← Book details El Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 39

Sashe 21

El Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Umma tana zaune kan tabarma da wake a tray tana gyarashi suma kan tabarmar suka nemi waje suka
zazzauna.

"Lafiya dai Malam na ganku haka kamar ba cikin nutsuwar ku ba?". Umma ta tambaya ganin yanayin su
kamar akwai wani abu dayake faruwa.

"To nima dai zan fita muka had'u dashi zai shigo, muna jinka Mustapha meye ya d'aga maka hankali
haka?".

Zama Mustapha ya gyara yana fad'in

"Yanzu Isma'eel ya nuna min wani hoto wai ta b'ata ana cigiyar ta a Kano". yayi maganar yana mik'awa
Baba wayar, shi kanshi Baba saidaya zaro ido ganin Heedayah k'uru k'uru wai ta b'ata, kalmar innalillahi
kawai yake ambata cikin tsananin tashin hankali Heedayah ta b'ata amma meyasa Ramlah bata kira ta
sanar dasu halin da ake ciki ba? b'atan d'an mutum sukutum da guda?.

Umma ya mik'awa wayar ta karb'a ta duba hoton dayake ita mace ce akwai raunin zuciya har tafara
hawaye ganin Heedayahnta a matsayin wadda ta b'ata dama rabon ayi hakane yasa tabar gabansu tabi
Ramlah Kano?

Wayar Baba ya karb'a daga hannun Umma data tsurawa hoton Heedayah ido tana hawaye ya mik'awa
Mustapha wayar yana fad'in

"Kiramin y'ar uwarka Ramlatu inji dalilin dayasa ta b'oye mana irin wannan muhimmiyar maganar
saboda shashanci".

Wayarshi ya zaro daga aljihun gaban rigarshi yasa password ta bud'e ya shiga jerin numbers yana
neman number Aunt Ramlah.

Bata dad'e tana fara ringing ba akayi picking sai yasata handsfree ya rik'e ta a hannunshi yana amsa
sallamar Aunt Ramlah.

"Ramlah Baba ne zakuyi magana dashi gashi a kusa dani".

"Yauwa dama Mustapha dama ina niyyar kiransu, jin haka yasa gabansu ya k'ara fad'uwa, cikin b'acin
rai Baba ya fara magana da fad'in

"Haba Ramlatu, ya ina ganinki kamar mai wayo ashe ba haka bane inbanda sakarci taya zaki b'oye mana
irin wannan maganar?.
MG'S SKINCARE

In kid'a ya chanza rawarma semutaru asauyata,

Wani Kaya se amalende

Haka Wani Hadi na musamman se MG'S,

Ina ma'abota amfanida kayan MG'S SKINCARE?

To bana fa tafi bara munqarawa kayanmu inganci muncire muntsefe munkawo maku qayatattun kayan
gyaranjiki da Baki taba amfanida irinshiba a wannan qarnin,

Wani irin salo na gishirin kyan daukar magana zakiyi duk kikayi amfanida hadinmu b cika bakiba,ko yayan
Hutu basa nuna maki tsadar fataba,duk a 11k fa kachal👌🏻

Beauty kit:11k

Student package:7k

Soap:3k

Bridal kit 18k

Kicire kokonto ki warwaro Lalita kidebi Kaya n kerewa SAA

Chat:08062991549 or 07046881166 or 07067210195

Call:08064532391

Available in Kano and Kaduna
We also have beautiful yet luxury and unique frames for your apartments chat or call 07046881166

Serious buyers only please,

Inamasu bukukuwa😍

Kugarzaya @inteesar cakes nd more kuyi order small chops domin bakinku irinsu

Cupcake,fishroll,samosa,spring rolls dama duk kayan kwalam da makulashe kunemata 07067210195

Cika alkawari shine takenmu🤝

Thank you

*EL HABEEB*💥

©️Oum Hanan.

Writer of DR SAIF

*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡

(Home of expert & perfect writer's).

D'imbin godiya ga masu bibiyar littafin nan nagani kuma na yaba sak'onnin ku na riskata ako yaushe
thank you very much ALLAH yabar k'auna alkhairin ALLAH yakai muku aduk inda kuke sakallahu
khayran.💖

No 21.

Gaba d'aya sai Aunt Ramlah ta kasa gane inda maganganun Baba suka dosa musamman dataji yana
k'ara fad'in
"Duk duniya su ya kamata ace ta fara sanarwa wannan labarin ta inda yake shiga bata nan yake fita ba
itama Umma tasa baki sukayi tayi, sosai hankalin Aunt Ramlah ya tashi dataji Umma na kuka take
maganar cikin sanyin murya tace

"Baba, Umma har yanzu fa ban gane akan abinda kuke magana ba wllhy dan ALLAH ku sanar dani laifin
danayi".

"Haba Ramlatu ace Heedayah ta b'ata har kwanaki biyu amma baki sanar damu ba? yarinyar nan fa
amana ce a wajenmu idan baki fad'a mana ba wa zaki fad'awa? saifa yanzu da Mustapha yagano hotonta
a wayar Isma'ila abokinshi ana cigiyar ta sannan yazo hankali tashe yake nuna mana".

Aunt Ramlah batasan lokacin datayi murmushi ba idan ta fahimta daidai suma sunga yarinyar nan irin
Heedayah suke zaton Heedayahn su ce. Dariya ta d'anyi wadda tasa mamaki ya k'ara kamasu kafin wani
yayi magana tace

"Ku kwantar da hankalinku Baba wannan yarinyar ba Heedayah bace yarinyar ku lafiyar ta k'alau muma
munga hoton yarinyar haka mukasha mamaki wlhi yanzu ma Abban Nu'aym ya dawo da ita daga
makaranta suma shugabannin makarantar sunyi zaton itace da k'yar dai suka yadda shine duk ta tsorata
ta kasa zaman school d'in ta biyoshi suka dawo gida".

"Hukmullah la ajab". Haka kawai Baba ya fad'a yana faman jijjiga kai, Umma da Mustapha ma sakato
sukayi suna saurarar Ramlah cikeda d'imbin al'ajabin abinda take fad'a, yayin da Umma kuma ta d'auki
tunanin ta cak ta maidashi wani waje daban tana ayyana abubuwa da dama a k'asan ranta.

Y'ar dariya Aunt Ramlah ta k'ara yi tace

"Baba bari ku tabbatar ma da abinda nake fad'a bari in kirawo ta ku gaisa". murya tasa ta kira sunan
Heedayah da k'arfi wadda suke kitchen itada Zainab suna shirin d'ora abincin rana, Heedayah ta amsa
tareda ajiye albasar datake yankawa ta wanke hannunta a sink ta fito daga kitchen d'in zuwa falon inda
Aunt Ramlah ke zaune kan kujera, wayar ta mik'a mata tana fad'in

"Su Baba ne zaku gaisa dasu". karb'a tayi cikin murna tana murmushi takai kunnenta tayi sallama tana
gaishe da Baban ya amsa cikin jin dad'i haka ma Umma wadda tuni tabar kukan datake farin ciki ya maye
gurbinsa, har da Yah Mustapha saida suka gaisa yayin da Baba ya tubure shi lallai saidai Heedayah ta
dawo Katsina shi ya tsorata da wannan al'amari da k'yar Aunt Ramlah ta shawo kanshi ya hak'ura ko dan
saboda karatun data fara, haka dai ya hak'ura bada son ranshi ba sai dan irin magiyar da Ramlahn ta
dinga zabga masa.

Sun jima suna hira har saida credit d'in ciki ya k'are wayar ta katse sannan suka hak'ura, a tare su Baba
suka sauke ajiyar zuciya sai yanzu hankalinsu ya kwanta tashi Mustapha yayi ya d'auki wayarshi data
Isma'eel daya taho da ita ya k'ara yimusu sallama ya fita.

Baba ya juya ya kalli inda Umma take yaga itama kallon nashi take kowa da abinda yake tunani a ranshi,
numfashi ya sauke yace
"Anya Sa'adatu babu wani b'oyayyen abu a cikin wannan al'amarin? abin nan fa akwai d'aure kai da
tsantsar mamaki".

"Wallahi Malam abinda yake raina kenan tun lokacin danaji ba Heedayah bace yarinyar nan anya ba
y'an biyu bane ba kuwa? dan wannan ba za'ace iya kamanni kawai suke da Heedayah ba dan wllhy idan
an kwana dubu ana ce min ba Heedayah bace bazan yardaba kaga abu saikace almara". Umma ta k'arasa
maganar tana rik'e hab'arta tana k'ara jinjina girman al'amarin. Shima Baba kai ya shiga jinjinawa
hundred percent ya yarda da maganar Umma datace ko y'an biyu ne ba shakka wannan babban al'amari
ne dayake buk'atar bincike sosai idan ya kasance hakan ne kuwa zaifi kowa farin ciki zai sada Heedayah
da asalin iyayenta duk da yasan ba k'aramin rud'ani da tashin hankali Heedayah zata shiga ba lamarin zai
girgizata, Baba sun dad'e suna k'ara tisa maganar da Umma kafin shima ya tashi yayi mata sallama ya fita
dama ya fitan wani abin ne ya dawo dashi.

Matuk'a Aleeyu yake kula da Seeyamah zuwa yanzu harta fara sabawa da zaman kad'aitakar da
wannan azzalumin ya gadar mata, wani har hira suke zama suyi da Aleeyu. Habeeb kuwa tun ranar
dayaje batada lafiya har akayi mata allura bai k'ara zuwa ba ako yaushe dai yana kiran Aleeyu yaji lafiyar
ta, sau d'aya ya tab'a cewa Aleeyun ya bata suyi magana shima ba wata maganar arzik'i bace cewa yayi
idan ta shirya barin gidan ta fad'awa Aleeyu shikuma zaizo ta fad'a masa waye shi da dalilin dayasa take
masa BASAJA bai saurari cewarta bama ya datse kiran tasha kuka a ranar har saida kanta yayi ciwo
Aleeyu yana rarrashinta bama ta kulashi ba ta cigaba da kukanta zuciyarta na mata zafi.

Ta b'angaren Mujaheed kuwa sosai yasa ido akan duk wani takun abokin nashi batare dashi Habeeb
d'in yasani ba, yayi busy sosai cikin kwanakin dan anfara ginin d'aya kamfanin na sark'ok'i da fidda design
d'insu hakan yasa sam baya samun lokacin kanshi ma.

Police suna iya bakin k'ok'arinsu matsalar da har yanzu wad'anda sukayi garkuwar da ita basu kira waya
anji daga garesu ba bare aji kud'in da zasu yanka wanda za'a fanshe ta har abi diddiginsu abin dai sai
addu'ar ALLAH ya bayyana ta kawai.

★★__________★★.

K'arar spoon kawai ke tashi a dinning area d'in Ummi da Neehlah su kad'ai ne masu cin abincin
Habeeb kam wayace a hannunshi yana ta faman danne danne kanshi a k'asa ga abincin a gabanshi
amma kota kanshi baibi ba hakan yasa da Ummi ta gaji tace

"Ajiye wayar nan ka kama abinci kaci". d'agowa yayi ya kalli Ummin ya d'an b'ata fuska da fad'in

"I'm full fa Ummi tea ma kawai is okay".

Had'e rai Ummi tayi tace
"Ban yardaba Abbuna meyasa kake son yin wasa da cikinka ne? maza kaci abinci kafin inyi maka d'ura
yanzun".

Dariya ce ta tahowa Neehlah jin abinda Ummi ta fad'a tayi saurin maidata tana toshe bakinta ya ganta
sarai hakan yasa ya had'e rai sosai yana hararar ta yace

"Tashi kibar wajen nan". a marairaice ta d'ago tana kallonshi kafin ta maida kallonta kan Ummi taji ko
zatayi magana mutumin nan ya cika takura wllhy indai yana waje ba damar mutum ya sake.

"Akan me? banason rigima fa Abbu ya tana cin abincin ta zakace ta tashi kai waye ya takura maka? ka
kuma ajiye wayar nan kayi abinda yake gabanka".

Saidaya dallawa Neehlah harara wadda duk take a tsorace kafin ya ajiye wayar a kusa dashi yaja plate
d'in gabanshi ya fara ci, kad'an ya tsakura ya ture plate d'in ko ruwa baisha ba ya yagi tissue yana goge
bakinshi lokaci d'aya yana mik'ewa tsaye tareda d'aukar wayarshi, yana shirin barin wajen Ummi tace.

"Zauna, Hajiya Inna ta kawomin k'ararka d'azu dana shiga gaisheta".

Zama ya k'ara yi yana kallon Ummin yaji abinda zatace ya yatsina fuska yace

"Ummi ki k'yale tsohuwar nan ita indai bata fad'i laifin mutum ba batajin dad'i". d'an rank'washi Ummi ta
sakar masa a kanshi ya dafe wajen kuwa yana b'ata fuska yace
Chapter 21 · 0% Book details