta yau gata itama an maida ita ƴa kamar kowane ƴaƴa za'a bata
dukkan gata da kulawa tana fata da burin ace wata rana zata zauna da iyayenta haka batasan wani irin
kalar farin ciki da murna zatayi ba a duk ranar data haɗu da iyayenta saidai abinda bata saniba a raye
suke? kokuwa a mace? wani abu ne yasa suka banzatar da ita suka wofintar da rayuwar ta haka? ba zato
taji hawaye na bin kumatunta ranta na wani irin suya batada mutum ɗaya da zata iya nunawa a faɗin
duniyar nan wanda zata bugi ƙirji ta nuna shi tace wannan ɗan uwanta ne shi kanshi wanda ya tsinto ta
ya kawota gidan marayun ance tunda ya kawota bai ƙara dawowa ba ba'a ƙara ganinshi ba, hijabin ta
tasa ta share hawayen fuskar ta.
Tun batasan kanta ba take ji a jikinta kamar wata rana iyayenta zasu nemeta kamar zatayi rayuwa da
iyayenta bayan rayuwar gidan marayu datayi da farko koma dai meye tana roƙon ubangiji ya zaɓa mata
mafi alkhairi idan da rabon zasu haɗu ɗin ALLAH ya haɗa fuskokinsu da alkhairi. Ta daɗe zaune a wajen
cikin tunani daga bisani tayi addu'a ta shafa ta tashi ta ninke dardumar ta ajiyeta a mazaunin ta, ƙofa ta
buɗe ta fita ta sauka downstairs ta shiga dube duben inda zataga abin shara cikin sa'a ta gansu da abin
yin mopping dama abinda ta sauko nema ɗin kenan dan haka ta ɗauka ta koma upstairs ɗin ta fara
gyaran ɗakin tayi shara da mopping ta wanke toilet duk Neehlah tana kwance tana uban barci batasan
abinda take ba.
Downstairs ta ƙara saukowa nan ma ta hau gyaranshi duk da dai ba wani datti a ciki ta share tayi
mopping ta maida kayan sharar inda ta gansu ta koma bedroom ɗin har lokacin Neehlah bata tashi ba
dayake ba school yau, kwanciya ta ƙara yi itama dan ba ƙaramin gajiyar da ita mopping ɗin falon yayi ba
saboda girman shi bata daɗe ba kuwa barci ya ƙara yin gaba da ita.
Lokacin da suka tashi ƙarfe goma ta kusa wanka sukayi Neehlah tace ta buɗe wardrobe ta zaɓi duk kalar
kayan da sukayi mata ta ɗauka tasa, saita rasa ma wanda zata ɗauka ɗin saboda yawansu kayane gasu
nan birjik laces, atamfofi, material's, dogayen riguna,shaddoji da English wear sai wanda ka zaɓa lallai
masu kuɗi sun more ba abinda ya damesu (A naki ganin ko? kowane ɗan adam baya rasa abinda yake
damunsa).
Wata atamfa ta zaƙulo riga da siket saidai tana ɗauko ta ma taga sabuwa ce ko sakawa ma ba'ayi ba
niyyar maidawa tayi Neehlah tace sam bata isa ta maida taba tasa kawai meye amfanin kayan, ash color
ce atamfar da touch ɗin fari da baƙi ɗinkin simple ne bawata kwalliya kuma sunyi mata matuƙar kyau ta
shafa turaruka, hijabinta ta ɗauka zata zumbula Neehlah ta ƙwace ta ɗauko mata mayafi ash mai ɗan
girma tace shi zata saka ita ko gajiya batayi da saka hijabi, haka dai ta karɓa ta yafashi tana jinta duk
wani iri saboda bata saba ba tafi ganewa hijabanta masu girma tai ta yawo a cikinsu.
Neehlah doguwar riga kawai tasa ƙirar Saudi blue black ta yafa gyalen rigar suka sauka ƙasa dan yin
breakfast.
Saukowar Ummi kenan suma suka sauko cikeda farin ciki take kallonsu tana amsa gaisuwar su kafin ta
ɗora da faɗin mai yi musu gyara tazo ɗazu tace mata an gyara ko ina kuma tasan ita tayi kar ta ƙara yi
akwai masu zuwa suyi ta amsa da to daga nan suka wuce dinning Neehlah tayi serving ɗinsu dama Ummi
batasa ran ganin Habeeb yanzu ba dan indai ba ranar aiki bace sai yakai ƙarfe ɗaya bai shigo yayi
breakfast ba.
Seeyamah ce ta gyara kan dinning ɗin bayan sun gama duk da yadda Ummi ta hanata kuwa ta kwashe
kayan da aka ɓata taje kitchen ta ɗaurayesu daga nan suka koma upstairs dama tuni Ummi ta koma
bedroom, Indian film Neehlah ta kunna musu a system ɗinta suka fara kallo.