← Book details Dr Habibullah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 4 OF 4

Babi wanda yayi magana har ya ajiye ya juya sannan ta shige cikin makarantar..

Dr Habibullah Part 1 Complete Hausa Novel · about 140 min read

Zaune suke ita da kawarta Amra suna hira Bayan tagama bata labari me tace..
"Gaskiya Amra na kusa tafka kuskure wanda na kusa shiga Uku wajan yaya Habib"
Shekeke Amra ta kalle ta tace "kyaji dashi jiddah, ke kika jama kanki ai asirin ki ya kusa tonuwa meyasa baki neme ni ba, kinsan fa Ni nayi abortion yafi sau biyu"!
Da mamaki jiddah ta lalle ta "amma mijinki bai sani ba"
"Tayaya zai sani tunda na hada baki da docton, ki bari zan raka ki ayi miki hankali kwance dama yanzu cikin ba wani kwari gareshi ba"
Gaban jiddah ne ya fadi ta dafe kirji tana zaro ido harga Allah itama bata tashi haihuwa yanzu ba sannan tana tunanin da zarar ta haihu Habib zai cigaba da wulakanta ta tunda cikin yake so ba itaba amma kuma tayaya zata iya wannan gangancin..
Amra ce ta katse ta da "karki tsaya wani tunanin next week zamu fara exam zakizo kina shiga damuwa dan karatu saiya gagareki da wannan cikin wlhy"
"Gaskiya Amra bazan iya ba Ina tsoro wlhy"
Tsaki Amra tayi tace "bafa zai gane idan ma zai gane ai bazai dau wani action ba tunda dama ba san juna kuke ba hakan zaisa yaji haushi ya rabu dake"
Shiru jiddah tayi tana tunanin maganganun Dr Ahmad na Karta sake kokarin zubar da ciki za'a iya samun matsala...
Ji tayi Amra ta dafa tace "jiddah ki kwantar da hankalin ki idan na raka ki yanzu saiki tsare-tsaren da Dr yake dashi wanda asirin ki bazai tonu ba, da zarar kimgama school saiki samu ciki a lokacin ki haihu bakida wata damuwa"..
Nan ma jiddah shiru tayi saidai ta yanke bin Amra kodan taji abinda Dr zaice..
Haka suka tashi tabi Amra suka bar makarantar kai tsaye asibitin da Amra tace suka nufa sunci Sa'a likitan na nan yana ganinsu ya fara dariya tareda yiwa Amra kirari da alamu sun saba..
"Ashe ana ganinku ma'am na zaki saina yanki ticket zan samu ganinki ai"
Wani irin fari tayi da idanun sannan tace "aikasan Ni ɗin koda yaushe zaka iya ganina saidai idan kaine bakaso ba,, yanzu dai ba wannan ba akwai abinda ya kawo mu"
"To inaji fadi yanzu a biya miki bukatar ki"
Jiddah dake gefe tayi tsuru tana ganin ikon Allah, ta nuna sannan tayi masa bayanin suna so ne a zubar da cikin dake jikinta saidai 4month ne amma tayi zubar jini wancan satin sanadiyyar yunkurin zubar da Cikin...
Murmushi docton yayi sannan yace "babu matsala mu dama ai wannan aikin mun kware a bangaren yaushe kuke so ayi aikin"
Kallan jiddah wacce keta faman kallan wayarta tana tsoron karsu dade Habib yaje school bai dame taba..
Tabo ta Amra tayi tace yaushe kike so ayi abortion din..
"Emm...Ina ganin..kamar rana ita yau.."
Dan murmushi Dr ya sakeyi ya gane a tsorace take yace "karki damu Hajiya komai zai tafi nrml ranar Monday kenan za'a yi saiku zo da misalin 8:30am Saboda lokacin ne nake Free"
Godiya sukayi masa sannan Amra tace ta Dan jirata a waje"
Fita jiddah tayi ta tsaya hankalin ta duk a tashe yake, saidai ta kusa 30m sannan Amra ta fito tana gyara head tie dinta...

Napep suka tare suka tafi saidai jiddah hankalin ta duk ya tashi tana ki Amra na cewa wai docton yace subar kudin zai musu kyauta,,.
Mamaki ne ya kamata hartayi niyyar magana sai kiran wayarta ya katse ta..
Mummunan faduwar gaba ne ya ziyarce ta, kasa daga wayar tayi harta gama ringing sannan tace mai napep ya kara sauri..

Habib ya dade a tsaye cikeda mamaki, meya hanata daukan wayar shi gashi dai yaji har an tashe su to ina taje Kenan..
Tuni ranshi ya gama ɓaci zuciyarshi tafasa kawai takeyi a take ya yanke wa kanshi jiddah tagama makarantar tunda iskanci da zata keyi kenan...
A hankali yake bin su da ido itada kawar Tata mai suffar karuwai a cewar shi,, kallo daya jiddah tayi masa taji gabanta ya sake faduwa har suka karaso wajan Amra ta gaida ko kallan inda take baiyi ba ya shige motar..
Sallama sukayi da Amra sannan ta shiga motar a darare ta zauna..
Yadda yaja motar kaɗai ya isa ya tabbatar mata da bakaramin ɓacin rai yake ciki ba..

Dakewa tayi kamar kamar batayi laifi ba ta kawar da kanta gefe kawai..

Yana gama Parking ta fara kokarin buɗe motar saidai jinta tayi a kulle ya rufe ta,, kallanshi tayi tace "yaya Habib zan fita"

Shiru yayi bai bata amsa ba kuma bai buɗe motar ba, saida ya dauki mintina sannan yace "daga yau na hana zuwa school dinki"

A zabure ta sake kallanshi idanuwanta suka fara kawo ruwa, cikin marairaice murya tace "me nayi, pls Dan Allah kayi hakuri karka hanani zuwa plsss"

Batareda ya kalli gefenta ba yace "nine mai baki umarnin fita,, right"!?
Daga kai tayi tana zubar da hawaye..
"To nace bazaki sake zuwa ba"!
Share hawayenta tayi tayi ta daga kai alamar to sannan ya buɗe motar yace "U can go"..

Da sauri ta fita ta nufi palourn tana kuka, mommy dake zaune tana ganin shigowar ta da kuka ta ajiye wayar tana janyota jikin ta..
"Meya faru, wani abu yayi miki"
"Mommy Wai bazan Kara zuwa school ba" ta fadi cikin kuka sosai..
"Ina Habib ɗin sam bazan yadda da wannan maganar ba tunda aiba shi ya sakaki ba"..
"Ya sake ficewa" jiddah tace kawai tana cigaba da kukan ta..
Tambayar mommy tayi laifin da tayi masa,,.
"Wai kawai dan fita dubo wata kasarmu ne nida Amra shine yazo ɗaukana bai sameni a school ɗin ba""..
Shiru mommy tayi dan tasan halin Habib wannan abin bacin da fushi ne a wajansa dole su kyale shi saiya sauko tayi masa maganar dan yanzu zai iya yin iko da matarsa ce ya hana babu kuma yadda zasuyi dole su kyale shi....

"Kinyi laifi jiddah da baki kirashi kin sanar dashi ba, yanzu ki bari zuwa Friday ya sauka a fushin sainayi masa maganar"
"Yanzu idan bai yarda ba shikenan narasa karatu na"
"A'a waya faɗa miki zaima yarda amma mubari zuwa Friday din, kinga Monday saiki je ko"
Daga kai kawai tayi sannan mommy tace ta tashi ta shiga ta shirya ta fito taci abinci...
Daki ta shiga dan shiryawa ta fito kamar yadda mommy tace..


Habibullah kuwa fasa fita yayi ya wuce part ɗinsa ya shiga bathroom saida ya daɗe sannan ya fito ya shafa wani tsadaddan mai da turare sannan ya kwanta yana tunanin inda jiddah ta tafi ɗazu..
Ko mommy tasa ya hakura to dole saiya rabata da wannan kawar Tata dan shi sam bai yadda da Ita ba..


Da kyar ya amince ya koma saboda mommy tasa baki saidai zuciyarshi takasa amincewa da komawar tata Amma babu yadda ya iya dole ya bar abin a zuciyarshi kawai..

Jiddah ta sanar da Amra Habib ne yasa kwana biyu bata shigo school ɗin ba, Amra tace shikenan ai tunda ya hana yanzu babu wata maganar zubar da ciki kuma amma kam ya cuceta dan yanzu ilimi shine kan gaba...


Yau takama Sunday tun safiya jiddah ke kiran Amra ta faɗa mata Habib ya barta gobe Monday zataci gaba da zuwa makarantar ta, saidai bata same ta, duk jiddah bataji dadi ba dan gobe sukayi da Dr zataje ayi abortion ɗin..
Shigowar ta daki Kenan taji kira tana dubawa taga Amra ce da sauri ta daga "Amra lpy na Kira wayarki tun safe a kashe".
"Lpy klau na ajiye ta kawai ta huta"
"Ok, gobe zan shigo school saboda ya barni naci gaba da zuwa"..
Wani ihu Amra tayi cikin murna tace saidai kuma harna kira Dr nace an fasa wannan maganar"
Tsaki jiddah tayi tace "to waye yace ki kirasa kice nafasa, ko munyi dake"?
"A'a nayi tunanin kin fasa ne tunda ga dalilin yi kuma yanzu babu wannan dalilin"

"Kinga Amra kirashi kice gobe zan zo ayi abortion din nan dan bazan zauna da cikin mugu ba wlhy sai zali na yakeci kuma shiba sona yake ba kamar yadda nima bai san ba sanshi nake ba, sam banaso wannan week din ya fita baayi ba dan asirina zai iya tonuw...." Wayarta ce ta fadi tsabar kaduwa da karar bugo kofar dakin ta da taji..

Habib ta gani wanda yaji duk maganar da takeyi tun fara zancan nasu mommy ce tace yazo ya kirata suyi lunch duk da baiso zuwan ba amma sai gashi yaji abinda ya firgita shi,,, duk ya fita kamannin sa tsabar bacin rai fuskar shi tayi ja har jikin sai tsuma yake idanuwan nan nashi kamar banashi ba,.. jiddah tuni tafara kuka tana matsawa jikin bango yanayin sa kaɗai ya gama tsoratata, kokarin zubewa kasa takeyi saidai tuni Habib ya damko hannun ta cikin wani irin zafin nama ,, da jikin bango Ya haɗe ta tareda zuba mata kyawawan mari har hudu sannan ya wurga ta kan bed, tuni bakinta ya fashe sai jini dake zuba tana kuka wanda bashida sauti tsabar shewar da yayi mata..

Ran Habib ya gama ɓaci fushinsa ya bayyana wanda jiddah bata taɓa ganin a wannan yanayin ba, cikin huci ya dauki littafin dake kan mirror ɗinta da biro ya rubutun shi sannan ya dawo kanta ya sake bata wani kyakkyawan mari ya fice da sauri cikin sassarfa zuciyarshi a matukar dagule...

Fitowar shi mommy tagani cikin wani irin yanayi saidai kafin tayi magana harya fice......


✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
[1/1, 2:25 PM] Aunty Usee: 🌹🌹🌹
*_DR. HABIBULLAH_*
🌹🌹🌹


*🌈K͎a͎i͎n͎u͎w͎a͎ W͎r͎i͎t͎e͎r͎s͎ A͎s͎s͎o͎c͎i͎a͎t͎i͎o͎n͎*



*🌹ʄɨʀֆt ʟǟɖʏ🌹*


*wαttpαd:-Ameenafirstladyy*


28


A hankali jiddah take sauke numfashi, saidai kana ganinta kasan bakaramar wahala tasha ba duk ta dan rame a fuska kamar wacce tayi jinyar sati guda...
A gefenta mommy ta zauna tana kallanta cikeda da tausayi dan jiddah ba yar riko bace a wajanta kamar yar cikinta take jinta,, kallanta ta dawo da shi kan Habib dake tsaye yana kallan fuskar jiddan.
"Habib ka koma gida kasa Laraba tayo abinci saboda karta farka babu abinda zataci"!
Daga kai yayi sannan ya fice batareda yace komai ba.
Yana fita mommy ta Kira Hibban ta sanar masa,, ciki kidima ya amsa da gasu nan tafe..


Cikin nutsuwa Habib yake driving ɗinsa saidai zuciyarshi taf take da sake sake Maganganun Ahmad, sam zuciyarshi takasa yadda da maganar tasa "to kodai yunkurin zubar da cikin tayi da kanta"? Ya tambayi kanshi yana dan dukan steering din motar tareda dan ajiyar zuciya,..
Cikin yan mintina ya karasa gida, a palour ya samu labara ya faɗa mata sakon mommy a takaice sannan ya nufi hanyar barin palourn,, tsayawa yayi sannan ya juyo ya shiga dakin jiddah yana bin dakin da kallo Kamar maisan ganin wani abu..
Ya dade a tsaye sannan ya karasa jikin mirror ɗinta, jakarta ya bude ya fara ciro wayar ta yana dubawa, cikin Sa'a yaga babu security, picture ɗinta ne a screen ɗin wayar hakan ya bashi damar kallan kyakkyawar fuskar ta sosai, tayi masifar kyau a hoton fuskarta dauke da kayataccen murmushi wanda yakara mata kyau sosai,, Habib ya dade yana kallan hoton sannan ya taɓe baki ya ajiye wayar dai dai da saukar idanuwanshi kan wani
Tablet din magani,, da sauri ya dauko cikeda fargaban Allah yasa ba zargin sane zai tabbata ba.
Tun Kafin yakarasa dubawa yaji zufa na karyo masa, a hankali ya zauna gefen bed ɗinta yana rintse idanuwanshi tareda dafe kanshi cikin matukar bacin rai da bakin ciki..
Ya dade zaune sannan ya tashi zai fice saikuma ya dawo ya dauki maganin ya fice zuwa part ɗinsa..


Bai dade da fita ba jiddah ta farka da kukan kiran mommy tana yunkurin tashi,, riketa mommy tayi tana fadin "gani jiddah ki nutsu kinji zaki samu lpy"
Gefen mommy dake rike da hannunta ta kalla wasu zafafan hawaye na zubo mata,..
"Barina kira doctor yanzu" mommy ta faɗa tana ficewa zuwa office din docton.
Rintse ido jiddah tayi hawaye suka sake zubo mata tareda tausayin kanta da mommy,,.
"Mommy zanyi mata wasu tambayoyi pls" doctor Ahmad yace yana shigewa cikin ɗakin.
A waje mommy ta tsaya saidai hankalin ta nakan jiddah gani takeyi kamar wani zai sameta..

Saida ya gama dube duben sa sannan ya kalli jiddah dake ta zubar da hawaye ya Kira sunanta cikin lallashi,, buɗe idanuwanta tayi saidai bashi take kallo ba gefe take kallo cikeda bakin ciki..
"Ki fara godewa Allah cikin da kikayi kokarin zubarwa bai zube ba"!
A dan zabure jiddah ta kalle shi tanajin wani sanyi da farin ciki yazo mata koba komai tasan su mommy zasuyi mata afwa..
"Jiddah meyasa kikayi yunkurin zubar da ciki bayan kinsan mai cikin yanasan abinsa"? Ya jefa mata tambayar kai tsaye..
Wannan karan wani kallo tayi masa na neman karin bayani..
"Kwarai kuwa Habib yanasan abinsa, saidai zan baki shawara karki kara kuskuren sake yunkurin zubar da ciki dan zaki iya samun babbar matsala wacce zakizo kina da kin sani"!
Kuka ne ya kwacewa jiddah cikin kukan tace "doctor banida wani sauran dana sani wanda ya kai na yanzu danake ciki, bansan da wanne fuskar zan kalli mommy ba kuma bansan irin hukuncin da yaya Habib zai yanke ba"..
Hakuri Dr Ahmad ya bata sannan ya faɗa mata bai faɗa musu gaskiyar komai ba saidai bai sani ba ko nan gaba su sani..!
Wani sassanyar ajiyar zuciya ta saki tareda yiwa Dr Ahmad godiya sannan tayi masa alkawarin bazata sake maimaita wannan kuskure ba..
Murmushi yayi ya fice zuwa wajan mommy dasu hibban da suka zo yanzu yace zasu iya shiga Yanzu..
"Sannu jiddah"
Hawaye ne ya zubo mata na tausayin mommy Dan tasan da mommy tasan maganar nan bazata taɓa jin dadi ba.
"Akwai matsala ne"?
"A'a mommy"!
Sannu suka dinga jera mata harda hibban da Afnan da suka zauna a dakin...


Habib ya dade a part ɗinsa sannan ya fito ya amshi abinci ya wuce ransa a matukar bace fuskar nan tayi ja kana ganin sa kasan ransa a bace yake matuƙa sosai..
Kai tsaye asibitin ya koma yana Parking ya nufi ɗakin da aka kwantar da jiddan,, duk su mommy suna zaune ya turo kofar dakin,..
A hankali ya shigo babu wanda yaji sallamar shi dan bai wani bude baki ba, saidai hibban naganin yanayin sa ya tashi shida Afnan suka fice dan sunsan halin sa sarai gashi kuma a yadda ya shigo rai a matukar ɓace..

Jiddah wacce ke kwance batasan shigowar shiba saida taji mommy tace "Habib ka dawo"..
A tsorace ta juyo inda taji mommy na Magana,,, karaf idanuwan su suka haɗu gabanta yayi mummunan faduwa dan ko ba'a tambaya ba tasan bakaramin ɓaci ransa yayi ba duk da batasan dalilin bacin ran nasa ba..
Wani kallo yayi mata wanda yasa saida cikin ta ya juya tayi saurin jiyar da kanta gefe tana maida numfashi..
"Akwai Wani abu ne? Mommy ta Tambaye shi ganin yanayin dayake ciki..
Girgiza kai kawai yayi sannan yayi hanyar fita.
"Habib kaje ka samu Ahmad ko za'a iya sallamar mu"
Baice komai ba ya fice cikin dacin rai da bakin ciki..
Hibban ya aika wajan Dr Ahmad dan haushin sa yake ji Musamman yadda ya iya zuba masa karya baya tunanin shima fa docton ne zai iya sani..
Barin hospital din yayi gaba daya ya koma gida dan yadda kansa ke masa ciwo sosai ga wani irin yanayi dayake jin kansa na tsananin zafin zuciya..

Dr Ahmad yayi dube sannan yace za'a iya sallamar su yanzu idan yaso Habib yasan abubuwan da za'a bukata na allurai da magunguna basai sun neme shiba..
Mommy tayi mamakin rashin Ganin Habib a asibitin saidai batace komaiba hibban ya kwashe zuwa gida..


Habib na kwance saman bed ɗinsa fitowar shi daga wanka kenan saidai har zuwa lokacin zuciyarshi na masa zafi ranshi yakasa kwanciya wani haushi da tsanar jiddah yaji a lokacin, sai lokacin ya tabbatar da jiddah bata sanshi bata kaunar shi tunda hartayi yunkurin zubar masa da cikin shi wanda yakejin tsananin san abinshi da kaunar sa..
Tabbas lokaci yayi da zai rabu da jiddah sannan ya kafa mata dokar karta sake yunkurin zubar masa da ciki idan kuwa ba haka ba saidai kotu ta rabasu dan yanzu yagama yanke zama da ita duk kuwa da irin soyayyar da yake mata,, wayar shi ce tayi kara kamar bazai dauka ba sai kuma ya mika hannu ya dauka batareda ya duba mai kiran ba..
Sultan kuwa jin Muryar Habib kawai ya tabbatar masa da ba lpy yake ba.
"Lpy kuwa naji sound dinka haka"?
"Sultan jiddah bata sona batasan haihuwa dani I don't know why"!? Ya faɗa cikin wani irin yanayi kamar mai san zubda hawaye..
"Kamar ya, bangane maganar taka ba"
Labarin komai Habib ya bashi duk da yanajin zafin abin,,..
"Saki kuma Habib Ashe ma bakaji haushin abin ba"!
"Kamar yadda ta nuna maka bata sanka batasan haihuwa dakai saika nuna mata kuskuren ta amma baka sake ta kai tsaye ba"
Shiru Habib yayi baice komai ba saidai tuni dama zuciyarshi tagama yanke irin hukuncin da yake tunanin saidai tabbas bazai ci gaba da zama da jiddah ba duk da yanzu yanajn wani abu gameda ita saidai baisan ko menene ba..!

Sallama kawai yayiwa Sultan ya kashe wayarshi dan yagama yanke hukunci bazai tsaya sauraran shiba a yanzu yadda yakejin kanshi,,, yanajin dawowar su mommy saidai ba fita daga part ɗin nasa ba saima gyara kwanciya da yayi..

Har dare su Afnan suna gidan itada afnan ɗin suna dakinta har hibban ya shigo yana tsokanar jiddan..
"Hankali ya tashi za'a rasa baby ko kunyar mommy bakuji ba keda yaya Habib"!
Dariya sukayi shida afnan jiddah kuwa murmushin kawai tayi tana hararan hibban ɗin dake kallanta yana dariya,, "waya faɗa maka mun damu"
"Gashi nan na gani harda su kuka"!
Dariya ta ɗanyi tace "kaga laifi nane"!?
"A'a ina fa bangani ba ko kadan saima kokarin ku dana gani dan da nine ko kaina bazaku gane ba"
Dariya sukayi su duka sannan yace Afnan ta tashi su tafi,, "kai yaya hibban tun yanzu" afnan tace tana langabe kai.
"Baku gama gulmar ba kenan ko dear" ya faɗa yana kallan Afnan tareda kashe mata ido.
"A'a mun gama muje kar wannan ta tsayar damu danta ga tana tareda nata mijin a gidan so take na manta da nawa" suka fice suna mata dariya tareda sake yi mata sannu..

Suna tafiya ta fito palour duk da batajin dadin jikinta duk ba kwari, saidai mommy Bata palourn sai Laraba kawai dake fito da kayan da aka ci a abinci..
"Laraba ina mommy"?
"Ta fita zuwa wajan Habibu wai zai siyo magunguna naji tace"
Shiru ta ɗanyi sannan ta koma ɗakin ta ta kwanta tana rufe ido..


"Habib wai lpy kuwa kake naga duk ka sauya kamar bakada lpy"
Habib dake kwance ya dan buɗe ido sannan ya tashi zaune "babu komai mommy"
"Wani ya bata maka rai ne" ta sake tambayar shi.
Baice komai ba sai kallo yabita dashi sannan yayi ƙasa dakai kawai yana jiran yaji me zatace..
Jin yayi shiru yasa mommy tagane miskilancin nashi ya motsa kenan hakan yasa tace "to shikenan ka tashi muje ka duba jikin jiddah saika siyo abubuwan da ake bukata tunda Dr Ahmad yace basai an neme shiba"
Tsuke fuska yayi saboda ko ganin jiddah bayasan yi yanzu dan ranshi sake ɓaci zaiyi yanzu da sauri yace "basaina dubata ba, zan siyo komai idan na fita"
"Shikenan to amma yanzu Yakamata kaje ka siyo dan kasan tana bukatar alluran da magungunan tunda babu wanda Dr Ahmad ɗin yayi mata"
"Ok momma" ya faɗa yana tashi yabi bayanta..


✍🏻✍🏻✍🏻
[1/1, 2:25 PM] Aunty Usee: 🌹🌹🌹
*_DR. HABIBULLAH_*
🌹🌹🌹


*🌈K͎a͎i͎n͎u͎w͎a͎ W͎r͎i͎t͎e͎r͎s͎ A͎s͎s͎o͎c͎i͎a͎t͎i͎o͎n͎*


*wαttpαd:- Ameenafirstladyy*



*🌹ʄɨʀֆt ʟǟɖʏ🌹*
ǟʍɛɛռǟ ʍʊֆǟ✍🏻


{30}


Ganin yanayin nasa yasa mommy tagane ba lpy ba, da sauri ta nufi ɗakin jiddah saidai yanayin da taga bakaramin tashin hankali ta shiga ba, da gudu ta karasa wajan jiddan saidai ina jiddah bata cikin hayyacin ta ga jini dake zuba daga bakinta da hannunta data ji ciwo a wajan..
A firgice mommy ta fice zuwa dakinta ta dauko Car key ɗinta sannan ta kira Laraba ta taya suka dauki jiddah zuwa motar ta..
Bata kula ba motar Habib ba dan hankalin ta a matukar tashi yake, gudu sosai takeyi da kyar ta iya neman layin hibban tace ya sameta a asibiti ko tambayar dayake mata bata tsaya bashi amsa ba ta kashe kiran tare kallo jiddah ta mirror ɗin motar...

Lokacin da hibban yazo tuni an shiga da ita dakin gaggawa,, yana gama Parking ya Kira mommy ta faɗa tana kusa da emergency room, cikin mintina ya karaso wajan,.
Kallo daya yayiwa mommy yasan hankalin ta a tashe yake sosai saidai Baiga Habib a wajan ba kuma ba jiddah kenan waye a cikin su ba lpy..
"Mommy waye ba lpy"?
"Jiddah ce"! Ta bashi amsa a takaice..
Bai sake magana ba suka hango Dr Ahmad tafe rike da abin lalubo numfashi..

Ita da hibban suna zaune suna jiran jin abinda ke damunta,,.
"Mommy kiyi hakuri gaskiya jiddah bakaramin wahala tasha ba, danta bugu a hannun ta sosai sannan tayi rauni a hannun wanda yasa ta zubar da jini sosai, Saboda haka yanzu muna bukatar jini wanda za'a kara Mata nan da 1hrs"
Gaban hibban yayi mummunan faduwa meyake shirin faruwa da jiddah ne,.,.
Mommy kuwa kasa magana tayi sai hibban ne yayi dauriyar cewa a gwada nasa ko zaiyi dai dai..
Babu bata lokaci Dr Ahmad yaja shi lab aka gwada sannan aka tabbatar babu wata matsala zai iya bata jini,..
Kusan 4hrs sannan aka kai jiddah dakin hutu tareda sa mata Oxygen Dan janyo numfashin ta..

Mommy rasa me zatayi ma tayi dan hawaye yaki zuwa mata a irin halin data samu jiddah, hibban kuwa kasa daurewa yayi saida ya zubar da hawaye dan fuskar ta ta kumbura saboda marin da Habib yayi mata ga sawun yatsun sa nan kwance a kan fuskarta,..
Sun dade babu wanda yayi magana sannan hibban ya share hawayen shi yafara ba mommy hakuri..
"Nayi kuskuren hada jiddah da Habib dama nasan halin su ba daya bane amma nayi tunanin Habib zai sauya idan ya auri Jiddah, soyayyar danake yiwa jiddah ne yasa banaso tayi aure a wani wajan sai a cikin ku, nasan kanasan jiddah a lokacin amma saboda kwadayin canza halin Habib yasa na canja ra'ayin ku,, kai kuma kayi kawaici da hakuri da kuma sadaukar da soyayyar ta ga Habib duk da naji dadin haka amma yau kam nayi dana sani"! Mommy takarasa cikin rauni sosai..

Kwarai naso jiddah kamar yadda naso rayuwa ta saidai banji haushin hada ta da yaya Habib da akayi ba, saidai har yanzu inajin tausayin jiddah marainiya Allah""" hibban ya faɗa a zuciyarshi yana riko hannun mommy.. "dan Allah mommy kiyi hakuri zubar hawayenki bala'i ne ga yaya Habib addu'a kawai zamuyi jiddah ta tashi lpy"..


(((Kome ƴaƴa sukayi kada iyaye su zubar musu da hawaye Saboda hawayen su bala'i ne ga ƴaƴansu✍🏻)))


Share hawayen ta mommy tayi da sauri tana girgiza "ba Habib nake zubarwa da hawaye ba jiddah nake zubarwa ina santa kamar yadda nake san ku hibban dole na tausaya mata ga ciki a tareda ita"
Hakuri ya sake bata sannan yace zai koma gida yasa Afnan ta hado mata abinci..
"A'a ka zauna tareda ita nizan je nayo mata yanzu Afnan tafara nauyi ba'a sata aiki ba".. mommy ta tashi ta fice..


Tsananin gudu Habib keyi saidai yakan sauke ajiyar zuciya lokaci zuwa lokaci,, kai tsaye booking flights yaje yayi ya samu Sa'a kuwa jirgin safiya ya samu zuwa Russia, yana dawowa gida ya wuce part ɗinsa ya shiga bathroom ya daɗe shower na zuba kansa sannan ya shiga bathtub ya salla wanka ya fito ya shirya cikin ƙananan kaya ya kwanta...

Tunani yakeyi meyasa jiddah takesan zubar masa da cikin sa wacce irin kiyayya ce takeso ta nuna masa ta haka,..
Tsaki ya danyi sannan ya tashi yafara hada kayansa..

Mommy na zuwa ta dafa ruwan tea ta zuba flask sannan ta haɗa mata jellof ɗin cous cous, sannan ta shiga dakinta dan dauko wayarta..
A kasa ta samu wayar ta tarwatse, dauko wayar tayi sai idanuwanta suka sauka kan takardar da Habib ya rubuta, hannu na rawa mommy ta dauka ta buɗe..
Zaro idanuwanta tayi cikin mamaki da tsoron abinda idanuwanta suka gani..
Saki ne Habib ya rubuta saki daya1, ran mommy yayi matukar ɓaci sosai haka ta fice rike da takardar a hannun ta ta koma palour..

Tsaf ya gama haɗa kayan sannan ya nufo part din mommy hango motar ne ya tabbatar da ta dawo..
A plaour ya sameta ta dauki abincin zata fice,, tana ganinsa annurin fuskar ta ya ɗauke..
Har ƙasa ya duka saidai kawar da kanta gefe tayi..
Duk da baisan halin da jiddah ke ciki ba yanzu ba kuma bai kula da irin abinda yayi mata ba, amma yasan yayi laifi tunda mommy ta sauya fuska,..
"Gobe zan koma Russia dan Allah..."
Katse shi tayi kafin yafara mata magiya dan yanzu bazata taɓa sauraran shiba yakaita makura a bacin rai..
"Allah ya kiyaye hanyar" tace tana barin palourn kai tsaye motar ta ta shiga ta fice daga gidan..
Ya dade a duke sannan ya shima ya fice zuwa part ɗinsa...

A asibitin mommy ta samu Afnan harta zo taji dadin hakan sosai, dan hibban ma yana ciki bai fita ba.. suna nan zaune jiddah tafara motsi da gudu hibban ya fice kiran Dr,, mintina biyu suka shigo tare..
Oxygen din ya fara cire mata dan har lokacin jinin da ake kara Mata bai kare ba, a hankali ta buɗe idanuwanta da sukayi ja harda taruwar jini hawaye ne ya zubo mata ta fara motsa baki tana kiran mommy,.
Dr Ahmad ne kaɗai dake kusa da ita yaji abinda take cewa sannan ya sanar da mommy ta karaso da sauri tana rike hannun jiddan..
"Mommy mutuwa zanyi hannu na zafi yake min"
"Jiddah bazaki mutu ba muna na tare da ke kiyi hakuri kinji"
Batace komaiba sai hawaye dake ta zubo mata mommy na sharewa..

Har akayi magrib jiddah bata sake magana ba, lokacin ancire roban jinin tana buɗe ido a hankali ta kalli su mommy. Dr Ahmad yayi mata allura sannan yace su bata wani abu ta danci..
Da dabara mommy ta dagata ta jingina da pillow sannan ta lallaba ta tasha tea mai kauri..


Zuwa dare jiddah tayi kwari saidai ba sosaiba har magana takeyi da murmushi dan kawai taga mommy ta fita a damuwa saidai har lokacin fuskar ta bata dawo dai dai ba....


7am su mommy suna zaune tagama ba jiddah tea danshi take sha tun jiya, turo kofar dakin ne yasa suka kalli Kofar, Habib ne cikin kyakkyawar shiga ya shigo sai zuba ƙamshi yake, alamar shirin tafiya yayi..

Yau su hibban duk basu fita ba shima bai damu da rashin fitar tasu ba,,.
Bai kalli gadon da jiddah take ba kamar yadda itama bata bata ko jiyo gefensu ba saima rufe ido da tayi danko ganin Habib batasan yi..

Mommy ma dauke kai tayi tana ji Habib ya kamo hannun ta yafara bata hakuri saidai bata juyo ba harya kau karshen maganar sa..
Juyowa tayi tace "Ni bakayimin laifi ba Habib kuma ban kullace ka abu daya na sani kawai ka hutar dani nemawa jiddah sakinta a wajenka, naga sakon takardar daka rubuta ta saki daya kuma mun gode sosai ka hutar damu nida ita, zatayi idda ta auri wanda takeso yake santa wanda bazai mata irin wannan cin mutumci ba"!

Ba hibban da Afnan kadai na har jiddah saida gabanta yayi mummunan faduwa jin abinda mommy tace, hawayene suka zubo mata sai yanzu ta gaskata irin tsanar da Habib ke mata tunda harta kai ga ya saketa tana kwance a gadon asibiti..
Takaici yasa hibban barin ɗakin Afnan tabi bayan sa itama hankali a dan tashe...

Sosai Habib yake ba mommy hakuri sannan ya faɗa mata abinda ya faru..
"Mommy koba yanzu ba nasan saita zubar da cikin nan, maganin da likitan ya bata magani ne wanda zai iya taba mata mahaifa saboda karfin sa, nayi kokarin ganar da ita amma takasa fahimta harta kai ga zata koma a karo na biyu ta zubar da shi wanda bansan mezai faru a lokacin ba.."
"Wannan shine dalilin dayasa ka ɗauki mataki kafin taje ta zubar ɗin ko"
"Da banji wannan maganar ba mommy yanzu da ba'a san halin da take ciki ba"..
Kwarai mommy bataji dadin abinda jiddah tayi ba kuma gaskiya Habib ya faɗa saidai bazata taɓa goyan bayanshi akan wannan ba tunda shima ya tafka babban laifi daya kasa faɗa mata ya dauki hukunci dakanshi....
"naji, hukuncin da kayi kam yayi, nina hakura aure ne dai yanzu ka raba shi Saika tashi ka tafi Allah ya kaika lpy bazan taba fushi dakai ba Habib"..
Jiki a sanyaye yayi mata sallama ta amsa ya fice zuwa airport..

8am jirginsu ya daga zuwa Russia✈✈


Jiddah ma tasan gaskiya Habib ya faɗa saidai bazata taɓa yafe masa wannan wulakancin dayayi mata ba harya saketa bayan tarin wahalar daya bata amma bai haƙura ba..
Juyo da kanta tayi tana kallan mommy tana zubar da hawayen nadama,.
Dakyar ta bude baki zatayi magana mommy ta dakatar da ita kawai tace "Ki bari ki samu lpy" daga haka ta tashi ta fice...


*Ɑɱɛɛɳɑ ɱuรɑ*✍🏻


4/12/2019


*ᴀᴍᴇᴇɴᴀ ғɪʀsᴛʟᴀᴅʏ*✍🏻[1/1, 2:25 PM] Aunty Usee: 🌹🌹🌹
*_DR. HABIBULLAH_*
🌹🌹🌹


вч
*🌹ʄɨʀֆt ʟǟɖʏ🌹*
ǟʍɛɛռǟ ʍʊֆǟ✍🏻

*wαttpαd:-ameenafirstladyy*


*🌈K͎a͎i͎n͎u͎w͎a͎ W͎r͎i͎t͎e͎r͎s͎ A͎s͎s͎o͎c͎i͎a͎t͎i͎o͎n͎*🤝🏻


{31}

Sosai mommy taci gaba da bawa jiddah kulawa kuma tana samun sauki sosai,, hibban da Afnan kuwa kullum suna asibitin dan anan yake barin Afnan ya tafi office saiya dawo yake ɗaukanta su tafi gida shima sai mommy tayi ta faɗan suzo su tafi saboda dare..

Kwanan su biyar jiddah ta warware sosai komai nata ya dawo nrml saidai rashin kwarin jiki saboda bata iya cin abinci sosai mommy tayi fadan harta gaji...

Kwana biyu jiddah ta kara taci gaba da zuwa makarantar ta hankali kwance saidai bata sake kula Amra ba Dan haushin ta takeji ganin take kamar ita taja mata koma menene..


Tare da mommy suka cigaba da rainon cikin nata wanda yanzu yafara girma duk da sai Afnan ta riga ta haihuwa, dan ita tuni hibban ya hanata fita ko ina..

tunda Habib ya koma sau biyu kawai sukayi waya da mommy saidai sama sama suke gaisawa ta kashe wayarta, duk da yasan dalilin amma yanaso yaji lafiyar dansa sannan ya sake yiwa jiddah jan kunne akan karta sake yunkurin zubar masa da cikin dan yasan ta da taurin kan tsiya kodan ta bata masa rai zata iya attempt din sake zubarwa..
tsaki yayi kasa ƙasa sannan ya ajiye book ɗin dake hannun sa ya dauki wayar shi yafara neman layin mommy..
mommy dake zaune itada jiddah sakamakon weekend ne, taji karar wayarta..
lokacin wayar na hannun jiddah tana ganin Habib ne ta sauya fuska sannan ta mikawa mommy wayarta tabar palourn Dan batasan ma abinda zai sake hadata da shi..
itama mommy ba yabo ba fallasa ta amsa gaisuwar,..
shiru yayi bai sake cewa komaiba, jin haka yasa mommy tace "akwai wani abu ne kuma"?
kamar bayasan maganar yac "a'a babu"!
"shikenan ka kulada kanka" kafin yayi magana mommy ta katse kiran sannan tabi bayan jiddah zuwa dakinta..
a kwance mommy ta samu jiddah tana karatu, saidai kallo daya tayi mata ta gane tunani ne fal zuciyarta,.
kusa da ita ta zauna sannan ta kamo hannun ta tareda kiran sunan ta.
itama jiddan kallan mommy tayi saidai tuni hawaye suka zubo Mata.
"meya faru"! mommy ta Tambaye ta..
cikin kuka jiddah tace "Ina tsoro kar yaya Habib ya mayar da auran mu, dan Allah mommy karki saurare shi dan wlhy kashe ni ne kawai bazaiyi ba muddin naci gaba da zaman aure dashi, nasan nayi kuskure kema bakiji dadin Hakan ba. "
hararan da mommy tayi mata ne yasa tayi saurin yin shiru.
"bana ce karna kara jin wannan Maganar ba tunda ta wuce, kuma saidai idan ke kika so Habib ya mayar dake"..!
kallan mommy tayi tareda taɓe fuska cikin shagwaba tace "Allah mommy bazan so ba, to tayaya ma zanso komawa wajan wanda baya sona.."
murmushi mommy tayi dan ta fahimci har yanzu da yarinta akan jiddah sosai.
"kinsan Habib bayasan raini bayasan wargi da taurin kai saboda haka ko mezai hadaki dashi saiki kiyaye ko kiranki yayi karki dagawa dan yanzu ya gano bakyasan zama dashi ne da zarar kinyi masa wani abu magana daya kawai zaiyi ya mayar dake kuma shikenan kinjawa kanki saboda saiki kiyaye"... mommy tace tana saukowa daga saman bed din sannan tace "kinji dai abinda ne idan kika jawa kanki babu ruwana".ta fice tabar jiddah a ɗakin..

maganganun mommy sun shigeta saidai har zuciyarta ta kudurta bazata taɓa daukan wulakanci daga Habib ba a yanzu saidai koma menene ya faru amma bazata dauki wulakanci ba ita kam..


Habib kuwa yakai makura wajan ɓacin rai sai faman tsaki yake shi kadai da tunanin jiddah a ranshi"muddin ta zubar masa da ciki to tabbas matakin da zai dauka bazaiwa kowa daɗi ba tunda ya fahimci har yanzu batayi hankali ba,..
jin ana masa nocking ne ya katse masa tunanin sa sannan yabda iznin shigowa duk yasan Sultan...
a hankali Sultan ya shigo saidai kallo daya yayiwa Habib ya gano ransa a bace yake, murmushi yayi sannan ya zauna yana daga kiran da Angelina tayi masa..
sun dade suna waya kamar karsu rabu sannan suka ajiye wayar yana maida kallanshi kan Habib wanda fuskar kamar hadari babu alamun fara'a ko kadan a kanta..
murmushi Sultan ya sakeyi sannan yace "ya akayi ne abban unborn"!
dan sassauta fuskan nashi yayi saidai baice komai ba.
"look habib fadamin Matsalar rike damuwa bashida wani amfani"!
saida ya dauki dan lokaci kamar bazaiyi magana ba sannan yace "Sultan kasan maganata bata wuce ta waccan yarinyar"
"wacce yarinyar kenan!?" Sultan ya tambaya cikin rashin fahimta.
tsaki Habib yayi sannan yayi banza dashi dan gani yake Sultan ya gane raina masa hankali yake..
"ohhh! jiddah kake nufi wai"?
"yahh! ita" Habib yace sannan ya faɗa komai har sakin da yayi mata sannan ya baro ƙasar..
sauke numfashi Sultan ya kalli Habib yace "gaskiya kayi kuskure Habib".
harara Habib yabi shi dashi sannan yace "danayi me"?
"jiddah tanada hakuri meyasa zakaga laifin ta bayan kaine mai laifi duk fa macen da nunawa kiyayya to zata iya abinda yafi wannan tunda itama ba sanka takeba, tana ganin kamar dan cikin kake santa duk ranar da babu zataga wulakanci to dole tayi yunkurin zubar dashi, kuma kaga har yanzu jiddah she's youn so saina lallaɓata sannan zata fahimce ka"!
wani kallo Habib yakewa Sultan harya gama, murmushi yayi dan maganar Sultan ɗin ta karshe dariya ma tabashi wai kamar jiddah zai lallaba..
"yanzu me kake nufi"
"ina nufin ka mayar da ita tunda har saita haihu sannan ta gama iddarta"
"na mayar da ita,"! Habib ya tambaya cikeda mamakin kalmar.
"eh mana haka nake nufi"
tsaki Habib yayi yace "never, tayaya kake tunanin Ni zan cigaba da zama da wannan yarinyar"!
mamaki ne ya kama Sultan dan shi sai yau ya dada tabbatar da cewa Habib baisan menene so ba..
duk yadda yaso ya fahimtar da Habib yaki fuskantar shi dole ya kyale shi suka rabu a haka tun kafin ya sauya mishi Yanzu...

Habib ya dade yana juya maganar Sultan a ranshi saidai shi sam baya jin zai iya sakewa harya mayar da auran nasu dan yanajin zafin abinda tayi har yanzu...


yau kwana biyu Kenan da Habib ya kira mommy saidai bai sake tunanin sake kiran nata ba duk da yanaso ya samu yaji lafiyar dansa saidai babu yadda zaiyi sai hibban ya kira yace ya dinga kaita duk inda zataje..
"to yaya".
"karka kara sakacin barinta zuwa wani wajan ita kadai"!
"Amma yaya akwai lokacin da nake tsaka da aiki mezai hana a samo mata driv.."
da kakkausar murya Habib ya kira sunan shi sannan yace "kafi kowa sanin banasan gaddama, ko"!
"I'm sorry Yaya"
tsaki kawai yayi ya kashe wayar, har zai ajiye sai kuma ya yafara neman layin jiddah,cikin fushi ya kara wayan a kunnen shi saidai tun kafin ta daga yaji kamar ya katse dan baisan me zaice mata ba...
cikin tsananin mamaki jiddah take bin wayar da kallo, maganganun mommy ta tuna yasa tayi saurin dagawa saidai Muryar a cunkushe..
"waye"? ta Tambaya cikeda rainin hankali..
wani bugu yaji zuciyarshi tayi cikin mamaki da takaici ya yanke kiran kawai yana huci..
ya dade yana juya abin a ranshi da kyar ya dauki wayar tashi ya tura mata da sako..
"karki sake fita batareda izinina ba, sannan hibban zai dinga kaiki duk inda zaki.."! Yana ganawa yayi sendind sannan ya shiga bathroom..

tsaki jiddah tayi ganin sakon nashi dan abin ma haushi ya bata wai karta sake fita waya faɗa masa yanzu zataji maganar shi bayan sakin dake tsakanin su, cikin takaici itama tayi masa reply..
"ohh Yaya Habib I'm sorry, saidai idan fita ta kamani zan fita kawai tunda baka nan, sannan ka kyale yaya hibban shima abubuwa sunyi masa yawa so zan dinga hawa na haya kawai, kuma ka rage isa yanzu akwai saki tsakanin mu watanni ya rage nayi iddah..."

fitowar shi kenan yaji karar shigowar sako, saida ya gama shiryawa sannan ya buɗe sakon saidai kafin ya gama karantawa kanshi yafara wani mugun sara masa babu shiri ya saurin zama kan bed ɗinsa Dan yadda yaji wata juwa na daukan shi ga wani zufa dake karyo masa tako ina kamar ba daga wanka ya fito ba...


✍️✍️✍️✍️
[1/1, 2:25 PM] Aunty Usee: 🌹🌹🌹
*_DR. HABIBULLAH_*
🌹🌹🌹


ռǟ
*🌹ʄɨʀֆt ʟǟɖʏ🌹*
ǟʍɛɛռǟ ʍʊֆǟ✍🏻

*wαttpαd:ameenafirstladyy*


*🌈ĸaιnυwa wrιтerѕ aѕѕocιaтιon*🤝


{32}


A hankali ya dafe kanshi dayaji yana sara masa, sam yaƙi yarda da jiddah ce kemasa magana haka..
To kodai ba ita bace"? Ya tambayi kanshi sannan ya tashi da sauri ya dauki Car key ɗinsa ya fice ranshi a matukar ɓace..

Murmushi jiddah tayi dan tasan yanzu bakaramin bata masa rai tayiba, koba komai yau ta rama wulakancin daya saba yi mata,,wani murmushi ta sakeyi sannan ta nufi palour wajan mommy..
Zama tayi tana murmushi wanda yaki yankewa fuskarta, mommy ta lura da hakan saidai batayi niyyar yiwa jiddan magana ba saida taga murmushin yaki karewa..
"Wai lafiyanki kuwa kike ta faman murmushi ke ɗaya"!?
Saita fuskarta ta ɗanyi sannan tace "babu komai fa mommy, Afnan ce ta kirani Wai Yaya hibban ya hanata fita"
"To kuma shine kike mata dariya kema ai na kusa hanaki fitar"..
Shiru jiddah tayi batace komaiba dan tasan idan taci gaba da jan maganar yanzu itama sai mommy tace ta daina fitar gaba ɗaya..


Har dare Habib yarasa abinda yake damunsa duk hankalin shi na kan abinda jiddah tayi masa saidai ya rasa taya zai nuna mata ƙarshen iskancin ta..
Wani irin murmushi yayi wanda har saida sautin sa ya fita sannan yayi kwafa yana jawo wayarshi yafara tura mata sako..
Yana gamawa ya tura mata sannan ya gyara kwanciyar shi yana ci gaba da murmushin wanda shi kadai yasan ma'anar sa...


Jiddah kuwa tanaji wayarta tayi kara alamun shigowar sako saidai bata duba ba saima hirar su suka cigaba dayi itada mommy hankali kwance sam batayi tunanin Habib bane..
Sallama tayiwa mommy Dan bacci ne sosai takeji sannan ta koma ɗakinta ta shirin kwanciya..
Buɗe sakon ɗazu saidai a zabure ta tashi tana dan zaro hankalin ta a tashe dan tuni hawaye suka fara sauka kan fuskarta..
Cilla wayar Tata tayi gefe sannan taci gaba da kukanta mai tsuma zuciya,,..
"Meyasa Habib yakemata hakane, meyasa bayaso takarasa rayuwar ta da wanda takeso, shi ba santa yakeba kuma yanzu bazai bari ta auri wanda takeso ba Kenan shiyasa yayi saurin mayar da auran nasu dan yaci gaba da cin mutuncin ta kenan"? Rasa amsar da zata bawa kanta tayi sai kuka da taci gaba dayi sannan ta kwanta dan zazzaɓi yafara rufeta sosai,,, da kyar ta samu bacci barawo ya sace ta bata sani ba....

Da sassafe mommy ta sauko palour saidai tayi mamakin rashin ganin jiddah dan ta saba kullum tana riga mommyn fitowa palourn, har ta nufi ɗakin jiddan sai kuma ta fasa ta koma kitchen dan haɗa coffee Kamar yadda ta saba,,,

Shiryawa jiddah tayi ta fito palourn, kai tsaye kitchen ta nufa wajan mommy ta gaida ta,.
"Jiddah lpy kuwa"!?
Kasa tayi da kanta sannan tace "babu komai mommy"!
Hankalin mommy ya tashi dan tasan jiddah kuka tayi amma taki faɗa mata abinda ya faru..
"Jiddah I'm your mother, tell me what happened"!?
"Mommy kaina ne yayimin ciwo jiya shine nayi kuka amma babu abinda ya sameni"
Sauke ajiyar zuciya mommy tayi sannan tace "kinsha magani ko"?
"Eh Nasha".
"tam jeki barina na hada miki wani abu kici"
da sauri jiddah tace "a'a mommy fita zanyi ai"!
"ina zaki da safiyar nan, yau ba school ko kin manta ne"!
"pls mommy gidan yaya hibban zanje, inaso naji yaushe zamu koma hospital awo ne" ta karasa tana kasa da kanta dan taga irin kallon da mommy ke mata.
"toke da bakida lpy kuma kibari saiki kira shi a waya"
"pls mommy Dan Allah kibarni naje"
"gaskiya jiddah kin fara koyan yawo sosai, Yakamata yanzu kisan kinyi nauyi 6month fa amma ke naga kamar bakyajin nauyin jikin ki,,kije saiya dawo dake karki dawo da kanki"
da hanzari tace "tam mommy ngd, I Miss you" ta faɗa tana ƙaƙalo murmushin dole..
"shikenan ki fasa zuwan kawai tunda idan kinje ma kewata zakiyi" mommy tace tana ci gaba da aikinta..
"a'a mommy aiba dadewa zanyi sosai" tana faɗa ta fice daga kitchen din da sauri kamar mommyn zatace ta dawo..
dan murmushi mommy tayi danta gane saurin da jiddan keyi..


napep ta tare har gidan hibban ɗin duk da ba wani nisa ne dasu sosaiba, tana zuwa ta biya me Napep din ta shige..

a palour ta samu Hibban ɗin yana kallan laptop ɗinsa, jin sallamar tane yasa shi dagowa, sai kuma yayi saurin tashi yana murmushi..
"yau uwar biyu ce a gidan da safe haka"!..
murmushi kawai tayi ta zauna dai dai fitowar Afnan tana "ashe yau za'a yi ruwa harda ƙanƙara kenan'!

gaida hibban ɗin tayi saidai bai amsa ba sai Binta da kallo da yayi yanasan nazartar fuskarta.
"jiddah akwai matsala ne"!?
hawaye ne ya zubo mata takasa bashi amsa Afnan kuwa na ganin haka ta basu waje dan tasan magana ce ta kawo jiddan tunda ga alaman ta fara kuka..

Afnan na barin palourn hibban ya dawo kujerar dake opposite ɗinta cikin nutsuwa yace "fadamin meya faru"?
share hawayenta tayi Sannan tace "yaya hibban wai yaya Habib ne yace ya dawo dani ɗakinsa..".. kuka ya sake kwace mata..
shiru hibban yayi na wani lokaci sannan yace "ma'ana kenan yanzu ke matarsa ce tunda bikiyi idda ba"?
daga kai tayi kawai batace komaiba..
sai can sannan tace "narasa me yaya Habib yake game dani, ko soyake saiya gama sa rayuwata a bakin ciki sannan zai rabu dani, sam bani yakeso ba tuntuni ya fadi haka har saida ya rabu hankalin shi ya kwanta amma saboda ya cimma wani kudirin yake muci gaba da zama, zaman na bazan san wanne irin zama zankira shiba" kuka ya sake kwace mata..

tabbas hibban yasan halin yayan nashi saidai zuwa yanzu yafara gano nasarar auran jiddah dashi dan ya sauya abubuwa da yawa daga cikin rayuwar dan uwan nashi, bazai taba so wani abu ya rabasu ba a yanzu, saidai bazai iya jure ganin jiddah a wani irin hali na bacin rai koda yaushe ba, saboda yanajinta kamar kanwarsa da suka fito ciki dayane kuma koba komai shine silar kasancewar ta anan a Yanzu dole ya damu da damuwar ta kuma dole ya sama mata yanci da kwanciyar hankali koya yayane..
da kyar ya iya saita yanayin shi ya fara yi mata a hankali..
"shine kike kuka jiddah"
ɗago kai tayi tana kallanshi da manyan idanuwanta, "ya kakeso nayi yaya hibban ko so kakeyi bakin ciki ya karasa Ni..."!
dan murmushi hibban yayi sannan yace "karki damu, yanzu dai ki samu kici abinci sai muyi maganar"..
"banaci na koshi" ta faɗa a hasale.
dariya hibban ya farayi mata "ke matsala ta dake kafiya da taurin kai yanzu idan bakici abinci ba tayaya zaki fahimci abinda zance miki"
share shi tayi kamar bada ita yake magana ba, har gabanta ya kawo abincin da kyar ya samu taci sannan yace ta huta tukun kafin yayi wanka ya fito..
a daki ya samu Afnan a kwance, zama yayi yana jawo ta jikinshi "babynah kalau kike kuwa"? dariya tayi tace "har kun gama maganar"?
"a'a wanka zanyi tukun, muje kiyimin naga kinfini sauri idan ke kikayimin"
"naki wayon salon duk ka jikani da ruwa bayan kasan yanzu nayi nawa"
dariya shima yayi sannan ya shige bathroom din yana rufo Kofa...


tsaf ya shirya ya fito palourn, lokacin Afnan na kitchen jiddah kuma na zaune inda ya barta..
zama yayi sannan yace "ina Afnan ɗin"
"tana kitchen"jiddah ta bashi amsa..
"ohh! ya Allah na hanata aiki sosai saboda yanzu tayi nauyi da yawa amma takiji" hibban ya faɗa yana Binta kitchen din.
jiddah na nan zaune suka fito rike da hannun juna sai shagwaba take masa ya barta tayi aikin shikuma yana mata dariya, bakaramin burge ta sukayi ba saitaji inama itace a wannan yanayin yanzu..
daki Afnan ta koma tace zata kwanta tunda yaki barinta tayi wanke wanken..
"yauwa my baby, dama bacci yakamace ki yanzu ai" hibban ya faɗa..
dariya tayi tabar musu palourn taje tayi kwanciyar ta abinta..


shawara hibban ya fara bata sannan yace tabi duk wata hanya da zata daina yawan hadata faɗa dashi..
"kenan naci gaba da zaman wulakancin"!?
murmushi hibban yayi yace "jiddah ke kika jawa kanki wannan"
da mamaki ta kalle shi tace "kamar yaya kenan"?
"yaya Habibullah yana sanki jiddah halayenku ne yasa kuka kasa fahimtar juna,tun farko ke kika nuna kina tsoron shi sosai Sannan Nasha faɗa miki duk yadda kika dauki yaya Habib haka zaki same shi"
"wlhy Habib baya kaunata ne yaya hibban, bazai taba sona ba kuma"..!
"shikenan ki gwada ki gani nina faɗa miki yaya Habib yana matukar kaunar ki amma bazaki gane hakan bane saikin gwada shi"...
a haka hibban ya dinga bata shawara karshe dai saida jiddah taji kwarin guiwa da kwanciyar hankali..
daga karshe jiddah ta kalli hibban tace ""Allah yasa karya bani matsala"
"saidai kiba kanki matsala, amma yaya Habib bashida wata matsala zaki fahimce shi fiye dani"..
saida Hibban ya tabbatar jiddah hankalin ta ya kwanta, sannan ya yace ta tashi ya mayar da ita gida tunda mommy harta fara kiran shi..


✍️✍️✍️
[1/1, 2:25 PM] Aunty Usee: 🌹🌹🌹
*_DR. HABIBULLAH_*
🌹🌹🌹


ռǟ
*🌹ʄɨʀֆt ʟǟɖʏ🌹*
ǟʍɛɛռǟ ʍʊֆǟ✍🏻

*wαttpαd:Ameenafirstladyy*


________________________
*🌈ᴋᴀɪɴᴜᴡᴀ ᴡʀɪᴛᴇʀs ᴀssᴏᴄɪᴀᴛɪᴏɴ*
```{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain & motives the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
_________________________


{33}


Suna zuwa kuwa mommy tafara yi masa faɗa akan meyasa ya bari takai rana haka..
Saurin tarewa jiddah tayi da cewa "mommy kinsan idan na hadu da Afnan bamasan rabuwa" hararan ta mommy tayi tace aina sani dama daga yau dai bazaki sake fita ba saidai awo ko school" tana gama fadan haka ta wuce sama ta barsu..
Hibban bai wani zauna ba yayi mata sallama ya tafi dan yanada aiki a gida.


Kwanaki sun ja kamar yadda cikin jiddah yanzu yakai 7month, yanzu kam tanajin nauyin kanta sosai, saidai hakan bai hanata zuwa makarantar taba sannan komai tanayinsa yadda Yakamata dan sosai ta mayar da hankalinta kan karatun nata..
Sam yanzu babu abinda ya sake hadata da Habib dan ko mommy yanzu ba sosai take samun shi a waya ba shiyasa take komai hankalin ta a kwance sannan take saurin manta wa dashi a matsayin matsalar ta, sai shirin exam kawai takeyi yanzu, bakaramin murna takeyi ba yadda abin yazo mata cikin sauki zata haihu batareda wani tunanin makaranta ba..

Yau da sassafe ta fito cikin shirin ta tana sauri sauri zata fice daga tsaye take breakfast din cikin sauri..
Mommy ce ta sauko palourn taga yadda jiddan ke sauri taki zama taci abincin cikin nutsuwa..
"Saurin duk tafiya school ɗinne"?
"Eh mommy karna makara shiyasa"
Kyaleta mommy tayi sannan ta wuce kitchen dan haɗa coffee.
Hibban na shigowa ta ajiye cup din hannunta tana fadin "yauwa yayana dama kai nake jira"
Dan kallanta yayi sannan yace "ai saki bari na gaisa da mommy ko" ya faɗa ya nufa kitchen din.
Tare suka fito da mommy sannan sukayi sallama suka fice daga gidan..


Cikin ikon Allah jidda ta fara exam hankali kwance duk da cikinta yayi girma sosai amma haka take kokari takeyi batareda wata damuwa ba, kullum hibban ke kaita kuma ya dauko ta shima kuma ba karamin tausayin ta yake jiba..

Da asuba mommy ta tashi jiddah tace zata tafi asibiti Afnan ce zata haihu, cikeda murna jiddah tace zata bi mommyn amma tace babu inda zata bita tunda yau ma tana da exam..

Jiddah na cikin shiri taji karar wayarta, sunan mommy ne yasa tayi saurin picking,, wani dan karamin ihu tayi na murna jin afnan ta haihu.
Mommy kuwa kashe wayarta tayi dan tasan halin jiddah yanzu saita fara yi mata shirme...
Jiddah sai ita kadai ta tafi dan hibban bai samu kaita ba, har aka tashi suka fito, tayi mamakin ganin hibban yazo ɗaukar ta da murmushi ta karasa jikin motar tana tsokanar shi..
"Yaya hibban yau an ka zama baba" ta faɗa tana dan taɓe baki.
Dariya yayi yace "saura ke zaki zama mama, wai wayaga jiddah da baby" shima ya faɗa yana mata gwalo..
Haɗe fuska tayi tace "wlhy kasan nikam zanyi kyau da baby ba Kamar kai ba".!
"Ni dama nace zanyi kyau ne, saidai ke mu jira muga irin kyaun da zakiyi ai"
Sarai tasan magana ya faɗa mata dan tsokana amma saita fuske ta shige motar yaja suka bar school ɗin..

Kai tsaye gidan shi tace ya kaita, acan ta samu mommy tana shiga ta fara murna tana daukan baby girl din tareda zuba mata ido kamar ta hadeyi ta..
Sai yamma itada mommy suka bar gidan,..
"Amma Afnan tasha wahala sosai ko mommy"?
"A'a bata sha wata wahala sosaiba"
"Amma naga ko magana batayi sosai" ta sake tambayar mommy..
Mommy dake driven kuwa dariya jiddan ta kusa bata amma sai make tace "nima dai bansan Dalili ba"..
Sai tambayoyi jiddan ke mata tana bata amsa sannan tace "mommy mu wuce shopping pls"
Batareda mommyn tace komaiba ta juya kan motar suka wuce shopping mall dan tasan idan ma bataje ba ta shiga Uku da shagwaban jiddah..
Sosai ta jidi kaya kamar hauka mommy kuwa duk siyayyar kayan babies tayi dan yanzu tana sane cikin jiddah ya shiga wata na tara, ba kananun kudi mommy ta kashe a lokacin ba ita kuwa jiddah batasan ma mommy nayi ba hankalinta yana kan kayan makulashe..

Yau su jiddah suka gama exam suka samu hutu bakaramin daɗi taji ba dan sunan Afnan zatayi shi hankali kwance gobe sai faman shiri sukeyi gidan..

Tun asuba ta tafi gidan hibban, acan ta shirya akaci suna aka zubar da dukiya dan hibban yayi bajinta ya zubar da kudi ba kananu ba,,..

Tunda Afnan ta tafi gida wanka badan hibban yaso ba ya barta dole ya dawo part ɗinsa Dan yace bazai iya zama gidan shi kadai babu matar sa ba duk sanda ta dawo ya saiya koma shima, jiddah tayi masa dariya da tsokana sosai saidai shi bai kulata ba saidai yayi dariya kawai...
Dakin mommy jiddah ta koma da kwana dan dole mommy ta tilasta Tata ta koma dan kar haihuwar tazo ba kowa kusa da ita..


_pls kuyi manage da wannan_👈


coммenт and voтe 🤝🏻

*ʄɨʀֆt ʟǟɖʏ*✍🏻
[1/1, 2:25 PM] Aunty Usee: 🌹🌹🌹
*_DR. HABIBULLAH_*
🌹🌹🌹


ռǟ
*🌹ʄɨʀֆt ʟǟɖʏ🌹*
ǟʍɛɛռǟ ʍʊֆǟ✍🏻


*wαttpαd:-Ameenafirstladyy*


*🌈ĸaιnυwa wrιтerѕ aѕѕocιaтιon*✍🏻


{35}


....Ranar suna yaro yaci suna Abdulmalik, mommy da hibban sunyi gwaninta dan an zubar da dukiya kamar hauka sun nunawa jiddah gata kamar yar cikin su, jiddah har kukan farin ciki tayi a boye dan batayi tunanin zata ga gata kamar haka ba, iya shagali kam anyi mutane sunyi sam Barka da tarin kyaututtukan da suka samu..

inna marka da sauran Yan uwan jiddan sunso tafiya da ita ƙauye amma fafur mommy taki yarda tace baza'a rabata da yarta ba idan tayi arba'in da kanta zata kawo ta, badan sun so ba bayan kwana biyu da sunan mommy ta haɗa musu sha tara ta arziki suka koma cikeda da farin ciki..


mommy da kanta take bawa jiddah kulawa sosai, Abdul kuwa sai kiba yake abinsa ga kamannin sa da mahaifin sa dake sake fitowa ziryan,..
iya so jiddah na nunawa Abdul dan yanzu kam ta gane ta kusa tafka kuskure na zubar da ciki da yanzu Abdul baizo duniya ba gashi yanzu wani irin so take masa wanda bazata iya fasaltashi ba..
kwana biyar ya rage ta koma school duk ta gama shirye shiryen ta, mommy Kam fafur tace ta dinga tafiya da Abdul dan bazata bar mata shiba..
"wlhy yacika fitina bazai barni nayi karatu yadda ya kamata ba"
"ai sai kiyi kuma, naga mai zaici idan kika barshi a gidan"mommy ta faɗa bata kalli inda jiddan take ba.
da sauri jiddah tace. "sai a siya masa Madarar jarirai"..!
kallan bakida hankali mommy tayiwa jiddan sannan tace "jiddah ki fita ido na na rufe ke haka akayi miki, tsabar iskanci gaki da lafiyar ki za'a sai masa wata madara saboda wani Banzan karatu naki, to wlhy baki isa ba tun kafin ranki ya ɓaci banasan sake jin wannan maganar..."! a fusace mommy tabar palourn..
duk jikinta sai yayi sanyi sam batasan zata bata ran mommy haka ba, dole ta ɗauki Abdul tabi bayan mommy Dan bata hakuri..


.."mommy dan Allah kiyi hakuri zan dinga tafiya dashi wlhy"!
juyowa mommy tayi yadda taga jiddan ta langabe kai har hawaye sun fara taruwa a idanun ta yasa mommy yin murmushi Dan batasan ganin hawayen jiddah ko kaɗan...
"waya faɗa miki nayi fushi, banaso ne Abdul ki saba da bashi madara bayan kinsan irin tarin sinadaran na nonon uwa ke dashi ga ƴaƴanta saboda nace ki dinga tafiya dashi kinji yar albarka" ta faɗa tana shafa kan jiddah dauke da murmushi..
itama jiddan murmushi tayi tace "samun uwa kamar ki sai an tona sosai shiyasa koda yaushe nake ganin babu wanda yayi dacen uwa kamar ni, ina sanki mommy fiyeda yadda nake san kaina".ta karasa tana lumshe ido tareda kwanciya kan kafaɗar mommyn..
har zuciyar mommy saida taji wani dadi da farin ciki da wani sake jin saban soyayyar jiddah a zuciyar ta dan tun ba yau ba ta fahimci irin san da jiddan keyi mata sam bata kallan ta a matsayin marikiya saidai a koda yaushe tana mata kallan cikakkiyar MAHAIFIYAR ta, hakan yake daɗa sa shakuwa tsakaninsu..
"Allah yayi miki albarka jiddah, tashi maza kije ki kwanta ki huta zan tashe ki an jima zamu fita"..
da murna jiddah ta tashi ta fice tabar Abdul a wajan mommy Dan hanata bacci zaiyi idan ta tafi dashi...


jiddah ta koma school ɗinta kuma sunci gaba da karatu sosai, tareda danta take tafiya kuma bai hanata komaiba hankali kwance take rayuwarta yanzu duk tana sane da auran Habib dake kanta saidai har yanzu sunki fadawa mommy itada hibban Wanda ya hanata faɗan..

tuni Afnan ta dawo gidan ta shiyasa hibban ma ya koma dan dama rashin ta ne yasa shi komawa wajan su mommy,..

hankalin jiddah yanzu ya kwanta babu mai takura mata a bangaren komai hakan yasa take bawa danta kulawa sannan ta mayar da hankali kan karatun ta, wanda yanzu ya rage saura shekara guda ta gama gaba daya..

Abdul yayi wayo sosai kamar bashi ba yaro mai shiga rai, yanzu a gida jiddah take barinsa da Yaddar mommy tunda yanzu bai wani damu da nono ba gaf take ma da yaye sa gaba ɗaya tunda ya iya tafiya duk da tafiyar ba wani kwari tayi ba..


shekarar Habib daya da rabi kenan da komawar shi Russia wanda yanzu yayi dai dai da kammala karatun nashi na cikakken likitan mata wato (gynecologist)..
yau ya kira mommy zai dawo jibi dan haka ta kira hibban akan gyaran gida..
hibban kuwa yayi farin ciki sosai jin ɗan uwansa kuma farin cikin sa zai dawo hakan yasa da ɗoki yace gobe zaizo da masu gyaran..

yau ta kasance Lahadi jiddah bataje school ba sannan batasan wainar da ake soyawa ba, dan tana dakinta itada Abdul yana sata nishadi dan ko kallan shi tayi saita tsanci kanta dayin murmushi mai tarin ma'anoni..

shigowar mommy ne yasa ta ɗago kai tana kallan mommyn dake rike da car key..
"tashi ki shirya Abdul ku same ni a mota"!
da murna jiddah ta sauko tana fadin "ina zamu mommy"
"gyaran jiki zamu kinga mun dade bamu je ba kuma naga kanki na bukatar gyara"
jiddah kuwa harda tsallen murna dan sun kwana biyu basu je, sam bata kawo komai a ranta ba ta shirya Abdul suka fice..
a mota suka samu mommy, suna shiga ta ja motar suka bar Compound din......


*ʄɨʀֆt ʟǟɖʏ*


*⒞* ᴀᴍᴇᴇɴᴀ ᴍᴜsᴀ sʜᴜ'ᴀɪʙᴜ
[1/1, 2:25 PM] Aunty Usee: 🌹🌹🌹
*_DR. HABIBULLAH_*
🌹🌹🌹


ռǟ
*🌹ʄɨʀֆt ʟǟɖʏ🌹*
ǟʍɛɛռǟ ʍʊֆǟ✍🏻


*_(FIRSTLADY'N KAINUWA)_*


*wαttpαd:-Ameenafirstladyy*


*🌈K͢a͢i͢n͢u͢w͢a͢ w͢ri͢t͢e͢rs͢ A͢s͢s͢o͢c͢i͢a͢t͢i͢o͢n͢*✍🏻


{36}


......wani haɗaɗɗen wajan gyaran jiki mommy ta kaisu, jiddah aka fara yiwa dan mommy saloon kawai akayi mata amma jiddah har gyaran jiki da kafa aka sake yi mata,..
fes jiddah ta fito da ainihin kyaun ta na Fulanin asali fatar ta har wani shining takeyi da haske kamar wata sabuwar amarya, ita kanta saida tayi mamakin kyan da tayi dan dama ta sauya sosai jikin ya sake fresh dashi ga wata yar kiba ta kwanciyar hankali da ta zauna mata tayi masifar kyau sosai..

sun dade a wajan sai yamma sannan suka koma gida bayan siyayyar da mommy ta wuce dasu har Abdul yayi bacci sai jiddah ce ta sabo shi a kafada suka shiga cikin gidan..
yau ta kasance Monday da sassafe jiddah ta shirya ta fito palour,..
mommy na zaune a palour tana shan coffee jiddah ta fito rike da Abdul, "mommy ni zan wuce"
"shikenan sai kin dawo, amma ki jira hibban yazo ya kaiki mana"
"na kira shi yace baya gida ma yanzu, zan je na hau taxi kawai"
mommy Kamar zatayi Magana sai kuma ta fasa faɗa mata dawowar Habib ɗin tace "shikenan sai kin dawo".
hibban kuwa baisha wahala samun masu aikin ba, suna zuwa suka fara aiki dama part ɗinsa kawai zasu gyara da kuma palourn mommy saboda haka da wuri suka gama suka tafi,,.
hibban har zai tafi mommy tace yaje ya dauko jiddah dan itama batasan tana hawa taxi dinnan....
"mommy tasan Yaya Habib zai dawo kuwa'!? hibban ya tambayi mommy.
"a'a bata sani ba amma yau zata sani ai"!
hibban bai sake cewa komaiba yayi wa mommy sallama ya tafi ɗauko ta..

..tunda yayi Parking take bin part din Habib da kallo dan tsaf ta gano saban fentin da akayi wa wajan, hand bag ɗinta ta dauka ta wuce ciki bata jira hibban ɗin ba, shima ya kula da yanayin ta saidai kawai yayi murmushi ya kuma ficewa daga Compound din..
da gudu Abdul ya cafe ta itama tayi sama dashi tana dariya duk da zuciyarta cikeda take da fargaba, kusa da mommy ta ƙarasa ta ajiye shi sannan tayiwa mommy sannu da gida ta wuce ɗakinta..

saida ta shirya tsaf sannan ta fito suka zauna cin abinci, kallan fuskar ta mommy tayi taga hankalin ta na kan abincin ta, ci kawai takeyi hankali kwance..
"jiddah kinsan gobe Habib zai dawo"
duk da gaban jiddah ya fadi da maganar mommy Amma Sam bata nuna ba saima murmushi da tayi tace "na sani mommy, ai naga an gyara part ɗinsa yanzu, karfe nawa Flight dinsu zai sauka"!?
"5:30pm yace min ɗazu, ai lokacin kin dawo ko saiki raka Ni keda Abdul ɗin"!
shiru jiddah tayi kawai dan batasan zuwa saidai bazaki maganar mommy ba..
babu wanda ya sake magana sai Abdul dake ta gwarancin shi, shi kadai..


yau Tuesday, jirginsu Habibullah yau zai sauka tuni mommy ta gama shiryawa ta shirya Abdul bakaramin kyau yayi ba, jiddah kawai suke jira data dawo daga school yanzu, mommy ce ta kalli Watch ɗinta ta ɗanyi tsaki tana fadin "jiddah wai yaushe za'a daina jiranki a shiri ne, mu mun tafi nida Abdul lokaci yafara kurewa ke ki zauna a gidan sai mun dawo'! mommy ta faɗa tana daukan Car key ɗinta dake saman Centre table ta dauki Abdul suka fice..
tana jin tashin motar su ta sauke ajiyar zuciya dama basan zuwa takeyi ba, tabi lafiyar gado abinta tafara bacci..


5:30 daidai Flight dinsu Habib ya sauka, mommy sai zuba ido takeyi ta hango,,, tafe ta hango shi yana tafiya kamar bayasan saukowa sanye yake cikin bakaken suit sunyi matukar amsar shi hasken fatar shi ya bayyana sosai, wani farin ciki ne ya mamaye zuciyar mommy Dan kallo daya tayiwa Habib ta tabbatar da kwanciyar hankali da hutu sun ratsa shi yadda ya haske mutanen dake kusa dashi kamar wani Balarabe a cikin bakar fata,, bakaramin sauyawa yayi ba kamar bashi ba yakara kyau da kwarjini uwa uba aji da gayu kamar wani matashi..
sannu a hankali ya sauko ya fara waige, idanuwan shi sanye cikin wani siririn farin medicated glass Wanda ya Kara masa kyau sai wani basar wa yake..
hango mommy da yayi ne yasa ya dan saki murmushi sannan ya karasa kusa da ita saidai cike da mamaki yake kallan Abdul dan ko ba'a faɗa ba ya gane shi...
"Welcome back my son"!
murmushi ya sakeyi sannan ya amshi Abdul, a hannun ta suka wuce mota tana rike da jakar shi..
sosai yake wasa da Abdul murmushi yaki yankewa a fuskarshi, mommy sai hira take masa amma sam hankalin sa baya wajan, lura da tayi hankalin sa na kan dansa yasa tayi shiru a zuciyarta tana jinjina irin tsantsan soyayyar Abdul ta gani a idanun Habib ɗin, tabbas yanzu ta yarda bakaramin so yakewa dan nasa ba dama kullum shine abin tambayar shi..


babu kowa a palourn iya waige waigen sa bai ganta ba, baiji daɗin hakaba amma sam fuskar shi bata nuna ba yana maƙale da dansa sai zuba masa shirme yakeyi,,.
bai dade a palourn ba ya tashi saɓe da Abdul a kafadar shi, yayi magana kamar mai rada cikin dakakkiyar Murya "mommy zanje na ɗanyi wanka na fito" ya faɗa yana hanyar fita,
"da Abdul ɗin zaka tafi" mommy ta Tambaye shi..
batareda ya juyo ba yace "eh zamu dawo yanzu" ya faɗa ya ficewa..

tsaff ya samu palourn nashi sai ƙamshi mai daɗi dayake fita ya samu komai nitse kamar yadda yakeso, hakama dakin nasa saida ya dade a tsaye sannan ajiye Abdul a kujerar dake cikin dakin ya bashi ƙaramar wayar shi ya shiga wanka..
ya dade a bathtub Sannan ya fito jin Abdul yafara aniyar zaiyi kuka..
jallabiya jalar sky blue ya zura ya dauki Abdul ɗin suka yo part din mommy, yana ajiye shi ya fice zuwa masallaci zuciyarshi cikeda da tunanin inda jiddah ta shiga...


*ʄıγʂɬ ιąɖყ'ŋ ƙąıŋųщą*

*🌹αмєєиα мυѕα ѕнυ'αιвυ*🌹
[1/1, 2:25 PM] Aunty Usee: 🌹🌹🌹
*_DR. HABIBULLAH_*
🌹🌹🌹


ռǟ
*🌹ʄɨʀֆt ʟǟɖʏ🌹*
ǟʍɛɛռǟ ʍʊֆǟ ✍🏻


*wαttpαd:-Ameenafirstladyy*


{34}


Yauma zaune suke suna breakfast jiddah sai juya abincin kawai takeyi amma ba wani ci takeyi ba, hibban ne ya lura da haka yace "jiddah meye hakane sai faman juya spoon kike kin kasa cin abincin"..
Dan hararan shi tayi tace "kai kuma idanka na nan saika hadani da Mommy",,,
"Jiddah ko bakida lpy ne.."? Mommy ta Tambaye ta cikin kulawa.
Da sauri tace "a'a mommy kawai na koshi ne kinsan yau tare muka sha coffee ɗazu".
"Ban yarda ba sauri ki cinye abincin nan ki tashi banasan gaddama"! Mommy ta mayar da hankali kan abincinta..

Sai hararan hibban takeyi a boye shi kuma yana mata dariya ƙasa ƙasa dan yasan ranta bakaramin ɓaci yayi ba, suna gamawa ta tashi zata wuce daki taji Muryar hibban yana ce mata "kizo mu fita shopping".
"Banaso kaje kai ɗaya" ta faɗa ko jiyowa batayi ba, tanaji yana mata dariya mommy na masa faɗa ya daina..
Dariya ya kumayi yana faɗin"duk cikin yasa ta sauya kamar ba itaba ta ɗanyi muni"..
Hararan shi mommy tayi tace "dayake ai matarka kyau tayi sosai da tanada cikin ko"? Shiru yayi baice komai ba dan ya gano mommy magana ta faɗa masa,,,har zai kuma yin magana mommy ta dakatar dashi tace "tashi ka ficemin daga palour dan bazaka dinga ciwa ƴata fuska a gabana ba"..
Tashi yayi ya fice yana cigaba da dariyar sa yadda yaga mommy ta dage bataso ya fadi gaskiya...


Jiddah kuwa tana zuwa daki ta kwanta, kiran Afnan tayi suka dade suna waya sannan ta kuma kiran khairat suka gaisa..
Tana gama wayar bata dade ba bacci yayi awon gaba da ita..


Satin Afnan uku da haihuwa amma kusan kullum sai hibban yaje, mommy tayi masa magana ya rage zuwan amma yaki karshe ma ce mata yayi saidai idan sun gaji su dawo masa da matarsa, hakan yasa Mom bata sake yi masa magana ba ta kyale shi..
Yau jiddah tun dare takejin ciwan mara saidai tayi ta juye juye a hankali dan kar mommy ta fahimta, saida safe sannan ciwo ya karu jiddah ta fara juye juye tana kiran sunan mommy cikin wahalalliyar Murya, a rude mommy ta Kira Hibban ya fito da mota, shima hibban a matukar kidima ya fito da motar lokacin tuni mommy ta fito da jiddan suka dauki hanyar asibiti..

Tun safe sai bayan azhar sannan jiddah ta haifo kyakkyawan baby boy ƙato dashi..
Murna wajan mommy da hibban kuwa ba'a magana bakinsu har kunne, yaron na hannun mommy sai kallan shi takeyi takasa tantance kamar yaron dan yafi jiddan kyau nesa ba kusa ba saboda hasken fatarsa sai tafi dangantashi da mahaifinsa...
Sai yamma sannan aka sallame su saboda jiddan kalau take yanzu, cikin kankanin lokaci ƴan uwanta na ƙauye da sauran mutane suka san haihuwar jiddah, kowa murna yake musamman da sukaji lafiya take..

Zuciyar jiddah cike take fal da tunanin yadda zasu kaya da Habib, sau daya kawai sukayi waya tunda ya tafi shima ba wani magana sukayi ba, mommy ce kadai zata iya kiran shi ta faɗa masa duk da batasan yadda zai dauki maganar ba... jin an shigo dakin nata ne yasa ta ɗago kai tana kallan Hibban dauke da cup a hannun shi.
Tea ne mai kauri mommy tabashi ya kawo mata ganin tana tunani ne yasa hibban tambayarta lafiya kuwa..
"Lafiya lau yaya hibban kawai banaji na nrml ne"!
Murmushi yayi mata yace "keda jin nrml kuma aiba yanzu ba jiddah, gashi nan mommy tace ki shanye tas tana can tana hada miki abinci da kanta" ya faɗa yana hanyar ficewa daga ɗakin..


Kwana biyar kenan da haihuwar jiddah yan uwa da abokan arziki duk sunzo, su inna marka kuwa tun safe suka zo sai bayan suna zasu tafi, hankalin jiddah duk ya tashi dan batayi tunanin Habib bazai dawo ba,.
Tana dakinta ita Afnan da tazo tun safe sai faman kuka takeyi afnan harta gaji da lallashinta dan batasan kukan me takeyi ba,sai hibban ta kira tace yazo yaji kukan me takeyi..
Mintina kadan hibban ya shigo cikin kyakkyawan shiga harda hula, ficewa Afnan tayi ta basu waje dan duk lokacin da zasuyi magana bata zama a ganinta yan uwane dole akwai sirri tsakanin su.
Zama yayi gefenta bai tambayi inda jaririn yake ba tunda ya ganshi hannun mommy a palour.
Kwantar da murya yayi yace "jiddah meya faru, Meyasa kikeso ki dinga sa kanki damu a damuwa"!?
"Yaya hibban dole nayi kuka a wannan lokacin, shikenan yan uwana zasu fahimci irin auran danayi, wancan lokacin da kyar mommy tasa yazo suka ganshi amma wannan lokacin gashi bashida alamar dawowa har sai sun fahimci ba auran soyayya mukayi ba, tunda gashi ko murnar samun dan baiyi ba dama nasan hakan saita faru..."kuka ya sake kwace mata.
Shiru hibban yayi baice komaiba, saida ya jima a zaune sannan ya fice zuwa dakin mommy..
Bata palourn sai baki dake ta hira abinsu, hakan yasa kai tsaye ya haura upstairs ɗakin ta ya shiga ya same ta zaune tana danna wayarta, ganin hibban a ɗakin ta ya tabbatar mata akwai maganar da ta kawo shi,..
wayar Tata ta ajiye sannan ta fuskance shi tace "hibban akwai wani abu ne"!?
zama yayi yace "eh mommy"! ya faɗa yana zama kusa da ita.
"mommy jiddah tana can tana kuka, kuma banga laifin taba dan yaya Habib ya wulakantata wancan lokacin gashi wannan karan ma zai maimaita, kaf yan uwanta bazasu ji daɗi ace yarinyar su ta auri wanda baya santa bata sanshi ba kuma suna gaf da gano hakan, dan Allah mommy ki takura masa ya dawo ko jiddah zataji daɗi"..! harya kai aya mommy bace komai ba saida ya tsaya da maganar tashi sannan tace "nina hana shi dawowa hibban, tun ranar data haihu yake damuna da zai dawo yanzu shigowar kama dashi na gama waya na ja masa kunne akan karya dawo, kafi kowa sanin halin Habib indai har ya dawo to sai yayi abinda ran kowa saiya ɓaci musamman akan jiddah"..
"amma mommy yanzu ita jiddan me zata cewa yan uwan nata"!
"karka damu Hibban na riga na faɗa musu mijin nata baya nan, tunda dama basu san cewa yanzu ba matarsa bace"
da sauri hibban ya kalle ta zaiyi magana sai kuma ya fasa tunawa da yayi har yanzu mommy batasan auran Habib akan jiddah ba.
"akwai wata Matsalar ne"!? mommy ta sake tambayar shi.
"a'a mommy, saidai kije ki lallashe ta da kanki zatafi yin shiru"!

"shikenan yanzu zanje"..


jiddah na zaune a ɗakinta ta gama kukan nata mommy ta shigo, murmushi ta ƙaƙalo tayiwa mommy sannan hawaye ya fara zubo mata..
"jiddah ki daina damuwa haka mana, ni da kaina na hana Habib dawowa tunda dawowar tashi ba wani abu zata karemu da shiba, kuma kinga watanni ya rage masa ya gama karatun nashi, saikiyi fatan Allah ya fito miki da wani mijin na gari ki aura nasan dama ba komawa Habib zakiyi ba kuma nima na yarda da hakan, saboda haka ki daina damuwa kinji"
daga kai kawai jiddah tayi jikinta yayi sanyi dan tasan bata fadawa mommy komai tsakanin ta da Habib ba tun bayan dayayi mata saki ɗaya..
haka mommy tayi ta yimata nasiha sannan ta fice daga ɗakin nata..


✍️✍️✍️✍️✍️✍️
[1/1, 2:25 PM] Aunty Usee: 🌹🌹🌹
*_DR. HABIBULLAH_*
🌹🌹🌹


ռǟ
*🌹ʄɨʀֆt ʟǟɖʏ🌹*
ǟʍɛɛռǟ ʍʊֆǟ✍🏻


*_(Firstlady'n kainuwa)_*


*wαttpαd:-Ameenafirstladyy*


*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*


{37}


Jiddah na tashi daga bacci tayi Sallar magrib sannan ta fito palour dan neman abin da zataci.
Mommy ce kadai da Abdul a palourn sai wasan shi yake yi, kusa da mommy ta zauna tana kwantar da kanta saman cinyar mommyn..
"Mommy yunwa nake ji sosai wlhy"!.
"Gashi ba'a gama dinner ba saidai ki shiga kitchen ki dan dafa ko indomie ce" mommy ta Bata amsa tana shafa kanta.
Tashi tayi ta wuce kitchen din ta fara girkin ta hankali kwance harta gama sannan ta fito, dai dai shigowar Habib daga masallaci..
Sam shi bai kula da itaba yana shigowa ya zauna yana jawo Abdul jikin shi..
Sororo ta tsaya kallan Habib cike da tsananin mamaki ganin yadda ya sauya kamar bashi ya kara kyau da kwarjini, kamar mara Laka a jiki itama ta karasa shigowa ta zauna kamar munafuka..
"Jiddah yadai ko bakida lpy ne"!? Mommy ta Tambaye ta Ganin ta zubawa abinci ido..
A hankali ya ɗago kanshi jin an ambaci sunanta, kallo daya yayi mata ya dauke kai tare da saurin rintse idanuwanshi yana jin wani abu na fizgar zuciyarshi..
"Babu komai mommy" ta fada sannan ta fara cin abincin tana satar kallan shi ta gefen ido..
Babu wanda ya sake magana a palourn dai Abdul dake wasannin shi, shi kuwa Habib kanshi na kan waya saidai kuma tunanin shi na kan jiddah,..
Mommy ce ta katse shirun da cewa su tashi suyi dinner an kammala..
"Na koshi Ni" jiddah ta faɗa..
"Ai dama nasan ke baci zakiyi ba tunda kinci abinci Yanzu"

Habib ma tashi yayi ya nufi hanyar fita, mommy ta dakatar dashi "ina kuma zakaje"?
"Part ɗina, Amma a kawo min coffee yanzu" ya faɗa yana ficewa..
Sarai jiddah ta gane da ita yake amma tayi fuska ta wuce ɗakin ta mommy kuwa batace komaiba itama taci abincin ta ta wuce ɗakin ta..


Tun yana jiran coffeen harya gaji bacci ya sace shi cikeda takaici..


Kashe gari yaba mommy tsaraba yace tabawa kowa, jiddah har mamakin kayan tayi musamman na Abdul wanda tasan ba ƙanan kudi ya kashe ba,...

Kwanan shi biyu da dawowa kullum saiya dauki Abdul sun fita yawo ko zancan fara fita aiki bayayi, sai dare suke dawowa, yauma dawowar su kenan ya ajiye Abdul ɗin wajan mommy ya fice ya nufi part ɗinsa, yana zuwa ya kwanta bacci ya sace shi dama a gajiye yake..
Cikin dare ya farka tare da wani irin ciwan mara mai zafi wanda yake damun shi kwana biyun nan, da kyar ya iya jingina da jikin pillow dinsa yana rintse idanuwanshi tareda cije lips ɗinsa, saida ya kusa mintina goma sannan ya zufa ta fara karyo masa ya fara maida numfashi a hankali jin ya dan samun relief, drawer dake jikin mirror dinsa ya janyo, wasu magunguna tablet ya dauka tare da fita palourn shi..
Ruwa ya dauka cikin fridge sannan ya koma dakin sa, ya zauna gefen bed, tas ya shanye maganin yana wani yamitsa fuska, ya dade a zaune a wajan sannan ya kwanta cikeda takaici da ɓacin rai yana da matar sa amma duk yabi ya saka kanshi cikin wani tension din na ban, dole ma gobe ya cire kunya ya nuna yana bukatar matarsa dan yasan mommy ce ta hanata dawowa part din nasa duk da baisan Dalilinta ba, amma tabbas shi yanzu yakai makura da bukatar matarsa a kusa dashi duk da babu soyayya tsakanin su amma yanzu yana jin wani abu game da ita a koda yaushe, da wannan tunanin wani wahalallan bacci ya sake dauke shi..


Yau ya shirya fita aiki, da sassafe ya shirya ya nufi ɓangaran mommy, babu kowa palourn sai Laraba dake gogo goge, haurawa sama yayi dakin mommy ya sameta tana sawa Abdul kaya da alamar a wajan ta ya kwana...
Yana gaida Mommyn ya dauki Abdul din sannan ya mayar da kallan shi ga Mommy "mommy anan ya Kwana ne"?
"Eh dama anan yake kwana mana tunda ta yaye shi"
"Yaye" ya maimaita kalmar kamar bai santa ba..
"Eh haka nace"!
"Amma mommy Abdul ai bai isa yaye ba" ya faɗa a dakile..
"To ai saika nemo masa wata uwar tacigaba da shayar dashi tunda bai isa yaye ba kamar Abdul" mommy ta mayar masa da amsa a dan zafafe..
Shiru yayi baice komaiba ya ajiye Abdul yana mata sallama zai wuce aiki..
"A dawo lafiya"
A zuciyarshi kawai ya amsa ya fice daga ɗakin..

Ya dade a palour yana kallan dakin jiddah kamar mai san ganin wani abu sannan ya danyi tsaki ya fice..

Ya samu sauƙin aiki sosai, dan yanzu Ameenu ke kula da sauran bangarorin hakan yasa yake da saukin aikin sosai..

Ko breakfast jiddah batayi ba hibban yazo kaita school, mommy ce keta faman faɗa akan lallai ta nemi wani abu taci acan karta zauna da yunwa danta fahimci yan kwana biyu nan gaba daya jiddah batada sukuni sosai akan abinci...
Hibban da jiddah sai dariya suke yi ganin yadda mommy ta dage kamar zata ari baki..
"Au dariya ma kuke min ko"?
Kwantar da kanta tayi a kafadar mommy tana murmushi "haba mommy mu mun isa, ki kwantar da hankali zanci abinci sosai acan banaso na makara ne shiyasa"!
"Naji to ki kula da kanki"
"Tom sweet momma"
Hibban dake tsaye yana kallan su cikeda kauna da kuma sha'awar kaunar da suke nunawa junansu wani lokaci har mamaki yake..
"Mommy ni bakice na kula da kaina ba" hibban yace yana dan bata fuska..
Hararan shi mommy tayi tace "ban sanka ba ƴata kawai na sani saura kayi gudu da ita a mota"!
Fita sukayi suna cigaba da yin dariya abinsu dan bakaramin dariya mommy ta basu ba..
hibban na ajiye ta ya wuce wajan aikinsa,..
saida suka fito lecture farko sannan ta wuce neman abinda zataci..
kaɗan taci abincin duk ya fice mata a rai saboda tunanin Habib daya tsaya mata a rai, tarasa dalilin da yasa tun ranar daya dawo ta ganshi zuciyarta takasa samun sukuni da tunanin shi a koda yaushe, haka kawai zata tsinci kanta da tunanin shi wani lokacin har murmushi kan suɓuce mata, saidai tayi aniyar rabuwa dashi ta har abada ta nemi wanda yake santa kuma bazai wulakantata ba kamar Habib ɗin duk da har yanzu a matsayin matar shi take dole ta nemi hanyar dazai karasa saki biyun dake tsakanin su, Gara tunanin shi ya kashe ta data koma gare shi....


*ʄıγʂɬ ιąɖყŋ ƙąıŋųщą*

*ąɱɛɛŋą ɱųʂą*✍️
[1/1, 2:25 PM] Aunty Usee: 🌹🌹🌹
*_DR. HABIBULLAH_*
🌹🌹🌹


ŋą
*🌹ʄıγʂɬ ιąɖყ🌹*
ąɱɛɛŋą ɱųʂą✍

*{ʄırʂɬ ιąɖყ'ŋ ƙąıŋųщą}*


*wαttpαd:-Ameenafirstladyy*

_________________________
*_🌈Kainuwa Writers Association_*
```{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https//www.Facebook.com/Kainuwawritersassociation
_________________________


{38}


Sai yamma hibban yaje ya dauko ta jiddah har tausayin shi takeji ta yadda bai taɓa gajiyawa ba kullum yana kan hanyar kaita da dauko ta...
"Yaya hibban kana kokari, yakamata a samomin driver ko kuma a koyamin tukin na dinga zuwa da kaina"! Ta faɗa tana kallan gefen shi..
Dan murmushi yayi yace "haba dai, saura watanni fa ki gama wanne gajiya zanyi saidai ki koya kodan kai Abdul school idan an saka shi"..
Shiru kawai tayi tana dan murmushi bata sake magana ba har sukaje gida..


Mommy ce kawai a palourn itada Abdul dake jikinta a kwance, tana ganin shigowar jiddah ta fara murmushi, "kin dawo"?
"Eh mommy, ya gida"!
"Kalau, yanzu dan rigimar taki ya gama kukan kiran ummin shi" ta faɗa tana kallan Abdul ɗin ..
Dariya jiddah tayi tace "gajiya yayi kenan yayi bacci, da baiyi bacci ba da yaya hibban ya tafi dashi can ai".
Da sauri hibban yace "tab nayi yaya dasu su biyu duk yan rigima ne ai"!
Dariya mommy tayi sannan hibban yayi musu sallama ya tafi gida..


Har dare jiddah bataji motsin Habib a gidan ba gaba daya, tanasan tambayar mommy saidai batasan tayaya zata fuskance ta da Maganar ba hakan yasa tayi shiru da bakinta kawai saidai zuciyarta cike take da tunanin inda ya tafi har bayan isha haka.
Shi kuwa Habib yana office ayyuka sun tsayar dashi, duk haushi ya kama shi ga dare yayi dole ya ajiye komai ya nufo gida yana faman tsaki,..
Ko mai Gadi bai kula ba dayake faman yi masa sannu da zuwa fuska a haɗe ya shiga palourn mommy yaga babu Kowa, tsaki ya kumayi ya wuce part ɗinsa rai a dan ɓace kamar ya hadiyi zuciya haka yake ji..

Kamar yadda ya saba al'adar sace sai yayi wanka yake kwanciya, yau ma yana fitowa ya sanya sleeping dress ya Kwanta, saidai kuma baccin sam yaƙi zuwa saima ji yayi duk baccin da gajiyar sun gudu,, tashi yayi yana duba agogon dake jikin drawer gefen bed ɗinsa, ganin dare baiyi wani sosai ba 8:30 ya tashi ya nufi part din mommy..
Kai tsaye dakin ta ya wuce dan yayi mata maganar ya kamata jiddah ta dawo part ɗinsa kafin ya kamalla ginin sa dayake san Zama dan yasan tabbas mommy zata fahimci abinda yake nufi..
A hankali ya tura ɗakin nata, a zaune ya sameta tana yiwa Abdul addu'a wanda ke bacci kusa da ita, jin sallamar shi ne yasa ta ɗago kai cikeda mamaki tana kallan shi saidai kallo daya tayi masa ta dauke kai tana fadin "lafiya Habib a cikin wannan daran"!?
"Abdul yayi bacci ne"? Ya mayar mata da tambayar..
Wata harara ta maka masa "au Ina tambayar ka shine Nima ka maido min da tambayar Ko"?
Shiru ya ɗanyi yanaso yayi Magana amma yarasa ta ina zai fara.
Ganin yanayin sane yasa ta gane da magana yazo..
"Habib menene fadamin ina sauraran ka"?
Shiru ya sakeyi na wasu mintina sannan yace "mommy dama.. maganar...."""
Katse mommy tayi ganin yana kame kame "idan bazaka iya faɗa ba ka tashi ka ficemin a ɗaki zan kwanta"!
"Maganar waccen yarinyar ce dama nace Yakamata ta dawo part ɗina kafin na gama.."
"Dakata Habib, wai jiddah kake nufi.."?
Gaba daya jikinsa yayi sanyi tunda yaga ta dakatar dashi yasan abu ne mai wahala ta Amince... Kai kawai ya iya daga mata batareda yace kala ba..
Kallan mamaki mommy tafara yi masa da tsananin bacin rai "Habib kana kuwa da hankali, tayaya matar da kayiwa saki ɗaya tayi iddah zakace ta koma part dinka da kwana koka manta yanzu ba matarka bace har saita yarda sannan za'a mayar da auran ku.."
Shiru yayi bai bata amsa ba dan Maganar tata ta gama daure masa kai..
"Da alamar zama cikin waɗan da ba musulmai ba yafara sauya ka, tsabar rashin kunya kazo gabana kanamin zancan jiddah..."ta karasa maganar tana kallan face ɗin sa da yayi kasa da ita..
Jin tayi shiru ne yasa Habib ya ɗago kai, jijiyoyin kanshi duk sun tashi, kallo daya tayi masa taji jikinta yayi sanyi saboda tabbas tasan yanzu Habib dole ya bukaci mace kusa dashi saidai bazata biyewa san zuciya ta sake hadashi da jiddah a karo na biyu ba dole tabawa jiddah dama ta samo miji irin wanda takeso yake santa..
Kwantar da murya tayi ta sigar lallashi tace "Habib kayi kuskure na sakin jiddah da kayi samun mace kamar ta zaiyi wahala a yanzu, amma nabaka dama ka gwada Sa'a ka lallaɓata ko zata amince ta sake zama dakai.."!
Nan ma daga kai kawai yayi dan ya zama speechless gaba daya a yanzu abubuwan sun gama daure masa kai ɓacin rai da takaici ya hanashi yin magana tabbas yasan mommy batasan har yanzu da auran shi da jiddah ba, to Amma Meyasa bata fadawa mommy ba gashi yanzu yasan mommy bazata taɓa yarda da maganar shiba"...
"Yanzu ka tashi kaje ka huta.."!
Tashi yayi sannan yace saida safe ta amsa masa, harya kai bakin kofa ta kira sunanshi "kaji dai abinda na faɗa maka ka lallaɓata ta amince sannan zan iya wani abu"!
Daga kai ya sakeyi sannan ya fice..
A palour ya tsaya yana dafe kanshi cikeda bacin rai, ɗakin jiddah yake kallo kamar wanda zai gano ta, a zafafe ya yakarasa kofar dakin nata sannan ya murda handle din Cikin Sa'a yaji a bude dakin yake, kai tsaye ya shiga cikin....

Cikin baccin ta taji an buɗe dakinta a ɗan hanzarce ta buɗe idanuwanta, ganin Habib ne ya shigo yasa ta tashi a zabure tana saukowa daga saman bed ɗinta haɗe da zaro idanuwa..
"Me kakeyi a ɗakina Yanzu"!? Ta tambaye shi tana dakewa bata nuna alamar tsoro ba...
Hura hanci yayi yana fitar da iska ta bakin shi sannan yace "mene, kina nufin nayi laifi ne bayan dakin matata ne"! Ya faɗa batareda ya saki fuska ba..
"Kaine kasan wannan"! Ta mayar masa da amsa..
Wani takaici ne ya kara kamasa ganin yadda take mayar masa da amsa kai tsaye..
Gyara tsayuwar shi yayi yana kokarin boye fushin sa, "meyasa baki fadawa mommy na dawo dake ba"..
"Zata sani amma sai lokacin da ka datse ragowar igiyar auran mu dakai.."
Shiru yayi yana juya maganganun nata a ranshi tabbas yasan harda yarinta ke damun jiddah saidai yau duk fushin sa yakasa yi mata komai..

Wani murmushi mugunta yayi sannan yafara matsowa kusa da ita, ganin haka yasa jiddah cikin tsoro tafara ja da baya.....


*ąɱɛɛŋą ɱųʂą*
*ʄıγʂɬ ιąɖყ*


31/12/2019
[1/1, 8:06 PM] 🌹Aɱɛɛŋą fírѕtlαdч 🌹: 🌹🌹🌹
*_DR. HABIBULLAH_*


ŋą
ąɱɛɛŋą ɱųʂą✍
*🌹ʄıγʂɬ ιąɖყ🌹*


*wαttpαd:-Ameenafirstladyy*


*{fírѕt lαdч'n kαínuwα}*


{39}


Jinta tayi a jikin bango hakan yasa ta buɗe idanuwanta da sauri, saidai a tsaye ta ganshi ya kafe ta da matattun idanuwan shi masu rikita ta...
Saurin yin kasa da kanta tayi jin wani abu na taso mata game dashi..
"Ɗago idanuwanki ki kalle ni sannan ki sake maimaita kalmar bakya san sake zama dani"! Ya katse mata tunanin ta..
Da sauri ta ɗago kanta saidai takasa kallan kwayar idanuwan shi hakan yasa ta kalli gefe..
Kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa ya juya ya fice cikin sassarfa..

Ajiyar zuciya tayi sannan ta zauna a gefen gadon ta hawaye na zubo mata wanda batasan kona menene ba, tabbas tasan karya takeyi tace batasan Habib dan shi ne mutum na farko da zuciyarta ta tsumu da tunanin shi tun kafin idanuwanta su ganshi tana san Habib irin soyayyar da bazata iya fasalta shiba saidai bazata juri irin wulakancin dayake yi mata dole ta nemawa kanta yanci koda hakan zai sa ta sallama farin cikin ta to amma tayaya zata jure rabuwa dashi ɗin anya kuwa zuciyarta zata iya karbar wannan hukuncin".. rashin samun amsar tane yasa ta rufe idanuwanta tana hasko Habib a zuciyarta..


Habibullah kuwa daran yau gaba daya sam bacci baiyi nasarar sace shiba, gaba daya tunanin jiddah yau yayi "tayaya zai iya rabuwa da ita, meyasa yakejin zuciyarshi bazata iya rabuwa da itaba, meyasa yake jinta a jinin jikin sa"..! Da wannan tunanin sai sallar asuba yaji ana kira, baiyi mamaki ba danshi dama ƙaguwa yayi safiyar tayi..
Alwala yayi sannan yayi nafila ya dade a zaune kan mat sannan ya fice masallaci jin ana kiran sallar shiga....

Wanka yayi ya shirya cikin kyakkyawar shiga ya nufi wajan mommy, a palour ya same su itada Abdul yana shiga Abdul yayo kanshi da gudu..
"My boy harka tashi"! Ya faɗa yana kama hannun shi suka koma wajan mommyn..
"Good morning momma"!
"Morning too, har zaka fita'.
"Eh" ya bata amsa a takaice..
"Ka wuce da jiddah dan Yakamata hibban ya huta haka"!
Shiru yayi sannan ya nemi waje ya zauna kawai, fitowar jiddan ne yasa ya dan daga kai ya kalle ta sannan ya yaci gaba da danna wayarsa..
Tana ganin shi tayi saurin nutsuwa sannan gaida mommy ta juya ta gaida shi..
Lafiya" kawai yace sannan ya fice yana faɗin "ki sameni a mota"!

A mamaki ta kalli mommy "mommy shine zai kaini"?
"Eh nice nace ya kaiki"
Handbag ɗinta ta dauka sannan ta fice dan tasan bayasan jira..
A zaune ta same shi cikin motar ita kawai yake jira, tana shiga ya tayar da motar suka fice..
A wani shopping na saida drinks ya tsaya, bai wani dade ba ya fito rike da wata ƙatuwar leda, kallo daya tayi masa ta waigar da kanta gefe, shima baiyi wata magana ba yaci gaba da driving ɗinsa batareda ya kalli inda take ba..
Har sukaje makarantar babu wanda yayi magana sai picking call kawai da yayi..
Yana gama Parking ta buɗe motar tayi ta fice taku daya tayi taji yace "Wait"..!
Tsaya tayi sannan ta juyo tana kallanshi, zagayo wa yayi rike leda a hannun shi da alamar wacce ya tsaya yayi shopping ce..
Miko mata yayi batare da yayi magana sai kafe ta da ido yayi yana kallanta alamar ta karba..
Amsa tayi cikeda da mamaki a ranta dan bata taɓa tunanin ita ya tsaya siyawa ba..
"Nawa ne"? Ta tambaya tana san gasgatawa..
"Eh, yayi sanyi da yawa ki bari yadan huce sannan kisha" ya faɗa yana juyawa zai tafi..
"Amma..naga kaima bakaci komaiba".
Cak ya tsaya jin Maganar tata saidai bai jiyoba, baiyi tunanin ta damu dashi haka ba, wani murmushi yayi wanda har saida ya fitar da sauti sannan ya juyo yana kallan ta.
"Eh banci ba, kin damu da hakan ne"!?
"A'a ban wani damu ba saidai Yakamata ka nemi wani abu kaci kaima"
Dan tsuke fuska yayi dan yaji haushin amsar Tata sannan yace "I'm full" ya faɗa yana juyawa..
Harya kama handle din motar ya rike saidai jin Maganar ta yasa ya sake tsayawa cikeda tsananin mamaki...
"Mene"! Ya tambaye ta yana sake kafe ta da wani irin kallo wanda ke sake rikita ta.
"Eh nace nima bazan ciba idan bazakaci ba"! Ga mamakin ta saita ga yana murmushi tare da kallan gefe yana wani motsa baki zaiyi Magana..
Takowa yayi har kusa da ita sannan ya zura hannuwanshi cikin aljihu ya kalle fuskarta..
"Shikenan saiki zubar tunda bazaki ci ba".. yana faɗa ya juya ya shiga Mota ya barta a wajan tsaye..

Cikeda jin haushin kanta tace "to maye nawa a ciki dana nuna na damu dashi karma yaci mana, gashi nan ya wulakanta Ni a Banza".! Tayi tsaki tabar wajan saidai har zuciyarta taji dadin hakan..


Tuki yake yi fuskar nan ba yabo ba fallasa, saidai kallo daya zakayi masa ka gane yana cikin farin ciki..
"Ashe ta damu dani" ya tambayi kanshi yana lumshe idanuwan shi..
Sam ya kasa yarda da abubuwan dayake tunanin dan wannan abun daya shiga tsakaninsu daga daran jiya zuwa yau yakasa yadda dashi ji yakeyi kamar bashi ba zafin kanshi duk ya ragu..


Gaba ɗaya yau jinshi kanshi yakeyi kamar bashi ba, har mutanan wajan aikinsa sun fahimci hakan har tsokanar shi Ameenu yayi amma bai kula shiba sai haɗe fuska yayi yace "shut up and get out"
Sum sum Ameenu ya fice ganin ya dawo Dr Habibullah dinshi lokaci guda..
Lokaci zuwa lokaci yake kallan Watch ɗinsa, Sam bayaso ya makara wajan dauko ta..
Message ya tura akan ta jira shi zaizo ɗaukan ta idan sun tashi..

Lokacin tana zaune a capteria duk da ba abinci take ci ba tunani ne fal zuciyarta akan Habib..
Tana cikin tunanin ne taji karar shigowar message, ganin sakon yasa ta saki wani kayataccen murmushi tabbas yanzu ta yarda da soyayyar Habib ta gama rike mata zuciya kamar yadda ta lura shima ya fara canzawa..


*hαppч nєw чєαr*❣

1/1/2020
{wєdnєѕdαч }
[1/6, 8:21 AM] 🌹Aɱɛɛŋą fírѕtlαdч 🌹: 🌹🌹🌹🌹
*_DR. HABIBULLAH_*
🌹🌹🌹🌹


ŋą
*🌹ʄıγʂɬ ιąɖყ🌹*
ąɱɛɛŋą ɱųʂą✍

*{ʄıγʂɬ ιąɖყ'ŋ ƙąıŋųщą}*


_____________________________
*_🌈 Kainuwa writers association_*
```{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/Kainuwawritersassociation
_____________________________


{40}


5pm dai dai ta fito daga lecture a matukar gajiye, ita harta manta ma sunyi dashi zai dawo daukan ta sai ganin shi tayi tsaye jikin motarshi yana kallan Watch ɗinshi..
Da kyar ta iya ƙarasawa kusa dashi tace "sannu da zuwa"!
Can kasa ƙasa ya amsa da yauwa sannan ya buɗe mata gaban motar ta shiga shi kuma ya zagaya ya shiga ya tayar da motar..

Sun ɗanyi tafiya mai nisa babu wanda yayi Magana kamar lokacin tahowar su..

kallan gefenta yayi yaga ta kwantar da kanta jikin seat tana dan cije lips ɗinta..
"are you okay"!?

ɓude idanuwanta tayi tace "I'm okay" sannan ta mayar ta rufe..
bai sake cewa komaiba yaci gaba da abinda yake har suka je gida..


yana gama Parking jiddah ta fice zuwa part ɗinsu, shima part ɗinsa ya wuce ya duba wani file sannan ya nufo ɓangaran su.

tana shiga palourn taga babu kowa kai tsaye ɗakin ta ta shiga tayi wanka, bata wani dade ba ta fito ta shirya cikin doguwar riga yar kanti sannan ta fito palour..
tana fitowa dai dai shigowar Habib, kallan kallo suka shiga yi, itace tafara janye idanuwan ta, ta karaso ta zauna kan kujera sannan shima ya zauna yana amsa waya saidai idanuwan shi na kanta yana nazarin ta ganin yadda ta ɗan sauya..

mommy ce ta sauko palourn "har kun dawo"?
a hankali jiddah ta buɗe idanuwanta tace "eh mommy"!

"saiku wuce kuci abinci"
"to" kawai jiddah tace amma bata tashi ba. tana jiran ya gama wayar.

yana gamawa ya tashi yace "mommy saina dawo"..
da mamaki suka kalle shi, "ina kuma zakaje"? mommy ta Tambaye shi.
"zan koma office ne inada baki daga Abuja zasu ganni" yana daukan jacket dinshi ya fice..

takaici ya hana jiddah magana musamman da tuna tun safe baici komaiba, duk da batajin dadin jikinta haka ta tura abincin ta dawo palourn tana tambayar Abdul.
"Sai Yanzu kika tuna dashi, to hibban yazo ya tafi dashi tun safe. "
dariyar dole tayi tace "aikuwa yaya hibban ya kyauta dan mun huta da rashin jin shi.."!


tunda ya koma office yake aiki, kusan mutane goma ya gani waɗan da suka yanki card, yana cikin hada files ɗin dake kan table dinsa wata nurse ta shigo..
"yallabai Habib akwai sauran mata uku kuma sun yanki card tun azhar"..
da wani kallo ya bita wanda yasa tayi saurin bashi hakuri "sorry yallabai"

tsaki yayi sannan yace"kya iya sallamar su zuwa gobe" yana faɗa ta fice da sauri tana fadin to..

Sai bayan da yayi isha a masallacin dake cikin hospital din sannan ya nufo gida a gajiye sosai ga yunwa da take damun shi..
kai tsaye ɓangaran shi ya wuce yayi wanka sannan ya ɗauki ledar magungunan da allurai daya taho dasu danyi wa jiddah dan tuni ya gane abinda ke damunta..

yana shiga palourn ya samu mommy tana hada mata tea, ganin shine yasa tace "yauwa Habib jiddah ba lafiya ka shiga ka duba ta"!
kafin Mommy tagama magana ya nufi ɗakin nata..
a kwance ya sameta saidai idanuwanta a rufe suke jin ƙamshim turaren shine yasa ta buɗe idanuwanta sannan ta tashi zaune.
tana ƙasa da kanta.
a gefenta ya ajiye ledar ya fito da allurar sannan yace ta miko hannun.
cikin kidima tace "yaya Habib na warware fa"!
tsaki ya danyi sannan yajawo hannun nata.
tanaji allurar ta shiga ta toshe bakinta tana kuka, saida ya gama ya ɗago kanshi yana kallan fuskar ta.
"idan ance ki daina shan zaki bakya dainawa amma wajan allura kin iya kuka" ya faɗa yana miko mata magungunan.
amsa tayi tana share hawayen ta, duk haushin shi takeji harda mugunta ya haɗa mata tana sane.
"hararan ta mene haka"!? ya sake faɗa yana daga mata gira.
harta bude baki zatayi Magana mommy ta shigo dakin rike da cup din tea a hannun ta,.
Habib kuwa shigowar mommy ya fice daga ɗakin, ya wuce dining room yaci abincin sa sannan ya haɗa coffee yasha ya fice..

kwana biyu kenan jiddah bataje school ba duk da ta samu sauki amma bata koma ba, Habib kadai ke tafiya wajan aikin sa shima bai wani damu da rashin zuwan nata ba..
yau weekend Habib baije wajan aiki ba yana zaune a gida, gama lunch ɗinsu Kenan mommy tace ya dauki su jiddah su fita shopping.
"mommy shopping kuma"?
"eh mana, duk weekend haka nake daukan su muje tunda ka dawo bamu jeba dan haka saika kaisu yau"!
kamar zaiyi magana sai kuma yayi shiru kawai...

suna gama shirin jiddah ta riko hannun Abdul tace "yaya Habib mun shirya"
tashi yayi kawai yace su tafi.

babban shopping mall ya kaisu, suna fita yace idan tagama ta kirashi shi bazai shiga ba dan bayajin dadin jikin shi kawai dai bayasan yiwa mommy gaddama ne shiyasa ya kwaso su ya kawo su.
sosai ta jidi kaya, saida ta gama ta kira wayarshi tace sun gama ya shigo ya biya.
a hankali yake driving din murmushin dole kawai yakewa Abdul jiddah na kula da hakan.
suna zuwa gida yayi Parking ta fice itada Abdul ɗin suka barshi a Mota.
sosai yake jin ciwan cikin haɗe da wani zazzafan zazzaɓi dauriya ce kawai yake yi shiyasa ko ɓangaran su jiddan bai shigaba ya wuce part ɗinsa.

"Ina Habib din"? mommy ta Tambaya tana duba kayan da suka siyo.
kallan kofar shigowa jiddah tayi tace "may be yana mota"! tace tana wuce wa dakinta.

har dare bai shigo ba, saida suka zauna yin dinner sannan mommy tace taje ta kirawo shi.

shikam harya kwanta ya rufe jikinsa da blanket sai rawar sanyi yake yi.
da sauri ta karaso kusa dashi tana yaye bargon tare dafa kanshi.
"yaya Habib meyake damunka"!
buɗe idanuwan shi yayi da sukayi masa nauyi da zafi sannan ya kalli fuskarta baice komaiba ya mayar da idanunshi ya rufe.
a rude ta tafara danna wayarta,jin Muryar shi tayi a matukar wahale "yace me zakiyi"!?
"mommy zan kira mana na sanar Mata"
wani takaici ne ya kamashi duk dayasan ba laifinta bane amma Yakamata taji tausayin shi ta duba halin dayake ciki ta yarda ta su koma gidan daya gama kammalawa amma yarasa dalilin ta nakin amincewa.
ganin ya kura mata ido ne yasa ta tashi zata fice, kamo hannun ta taji yayi ta rintse idanuwanta jin hannun nashi zafi rau..
"yaushe zaki fara tausayina ne jiddah, kefa ba yarinya bace, kinsan hakkin mace akan mijinta amma meyasa kike wasa da haka" Habib ya faɗa cikin irin wata kasalalliyar Murya wacce baisan ma yayi taba.
kam ta tsaya a tsaye takasa motsa koda dan yatsan tane ƙwaƙwalwar ta ta daina aiki dan bata taɓa tunanin jin irin wadannan kalaman daga Habib koda a mafarki...
janye hannun ta tayi ta fice a hanzar ce kamar wacce zai biyo, tana shiga palour ta wuce ɗakin ta, ta kwanta saidai ta rasa wanne irin tunani zatayi "shin dagaske Habib ne wanda ta sani kokuma kunnuwan tane suka ji maganganun nashi ba dai dai ba" kiran mommy ne ya katse mata tunanin nata.
"jiddah muna jiranku fa, ina Habib ɗin"
"gani nan mommy Ina ɗaki yanzu zan fito" ta yanke kiran dan harta manta ma abinci zasuci ta tafi kiran shi.

da kallo Mommy tabi ta harta zauna ta fara cin abincin saidai sam ya fitar mata a rai sai juya spoon din kawai takeyi.
"jiddah meya faru ko yayi miki wani abu ne, naga daga kiran shi kika dawo a haka"!
da sauri ta girgiza kai tace "a'a mommy cewa kawai yayi bazai ci ba"!
"shi ne kika wani canza haka"!
murmushi tayi wanda iya kacinsa lips ɗinta sannan tace "nima ai a koshe nake shiyasa"! ta faɗa tana tashi, tanaji Abdul yana kukan zai bita dakinta amma ko kallan shi batayi ba dan tasan damunta zaiyi ga kanta nayi mata ciwo.


✍️✍️✍️✍️✍️[1/7, 10:06 AM] 🌹Aɱɛɛŋą fírѕtlαdч 🌹: 🌹🌹🌹🌹
*_DR. HABIBULLAH_*
🌹🌹🌹🌹


вч
ⓒᴀᴍᴇᴇɴᴀ ᴍᴜsᴀ
*🌹fírѕt lαdч🌹*✍


*wαttpαd*
@Ameenafirstladyy


*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*


{41}


Da kyar mommy ta lallashi Abdul yayi shiru suka je suka kwanta..

Sai juyi jiddah takeyi saidai takasa baccin tunanin Habib ne yasa duk baccin yakasa zuwa mata, tunanin ta yana kan yanayin data baro shi, dama ta sani ta zauna dashi dan tasan yana bukatar kulawar ta saidai bazata iya ba idan ta biyewa san zuciyarta ta nuna soyayyar gareshi a fili kamar zubar da aji ne a wajanta...
Tsaki ta dinga yi kamar wani na jinta har asuba batayi wani baccin kirki ba haka ta tashi idanuwanta duk sun kumbura alamar bata samu bacci sosai.
. mommy duk abin yafara daure mata kai, tun jiya bata gane kan Habib da jiddah kardai daga ya shawo kanta yaja wata Matsalar kuma"'!
"Ohh! Ya Allah, Habib bayajin magana idan taki basaiya hakura ba ya nemo wata ba ko ana dole ne! Tayi maganar a cikin ranta..
Fitowar jiddah kenan ta samu mommy a palour, saurin sakin murmushi tayi dan kar mommy ta gane wani abu.
"Ina kwana mommy"!?
Kusa da ita mommy ta karaso batareda ta amsa gaisuwar ba,
"Jiddah meya samu idanuwan ki, baki samu bacci bane, meya hanaki bacci" ta jerowa jiddah tambayoyin a jere saboda a ruɗe take a yadda taga jiddan.

Murmushi jiddah ta kuma ƙaƙalowa ta riko hannun mommyn tace "wlhy mommy kalau nake Ido nane yakeso yayimin ciwo shiyasa kika kika ga haka"!

"huh! Harna ji daɗi, yanzu muje kiyi breakfast kar lokaci ya kure miki"
Badan taso cin abu ba tabi mommy har kan dining table, saida suka fara ci sannan mommy tace "meya hadaki da Habib"
"Babu komai, ya fita aiki ne"? Ta kawar da zancen.
"A'a bansan meyasa har yanzu bai shigo ba, bari naje na duba karya sa ki makara"!
Jiddah kamar ta hana mommy zuwa haka taji amma ba yadda zatayi tana kallo mommy ta fice zuwa part ɗinsa.


Da kyar ya iya Sallah kwana biyu shi kanshi yasan ya sauya amma jiddah ce ta sauya shi, baiga macen data dace dashi kamar jiddah ba idan yace zai rabu da ita wa zai aura..
Jin anayin nocking ne yasa yayi saurin tashi dan yasan mommy ce.
Bata izinin shigowa yayi sannan ta shigo tana kare kallo.

Har wata rama yayi sosai daga jiya zuwa yau, mommy ta Dan tsorata Amma Bata nuna ba.
"Habib lafiya kake kuwa"

Rigar jikinsa ya zame yana murmushi ya saura daga shi sai vest da wando trouser.
"Eh mommy lau nake!"
Ya Bata amsa a wata irin Murya ta marasa lafiya.
"Amma tun jiya nake ganin ka kamar akwai wani abu dayake damunka"

"A'a babu komai, zanyi wanka na wuce wajan aiki" bai jira amsar taba yayi hanyar bathroom ɗinsa rike da bathrobe a hannun shi.

"Habib"!!!!...

Cak ya tsaya jin yadda ta kira sunan nashi cikin taushi da nuna kulawa.
Bai amsa ba saidai ya juyo yana kallanta.
Har kusa dashi ta matso sannan ta jashi kan kujerar dake cikin ɗakin ta zaunar dashi itama ta zauna..
Saida suka dauki kusan mintina biyu sannan tace "ni mahaifiyar kace, zan gane kowacce irin damuwa idan ka shige ta, kuma nasan duk akan jiddah ce ko"!? Ta tambaye shi saidai bai amsa mata ba sai kasa yayi da kanshi duk jijiyoyin kanshi sun tashi.
"Na fahimci irin san da kake mata tun ba yanzu ba hakan ne yasa na haɗa auran ka da ita amma ka watsa min ƙasa a ido, yanzu gashi ta kasa fahimtar ka, kaci gabada hakuri da lallaɓata zata dawo gareka amma karka nuna mata isa da wulakanci yanzu yashi kayi wankan tana jiranka karku makara"

Yanaso ya fadawa mommy jiddah har yanzu matarsa ce amma yakasa faɗa mata tunda har jiddah bata sanar da ita ba koya faɗa ba lallai ta yarda ba, zaici gaba da hakuri har sai ta faɗa da kanta kuma ta amince batareda yayi mata dole ba.
Kamar wani mutum mutumi haka ya tashi ya shige bathroom tana binsa da kallo sannan ta koma part ɗinta..

A kofar shiga taga jidda zata fito, da mamaki tace "ina zakije"

Marairaice murya jiddah tayi tace "pls mommy khairat sai kirana takeyi nayi sauri inada test kuma yaya Habib kafin ya shirya aiki ne zan tafi na hau taxi"!
"Shikenan kije amma ki kula fa"
Tam mommy ta fada tana rungume ta sannan ta fice da dan gudu..


Bai wani dade ba ya shirya ya fito dan yasan jiddah na jiranshi, yana shiga palourn ya fara baza idon inda zai ganta.
"Jiddah ta tafi tagaji da jira, saika zo kayi breakfast ka wuce wajan aikin"!

"Whattt ta tafi, waya kaita"?
"Taxi tace zata hau"
Hanyar fita yayi mommy tace "abincin fa"?
Dan tsayawa yayi bai jiyowa ba yace "na koshi mommy zan sameta a bakin titi ai" bai jira amsar mommy ba ya fice da sauri..


Tana tsaye bakin titi sai tsaki takeyi khairat ɗin taki fitowa ga taxi da napep sai wucewa sukeyi babu kowa ciki amma saboda jiran khairat yasa taki tafiya..
Wata red din mota ta tsaya gabanta, sannu a hankali ya sauke glass din motar.
Sosai tayi mamakin ganin shi dan Afnan tace mata yaje karo karatu England..
Muryar shi taji a kusa da ita "ina zakije ne haka jiddah"
Murmushi ta ɗanyi tace "school zanje khairat nake jira, ina kwana" ta gaida shi tana cigaba da murmushi.
"Lpy kalau, muje na sauke ki mana nima hanyar can nayi.
Kamar zatayi masa musu lura da hakan ne yasa Kabir yin murmushi yace "jiddah ki manta baya ki kalli yanzu, ni yayanki ne a yanzu kodan afnan dake auran yayanki saboda bazan cutar dake ko nayi miki wata magana wacce bata dace ba saboda nasan ke matar wani ce umm" ya faɗa yana kallan fuskar ta.
Murmushi tayi dan tasan gaskiya ya fada, hakan yasa ta wuce ta shiga motar shima ya zagaya ya shiga suka tafi..

Akan idan Habib akayi komai, tsananin bakin ciki da bacin rai ne suka taru a zuciyarshi ko office bai wuce ba ya nufin gida Allah ne kaɗai ya kaishi dan wani mahaukacin gudu yakeyi kamar zai tashi sama.
Mommy taji dawowar shi har zata je ta tambayi abinda yasa ya dawo saita fasa kawai dan tayi tunanin wani abin ya manta..

Fadawa saman bed ɗinsa yayi ta baya tareda lumshe lum sassun idanuwan shi yana fitar da wani zazzafan huci.
"Waye shi, meyasa ta shiga motar shi meyasa yake mata murmushi tana mayar masa"! Ya jerowa kanshi tambayoyin da suka kara masa zafin zuciya..


Tsananin mamakin jiddah tayi ganin sun doshi gidan su khairat kasa shiru tayi tace "ina zamu je"
"Wajan khairat mana"!
Bata sake magana ba tana kallo ya kira khairat ɗin yace ta fito gashi shida jiddah suna jiran ta.
"Ya akayi kuka haɗu" khairat data fito yanzu ta tambaya tana murmushi.

Wani murmushi taga Kabir yayi haɗe da wani kallo daya tabbatar mata da su ɗin masoya ne.

"A hanya muka haɗu tana jiran zuwan ki"
"Ohh! Ku muje to"!
Babu bata lokaci suka shiga ita dai tana baya tana jin hirar su har ya sauke su..


"Amma khairat naji daɗi wlhy, shikenan mu duka uku yanzu mun sake zama daya"!
Dariya khairat tayi tace ai tun bikin su muka haɗu dashi wajan party na Afnan.

Jiddah bakaramin daɗi taji ba, haka suka lecture suna ta Hira akan maganar..

4:30 Kabir ya koma dauko su dai dai lokacin fitowar su lecture din karshe, hankali kwance jiddah tabi su, har shopping ya wuce dasu sannan ya fara sauke khairat dake kan hanya ya taho da jiddah gida, jefi jefi suke hira wanda shi yake tambayar ta tana bashi amsa.
"Ya sunan yaron ki"
"Abdulmalik, amma ya akayi kasan shi"
"Na haɗu dashi a gidan afnan ai"

Habib na kwance dafe da kanshi kamar ya tsage haka yake ji, kira ne ya shigo wayar shi yasa hannu ya zaro ta daga kasan pillow dinshi ya daga yana karawa a kunnen shi.
"Hello yallabai akwai masu san ganinka yanzu"!
Tsaki yayi dan sai yanzu ya tuna sannan yace "ok gani nan"!

Yana tashi kiran mommy ya shigo
"Kaje ka dauko jiddah lokacin dawowar ta yanzu yayi"

"To"
Muryar shi kawai taji tasan bashi da lafiya, a Compound ya samu mommy tana jiran fitowar shi.
A hankali yake tafiya tabbacin bashida cikakkiyar lafiya da sauri ta karaso tace "Habib kabari zanje dauko ta kawai"

"Mommy kaina ne kawai yake ciwo, ki bari zanje daga nan zan wuce office ana San ganina"!
Zata kuma magana taga yayi murmushi ya kamo hannunta ya manna mata miss yace "karki damu zan iya zuwa"
Itama murmushi tayi tace "shikenan Allah ya kaika lpy" sannan ta koma bangaren ta..


Yana kokarin buɗe motar sa yaji shigowar, tsayawa yayi yana kallan motar har sukayi Parking jiddah ta fito shima Kabir ya fito yana miƙa mata ledar hannun shi.
Baiji abinda suke cewa ba saidai ya lura kamar bata yake tana kin amsa..

Dakyar jiddah ta amsa jin yace ba ita yayoba Abdul yayi wa ko zata raba ɗa da uba sannan ta amsa tayi masa godiya..

Saida ya tafi ta jiyo tana kallan Habib, murmushi tayi kasa kasa yadda bazai gane ba dan tagano tsananin kishi a cikin damuwan shi dama haka taso daga yau zata gane irin san dayake mata, makewa tayi zata wuce ta gaban shi..

"Waye shi"
Taji ya faɗa cikin wata irin Murya kasa ƙasa.

Bata kalli inda yake ba tace "bayan ka sake Ni shine wanda zan aura kuma nasan ka gane shi ai"

Daga hannu yayi cikin wani irin fushi zai mare ta, Kara tayi tana rufe ido tana jiran taji saukan mari, jin shiru yasa ta ɗago kai tana kallan shi.
Sosai ya rintse ido ya rasa wanne irin abu yake ji zuciyarshi na masa wani irin zafi ga ciwan kai ɗaya kara karuwa, cikin zafin rai ya buɗe motar shi ya fice da wuni irin gudu wanda ya tsorata jiddah ta shiga part ɗinsu, ta wuce ɗakinta da sauri tana sauke ajiyar zuciya Allah yaso mommy Bata palourn..


Gudu yakeyi sosai, duk inda ya gifta mutane magana sukeyi saboda gudun gangancin dayake yi, shi kam baima san abinda yake faruwa ba dan baima san gudu yake ba dan baya cikin Peace of mind dinshi hannun shi na dafe da saitin zuciyarshi da ɗaya hannun kawai yake driving yana dan rufe idanuwan shi..
Tuna yadda suke magana yayi tana mayar masa da amsa, wani duhu duhu ya gani ya gifta ta idan sa hakan yasa ya saki steering din motar ta kwace masa......


*_first lady_*✍✍


7/1/2020
[1/14, 11:10 PM] 🌹Aɱɛɛŋą fírѕtlαdч 🌹: *بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*


🌹🌹🌹🌹
*_DR. HABIBULLAH_*
🌹🌹🌹🌹


By
ⓒᴀᴍᴇᴇɴᴀ ᴍᴜsᴀ
*🌹ғιrѕт lady🌹*


*wαttpαd*
Ameenafirstladyy


{42}


cikin firgici jama'ar wajan suka fara kokarin taimakon shi, da kyar suka iya ciro shi daga motar aka wuce dashi asibiti cikin gaggawa..


jiddah kuwa tana shiga ɗakinta wanka tayi sannan ta shirya ta fito palour, da mamaki mommy ta kalle ta tace "yaushe kika shigo bayan yanzu na aika Habib ya ɗauko ki"!
murmushi ta ɗanyi sannan ta zauna kusa da mommy tace "ban dade da shigowa ba, gajiya nayi da jira saboda yunwar danake ji shiyasa kawai na taho"!
"kin kyauta ai, saiki je kici abinci!
"ina Abdul fa"?
"yana daki na yana bacci"
bata sake magana ba ta wuce dining room duk da bawata yunwa takeji ba ta faɗa ne kawai dan kar mommy tace Meyasa bata jira shi ba..


emergency room aka shigar da Habib, da kyar kwararrun ma'aikata suka samu damar saita numfashin sannan aka kaishi ɗakin hutu..

"an samu wayar shi a tareda shi kuwa" dan sandan dake wajan ya faɗa yana kallan wani dattijo wanda dashi aka kawo Habib ɗin asibiti..
"eh yallabai gata nan, cikin ikon Allah kuma babu abinda ya samu wayar" ya faɗa yana mikawa dan sandan wayar..

mommy na zaune tana yankewa jiddah Kumba sai faman shagwaba takeyi Abdul na gefe yana wasa wayar mommy tafara kara, ganin Habib ne yasa mommy ta ɗaga..
"Habib..."! Muryar dataji ne yasa tayin shiru tana sauraran abinda dan sandan ke faɗa.
a razane ta mike tana fadin "wanne sabitin ne"?
"shikenan gani nan"! tana faɗa ta ajiye wayar tana hanyar hawa upstairs.
"mommy meya faru, waye a asibiti"!
batareda mommy ta tsaya ba tace "Habib ne yayi accident suna special hospital" Bata jira amsar jiddan ba tabar palourn ta haye sama dan dauko Car key ɗinta..

tarasa wanne irin yanayi take ciki gabanta ke tsananin faduwa dan tasan tabbas abinda ya faru ɗazu ne yasa shi yin accident..
tana kokarin tashi ne mommy ta fito tace "ki zauna a gidan zan kira hibban ya same ni acan"!
har mommy zata fice jiddah tace "dan Allah mommy ki tafi dani bazan iya zama batareda nasan halin dayake ciki ba"!
"ki same ni a mota da sauri" mommy ta faɗa tana ficewa cikin sauri dan hankalin a matukar dagule yake..
hijjabin ta kawai ta dauka sannan ta dauki Abdul suka fice...

kafin su karasa asibitin mommy ta Kira Hibban tace ya same a special hospital, shima cikin kaduwa ya taho duk hankalin sa a tashe..

saboda gudun da mommy keyi mintina kaɗan ne suka kaisu asibitin, sosai tayiwa mutanan da suka kawo shi Godiya sannan ta bukaci ganin doctor ɗin..

"kiyi hakuri Hajiya amma gaskiya abubuwan da suke damun shi suna da matuƙar haɗari, Yakamata ace kinsan damuwar danki kuma kin guji abinda zai shafi lafiyar shi"
cikin zakuwa mommy tace "Dr, ban fahimci bayanin kaba, kayi yadda zan gane"!
cire Glass din idanuwan shi yayi sannan ya kalli mommy yace "doctor Habibullah yana tare da hawan jini, sannan akwai wata cuta da aka haife shi da ita wadda nasan kin san hakan, wato duk lokacin da yaji kara ko ihu ko makamancin wannan abubuwan to zaiyi ciwan kai mai zafi a takaice dai komai zai iya faruwa"..

kasa mommy tayi da kanta tana maimaita innalillahi, jiddah kuwa har idanuwanta sun fara kawo ruwa..
"yanzu doctor zan iya ganin shi"!?
shiru docton yayi yana dan kallan watch hannunshi sannan yace "eh zaku iya ganinshi saboda nasan zuwa yanzu allurar da mukayi masa tana gaf da sakin shi, amma kafin nan ga waɗannan magungunan a nemo su da sauri"!
"To doctor mun gode" mommy ta faɗa suna ficewa ita da jiddah..
suna fita motar Hibban ta shigo asibitin, a ruɗe ya karaso kusada mommy yana tambayar ya jikin Habib ɗin..
"da sauki, tunda kazo ga waɗan nan magungunan kaje a siyo su Yanzu, anaso daya farka yasha, sannan ka tafi da Abdul ka mayar da shi gida"!
amsa hibban yayi ya fice daga asibiti, sannan mommy da jiddah suka nufi ɗakin da aka kwantar dashi..

tun daga bakin kofa jiddah take kallan shi cikeda karaya ganin yadda yaji raunuka har biyu, gaba daya an zagaye fuskar shi da bandage, sai damtsen hannun shi, mommy ma dauriya kawai tayi bata nuna karayar taba, tasan Habib da zurfin ciki amma batayi tunanin zai iya boye damuwar shi harya ki sanar mata ba..

har lokacin bai farka ba, likitan ne ya shigo yace "har yanzu bai farka ba"?
"eh doctor akwai matsala ne"? mommy ta Tambaya..
"a'a babu wata matsala, karki damu zai iya farkawa at any time"! ya faɗa yana ficewa daga ɗakin..
duk sunyi jugum jugum gashi hibban har lokacin bai dawo ba, tashi mommy tayi tunawa da tayi hibban baisan inda suke ba tace "jiddah ki kula dashi zanje na taro hibban da bai san inda muka yo ba"!
da kyar ta iya buɗe baki tace "to" amma duk da haka idanuwan ta na kan Habib..

mommy na fita yafara buɗe idanuwan shi a hankali harya bude su tar akan jiddah dake facing ɗinshi, da sauri ta matso kusa dashi tana jera masa Sannu..
kallanta yake kamar mai tuna wani abu sai kuma ya kawar da kanshi gefe yana dan lumshe idanuwanshi..
"ina mommy"!? ya Tambaya can kasan makoshin shi..
zata bashi amsa ne su mommy suka shigo, su duka sukayo kanshi da sannu..
murmushi kawai yake ɗanyi dan kwantar musu da hankali..
"ina Abdul fa"!? ya sake faɗa yana kallan mommy.
"hibban yakai shi gida"!
bai sake magana ba har doctor ya shigo ya dan duba shi yace "yanzu ya danci wani abu saiya sha magungunan da aka siyo" yana faɗa ya maida kallanshi kan Habib.
"yace doctor Habib, ka taki Sa'a bakaji wani rauni sosai ba, amma dan Allah a kiyaye gaba kana consultant doctor yakamata kafi kowa kiyaye lafiyar ka ba"
har doctor ya gama jawabin shi Habib baice komaiba sannan ya fice daga room..

saida yaci abincin da Afnan ta aiko dashi sannan yasha magani..
lokaci zuwa lokaci yana satar kallan jiddah wadda tayi kasa da kanta,..
"Habib meyake damunka ne wanda bakaso na sani harya kai da zakayi sanadin ranka, na lura yan kwanakin nan kana cikin damuwa da cuta amma sam kaki fadamin, meyasa bakaso na sani" mommy ta faɗa tana riko tafin hannun shi..
murmushi yayi mata yace "babu komai mommy, Nima kaina narasa abinda yake damuna saidai inaji kamar akwai wani abu danake so yake niyyar suɓuce min wanda rasa shi kamar rasa rayuwa tane da farin ciki na,"!
da mamaki su duka suke kallan shi har jiddah wacce take jin maganar tashi kamar almara ko mafarki..
cikin kwantar da murya mommy tace "Habib duk duniya ku biyu kaɗai kuka rage min, kune farin ciki na kune rayuwata dukiya da arzikin danake dashi basuda wani amfani idan bana tare daku, ka faɗa ko menene idan har karfi da dukiya ta zasu iya nemo shi..."!
"mommy karki damu addu'a kawai zakiyi min, Allah yasa ya kasance a tare dani" ya faɗa yana sake yin wani murmushin wadda yakara masa kyau..

haka suka zauna har dare sannan aka sallame su, duk Wani motsi na jiddah akan idan Habib takeyin shi, yanaji wani irin soyayyar ta wadda yanzu ya gama yadda ita kadai zuciyarshi ta kamu da kaunar ta tun baisan menene soyayyar ba, sai yanzu ya gaskata maganar Sultan tacewar jiddah ce kadai soyayyar shi ta gaskiya..

jiddah kuwa duk tunanin ya tsaya a kalaman Habib, kenan da gaske hibban yake dayace Habib yana santa kodai duk mafarki takeyi kalaman Habib a kanta...
kai tsaye ɓangaran shi hibban yakai shi har zai fita yace "kasa a kawo min coffee right now"! fuskar nan a haɗe..
"To yaya" ya faɗa yana ficewa cikeda mamakin yayan nashi, mai hali dai baya fasa halinshi saidai ya rage wani abu ya faɗa yana yin murmushi..

yana shiga palour yaga mommy tana haɗa masa coffeen, dariya yayi yace "tabb yaya Habib fa ba lpy, yanzu hankalin mommy a tashe yake har sai first born ya warke"
"eh naji dama haka ce ta dawo dakai part ɗina Kenan"?
"a'a ba wannan bane patient dinki ne yace a kawo masa coffee, sai gashi ma naga har kin gama haɗa masa"! ya karasa yana kumshe dariyar sa..
"tunda ka isar da sakon saika barmin gida ai"..
saida yagama tsokanar mommy sannan ya fice yace Abdul zai kwana a can duk da yasan idan ya hadu da khaleesat yarshi har gajiya suke da rashin ji..


✍️✍️✍️✍️
[1/17, 3:53 PM] 🌹Aɱɛɛŋą fírѕtlαdч 🌹: *بسم الله الرحمن الرحيم*


*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*


🌹🌹🌹🌹
*_DR. HABIBULLAH_*
🌹🌹🌹🌹


вч
aмeena мυѕa
*🌹ғιrѕт lady🌹*


*waттpad*
Ameenafirstladyy


{44}


.....bata wani dade ba ta gama cin abincin, Sannan ta shigo palourn.
a zaune ta same shi yana ganin shigowar ta ya mike tsaye yace "muje ko"!
da mamaki tace "ina zakaje kuma kaida bakada lafiya"
"saina ce miki bazan iya driving a haka ba kuma"
shigowar mommy palourn ne yasa suka yi shiru kamar munafukai.
"yadai na ganku a tsaye, ko kin fasa zuwa school ɗin ne"!? ta faɗa tana kallan fuskarta.
"mommy Wai a haka zai kaini school"!
kallan shi mommy tayi tace "haba Habib kabari ta hau taxi, kaga fa fuskar ka da hannun ka duk bandage"!
cikin takaici ya kalli jiddah sannan ya mayar da kanshi ga mommy baice komaiba.
"gaskiya bazan bari ka fita haka ba, kabari idan ka samu sauki saika koya mata motar a hankali kokuma ka dinga kai tan"! tana gama fadan haka ta wuce ɗakin ta.
mommy na barin palourn ya zauna cikin tsananin baƙin ciki dan bazai iya yiwa mommy musu ba.
ko kallan inda take bai sake yi ba hakan ya tabbatar mata da fushi yayi.
ficewa kawai tayi dan tasan ko ta tsaya bashi hakuri bazai saurare taba.

dakyar ta samu ya hakura, dan yanzu babu laifi suna nunawa junansu kulawa duk da haryanzu mommy batasan komai a kansu ba, saidai tanajin daɗin yadda yanzu suke shiri sosai, ko fita zaiyi suna fita tare bai kara nuna mata wani abu ba ko tazo part ɗinsa kawo masa coffee amsa kawai yakeyi ta fita batareda ya tsayar da ita ba shiyasa yanzu ta saki jiki dashi, shi kuwa ya kyaleta ne kawai yaga iya gudun ruwan hakuri kawai yakeyi yana saita kanshi..


cikin sati ɗaya Habib ya warke yaci gaba da zuwa aikin shi, jiddah kuwa yanzu shirye shiryen passing out sukeyi, Habib ya kashe mata kudi har saida tace ya isa haka amma ko sauraran ta baiyi ba,
ranar taron kuwa ya nuna bajinta, sai yamma sosai dan gaf da magrib ne lokacin sannan suka dawo gida.
anan su hibban da Afnan suka wuni da yarinyar su khaleesat yarinya mai kyau da wayo.
suna zaune duk suna cin abinci Habib ne kawai baya wajan, mommy ce "hibban Yakamata a nemawa su Abdul da khaleesat school yanzu"
"to mommy za'a nema"
daga haka suka cigaba da cin abincin su.

duk sun tafi mommy ce kadai da jiddah a palourn, sai Habib dake zaune can gefe yana danna wayarsa,.
"Yakamata ki samu wanda zuciyarki ta aminta dashi ki kawo shi ayi magana, zamanki a haka bashida wani amfani jiddah"
gabanta yayi mummunan faɗuwa ta juya ɓangaran da Habib ke zaune taga hankalin shi baya wajansu da alama ko maganar tasu baya saurara idanuwan shi na kan wayar shi.
ƙasa tayi da murya tace "mommy..."
katse ta mommy tayi tace "cikar mutumcin ki yanzu shine aure, kada tsoran Habib yasa ki kasa fitar da wanda kike so, saboda haka na baki kwana biyu kizo da magana mai Ma'ana dan nagaji da wannan shashancin naki"
kasa koda daga baki jiddah tayi dan batasan taya zata zata faɗawa mommy ba Dan wata irin kunyar ta takeji gashi Yanzu itama tana buƙatar komawa ga mijin ta.

"ina zakaje a daran nan" mommy ta Tambayi Habib dake kokarin fita.
fuskar shi ba yabo ba fallasa yace "zan kwanta ne"
"ok good night"!
bai amsa ba yasa kai zai fita sai kuma ya juyo ya kalli jiddah dake zaune kamar an dasa ta.
"ki kawo min coffee ko lemon tea"! yana faɗa ya fice ranshi a matukar ɓace.

yana shiga part ɗinsa ya shiga bathroom yayi wanka sannan ya fito duk da haka kallo ɗaya zakayi masa kasan ranshi a bace yake sosai, sai faman huci yake yana ɗan hura hanci.

jin anayin nocking ne yasan itace yayi banza da ita, gajiya tayi da nocking ta tura ɗakin ta shiga.
yana zaune da wasu files a gabansa, harta matso kusa dashi ta ajiye masa cup ɗin bai ɗago ya kalle taba.

"yaya Habib ga lemon tea ɗin"
sai sannan ya ɗago kai ya kalleta, kallo daya tayi masa ta gano ɓacin ransa.
ta ɗan tsorace tace "yaya Habib waye ya bata maka rai"
tsaki yayi sannan taga ya mike zai bar ɗakin da sauri ta riko hannuwanshi tana ɗan girgiza kai.
"pls ka fadamin meya faru"!?
kara kuluwa da takaici yayi ya fizge hannun shi, yabar dakin.
palour ta bishi ta zauna kusa dashi tafara hawaye.
jin saukar hawayen tane yasa shi saurin kallanta yayi zuciyarshi ta karye ya kamo hannunta cikin nashi yafara yi mata magana kamar raɗa.
"jiddah bazaki gane irin yanayin da halin danake ciki ba, shekaru na sun kai na yadda dole zan damu, nayi hakuri nayi kawaicin amma duk baki fahimta ba toya kikeso nayi, ina bukatar ki a kusa dani tayaya raina bazai ɓaci ba kin kasa faɗawa mommy gaskiya bayan kinsan Ni bazata yadda da tawa Maganar ba" ya karasa yana dan fitar da huci ta bakinsa.
sai yanzu itama ta ɗago kanta tace "amma kasan dole naji kunyar mommy akan wannan maganar, tayaya zan iya tarar ta da wannan maganar".!
"shikenan yanzu kwana biyun meza faɗa mata"!? ya tambaye ta yana kafe ta da kyawawan idanuwan shi.
"zan sanar da ita komai zuwa kwana biyun"!
murmushi ya ɗanyi sannan yace "idan bahaka ba fa"? ya faɗa yana kashe mata ido.
kasa tayi da kanta cikin kunya batace komaiba.
"wato dai wannan kunyar taki na fahimci itace babban Matsalar ta dake, zan san abin yi a kanta very soon"!
dariya kawai tayi ta tashi zata tafi ya riƙo hannun ta yace "nayi zaton anan zaki kwana ai"
zaro idanuwanta tayi tace "wa.. ni".. tabb,. da safe nace wa mommy me"!
maƙe kafaɗa yayi yace "sai kawai kice wajan mijinki kika kwana inaga daga nan zata fahimci sauran zancan"!
sosai yaba jiddah dariya, kamar karsu rabu haka taji dan sai yanzu ta kara tuna maganar hibban dayace duk zafin zuciyarshi yanada sauƙin kai da daɗin zama gashi cikin lokaci guda sunyi sabo har tana fahimtar shi akan komai.......


Cikin kwana biyun da mommy taba jiddah, saura kwana ɗaya duk hankalin jiddah a tashe yake dan batasan amsar da zata bawa mommy ba..
da safe Habib ya shirya zuwa wajan aiki dan sai faman kiran shi akeyi, yana rike da jacket ɗinsa ya tashi daga kan dining table ɗin sannan ya ɗauki wayar shi dake ta faman kara ana kiran sa a office.
sallama yayiwa mommy sannan yace jiddah tabiyo shi da brief case ɗinsa.
kallan mommy tayi wacce ke cin abincin ta bata kalli ko inda suke ba.
a cikin mota ta sameshi yana Ganin karasowar ta ya fito rike da key ɗin shi.
"kar kunya ta hanaki faɗar Gaskiya"!
yana faɗin haka ya amshi jakar shi ya shige mota ya bar gidan...

tafiyar Habib yasa ta koma ciki duk jikin ta a sabule, mommy na lure da ita saidai ko ta kanta bata bi ba harkokin ta kawai takeyi..


yana zaune a kan kujerar shi a office idanuwan shi a lumshe yana dan cije lips, da kyar ya iya kiran Ameenu mintina biyu ya shigo.
ko zama baiyi ba Habib ya faɗa masa wani magani yace ya nemo masa shi yanzu sannan kar a bari wani ya shigo min nan.
ɗan tsayawa Ameenu yayi kamar zaiyi magana sai kuma ya fice yana girgiza kanshi cike da tausayin mai gidan nashi.
a hankali yake fitar da numfashi dan ya fara galabaita, shigowar Ameenu ne yasa shi ɗago jajayan idanuwan shi.
saida yasha sannan ya ɗan kwantar da kanshi yana maida numfashi a hankali.
"Dr I'm sorry to say, wannan maganin yanada matsala yawan shan shi, kuma yan kwanakin nan kullum saika sha inaga kamar hakan zai iya haifar maka da matsala aure shine....."!
wani kallo ya watsawa Ameenu da jajayan idanuwan shi sannan yace "get out of my office"
da sauri Ameenu ya bashi hakuri ya fice cikeda mamakin wannan hali irin na mai gidan nashi da shegiyar kafiya.


*🌹 firstlady 🌹*✍️✍️✍️
[1/19, 11:31 AM] 🌹Aɱɛɛŋą fírѕtlαdч 🌹: *بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*


🌹🌹🌹🌹
*_DR. HABIBULLAH_*
🌹🌹🌹🌹


вч
ᴀᴍᴇᴇɴᴀ ᴍᴜsᴀ
*🌹ʄɨʀֆt ʟǟɖʏ🌹*


*wαttpαd*
Ameenafirstladyy


{43}


...... mommy har zata kai masa da kanta sai kuma ta nufi ɗakin jiddah..
a kwance ta sameta idanuwanta a rufe, jin an buɗe dakin tane yasa ta buɗe idanuwanta ta ɗago kanta.
"jiddah lafiya kike kuwa"!?
"eh mommy na gaji ne kawai"
"to tashi ki kawai Habib coffee saiki bashi magungunan shi daga nan, Ni zanje na gyara dakina"!
dan sauya fuska tayi tace"wlhy mommy bazan iya da masifar wannan mutumin ba"
dariya mommy tayi tace "babu abinda zai miki wanda bashida lafiya ina yaga ta faɗa"!
kamar zata sakeyin magana sai kuma ta amsa ta fice daga ɗakin..

a hankali ta shiga palourn tana bin ko ina da kallo, ganin baya palourn ne yasa ta wuce ɗakinshi saidai kasa shiga tayi tana dan tsorace dan har yanzu da sauran tsoran shi da take ji Musamman data san itace silar accident din nashi.
kasa ƙasa tayi sallama dan ta tabbatar bazaiji sallamar Tata ba, a kwance ta hange shi ya dafe kai da lafiyayyan hannun shi, ɗan ɗaga murya tayi ta sakeyin sallamar..

ƙasa ƙasa shima ya amsa sannan ya tashi yana kallanta duk da tayi kasa da kanta, har tazo kan Centre table ɗin kusa da bed ɗinsa ta ajiye sannan ta ɗago kai suka haɗa yayi saurin kawar da kanshi gefe yana ɗan tsuke fuska.
"gashi mommy tace kasha sannan na baka magungunan ka"!
banza yayi mata kamar baisan akwai mutum a kusa dashi ba.
ganin haka yasa jiddah ta kwantar da murya tace "dan Allah yaya Habib kayi hakuri, nasan nayi laifi amma wlhy ba abinda na faɗa maka bane a zuciyata kawai a hanya muka haɗu ya rage min hanya amma babu wata soyayya tsakani na dashi"
saida ta gama sannan taji ya sauke ajiyar zuciya tareda lumshe idanuwanshi baice komaiba ya fara sipping coffee ɗinshi harya gama sannan ta dauko magungunan tana bashi yana sha harya gama tas. sannan ta tashi zata tafi, ji tayi ya riko hannunta ta baya, jiyowa tayi tana kallanshi tareda daga masa gira tana kallan hannun nasu.
kamar mai koyon magana yace ta zauna.
batayi masa musu ba tazauna tana cigaba da kallan shi.
"wannan kallan fa, na mene"!
"nasan sanin dalilin hanani tafiya mana"
taɓe baki taga yayi sannan yace "a bayanai da kikayi na fahimci kema kina sona wani dalilin ki mara amfani shine ya hanaki faɗa wa mommy matsayi na a wajan ki ko"? ya tambaye ta yana kallan kwayar idanta.
"ni banida wani dalili, kuma ai bakaji nace ina sanka da bakina ba ko"! ta karasa tana haɗe fuska tare da kawar da kanta.
murmushi yayi har saida taji sautin fitar shi, kamar bazaiyi magana ba taji yace "amma nasan kema kina bukatar wani a tare dake, shiyasa har kika kasa hakuri kike so na sake ki ki auri wani, koba haka bane "? ya sake jefa mata tambayar yana wani shu'umin murmushi..

da sauri tace "banajin wani abu ni, dan zan iya karasa rayuwa ta ba tareda na nemi wani da namiji ba..."

maƙale kafaɗa yayi yace "shikenan tunda haka kikace bari na tabbatar da gaskiya kika faɗa.."!
tashi tayi zata gudu taji ya fizgo da ƙarfi, mutsu mutsu ta shiga yi dan kwatar kanta amma ko gezau hannunsa baiyi ba, kamar jira yake yake ta buɗe baki zatayi Magana saiji tayi ya haɗe bakin su waje ɗaya..
wani zazzafan kiss yake yi mata kamar zai cinye bakin gaba daya, duk yadda taso ya sake ki yayi, tun tana kokarin kwantar kanta har saida ta gaji ta hakura.

Habib kuwa tuni ya fara nisa, dayake Gwarzo ne wajan iya abin tuni ta fara mayar masa da martani suka cigaba da aikawa da juna sakwanni..
sunyi nisa sosai harya fara zarce wa da romancing yaji karar wayar shi.
zare jikin shi yayi daga nata yana maida numfashi idanuwan shi duk sunyi ja, jiddah kuwa ƙasa tayi da kanta cikin tsananin kunyar biye mai da tayi.
cikin husky voice taji yace "yanzu na gano gaskiyar"!.. jin an sake kiranshi ne yasa ya matsa yana daga wayar ganin mommy ce.
dakyar ya iya saita kanshi ya daga wayar.
"Habib ina jiddah ne tun ɗazu bata dawo ba.."!
"gata nan tana dan dafa min ruwan zafi ne, zan gasa jikina saboda ko motsi nakasa yi"
"ok tayi hanzari ta dawo to"!
"ok Mom" yayi saurin ajiye wayar jin tana ta kokarin fizge hannun ta.
"an faɗa miki nidin rago ne da zaki iya kwace wa a hannun na"
"dan Allah yaya Habibullah ka sakemin hannu na tafi"
murmushi yayi yace "yau ai anan zaki kwana, better for you kawai ki nutsu ma yarinya"
ganin da gaske yake bazai barta tafi ba tace "shikenan naji amma kasan me zaka fadawa mommy da safe"!
kallan fuskarta yayi ya danyi murmushi yace "naji,"
"to sakemin hannu nayo wanka"
sam bai kawo guduwa zatayi ba yana sakinta tayi hanyar fita da gudu, sannan ya leko yanayi masa gwalo yana daga Kafa ta sa gudu tabar ɗakin yana jiyo rufe palourn shi datayi.
dariya ta bashi ganin yadda take cin uban gudu kamar zata tashi sama, saida ya gama murmushin shi sannan ya tashi ya shiga wanka cikeda farin ciki..

a firgice ta shiga palour, mommy na ganinta tace "keda waye kike gudu haka, "mommy kin sanni da tsoro"
"shine kike wannan gudun, ta faɗa tana dan nazarin jiddan"
"eh wlhy, ji nake kamar an biyo NI"! tana faɗa ta wuce ɗakin ta dan ta lura da irin kallan da mommy keyi mata..


sai wajan 8:00am jiddah ta tashi, dan sosai yau bacci yaki sakin ta, da sauri sauri take shirya wa tana gamawa ta dauko jakarta ta fito palour.
kai tsaye dining room ta shiga, yana zaune cikin wani ligt blue na yadi mai shegen taushi gaba daya dakin ya gauraye da ƙamshin turaren sa, cak ta tsaya takasa ƙarasawa kusa dashi, bai kula da ita ba saida ya ɗago ya ganta takasa karasowa.
harya buɗe baki zaiyi magana mommy ta shigo, "ya kika tsaya anan, lokaci fa ya kure zakiyi asarar lecture ta farko"!

"umm kyaleta mommy, may be wani abu take tunawa take tsoron kar a maimaita" yayi maganar shi hankali kwance.
"wanne abu Kenan" mommy ta tambaye shi.
"ina nufin may be tana tunani kar tayi asarar text ɗin da zatayi irin na wancan satin"!
"ok to kinji saikiyi saurin kammalawa ki wuce".
Habib yagama ba jiddah mamaki, saiya yanko magana ta wayance dayin karya, sam yanzu yagama sauyawa halayen sa sun canja sosai ba kamar da ba mommy kuwa saurin yadda takeyi dan tasan Habib bai iya tsara zance ba.
kuma abinda yafi bata mamaki ko alamun sakin fuska babu a tare dashi fuskan nashi a haɗe ta yadda dole mommy ta yadda da maganar shi.
zama tayi kawai tafara cin abincin, kasa ƙasa yayi da kanshi saitin kunnen ta yace "kin gama gudun yanzu kuma gamu tare" yana faɗa ya tashi ya fice palour.


*Kuyimin afwa readers rashin yin typing dina inada babban dalilin shiyasa amma yanzu komai yayi dai dai, na dawo da hot ɗina😀😛😛*

Maman hajiya
shamsiyya mamman
Maman hmy
fathema abdull dnj
firdausi daughter
Kuna Raina a kowanne lokaci 🌹🌹
[1/19, 11:33 AM] 🌹Aɱɛɛŋą fírѕtlαdч 🌹: *بسم الله الرحمن الرحيم*


*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*


🌹🌹🌹🌹
*_DR. HABIBULLAH_*
🌹🌹🌹🌹


вч
αmєєnα muѕα
*{🌹fírѕt lαdч🌹}*


*wαttpαd*
Ameenafirstladyy


{45}


...Fitar Ameenu daga office ɗin ya ɗan kwantar da kanshi kan table ɗin dake gabansa, sam bai damu ba saboda yasan yau zai kasance da matar sa danya tabbatar zuwa yanzu mommy tasan komai..


mommy kuwa ko tayar da maganar batayi ba ta kyale jiddan, ita kuwa ganin mommy batayi mata magana ba yasa tayi shiru batace komaiba ba sai murna da takeyi a ranta, duk da batasan yadda zata kaya tsakanin ta da Habib ba.


sai yamma sosai ya nufo gida, da kyar ya iya kai kansa gida saida Ameenu ya dage ya bari ya kaishi amma yaƙi yace yayi driving ɗinsa da kanshi.

ko jakar shi bai ɗauka ba ya nufin part ɗinsu mommy,..
tana zaune a palour taga shigowar shi, da sauri ta tashi tana masa sannu da zuwa.
murmushi yayi kadan kawai ya zauna yana lumshe idanuwanshi.
"Habib yanzu ka dawo ne"! mommy dake saukowa ta tambaye shi.
"eh yanzu na shigo"
"kalau kake kuwa na ganka kamar baka da lafiya"!
"kalau mommy na, kawai gajiya ce"
"alhamdulillah to saika tashi kayi Sallah kazo muyi dinner"
a hankali ya tashi dan bayaso ta fahimci wani abu, wani kallo yayi wa jiddah dauke da murmushi sannan ya fice ya bar palourn.

wanka ya faɗa ya gasa jikinshi sosai da ruwan zafi sannan ya fito ya shirya yayi Sallah, ji yayi bazai iya komawa wajan su mommy ba gashi har yanzu baya jin shi dai dai juriya kawai yakeyi.
wani farin ciki yake ji a ranshi saidai baiji mommy tayi masa wata magana data danganci maganar su shida jiddah ba.
"to kodai so takeyi saimun gama dinner Sannan tayi min maganar"!? ya tambayi kanshi, baiso komawa part ɗin nasu ba amma haka ya tashi ya nufi ɓangaran nasu cikeda kwarin guiwa..

duk sun zauna shi kawai suke jira ya shigo sai zuba ƙamshi yake yi.
"kabari sai jiran ka mukeyi"
"I'm sorry mommy wanka na ɗanyi"
"shikenan" kawai tace tafara cin abincin ta
har suka gama cin abincin ya zauna yana kallan dole danshi ba ma'abocin kallo bane, ganin babu alamar yi masa maganar ne yasa ya tashi yace saida safe mommy, sannan ya kalli jiddah da Abdul ke kwance kan cinyar ta yace "ki kawo min wani abu mai dan zafi nasha"!
"kace ta kawo maka coffee ko ruwan lipton kawai meye ne wani abu mai zafi"
murmushi kawai yayi jin Maganar mommy baiyi magana ba ya fice daga palourn..
mommy ta mikawa Abdul sannan ta shiga kitchen ta haɗa masa hot coffee, har zata fita mommy tace "Ni zanje na kwanta ki dawo da wuri ki kwanta"
"tam mommy, yanzu zan dawo"

palourn nashi a rufe saida tayi nocking sannan ya fito ya buɗe, saurin kawar da kanta tayi ganin shi babu riga sai wando trouser.
shikuwa yana buɗe mata yaga tayi saurin kawar da kanta ya taɓe baki, a zuciyarshi yace "kiyi ki gama yau kam bazan kyale ki ba" yana gama zancan zucin sa ya wuce daki ya barta da cup a hannu.

ajiyar zuciya ta saki dan ganin Habib haka saida ta dauke numfashi, zama tayi akan kujera tana raba idanuwa dan bazata iya shiga yana irin yanayin ba, kusan mintina goma ta dauka a zaune bata shiga ba, cikin kwarin guiwa ta nufi ɗakin nashi dan tasan zuwa yanzu ya gama shiryawa kuma tasan ko kwana zatayi a zaune anan bazai fito ba.
ganin baya dakin ya tabbatar mata da yana bathroom, ajiye cup din tayi zata fice dai dai fitowar shi daga bathroom din yana rike da towel yana goge kai.
kallan kallo suka shiga yi ita kuwa sam hankalin ta bata tareda shi duk da idanuwanta na kanshi amma sam ƙwaƙwalwar ta bata wajan.
murmushi yayi ganin ta zaro dara daran idanuwan ta kuma da alama bashi take kallo ba.
a hankali ya tako zuwa kusa da ita, batayi tsammani ba saijin numfashin ta tayi yana haduwa da nashi, a razane ta ɗago kai tana kallan shi, kallan dayake mata ne yasa tayi kasa da kanta kan faffadan kirjin shi wanda ya yalwatu ta gashi kwance, jikin shi murde na cikakken namiji..
"yadai, wannan kallo haka"! ya faɗa yana kara matso da kanshi saitin fuskarta.
baki ta turo gaba "mezan kalla wanda ban sani ba"..!
"gashi kuwa duk kin kasa komai ganina a haka"!
a tsorace ta ɗago kanta dan batayi tunanin a fili tayi maganar tata ba sai amsar shi kawai taji.

kasa motsi tayi tana ji yayi murmushi mai sauti sannan yabar kusa da ita,,.
jin alamun yana rufe kofar dakin ne yasa jiddah dagowa a zabure tana cigaba da zaro idanuwanta.
gira ya daga mata yana wani ni'imtaccen murmushi wanda tafara gano ma'anar shi.
"yaya Habib dan Allah ka buɗe min na fita"!
make kafaɗa yayi yana wuce wa ta gabanta zuwa wajan mirror ɗinshi yafara ƙalƙale jikin shi bai jiyo ya kalleta ba..
kamar zatayi kuka ta sake cewa "dan Allah ka buɗe min"
kallo ta yayi ta mirror yace "ki ɓude mana ki fita ga hanya nan" ya faɗa yana cigaba da abinda yakeyi.
yana kallanta ta isa bakin kofar tana kokarin budewa dariya ta bashi ganin yadda ta dage tana bugun kofar..
har saida hannun ta yafara zafi sannan ta dawo bakin gadon ta zauna ranta a ɓace

tsaf ya gama shirin shi sannan ya dauko maganin shi yasha ya dawo kusa da ita..
yana zama ta tashi tsaye ya riko hannunta sannan ya juyo da ita yana kallan fuskarta..
"meyasa baki sanar da mommy ba"!? ya jeho mata Tambayar..
"batayi min zancan ba, ni...kuma..ina.kunyar faɗa mata". ta bashi amsa cikin in Ina.

cikeda jin haushi yace "kunya kike ji shiyasa kika kasa faɗa mata kenan"
"eh" ta bashi amsa.

"shikenan tunda bazamu iya faɗa mata ba, zata gane da kanta"
ɗago kanta tayi ta kalle shi, sai taga ya kashe mata ido yana murmushi.
"gaskiya bazan iya ba"
"Ni kuma zan iya"
zata fara marairaice murya taji ya haɗe bakinsu waje ɗaya..
cikin kankanin lokaci suka fice hayyacin su nayi saurin barin ɗakin 🏃🏃🏃..


(Anki a dauko rahoton😂😂)


tuni bacci ya dauke ta sai sauke ajiyar zuciya take tana fitar da numfashin wahala kana gani kasan ba baccin daɗi take ba, shi kuwa yana kwance gefenta ya zuba mata ido murmushi ya kasa kwacewa fuskar shi, ya rasa ta yadda zai misalta yanayin dayake ciki a yanzu, wani lallausan murmushi ya sakeyi daya tuna magiyar ta a daran jiya, sannan ya gyara mata bargon daya rufe ta ya tashi ya shiga bathroom dan bazai iya komawa baccin a wannan lokacin ba.


sallah yayi raka'a biyu sannan ya zauna yana addu'oi har aka kira sallar asuba,.
motsi ta farayi jin sanyin asuba, a hankali ta buɗe idanuwan ta da sukayi ja tana buɗe wa suka hada ido tayi saurin rufe wa.

jin maganar shi tayi a kusa da ita "my half ki tashi asuba tayi"!
ko motsi batayi ba balle yasa ran zata amsa masa.
murmushi ya sakeyi mai sauti yace "kunyar ce har lau, ashe akwai sauran aiki kenan, bari nayi kokarin ƙarasawa" ya faɗa yana yaye blanket din data rufa, wata yar siririyar karar shagwaba ta saki tana rike bargon.
shi kuwa saurin rufe kunnen shi yayi yana dariya, sannan yace "to tashi na kaiki bathroom din"!
girgiza kai tayi tace "zanje"
da kyar ya lallaɓata kamar wata yarinya ta nufi bathroom din a hankali take tafiya..

saida ta shiga sannan yayi murmushi ya gyara gadon da dakin..


haka ta dinga zuba masa shagwaba iri iri, dan itama yau wasai take jinta..
da kanshi ya haɗa mata ruwan tea Tasha danya warware mata ciki sannan ya bata magunguna tasha dan yaga tafiyar bata sauya ba, tana sha wani baccin ya ɗauke ta..


tsananin mamaki ne ya kama mommy ganin jiddah shiru bata fito ba, ɗakinta ta shiga taga wayam har bathroom da toilet da duba bata ga jiddah ba, ga wayarta a kan bed ɗinta bataje ko ina da wayar tata ba.
Kiran Habib tayi shima wayarshi a kashe tuni gabanta ya fara faduwa tana Tambayar kanta inda jiddah ta tafi, dan sam bata taɓa kawowa kanta tana wajan Habib ba..


a firgice ta tashi tana kallan agogon dake gefen gadon shi kan drawer, ganin 9:25 yasa tayi saurin saukowa daga saman bed din tana waige waige, ganin baya dakin yasa ta nufi palour.

yana zaune da laptop a gabansa da alamu aiki yakeyi sosai, yana ganin fitowar ta ya tashi yana mata murmushi.
"my cute, kin tashi"?
hawaye ne ya zubo mata da sauri ya matso kusa da ita yana rike kafadun ta yana kallan face ɗinta yace "lafiya meya faru, ko haryanzu kina jin ciwo ne"? ya jero mata Tambayar a jere.

kai ta girgiza, yace "to menene"?
da kyar bakinta ya furta "mommy"!
ajiyar zuciya ya saki sannan yace "karki damu muje nizan faɗa mata komai, kuma idan zatayi faɗa Ni zatayi wa ba ke ba kinji"! ya faɗa yana rungume ta tsam a jikin shi, sannan ya ɗago ta ya share mata hawayen ya rike hannun yace "muje to"!
dakile wa tayi taki tafiya ya juyo yana kallanta "muje mana"!
"kabari zanje nayi mata bayani nasan zatafi fahimtata"!
"idan tayi miki faɗa fa"?
"bazata yi ba mommy tana sona bazatayi min faɗa ba saidai nasiha" ta faɗa tana yin murmushi danta kwantar masa da hankali.

"shikenan muje na raka ki"
"a'a ka barshi, banaso tasan tare muke"!
murmushi yayi mata ya manna mata kiss a goshinta da lips ɗinta sannan ya rike hannunta suka fita.
suna fita tace ya koma da kyar ta samu yabarta ta tafi yana hango ta harta kusa shiga sannan ya koma ciki ya fara shirin tafiya wajan aiki.

ta daɗe a tsaye kofar shiga palourn ta kasa shiga, saboda tsabar fargaba, batasan me zata cewa mommy ba Dan tasan idan shine yazo da kanshi saiya fi shan faɗa amma idan itace bazatayi mata sosai ba shiyasa kawai ta taho ita kadai dan bataso ranshi ya ɓaci tunda itace silar komai..

mommy na zaune ta zuba uban tagumi taga shigowar jiddah, kamar munafuka, da hanzari mommy ta tashi tana fadin "jiddah ina kikej...." cak ta tsaya ganin irin tafiyar da jiddan keyi kuma tana hawaye....


*🌹 First lady🌹*✍️
[1/26, 9:07 AM] 🌹Aɱɛɛŋą fírѕtlαdч 🌹: *بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*


🌹🌹🌹🌹
*_DR. HABIBULLAH_*
🌹🌹🌹🌹


вч
αmєєnα muѕα
*🌹fírѕt lαdч🌹*


*wαttpαd*
Ameenafirstladyy


{46}


cikin wata razananniya da firgitacciyar murya ta kamo hannun jiddah "na shiga Uku jiddah daga ina kike meya same ki" ta jera mata tambayoyi har biyu.
kasa amsawa tayi taci gaba da hawayen ta dan batasan ta yadda zata fara ba kuma dayake tasan babban laifi ne sukayi ita da Habib ɗin saidai dole yau mommy ta sani ko wanne irin hukunci zatayi musu...

kamata mommy tayi har ɗakinta ganin bazata faɗa mata komai ba, saida ta tabbatar tayi shiru sannan tafara lallashin ta cikin taushin murya.
"jiddah ni mahaifiyar kice, zan iya gane duk wani yanayi da kike ciki kuma zanji daci da bakin ciki musamman idan na tuna ke kamar amana ce a wajena, nasan kinyi kokari wajan kare mutumci da kimar ki na wasu shekaru amma yau daya kin zubar da wannan kimar da mutumci...." hawaye ne suka zubowa mommy na kunar zuciya.
a firgice jiddah ta kalli mommy tsoro biyu ya haɗe a zuciyarta, kenan mommy zarginta takeyi da tabi wani namiji, sannan harta kai da ta zubar da hawayen ta..

tashi mommy tayi zata fice bayan ta share hawayenta, ji tayi jiddah ta kamo hannun ta, dan juyowa mommy tayi tana kallan jiddan fuskarta babu alamar walwala.

cikin kuka jiddah tace "mommy Dan Allah kiyi hakuri ba yadda kikayi tsammani bane, Habib.. Habib..ne...! shiru tayi takasa ƙarasawa.

jagwab mommy ta zauna kusa da jiddan, dan ta fahimci zancen jiddan tunda ta ambaci sunan Habib.
kamo hannunta mommy tayi cikin nata sannan tace. "Habib ne"?
daga kai jiddah tayi batace komaiba.
a zafafe mommy ta tashi zata fice da sauri jiddah ta tare gaban tana rungume mommy.
"mommy karki ga laifin shi nice mai laifi dana kasa faɗa miki gaskiya tun lokacin daya mayar da auran mu, nayi hakane saboda wani banzan dalili na amma nagane kuskure na dan Allah mommy kiyi haƙuri"!

mamaki da farin ciki ne ya gama kama mommy, takasa boye farin cikinta ta ɗago da Jiddah...
"shikenan bari na haɗa miki ruwan zafi kiyi wanka muke kiyi breakfast" tana gama faɗin haka tabar ɗakin ta shige bathroom ɗinta ta haɗata mata ruwa mai zafi sannan tace ta tashi ta shiga, saida taga shigewar jiddan sannan ta fice dauke da murmushi..


gajiya yayi da zaman jiran ya kira wayarta yaji yadda tayi da mommy Amma yaji a kashe, tsaki ya danyi cikeda fargaba ya shiga wanka dan tafiya office..

yana fitowa kiran mommy ya shigo, a darare ya daga wayar haɗe dayin sallama.
"bazaka je office bane yau"?
"zanje yanzu zan shigo ai"
"shikenan ina jiran ka" tana gama faɗa ta ajiye wayar ta, sannan ta ɗauki abincin jiddah takai mata dakinta.
cikin kunya jiddah takasa ɗago kai ta haɗa ido da mommy, murmushi mommy tayi ta ɗago kan mata tace "yau kuma mommyn taki kike jin kunya"
ƙasa ta kumayi da idanuwanta, sannan taji Muryar mommyn ta sake katse ta.
"jiddah kinasan ci gaba da zama da Habib"?
jin Tambayar mommyn ne yasa ta ɗago kai tana kallan mommyn har hawaye sun fara taruwa a idanuwan ta.
"wlhy ina sanshi mommy dan Allah karki ce zaki raba mu"!...
katse mommy tayi dauke da murmushi tace "nima ba niyya ta kenan ba, zanfi kowa jin dadin kasancewar ku tare amma banaso nayi miki dole a wannan karan, tunda kin amince shikenan zanyi magana dashi Habib ɗin naja masa kunne akan ki sannan banaso ki ƙara yadda dashi har sai kin tare kamar yadda aka tsara tun farko"
nodding Kai kawai jiddah tayi sannan mommy ta fice daga ɗakin..

yana gama shiryawa ya nufo ɓangaran mommy cikeda kwarin guiwa, babu kowa palourn ya nufi dining room, mommy na zaune tana gyara table ɗin taji ƙamshin turaren shi.
juyawa tayi ta kalle shi ta ɗauke kai.
"bazaka shigo bane ka tsayamin anan"
basarwa yayi ya shigo ya ajiye jakar zuwa aikin shi sannan ya gaida ta ta amsa amma bata saki fuska ba.
"idan ka gama ka same ni a sama" bata jira amsar shi ba ta fice..

yana shiga ya same ta a Zaune tana jiran zuwan shi, kasan kafarta ya zauna yayi kasa da kanshi kamar mara gaskiya.
"Habib.!"
"na'am"!
"meyasa ka ɓoyemin maganar auranka da jiddah tsawon lokaci kana zalin tar kanka"?
shiru yayi yakasa bata amsa.
"ta fadamin komai kuma na gamsu dan nasan bazata yi min karya ba, Sa'a daya kaci jiddah nada hakuri da harta amince da cigaba da zama dakai, tunda kun sasanta kanku saika fara shirin tarewar ku a saban gidan daka gama dan baza'a fasa ba, sannan ka samu lokaci kuje can ƙauye ku sanar dasu.."
murmushi ne kwance kan face ɗinsa, har mommy tagama jawabin ta yace "Nagode mommy nizan wuce asibiti"
"saika dawo"
harya tashi zai fita tace "sannan banaso wani abu ya sake shiga tsakanin ku har saikun tare ina fatan kaji abinda nace"
dariya yayi kasa ƙasa yace "angama mommy baza a sake ba"
dariya tayi tana yi masa daƙuwa, shima yana dariyar ya fice.
a palour ya tsaya kamar ya shiga ɗakin nata sai kuma ya fice kawai cikin farin ciki..

tana daki taji fitar shi, wayar ta ta dauko ta kira Afnan da khairat ta sanar musu.
"sai wani ɗoki kikeyi kamar ba kece me cewa batasan Habib ba wancan lokacin" cewar khairat wacce itama ake shirye shiryen bikinta da Kabir..
"da kenan yarinya ai yanzu inasan abin na".. haka dai suka dinga hirar su tsakanin su..


yau Habib kowa yayi mamakin sa a wajan aiki dan babu faɗa ba wani dacin rai sosai amma babu wanda ya tambayi dalili musamman da suka san halin shi yanzu saiya juye musu.


sai yamma ya dawo, a palourn ya samu su hibban da Afnan sai khaleesat da Abdul da suke ta faman rashin ji, gwanin sha'awa sai hira sukeyi.
yana shiga jiddah tayi kasa da kanta dan yanzu kam nauyin shi takeji sosai, yana ankare da ita murmushi kawai yayi ya ida shigowa palourn, mommy na ganin shi ta dan taɓe baki tace "hmm yau kuma"!
babu wanda ya gane abinda take nufi sai hibban ne ya lura da fuskarshi wasai ba damuwa yace "yaya yau lafiya kuwa kake ta fara'a haka.."!
hararan shi Habib yayi kamar zaiyi magana sai kuma yayi shiru yana tsuke fuska.
"kayi murmushi mana tunda matarka ta dawo, nidai abinda nasani ko bacin rai ka sata saina raba auran dan ina san ƴata fiye dakai Gara ma kaji karka dinga bata mata rai atoh"..
su duka sukayi dariya har Habib ɗin saida yayi murmushi sannan ya tashi ya fice ya barsu suna cigaba da dariyar su..


"gaskiya naji daɗin haka jiddah, dama na faɗa miki yaya Habib yana sanki lokaci ne bai bada damar kisan haka ba amma gashi yau yabaki dama" hibban ya faɗa yana mata dariya.
Afnan na zaune itama tace "ammafa duk da haka saikin dinga haɗawa da hakuri, dan wannan halin nashi na miskilanci da sakin fuska duk bazai daina suba saidai ya rage.."
hararan wasa jiddah tayi mata tace "bakisan yanzu su nafi so a game da halayensa ba ni sai yanzu ma na yarda yaya Habib na musamman ne a cikin maza.."
"eee lallai yau kanwata ta rufe idanuwanta" hibban ya faɗa yana riƙe haɓa..
dariya suka dinga yi masa daga karshe ya bar musu dakin shima yana dariya..


cikin yan kwanaki mommy ta tsara komai har sabbin akwatuna da furnitures tayo odar su wanda ta kashe kudi harda na ban mamaki, Habib yaso hanata yace zai siya tace ita bata yarda ba so takeyi tayiwa yarinyar ta kamar yadda kowacce uwa kewa yarta haka ya kyale ta tayi da kanta.
sati biyu kawai aka tsayar da ranar, tuni mommy ta ɗauko mai gyaran amarya tafara gyara jiddah gyara na musamman.
yau suka shirya zuwa ƙauye su fado tarewar, daga mommy sai jiddah sai Habib ɗin dake yin drivern.
an tarbe su hannun bibbiyu..
sun so tahowa da jiddah amma inna marka tace abar mata ita tayi kwana biyu zata haɗa mata nasu magungunan irin na ƙauye badan mommy taso ba tabar jiddan tace zata dawo da tafi da ita jibin, har bakin mota ta rako mommy suka tafi, Habib kuwa ko kallan inda take baiyi ba tsabar takaici dan gani yake kamar itace tace zata zauna.
"amma mommy bai kamata ta zauna har kwana biyu a irin wannan ƙauyen ba, dan ko abincin su ba lallai ta iya ci ba"!
haɗe fuska mommy tayi tace "banasan zancan banza, kai zasuyi wa gata ai saina hana su kake so kome"..!
"gata sukemin ko cuta ta dai"! ya faɗa a ranshi..

sai dare suka isa gida, ta kira wayar mommy suka sha waya sannan mommy tayi mata faɗa akan duk abinda suka bata ta tabbatar tasha gata suke mata, cikeda kunya tace "to momma" sannan sukayi sallama, ta kira Habib.
kamar bazai daga ba saida ta kusa yankewa sannan ya daga a daƙile ya amsa sallamar Tata.
murmushi ta ɗanyi dan tasan bakaramin zuciya yayi ba tunda taji shi haka.
"idan bakida magana zan yanke wayata"
"dama cewa zanyi kunje gida lpy"
"eh munje"! ya bata amsa a takaice.
"kayi hakuri bazan iya yin jayayya da maganar su.."!
"ok shiyasa kika manta da neman izinin a wajena kenan"
"I'm sorry izinin mommy nabi but I'm so sorry"!
tanaji ya saki ajiyar zuciya sannan yace shikenan ya hakura suka ci gaba da wayarsu cikin nishadi da kaunar juna..

kwana biyu mommy tazo ta ɗauke ta suka koma gida akaci gaba da gyaran jiki.....


*Alhamdulillahi Ala Kulli Halin*✍️
[1/26, 9:07 AM] 🌹Aɱɛɛŋą fírѕtlαdч 🌹: *بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*


🌹🌹🌹🌹
*_DR. HABIBULLAH_*
🌹🌹🌹🌹


вч
αmєєnα muѕα
*🌹fírѕt lαdч🌹*


*wαttpαd*
Ameenafirstladyy


{47}


.... Tunda ta dawo mommy ta hanata fita daga daki sai ɗaki dan ko palour bata fita koda yaushe suna daki ana mata gyaran jiki ko shan magunguna kala kala harta fara gajiya.
Habib tun yana nacin da faɗa harya gaji ya kyaleta kawai yaci gaba da shirye-shiryen taron da zasuyi..
saidai koda yaushe suna maƙale ta waya ba dare ba rana..

kwana huɗu ya rage yau mommy ta shirya kamu na Musamman, anyi kamu angama lafiya gida duk ya tara jama'a..
washe gari da yamma aka dunguma zuwa walima cikin wani babban hall da aka kayata shi abin sha'awa.
yaso mommy tace yazo ya kaisu danya ga jiddah amma tace bata yarda ba saidai yayi nashi zuwan daban shida abokansa tunda walimar harda shi aka tsara.
tare yaje dasu Sultan da Dr Ahmad daman sune manyan abokan nashi da yake dasu, saida kowa ya hallara sannan su mommy suka zo wajan tana rike da hannun jiddah wanda yasha bakin lalle da ja.
kanta na kasa rufe har mommy ta kaita kusa dashi ta zaunar da ita sannan ta dan matsa kusa dashi daya kafe su da idanuwa Kamar ya lashe..
"saura kayiwa mutane rashin kunya a wajan walima"
murmushi shima yayi ya matso da kanshi kusa da mommy yace "amma ai ta buɗe fuskar tata ko mommy"!
dukan wasa takai masa ya farayin dariya, basu wani daɗe da zuwa ba malaman da aka gayyato suka fara nasiha da wa'azi duk hall ɗin yayi tsit da alamu maganganun suna shigar su..
har aka gama ba wani hayaniya shiyasa Habib bai damu ba shida bayasan hayaniya ko kadan, lokaci zuwa lokaci yake kai kallanshi kanta amma sam har aka tashi bata ɗago ba kanta na ƙasa cikin wani mayafi mai shegen kyau..

a matuƙar gajiye suka koma gida, shi dai Habib duk takaici ya gama kama shi na hanashi ganin amarya shi da akayi, yanzu ma dayake driving zaikai Dr Ahmad gida da Sultan tare da matan su sai surutu sukeyi shidai yayi shiru kawai..
"wai Habib yadai duk ka wani shiru kamar ba shagalin ka akeyi ba"
tsaki ya ɗanyi sannan yace "Sultan kyale ni kawai ina bukatar matata amma ko ganinta ya faskara"!
su duka sukayi masa dariya har Angelina da take ɗan jin Hausa yanzu.
"kaida zaka tafi da ita gaba daya kubar gidan ma meye na wani jin haushi"
shiru yayi kawai bai ba Dr amsa ba dan yasan bazasu fahimci irin abinda yake ji gameda matar tashi ba..


dare nayi ya shigo palourn su, mutane sai tsokanar shi sukeyi amma bai saurare suba, yanaji suna masa tsiya wai dama wannan ɗan kurman ba kula ku zaiyi ba wannan jiddah ta shiga Uku kafin ma ta koya masa magana aiki ne balle akai ga su saba..
sosai maganar tasu tabashi dariya har ya shiga dakin mommy yana murmushi.
"kalau kuwa ka shigo kana faman murmushi kai kaɗai"?
"babu"
"to me ya kawo ka dakina na"!?
"ohh! momma coffee nakeso kisa jiddah ta haɗa min"...
kallan shi tayi kamar tanasan cewa wani abu sai kuma yaji tace "shikenan zata kawo maka"!
bai ja maganar tasu ba ya fice yana godiya kawai tun kafin ta sauya shawara..

dakin jiddan ta shiga tana zaune da wasu ƴaƴan makwabtan su na ƙauye da aka zo dasu suna ta hira mommy ta shigo tace ta shirya taje ta haɗa masa coffee yace takai masa part ɗinsa.
amsawa tayi sannan ta shiga kitchen ta haɗa masa hot coffee ta ɗauko mayafinta ta wuce kai masa..

tunda ta shigo dakin ya kafe ta da idanuwanshi ko ƙiftawa bayayi harta karaso ta ajiye masa kan table tace "ga coffeen Nan na kawo"!
murmushi yayi sannan ya taso ya riƙo hannun ta yace "aiba yanzu zan sha ba"
ɗago dara daran idanuwan ta tayi zatayi Magana taji yace "mata ta naso gani dama, ko nayi laifi"!?
"a'a bakayi laifi ba amma haɗa zance babu kyau ai"
wani lallausan murmushi yayi har kyawawan fararan haƙoransa suka bayyana reras dasu.
"haɗa zance ma kamawa takeyi ai, anayin tane dan asamu hanyar bullewa.."
dariya itama tayi tana ƙasa da kanta..
"zan koma kar mommy ta dawo taji ban dawo ba"
"to menene aita san kina nan wajan mijinki"
"amma.."!
"shhht! ki saki jikin ki babu abinda zata ce nima kuma babu abinda zanyi miki kawai zaki ɗan tayani hira ne before you leave"!

saida ya gama shan coffeen sannan yace ta taimaka ta dafa masa noddle Dan yunwa yake ji..
bata tafi ba saida ta dafa masa sannan ya zaunar da ita yace tare zasu ci danya fahimci bataci komai ba itama..
dakyar ta samu ya rako ta ta dawo sannan ya koma cikeda kewar matarsa..


ranar dinner party kuwa sai yamma sannan aka fara shirya jiddah, tana dakin su inna marka can aka kai makeover tafara tsantsara Mata kwalliyar ban mamaki..
"wannan kwalliya kamar baza a goge taba kai jama'a ƴan birni kuna abinda kuka ga dama a bi a narka kuɗi akan wannan aikin banzan" inna marka take ta faman tsiya kamar wacce da kuɗin ta zata biya.
"inna idan kinaso kema ki zauna ayi miki idan bahaka ba ko hall ɗin baza a barki ki shiga ba".
"yo Kar a bari mana dama nace muku zanje ne irin wannan wajan saika ga wata kamar aljana haka kawai nakai kaina na dawo a razane"
dariya sukayi tayi mata har aka gama mommy ta kawo mata kayan ta.
wata haɗaɗɗiyar dinner gown ce sky blue har Ƙasa take ja cikin kankanin lokaci aka cakara mata head tie ɗinta ta fito kamar ba ita ba..

tuni motocin kawayen ta suka tafi, dama Habib ya dame su da kira tayi sauri ta fito lokaci yana kurewa..
Sultan ne yaja su har hall din suna zuwa suka wuce wajan da aka tanadar musu sannan aka fara gudanar da taro sun zama taurari a wajan kashewa kowa ido sukeyi da kyaun su..
duk wani motsin su tare da yaron su sukeyi wanda shima aka ƙure masa wanka kamar ba yaro ba yana tsakiyar su abin gwanin sha'awa...


(wannan shine ake kira da ƙara'i😂😂😂😂)


a matuƙar gajiye suka dawo daga wajan dinner saidai duk takasa cin abinci duk da tana jin yunwar, mommy harta gaji da lallashinta ta fice tace ai cikin tane..

Habib na shigowa palourn mommy ta fito daga ɗakin jiddan tana mita.
"yauwa tunda kai tanajin tsoron ka har Yanzu saikaje kasa ta taci abinci tunda ni bazataji tawa ba, ayi yarinya da shegiyar kafiya" ta faɗa tana barin palourn..
kai tsaye dakin ya shiga, kawayen nata na ganin shi fuskar nan a haɗe suka fice, da sauri ta tashi tsaye tana rarrabe idanuwa kamar munafuka.
jin saukar hannuwanshi tayi a ƙugunta tago kai tana kallan shi..
"meyasa ƙika ƙi cin abinci"!?
"na koshi ne..."!
ji tayi ya haɗe bakinsu waje ɗaya ya fara yi mata wani salo na musamman saida ya tabbatar ta nutsu sannan ya sake kallanta da idanunshi da suka yi wani iri yace.
"kinaso ki jamin matsala ne, kinsan fa ba'a so mace ta zauna da yunwa kota dinga ci fiye da ƙima duk suna haifar illa.."!
zata sakeyin magana ya kuma haɗe bakin nasu, wannan karan kam saida tafara kokarin kwantar kanta sannan ya sake ta yana murmushi.
"muje kici abinci, ko kuma.." yayi shiru yana ɗan cizan lips ɗinshi haɗe da cigaba da kallan ta da rikitattun eyes ɗinsa...


✍✍[1/27, 9:49 PM] 🌹Aɱɛɛŋą fírѕtlαdч 🌹: *بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*


🌹🌹🌹🌹
*_DR. HABIBULLAH_*
🌹🌹🌹🌹


вч
αmєєnα muѕα
*🌹fírѕt lαdч🌹*


*wαttpαd*
Ameenafirstladyy


{48}


...... kamar yarinya haka ya kama hannunta har dining room, saida ta zauna sannan yasa mai girkin ta kawo masa abinci.
fafur taki yadda ya bata tace da kanta zata ci basaiya bata ba, kyaleta yayi kawai ya fice yana dariya....

tana gama cin abincin ta, ta koma ɗakinta tanaji kawayen nata na tsokanar ta amma bata kula su ba tunanin mijinta ne fal zuciyarta har bacci ya ɗauke ta.

tsabar gajiyar jiya saida ta makara tashi da safe tunda tayi sallar asuba ta koma bacci, saida mommy ta turo abdul tace yazo ya tashe ta sannan ta tashi.
"good morning ummy" Abdul ya faɗa yana dariya.
hararan shi tayi tace haka ake tashin mutum daga bacci ayi masa ƙara a kunne"!
marairaice murya dan yaga ta bata rai yace "I'm sorry ummy bazan sake ba"..
"hmm, da kyau yarona kaje kacewa mommy gani nan fitowa"!
"to" ya faɗa yana ficewa sannan ta shiga bathroom danyin wanka..

saida ta gama wanka ta fito sannan taji ƙarar wayarta tana dubawa taga Habib ne, fuskarta ɗauke da murmushi ta daga da sallama.
amsawa yayi sannan yace ta zo tayi masa abinci yunwa yake ji..
"mommy bazata barni ba saidai nayi na aiko maka dashi"
"No kibari kawai" yana faɗa ya kashe wayarshi tasan haushi yaji amma babu yadda zatayi dan mommy ba barinta zatayi ba.


da kanshi ya tashi ya daga noddle, kaɗan yaci ya tashi ranshi a bace ya bar gidan gaba daya..

ganin bai sake kira bane har azhar ya tabbatar mata da fushi yayi sosai, sau biyu tana kiran shi yaki dagawa hakan yasa itama ta share shi kawai taci gaba da sabgar ta.

mommy da kanta taje gidan daya gama aka shirya wa jiddah kayanta duk da sun samu nashi wanda aka riga aka jera su amma mommy Bata fasa zuba nata a palourn sama ba, gidan yayi masifar kyau dan sam ba tsarin kasar bane sama da kasa ne duk wanda yaga gidan saiya yaba da kyan shi..

tunda akayi sallar magrib aka fara shirya jiddah dan kaita gidanta, saidai kukan da takeyi ne yabawa kowa tausayi musamman Wanda yasan dalilin kukan nata.
dan dole aka fasa yi mata kwalliyar sai light makeup kawai Afnan tayi mata, mommy ma tana ɗaki zuciyarta a karye sam batasan rabuwa da jiddah saidai babu yadda zatayi dole su rabu ta tafi gidan mijinta..
duk yadda suka so jiddah tayi shiru ki tayi dan ko sauraran su batayi, saida akayi isha sannan mommy ta shigo dakin nata mutanen duk suka fita..
rungume mommy tayi tana kuka kamar wata karamar yarinya "dan Allah mommy kicewa Yaya Habib mu zauna anan wlhy banasan tafiya na barki"!
murmushi dole mommy ta ƙaƙalo Dan kwantar mata da hankali sannan ta farayi mata nasiha mai ratsa jiki, da kyar ta samu ta hakura sai dai bata daina kukan ba...

da kyar aka raba ta da mommy suka tafi tana kuka sosai..


kowa ya yaba da kyan gidan musamman mutanan ƙauye,..
Afnan da khairat ne keta faman lallashin jiddah amma takiyin shiru haka suka kyaleta suka ci gaba da hirar su kafin su tafi.
inna marka kuwa sai raba ido takeyi tace "oh Ni Marka!! jiddo ya zaki iya zaman gidan nan ke ɗaya kuwa"!
dariya su Afnan sukayi sannan khairat tace "inna ko zaki taya ta zama ne"
daƙuwa inna marka tayi mata "gidanku khairat kinga nayi kama da zama a irin wannan gidan, kaɗaici ma kawai ya isheka".
dariya suka kumayi su duka, jiddah dai tana jinsu batace komaiba ba dan har yanzu hawaye takeyi..

tanaji suka tashi tafiya, babu yadda zatayi haka suka barta ita kadai tana hawayen ta dan kukan ya daina fita mommy kawai take tunanin, saida ta gaji dan kanta sannan tayi shiru ta share hawayenta..

basu wani daɗe da tafiya ba taji shigowar motar Habib, gabanta ne ya fadi dan sai yanzu ta tuna tun safe da yayi fushi basu sakeyin waya ba...

tana nan zaune taji shigowar shi, tago kai tayi tana kallanshi suna haɗa ido tayi saurin yin ƙasa da kanta ganin irin kallon dayake mata.
murmushi ya ɗanyi sannan ya ajiye ledar dake hannun shi ya karaso kusa da ita ya zauna.
ɗago kanta yayi yana kallan fuskarta saidai ita kasa ɗago kanta tayi sai hawaye daya zubo Mata.
hannu yasa ya share mata hawayen sannan taji maganar shi ƙasa ƙasa.
"kukan farin ciki ne na gani a tare dake har abada ko kuma na rabuwa da mommy da Abdul ne"!? ya tambaye yana kafe ta da idanuwanshi.
tasan tsokanar yakeyi shiyasa tayi shiru bata tanka masa ba.
tanaji yayi murmushi mai sauti sannan ya tashi yana cire Watch ɗinshi,.
"shikenan ki tashi muyi salla naji matsalar daga baya"! ya faɗa yana sake kai kallanshi kanta.
shiru tayi masa tana kallo ya shige bathroom din bai wani jima ba ya fito sannan ya kalle ta yace "oya tashi kiyo alwala"!
kallan tayi kamar bazata tashi ba.
"ko saina raka ki ne"..
saurin girgiza kanta tayi sannan ta shige bathroom din tana jin dariyar shi kasa ƙasa..


sun daɗe suna addu'a bayan idar da sallar sannan suka tashi.
ɗakin sa ya koma yayi wanka ya shirya cikin jallabiyar shi sky blue sannan ya dawo dakin nata..
tana cikin saka kaya taji shigowar shi, da sauri ta juya tana kokarin karasa sawa, ji tayi ya rike hannunta ta baya kasa juyowa tayi kuma takasa ƙarasa saka rigan sai jikin ta daya fara rawa.
ganin haka ya sake ta ya koma Palour saida ya tabbatar ta gama shiryawa sannan ya shigo ya sameta a zaune gefen gado..
taɓe baki yayi sannan ya wuce ya kwanta abinsa saiji tayi ya janyo ta jikin shi ya rufe su da blanket..
cikin kunnen ta taji maganar kamar raɗa "ki saki jikin my wife"..
tanaji ya fara sarrafa ta, ta gurzu iya gurzuwa har saida taji Kamar First night ɗinta..

Tasha kuka da kiran mommy, lallashi da lallaɓata kam yayi tana sane take dada shagwabewa duk tabi ta ruɗa shi takasa komawa bacci, saida yayi mata allura sannan ya samu bacci ya dauke ta..


da asuba ya tashi ya wuce masallaci dan yasan ba yanzu zata tashi ba saboda allurar dayayi mata sai zuwa 7 na safe hakan yasa yana idar da Sallah ya dawo gida..


sai bayan 7 sannan ta tashi, a hankali ta buɗe idanuwanta da sauri ta tashi ta sauko gadon dai dai shigowar shi dan lokaci zuwa lokaci yake lekowa kota tashi..
kokarin shigewa bathroom tayi saiji tayi ya dauke ta gaba ɗaya har bathroom ɗin.
kuka tafara yi masa akan ya ajiye ta sannan ya fice yana murmushi danya gano harda shagwaban ta...


sauti sauri take shiryawa karya shigo, tana gamawa ta fito palour, cikeda mamaki take kallan yadda ya gyara palourn sai ƙamshi ke tashi.
"lallai yaya Habib akwai tsafta"..

da kanshi ya haɗa musu breakfast, Tasha mamakin yadda yayi wannan aikin duk shi kadai.
"kina mamaki ne"?
"eh tayaya..."
"kinga let's eat first sannan seki Tambaye ni"
tare suka ci abinci tun tana dari ɗari dashi harta sake danta fahimci basan kunyar yakeyi ba..


✍️✍️✍️
[1/28, 6:30 PM] 🌹Aɱɛɛŋą fírѕtlαdч 🌹: *بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*


🌹🌹🌹🌹
*_DR. HABIBULLAH_*
🌹🌹🌹🌹


вч
αmєєnα muѕα
*🌹fírѕt lαdч🌹*


*wαttpαd*
Ameenafirstladyy


{49}


....Duk wani motsin da jiddah zatayi yana manne da ita, har mamaki takeyi yadda gaba daya ya sauya kamar ba Habib ɗin data sani ba..

"yaushe zamuje dauko Abdul ne" ya katse mata tunanin ta.
kallan shi ta ɗanyi sannan tace "mommy fa bazata bamu Abdul ba, Gara ma mubar mata shi kawai dan yafi sabawa da ita.."!
bata tsammani ba saiji tayi ya dauke ta cak ya nufi ɗakin shi da ita, sai faman wutsil wutsil takeyi yaki sauke ta sai dariya yake mata.
yana ajiye ta saman bed ɗinsa ta tashi zata sauko ya riƙo ta.
"babu inda zaki saimun samawa Abdul kanwa ko Kani"!
"what..."! ta faɗa tana zaro idanuwanta.

ido ɗaya ya kashe mata sannan ya janyo ta jikin shi..

wunin ranar abu guda Habib ya dinga yi, tun tana janye wa harta saki jikinta bata koyi masa musu..
tsantsan soyayya zalla Habib ya nunawa jiddah a wannan ranar duk saita gane ashe duk yadda ta dauke shi bahaka yake ba..


cikin sati ɗaya har fatar jiddah saida ta sauya kallo ɗaya zakayi mata ka gano tsantsan jin dadi da farin ciki a tareda Ita, ɓangaran Habib kuwa har wani shining fatar jikin shi keyi tabbacin samun kwanciyar hankali a tare da shi..

yauma kamar kullum yadda yake taya ta haɗa breakfast Dan baya barinta da aiki ko kadan ne saiya ce zai taya ta, saida suka gama breakfast ɗin sannan ya shirya zai fita, ji yayi ta riko shi ta baya tsam.
"ohhh! my wife kinaso na makara ne!
"a'a banaso ka makara"! tayi Maganar cikin shagwaba.
riƙo hannun ta yayi ya zagayo da ita gabansa sannan ya kafe ta da eyes ɗinshi yana faɗin.
"to shikenan ki barni na tafi"!
"pls ka kaini wajan mommy"!
shiru ya ɗanyi kamar bazaiyi magana, saida yaga ta langabe kai tana maimaita plss cikin wata irin Murya mai jan hankali sannan yayi murmushi yace "ok ki sameni a mota, idan kika wuce 5mnt saidai kiga babu Ni nayi tafiya ta na barki"!
wani tsallen murna ta saki ta nufi ɗakin ta, shi kuwa ficewa yayi kawai yana murmushi ƙasa ƙasa.


mommy taji dadin ganinsu musamman yadda taga ƴar tata ta zama wata babbar mace.
yana ajiye ta ya wuce office yace zai dawo ya tafi da ita..

sai azhar ta kira shi tace zata wuce gidan Afnan saboda shirye shiryen bikin khairat da suka fara.
"Mrs Habibullah banasan yawo fa, ki hakura kawai"!
"khairat bazata ji daɗi ba baka yadda tasha wahala a namu bikin ba"!

ɗan taɓe baki yayi sannan yace "shikenan sai akace saikin rama mata wahalar datayi miki"!
kamar yana ganinta haka ta girgiza kai.
jin tayi shiru ne yasa Habib ɗorawa da "bazaki ba ina ganin ki hakura da zuwan zaifi"
"shikenan na haƙura.."! tana faɗa ta kashe wayar kawai ta kwanta duk ranta a ɓace.
mommy ce da Abdul suka shigo palourn Abdul na sanye da kayan gym.
kiss ya manna wa jiddah a cheek ɗinta, ɗago Kai tayi tana dariya.
"my son Ina zuwa haka"!
"gym room zani!
"ohh, that's good my dear"

mommy ce tace "wuce ka tafi zaka dame ta da shegen surutun ka ko"!
saida Abdul ya fita ya fita sannan mommy ta maida kallanta kan jiddah tace "lafiya naga duk kin sauya"!
cikin shagwaba tace "mommy ya hanani zuwa gidan Afnan, kuma bikin khairat ya matso shine muke ta shirye shirye"!
murmushin manya mommy tayi sannan tace "tsakanin kune wannan saiki bari ya dawo ki sake Tambayar shi".
jiddah bata sake magana ba ta kwanta abinta cikeda takaici..


tana nan kwance taji ihun Abdul yana kiran sunan Daddy, hakan ya tabbatar mata da Habib ne ya dawo.
haushin datake ji ne yasa bata tashi daga inda take ba harya shigo palourn Abdul na hannun shi.
mommy ce tayi masa sannu da zuwa sannan tace "jiddah jeki haɗa masa abinci ki kawo masa nan"

kallan inda jiddan take yayi harta tashi zata shiga kitchen din taji yace "a'a mommy fita zamuyi kuma a koshe nake."!
"ina zaku je kuma"!? mommy ta Tambaye shi..
"anguwa zamu ɗan fita badai zamu dade ba zamu dawo" yana gama faɗin haka ya tashi yana kallanta yace ta same shi a Mota..

da murnarta tabi bayan shi, tana shiga ya tayar da motar saida sukayi nisa sannan ta kalle shi fuskarta a marairaice.
"kayi hakuri yaya Habib"
"da kikayi laifin me"
"dana kashe maka waya ɗazu"

baice komaiba yaci gaba da driving ɗinsa har sukaje gidan hibban yayi Parking Yana jiran ta fita dan wajan aiki zai koma.
ganin taki fita yasa shi ɗan kallan gefenta.
"sauri nakeyi ki fita zan koma jirana akeyi"

girgiza kai tayi tace "a'a mu koma kawai na hakura da zuwan"!
tsaki ya danyi yana dan fitar da iska ta bakin shi. sannan ya kuma kallanta yace "karki batamin lokaci, saboda naki kawo ki har fushi kikayi dani saida mukazo sannan kice kuma kin fasa"...

hakuri tafara bashi kamar zatayi kuka dan tasan ranshi ya ɓaci yayi hakane kawai dan karta ji haushi itama nata ran ya ɓaci shiyasa ya kawo ta.

"look dear bafa Wai fushi nayi ba, kawai banji dadi bane amma yanzu I'm ok na haƙura ki shiga idan kun gama saiki kirani nazo na maida ki"

nodding kanta tayi sannan ta juya zata fita ya kamo hannunta ta juyo.
"bazakimin murmushi ba, ko so kike nakasa yin wani abin kirki a office din"
dariya tayi tana kai masa bugun wasa sannan ta fice tana dariya shima ya juya motar shi yabar gidan cikeda farin ciki...


kullum yanzu tare suke fita da jiddah Saboda bikin khairat, taci Sa'a ya barta anyi komai da ita taron mutane ne kawai ya hanata ta haƙura,..
soyayya yake nuna mata bata wasa ba, duk wanda yaga Rayuwar su saita birge shi bashida wata matsala yanzu saidai kuma ta wacce baza'a rasa ba..


8month later

kwance take saman faffadan kirjinshi tayi luf yana shafa bayanta a hankali kamar wata baby girl, a hankali ya kira sunan ta cikin rada ta amsa.
"yadai ciwan kan ya sauka" ya tambaye ta yana leka face ɗinta.
cikin muryar shagwaba ta amsa masa da eh.
cikin dabara ya kwantar da ita shi kuma ya tashi yana mata messages a jikin ta, cikin kankanin lokaci bacci mai daɗi ya kwashe ta sai numfashi take saukewa a hankali.
saida ya tabbatar baccin ta yayi nisa sannan shima ya kwanta..


cikin baccin ta taji yana wasa da gashin kanta, a hankali ta buɗe idanuwanta tana kallan shi dauke da wani tsadaddan murmushi.
"my life, ki tashi ki shirya muje kiyi breakfast"
da sauri ta tashi zaune tana kallan shi saidai wannan lokacin kallan mamaki take masa.

ganin irin kallon da take masa ne yasa shi yin murmushi tareda daukan ta cak har bathroom.

tare sukayi wankan sannan suka fito, saida ta fara shiryawa sannan ta matso tana taya shi sa neck tie ɗinsa..
sai faman bata masa lokaci takeyi duk tare yake so su fita ya sauke ta wajan mommy..
ganin tana bata masa lokacin ne yasa yace "oh my God, kullum saina makara wajan wannan shirin daga yau nizan dinga yin abina dan na fahimci kina sane kike batamin time"

dariya tayi masa harda gwalo sannan ta fice da dan gudun ta daga ɗakin..
yana tsaye yaga ta dawo.
"badai kaine ka hada mana breakfast ba"
murmushi yayi yana janyo ta jikin shi tareda haɗe fuskarsu waje ɗaya,.
"nine nayi, saboda jiya kin kwana da ciwan kai kuma banaso ki wahala that's why nayi da kaina".

fushi tayi zata fice ya sake kamo hannunta, "haba my dear badai fushi kikayi ba"

"ohh Tambaya ta ma kakeyi, meyasa baka tashe ni munyi tare ba tunda haka muka saba shine zakayi duk wancan aikin kai kaɗai"?
"naga bakyajin dadi ne ai, yanzu dai kinga lokaci na wucewa muje muyi breakfast I'm hungry"!

har dining table ɗin suka karaso hannun su na sarke cikin juna.
zama yayi yana nuna mata kan cinyar shi alamun ta zauna.
gefe ta juyar da kanta tana basarwa tace "bana ci kaci kai kaɗai kowa ya dafa nashi"!

"ok shikenan Ashe bazaki wajan mommy ba Kenan" ya faɗa yana kokarin tashi..
da sauri ta zauna tana dariya shima murmushi yayi sannan suka fara cin abincin cikeda farin ciki sosai...

mommy tayi farin cikin ganinsu sosai duk yanzu duk bayan sati yana kawo ta su wuni anan wajan mommyn..

sai yamma sannan ya dawo suka tafi bayan sunyi dinner a can..

yauma kamar kullum da sassafe ya shirya ya fice office, sai yamma ya dawo gida yana shigowa palour yaga bata nan kamar yadda ya saba yana shigowa take dafe masa tana masa Oyo yoo..
kai tsaye ɗakin ta ya shiga ya hange ta kwance cikin blanket.
da sauri ya ajiye breif case ɗinsa ya karasa kusa da ita yana jera mata tambayoyin lafiya take kuwa.
jin jikinta yayi zafi sosai, duk yabi ya ruɗe.
murmushi tayi masa tana tashi Zaune "fever ne tunda ka tafi nake kwance amma yanzu I'm feeling better tunda ka dawo lpy"
"meyasa baki kirani kin fadamin ba, kinji yadda jikin ki yake kuwa"
zata sakeyin magana ya cire bargon yan dauke ta har ɗakinsa sannan ya dauko first aid box din dake ɗakinsa. dakyar ya lallaɓata tasha magani sannan ta kwanta wani wahalallan baccin ya sace ta...


*first lady*


27/1/2020


NOT EDITED 〰️〰️
[1/29, 7:59 PM] 🌹Aɱɛɛŋą fírѕtlαdч 🌹: *بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*


🌹🌹🌹🌹
*_DR. HABIBULLAH_*
🌹🌹🌹🌹


вч
αmєєnα muѕα
*🌹fírѕt lαdч 🌹*


*wαttpαd*
Ameenafirstladyy

🔚

{50}


... kafin yamma jiddah ta wahala sosai har ƙarin ruwa yayi mata da allurai, sai faman lallaɓata yake taki cin abincin sai shagwaba take masa.
"pls dear kici koyaya yake saiki sha magani"!
tana kwance jikin shi tayi luf tace "nifa banci danko ƙamshin abinci ma banaso"!
"little baby meyasa kake wahalar da ummin ka" ya faɗa yana sumbatar cikin nata.

"yanzu me kikeso kici"
"dan wake" ta bashi amsa idanuwanta a rufe.
"dan wake.."! ya maimaita kalmar danshi bai taɓa ciba ko a gida idan mommy tayi ko ganin shi bayasan yi dan yafi kaunar abincin turawa tunda dashi ya saba amma yanzu gashi kaddara ta hau shi na dole ya nemo shi..
"haba my baby wannan abincin zakici kuma, yanzu a ina zan samo shi". ya faɗa yana daɗa rungume ta tsam a jikin shi.
"nidai gaskiya idan bashi ba saidai ka kyale ni haka dan bazan iya cin komai ba"
"a'a baza'a yi haka ba bari na kira mommy naji ko za'a samu" bai jira amsar taba ya janyo wayarshi dake kan stool ya Kira layin mommy bugu biyu ta daga.
saida ya gaida ta sannan yace "mommy za'a samu Wannan a gidan nan kuwa"!
jiddah najin yace wannan tafara dariya kasa ƙasa.
"meye kuma wannan bashida suna ne Habib"!
"dear yana sunan shi"
"dan wake" ta bashi amsa sannan ya sake Tambayar mommyn.

dayake mommy tasan zancan da hanzari tace za'a samu yazo ya karba mata, sannan tace yaba jiddah wayan.
bata yayi sannan ya shige bathroom danyin wanka..


tun kafin yaje mommy ta gama haɗa mata, yana zuwa ya amsa ya koma gida, a zaune ya sameta tana game a wayarta.
ajiye abinci yayi ya tashi zai bar wajan yaji ta riko hannun shi.
"mene kuma"?
kallan abinci tayi sannan ta kuma kallanshi batace komaiba sai murmushi da takeyi.
"badai kina nufin nima naci ba"!
"eh haka nake nufi naga kaima ai bakaci komaiba"
"haba never kedai daya zame miki cuta saiki ci ai, Ni zanyi nawa abinci da kaina" ya faɗa yana tashi.
ture cooler Abinci tayi tace nima banaci to.
badan yaso ba ya koma ya zauna suka fara ci tare, tana ci tana masa dariya dan ci daya yayi ya tashi yana bata fuska..


tunda ta samu cikin ba sosai yake zuwa aiki ba kullum suna manne da juna, duk wani motsin ta yana lure da shi ko aikin ya fita suna maƙale a waya..
watan cikin bakwai mommy tace su dawo gidanta saisu koma part ɗinsa da zama, haka kuwa akayi yasa aka gyara masa part ɗinsa suka dawo mommy taci gaba da bata kulawa..

yauma tunda ya fita tana wajen mommy, azhar nayi sukaji sallamar shi yana riƙe da brief case ɗinsa ya shigo palourn.
ita kadai ya samu a palourn dan Abdul yana school.
kiss ya manna mata sannan ya ajiye breif case ɗin ya zauna ya jawo ta jikinshi.
zaro idanuwanta tayi tace "kai hubbi mommy fa tana daki tana bacci"
"ai kinji bacci takeyi, Ni kuma kewar ki nakeyi shiyasa ma na dawo"...


watan haihuwar jiddah ya kama, Habib gaba daya ya bar zuwa aikin cewar shi kar haihuwar tazo bayanan a rasa mai kaita hospital.
"ai dayake ni ka raina driving dina ko" mommy ta faɗa tana hararan shi.
sosa kai yayi yana murmushi yace "a'a ba haka nake nufi ba Mom"...


7yrs later


"pls dear kabari mana na dinga zuwa kai Nihal school dakai na"
yana tsaye yana daura neck tie ya Dan kalleta yace "kibari hibban zai dinga kaita kinga bai kamata kifara fita da Aiman yana jariri haka"

kallan Aiman tayi yaron da yake rarrafe ake cewa jariri.
dariya abin ma ya bata tace "Aiman ɗinne jariri, kawai dai baban Aiman ɗinne bayasan bari fitar"

jitayi ya janyo ta jikin shi, ta faɗa tana Yar dariya.
"ashe kin gane banaso ki wahala ne"
da kyar ya yarda da ta dinga kaisu school ɗin saita jira a tashe a gidan mommy ta wuce ta taho dasu.

tare suka fito palour da gudu Nihal tazo ya rike Habib.
"Nihal yau ba homework ne kika zauna kina kallan kwallo"

"nayi ai"
"that's good my love"

jiddah ce ta janye ta daga jikin Habib ɗin tana faɗin "Nihal kibari Abbi ya tafi aiki ko"

kafaɗa ta maƙe tace "a'a zan bishi ya kaini wajan yaya Abdul ne" ta faɗa tana sa rigima.

Habib ne yacewa jiddah ta dauko Aiman kawai na ajiye ku a wajan mommyn..


suna mota Nihal na rike da Aiman a back seat suna wasa, su kuma suna front seat.

"dear dafa nice nace ka kaimu bazaka kaimu ba ko"!?
dan kallan gefenta yayi sannan yaci gaba da driving ɗinsa, sannan yace "ai kinsan wata kusan tafi wata kusan"
da sauri ta kalle shi tace "wato sun fini kenan kake nufi"

shiru ya ɗanyi Kamar bazaice komaiba, sai kuma ya ɗan taɓe baki yace "mamaki kikeyi wai"? ya karasa yana dan kallan face ɗinta.

ganin ta haɗe rai ne yasa shi yin murmushi yace "see you, I'm joking keɗin rayuwa ta ce dan bazan iya rayuwa babu ke ba"

murmushi tayi tana yi masa dukan wasa sannan ta kwantar da kanta jikin kafaɗar shi..


a gidan mommy suka samu su hibban da Afnan tare dasu khaleesat sai Abdallah karamin yaron su, duk sun cika palourn da hayaniya.

Habib yana shiga sukayi shiru suna mazurai, yana gaisawa da mommy ya fice dan kanshi harya fara ciwo ɗan hayaniyar dayaji hakan yasa da sauri ya fice...


mommy dake zaune Abdul na gefenta tunda ya gaida baban nashi ko ɗago kai bai sakeyi ba fuskar nan babu fara'a a tare da ita.

"Lallai Habib wannan cutar taka tana bukatar magani, ayi mutum baisan hayaniya bayan gashi nan kafara tara iyalai, duk ka koya musu halinka yara kamar basu a waje idan kana tare dasu" mommy ta dinga mita suna dariya..

"ai gashi nan ya koyawa wannan tunku ɗin koda yaushe fuska a haɗe harta na fara tunanin korashi wajan iyayen su sukarata dashi can tunda sun saba" mommy ta sake faɗa tana kallan Abdul, wanda ya tashi fuu yayi Dakin shi..


"yaya hibban yau bazaka je aiki bane" jiddah ta Tambaye shi.

hararan wasa yayi mata yace "ban sani ba, ai kinga dai tare nake da matata ba zaman banza nake ba"
daƙuwa mommy tayi masa tana barin palourn danta fahimci yanzu zata fara raba faɗa dan hibban da jiddah indai suka haɗu sai sun tsokani juna..


cikin ikon Allah rayuwar jiddah da Habib kamar rayuwar hanta da jini ne dan koda yaushe suna tare koda yana wajan aiki basa jimawa basuyi waya ba..

babu laifi tana kaiwa ƙauye ziyara time by time, dan yanzu kawu Audu yana sana'ar shi a gida wanda jiddah ce ta buɗe masa katon shago a kofar gidansa...

*******


*Alhamdulillah ina godiya ga Allah daya bani ikon gama wannan Novel lpy, Kuma Allah ya yafemin kura kuran danayi a cikinsa,,, saimun haɗu a sabon Novel dina*


*RANA TSAKA*✍️✍️✍️

ina godiya gareku mutanan Wattpad, godiya mai tulin yawa👏


*🌹first lady🌹*


29/1/2020
Chapter 4 · 0% Book details