← Book details Dr Habibullah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 2 OF 4

Part ɗin Habib ta hango alamun baya nan da sauri nufi inda saurayin yake.

Dr Habibullah Part 1 Complete Hausa Novel · about 49 min read

Saurayi ne babu laifi kyakkyawan ne dai² misali, sallama tayi masa ya amsa sannan ta gaida ya amsa a sake.

Saida ya gama gabatar da kanshi sannan ta bude baki zata bashi hakuri saidai ina tuni ta zato idanuwanta ganin Habib yayo wajanta kai tsaye fuskar nan har wani ja tayi.
Kafin ya karaso da gudu ta nufi palourn su tana shiga ɗakinta ta wuce ta rufo kanta.


Shima saurayin mamaki yayi ganin Habib yasa tabar wajan, Habib na karasowa saurayin ya mika hannu su gaisa saiya ga Habib ɗin ya sake tsuke fuska nan.

A hankali Habib ya fitar da wani huci daga bakinsa sannan ya sake kallan saurayin a lalace a wulakance.
"Malam karna sake ganinka a gidan nan," har zai wuce yaji saurayin yace "koza iya fadamin meyasa."
"Saboda tanada wanda zata aura" Habib ya fadi maganar bayareda wani tunani ba.
"Amma ai banji labari ba kafin zuwana" ya sake jefawa Habib maganar.

Wani murmushi wanda yafi kuka ciwo Habib yayi sannan ya juyo yana karewa saurayin kallo "ai gashi yanzu kaji" Habib ya faɗa yana barin Wajan.
Yanajin tashin motar saurayin wanda ya tafi cikeda mamaki.


A zuciye Habib ya shiga palourn, idanuwan shi sun kankance sunyi ja, kai tsaye ɗakin ta ya nufa ,.
Kiran mommy ne yasa ya tsaya yana rintse ido sannan ya juyo yana huci.

"Habib waikai wanne irin mutum ne, meyasa bazaka iya boye fushin ka na wani lokaci ba kullum kai a zafin kai kake"

Idanuwan shi ya buɗe jin fadan mommy,,.
Dakyar ya iya magana a hankali.
"Mommy jiddah harta San tafara kula samari... Yayi shiru yakasa ƙarasawa.

"Ikon Allah to sai yaushe kakeso ta fara kula samarin tunda naga kaine uban nata yau kuma" mommy ta faɗa tana tsare shi da kallo.

"Jiddah fa yanzu saura wata biyu kacal tagama makarantar to yaushe kakeso ta tsayar da wanda zata aura Sarkin fushi,,,, to wlhy ka kyalemin ya ta zabi wanda takeso tun wuri duk kabi ka gama tsorata yarinya data ganka zata fara cin gudu tana buya kokuma tafara kuka Habib ka fita ido na na rufe fa.." mommy taci gaba da fadanta...


Saida ta gama sannan Habib ya fice zuciyar shi na suya har wani juwa yake gani a haka ya shiga part ɗinsa.
"Meyasa nake jin zafi ne akan wannan yarinyar, meyasa banaso na ganta da wani..,,""? Ya jerowa kanshi tambayoyin da basu da amsa...

Jiddah kuwa har akayi magrib bata fitoba tana tsoron karsu hadu a palour.
Saida akayi isha sannan ta fito tayi dinner, mommy kuwa batace komaiba akan maganar.
Tana gama dinner ta koma ɗakinta ta kwanta.

Habib ma badan yaso ba saidan mommy ta takura yazo yayi dinner, coffee kawai yasha yana wani yamitsa fuska da jan tsaki kasa ƙasa wanda baisan dalilin yinsa ba, yanaji hibban yana magana amma ko kallan shi baiyi ba ya fice.
Murmushi mommy tayi danta fahimci abinda Habib ke nufi saidai tasan yadda zatayi dashi....


Ɗakinsa mommy ta nufa dauke flask Wanda ta zuba masa coffeen shi na dare aciki.
Zaune yake da computer a gabansa, ɗago kai yayi yana kallan mommy sannan yayi murmushi ganinta da flask..

A kan Centre table ta ajiye sannan ta dawo gefen shi ta zauna tana kiran sunan shi.
"Na'am mommy". Ya amsa dai² yakai coffee bakinsa.
"Habib ina san ka auri Jiddah.....";!

Wani irin faduwar gaba tareda razana yasa Habib kwarewa da coffee take yafara tari.
Da sauri mommy ta amshi cup din hannunshi ta ajiye sannan takama tafara shafa kanshi a hankali.
Saida ya tsagaita sannan ya kalli mommy cikin murya mai rauni "mommy bazan iya auran...." Kafin ya ƙarasa yaji mommy tace "umarni nane wannan ba shawarar ka nake nema ba".
Gaba daya ji yayi kanshi ya fara ciwo a haka ya ɗago jajayan idanuwan shi da suka fara rufewa yace "shikenan mommy" daga haka bai sake cewa komai ba.

"Allah yayi maka albarka my son, ka kwanta ka huta" ta faɗa tana tashi ta fice.

Tana fita Habib ya kwanta, yakasa tantance wanne irin yanayi zai fassara hakan dashi yakasa tabbatar da yadda yakeji a ranshi.
"Ya Allah" ya furta a hankali yana rintse idanuwanshi....


Mommy Kai tsaye dakin jiddah ta wuce zuciyarta cikeda farin ciki dan tasan jiddah bazata ki amincewa da zancan taba.
Jiddah na kwance taji bude dakinta, murmushi tayi ganin mommy ce.
"Jiddah tashi zamuyi magana" mommy tace da ita.
Babu musu jiddah ta tashi dan yauce rana ta farko da mommy tace zata magana da ita.

Kamo hannunta mommy tayi sannan tace "jiddah inaso ki auri Habib duk na nasan hakan zai zama kamar takura a wajanki..." A hanzar ce jiddah ta ɗago tana rufe bakin mommy duk da irin yanayin data tsinci kanta wanda bazata fassara shiba.
"Haba mommy ya kikeso ki banbanta ni da yar da kika haifa da kanki, umarni kawai zaki bani dole zanbi tunda na ɗauke ki kamar *MAHAIFIYATA* wacce na rasa.." ta faɗa Muryar ta na rawa.
"Jiddah idan bakyasan shi bazan yi miki dole ba, ki fadamin yanzu"
"Ina sanshi mommy" ta faɗa amma a zuciyarta kamar ta face da kuka haka takeji.
"Amma saidai shi yaya Habib ba lallai ya..."
"A'a jiddah shima Habib yana sanki, saidai bazai iya faɗa miki bane nice na gano hakan, kuma yanzu da kanshi yace na tuntubae ki naji idan zaki amince"..

Tsananin mamaki ne yakama jiddah, jin Habib da kanshi ya amince harya turo mommy me hakan ke nufi Kenan dama can yana santa kishi ne yasa yake azabtar da ita idan yaganta da wani..
Muryar mommy ce ta katse mata tunanin "kiyi tunani jiddah zuwa wani lokaci idan kinga zaki iya auran nashi sai a tsayar da lokaci da zarar kin gama makaranta sai ayi auran"... Mommy ta faɗa tana tashi ta fice...


Sam jiddah takasa wani tunani, cikin kankanin lokaci bacci ya sace ta cikeda mafarki kala kala...

Habib kuwa ya dade baiyi bacci ba, shikenan yasan raini dole zai shiga tsakaninsu da yarinyar wanda shi bazai dau hakan ba, dole ma yasa yarinyar ta gane tayi kuskure data nuna tana sanshi.......


Mommy kuwa cikeda farin ciki tayi bacci dan tasan shikenan lokacin sauyawar Habib tayi sannan bacci ya sace ta.


Kuyi manage da wannan👈


*_🌹 FIRSTLADY CE🌹_*✍🏻


```VOTE
COMMENTS
&
FOLLOW```🤝🏻
[1/1, 2:24 PM] Aunty Usee: 🌹🌹🌹
*_DR. HABIBULLAH_*
🌹🌹🌹


*_Writing by_*📚✍🏻
*_🌹 FIRSTLADY🌹_*


*WATTPAD*
@Ameenafirstladyy


*_🌈 KAINUWAWRITERSASSOCIATION_*


*https://www.Facebook.com/Kainuwawritersassociation*


12


.....yau da wuri jiddah ta tashi, ko breakfast batayi ba ta shirya tafiya school saboda exam din da zasu fara kwana nan.

School bag ɗinta ta dauka sannan ta fice jin hibban nayo mata alamun ta fito.
Tana shiga hibban ya tada motar suka fice,. Akan idon Habib suka fice taɓe baki yayi sannan ya nufi wajan mommy.


Hibban Yana lure da jiddah duk jikinta a sanyaye yake tun safiyar Yau.
"Jiddah akwai matsala ne"..?

Girgiza kai tayi sannan taci gaba da wasa da yatsun hannunta.
Saida Hibban yayi murmushi sannan yace "bakya sanshi ne, saboda halin shi ko dakuma abinda yake miki"? Yasake jeho mata tambayar.

Cikin tsananin mamaki jiddah ta kalle shi jin yasan maganar,.
Waigowa yayi yana kallanta dauke wani murmushi sannan ya daga mata gira yace "Yes kina mamaki ne ya akayi nasan zancan,. Tuni na sani ai tun dawowar yaya Habib shawarata kawai ki amince nan gaba zakiji dadin rayuwa dashi dama na faɗa miki shi yaya Habibullah duk yadda kika dauke shi haka zaki fahimce shi..." Sosai hibban yaci gaba da kwantar mata da hankali sannan ya sauke ta a school batareda ta furta komai ba saidai tarin tunanin yadda zata iya soyayya da Habib...


Habib kuwa saida yayi breakfast sannan mommy tace "Habib na bawa jiddah kwana biyu tayi tunani akan maganar banaso naji wani abu ya biyo baya dazata ki amincewa.."

"Inshallahu mommy" Habib yace yana jin wani farin ciki sannan yayi mata sallama ya nufi hospital.
"Tabbas saiya san yadda yayi ya janye maganar nan, to amma ta yaya..'?
Murmushi yayi sannan ya ciro wayar ya fara kiran layin hibban wanda lokacin yana zaune a office ɗinsa.
"Hello yaya.."
"Wanne lokaci ake tashin su"?
"Wa fa"? Hibban ya tambaya cikin rashin sani.
Tsaki Habib yayi cikeda takaici, jin haka hibban yayi saurin faɗa masa lokacin.
"Ok" Habib yace yana katse kiran.

Hibban ya dade yana mamaki amma saiya make yaci gaba da aikin shi.

Jiddah kuwa jiki a sanyaye take komai, lokaci zuwa lokaci takan yi murmushi idan ta tuna Habib tabbas tasan Habib dole kowacce mace tayi fatan samun miji kamar shi saidai bazata iya rayuwa cikin yanayin dayake nuna mata ba, kuma sam bazata iya kin yarda da tayin mommy ba ga hibban wanda ya dauke ta kamar kanwar shi ciki daya.
Haka jiddah taci gaba da tunanin karshe dole ta yanke shawarar amincewa koda kuwa hakan na nufin sallama farin cikin ta a gidan Habib.....

Bata taɓa kawo Habib ne zaizo ɗaukan taba, hakan yasa bata ji komaiba lokacin data ga Kabir yazo daukan su.


Lokaci zuwa lokaci Habib na kallon gold watch dake daure a wrist ɗinsa, lokaci nayi ya fito dauke da jacket dinshi a hannu,.
Wata nurse ce ta fito tana fadin yallabai akwai wadanda suka kawo emergency yanzu..
Wani Banzan kallo yayi mata a dakile yace "ku nemi Ameenu I want do something at home" ya faɗa yana ficewa batareda ya waigo ba.

Da gudu yaja motarshi dan ganin lokaci yana kurewa, cikin wani irin yanayi yake binsu da kallo, kamar yaso gane guy din kamar shine wanda ya gansu a dinner tare.

Jiddah sam batasan yazo ba fara'ar ta kawai takeyi suna jiran fitowar afnan da khairat,.
"Waye wancan naga alamar kamar ke yazo ɗauka" Kabir yace yana yi mata nuni da motar Habib wanda yake danna wayarsa amma sam hankalin shi baya kai tsananin bacin rai ne kwance a zuciyarsa.

"Innalillahi.."! Jiddah ta faɗa tana zaro manyan idanuwanta da suka nuna tsoro karara.
"Lafiya jiddah" Kabir ya tambaye ta.
Ko sauraran shi bata yiba jiki a sanyaye kamar munafuka ta zagaya ta shiga motar.
Habib wanda baka iya tantance damuwarsa da farin cikin sa sam bai nuna yasan ta shigo motar ba, saida ya dau kusan mintina goma sannan ya tayar da motar batareda ya kalli inda take zaune ba..

Yanayin gudun dayake kaɗai ya isa ya tabbatar da cikin bacin rai yake,,, jiddah kuwa kasa ɗago kanta tayi tsabar tsorata da yanayin sa.

Yanayin Parking jiddah ta fice da sauri harda haɗawa da gudunta, wuf ta shiga palour ko sallama babu,,, mommy dake zaune a palourn da mamaki tace "kalau kike gudu haka jiddah keda waye"?
Kofar shigowa ta nunawa mommy saidai mommy bataga kowaba tasan dai baya wuce Habib ne.
"Habib ne"!? Mommy ta tambaye ta.

Daga kai tayi kamar zatayi kuka.
"Ke dalla can shine kike wannan numfashi kamar wadda batada gaskiya.."!
Tsuru tsuru jiddah tayi tareda share hawayen ta da suka zubo mata.
Ganin haka mommy ta sassauta Muryar ta sannan tace "jiddah bafa dole zamuyi miki ba kema yata ce kamar su saboda haka idan bakyasan Habib ki fadamin zan janye maganar.."
Girgiza kai Jiddah tayi dan bata da bakin da zatace batasan dan mommy dole ta amince "mommy Ina sanshi.." ta faɗa tana kara share hawayen.


Alhammdlilh mommy ta furta a zuciyarta sannan tace jeki shirya ki fito sai muyi maganar karki damu babu abinda zaiyi miki..
Kafin mommy ta rufe baki tuni jiddah ta wuce dakinta da sauri..

Habib ya dade a zaune baisan inda kanshi yakeba tsabar ciwan kai, har duka zuciyarsa keyi gashi mommy bazata barshi yayi wani hukunci ba koda da baki.
"Ohhh! Ya Allah" ya furta a hankali sannan ya buɗe motar ya fice.

Wanka yayi sannan ya kwanta dai² shigowar mommy ɗakin.
"Habib me jiddah tayi maka naga ta shigo a rude".
Taɓe baki yayi yace "babu mommy sharrinta ne kawai".
Ya faɗa yana lumshe idanunsa.
Kamar maisan gano wani abu mommy ta tsaya sannan tace "kayi lunch acan ne"?

"No I'm full"?yace kawai.
Saidai kisa ta kawomin coffee Yanzu mommy.
Batace komaiba ta fice daga ɗakin.

Kusan mintina shida jiddah tayi dauke da coffee tarasa tayaya zata shiga ɗakin, cikeda tsoro tayi nocking Kamar yasan itace yaki magana saida tagaji sannan ta shiga cikin sanɗa.
Kwance ta ganshi idanuwan shi a rufe yake kamar mai bacci.
Cikin sanda ta shiga ta ajiye cup din zata fice.
"Waye shi..."!?
A firgice ta juyo dan bata taɓa tunanin idanshi biyu ba sai maganar shi taji.
Tashi yayi fuskar nan a haɗe idanuwan shi farare tarr dasu saidai ya kankance ya tattare fuskar nan babu alamar wasa.
"Bana maimaita tambaya kuma nasan kinji Ni" ya fada yana daɗa haɗe fuska.
"Yaya Habib nima bansan shiba tambaya ta yakeyi.." ta bashi amsa a takaice.
Wani malalacin murmushi yayi wanda jiddah tasan na mugunta ne.
"Ni zakiyiwa karya eyy" ya faɗa yana tashi tsaye.
Matsawa tafara yi ganin yana nufo ta.
Cikin hawaye tafara magana "dan Allah yaya Habib kayi hakuri wlhy yayan afnan ne kuma mun dade muna tareda shi"ta faɗa tana cigaba da kukan.
Habib jin ta ambaci sun dade tare tuni yaji zuciyarsa tayi wani baki da zafi,..
Ganin yanayin shi ya sauya ne yasa jiddah tafara tsorata tana yin baya.
"Kina sanshi kenan..."? Kafin ya ƙarasa tayi saurin girgiza kai "a'a wlhy banasan shi yaya Habib" ta faɗa batareda tayi wani tunani ba Dan fitar da kanta.

Taɓe baki yayi sannan yace "ficemin a daki".
Da sauri tayi hanyar fita tsayar da ita yayi cikin tsawa "share wannan hawayen kafin ranki ya ɓaci" ya faɗa ko jiyowa baiyiba.
Sharewa tayi sannan ta fice da gudu ta nufi part ɗinsu,Kai tsaye ɗakinta ta faɗa tafara kuka mai tsuma zuciya....


Habib kuwa murmushin mugunta yayi sannan yasha coffeen yana wani lumshe ido koba komai dai yayi maganinta ai....


I'm sorry my Fans I have lots of things that's why manage this👈


*_FIRSTLADY🌹_*✍🏻
[1/1, 2:24 PM] Aunty Usee: 🌹🌹🌹
*_DR. HABIBULLAH_*
🌹🌹🌹


_writing by_📚✍🏻
*_🌹 Ameena firstlady🌹_*


*WATTPAD*
@Ameenafirstladyy


*🌈 Kainuwawritersassociation*


https://www.Facebook.com/Kainuwawritersassociation


*_(This page is yours my sweet sisters Husaina sunusi ibadan thank you so much I'm so proud of you)_*💓💓

```I can't forget you my daughter NEESHER JAY```🌹🌹


13


_________________________


Jiddah saida taci kukanta Sannan ta share hawayenta ta shiga wanka.
Tana fitowa kiran hibban ya shigo ta daga fara'a.
"Yaya hibban ya aiki.."?
"Kalau kanwata, badai wata matsala ko?
"Eh babu" tace.
Murmushin jin dadi yayi sannan yayi mata sallama yaci gaba da aikinsa.

Cikin Wata ash color din atamfa docuwar riga ta shirya, bakaramin kyau tayi ba,, har zata fita kiran Kabir ya shigo wayarta.
A sanyaye ta daga tareda sallama dauke a bakinta.
Amsa mata yayi sannan yace "jiddah waye wannan wanda yazo ɗaukar ki".. ya jeho mata tambayar.
"Yayana mana"
"A'a jiddah bayan wannan fa"? "Kabir bazan boye maka ba amma kayi hakuri zakaji bayani a daga afnan amma karka ga laifi na dan Allah".
Kabir kasa fahimtar bayananta yayi hakan yasa ya katse kiran kawai dan hankalin shi ya fara tashi..

Jiddah kuwa jagwab ta zauna kan katifar ta tana rintse ido, sam bazata iya misalta yadda takesan Kabir ba shi kadai ta bawa soyayyar ta gashi ƙaddara tasa zata rabu dashi ta auri wanda babu soyayyar shi ko kadan a zuciyarta.
Palour ta fita ta zauna tana jiran a kirawo sallar la'asar sannan ta tashi.


Habib yana gama shan coffeen shi ya sake shiga ya sheka wanka sannan ya fito ya kwanta bisa three sitter dake ɗakin kanshi na kallan silling..
"Meyasa nake damuwa da ganinta da wani danayi, mezai sa na damu bayan sam babu soyayyar ta a ranshi infact ma shi tsanarta ce a ransa dan Baiga abin so a jikinta ba..."
Tunanin shi ne ya tsaya tunawa da yayi ta amsa zata aure shi cewar mommy, rintse idanuwanshi yayi da sukayi masa zafi da nauyi.
"Zaki gane kuskurenki very soon,," ya faɗa ko bude ido baiyiba.
Jin ana kiran sallah ne yasa ya fice dan zuwa masallaci....


Suna idar da Sallah tareda hibban suka shigo gidan,, tana zaune a palour taji sallamar su sannan ta amsa tana kasa dakanta dan batasan su hada ido da Habib.
"Kanwata" hibban ya kirata cikin fara'a.
Ɗago kanta tayi da murmushi tace "yaya hibban sannu da dawowa"
"Yauwa jiddah, tashi muje ki tayani gyara dakina" ..
Tashi tayi da sauri dan dama a kuntace take a palourn.
Kallon gefen da Habib yake tayi yana zaune cikin wani tsadaddan farin yadi wanda ya amshe shi sosai ya fito da ainihin farar fatar shi saidai fuskar nan a haɗe kamar kullum,,.
Taɓe baki jiddah tayi tace "mutum a cikin gida ma bazaiyi fara'a kamar sauran mutane ba" ta faɗa tana bin bayan Hibban.
Sarai Habib ya ganta wanda tuni zuciyarshi tafara zafi da tafasa saidai bai nuna ba duk da shi kadai ne a palourn lebensa ya ciza sannan ya wani hura baki ya fitar da iska cikeda bacin rai...

Hibban da jiddah kuwa hirar su sukeyi harda dariya "yaya hibban nifa nayi maka mata kawai kai nakeso ka motsa"
"Uhmm wacece fadamin"
"Afnan na baka kuma na yarda da ita sosai.."
Dariya yayi yace "angama kanwata jeki shirya ki raka ni"
Cikeda mamaki ta kalle shi "da gaske kake yaya hibban ka amince"
Kautar da kanshi yayi yana barin wajan zuwa bathroom danyin wanka sannan yace "naki wasa ne yar nan Ni kingama wanka zanyi ke kawai zan jira" ya shige batareda ya kuma cewa komaiba.
Abin ya ba jiddah mamaki sosai, part ɗinsu ta koma lokacin Habib bayanan kai tsaye ɗakinta ta wuce ta dauko mayafinta sannan ta haifa sama wajan mommy.
"Mommy zamu fita nida yaya hibban"
"Ina kuma zakuje sarakan yawo"?
"Da alamar dai yau suruka zamo samo miki" jiddah tace tana dariya.
"Aaa toku je maza a zabo mai kyawawan halaye dai" mommy tace.
Da gudu jiddah tayi hanyar fita tana dariya "aima mommy tanada kyawawan halayen ma" ta faɗa tana ficewa.

Motarsu na tsayawa jiddah zata fice hibban ya dakatar da ita.
"Let's me call her" yace yana zaro wayarshi.
Jiddah sakin baki tayi cikeda mamaki wato ma har waya sunayi kenan.
"Hello My dear, ki fito ina waje".
Daga can ɓangaran afnan tace to gani nan.

Jiddah kasa cewa komai tayi mamaki ya gama kasheta a tsaye,, tun daga nesa ta hango afnan taci uwar kwalliya.
Tana karasowa tayi dariya cikeda farin cikin ganin shi tareda jiddah.
"Jiddah yau kuma harda ke"?
Harara jiddah ta maka mata sannan ta nufi cikin gidan dan gaida Mama.
Sun dade suna soyewar su sannan yace ta shiga tace jiddah ta fito yana jiranta.
"I'm sorry jiddah shiyace karna sanar miki soyake yayi suprise dinki" afnan tace tana nuna alamun damuwa.
"To ai kun kyauta gashi kuma yayi".
Ta faɗa suna ficewa..

A mota jiddah shagwaba ta dingayiwa hibban wai tayi fushi ace yana soyayya da Aminiyarta amma bata sani ba sai yau.
"To yar rigima ta dalilinki nasan ta ai idan bakyaso saina kyaleta ai na nemi wata".
"A'a inaso mana kaga kuwa yadda kuka dace da ita"
"Bangani ba sai yanzu da kika faɗa"
"Kuma auranta zakayi da gaske yaya hibban" ta sake tambayar shi.
"Eh mana so nakeyi a saita bikin da naku keda yaya Habib..."!
Tsit tayi bata sake magana ba dan gaba daya jikinta sanyi yayi.
Hibban kunshe dariyar shi yayi ganin harta nutsu kamar ba itace take faman zuba surutu ba.
"Yadai jiddah akwai wani abu ne"!
"A'a babu komai" tace kawai.
Murmushin hibban yayi sannan yaci gaba da driving ɗinsa.....


Yanzu su jiddah tuni sun fara exam ɗinsu sosai suke shan wuya,,,tuni Kabir ya hakura saidai bakaramin jinyar zuciyarshi yayi ba akan soyayyar jiddah hakan yasa lokaci zuwa lokaci yake kiranta su gaisa..

Kullum hibban ke kaita school ya dauko ta dan fafur Habib yace bai yarda akawo wani kato wai driver ba gara hibban ya dinga zuwa ɗaukar ta...

Har yanzu babu wata jituwa tsakaninta da Habib yanzu ko gaisuwa saidai idan mommy na wajan yake amsawa,,, duk wata hanya dazai bi wajan ganin ya warware maganar abin yaki yiyuwa..
Yauma kamar kullum jiddah dawowarta kenan daga school a gajiye saboda yanayin exam,,, ko abinci bataci ba Habib ya shigo palourn..
Har zata shige ɗakinta taji yake kee kamar yadda yake kiranta koda yaushe.
Jiyowa tayi bata amsa ba dan itama abin yafara bata haushi.
"Ki gyaramin dakina Yanzu" yace yana hanyar fita.
"Kabarta ta huta ai ko baba Sarkin saka aiki"
Baice komai ba ya fice ya nufi part ɗinsa.
Jiddah kuwa kaya kawai ta sake ta fito zata wuce part ɗin nasa.
Mommy dake zaune gefe ta tsayar da ita.
"Ina zakije bikici abinci ba"!
"Mommy zanje na gyara masa dakin ne yanzu zan dawo kinsan halinshi yanzu sainayi laifi".
Mommy batace komaiba Dan Yanzu abin har haushi yake bata yadda jiddah ke tsoron Habib kamar wani aljani...
Jiddah kuwa ganin mommy batace komaiba yasa tayi saurin ficewa..
A hankali ta tura kofar palourn nashi,wani daddan ƙamshi ne ya ziyarci hancinta tareda sanyin a.c mai ratsa jiki..
Lumshe ido tayi yadda taji ƙamshin yayi mata daɗi ga palourn tsaff kamar ba'a shiga cikin sa.
Kallan palourn tayi babu wani abin gyarawa kuma shima baya palourn, dole ta nufi ɗakin shi dan sanin inda zata gyara.
Zaune yake hannun shi rikeda da ƙatuwar wayarshi da alamu wani abu yake dubawa...
A hankali ta shigo dakin sannan tayi dauriyar cewa "gani yaya Habib"...
Ko kallan inda take baiyiba ba kamar ma baisan da wata halitta a wajan ba..
Jiddah ta dade a tsaye har kafafunta suka fara gajiya bashi da alamun ɗago kai yayi mata magana gashi babu damar fita ta shiga Uku wajanshi.
Takaici ne ya kamata ganin bashida bashida alamar yin Magana...
Saida ya Kara dadewa sannan ya ɗago fuskar nan tashi kamar haduwar hadari yana kallanta kallan wulakanci.
"Meyasa kika amsawa mommy zaki aure ni" ya jeho mata tambayar babu alamar wasa sai zallar bacin rai.
Cikinta ne ya wani juya jin tambayar da batasan amsar da zata bashi ba hakan yasa tayi shiru.
Taɓe baki yayi yaci gaba da danna wayarshi a zuciyarshi yace baki gaji ba kenan.
Jiddah tasan ko kwana zasuyi indai bata bashi amsa ba saidai su kwana a haka ga yunwa tanaji.
"Babu komai"
Har zuciyarshi yaji haushin Maganar Tata amma saiya make tareda yin wani shu'umin murmushi sannan ya sake haɗe fuska.
"Jiddah bana sanki dan banga abin so a tareda keba sam baki kala da irin matan da zan iya koda soyayya dasu ba," ya faɗa yana yi mata wani irin kallo kamar yaga kashi.

Har zuciyarta taji haushin Maganar tuni hawaye suka zubo mata tafara sharewa.
"Saboda haka ki samu mommy kice bakya Sona idan ba hakaba kuwa,, should you be a trouble"""" yace yana wani sakeyin murmushin wulakanci.

Yana jinta tana alamar kuka dama haka yaso sannan yace ta fice mai a daki,, aikuwa da gudu ta fice tana kuka.

Murmushin ya sakeyi "yanzu ma kika fara kuka.."

Jiddah tasha kuka amma ko mommy Bata fadawa komai ba sai hibban kawai ta sanarwa shima baiji daɗi ba amma sai hakuri ya bata tareda kwarin guiwan tayi hakuri dole watarana zai sota....
Habib kuwa kullum saiya kasa kunne yaji mommy tace jiddah tace batasan shi saidai ina baiji komaiba gashi gu sai kurewa yakeyi sun kusa gama exam..

Jiddah kuwa bata sake bi ta kanshi ba da sassafe kafin ya shigo sun fice itada hibban zuwa school kuma idan ta dawo bata fitowa saita tabbatar baya nan.
Sam itama yanzu wani haushin shi takeji musamman idan ta tuna irin maganganun daya faɗa mata "kowa ya faɗa masa Nima Ina sanshi oho" ...

Wasan yar buya yanzu sukeyi sosai sai wajan cin abinci kawai suke haɗuwa nan ma bata bari su hada ido kuma tana gamawa zata bar palourn ya Karaci hucin shi ya fice danta dana masa tarko tunda yaci mata mutumci kodan ta bakanta masa bazata ce batasan shiba kodan Mommy..

Habib yakasa tantance irin yanayin dayake ciki,,, mommy kuwa batasan abinda ke faruwa ba kota tambayi jiddah saitace baya mata komai...

Habib Zaune a makeken office ɗinsa, hankali kwance yake aikinsa saidai cikin zuciyarshi ranshi ya ɓace yake..
Wata farar takarda ce a hannun shi yana dubawa.
Tsaki yayi sannan ya danna wani abu yayi ƙara.
Cikin sakanni wata nurse ta shigo jiki na rawa.
"Yallabai gani"
"Ina Ameenu?
"Yallabai saidai a kirawo shi" tace tana kallan fuskar shi.
Bai bata amsa ba kusan second goma sannan ya dago fararan idanuwanshi yace "Are You mad, bakisan aikin bane"
Da sauri ta fice daga office din Dan Kiran Ameenu.
Tare suka shigo tace "gashi yallabai zan iya tafiya" shiru yayi baice komai ba hakan yasa ta gane ba sauran wani abu sannan ta fice tana rufo Kofar.

Saida suka kusan mintina shida sannan ya ɗago sexy eyes ɗinsa ya karewa Ameenu kallo.
A dakile yace "zaka cigaba da kulada komai zanbar asibitin nan a hannunka""
"Meyasa Dr. Habibullah" Ameenu ya tambaya cikeda mamaki.
"Wannan ba matsalar ka bace". Ya bashi amsa a takaice.
"Shikenan Dr. Zanyi iya kokarina akan haka".
"Ok you can go" Habibullah yace yana maida hankali kan aikinsa...


Lokacin daya dawo gida tuni su jiddah sun dawo,,,

Kai tsaye part ɗinsa ya nufa ya sheka wanka sannan ya fito ya shirya ya nufi part ɗin mommy yana fatan Allah yasa ta amince da buƙatar sa....


```vote
Share
&
Comment```


*_FIRSTLADY🌹_*✍🏻
[1/1, 2:24 PM] Aunty Usee: 🌹🌹🌹
*_DR. HABIBULLAH_*
🌹🌹🌹


_writing by_📚✍🏻
*_🌹 firstlady🌹_*


*_WATTPAD_*
@Ameenafirstladyy


__________________________
*_🌈 KAINUWA WRITERS✍🏻 ASSOCIATION🤝🏻_*

```{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```


*https://www.Facwbook.com/Kainuwawritersassociation*
___________________________


14


... Kai tsaye upstairs ya haye ɗakin mommy ya shiga dauke da sallama a bakinsa.
Jiddah dake kwance saman bed din mommy tana jin sallamar shi ya boyewarta ta rufe ido kamar mai baccin gaske.

Mommy ce ta amsa masa sallamar tana zaune gefen mirror ɗinta,.
Kallan jiddah dake kwance yayi sannan ya taɓe baki ya zauna gefen gadon yana yiwa mommy sannu da gida.
"Yauwa, harka dawo daga wajan aikin kenan"?
"Eh mommy" yayi shiru yarasa ta yaya zai faɗa mata yana san komawa Russia ba.

Ƙarfin hali yayi yace" Amm., Dama mommy inaso zan koma Russia ne"!!
Juyowa mommy tayi tana yimasa Wani kallo wanda yasa gaban Habib faduwa dan ya gano kamar ranta ya ɓaci.
"Me zakayo a Russia kuma, ina ka gama course din daya kaika"? Mommy ta tambaya tana cigaba da kallonsa.
"Eh mommy na gama" ya faɗa a takaice.
"To kuma mezakaje kayi?"
Sam Habib bayasan maganar sosai amma ya fahimci idan baiyiwa mommy bayani ba bazata barshi ya tafi ba, dan saita gano tserewa maganar auran nashi yakeyi.

Numfashi yaja sannan yace "mommy inaso zan koma nayi ɓangaran mata"!
"Bangane ba Habib banasan maganar wai gynaecology kake san ka koma kayi"? Mommy ta tambaye kai tsaye.

"Eh mommy Dan Allah karki hanani komawa likitocin mata sunyi mana karanci kuma shi nakeso yanzu na karanta saboda asibitina....."

Katse mommy tayi da fadin "to maganar auran naka kuma fa"?.
"Saina dawo sai ayi" ya bata amsa.

"To ban yarda ba Habib, saura sati biyu ta gama makaranta kuma so nake data gama muje can kauyan nasu mu nemo auran dan banaso bikin ya wuce wata biyu masu zuwa tunda Hibban ma ya samo wacce zai aura sai a hada kawai.." mommy ta faɗa tana tashi daga gaban mirror ɗin zata fice...

Da sauri yace "plsss mommy Dan Allah karki hanani tafiyar nan ki san burina kenan a rayuwa" ya marairaice murya kamar karamin yaro...

Murmushin mommy tayi dan tasan halin dan nata amma bazata iya bari ya tafi ba'a yi auran nan ba danta gano hakan ne yasa yakesan tafiyar wato sai an ganshi kenan.
Zama ta kumayi sannan ta kamo hannunsa cikin nata. "Naji Habib zan Barka ka tafi.."
Wani irin farin cikine ya rufe shi har saida yayi murmushi..
"Amma sai bayan anyi auran tukun saika tafi kabarta a wajena itama saita ci gaba da karatunta kafin ka dawo"...


Cikin wani irin yanayi wanda yakasa tantance wanne iri ne yake kallan mommy Sam bashi da bakin kin amincewa dole ya daga bakinsa dakyar yace.
"Shikenan mommy yayi"
Murmushin ta sakeyi cikeda farin ciki "yauwa Allah yayi maka albarka, Habib" ta faɗa tana ficewa daga ɗakin zuwa palour.

Kanshi yaji yafara ciwo hakan yasa ya tashi shima ya fice cikeda bacin da kissima abubuwa da yawa a ranshi...

Jiddah kuwa taji komai tuni jikinta yayi sanyi jin maganar mommy bataso ko kaɗan wani abu ya sake hadata da inna marka, saidai babu yadda zatayi dole ta hakura farin cikin ta daya jin zataci gaba da karatu burin mahaifin ta zai cika kenan..


Mommy da kanta ta nemi yan uwan mahaifinsu Habib sukaje neman auran afnan, saboda sanayya yasa aka amince tareda saka rana wata biyu kacal,,.
Hibban yaji dadin hakan saidai yana tausayin jiddah dan yanzu kana ganinta kasan tana cikin damuwa har wata yar rama tayi ta tunanin auran Habib wanda ko yaushe yana faɗin bayasan ta duk da itama ba sanshi takeyi ba amma tanajin yadda auran nasu zai kasance...

Su duka suka shirya zuwa kauyen saidai Habib cewa yayi yanada aiki bazai samu zuwa ba dole saida Hibban suka tafi jiddah jikinta a sanyaye.
Suna shiga kauyan aka fara bin motarsu da kallo yara nata ihu kamar basu taba ganin motaba,,,. A kofar gidan kawun nata aka tsaya sannan hibban ya fito ya buɗe musu motar.
"Jiddah ki saki jikin ki zasu yarda kuma bazasu hanamu komawa dake ba kinji" mommy tace dan kwantar mata da hankali.
Ƙaƙalo murmushi jiddah tayi tana daga kai sannan suka fito suka shige gidan.....


Inna marka kamar a mafarki taga jiddah dakyar ta ganeta ganin yadda tayi wani kyau suffar Fulani sak daga ganinta,, cikin murna ta taresu tana kawo musu ruwa sannan ta aika aka kira kawun jiddah,, wato kawu Audu..

Shima yayi farin ciki ganinta sosai musamman dayaji neman auranta aka zo ba bata lokaci ya amince musu tareda yi musu da neman tafiyar jiddah.
"saidai kuma auran yayi kusa da yawa.."
Mommy ta fahimci meyake nufi hakan yasa tayi murmushin manya "karka damu jiddah yanzu ai yaya ce dama kawai yardar Ka muke nema ganin kaine mahaifi a gareta yanzu.."

"To Nagode Allah yakara arziki,, ince wannan ne siririn namu ko" kawu Audu ya faɗa yana kallan Hibban.

Mommy ce tace "aa shi sirikin naku aiki ne ya tsayar dashi shiyasa wannan kanin sa ne"!
"Masha Allah Allah ya kaimu lokacin babu komai" kawu Audu ya faɗa..

Inna marka ta kawo musu fura da nono wacce aka dama da dabino saiga Hibban yasha sosai suka dinga yi masa dariya shikuwa bai kulasu ba..

Sai yamma sannan sukayi sallama suka hau motarsu suka wuce,, jiddah har hawayen farin ciki tayi ganin yadda su kawu Audu suketa faman rawar kan ganinta koba komai yanzu tasan batada sauran matsala a wajansu.


Kiran Habib mommy tayi a waya bugu biyu ya daga tareda yin sallama "Habib sun amince gamu nan hanyar dawowa".
Cikin wani takaici yace "alhammdlilh" ya dakile.
Katse kiran mommy tayi tana murmushi jiddah kwance a cinyarta.
Cikeda tsokana hibban ya waigo "sarkin san jiki idan anyi auran ya Habib dai bazai dauki wannan halin ba".
Shiru tayi bata bashi amsa ba ganin mommy a wajan.
"Hibban banasan tsokana ka mayar da hankali kan abinda kake yi" mommy tace..


Sun isa gida lafiya Habib yaji dawowar su saidai bai kula inda suke ba saima wani huci yayi cikin bakin ciki.........


Tunda suka dawo mommy tafara Shirin bikin ko su hibban ɗin basu sani ba,, jiddah kuwa hankalin ta mayar kan exam din da suka kusa kammalawa.
Yau da sassafe Habib ya shigo palourn nasu,, mommy na kichine yada coffee,, har kichine din ya shigo ya gaida ta.
"Nasan coffee ne ya shigo dakai Yanzu"
"Eh momma"
"Nagama ai har breakfast din anyi" ta faɗa tana Miko masa kayana "tayani fitar da su"
Babu musu ya amsa yana tayata fiyarwa zuwa dining room.
Saida suka gama suka fito dai dai shigowar hibban.
Shima mommy ya fara gaisawa sannan yace "good morning bro"
"Morning too" kawai yace yana matsawa jikin table din.
"Yauwa Habib jeka kira jiddah muyi breakfast din"!
Dumm yaji maganar wani iri, ko konto yakeyi kodai bada shi mommy take ba shidin ne zaije ya taso ta kenan lallai akwai matsala shikenan raini zai fara shiga tsakaninsu daga yau kenan...
"Habib dakai nake fa koni zan tashi ne"
"No mommy " ya faɗa yana barin ɗakin..

A palour ya tsaya yana tunanin wanne ne dakin nata,, dakin dayaji kamar ana magana kasa kasa ya nufa cikin zuciyarshi kuwa tab da bakin ciki.
Ya dade a tsaye kofar dakin sannan ya tura a hankali ya shiga.

Sam jiddah batasan shigowar shiba ta juya baya tana waya da Kabir cikin shagwaba take magana harda lankwasa Murya...

Jin a fizge wayar ne yasa tayi saurin tashi,.
Wani wawan mari Habib ya dauke ta dashi wanda yasa ta ganin taurari sun gifta,, tsoro ne ya kamata ganin yadda idanuwan shi suka kankance fuskar nan tayi ja kamar wuta ..
Wayar aka sake kira, jiddah gabanta ya sake faduwa shikenan yau mutuwa tazo.
Daga wayar yayi ya kara a kunnen shi..
"Hello sweetheart" Kabir ya faɗa daga can ɓangaran.
Rintse idanuwanshi yayi yana jin wani zafi a ciki,, karar tarwatsewar wayar ne yasa jiddah zaro idanuwanta.
Hanyar fita tayi da gudu,, taku biyu yayi yasha gabanta cikeda bacin rai.
"Waye shi"? Ya fizgo dakyar ya tambaya.
Jiki na rawa tana yarfar da hannu tace "wlhy saurayina ne amm.."
Hannu ya daga cikin zafin rai zai sake marinta.
Wani gigitaccen kara ta saki, wanda ya jawo hankalin su mommy da hibban da gudu suka shigo ɗakin.
Habibullah kuwa jin karar da sauri ya toshe kunne saidai ina, kanshi ne yayi masa nauyi sosai tareda wani irin zafi, tuni yafara fita hayyacin sa.
Su mommy kuwa kan jiddah dake kuka sosai suka nufa suna tambayar lafiya.
Kin faɗa tayi saidai mommy taga zanan yatsun mari kwance fuskarta hakan yasa ranta ya ɓaci ta juyo ɓangaran ganin daya riƙe kai.

Sam Habib baya jin komai dan gaba daya jiwa yake ji.
Ƙafafuwan shi ne suka gaza ɗaukar shi yadda zuciyarshi ke harbawa da sauri da sauri,.
Dai dai matsowar mommy Habib ya sulale a Ƙasa a sume.

Da sauri hibban da mommy harma da jiddan sukayo kanshi suna jijjiga shi saidai ina tuni numfashi sa yayi nisa...


Babu shiri mommy ta dauki car key,, da taimakon gateman suka fitar dashi zuwa Mota.
Su duka suka shiga motar hibban ya figeta a guje zuwa babban hospital dake kusa.....


*Waiting next page*✍🏻✍🏻
````AMEENA MUSA```
*_🌹 firstlady 🌹_*✍🏻
[1/1, 2:24 PM] Aunty Usee: 🌹🌹🌹
*_DR. HABIBULLAH_*
🌹🌹🌹


_by_✍🏻
*_🌹 firstlady🌹_*


*_WATTPAD_*
@Ameenafirstladyy


*_🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_*✍🏻


15


Cikin gaggawa aka amshe shi sanin shi a matsayin consultant doctor.
Kusan mintina 40 likitocin sukayi basu fito ba,, mommy da hibban duk hankalin su a tashe.
Jiddah ma duk sai taji babu daɗi jikinta yayi sanyi.
Likitan yana fitowa mommy tayi saurin tashi tana tambayar lafiyar danta.
"Karku damu ku same ni a office" doctor Ahmad yace yana barin Wajan..

Hibban da mommy ne suka bishi office din, jiddah kuma ta shiga dakin da aka kwantar da Habib.
Sambal yake kwance a saman gadon idanuwan shi a rufe an rufe shi da wani katon bargo sannan ga drip a hannun shi.
A hankali yake fitar da numfashi, jiddah kura mai ido tayi kamar mai san ganin wani abu,,.
Wani murmushi ne ya suɓuce mata "gaskiya Habib ba karamin kyakkyawa bane dole yace baya santa ita ba class ɗinsa bace" a hankali ya lumshe idanuwan ta tareda sakin wani murmushin.


"Ba wani abu bane akwai mutanen da ake haifar su a haka kwakwalwar su bata ɗaukar kara ko wani ihu, hakan zaisa tayi nauyi harta girgiza sannan ta sakar musu da ciwan kai mai tsanani,, to wannan shine ya faru da doctor Habibullah sai kuma bacin rai wanda yasa zuciyarshi harbawa da sauri, idan harbawarta ya wuce haka za'a iya samun matsala"
Ba mommy kaɗai ba har Hibban saida yaji gabansa ya fadi duk da sunsan dama ba san kara yake ba ko kadan amma sam basu taba tunanin hakan ne dalili ba.
"Amma doctor babu yadda za'a yi.."
Dariya yayi yace "kiyi hakuri mommy gaskiya babu tunda haka aka haifeshi ba samu yayi daga baya ba,, saidai zamu rubuta magunguna saiya dage da sha"
"Babu matsala Ahmad mun gode" mommy tace tana miƙewa.
Tare suka fita da hibban ya wuce siyo maganin ita kuma ta wuce ɗakin da aka kwantar dashi.
Jiddah na tsaye mommy ta shigo ta zauna gefen sa tana kare masa kallo cikeda da tausayin dan nata.
"Jiddah bai tashi bane tunda muka fita"
"Eh mommy bai tashi ba"!
"Amma meya hadaki dashi"? Mommy ta sake tambaya.
Labari jiddah ta bata,, mommy ta sauke ajiyar zuciya,, tasan Habib yana saurin fushi da zuciya saidai batayi tunanin yanada zafin kishi haka ba.
Suna nan zaune Habib ya fara motsi da idanshi.
Tar ya budesu kan jiddah dake zaune facing dinshi.
A hankali ya sake lumshe ido tareda tuna abinda ya faru.
"Sannu Habib" mommy ta karaso da sauri kusa dashi.
Jiddah ma matsowa tayi kusa dashi "sannu yaya Habib" tace.
Kallanta yayi da sexy eyes ɗinsa sannan ya kawar da kanshi gefe.
Tashi yayi niyyar yi mommy tayi saurin taimaka masa ya jingina da pillow dake bayansa.
Dai dai shigowar hibban dauke da ledar magungunan a hannu.
"Yauwa hibban kira doctor kace ya tashi" har Hibban zai fita yaji Muryar Habib ya tsayar dashi.
"I will do myself" ya faɗa yana cire drip din.

"Mommy ga maganin saiya sha ai" hibban yace yana miƙa mata ledar.
Idanuwan shi dake rufe ya bude yana kallansu saidai baice komai ba.
Kallan shi mommy tayi alamun tana jiran yace wani abu.
Da kyar kamar mai koyon magana yace "I need to eat something before.." shiru yayi bai karasaba yana wani yamitsa fuska.
"Ohhh haka fa bakaci komaiba,," mommy ta faɗa tana kallan jiddah.
"Jiddah jeki hau napepki koma gida kiyowa Habib girki pls".
"No mommy coffee kawai" Habib yace.
"Coffee Habib kaida bakada lafiya tun jiya fa bakaci komaiba"
Nodding kansa kawai yayi.
"Shikenan jiddah kinji, saiki zauna kiyi karatun ki kawai kibar driver ya kawo"
"Langabe kai Jiddah tayi alamun shagwaba "gaskiya nidai mommy zan dawo da kaina plss"!
Rintse ido ya sakeyi tuna yadda take yiwa saurayin nan shagwaba kenan wannan halinta ne kowa ma zata iya yiwa" Habib ya faɗa a ransa yana jin wani daci a ransa.
"Naji jeki dawo ɗin" mommy tace kawai.

Harta fita Habib ya bude ido tunawa da yayi mommy tace ta hau napep.
"Hibban ka kaita mana"
"Yaya banaso nayi nisa ko akwai Wani abin da..."
Wani mugun kallo Habib yayi masa dayasa yayi saurin hadiye maganar tasa sannan ya fice da sauri.

Jiddah harta fita gate taga hibban ya fito da motar sa,, motar ya bude yace "shigo na kaiki"
"Amma yaya hibban za'a iya neman wani abu fa..."
"To ya zanyi Sarkin kishi bai yarda ki hau napep ba" ya faɗa yana dariya kasa ƙasa.
Dariya jiddah ma tayi kawai ta shiga motar...


Suna fita mommy ta dawo da kanta wajan Habib,, daya rufe ido.
"Habib"! Ta kira sunan shi a hankali.
Bai amsa saboda har lokacin yana jin jiki dan zuciyarshi bata daina harbawa da sauri ba,, kallan mommy yayi da kyawawan idanuwanshi.
"Dan Allah Habib ka rage saurin fushi da zuciya, banaso wani abu ya sameka ta dalilin haka.."
Kafeta yayi da idanuwan shi kamar mai tuna wani abu.
"Meya haɗaka da ita"
Nanma shiru yayi yana kallanta sannan ya rufe idanuwan nasa yanajin wani abu a zuciyarsa mai zafi.
"Babu" kawai yace yana rike kansa da yafara ciwo.
"Shikenan shikenan bari na kira doctor ya sake duba ka" mommy ta faɗa a tsorace ganin yadda ya rike kai yana cike lips ɗinsa.

Tare suka shigo da doctor din, dubashi ya sakeyi sannan yace "haba doctor Habib ka daina yawan damuwa mana saikace bakasan hadarin haka ba," docton ya faɗa cikin yanayin nasiha.
Drip yakara daura masa sannan yace lallaifa yasha maganin sa sai zuwa dare za'a sallame su idan jikin yayi kyau.
Shidai Habib baice komaiba sai rufe idanuwan shi yayi kamar mai bacci yana jin doctor Ahmad din.


Jiddah na zuwa gida da sauri da sauri ta haɗama mommy breakfast sannan ta haɗa coffeen ta zufa a flask sannan ta sakeyin wanka ta fito.
Light makeup tayi dan lipstick kawai tasa sannan ta dau mayafinta ta fito palour.
Shima hibban saida yayi wanka sannan ya fito suka taho,..
Hibban sai tsokanar yakeyi wai dan miji ba lpy duk ta rude.
"Da afnan ce ba lafiya da yanzu bamu gane kanka ba kaima ai"
Dariya sosai hibban yayi har zuciyarshi yaji dadin yadda take nuna san yayan nashi a gabansa.
Saida suka biya suka siyi snacks sannan suka shiga hospital din.
Lokacin da suka shigo an cire drip din sai Mommy na zaune suka shigo, Habib dan buɗe ido yayi jin sallamar ta,, tayi masa kyau sosai hakan yasa ya buɗe ido gaba daya saidai bai kalli ta kai tsaye ba sai satar kallanta yakeyi.
"Tashi kasha coffeen Habib"
Hibban tayar dashi cikin dabara...
"Zubo masa jiddah"hibban yace.
Da hanzari jiddah ta dauki cup din ta zuba masa.
Yana kallanta yadda kayan suka amshi jikinta tsaki yayi kasa ƙasa "wannan yarinyar bataji" ya faɗa a ransa.
"Lafiya Habib"
"Kalau mommy" yace yana murmushi dole.
Itama murmushi tayi sannan tace jiddah ta mika masa cup ɗin.
Kusa dashi ta tsaya sannan ta mika masa cup din, kallanta yayi idanuwan su suka haɗu, saurin tsuke fuska yayi sannan ya amshi cup din yafara sipping a hankali.
Dakyar ya shanye cup guda sannan mommy ta bashi magungunan nan ma dakyar yasha dan bayasan magani ko kaɗan.
"Kana doctor Amma bansan meyasa bakasan magani ba" mommy tace.

Sai dare sannan doctor Ahmad ya shigo ya basu sallama tareda nasiha akan ya rage shiga damuwa tunda yasan matsalar hakan..
"I will take care inshallah" Habib yace.

Su duka suka tafi gida, suna zuwa hibban ya taimaka masa ya wuce part ɗinsa.
Wanka yayi ya dade a bathtub sannan ya fito ya kwanta.
Mommy saida ta sake dubo jikin nashi sannan taje ta kwanta.

Sai yanzu jiddah ta tuna da Habib ya fasa wayarta Allah yaso sim card din na wajanta tun dawowar ta ta ɗauke abinta ta boye,, sam bataji dadi ba ta saba kullum sai tayi waya da Kabir kafin ta kwanta gashi yau babu damar yin wayar.
"Allah ya sakamin wlhy" ta faɗa a ranta....


Da sassafe jiddah ta shirya tafiya school, tana fitowa palour ta samu Habib zaune kan kujera.
Mamaki ne ya kamata abinda bata taɓa ganiba kome ya kawo shi da safe haka kuma oho ta faɗa tana taɓe baki.
Kai tsaye upstairs ta wuce yiwa mommy sallama.
Tare suka fito da mommyn har palour, dai dai shigowar hibban.
Mommy ce tace "hibban yau ku jira kuyi breakfast"
"A'a mommy zan iya makara fa saidai na tafi tabi taxi ko napep"
"Gaskiya tafi dan yarinya ta bazata tafi batayi breakfast ba" mommy ta faɗa tana kama hannun jiddah.
Hibban ficewa yayi dama haka yaso dan yau makara zaiyi idan yace saiya kaita..
Dakyar mommy tasa habib yaci wani abu dan bayasan cin abinci koda can balle yanzu daba lpy.
Suna gamawa jiddah ta mike zata fita,.
Habib car key ɗinsa ya dauka sannan ya kalli jiddah yace "ki same ni a mota" ya faɗa yana ficewa.
"Mommy zai iya zuwa kuwa"
"Oho masa muje naji koni zan kaiki"
Tare suka fita itada mommy har wajan motar da yake ciki.
Fitowa yayi yana shafa sajan shi daya kwanta luff.
"Habib zaka iya zuwa kuwa, ka bari mana ta hau napep din"
Da sauri yace "a'a zan iya" dan har zuciyarshi bayasan yaji an ambaci napep ko taxi ɗin nan.
"Shikenan ka kula sosai"
"Ok Mom" yace yana komawa cikin motar.
Zagayowa jiddah tayi ta shiga sannan suka fice daga Compound din..


A mota kuwa jiddah sai raba ido takeyi dan ta saba idan shine yake driving gudu yakeyi sosai.
Ko kallan inda take baiyi ba, saida ya tsaya ya siyo drinks da snacks sannan ya dawo yaci gaba da driving ɗinsa.
A bakin gate ya sauke ta sannan ya dauko ledar ya mika mata baice komai ba.
"Nagode yaya Habib" tace kawai.
Bai jira komaiba yayiwa motar key yabar wajan.
Kai tsaye gidan Sultan ya wuce,, yana shiga yayi Parking sannan ya kira Sultan yace gashi a gidan.

Angelina ta amshe shi hannu biyu² sama sama yake tayasu hirar,,.
"Wanne irin gagarumin taro ka shirya mana ne"
Tsaf Habib ya gane me yake nufi aikuwa ya tsuke fuska "bansaniba ba kaida abin ya dameka saika shirya ai"
Dariya Sultan yayi "lallai yau na yarda bakasan auran, nima na shirya idan zaka koma Russia tare zamu tafi kawai"
Shiru Habib yayi kawai dan ji yayi maganar auran da Sultan yayi masa ta bata masa rai.
Lokaci zuwa lokaci yake duban wrist watch ɗinsa kirar vertex, tun safe har lokacin tashin su jiddah yayi..

Sallama yayi musu sannan ya wuce makarantar.


...."gaskiya jiddah saidai kiyi hakuri da wannan yayan naki mutum kullum ba fara'a" afnan ta faɗa tana dariya.
Harara jiddah tayi mata tace "toshi yaya hibban ɗin aka faɗa miki yanada fara'a ne"?
Bata rai afnan tayi "kinga Malama karki zagarmin miji na ehe" ta faɗa cikin sigar wasa..
Dariya sukayi su duka ukun har khairat dake faman shan sweet ɗinta.
"Ni kuwa jiddah kinjin dadin soyayya da ya Habib ɗin nan kuwa" khairat ta tambaya.
"Bansaniba kedai sha zakin ki yar nan"
Dariya suka sakeyi su duka suna fitowa daga school ɗin.

Zaune yake saman motar, yana jiran fitowar su,.
Jiddah na ganin shi tayi saurin yi musu sallama ta matsa jikin motar.
Ya dade zaune bai ɗago kai ba kuma yasan zuwanta wajan,, jiddah kuwa takaici ne yasa tayi shiru dan tasan yaga zuwanta wajan..

Saida ya daɗe sannan ya sauko ya wuce cikin motar tana biye da shi.
Tana shiga ya figi motar suka bar wajan.....


FIRSTLADY✍🏻
[1/1, 2:24 PM] Aunty Usee: 🌹🌹🌹
*_DR. HABIBULLAH_*
🌹🌹🌹


_By_✍🏻
*_🌹 FIRSTLADY🌹_*


*_Wattpad_*
@Ameenafirstladyy


__________________________

*_🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_*✍🏻
```{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/Kainuwawritersassociation
____________________________


16


Tafiya sukeyi babu wanda yayi magana a cikinsu sai jiddah dake duba littafin ta.
Suna zuwa gida yayi Parking, da sauri ta fice zata shige ciki.
Dakatar da ita tayi yana mata wani kallo dayasa tayi kasa da kanta.
"Saurin na menene haka"
"Babu komai"! Tace kanta na ƙasa.
Bai sake Magana ba ya wuce yabarta ya nufi part ɗinsa.
Tsaki jiddah tayi kasa kasa sannan itama ta nufi nasu part din.
Mommy na zaune palour taga shigowar jiddah.
"Waya dawo dake"?
"Yaya Habib ne"
Shiru mommy tayi cikin zuciyarta kuwa daɗi taji...

Hibban bai samu dawowa da wuri ba hakan yasa su uku kawai sukayi lunch, mommy nagama cin abincin ta ta wuce dakinta dan ta kwanta.
Shima Habib barin palourn yayi cikin dakewar fuska yana fita jiddah ta taɓe baki "kaji dashi kai kaɗai" ta faɗa tana barin palourn itama...


Yanzu kullum Habib ke kaita school kuma ya dauko ta jiddah harta saba da zuwa ɗaukar ta dayake yi saidai har yanzu bata sakin jiki dashi dan sam bata ganin fara'ar shi ko kodan.

Tuni mommy tafara gyarata ita dai jiddah duk abinda mommy ta Bata sha takeyi dan ko tayi gaddama mommy cewa takeyi zata hada ta da Habib aikuwa nan da nan zata shanye shi tass.
Ita kanta jiddah taji sauyi a jikinta saidai yanzu hankalin ta yana kan final exam ɗinsu....

Ranar da sukayi final anyi shagali sosai dan har taro akayi na iyayen yara akaci aka sha tareda bawa yara kyaututtuka daban daban ciki harda jiddah ta samu kyaututtuka har kusan kala huɗu...
Duk da Habib baije wajan ba yaji daɗi sosai saidai bai nuna hakan ba koda mommy ta nuna masa kyaututtukan taɓe baki kawai yayi baice komai ba.

Biki sati Uku kawai ya rage mommy yanzu batada hutu tako ina.
Hibban ma kazar kazar yake yi sosai amma Habib ko a kanshi bai damu ba saima daina wunin gidan yayi ya koma hotel dan samun hutu..

Jiddah kuwa shan gyaran jiki takeyi kamar hauka harta fara gajiya,, kullum da kalar abinda za'ai mata musamman mommy ta dauko masu gyaran jiki,,...

Yauma kamar kullum wajan azhar Habib ya shigo gidan cikin tamfatsetsiyar motar shi yana gama Parking hibban ma ya shigo yayi Parking.
"Yaya Habib sannu"
Baice masa komai ba suka nufi palourn mommy.
Tun a bakin shiga sukaji mommy nawa jiddah faɗa.
"Karki sha kiyi ta zama a wajan ke kullum sai anyi fama dake wajan shan magani kamar karamar yarinya kanki zakiyiwa ai"..
Sallamar su ce tasa mommy yin shiru tana fadin "yauwa aiga maisa ki sha nan yazo"
Jiddah najin haka ta daga maganin kamar zatayi kuka ta shanye tass.
Hibban ne yafara yi mata dariya cikin tsokana "yanzu maganin kikewa wannan yamitsa fuska kamar zakiyi kuka"...
Wani kallo Habib yayi masa mai tattare da gargadi wanda yasa hibban saurin yin shiru ya zauna yana dariya kasa ƙasa..
Habib kuwa ficewa yayi baiyi magana ba dan yasan yanzu ranshi zai iya ɓaci idan yace zai zauna a palourn...


Biki ya matso mommy ta kashe kudi har ba'a magana, jiddah tayi kyau kamar ba itaba dan fatar jikin ta kaɗai ya isa ya tabbatar data sha gyaran jiki.
Sam yanzu Habib bai fiye zuwa gidan ba shiyasa babu wani abu daya sake shiga tsakaninsu...

Yau tun safe Habib ya shigo gidan saidai Baiga alamar jiddah na gidan ba yana gaida mommy ya fice yana faɗin a kawo masa coffee part ɗinsa..
Kusan mintina goma ya ɗauka shiru babu wanda yazo kawo masa.,, Cikeda takaici Habib keta faman tsaki.
Shigowar jiddah kenan daga gidansu afnan tun safe hibban ya kaita dansu tsara abinda suke bukata hira ce tayi daɗi ganin harda khairat yasa jiddah dadewa sai yanzu ta dawo..
Harara mommy tayi mata sannan tace "sai yanzu kika ga damar dawowa"
"I'm sorry momma mun tsara abinda muke so ne nida su khairat"
"Amma kinsan yayanki bazai yadda da wannan tsarin ba ko"
Shiru jiddah tayi tunawa da dan rigimar ta datayi .
"Na manta yace akai masa coffee jeki kaimasa part ɗinsa" mommy tace tana barin palourn.
Gaban jiddah ne ya fadi shikenan tasan saiya ci mata mutunci yanzu,, jiki ba kwari ta nufi kichine ta dauko flaks din ta wuce part ɗinsa.

Ta daɗe a tsaye tana tunanin yadda zasu kaya dashi,, a haka jiki a sanyaye ta tura kofar palourn ta shiga da sallama a bakinta.
Tunda ta shigo Habib ya kureta da ido bakaramin yi masa kyau tayi ba dan wata doguwar riga ce ta shadda a jikinta tayi mata das kamar a jikinta aka dinka.
Ya shagala da kallanta yakasa ɗauke ido daga kanta,, jin shiru yasa jiddah ɗago kanta.
Karaf idanuwan su suka haɗu, tsuke fuska yayi saurin yi tareda tsaki sannan ya kawar da kai gefe.
"Ikon Allah na kama ka kana kallo na kuma kabini da tsaki" jiddah ta faɗa a ranta.
A saman Centre table ta ajiye flask din "ga coffeen Yaya Habib" tace masa cikin sanyin Murya.
Jin Muryar ta ne yasa ya lumshe idanunsa a hankali yadda yaji tayi maganar kamar ba Muryar taba....
Buɗe idanuwan nashi yayi yana wani yamitsa fuska yace ta dauko masa cup a kichine ɗinsa.
Babu musu ta dauko ta ajiye sannan tayi hanyar fita.
"Jiddah..!!!!?
Cak ta tsaya takasa jiyowa dan wani abu taji har cikin zuciyarta yadda ya ambaci sunanta karo na farko a rayuwarta sai taji kamar babu wanda ya iya furta sunanta kamar shi.
A dan tsorace ta juyo jin yayi tsaki,, "na'am yaya Habib"
"Ina kikaje"? Ya jeho mata tambayar.
Cikin in Ina tace "babu inda naje ina ɗaki"..
Fuska a haɗe ya ɗago kai cikin bacin rai baice komaiba.
Ganin irin kallan dayake mata ne yasa tagane gargadi yake mata akan ƙaryar da tayi masa.
"Kayi hakuri yaya Habib wajan afnan naje saboda mu shirya..." Kafin ta karasa taji yace "A haka kika fita"
Bata kawo komaiba tace "eh"
Cikin zafin rai ya taso ganin a yadda ya taso yasa jiddah ficewa da gudu kamar wacce taga dodo.
Wani zazzafan huci ya fitar tareda saurin rike kansa yana zama saman kujerarsa...


Jiddah kuwa dakinta ta shige ta rufo kofa "wlhy na daina zama kana Marina kamar ka samu jaka" ta murguda baki kamar yana ganinta.

Habib kuwa saida ya daɗe a zaune sannan ya tashi ya dauki car key ɗinsa ya nufi wajan mommy.
Yana shiga daidai mommy ta ajiye wayar hannunta "yauwa Habib kaya sun karaso yanzu zan aika driver ya ɗauko"
Taɓe baki yayi duk da baisan kayan me mommy take nufi ba,.
"Lafiya kuwa naga alamar ranka a bace yake" mommy ta tambaye shi..
Shiru yayi na wani lokaci sannan yace "mommy karta sake fita"
Da mamaki ta kalle shi tagane me yake nufi saidai ta waske tace "wa Kenan kake nufi"
Shiru yayi bai bata amsa ba dan baisan me zaice mata ba.
"Naji bazata sake fita ba, amma kasan yanzu dole ne fitar kokuma ka sai mata waya ta dinga maganar ta waya"
Nan ma shiru sannan ya fice batareda yace komai ba.
Kai tsaye motarshi ya shiga ya fice daga gidan.
Yana fita jiddah ta fito palourn.
Kallan mommy tayi tace "laifin me kikayi masa"?
Jiddah ta gane wanda mommy ke nufi hakan yasa ta marairaice murya tareda langabe kai "mommy kawai dan naje gidansu afnan"
"To yace karki sake fita kin jawa kanki".
"Karna sake fita kuma mommy"
"Eh haka yace saiki jira ya dawo saiki tambaye shi karin bayani"...
Kamar tayi kuka haka jiddah taji amma dole ta hakura ta koma ɗakinta...


✍🏻✍🏻✍🏻
[1/1, 2:25 PM] Aunty Usee: 🌹🌹🌹
*_DR. HABIBULLAH_*
🌹🌹🌹


_By_✍🏻
*_🌹Ameena firstlady🌹_*


*_Wattpad_*
@Ameenafirstladyy


*_🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_*🤝🏻


*(Ina ganin sakonnin ku kuma inajin dadi hakan yake karamin Kwarin guiwa I so much love you my Fans Ina yinku irin 💯💯💯 dinnan)*💗💗💗


17


Habib kai tsaye wajan saida waya ya nufa,, yana gama siyan ya biya kudi yabar wajan ya nufi komawa gida har lokacin ransa a dan ɓace yake.

Mommy ya bawa wayar ya fice bai nemi inda take ba,,
Ganin wayar ce yasa jiddah murna harda su tsalle tsallen murna tana komawa daki tasa sim ɗinta ta kira afnan....


Tun daga lokacin basu sake haduwa ba kuma bata sake fita ba kamar yadda yace,, afnan ce da tazo yaji labarin ya hanata fita tsaki tayi "ke dai wlhy sokuwa ce dole ma ya rainaki kuma nan gaba saikin zubar da hawaye akan wannan tsoron nashi da kikeji, garama ki daina jin tsoro dan zaman aure bazai yiyu a haka ba wahala zaki sha" afnan ta karasa maganar cikeda takaici..

"Dama waya faɗa miki zanji dadin zaman auran nashi bayan da kanshi ya furta cewa ya tsaneni baya kaunata niba class ɗinsa bace"..
"To sai me kema ai basan shi kike ba, saiki nuna masa hakan dan kwatowa kanki yanci" afnan tace mata..
Shiru jiddah tayi da alamun Maganganun sun shige,,
Afnan ce ta sake katse mata tunanin "Malama dole fa ki fita dan tare zamu raba invitation card dan bazanyi ni daya ba"
"Shikenan naji sai muyi tare ɗin"
Daga nan suka faɗa wata hirar sai yamma hibban ya maida ta gida...


Jiddah kuwa fitar ta kawai takeyi suna sha'anin biki, dan yanzu 6days ya rage tuni danginta na ƙauye su inna marka da sauran Yan uwa duk sun zo har kawu Audu.
Shagali sosai akeyi koda yaushe gida a cike yake da jama'a,, mommy tayi rawar gani wajan akwatuna dan kowacce dozin aka yi mata kuma oda mommy Tayo musamman har kayan fitar biki da tayiwa jiddan.
Habib kuwa sam baya zuwa gidan saboda hayaniya mutane, koda mommy tayi masa zancan dinner cewa yayi babu inda zaije dan ciwan kai za'a sashi a wajan.
Jiddah bataso hakan ba dan zai barmata abin magana wajan kawayen ta.
Ranar har kuka tayi jin abinda yace mommy data matsan ta masa akan ya daure yaje karshe cewa yayi tayi hakuri da magana dinner tunda ba yanzu zasu tare ba sai bayan ya dawo daga Russia,,, dole suka kyale shi dan sunsan halin shi sarai....

Ɓangaran Habib kuwa sam baisan meyasa har yanzu bayasan yarinyar ba kodan baisan menene soba shiyasa, tabbas bazai ce bayasan yin aure ba dan zuwa yanzu yana bukatar mace a tareda shi lokuta da dama yakan tsinci kanshi a wani yanayi na bukatar mace amma sam baya murna da wannan auran.
Cikin tunanin nasa ne yaji ring din wayarsa dakyar yakai hannu ya daga ganin mommy ce ke kiran..
"Habib meyasa kake haka ne, umarnin nawa ne yazama na banza kome dangin yarinyar nan har sai sun gane wani abu kowa tambayar ina sirikin nasu yakeyi amma kaki zuwa ka gaida su gashi har gobe daurin aure,,, na yarda da cewa ba yanzu zata tare ba sannan na yarda ba saika ke kowanne event ba duk dan hankalin ka ya kwanta amma a duk a banza.." mommy ta karasa faɗa sosai.
Iya mamaki Habib yayi dan yauce rana ta farko da mommy tayi masa faɗa har haka.
Da kyar ya iya motsa bakinsa kamar mai ciwan baki yace "I'm sorry mom zanzo yau inshallahu"
"Karma kazo idan kanasan ganin bacin raina" ta katse wayar batareda ta tsaya jin wani abu ba.
Ya dade a kwance kafin ya tashi ya shiga bathroom din dake cikin dakin,.


"Pls jiddah kije ki karasa rabawa kinga yayanki ne zaizo ,,daga yau fa shikenan kuma ita kadaice ba'a kaiwa ba wayarta kuma bata shiga"
Kallanta jiddah tayi tace "kinsan fa Mommy batasan na fito ba yau,"
"Nasani aiba dadewa zakiyi,, bari ma nasa yaya kabir ya kaiki ai naji shigowar shi"
Kafin jiddah tayi magana afnan ta saurin ficewa daga palourn.
Tana nan tsaye suka shigo tareda Kabir ɗin murmushi sukayi wa juna sannan Kabir yace "amayar gobe ce a waje haka"
Kasa tayi da kanta kawai batace komaiba.
"Shikenan tunda kunyar magana kikeyi, muke na kaiki ɗin kafin ango ya rude Baiga amayar Saba"
Nanma shiru tayi sai afnan ce take ta dariya.

Kai tsaye motar shi suka shiga sannan suka fice daga Compound din..

Fitowar Habib daga wanka kenan ya shirya cikin wani tsadaddan farin yadi mai taushi wanda tsadar shi ta bayyana tun daga kallansa,, gyara sumar kanshi yayi tareda daura Watch ɗinsa sannan ya feshe jikinsa da wani daddan turare.
Bakaramin kyau Habib Yayi ba, car key ɗinsa ya dauka sannan ya fice.
kirar Mercedes Benz ya hau tareda yi mata key ya fice daga hotel din.

Tafiya sukeyi jefi jefi sukeyin hira saidai jiddah bata saki sosai ba, ganin ya gangara ya tsaya ne yasa ta kalle sa.
"Yadai lafiya kuwa" ta tambaya.
"Sorry zan sha mai ne "
"Ok" tace.
Fita yayi daga motar ita kuma ta zuge glass din motar dan ganin gari.

Habib daya tsaya shopping dan kaiwa yan uwan jiddan, fitowar shi kenan ya shiga Mota.
Har zai tayar idanuwan sa suka sauka kan jiddah dake cikin mota.
A hankali ya sauke Glass din motar shi dan tabbatar da zargin shi,tuni idanuwan shi suka sauya launi zuciyarshi tafara tafasa.

Jiddah kuwa kallan Kabir tayi daya shigo yanzu yana faɗin "sorry amarya na makara ko"
Maganar tasa ce tasa ta yin dariya tareda waigar da kanta gefe.
Idanuwanta ne ya sauka kan Habib daya zubo musu ido cikin wani irin kallo, fuskar tashi tayi jajir idanuwan shi sun bayyanar da tsantsan bacin rai.
Da gudu taga ya figi motar shi hakan ya tabbatar mata da bakaramin fushi da zuciyar yayi ba.
A firgice ta waigo cikin tsoro tace "yaya Habib"
"Yana ina" Kabir ya tambaye ta dan yasan wanda zata aura take nufi.
Nuni tayi masa da motarshi datayi musu nisa tana fadin "dan Allah Kabir kabi bayanshi pls karya samu matsala kaga fa gudun dayake yi" ta faɗa Muryar ta na cracking..
Kabir shima bayan Habib yabi saidai ina ko kurarsa basa hangowa yayi nisa.

Gudu yake sosai saidai yadda kanshi ke ciwo zuciyarshi tayi masa nauyi yana dafe da wajan baisan ina yake yiba shidai driving kawai yakeyi,,,,,,
Lokaci zuwa lokaci yake lumshe ido tareda cizan lower lips ɗinsa "meye hadinta dashi meyasa ta fita bayan na hanata" ya faɗa a zuciyarshi tareda sake lumshe idanuwanshi,,,
Daidai zai shiga layinsu wata mota ta bige motar shi mutanen wajan sukayo wajan tareda salati....

Hankalin jiddah yagama tashi a haka suka karaso wajan da mutane suke tsaye.
"Jiddah hawaye ne suka zubo mata,, tareda saurin buɗe motar ta fita.

Habib kuwa tuni ya suma baisan abinda ke faruwa ba,,,, da taimakon Kabir aka sashi a motarsa suka nufi hospital din Dr Ahmad..

Saida aka shiga dashi wani daki sannan jiddah ta kira hibban ta fada masa.
"Whattt kuna ina yanzu""
Cikin murya mai sanyi jiddah ta faɗa masa suna hospital din Ahmad.
Hankalin mommy ya tashi sosai tareda mutanen da suka zo biki saidai mommy da hibban ne kaɗai suka tafi hospital ɗin..

Kusan awa daya sannan aka kaishi dakin hutu, mommy Bata tambayi jiddah komaiba dan hankalin ta a tashe yake..


"Mommy gaskiya Habib yana wasa da lafiyar shi bansan damuwarsa ba saidai ku bari idan ya tashi saiya yi muku bayani" Dr Ahmad ya faɗa yana ci-gaba da basu bayani akan maganar.
"Amma baiji ciwo sosaiba ko"? Mommy ta tambaya.
"Eh babu wani ciwo sosai a hannu ne kawai shima bugawar kashi ne very soon zai dawo nrml"
Mommy da hibban harma jiddah sauke ajiyar zuciya sukayi sannan suka bar office din zuwa dakin da aka kwantar dashi.
Kabir kuwa tuni yabar hospital din ya koma gida,, shima hibban ganin yamma ta gabato yasa ya nufi gida dan tarbar manyan bakin da zasu zo yau.
Da kyar mommy ta lallabi jiddah akan ta koma gida saboda baki idan yaso zuwa dare saita dawo.
Haka jiddah ta tafi cikeda tsoron farkawar Habibullah yadda zata kasance abu daya take tunani bazai wuce yace ya fasa auran ba wanda ita kuma a daɗin ta haka zata so......


😍😍Mush love you my Fans💗💗🤝🏻🤝🏻


Yar mutan garo✍🏻
Ameena firstlady
[1/1, 2:25 PM] Aunty Usee: 🌹🌹🌹
*_DR. HABIBULLAH_*
🌹🌹🌹


_By_✍🏻
*_🌹 Firstlady🌹_*


*_Wattpad_*
@Ameenafirstladyy


_____________________________
*_🌈 KAINUWA WRITERS✍🏻 ASSOCIATION🤝🏻_*
```{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
*https://www.Facebook.com/Kainuwawritersassociation*
_____________________________


18


Jiddah na zuwan gida tayi wanka taci abincinta sannan ta wuce wajan ƴan uwanta dan tayasu hira duk da hankalin ta na wajan Habib..

Zuwa dare gida yagama cika itama shiryawa tayi sannan ta haɗawa Habib coffee Dan tasan zai bukata da zarar ya farfaɗo, tana gamawa hibban ya shigo kichine ɗin.
"Yauwa ki same ni a mota mu wuce" yana gama faɗin haka ya fice.

A mota ta sameshi tana shiga ya tayar suka fice daga Compound din, tunda suka fara tafiya yake waya da Afnan ita kuwa kanta ta waigar window tana kallan gari.


Sai bayan magrib sannan Habib ya farko daga sumar da yayi, da sauri mommy ta Kira Dr Ahmad suka shigo tare lokacin harya cire karin jinin da ake masa ya rufe idanuwan sa.
Shigowar su ce tasa ya dan buɗe ido yana kallan su, allura uku akayi masa sannan Dr Ahmad ya fice yace yanzu zai dawo mommy ta kula da shi.

Habib na jin jiki sosai dan kanshi bakaramin ciwo yake masa ba ga zuciyarshi na zafi ido kawai yake binsu dashi lokaci zuwa lokaci yake rintse idanuwanshi da sukayi masa zafi..
Motar su jiddah na tsayawa ta nufi room tabar hibban a wajan yana wayarsa.
Tura kofar dakin tayi tareda sallama a bakinta,,, mommy ce ta amsa mata tana kallan shigowar ta.
"Kin dawo"
Jiki a sanyaye Jiddah tace "eh mommy ya jikin yayan"
"To gashi nan dai da sauki"
Jiddah bata sake cewa komaiba ta ajiye flask din hannunta ta zauna.
Habib yana jinsu tun shigowar ta saidai tsananin haushin ta tareda zargi zuciyarshi yasa yakasa bude ido balle ya kalleta dan ko ganinta bayasan yi a Yanzu.
Sun dade a haka sannan Dr Ahmad ya shigo yana faɗin.. "mommy a bar sallamar taku sai gobe muga yadda jikin nashi zaiyi".
A hankali Habib ya motsa bakinsa cikin yanayin cuta yace "no I can't sleep here,"!
Duk yadda mommy taso ya bari zuwa safiya ki yayi yace bazai iya bacci a wajan ba dole aka sallame su kuma da kanshi yaje har wajan Mota.
Yadda jiddah taga ko inda take baya kallo ya tabbatar mata tashiga uku wajan shi ala bashi yaga gobe za'a daura auren su.
A haka har suka je gida mommy kadai ke Jero masa sannu jiddah kuwa tunda tace sannu taga irin kallan tsanar da yayi mata tayi shiru bata sake magana ba.
Chapter 2 · 0% Book details