← Book details El Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 39

Sashe 22

El Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kai Ummi me tace nayi ne? nifa rabon damu had'u ma harna manta".

"Eh, ai akan hakan ne tace ka daina shiga gaisheta gaba d'aya why?".

"Oops! wllhy Ummi ayyuka ne suka sha min kai saboda ginin danace miki za'a fara amma insha ALLAH
yau idan nadawo office zan shiga mu gaisa kafin ta kawo wani laifin tace nayi". duka Ummi takai masa ya
goce da sauri yana murmushi ya tashi yayi mata sallama ya fita daga falon ta bishi da kallo tana
murmushi.

Baki Neehlah ta tura tace

"Please Ummi ki samowa Yah Habeeb mata yayi aure ni wllhy yana takuramin dayawa".

Dariya Ummi tayi tace

"Nice ma zan samo masa? shi zai nemo abarshi da kanshi". Cikeda shagwab'a tace

"To ai Ummi shifa baya kula mata bare yasamu matar aure ALLAH nina gaji da zamanshi a gidan nan
kawai kibada sadakar shi".

"Lallai Neehlah kiyi addu'a kar yaji wannan maganar Abbun nawa zan bayar sadaka?". Ummi ta k'arasa
maganar tana dariya, itama Neehlahn saidata fad'i hakan saikuma tayi saurin toshe bakinta tana rarraba
ido cikin falon kamar wadda zata ganshi Ummi nayi mata dariya.
Kamar yadda yayi alk'awari washegari yana dawowa daga office bai k'arasa gidansu ba yayi parking a
k'ofar gidan Hajiya dan yanzu shi yake driving d'in da kanshi ya sallami driver'n sai jefi jefi idan yaji
bayajin yin tuk'in yake nemanshi suma bodyguard d'in duk ya sallamesu dama bawani so yake ba
Mujaheed ne ya kawo shawarar hakan lokacin daya dawo zai fara aiki a matsayin shi na C.E.O. da yak'i
yarda munafukin saiyaje ya had'ashi da Kawu Sulaiman shima ya kirashi yace ya kamata hakan yanzu
kuwa ya kori kowa.

Sanye yake cikin American suit black and white wandon da rigar ne bak'ake sai walk'iya suke yayin da
shirt d'in ciki ta kasance fara k'al mai dogon hannu butterfly tied yayi amfani dashi shima black color ya
matse k'ugunshi da bak'ar belt ta kamfanin D&G k'afarshi bak'in takalmi ne cover shoe na kamfanin
Gucci kamar yadda hannunshi ma ke d'aure da bak'in agogon fata na Gucci yayi matuk'ar yin kyau sai
baza k'amshi yake mai sanyin k'amshi da sanya nutsuwa.

Da k'akk'arfan takun nan nashi mai cikeda kuzari da koshin lafiya da ubangiji ya wadata shi da ita yake
takawa har zuwa inda k'ofar da ake shiga falon Hajiya duk da irin gaishe shi d'in da maigadi yakeyi hannu
kawai ya d'aga masa.

Hannu yasa ya kama handle d'in k'ofar ya bud'e ya shiga bakinshi d'auke da mak'alalliyar sallama
wanda ya saba yinta a saman leb'enshi ya shiga cikin falon.

Idanu, baki, hanci da dukkan gangar jikinshi ya saki yana kallon inda Hajiya Inna take zaune ga yarinyar
dayasa aka k'wamuso masa zaune kusa da ita tana ta mata surutu sunata dariya suman tsaye yayi ya
runtse idonshi zuciyarshi na kai da kawowa ya damk'e hannayenshi ya k'ara bud'e idanunshi da tunanin
basu gwada masa daidai bane saidai still tana nan yana ganinta ita d'ince dai ba wata ba.

"K'araso mana maigidana yau an tuna dani kenan duk da nasan yanzu haka Afeefah ce tayi maka
magana".

Sam baiji wani irin maganganu Hajiyan keyi ba Heedayah kawai yake kallo wadda tun shigowarshi tayi
tsuru tsuru ta sunkuyar da kanta k'asa kamar munafuka tana wasa da yatsun hannunta wad'anda suka
sha jan lalle ya kama sosai har yayi maroon color.

Wani irin juyawa yayi da dukkan k'arfinshi da wata irin sassarfa ya fice daga falon cikin wani irin taku
kamar zaki Hajiya da Heedayah suka bishi da kallo baki bud'e....

Mrs Salees Mu'az 💝

*EL HABEEB*💥
©️Oum Hanan.

Writer of DR SAIF

*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡

(Home of expert & perfect writer's).

Wato reader's kunsan ta kan mugunta ko😝😂 kowa fata da burinshi yaga yadda Gashua zaiyi idan yaje
yaga yarinyar gidan Hajiya daban wadda yasa aka k'wamuso masa itama kunsan gogan naku ai jarumi
ne 😉 mazewa zaiyi ya basar kamar baiga komaiba koya kukace 😅🤣.

No 22.

"ALLAH mai iko lafiyar Habibu k'alau kuwa yaro saikace mai jinnu". Hajiya tayi maganar tana kallon
Heedayah bayan fitar Habeeb, itadai Heedayah batace komaiba to me zatace? duka fa wannan ce
had'uwarsu ta biyu bayan wadda suka had'u akan layi, baki Hajiya ta tab'e tana fad'in

"ALLAH ya kyauta".

Da wani irin sauri yake tafiya lokaci d'aya yana lalubo number wayar Aleeyu ya sauke masa tijara da
kwandon masifa wane d'an iskan ne yace yayi sakaci har tasamu damar fitowa? akanme zai bari yarinyar
nan ta gudo gashi har ta k'ara zuwa wajen Hajiya saidai kuma sam wayar Aleeyun tak'i shiga hakan yasa
ranshi ya k'ara b'aci sosai tsaki kawai yake faman saki yana cije lips, dama a wajen gate yayi parking d'in
motarshi bai shigo da ita ciki ba. Bai saurari maigadi daya taso dan ya bud'e masa k'ofar ba ya bud'e da
kanshi ya fice tamkar zai tashi sama maigadi ya bishi da kallon mamaki.

Har ya bud'e k'ofar motar zai shiga saikuma ya fasa yayi tsaye rik'e da murfin motar kanshi a k'asa yana
wani tunani idan ya tafi yabar yarinyar nan anan ai yayi rashin dabara ma dole yasan yadda yayi ya fita
da ita dan k'ara tabbatarwa waccan ce kokuma watace daban, dan haka ya juyo a sukwane yakoma cikin
gidan bayan ya aro nutsuwa ya d'ora saman fuskarshi.

Har lokacin Hajiya da Heedayah suna zaune sai gashi ya k'ara shigowa baiyi magana ba ya nemi kujera
1sitter ya zauna yayi crossing legs d'inshi yana girgizasu, Heedayah kam kallon ikon ALLAH kawai take
cikin ranta take fad'in

"Da gani wannan mutumin ba mutunci zaiyi ba wllhy jifa yadda yazo ya zauna yana wani girgije girgijen
k'afa".
"Tohh yau kuma da wannan aka shigo?". cewar Hajiya tana kallonshi, shidai baice uffan ba sai gaisheta
dayayi ta amsa tana masa mitar kwana biyu ya yada ita, kamar mai ciwon baki yace

"I'm very busy Hajiya but I'm sorry yanzu ma wucewa zanyi akwai important issues dazan gabatar". yayi
maganar yana satar kallon Heedayah ta k'asan idanunshi ba wanda zaiyi zaton ita d'in yake kallo saboda
yasan takunshi.

"Aifa agogo sarkin y'an aiki ina zaka aiki ina kadawo aiki, tohh ALLAH dai ya taimaka yabada sa'a amma
kana k'ok'ari kam ALLAH yaji k'an mahaifinka".

Da Amin ya amsa itama Heedayah ta amsa, tsaye ya mik'e ya d'auko wallet d'inshi a aljihun bayan
wandonshi ya bud'e ya ciro kud'i masu yawa ya ajiyewa Hajiya a gefenta ta shiga yimasa godiya tana sa
masa albarka duk cikin jikokinta tafi cin gajiyar Habeeb zuwa goma idan zaiyi saiya mata kyauta kuma ba
k'arama ba banda sauran kayan buk'atu na yau da kullum dayake aiko mata dasu duk da cewa dai bata
nemi komai ta rasaba haka yake kyauta a jininshi take.

"Yauwa Habibu tafi da yarinyar nan ka kai min ita gida dan ALLAH dama shirin tafiya take yanzu". Cak ya
tsaya daga shirin fita dayake jin abinda Hajiya ta fad'a, daga Hajiyan har Heedayah sunyi zaton zai
musawa abinda Hajiyan tace saikuma sukaji yace

"Okay I'm waiting". yana fad'in haka yasa kai ya fice daga falon. (Yo dama nema yake ina zai musa 🤣).

"Ni Hajiya da kin k'yaleni kawai na tafi wllhy". Heedayah tace tana tura baki, dariya Hajiya tayi tace

"A'a gashi dai zai tafi d'in ke ba sauk'i na nemar miki bama samun abin hawa a layin nan namu ma ai
aikine tashi maza kiyi da jiki Habibu d'an gaggawa ne bai son jira". Haka nan ba dan ranta yaso ba ta
tashi tasa hijabinta wanda ya tsaya mata iya gwiwar ta mai hannu ash color wanda yahau da atamfar
jikinta kalar ash da fari ta rataya side bag d'inta mai sark'a ta yiwa Hajiya sallama, cikin kud'in da Habeeb
ya ajiye mata ta zaro 5k ta bawa Heedayah farko k'in karb'a ma tayi sai dataga Hajiyan ta had'e rai sosai
zata fara fad'a sannan ta amsa tayi godiya ta zurasu a jaka, farkon shigowa falon inda takalmin ta yake ta
k'arasa ta saka Hajiya har k'ofar falon ta rakata sannan suka k'ara yin sallama ta tafi tana tunanin ya zasu
k'are da wannan jikan Hajiyan yai ta wani cin d'aci yana cika da batsewa yana ma mutane muzurai itadai
yai mata wllhy ba k'yaleshi zatayi ba. tayi maganar a fili har da murgud'a baki.

Habeeb bai san hidimar datake bama yana zaune cikin mota yana jiranta sai sakin tsaki yake yana duba
agogon hannunshi, tunda ta fito daga gidan ya k'ura mata ido ta cikin glass d'in motarshi cije baki yake
yana wassafa irin d'iban albarka da rashin mutuncin dazai shuka mata idan harya kasance itace (Sam ya
manta da idan itace d'in dole ta razana idan ta ganshi amma wannan ko a jikinta sai ya alak'anta hakan
da duk cikin makircin ta ne).

A hankali ta k'araso ta bud'e front seat ta shiga ko gama daidaita zamanta batayi ba ya figi motar yabar
layin, kauda kai kawai tayi tana tab'e baki dama tasan dame Hajiya ta had'ata.

A wani irin slow motar take tafiya ga sanyin A.C da daddad'an k'amshin turarenshi dana freshner d'in
motar da suka had'u suka cakud'e suka bada wani lafiyayyen k'amshi wanda yasa dole Heedayah ta
lumshe idanunta tana sakin k'aramar ajiyar zuciya wadda ita kad'ai taji abarta. Duk a zatonta zai
tambayeta ta fad'a masa address d'in inda zai kaita saikuma taga ya d'auki wata hanyar daban hakan
yasa ta juya ta kalleshi taga ko b'arin datake bai kalla ba taga dai tafiya yake hankali kwance ya murtuke
fuska.

"Wai Malam ina zaka kaini ne bafa nan bace hanyar gidan".tace hankali tashe tana kallonshi, idan
kujerar dayake kai ta tankata to shima ya tanka kawai ya cigaba da bawa mota wuta hankalinta ya k'ara
tashi kamar zata sakar masa kuka tace

"Dan ALLAH bawan ALLAH kayi hak'uri ka saukeni insamu abin hawa please". Habeeb dai gabanshi
kawai yake kallo yana driving d'inshi magiya ta cigaba dayi masa akan ya sauketa amma yayi biris da ita,
ganin dai magiyar bazata kaita ba yasa cikeda tsiwa da rashin kunya take fad'in

"Wllhy ko ka tsaya in fita ko inyi maka ihu yanzun nan in tara maka jama'a". ta k'arasa maganar tana
k'ok'arin bud'e motar saidai da alamu anyi locking d'inta.
Chapter 22 · 0% Book details