Sashe 23
El Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai a lokacin Habeeb ya d'an juyo ya kalleta wani murmushin gefen baki ya sakar mata kafin yace
"Koba ihu ba? kiyi ihun mana kiga idan akwai wanda zaizo ya ceceki anan stupid d'in yarinya kawai". ya
ida maganar yana hararar ta ya juya ya cigaba da tuk'inshi
"To wai ina zaka kaini ne?". Da k'arfi tayi maganar cikin muryar kuka tana faman juye juye kan kujerar
datake tak'i zama waje d'aya.
Kai tsaye batare daya juyo ya kalleta ba yace
"Zan siyar dake ne ki nutsu kuma ki daina min mutsu mutsun nan inba hakaba zan baki mamaki yanzun
nan". yadda ya k'arasa maganar cikin hargitsattsiyar murya yasa tayi gum da bakinta ta zauna sosai
gabanta na fad'uwa shiyasa fa dama tacewa Hajiya bazata biyoshi ba yanzu batasan gidan uwar dazai
kaita ba ga magreebah takawo kai.
Haka suka cigaba da tafiya ba tare daya k'ara kallon side d'in datake ba, lokaci lokaci take sanya hannu
tana d'auke k'wallar dake taho mata da haka har suka k'arasa lamid'o crescent dayake farkon shiga layin
ne suna fara tafiya bayan sun shiga layin yayi parking, kallon inda yayi parking d'in tayi taga wani plat
house ne mai kyau sosai kafin tayi yunk'urin yin wata magana ya fice daga motar da azama takai hannu
zata bud'e ta fice taji anyi Lock d'inta ba damar fita.
"Wllhy bazan yafe maka kukan daka sani ba aikin banza nunar rana kawai". tace tana share hawayen
idanunta da hijab d'inta.
Knocking door yayi bayan ya shiga gidan ba dad'ewa Aleeyu yazo ya bud'e masa k'ofar daga irin kallon
dayake jifan Aleeyu dashi yasha jinin jikinshi saiya matsa masa hanya ya shiga hannayenshi zube cikin
aljihun suit d'inshi yana k'arewa falon kallo kamar yaune ya tab'a shiga cikinshi, Aleeyu ya rufe k'ofar
yabi bayanshi yana fad'in
"Yallab'ai barka da zuwa".
Bai amsa ba sai idanu daya tsare Aleeyun dashi, wasu irin idanuwa ALLAH ya bashi kaifafa wanda ko d'a
namiji ya kalla dasu wanda aka kalla d'in yakan rissina duk tsaurin ra'ayin shi kuwa bare y'a mace da cikin
y'an sakanni yake ladabtar da ko wacece ta cikin idanunshi, k'asa Aleeyu yayi da kanshi yana sosa kai da
tunanin laifin me yayi ne ake masa wannan kallon tuhumar?
"Where is she?". haka kawai ya cewa Aleeyun fuskarshi a d'aure.
"Tana ciki yallab'ai". Aleeyu ya bashi amsa.
"Sure?".
"Yes sir".
Har yanzu dai zuciyar shi bata gama yarda da abinda yake tunani ba hakan yasa batare dayace komi ba
ya shiga takawa zuwa bedroom d'in da Seeyamah take ya kama handle d'in k'ofar ya bud'e a hankali
wani irin bugawa gabanshi yayi lokacin daya hangeta a zaune kan pray mat da k'aramin Alqur'an a
hannunta tana karantawa a hankali, koda wasa Seeyamah bata d'ago kaiba dan duk zatonta Aleeyu ne
kawai sai ta cigaba da karatun ta.
Ajiyar zuciya da numfashi ya sauke a lokaci d'aya yana dafe goshinshi yanzu dai ko yanaso ko bayaso
dolenshi ya yarda su d'in twins ne wani abu ya rabasu to meye ya rabasu d'in? amsar da bazai iya bawa
kanshi amsa ba dan haka yaja k'ofar ya k'ara rufewa ya juya. Seeyamah datake ta jiran taga shigowar
Aleeyu taji shiru saita d'ago kai ta kalli k'ofar taga an rufeta sai a lokacin kuma k'amshin mutumin da
bazata tab'a mantawa dashi ba ya iso hancinta to ko shine yazo? rabon data sashi a idanunta tun ranar
da akayi mata allura bata bari tunanin shi yayi tsaho ba ta yakice ta cigaba da karatun ta.
"Ka cigaba da kula da ita zuwa jibi zaka maida ita inda ka d'aukota ka gane?".
Kai Aleeyu ya gyad'a cikeda jin dad'i dan harga ALLAH ya mugun gajiya da wannan zaman ALLAH yasa
karya canza ra'ayi dan sarai yasan halin ogan nashi wahainiya ne wajen canza kala.
Kud'i ya ciro masu yawa ya bashi sannan ya fice daga falon.
Tunanika kala kala ne ke masa yawo cikin k'wanyar kanshi ya zama dole yaje ya zauna da Hajiya suyi
magana yaji wannan yarinyar datake zuwa wajenta ita d'in wacece? meye had'in Hajiyar da ita? yana
ganin komai yazo k'arshe yanzu dole ya saki yarinyar nan kafin wani ya ankare.
Yana fitowa yasa remote ya bud'e motar ya k'arasa ya shiga, tunda ya shiga motar take faman hararar
shi jitake tamkar ta kikkifa masa mari, tayi zaton yana shigowa zai tada motar su tafi sai taga kawai ya
rufe idanunshi gamida yin relaxing akan seat d'inshi kamar wanda zaiyi barci gashi dama Aunt Ramlah
sau biyu tana kiranta taji ta shiru har yanzu bata koma ba sai k'arya tayi mata tace tana gidan Hajiyan
yanzu dai zata taho har Aunt Ramlahn nayi mata fad'an magreebah data kai.
Wani bak'in ciki ne ya kama Heedayah mutumin nan mugun d'an latsi ne wllhy ya kawota inda bata
soba, ya shiga ya barta tun d'azu tana zaman jiranshi and now yazo kuma ya wani hakimce kan kujera
kamar ma bashida alamun tafiya.
"Nidai dan ALLAH ka budemin in tafi wai malam meye hakane". Cikin masifa tayi maganar tana hararar
shi.
Habeeb da har lokacin bai bud'e idanunshi ba kuma a lokacin ne kalmar nan ta nunar rana ta fad'o masa
a rai dan shifa har yanzu bai yadda yarinyar nan ba zaginshi tayi ba dan haka yau saita fad'a masa
ma'anar ta sannan zai maida ita gida tunda ita fitsararriya ce batada kunya shikuma wancan d'an iskan
ba abinda ya sani a hausar ma sai tsabar cika bakin shi bahaushe ne, batare daya bud'e ido ba k'asa k'asa
kamar wanda aka tilasta yace
"Definition of nunan rana nakeso in sani".
Baki Heedayah ta bud'e tana zaro ido jin abinda ya fad'a ita wllhy sam ta manta ma ta tab'a fad'a masa
wannan kalmar yanzun ma haushin ya tafi ya barta ne yasa tace haka wannan guy d'in d'an bala'i ne
wlhi, fuska ta marairaice tana kallonshi.....
Maryam Ibraheem Aleeyu
Mrs Salees Mu'az 💝
*EL HABEEB*💥
©️Oum Hanan.
Writer of DR SAIF.
*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡
(Home of expert & perfect writer's).
This page all dedicated to
Aunt jamila
Mom sayyeed
Aunt Fareedah
Maryam Bello
Maryam Shuwa
Habeebah zailani
Haleemah Dayyab
Lubnah
Oum Ramlah
Mummy musaddiq
Ice
Aisha
Smiling
Mammyn Baffah
Humayrah
Da sauran wad'anda ma basuji sunayen suba duk nagode ALLAH yabar zumunchi da k'aunar juna
jazakumullah khair 💗.
No 23.
Taga alamun gayen nan masifa da bala'in mutum bashi zaisa ya canza ra'ayin abinda yayi niyya ba dan
haka ta marairaice murya tace
"Dan ALLAH bawan ALLAH ka taimakeni ka budemin in fita bama saika kaini ba please".
Idanunshi ya bud'e ya kalleta ba shiri tayi k'asa da kanta gabanta na fad'uwa saboda kaifin idanunshi,
cikin dakakkiyar murya yace
Ashe kuwa zamu kwana anan kenan dan sai kin fad'amin abinda kike nufi da kalmar nan". Batayi gigin
k'ara d'agowa bare ta kalleshi tace
"Nifa ban tab'a fad'a maka haka bafa".
Kamar bazaiyi magana ba saikuma yace
"Kinyi zaton na manta ne? Habeeb baya mantuwa idan kin shirya tafiya zuwa gida yanzu ki fad'amin". ya
k'arasa maganar yana k'ara maida kanshi kan seat d'in ya kwantar harda lumshe ido, Heedayah ji take
tamkar ta tsala ihu meyasa bazai fahimta bane? magreebah fa tayi har tafara jiyo kiran sallah a unguwar,
ta bud'e baki zatayi magana kenan ya rigata da cewa
"Wato kinyi amfani da salon zagi irin na hausawa kin zageni ko?". Ido Heedayah ta zaro sosai tace
"Zagi kuma? wllhy nifa ba zaginka nayi ba ALLAH". Tayi maganar kamar wadda zata sakar masa kuka, ba
tare daya d'ago kanshi daga kan kujerar ba ya bud'e idanunshi yace
"Ba zagi bane? meye to?".
Saidata tura baki cikeda shagwab'a tace
"Kawai fa gani nayi farinka yayi yawa mu a hausa idan akaga irin fararen nan basuda k'wari sai ace musu
nunar rana amma wllhy ba zagi bane".
Idanunshi ya d'an waro ya taso daga kan kujerar yana fad'in
"Sa'anki ne ni? ko abokin wasanki ne ni d'in, nine mara k'wari ko?". ya ida maganar yana nuna k'irjinshi
da d'an yatsanshi.
"Nidai kayi hak'uri please ka maidani gida Auntyna tana ta kira tun d'azu taji shiru ban komaba". Kai
kawai yake kad'awa ya tada motar kuma bawai dan maganar datayi masa ba kawai idan ya cigaba da
zama anan zaiyi missing sallah ne da saiya tsaya ta nuna masa inane bashida k'warin a jikinshi shi zata
rainawa hankali?.
Tafiyar kurame ce akayi ko tari ba wanda ya k'ara yi bayan sun tafi kowa da irin tunanin dayake a
ranshi, gaba d'aya shi tunanin Habeeb ya tafi kan ya akayi suna matsayin twins amma d'aya a gidan
marayu meyasa hakan? lallai akwai wani b'oyayyen sirri ma'ana ita wannan dayake gani a wajen Hajiya
itace take tare da iyayensu? duk yadda akayi ita ta gidan marayun ta b'ata ne tun tana yarinya, dole zaiyi
bincike akai amma kafin nan saiya zauna da Hajiya yaji tarihin wannan d'in saboda yasan ta ina zai fara
binciken nashi. Haka ya dinga sak'a da warwara har lokacin da suka iso gidan Aunt Ramlah ta hanyar
kwatance da Heedayah take masa, yana yin parking Heedayah tasa hannu da sauri da nufin ta bud'e
k'ofar motar taji ta a rufe gam runtse ido tayi cikeda takaicin abinda guy d'in nan yake mata ta fuskanci
mugun d'an tijara ne amma yanzu ita take nema dole ta kwantar da kai dan haka ta kalleshi a marairaice
kafin ma tayi magana yasan abinda zata fad'a shima kuma sauri yake dan haka yayi unlocked tanajin
alamun an bud'e tayi saurin bud'ewa ta fice ko godiya bata tsaya yimasa ba.
Nagode nunar rana". tace tana d'an d'aga murya yadda zaijita tana fad'a ta shige gidan da sauri tana
dariya, baisan ya akayi ba ya tsinci kanshi da sakin wani munafukin murmushi yana cije baki wato
yarinyar nan ta maidashi wani abokin wasanta ko? ALLAH ya k'ara had'ashi da ita zatayi masa bayani ne
dalla dalla wata k'aramar k'wafa ya saki yana jijjiga kanshi yabar unguwar da gudu.
Tana shiga ta samu Aunt Ramlah dasu Nu'aym a falo suna kallo ita Zainab taje gida sai gobe zata dawo,
sallamar datayi Aunt Ramlah ta amsa tana binta da kallo tasamu kujera ta zauna tana mata sannu da
gida Aunt Ramlah ta amsa tana fad'in