Part ɗin mommy suka sauka saboda yan bikin part guda aka ware musu shiyasa babu yawan hayaniya a Wajan.
Dr Habibullah Part 1 Complete Hausa Novel · about 72 min read
Kai tsaye jiddah dakinta ta wuce,, hibban ma part ɗinsa ya je ya shirya...
Mommy dake zuba masa coffee kallan shi tayi taga yana rike da kansa.
"Habib yadai"
Shiru yayi baice komai ba can yace "Dan Allah mommy Kar a daura auran nan gobe banasan ta ku....."
Kallan zallar bacin rai mommy tayi masa sannan ta ajiye coffeen tabar palourn cikin bacin rai..
"Ohh help me God" Habib ya faɗa yana rintse idanuwanshi,, sannan ya bi bayanta.
Kayan fitar bikin jiddah take linkewa taga shigowar shi yana tafiya a hankali saidai bata da daga kai ta dubeshi ba.
"I'm sorry momma plss"!
Yadda yayi maganar ne yasa ta kalleshi zuciyarta ta karaya.
"Habib narasa meyake damunka jiddah ce bakaso ko kuma auran ne bakaso nasan cutar dake damunka saina fara nema maka magani"
Shiru yayi nan ma dan ya gane me mommy ke nufi.
"Shikenan na fahimci jiddah ce bakaso to wlhy akan maganar nan Habib saidai ka canja mahaifiya ..."
A gigice ya ɗago kai yana kallanta cikin wani iri yanayi wanda yasa kanshi yafara mugun yi masa ciwo yafara magiyar bata hakuri.
Saida ya tabbatar mata bazai sake irin maganar Bama sannan ya tashi zai fice.
"Coffeen fa"? Mommy ta tambaye shi.
Shiru taji yayi hakan yasa tace "jeka jiddah zata kawo maka"!
Ji yayi sam coffeen ma ya fice masa a rai amma babu yadda zaiyi "shikenan mommy" yace yana ficewa.
Yana zuwa ɗakinsa ya shiga wanka ya dade shower na zuba a kansa sannan yayi wanka ya fito yana wani hucin bakin ciki.
"Very soon zata gane kuranta"! Ya faɗa yana kwanciya batareda ya sa kaya ba.
Tunda mommy tace takai masa coffee gabanta ya fadi, hatta je bakin ɗakinsa ta dade a tsaye sai ta tuna shawarar da Afnan ta bata akan ta rage tsoron shi hakan yasa ta aro jarumta ta tura kofar dakin ta shiga.
Yana jin bude ɗakinsa ya tashi yana kallanta cikeda bacin rai,,,
Ganin shi da towel ɗaure a kugunsa yasa jiddah gabanta ya sake faduwa dan sai yau taga cikar haibar shi gaskiya Habib cikakken namiji ne ga faffaɗan ƙirjin shi daya yalwatu da gashi sun kwanta luff,,.
Kallanta tsana Habib yayi mata sannan yayi tsaki a zuciyarshi yace "dole ki tsaya mana tunda kin saba ganin maza haka"
Jiddah kuwa tunda tayi kasa da kanta ko motsi ta kasa ji tayi kamar kasa ta tsage ta shige dan kunya saidai shi taga ko a jikinsa.
"Basai kin nuna kin saba ganin maza a haka ba,,, saiki ajiye ki ficemin a ɗaki" ya faɗa yana kare mata wani mugun kallo.
Har zuciyarta taji haushin abinda ya faɗa kenan yana nufin tana bin maza kome yake nufi.
Dan ta bashi haushi tabe baki tayi tace "ai shiyasa yau ban tsorata ba"..
Mamaki ne ya cika Habib tareda wani baƙin ciki,, cikin fushi yayo kanta ai da gudu ta fice daga ɗakin zuwa part ɗinsu.
Garam ya rufe kofar sa sannan ya kaiwa bango duka tareda fitar da wani huci.
"Me Kenan"? Ya tambayi kanshi wata zuciyar tashi ta bashi amsa da "raini kenan"..
Wani huci ya sakeyi sannan ya zauna yana dafe da kanshi "zaki gane matsayin kowanne namiji very soon" ya faɗa sannan ya nufi wardrobe ɗinsa dan shiryawa.
A tsorace ta shiga palourn,, mommy dake zaune ta kalle ta "lafiya kike wannan gudun cikin dare ko wani abu yayi miki"
"A'a mommy tsoro naji ganin Compound din babu kowa"
Tsaki mommy tayi sannan tace "kedai naga lokacin da zaki girma wlhy" tabar palourn ta nufi upstairs.
Itama jiddah dakinta ta wuce ta kwanta luf "daga yau na daina jin tsoron naka tunda abin haka ne" ta faɗa tana juya kwanciyar ta.
Habib bai samu wani bacci sosaiba har safiya, mommy da kanta tazo duba jikin nasa da safe.
Da sauki yace mata sannan yace zai koma hotel saboda hayaniya mutane daya dameshi.
"Shikenan amma ka tabbatar ka dawo before a daura auran"
Dumm yayi sannan yace"to"
Saida ya biya ya gaida yan uwan jiddan kamar yadda mommy tace sannan ya shiga motar shi yabar gidan ya koma hotel.
Yau jiddah da wuri ta tashi saboda zuwan kawayen ta,, a ranar mommy ta dauko makeover,,,..
Habib kuwa yana zuwa hotel ya kwanta tunani fal zuciyarshi sam shi har Yanzu bai yarda yau zaiyi aure ba,, tsaki yayi sannan ya ciro wayar shi ya kira Sultan.
"Ango kana ina ne"?
Tsaki yayi sannan yace "kafara shirin komawar mu Russia banasan kuma a samu Matsala'
"Shikenan Amma pls kana ina"
Faɗa masa inda yake yayi sannan ya kashe wayar tashi ya kwanta.
Mintina kadan Sultan yazo,, yayi mamakin ganin shi a hotel amma saboda sanin halin abokin nasa yayi shiru bai tambaye shiba.
Sai 2 daurin auran shiyasa tun 1 mommy take kiransa akan lallai ya shirya batasan yabata lokaci.
Sultan ne ya kawo masa kayansa wata bugaggiyar shadda ce gezna wacce ta amsa sunan kuɗin da aka siyeta.
1:30 Habib ya gama shirinsa tsaff.
Masha Allah,, Habibullah bakaramin kyau yayi ba kamar jinsin larabawa ya fito da asalin kyaun sa sak sai zuba ƙamshi yake yi,, sumar kan nan nashi kamar ta larabawa.
Yana cikin daura gold Watch ɗinsa yaji kiran mommy.
Yana dagawa tace "mutane fa su taru me kakeyi har Yanzu"
"I'm sorry momma on my way now" ya faɗa yana ajiye wayar hannunshi...
2:00 dai dai daruruwan jama'a suka shaida daurin auran Dr Habibullah da jiddah sannan aka daura nasu hibban da Afnan,, duk mutane kowa fuskar shi dauke da farin ciki,,,.
Habib kuwa ana gama daurin auran yabar taron mutane dan hayaniyar tayi yawa,,, sai neman shi akayi baya wajan Hibban baiji daɗi ba shida Sultan ganin abokansu sai neman shi sukeyi.
"Habib badai komawa hotel din kayi ba, ga friends sai neman ka sukeyi"
"Eh na koma kuma bana bukatar kowa yasan ina nan" ya katse wayar tashi tareda shan magani ya kwanta...
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
[1/1, 2:25 PM] Aunty Usee: 🌹🌹🌹
*_DR. HABIBULLAH_*
🌹🌹🌹
_By_📚✍🏻
*_🌹 Ameena firstlady🌹_*
*_Wattpad_*
@Ameenafirstladyy
*_🌈 Kainuwa writers association_*
19
A ranar ansha shagali sosai Hibban ji yakeyi kamar yafi kowa farin ciki a Yau..
Sai yamma sannan amare suka fara shirin zuwa dinner,,sosai aka bata lokaci wajan tsara musu tsantsararriyar kwalliya ta gani ta faɗa.
Jiddah kamar ba itaba tayi masifar kyau cikin English weeding gown Wanda mommy Tayo mata odarta daga waje..
Saida suka gama shirin sannan mommy tace "jiddah ki kirashi ki tambaye shi kinsan halin Habib sarai"
Taɓe fuska tayi kamar zatayi kuka tace "mommy bazan daɗe bafa kinga idan banje lokacin nawa shagalin babu mai zuwa"
Kallanta mommy tayi tace "babu ruwana nidai kinsan yanzu dole saida izinin shi zaki fita"
Jiddah batace komaiba ta fice ta nufi ɗakinta.
Yauce rana ta farko da zata kira Habib da wayarta,, bata ma sani ma ko yanada number nata Saidai tasan zata sha wulakanci... Habib kuwa lokacin yana kwance daga shi sai wata farar jallabiya mai shegen kyau,, hankali kwance yake danna wayarsa yana dube duben sa.
Dakyar jiddah ta iya danna number tafara Ring.
Ya daɗe yana kallan number duk baisan number ba hakan yasa harta katse bai daga ba.
Tsaki tayi tana fadin "na hakura dan bazan juri wulakanci ba"
Tunawa tayi ita zata cutu hakan yasa ta sake danna masa kira.
Wani siririn tsaki yayi sannan ya daga wayar yayi shiru.
Tattara nutsuwar tayi sannan tace "yaya Habib zamu dinner"
Tsintar kanshi yayi da yin murmushi sannan yace "to mene nawa aciki"?
Shiru tayi cikeda baƙin ciki wato ma mene nashi a ciki.
Jin tayi shiru yasa Habib yin tsaki zai kashe wayar,, da sauri ta marairaice murya tace "pls Yaya Dan Allah kabarni"
Shiru yayi yana tunanin yadda maza da mata ke zuwa irin wannan wajan cikeda izza yace "ban amince ba" ya faɗa yana katse wayar shi,,,.
Har zuciyar jiddah bataji dadi ba,, tasan babu ta yadda za'ayi ta fita dan mommy bazata barta ba gashi bazata dauki wulakanci ba balle ta sake kiranshi...
Tanaji tana gani motocin daukar su tazo aka tafi aka barta sai dariya suke mata duk irin kwalliyar data ci dole ta hakura..
Daki ta koma tasha kukanta sosai a zuciyarta tana fadin wannan wanne irin aure ne ace dan baza'ayi tarewa yanzu ba shikenan komai ma baza'ayi ba Kenan...
Mommy kuwa batasan banda jiddah aka tafi ba harkan jama'a kawai takeyi...
Murmushin mugunta Habib yayi dan yasan bakaramin bata mata rai yayi ba "kaɗan ma kika gani yarinya" ya faɗa yana cizan lips ɗinsa tareda sakeyin wani shu'umin murmushin....
Hibban ma sam baiso hakan ba daya kira jiddah ta faɗa masa amma babu yanda zaiyi sai hakuri ya bata...
Kashe gari aka kai Afnan gidan hibban dake cikin anguwar wanda ya gama tuntuni basu da wata tazara sosai sun sha nasiha sosai a wajan mommy sannan ta sake yiwa hibban nasiha akan hakuri..
Next day baki kowa ya watse har mutanan ƙauye jiddah kamar tabisu haka taji dan yanzu soyayya suke nuna mata sosai dakyar mommy ta Bata hakurin watarana Habib ya kaita taje da dade musu.....
Haka tabarsu suka tafi aka bari daga ita sai mommy a gidan.
Jiddah ji takeyi kamar ita ɗin ba matar aure bace takasa yarda da hakan shiyasa yau tun safe take bacci abinta dan huta gajiyar biki..
Sai yamma mommy ta Kira Habib tace Lallai yau ya dawo tunda taro ya tashi lafiya.
"To mommy zan dawo" yace kawai.
Sai dare sannan ya shirya ya nufi gidan nasu cikin jibgegiyar motarshi,, yanayin horn mai Gadi ya wangale masa gate ya danna hancin motarsa.
Ya dade a cikin motar kamar bazai fito ba saida ya dau lokaci sannan ya fito sanye da siririn farin glass ɗinsa.
Jiddah na zaune a palour Tasha light makeup tayi kyau sosai kana ganinta kaga amarya.
A hankali ya tura kofar main palourn nasu tareda yin sallama wanda sai mutum ya kasa kunne zai iya ji.
Bataji sallamar tashi ba sai ƙamshin turaren sane ya sanar da ita zuwanshi palourn hakan yasa ta dan ɗago kanta tana satar kallan shi,.
Yayi mata masifar kyau sosai shiyasa takasa ɗauke kanta daga kallansa.
Shima a sace ya kalleta kamar baisan da da mutum a palourn ba yayi hanye upstairs..
Taɓe baki tayi a zuciyarta tace "sarkin izza kamar wani jinin sarauta" ta faɗa yana mayar da hankali kan charting din da takeyi..
A zaune ya samu mommy tana waya da alamar yan uwan jidda ta kira tana musu ya gajiya tunda yaji ta ambaci sunan Inna marka..
Saida tagama sannan ya gaida ta amsa masa sannan ya tashi zai fice..
"Habib"
"Na'am"!!!!
"Idan kayi sallar isha kazo inasan ganinku"
Maimaita zancan yayi a zuciyarshi "ganin mu kuma"
Kamar tasan me yake tunani tace "ina nufin kaida jiddah"!
Da kyar ya iya cewa "to momma" ya fice daga ɗakin nata.
Kamar yadda ya barta a zaune haka ya dawo ya sameta har zai fita yaji tace "a dawo lafiya"..
Dan tsayawa yayi cikeda mamaki saidai ko jiyowa baiyi ba yasa kai ya fice tareda taɓe baki yana faɗin "da alamun wannan ta zata fiye zakewa da yawa"..!! A zuciyarsa.
Kamar yadda mommy tace yanayin sallah ya dawo gida lokacin har sun zauna yin dinner itada jiddah.
Zama shima yayi kujerar kusa da mommy yana fuskantar jiddah dake cin abincinta hankali kwance..
Saida suka gama cin abincin suna zaune a palourn mommy ta kalli Habib da yake zaune fuskar nan kamar bai taɓa dariya ba.
Nasiha tafara yi musu mai ratsa jiki sannan ta sake kallan Habib ɗin.
"Dan Allah Habib ka kula da jiddah dan kamar amana ce a hannun mu saboda haka banasan naji wata matsala ta biyo baya".. sannan ta koma yiwa jiddah nasiha sosai har saida jiddah ta zubar da kwalla tareda sake jin soyayyar mommy har cikin ranta.
Saida mommy ta gama yi musu nasihar sannan tace jiddah tabishi part ɗinsa kafin komawar tashi saita dawo wajanta,,. Gaban jiddah bakaramin faduwa yayi ba dan tasan shikenan tashiga wani hali muddin aka barsu tare ita zata sha wahala.
Habib kuwa zuciyarshi baƙiƙƙirin tayi tareda wani takaici amma saiya make bai nuna ba.
Badan jiddah taso ba dole tabi bayanshi saidai zuciyarta cikeda fargaban abinda zai biyo baya dan ita bazata taɓa yarda wani abu ya shiga tsakaninsu ba tunda ba yanzu zata tare ba.
Har sukaje part ɗinsa bai jiyo ya kalleta ba,, suna shiga ta zauna kan kujerar dake palourn.
Wani wulakantaccen kallo yayi mata sannan ya nufi ɗakinsa cikeda takaici dan shi bai saba kwana da wani a part ɗinsa ba.
"Wane daki zan kwanta" ta tambaye shi tana miƙewa kanta a kasa.
Cak ya tsaya sannan ya juyo yafara takowa inda take,,,,, gab da ita ya tsaya har suna jiyo numfashin juna,
Jikin jiddah har rawa yakeyi dan ta tsorata sosai,,
"Ki kwanta duk a inda kika ga dama saidai karki sake zomin ɗaki na dan naga alamar kinyi sabo da kwana da maza sosai"..
Jiddah shiru tayi batace komaiba sai tarin bakin ciki dayasa takasa yin magana.
Tsaki yayi sannan yabara palourn ya nufi ɗakin sa batareda ya sake jiyowa ba.
Jiki babu Kwari ta nufi ɗakin dake gefen nasa,, bata sha wahalar guarashi ba dan baiyi wani datti ba sannan ta kwanta tareda share hawayen da suka zubo mata na bakin ciki....
Da sassafe tagama shirinta tsaff ta fito zuwa wajan mommy shima dai dai fitowar shi yana waya da Sultan kan maganar tafiyar su.
Hararar ta yayi ya kawar da fuska gefe,,, hartayi hanyar fita yace keeee.
Bata juyo ba saidai ta tsaya a inda take.
Yana karasowa ya wuce ya barta,, bin bayanshi tayi danta gane me yake nufi wato su jera tare..
Mommy taji dadin ganinsu tare sosai saidai ta fahimci babu abinda ya faru tsakaninsu bata so hakan ba dan so tayi da kanshi yafasa tafiya kamar yadda ya kudurta...
*🌹FIRSTLADY CE*✍🏻
[1/1, 2:25 PM] Aunty Usee: 🌹🌹🌹
_*DR. HABIBULLAH*_
ɳɑ
*🌹ᴀᴍʀᴇᴇɴᴀ ғɪʀsᴛʟᴀᴅʏ🌹*
ⓒ ᴀᴍᴇᴇɴᴀ ᴍᴜsᴀ sʜᴜ'ᴀɪʙᴜ
*wαttpαd*
@Ameenafirstladyy
*🌈Kᴀɪɴᴜᴡᴀ ᴡʀɪᴛᴇʀs ᴀssᴏᴄɪᴀᴏɴ*
20
Tare sukayi breakfast sannan Habib ya fice yabar gidan gaba daya..
A ranar hibban da Afnan a gidan suka wuni Gwanin sha'awa jiddah take kallan su abin har birgeta yayi suna kula da junansu sosai.
Sai yamma sannan mommy tace suzo su tafi gida kar dare yayi musu duk da a kusa suke.
Lokacin jiddah da Afnan suna tsohon dakin jiddah suna hira a tsakanin su.
Hibban ne ya shigo yana faɗin "dear tashi mu wuce ita wannan a gida take"! Ya kalli jiddah yana mata dariya.
Hararan wasa jiddah tayi masa tace "haba yaya hibban tun yanzu zaku tafi"
"Eh mana ko so kike wancan mijin naki ya dawo ya fara hade mana fuska.."
"A'a ba haka nake nufi ba" tayi saurin kawar da zancen.
Tare suka fita su duka suka yiwa mommy sallama sannan jiddah ta raka su,,, suna fita motar Habib na shigowa.
Baiyi mamakin ganinta a wajan ba,, yana gama Parking ya fito ba yabo ba fallasa,,.
Har fara tafiya taji yace "meya fito dake yanzu ko baki kula mai Gadi na Compound din ba"?
"Su yaya hibban na rako suka tafi"
"Saboda basusan hanya ba ko"..? Ya sake tambayar ta..
Shiru tayi dan bata da amsar bashi.
Tsaki yayi sannan ya wuce gaba tana bayansa cikeda takaicin wannan isar.
Tare suka shigo palourn mommy na zaune taga shigowar su.
"Ina kaje Habib"?
"Naje wajan Sultan ne akan tafiyar mu"!
"Yaushe ne tafiyar"? Mommy ta sake tambaya.
"Jibi ne inshallahu"
Mommy Bata sake cewa komaiba.
Tashi hibban yayi yana yiwa mommy saida safe ya fice bai jira jiddah ba,,,
Har zata tafi mommy ta tsayar da ita sannan ta nufi ɗakin ta...
Wani turare mai shegen ƙamshi mommy ta shafa mata sannan ta bata ragowar sannan tace ta dauki flask din coffee shi ta tafi mai dashi.
Ita kanta jiddah turaren ya birgeta sosai batayi musu ba ta ɗauka ta fice zuwa nasu part din,,.
Ta daɗe a tsaye bakin kofar shi,, shahada tayi sannan ta tura kofar dakin ta shiga da sallama.
A hankali Habib ya lumshe idanuwanshi jin ƙamshin turaren lokaci guda yaji wani irin yanayi tare dashi,,.
Buɗe idanuwan shi yayi kamar mai jin bacci sannan ya tashi yana kare mata kallo da sexy eyes ɗinsa da suka fara canja launi.
"Yaya Habib ga coffeen..." Kasa karawa tayi ganin yayo kanta fuska a haɗe.
"Ficemin a ɗaki" yace yana nuna mata hanyar fitar.
"Kabari na zuba.."
Wani dogon tsaki yaja wanda baima san ya iya shi ba ganin tana niyyar tasa ya zubar da ajinsa yanzu.
"Bana bukata,, kin saba kai kanki shine yau nima kika kawo kanki gare kina tunanin zan yadda""""! Ya karasa yana sakin wani shu'umin murmushi.
"To ba haka nake ba, Dr Habibullah yafi karfin haɗa jiki dake saboda haka ki ficemin before I open my eyes"
Wasu zafafan hawaye ne suka zubowa jiddah wanda bata taɓa jin irin suba dan yauce rana ta farko da aka taba ci mata mutumci kamar haka.
Jiki babu kwari ta fice ta shiga dakinta ta faɗa saman gado tare da sakin wani marayan kuka.
Habib kuwa tana fita ya rufe ɗakinsa sannan ya koma saman bed ɗinsa yana wani irin huci dan wani zazzaɓi ne ya rufe shi lokaci guda,, saida yasha magani sannan wani bacci ya dauke shi mai daɗi..
Jiddah kuwa dakyar bacci ya sace ta dan bakaramin kuka tayi ba ta dade tana zubar da kukan bakin ciki.
Da asuba ta tashi tayi sallah, sannan ta koma ta kwanta dan tashi tayi da ciwan kai sosai ga fuskar ta tayi ja idanuwan ta nuna alamun tasha kuka shiyasa taki zuwa Wajan mommy Dan Karta gane abinda ya faru..
Habib kuwa bayan yayi sallar asuba shima bacci ya koma sai kusan 11:39 sannan ya nufi part din mommy su gaisa..
Mamaki yagama kama mommy jinsu shiru saidai tana fatan abinda take tunani ne ya faru hakan yasa ta basar bata nemesu ba.
Jin sallamar Habib ne yasa mommy juyowa,, saida ta amsa gaisuwar shi sannan tace "ina jiddan take kuma"?
Cikeda mamaki yace "batazo nan ba"?
"Banasan iskanci Habib ya ina tambayar ka kana mayar min da tambaya idan batada lafiya ne saika sanar min ai"
Shiru yayi dan sai yanzu ya tuna rabuwar su a jiya Allah yasa dai ba wani abu bane ya sameta dan yasan ya shiga Uku wajan mommy..
Jin shiru bai amsa mata bane yasa tace "Habib ba daki daya kuke kwana bane da zakace bakasan halin da take ciki ba"?
Da sauri yace "a'a mommy na tashi naga bata dakin ne nayi tunanin nan tazo, sai yanzu na tuna ashe tace yau ita zata hada mana breakfast inaga tana kichine ne".. ya shararo mata karya wadda baisan ma ya iya ta ba sai yau data kama dole..
(O su Habibullah Allah ya shirya an fara karya kuma🤔🤔)
Kallan shi mommy tayi kamar maisan gano karya yayi sai kuma tace "shikenan naji, saika koma can kuyi tare ai"
"To momma" ya faɗa yana fice tareda sakin wani ajiyar zuciya ganin karyar shi ta amsu..
Kai tsaye motarshi ya hau ya fice daga gidan batareda wani tunani ba.
Sai rana sosai jiddah ta tashi cikin wani irin yanayi ga yunwa ga zazzaɓi gashi bazata iya zuwa wajan mommy ba Dan ko gani batayi sosai tsabar yunwa da zazzabin.
Da kyar ta iya tashi ta shiga bathroom tayi wanka tadan ji kwarin jikinta sannan ta fito palourn tana tafiya dakyar.
Ganin kofar dakin sa a rufe yasa tagane baya nan kenan.
Kichine ɗinsa ta shiga ta dade a tsaye tana tunanin mezata dafa.
Ji tayi komai ya fice mata a rai sai ruwan Lipton kawai tasha ta koma ɗakinta ta kwanta hawaye na sake zubo mata...
Mommy Bata kawo komai a ranta ba tayi tunanin suna tare shiyasa ko kiran jiddah batayi ba, saidai lokaci zuwa lokaci takan yi murmushin irin halin Habib.....
Har bayan la'asar jiddah na kwance da kyar take iya tashi tayi sallah sai yanzu take dana sanin amincewa da auran Habib da tayi,, duk lokacin data tuna kalaman da yayi mata wasu hawaye ne ke zubo mata,, amma tana mamakin abinda yasa mommy bata neme ta kodai yaje ya shirya wa mommy wata maganar matanar ne...
Tana nan kwance zuwa lokacin duk tagama galabaita ga wayarta ta mutu ko mommy ta kirata bazata sameta ba.
Da kyar ta iya tashi ta dauki wayar tasa a caji sannan ta koma ta kwanta.
Mommy abin harya fara bata tsoro wayarta ta dauko ta kira layin jiddah amma switch off, wayar Habib kuma busy, hakan yasa mommy ba shiri ta nufi part ɗinsu danta ga lafiyan jiddan.
Palour babu kowa kuma wajan tsit, dakin Habib ta shiga nan ma babu kowa hakan yasa ta nufi ɗakin kusa dashi.
Kwance ta hango jiddah cikin bargo, da sauri ta karasa tana fadin "jiddah lafiya kuwa."
Ta faɗa tana yaye blanket din.
Cikeda tsoro mommy ta ɗago jikinta taji jikin zafi,,
"Jiddah meya same ki"?
"Zazzabi ne mommy da ciwan kai"
Da sauri mommy tace "Ina Habib din kuma meyasa bai fadamin ba"
"Nima bansan inda yaje ba tun jiya ban sake ganinsa ba"
Mommy Bata sake cewa komaiba ta tashi jiddah ta kaita bathroom sannan ta ta fice kichine ta hadi mata tea mai kauri da jellof ɗin taliya da taji kifi.
Jiddah na fitowa ta shiga sannan mommy ta Bata tea Tasha sosai.
Saida ta tabbatar tea din tsirga mata sannan tasa ta taci abinci sosai..
Cikin kankanin lokaci zazzaɓin da ciwan kan suka gudu jiddah taji dadin jikin saidai babu kwari sosai.
Ran mommy yayi matukar ɓaci danta fahimci babu abinda ya shiga tsakaninsu Ashe Habib karya yayi mata kenan.
Jiddah dake kwance mommy ta kalla cikeda tausayi tace "jiddah zan tambaye ki ki fadamin gaskiya kuma banasan kiji kunya ta"
"To momma"
"Kun taba haɗa daki da Habib"?
Cikeda kunya jiddah tayi ƙasa dakai tare girgiza kai alamar a'a.
Ran mommy ya sake baci Amma Bata nuna ba sai hakuri taba jiddah sannan tace ta kwanta kafin a kira magrib.
Kwanciya tayi mommy ta fice zuwa part ɗinta Rai a bace..
Saida Habib ya gama shirin tafiyar sa gobe sannan yayo hanyar gida bayan yayi sallar magrib a hanya..
mommy saida tayi sallah sannan takira Habib cikin Sa'a ta sameshi.
"Kana ina Habib"?
Yadda yaji Muryar mommy ne yasa gabansa faduwa dan babu shakka yasan tagano karya yayi mata.
"Ina kan hanyar gida"
"Shikenan ina jiran ka" mommy tace tana yanke wayarta..
Ana kiraye kirayen isha ya shigo anguwar tasu,, saida yayi Sallah a masallacin anguwar sannan ya shiga cikin gidan.
Kai tsaye part din mommy ya wuce,, a zaune ya same ta a palour, ita kadai ce babu jiddah yadda ta amsa masa sallamar ne yaji gabansa ya sake faduwa.
Zama yayi sannan yace yayi mata ya gida,, banza tayi dashi bata amsa ba.
Saida suka dauki lokaci sannan mommy ta fara yi masa cikin faɗa faɗa.
"Habib meyasa kayi min karya ɗazu"?
Shiru yayi yakasa cewa komai.
"Dama nasan ai bazaka iya bani amsa ba,, to kasani koma me kayiwa yarinyar nan Allah bazai Barka ba kodan maraicin ta sannan kaida Allah daka kasa sauke hakkin ta dake kanka bazan sake yi maka magana akan haka ba tunda kaima kasan zunubin hakan"..
Mamaki ne da tsabar takaici wato jiddah rashin kunyar tata harya kai ta fadawa mommy bai taɓa kusantarta ba.
"Tashi ka bani wuri shashasha kawai"
Mommy ta faɗa cikeda bacin rai.
Hakuri Habib yabata sosai da kyar ta hakura bayan ya tabbatar mata da zai gyara inshallahu sannan yayi mata sallama ya fice.
Ran Habib yayi matukar ɓaci akan jiddah dan saida yasan ta sannan mommy tafara yi masa faɗa a rayuwarsa kuma ta dalilita dole ya nuna mata kuskuren ta kuma yau zataga karshen rashin kunya kuwa...
Ya faɗa a ransa yana shiga palourn..
Palourn babu kowa hakan yasa ya shiga ɗakinsa ya faɗa wanka.
Ya dade sannan ya fito ya shirya cikeda bacin rai ya nufi ɗakinta.
Jiddah na zaune kan capet ta idar da sallam taji anbugo kofar dakin ta.
A firgice ta ɗago tana kallan Habib daya haɗe fuska idanuwan nan nashi sun kankance cikin bacin rai.
Da sauri ta tashi a tsorace ganin yana matso kusa da Ita.
"Yaya Habib dan Allah kayi hakuri.."
Wani Banzan kallo yayi mata sannan yaja tsaki "ni zaki haɗa da mommy ko wato har kinsan ki faɗa mata magana ko".
Jikin jiddah ne yafara rawa dan sai yanzu ta fahimci abinda yake nufi tuni tafara bashi hakuri wanda shi ko kadan kukanta da hakurin datake bashi kamar Dada tunzura shi takeyi.
"Dan Allah kayi hakuri bazan sake faɗa mata ba"
Taɓe baki yayi sannan ya make kafada alamun bai dameshi ba.
Zata sake magana taji ya fizgo ta cikin mugunta ya haɗe fuskar su waje daya,, "yau zaki sha mamaki na"
Kafin tace wani abu tuni ya haɗe bakinsu waje ɗaya..
Yadda yake aika mata da zafafan kisses ne yasa jiddah tafara hawaye tana neman kwatar kanta.
Shikam Habib hankalin shi gaba daya baya tareda jikinsa dan har rawa jikinsa keyi,,.
Jiddah tun tana hawaye harta fara kuka sosai kamar ranta zai fita saidai ina cikin fitar hayyaci Habib yabi mata ta karfin tsiya wanda yasa jiddah sakin wata kara tareda sumewar azaba...
Sam Habib baisan meya aikata ba dan yana gamawa ya mirgina gefe yana fitar da numfashi ga wani zazzaɓi mai zafi daya rufe shi,,.
Dakyar ya tattaro sauran karfin da yake dashi ya shiga bathroom ɗinta,, jikinsa shima babu kwari ga wani irin yanayi dayake ji a jikin nashi yayi wanka ya fito,, lokacin aka fara kiran sallar asuba...
Sai yanzu Habib ya kalli irin barnar da yayi gabansa ne ya fadi kanshi ya kulle ga zazzaɓi yasa jikinsa duk yayi sanyi,,
Yana cikin kallan kyakkyawar fuskar ta dayake ganin sai yau yayi mata kallan tsaff, gani yayi tana motsa ido da sauri yayi kanta.
A hankali ta buɗe ido tana ganinsa ta saki wata kara mai karfi dayasa Habib saurin toshe kunne tareda dafe bango dan bai taɓa jin kara haka ba.
Kamar taga dodo haka tafara kokarin motsa jiki saidai ina jikinta duk ciwo yake mata ga wata irin azaba da taji ta kasanta wanda yasa ta saurin rintse ido tana cigaba da kukan.
Habib kuwa tunda yaji ihun nan kanshi yafara wani azababben ciwo tareda sara mai da sauri da sauri,,, jan ƙafarsa yayi yana rike dakai ya fice yabar dakin ya shiga ɗakinsa ya faɗa saman bed...
Jiddah kuwa batasan fitar shiba saboda numfashin tane yafara kokarin daukewa dakyar take janyo shi ta samu ta dauki wayarta ta danna layin mommy saidai kafin a ɗaga numfashin ta ya[1/1, 2:25 PM] Aunty Usee: 🌹🌹🌹
*_DR. HABIBULLAH_*
🌹🌹🌹
ɳɑ
*🌹ᴀᴍᴇᴇɴᴀ ғɪʀsᴛʟᴀᴅʏʏ🌹*
ⓒ ᴀᴍᴇᴇɴᴀ ᴍᴜsᴀ sʜᴜ'ᴀɪʙᴜ
*wɑttpɑɗ*
@ᴀmєєnαfírѕtlαdчч
*🌈ᴋᴀɪɴᴜᴡᴀ ᴡʀɪᴛᴇʀs ᴀssᴏᴄɪᴀᴛɪᴏɴ*🤝🏻
21
Mommy na zaune kan capet taji karar wayarta, cikeda mamaki ta janyo wayar tata dake saman bed,,.
Gabanta ne ya fadi ganin number jiddah da sauri ta danna layin ta kira saida harta katse ba'a daga ba,, hakan yasa mommy ta nufi part ɗin nasu cikeda fargaba....
Kai tsaye dakin jiddah mommy na nufa,, tana tura kofar dakin ta saki salati tareda faduwar gaba ganin halin da jiddah take ciki.
Da hanzari ta karasa jikin gadon tana girgiza jiddah saidai ina ko numfashi batayi cikin kidima mommy ta kama jiddah batare da bata lokaci suka fice daga part din..
Da kanta tayi driving zuwa hospital duk garin bai gama waye ba amma sun samu doctors kasancewar private,, emergency room aka wuce da ita kai tsaye tareda Dr Ahmad wanda ya tsayar da mommy yana ta kwantar da hankalin ta...
Cikeda tashin hankali mommy take Kai kawo tarasa wanne tunani Yakamata tayi,,, sai zuwa can sannan ta kira layin hibban.
"Ka sameni a hospital din Dr Ahmad" tana gama faɗin haka ta kashe wayar..
Shima Hibban cikin tashin hankali ya nufo hospital tareda fargaba fal zuciyarshi..
Abu kamar wasa saiga shi likitocin sun dade cikin emergency room din, babu wanda bai tausayawa jiddah ba musamman Dr Ahmad dayasan wacece ita kuma babu shakka yasan aikin Habib ne tunda yanada labarin komai saidai yaji takaici da tausayin ta musamman dayasa yarintar ta.
Kusan 2hrs suka kwashe sannan suka fito daga ɗakin, kallo daya Dr Ahmad yayi musu yaji tausayin su dan kana ganin mommy kasan bata cikin yanayi mai daɗi.
Mommy na ganin shi tayi kanshi "meya faru da ita Ahmad"
"Calm down mommy, ku same ni a office sainayi muku bayani" ya faɗa yana barin Wajan zuwa office ɗinsa.
Zaune sukayi mommy kanta na ƙasa tana jiran bayani daga bakin Dr Ahmad.
Saida yayi gyaran Murya sannan yace "karki damu mommy jiddah zata tashi saidai tana bukatar hutu yanzu dan doguwar suna tayi zata jima bata farfaɗo ba..."
"Meya sameta Kawai nake san ji" mommy ta sake maimaita tambaya.
Shiru ya danyi saboda yadda ya tuna abinda Habib yayi mata "kiyi hakuri mommy nasan jiddah tanada aure sanin haka ne yasa ban nuna damuwata sosaiba,, saidai Habib yabi mata ta karfi ta yadda har saida takai ga munyi mata dinki amma karki damu zata tashi nrml.."
Rintse ido mommy tayi cikin bacin rai da tashin hankali sam kasa magana tayi sai zuciyarta datayi mata zafi.
Dr Ahmad ne ya kalli hibban da yake tsaye fuskar shi ta nuna tsantsan dimuwa yace "hibban zan rubuta maka magunguna sai aje a siya, sannan ba'a bukatar bata abinci mai nauyi sai bayan 1week"..
Daga kai kawai hibban yayi mommy kuwa tashi tayi jiki a sanyaye ta fice zuwa dakin da aka kwantar da jiddah..
Habib sai 11am ya tashi cikin wani irin yanayi na kasala,, a hankali ya buɗe idanuwan shi tareda saurin tashi yana dafe kai da har yanzu yake masa ciwo, cikin hanzari ya shiga dakinta saidai babu alamar ta a dakin har bathroom,, shikenan yasan mommy zuwa Yanzu tasan komai dan yasan waccan yarinyar ta faɗa mata Yanzu.
Cikin dakewar zuciya ya nufi part din mommy bayan ya gyara dakin nata tsaff daya ɓaci har bed din saida ya sauya sannan ya fice,,,.
Cikeda mamaki ya fito daga part din mommy ya nufi gateman yana tambayar koyaga fitarsu.
"Eh yallabai sun fita cikin sauri zuwa asibiti"
Da sauri ya maimaita kalmar asibiti kuma?
"Eh jiddah ce babu lafiya da alamu ma baya cikin hayyacin ta lokacin..."
Bai karasa jin abinda yake cewa ba yabar wajan yana kiran hibban.
Lokacin hibban shigowar shi kenan dakin da jiddah take, mommy Zaune ta zubawa jiddah Ido saidai kana ganinta kasan ranta a matukar bace yake,,.
Cikin taushin Murya hibban yafara lallabar mommy "pls mommy karki sa kanki a damuwa kinfi kowa sanin halin yaya Habib yanada saurin fushi may be ta ɗanyi masa laifi ne shiyasa ya rama ta haka...." Wayar shi ce tayi kara hakan yasa ya ciro ta daga aljihu yana dubawa.
Kallan mommy yayi yaga hankalin ta baya wajan da sauri ya fice yana daga wayar.
"Hello yay..."
"Kuna ina" Habib ya katse shi da tambayar inda suke.
Cikin in Ina yace suna Ahmad City clinic.
Batareda ya sake jin wata magana ba ya kashe kiran,,.
Hibban kuwa shiru yayi duk da baiji dadin abinda yayan nashi yayi ba saidai babu yadda zaiyi ya nuna hakan,,.
Dakin ya koma yace "mommy Afnan zata zo yanzu da abinci".
Dakyar mommy tace "to Allah ya kawota Lafiya, saika je ka taho da ita dan bai kamata tahau motar haya yanzu ba"
"To momma" ya faɗa yana ficewa daga ɗakin..
Yana fita jiddah tafara buɗe idanuwan ta a hankali tareda zubar hawaye Masu zafi,, da sauri mommy tayo kanta tana jera mata sannu.
Itama jiddah tashi tayi niyyar saidai wata irin azaba da taji ta kasanta yasa tayi wata kara tareda saurin komawa ta kwanta tana rinste ido cikin azaba.
"Sannu jiddah bari na kira doctor" mommy tace tana ficewa.
Habib kuwa motarshi ya hau kai tsaye ya nufi hospital din,Parking yayi sannan ya nufi ɗakin da hibban ya faɗa masa kai tsaye..
A hankali ya tura kofar dakin,, ita ƙadaice a dakin idanuwanta a rufe sam batayi tunanin Habib bane tayi tunanin mommy ce ta dawo dakin..
Kyam Habib ya tsaya yana kare mata kallo tun daga bakin kofa har jikin gadon.
Ƙamshin turaren shine yasa jiddah bude fuska a razane tareda kokarin tashi duk irin azabar da take ji.
Shikam Habib kallanta yakeyi cikeda mugunta dan da alamar yayi mata hankali kenan.
Matsowa yayi saitin fuskar ta kamar zaiyi manna mata kiss.
Cikin wani wahalallan kuka jiddah tafara bashi hakuri tana juya fuskar ta gefe.
Murmushin mugunta yayi sannan yasa hannu yana juyo da kanta saitin shi.
"Ina fatan Yanzu kin gane waye Habib"
Shiru tayi tana kokarin kwace kanta saidai bakaramin riko yayiwa kan nata ba.
"Ok Bikiyi hankali ba kenan kokuma kin manta, bari na tuna miki.." ya faɗa yana kokarin yaye bargon dake jikinta.
Wani ihu tayi wanda yasa Habib saurin toshe kunne tareda rinste ido, dai dai shigowar mommy.
Cikin tsananin mamaki take kallansa duk da halin da yake ciki baisa mommy ta raga masa tace "Habib Wannan wanne irin iskanci ne zaka biyo ta har asibiti ka ƙarasa kashe ta wato Burin ka bai cika ba Kenan,, toka ficemin daga gani yanzu kuma jiddah ce tunda bakaso saika sauwake mata ta nemi wanda takeso yake santa"
Dumm yaji maganar duk da baya cikin hayyacin sa sosai saidai yaji Maganar tamkar saukar aradu, a kidime ya tashi yana rintse ido dan wata irin juya yaji na ɗaukar.
Har zaiyi magana mommy ta dakatar dashi tana fadin ya fice mata kafin ransa yayi mummunan ɓaci.
Kallan jiddah yayi wacce ke kuka haikan kamar wacce za'a zarewa rai duk ta fita hayyacin ta.
Tsawar da mommy ta sake daka masa ne yasa yayi saurin ficewa daga ɗakin yana layi tareda dake kanshi,.
Da sauri Dr Ahmad ya karaso yana saurin taro shi ganin zai fadi tareda kiran nurse..
Kai tsaye ya basu umarni dasu dauko gadon marasa lafiya aka tura Habib zuwa dakin gaggawa.
Babu bata lokaci Dr Ahmad yabashi taimakon gaggawa cikin kankanin lokaci Habib ya wuce baccin wahala..
1 dai dai Habib ya bude ido yana kallan dakin tareda tuna kalaman mommy ta kukan da jiddah keyi, wani zafi yaji a zuciyarshi tareda sarawa da kanshi yayi.
Dr Ahmad ne ya shigo dakin yana tambayar ya jin nashi, da sauki kawai yace batareda ya sake cewa komaiba.
"Habib zaka jawa kanka wata matsala wacce ba lallai bane ka iya magance ta,, kasani na sani wannan cutar taka bata bukatar hargitsi ko yaya yake kuma kasani zuciyarka na kamuwa da mummunan ciwo wanda zai iya sanadiyyar rayuwar ka, meyasa bazaka yiwa kanka faɗa ba".
Kiran wayar shine yasa bai yiwa Dr Ahmad magana ba ya daga kiran ganin Sultan ne.
Basu dade suna wayaba ya ajiye yana kallan Dr Ahmad.
"Shikenan zan kiyaye" ya faɗa yana tashi.
Sosai Dr Ahmad daya kasance abokinsa ne ya bashi shawarwari sannan ya fice dan lokaci Flight ɗinsu ya kusa.
Mommy kuwa tunda Habib ya fita ta dawo kan jiddah tana lallashinta dakyar jiddah tayi shiru saidai bata sake magana ba, sai ajiyar zuciya.
"Kiyi hakuri jiddah bazai sake yi miki komaiba saida amincewar ki zaki sake zama dashi.."
"Wlhy mommy Yaya Habib kashe Ni zaiyi indai na sake zama dashi baya sona baya kaunata bazan iya cigaba da zama dashi ba gara na zauna tareda ko auran ma bazan sake yiba" jiddah ta faɗa cikin zafin ciwo.
"Naji jiddah babu mai sake yi miki dole".
Hibban da Afnan ne suka shigo duk sun tausaya mata dan harta dan faɗa na rama, dakyar aka samu tasha tea sannan tasha maganinta.
Bacci ne mai nauyi ya dauke ta batasan inda kanta yakeba.
Cikin karfin hali Habib ya shigo dakin, mommy na ganinsa ta haɗe fuska.
Hibban da Afnan kallansu kawai yayi suka fice daga ɗakin, sannan ya dawo kansa wajan mommy.
"Mommy zan tafi amma..."
"Naji Allah ya kiyaye hanya, bana bukatar wata magana kuma jiddah ce dai bakaso kuma na amince sai ka aiko mata da takardar ta shikenan burinka ya cika"
A hankali ya dago kanshi yace "pls mommy Dan Allah kiyi hakuri"..
Katse ta sakeyi da cewa "na hakura Habib saidai bada wannan maganar ba kuma banaso ka sake furta wata kalma"
Bai sake magana ba ya tashi zai fice sannan ya sake jiyowa yana kallan jiddah dake sauke numfashi a hankali cikin wahala.
Ganin kallan da mommy tayi masa ne yasa yayi saurin ficewa daga ɗakin..
Ko kallan inda su hibban baiyi ba ya wuce ya fita.
Kai tsaye gida ya wuce ya shirya zuciyarshi fes baisan Dalili ba saidai da zarar ya tuna maganar mommy saiyaji gabanshi ya fadi,, a haka ya shirya cikin yadi sky blue Wanda ya amshi fatar jikin shi yayi masifar kyau ga wani annuri dake fita akan fuskar shi wanda bansan dalilin wannan annuri ba.
(Readers ko kun sani?🤔)
A haka ya fice cikin takama da izza kamar bashida wata matsala dan wasai yake jinsa, har yaje airport ya samu Sultan a can.
3 dai dai jirginsu Habibullah ya daga zuwa Russia dan karo karatu a bangaren mata....
Sultan da Angelina suna lure dashi lokaci zuwa lokaci yake murmusawa da alamu murmushin gaske yakeyi yau bana mugunta ba.
Sultan ne ya kalle shi yace "Mutumi na yadai yai naganka kamar kana cikin farin ciki"
Wani tsadaddan murmushi ya sakeyi har kyawawan fararan haƙoransa suka baiyana sannan ya motsa dan karamin bakinsa pink color yace "Sultan nima bansan dalili ba" ya faɗa yana shafa kyakkyawan sajensa tareda sake murmushi tuna irin shagwabar jiddah tareda magiyar da takeyi masa a daran jiya sai kuma a yadda ya baro tana bacci tana sauke numfashi a hankali fuskar nan tata fayau,, a hankali ya lumshe idanuwanshi yana jin wani irin abu a zuciyarsa karo na farko game da jiddah...
Waiting New page✍🏻
ᴀᴍᴇᴇɴᴀ ғɪʀsᴛʟᴀᴅʏ
[1/1, 2:25 PM] Aunty Usee: 🌹🌹🌹
*_DR. HABIBULLAH_*
🌹🌹🌹
nα
*🌹ᴀᴍᴇᴇɴᴀ ғɪʀsᴛʟᴀᴅʏ*🌹
ⓒ ᴀᴍᴇᴇɴᴀ ᴍᴜsᴀ sʜᴜ'ᴀɪʙᴜ
*wɑttpɑɗ*
@ᴀᴍᴇᴇɴᴀғɪʀsᴛʟᴀᴅʏʏ
____________________________
*🌈ᴋᴀɪɴᴜᴡᴀ ᴡʀɪᴛᴇʀs ᴀssᴏᴄɪᴀᴛɪᴏɴ*
```{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/Kainuwawritersassociation
____________________________
( *_Kuyimin afwa kwana biyu zaku jini shiru hakan ya faru ne dalilin uzuri danake dashi zanci gabada typing da zarar komai ya kammala na gode da kulawarku sosai_*)
22
...... jiddah kuwa sai yamma ta tashi duk da har lokacin jikinta babu kwari amma taji dadin jikin sosai.
Mommy ce ta haɗa mata tea mai kauri kamar yadda Dr Ahmad yace da kyar aka samu tasha kaɗan dan bakinta babu taste sosai,,,, hibban da Afnan ma sai yamma mommy tace ya kamata su tafi kar dare yayi suma zuwa safiya za'a sallame su.
Haka suka tafi cikeda tausayinta "gaskiya dear Yaya Habib baiyiwa jiddah adalci ba sam"
Hararan wasa hibban yayiwa Afnan yace "to ba matarsa bace koma me yayi mata ai babu wani abu"
"Duk da haka dai yayi rashin tausayi".
Murmushi kawai hibban yayi dan shima yasan gaskiya ta faɗa yaya Habib baiyi mata adalci ba gashi nan yanzu yaja mata kwanciya a asibiti.
Jiddah kuwa tunda ta farka tasha tea Bata sake magana ba dan batajin zata iya surutu a yanayin da take ciki., Lokaci zuwa lokaci dai takanyi hawayen baƙin ciki sai mommy ce kawai ke bata hakuri, a haka Dr Ahmad ya shigo dakin.
"Mommy zan wuce gida akwai wani abinda kuke buƙata"?
"A'a Ahmad mungode sosai"
Shiru yayi yana maida kansa kan jiddah dake kwance "ki lura wajan motsi da tashi saboda gudun matsala"
Daga kai kawai tayi dan haushi ma ya bata da maganar tasa.
Mommy ce tace shikenan zata kula ai.
Sallama yayi musu sannan ya tafi dan sai zuwa gobe zai sallame su.
Ko kaka jiddah tayi kyakkyawan motsi saita yi kuka sosai mommy kaɗai ke lallashin ta, har dare bata sake cin komaiba.
ʀᴜssɪᴀ:- ᴍᴏsᴄᴏᴡ ᴄɪᴛʏ
Azimut hotel. Fitowar shi Kenan daga hadaddan bathroom ɗinsa Yana tsane ruwan daya kwanta jikin kyakkyawar fatar shi, tsaki yayi yana matsawa jikin wani dan karamin table na glass, tafkekiyar wayarshi ya dauka tareda karawa a kunnen shi.
"Sultan ina san contact din shugaban makarantar yanzu"
Daga can ɓangaran Sultan yace "shikenan zan Turo maka amma kafara duba makarantar idan tayi maka"
"Ok" Kawai yace yana kashe wayarshi.
Kai tsaye wardrobe ya nufa ya shirya cikin ƙananan kaya wanda suka amshe shi tsaff ya feshe jikinsa da turare mai sanyin ƙamshi.
Laptop ɗinsa ya janyo ya yafara binciken makarantar babu bata lokaci yayi apply a RUDN University of Moscow.
Bai tashi ba saida ya kammala komai sannan ya tashi ya kira Sultan yace ya gama komai baya bukatar imel address din.
"Shikenan dama nasan zata birge ka ai, saika dage nima yanzu na dauki hutu ne saboda Angelina batada lafiya"
Habib kashe wayarshi yayi danya gaji dajin fadi ba'a tambaye kaba irin na Sultan.
Kwanciya yayi a saman bed ɗinsa yana lumshe ido, ya dauki lokaci kafin ya saki wani kayataccen murmushi yana tashi tareda lalubo wayarshi.
Wayar mommy ya Kira saida ta kusa katsewa sannan ta daga Muryar ta babu yabo ba fallasa.
Lokacin jiddah na zaune ta jingina da pillow,, tunda taga mommy ta daga waya babu fara'a ta mayar da hankalnta kan mommy.
"Mommy barka da dare" Habib yace.
"Ka sauka lafiya ko"? Mommy bta Tambaye shi.
"Eh mommy alhammdlilh"
"Masha Allah, saika dage da abinda kaje yi"
Shiru yayi baice komai ba, so yake ya tambayi ya jikin jiddah amma yarasa tayaya zaiyi tambayar.
"Akwai wani abu ne kuma"
"Ya jikin nata" ya faɗa batareda yayi wani dogon nazari ba.
"Da sauki,"! Kawai mommy tace.
Sallama yayiwa mommy ganin yadda take bashi amsa yasan har yanzu tana kan bakanta wanda yakejin bazai iya yiyuwa a yanzu yadda yake jinsa.
Jiddah kuwa sarai tasan dawa mommy take waya amma saitayi fuska kawai.
A hankali Habib ya ajiye wayar yana wani yamitsa fuska na takaici, daya sani ma bai kira ba Balle ranshi ya ɓaci.
A haka ya tashi ya fice daga wajan nashi ya shiga Motarshi yaja ta yabar hotel din Gaba ɗaya...
Kamar yadda Dr Ahmad yace da sassafe ya basu sallama yace zai dinga zuwa yana ganin yanayin jikin nata saidai a dage da bata magungunan ta sannan banda ɗaukar abu mai nauyi ko tsalle ko gudu har sai bayan 2weeks,, abinci kuma kar taci mai nauyi sai 1week.
Mommy ce ta amsa sannan hibban ya dauke su ya mayar dasu gida.
Dakinta na da ta koma abinta hankali kwance.
Tun daga lokacin jiddah bata sake damuwa ba musanman dataji mommy na yawan yiwa Habib maganar sakinta.
Sosai takeso ta koma makaranta saidai takasa yiwa mommy Maganar,.
Yau tana dakin mommy Habib ya kira,.
Saida suka gama gaisawa sannan mommy tace "Habib Wai meyasa kake daukan magana ta mara amfani ne, sau nawa zance ka sauwake wa jiddah tayi iddah dan ta samu miji tayi aure wanda yake santa"
Habib da kanshi yayi masa nauyi sosai ya rintse ido yanajin wani zafi a cikinsu, da kyar ya iya motsa bakinsa yace "I'm sorry momma"
"Sorry for what"? Ta Tambaye cikin fada fada.
"Kenan bazaka iya sakin nata ba kome"?
"A'a mommy"
"To Ina jiranka dan bazata ci-gaba da zama haka kawai ba"
Bai sake cin ba mommy harta gama fadan ta ta kashe wayar.
Ji yayi yarasa dalilin da yasa yake jin bazai iya sakin jiddah ba to akan me zai sake ma bayan yasan koya rabu da ita wani zataje ta aura ina never and impossible
Ya faɗa a fili..
Jiddah kuwa yanzu abin yafara damunta kusan 3weeks kenan amma mommy ta hanata fita ko ina gashi tanasan zuwa gidan hibban wajan Aminiyarta sau kusan shida suna zuwa amma mommy ta hanata zuwa yau kuma gashi har khairat zataje susha hirar su sai Kiranta suke suna tazo.
Da karfin guiwa ta shiga dakin mommy,.
"Mommy pls kubarni naje gidan yaya hibban yau"
Shiru mommy tayi mata bata kulata ba, cikin shagwaba jiddah tai aniyar fara kuka dan tasan mommy hakan ce kadai zaisa ta kulata.
Cikin sigar lallashi mommy ta jawo ta jikinta tafara bata hakuri.
"Banida ikon barinki ki fita jiddah saboda har yanzu kin karkashin ikon Habib ne, gashi kwana biyu baya kira saboda nayi masa maganar rabuwar ku, indai kinsan fita saiki kirashi da kanki ki tambaye shi.."
A dan tsorace ta ɗago kai tace "wlhy mommy idan na kira shi nashiga uku"
Tsaki mommy tayi tana barin Wajan "saiki ta zama ai, ashe bakya san Zuwan"... Ta fice daga ɗakin..
Zaune yake daga shi sai singlet fara tas sai trouser, gashin jikin shi kwance luf, wasu takardu kawai yake dubawa saidai hankalin shi sam baya kan takardun yana kan maganar mommy,, Dan tsaki yayi yana tashi cikeda jin haushin kansa "meyasa ma nakasa control ɗin kaina a waccan ranar?" Ya tambayi kanshi tsaki ya sakeyi sannan ya bar palourn zuwa ɗakinsa...
Jiddah kuwa ganin babu sarki sai Allah tasan mommy bazata taɓa barinta ta fitaba, dole ta dauki wayarta ta fara neman layinsa cikeda da tsoron yadda zasuyi dashi, duk yanzu batajin zata dauki wani wulakancin shi tunda ba sake zama zasuyi a matsayin mata da miji ba.
2times tana kira amma babu answer, tsaki tayi tana sake kiran wayar tashi.
Fitowar shi kenan palourn, ya dauki wayar yana kallan numban cikeda tsantsan mamaki.
"Tome ta kira tace min, kodai mommy ce tasa ta"
Katse kiran yayi sannan shiya kirata,.
Jiddah hatta ji haushi sai kuma taga kiran shi.
Tayi mamaki ganin katsewa yayi danya kirata, sannan ta daga dauke da sallama a bakinta.
Dan rintse ido yayi yadda yaji sautin Muryar Tata har cikin zuciyarshi.
Jin bai amsa mata yasa jiddah ta taɓe baki "zan fita ne mommy tace a Kira na sanar maka"? Ta fada kai tsaye.
Yaji haushin yadda tayi masa magana batareda wani tunani ba yace "haka ake tambayar miji fita"!?
Dumm taji kalmar datasa takasa cewa komai cikeda mamaki shaidai wannan ba'a gane gabansa da bayansa kam.
"Idan kin koyo Yadda ake tambayar miji fita saiki kirani" ya katse mata tunanin ta tareda kokarin kashewa.
Da sauri ta dakatar dashi ga mamakin ta saitaji bai kashe ba saidai baice komai ba, "pls Yaya Habib bazan daɗe ba kuma gidan yaya hibban zani fa" yadda tayi maganar har saida tsigar jikin shi ta tashi hakan ya saukar masa da wata irin kasala ya lumshe idanuwanshi a hankali tareda cizan lower lip ɗinsa.
Kallan wayar jiddah tayi a tunanin ta ya kashe ne saidai ga mamakin ta saitaga yana kan layi amsar ce dai bazai bata ba.
"Plss yaya Habib i promise bazan daɗe ba".
Tuni idanuwan shi suka fara sauya yanayi ganin zata iya gano halin dayake ciki ne ta raina shi yasa ya buɗe baki dakyar yace "kije" kawai yace yana katse kiran nata..
Sosai jiddah tayi murna dan bata taba tunanin zasuyi haka dashi ya barta cikin sauki ba "kodan baya nan ne"? Ta tambayi kanta,,, taɓe baki tayi tana fadin ina ruwana ma ni karma yayi tunanin nafara sanshi ne kawai danya barni fita ne. Ta faɗa tana shigewa bathroom..
Mommy kuwa batayi mamakin barinta da Habib yayi ba danta gama gano shi sarai saidai dayake shi ba'a gane masa ne sauya wa yakeyi any time.
Habib kuwa har dare yarasa abinda ke masa daɗi musamman idan ya tuna kasancewar shi da jiddah yanzu ya gama yadda akwai Abinda yakeso game da jiddah to amma menene wannan shine abinda yakasa tantance wa.
Coffee mai zafi ya haɗa yasha sannan ya samu bacci ya dauke shi cikeda mafarki iri iri..
✍🏻✍🏻
[1/1, 2:25 PM] Aunty Usee: 🌹🌹🌹
*_DR. HABIBULLAH_*
🌹🌹🌹
ηα
*🌹ᴀᴍᴇᴇɴᴀ ғɪʀsᴛʟᴀᴅʏ🌹*
ⓒᴀᴍᴇᴇɴᴀ ᴍᴜsᴀ sʜᴜ'ᴀɪʙᴜ
*wɑttpɑɗ*
@ᴀmeenafirstladyy
*🌈ᴋᴀɪɴᴜᴡᴀ ᴡʀɪᴛᴇʀs ᴀssᴏᴄɪᴀᴛɪᴏɴ*
23
...... jiddah kuwa sai yamma sannan ta dawo gida musamman data ga baya nan ba sanin lokacin data dawo zaiyi ba, mommy ce kawai tayi mata fadan kaiwa Yamma da tayi, hakuri taba mommyn sannan mommy tace kyaji dashi idan ya gano kin kai Yamma ai.
"Pls mommy karki faɗa masa"
Taɓe baki mommy tayi tana haurawa sama batareda tacewa jiddah komaiba..
Habib kuwa da sai yamma ya tashi ya danji jikinsa yayi kwari saidai ba nrml yake jinsa ba, kai tsaye wanda ya sakeyi sannan ya fice daga hotel din gaba daya ya nufi shopping..
Yanzu Habib yakan kira mommy lokaci zuwa lokaci saidai baya bari wayar tasu ta dade yake mata sallama ya kashe, saidai ya mayar da hankalinsa kan karatun dayake ka'in da na'in sosai yake jin dadin karatun nasa saidai zuciyarsa koda yaushe takan lissafo masa jiddah a yanayi da lokuta daban daban saidai kawai ya tsanci kanshi dayin murmushi..
Kusan 1month kenan da tafiyar Habib saidai basu sake waya da jiddah ba, duk lokacin da zasuyi waya da mommy tana wajan saidai bata damu da abata su gaisa ba dan yanzu baya gabanta harkar gabanta kawai takeyi wani lokacin har mantawa takeyi da tanada aure,, shikam Habib Dama kawai yakeso ya samu dan ya koma gida duk baisan dalilin da yasa yakesan komawar ba saidai zuciyarshi ta Dada tunzura da zuwa gidan.
Yau jiddah sosai take wa mommy kuka akan makarantar ta duk ta ruda mommy da shagwaba sai faman lallashin ta mommy keyi akan tayi hakuri har Habib ya dawo saitayi karatun nata hankali kwance bayan basa tare amma fafur jiddah taki yarda har su hibban da Afnan suka zo suka tarar da rigimar.
"Kwantar da hankalin ki kanwata Ni zan siyo miki form a wannan satin kinji" hibban ya faɗa yana mata dariya.
Mommy ma Kai tsaye ta amince da zancan kawai sannan tace ita zatayiwa Habib Maganar a yau dan ta san halinshi sarai.
Har yamma su hibban suna gidan, jiddah kuwa ta samu abokiyar hira a hirar tasu ne Afnan ta sanar da ita tana ciki na sati 3,.
"Amma fa karki fadawa mommy" Afnan tace.
Hararan ta jiddah tayi "dalla can meye na kar a faɗa mata bayan dole ta sani"!
"Eh dai naji ta gani amma dai karki faɗa mata da bakin ki"
Tsaki jiddah tayi cikeda takaicin wannan sakarci bayan mommy dole tasan maganar, "to meye ma Abin jin kunya tunda har anyin cikin" jiddah ta sake tambayar Afnan.
Bugun wasa Afnan tayi mata tana dariya "ke jiddah duk kin zama mara kunya tunda yaya Habib ya gama da shafinki".
Murmushi jiddah tayi "waya faɗa miki ya rufe shafina, kuma ku daina ganin laifins..." Kasa ƙarasawa tayi ganin irin kallan da Afnan take mata ta tsanin mamaki.
"Jiddah badai har kin saiya ra'ayi ba keda kike cewa a raba auran" Afnan ta tambaye ta.
Shiru jiddah kawai tayi dan ita kanta batasan dalilin da yasa kwana biyu takejin Habib a ranta ba ga wani irin mafarkai da takeyi tun abinda ya faru tsakaninsu dashi.
Girgiza kai Afnan tayi danta gama gano jiddah kawai shiru tayi bata sake magana ba suka cigaba da hirar su.
Sai dare sannan su hibban suka tafi gida,,,
Mommy kuwa suna tafiya ta dauki wayarta zata kira Habib..
Jiddah sake gefenta ta kalli mommy tace "mommy wazaki Kira"?
Hararan ta mommy tayi tace "yaushe kika fara samin ido ne jiddah, to Habib zan kira akan maganar makarantar ki amma idan kin hakura shikenan"!
"Aaa mommy ya haƙuri"
Batareda mommy tace komai ta danna layinsa.
Lokacin Habib na zaune a haɗaɗɗen palourn shi A.C na Ratsa sassan jikinsa idanuwan shi a rufe kamar mai bacci,, jin karar wayar shine yasa ya dauko wayar tareda karawa a kunnen shi ganin Mommy ce..
A hankali ya gaida ta ta amsa sannan tace "Habib naga bakada niyyar rabuwa da jiddah zan jira har dawowar ka amma yanzu nasa a nema mata makaranta..."?
Shiru yayi baice komai ba harta gama jawabin ta Sannan ya sauke numfashi a hankali.
"Mommy Ina ganin tabar karatun saina dawo sai a dub..
"Ban yarda da wannan maganar ba, Hibban yace zai nema mata tafara hankali kwance kafin ka dawo kuma karka sake ka hanashi neman mata kaji na faɗa maka"!
"To momma," kawai yace.
"Sannan kuma Habib karka manta wlhy idan har ba jiddah ce ta amince da sake zama dakai ba to dole saika rubuta mata sakin ta dan naga alamar kamar kanaso ka nuna ka manta"!
Rintse idanuwanshi yayi zuciyarshi ta dan harba, a hankali ya sake bude idanuwan nashi farare tarr dasu, saidai yakasa cewa komai, dakyar yace "to mommy"
Yanaji ta katse wayar saida ya kusa 10s sannan ya sauke hannun nashi sannan ya tashi ya shige ɗakin sa cikin wani irin yanayi da baisan dalilin shigar shi wannan halin ba.
Jiddah kuwa dake gefe sam bataso mommy tabi masa ta haka ba duk da har zuwa yanzu tana jin zafi da radadin abinda yayi mata a zuciyarta amma duk da haka bai kamata mommy tayi masa faɗa har haka ba.
"Amma mommy bakya ganin yaya Habib zaisa wannan maganar a ransa harya shafi karatun saba"..
Kallanta mommy tayi cikin mamaki "to saime yasa ɗin mana, kedai wlhy Allah ya shirya ki shashasha kawai" mommy tace tana barin palourn.
A daran Habib ya kira hibban ya ja kunnen sa akan ya tabbatar bayan jiddah ta samu admission shi zai dinga kaita kuma ya dauko bai yarda a dauki driver ba.
Amsa masa hibban yayi sannan yayi masa sallama..
Kamar Yadda hibban yace zai samar mata makaranta, a cikin satin ya sama mata gurbin karatu a jami'ar Bayero University, babu bata lokaci tafara zuwa cikeda farin ciki da murna kuma babu laifi makarantar tayi mata sosai tanajin daɗin karatu a ciki.
Kullum hibban ke kaita kuma ya dauko ta, saidai wani lokacin idan aiki yayi masa yawa take hawa napep ta dawo gida batareda sanin Habib ba.
Shima Habibullah yanzu karatun sa yayi nisa sosai kuma yana jin dadin jami'ar sosai ya mayar da hankali kan karatun nasa.
Jiddah ta rike mutuncin ta a matsayin matar aure duk da har yanzu batajin kanta a wacce zata cigaba da zaman aure da Habib ba, saidai takanyi tunanin lokaci zuwa lokaci wani lokacin taji haushin shi ya sake kamata musamman idan ta tuna irin abubuwan da yayi mata na wulakanci,,
Yanzu ta dada wayewa kamar ba itaba tayi kyau ta murje abinta hankali kwance take rayuwarta batada wata matsala ko tunanin data sawa kanta hakan yakara bayyana kwanciyar hankali a tattare da ita wanda yasa fatar ta sauyawa alamun jin dadi da kwanciyar hankali ya ratsa ta..
Habib kuwa yanzu ya tabbatar da yarinyar nan asiri tayi masa Saboda yawan tunanin ta dayake yi a kullum kuma akoda yaushe.
Yauma zaune yake yana Watching TV Sam hankalin shi ba akan tv yake ba jiddah ce kawai a ransa,,, tsaki yayi kasa ƙasa yana jin haushin kanshi "wai Meyasa nake yawan tunanin yarinyar nan"? Ya tambayi kanshi,..dan taɓe baki yayi tareda ta tabbatar wa da kansa "Saboda halin daka baro ta mana"!
Tsaki ya sakeyi sannan ya tashi yana barin palourn nashi...
3Month kenan da tafiyar Habib saidai yanzu gaba daya hankalin sa yayo gida kuma sam lokacin tafiyar tashi batayi ba dole ya sawa zuciyarshi hakuri duk da dama bashi da wani kwakwaran dalili na san Zuwan nashi gidan....
Jiddah kuwa wata uku kenan da Habib ya mayar da ita cikakkiyar mace, tayi kyau takara haske da ita duk kirjinta ya sake bayyana, duk wata boyayyar halittarta ta bayyana musamman hips ɗinta da suka sake fitowa dasu...
Yan kwanakin nan mommy na lure da ita tafiye shegen ciye ciye ga kwadayin kuma bata fiye cin abinci sosai kamar da ba ga bacci yanzu da take yawan yi da shegen san jikin tsiya koda yaushe tana kan cinyar mommy idan tana gida, hankalin mommy ya fara dan tashi duk da bata gama tabbatar da zarginta ba saidai alamomin masu ciki ya gana bayyana ga jiddah,.
Yau ta kasance Sunday, jiddah na gida tana dakinta sai faman bacci takeyi takeyi tun safe ta shiga bata sake fitowa ba..
Saida aka gama lunch sannan mommy ta taso ta suka nufi dining room,.
Mommy na ɓude abincin jiddah ta tashi da gudu ta nufi bathroom din dake cikin dining room din, ta daɗe tana kyalaya amai har saida ta galabaita mommy na rike da ita, saida ta gama sannan mommy ta kamo ta suka fita, dakinta mommy ta kaita sannan tace me takeso taci.
Ruwan Lipton kawai tace mommy ta hado mata tasha sannan bacci ya kwashe ta mommy tabar ɗakin..
Sai yamma ta tashi jikinta duk babu kwari, a palour ta samu mommy Zaune tana zuwa ta kwantar da kanta ka cinyar mommy zata fara shagwaba..
Mommy ce ta katse ta da tambayar "jiddah wata nawa kenan bakiyi menstruation dinki ba"
Shiru jiddah tayi tana nazari, sai kuma ta tashi da sauri tana fadin "3month Kenan Mommy, nashiga uku banda lpy ko?!
Murmushi mommy tayi danta gane jiddah haryanzu da yarinta kanta sannan bata shiga cikin mutane ballantana tasan irin wannan abubuwan..
"A'a kalau kike jiddah, kwantar da hankalin ki may be wahalar karatun da kikeyi ne yasa bakiyi ba har yanzu"!
Wata ajiyar zuciya jiddah ta saki tareda murmushin jin dadi danta yadda da maganar mommyn harga Allah.
Mommy kuwa yanzu ta tabbatar da zargin da takeyi na jiddah na ɗauke da cikin Habib harna wata uku tunda tafiyar shi da kwanciyar su a asibiti wata biyu kenan.
Wani farin ciki ne ya mamaye zuciyar mommy saidai bata nunawa jiddah ba dan tasan halin jiddah sarai yanzu saita sa mata rigima wadda batasan yadda zatayi da ita ba Gara ta rufe ta har abin ya bayyana saita san yadda zatayi da ita.
"Mommy yunwa nake ji" jiddah ta faɗa ta a wani yamitsa fuska.
"Me zakici to"? Mommy ta Tambaye ta.
"Sinasir zanci amma mara zafi nakeso a basshi saiya huce" ta faɗa tana dada wani yamitsa fuska.
Ga mamakin ta saitaga mommy batayi mata mita ba kamar yadda ta saba kullum idan tafara ciye ciyenta da tsirfa sai mommy tayi ta mata mita wai tafiye shirme amma yau sai taga mommy batace komaiba saima murmushi da tayi ta nufi kitchen da alamu da kanta ma zata hada mata.
Bata kawo komai a ranta ba ta kwanta a saman kujera tafara game a wayarta hankali kwance....
*ᴀᴍᴇᴇɴᴀ ᴍᴜsᴀ*
🌹ғɪʀsᴛʟᴀᴅʏ🌹✍🏻
[1/1, 2:25 PM] Aunty Usee: 🌹🌹🌹
*_DR. HABIBULLAH_*
🌹🌹🌹
вч
*🌹fírѕt lαdч🌹*
*ⓒ* ᴀᴍᴇᴇɴᴀ ᴍᴜsᴀ sʜᴜ'ᴀɪʙᴜ
*wαttpαd*
@Ameenafirstladyy
*🌈 ᴋᴀɪɴᴜᴡᴀ ᴡʀɪᴛᴇʀs ᴀssᴏᴄɪᴀᴛɪᴏɴ*
*(This page is yours, my dear sweet sis Maman Hajiya kiyi yadda kikeso dashi naki ne na mallaka miki)*🌹🌹
24
Mommy da kanta ta yi aikin ta gama sannan ta dawo palourn gun jiddah wacce har ta fara lumshe ido zatayi bacci,, da sauri ta tashi da fara'a tana fadin Sannu mommy meyasa baki kirani na tayaki ba.
Hararan mommy tayi tace "ai kinaji ina aikin ai shine kika kwanta harma zakiyi bacci"!
"Ayya mommy wlhy bansan meyasa nake yawan jin bacci ba yanzu ma duk jikina a mace yake wlhy" ya faɗa kamar zatayi kuka.
"Shikenan naji saiki tashi kici aiya huce ɗin"
Tashi tayi ta nufi dining room din saidai kadan taci taji duk batasan ci haka ta dawo palour suka ci gaba da hirar su itada mommy..
Da sassafe hibban yazo da hanzari ta shirya dan sai faman azalzalar ta yakeyi tayi sauri, ko breakfast batayi ba haka suka tafi, a mota sai faman zuba mita takewa hibban wai duk yasa jikinta ya gaji.
Taɓe baki yayi cikin salan tsokana yace "saika ce wata mai ciki, shikenan daga nasa kinyi sauri dan karmu makara shine zakice wani duk kin gaji" ya faɗa bai kalli inda take ba.
"Allah kuwa yaya hibban kwana biyu nima bansan meyasa nake yawan jin gajiya da bacci ba kullum sai mommy tayimin faɗa wai yanzu na fiye san jiki da yawa"!
Dan murmushi yayi yace "to kodai yaya Habib ya jefa kwallansa a raga ne"
Jiddah bata gane meyake nufi ba shiyasa batace komaiba saima cewa ta kumayi "nima wannan halin yafara takura min saboda banasan ya shafi karatuna"
Murmushi hibban ya sakeyi wannan karan yace "kar dai kicemin bakisan kina dauke da cikin yayana ba saboda nasan ɓangaran doctor kike karanta ai" duk da
Damm taji gabanta ya fadi me hakan yake nufi kenan hibban yana nufin ciki gareta,,,.
Innalillahi ta fara maimaitawa a zuciyarta shikenan tashiga uku idan kuwa hakan ya tabbata ta shiga Uku, to amma meyasa batayi tunanin hakan ba sai yanzu...
Jin tayi shiru yasa hibban kallan gefenta yace "yadai jiddah akwai damuwa ne"?
Nodding kanta tayi dan tazama speechless bazata iya cewa komai ba.
Har suka zo school din babu wanda ya sake magana, jiki a sanyaye ta fice ko sallama batayi masa ba shika murmushi kawai yayi danya fahimci maganar dayayi mata ce tasa duk tayi weak da ita,, murmushi ya sakeyi danshi tsokanar ta yayi har zuciyarshi bawai yasan komai bane,, haka ya tafi yana mata dariya a zuciyarsa..
Jiddah kuwa hankalin ta a tashe yake dan yanzu tagama tabbatar da maganar hibban duk sai yanzu take tunanin alamomin masu ciki duk sun gama bayyana akanta.
Sam hankalin ta yakasa kwantawa dole lokacin tashi baiyi yiba ta nufi hospital, sosai doctor ya gwadata sannan ya tabbatar mata da tanada ciki bayan urine test da akayi mata.
A firgice ta zaro idanuwanta kamar tasa ihu tace "doctor amm..."
"Kinga nasan me zakice, saboda haka kije wani Asibitin a sake dubawa amma duk result din daya ne indai dubawar za'a yi so karma ki batawa kanki time Gara kawai ki yarda"
Wani zazzaɓi ne ya rufe ta a take a wajan haka ta sallami doctor ta fice, kai tsaye gida ta nufa tana shiga palourn ta fashe da wani irin kuka.
Da sauri mommy ta riƙo ta hankali a tashe tana tambayar ta lpy.
Bata amsa ba sai kuka da takeyi kamar ranta zai fita, saida tagaji dan kanta tayi shiru sannan ta mikawa mommy takardar dake hannun ta.
Mommy bataji komaiba Dan dama tasan hakan amma a fili saita nuna tashin hankalin ta fili..
"Wlhy mommy banasan cikin nan, yaya Habib basona yake ba tayaya zaiso abinda ke ciki na mommy nashiga uku dan Allah a zubar da cikin nan kafin yaya Habib ya sani.." takarasa cikin kuka sosai.
Da sauri mommy ta rufe mata baki tana girgiza mata kai, nasiha sosai mommy tayi mata sannan tace "kema aiba sanshi kikeba nasani saboda haka na bari ya dawo saiya sake ki ki nemai wanda kikeso yake sanki, amma banaso nakara jin kalmar zubar da cikin nan".
Jin mommy kawai takeyi amma sam bazata iya barin wannan mummunan abu ya faru ba wai ta haife cikin Habib bayan irin tsanar dayake nuna mata inaga ta haihu dashi "mommy karatu na fa" ta sake tambaya.
"Ciki ai baya hana karatu jiddah ki kwantar da hankalin ki" mommy ta Bata amsa.
Dakinta kawai ta nufa saidai hankalin ta still a tashe yake dan ta tabbatar wulakanci ne zai biyo baya idan har Habib ya sani...
Cikin sati ɗaya kowa yasan jiddah nada ciki musamman kawayen ta da hibban duk sunyi farin ciki saidai yanzu bakaramin wahalar cikin take shaba sau biyu tana kwanciya a asibiti duk ta rame harda tunani ne yasa duk ta zange gashi ba komai take iya ci ba.
Mommy na tausaya mata amma a haka take zuwa makaranta kawayen ta na school suyi tayi mata dariya..
Wata cikin hudu kenan saidai bai nuna ba saboda jikin jiddah ga tsayi gata babu kiba saidai kana ganinta kasan tanada ciki saboda yadda takara kyau fatar ta murje sai sheki takeyi,,..
Yau mommy ta yanke fadawa Habib duk tasan ba lallai ne su kwashe ta kalau ba tunda tasan halin shi sarai saidai dole zata faɗa masa dan ya sani koma menene saidai yayi amma dole ya sani..
Sai dare sannan mommy ta kirashi lokacin yana kwance da wayarshi a hannun shi kiran mommy ya shigo.
Gabansa ne fadi dan yasan kiran mommy maganar ɗaya ce bata wuce sakin jiddah zatace ba shikam yanzu duk da yanajin jiddah a zuciyarshi bayajin zai dauki damuwa akan maganar sakin ta..
Da sallama ya daga ta amsa masa sannan ta fara sanar dashi maganar cikin jiddah..
Bazaka iya tantance irin yanayin da Habib yake ciki ba saidai za'a iya gane tsantsan farin ciki wanda har saida yasa Habib sakin wani kayataccen murmushi har mommy ta jiyo..
Murmushi itama tayi cikeda da jin dadi yadda ya amshi maganar.
"Mommy to akwai wani abu ne ko dole saina dawo" ya faɗa cikin zumudi.
"A'a Habib saidai ita jiddan tana shan wahalar cikin sosai amma komai yana tafiya dai dai ka zauna kayi karatun ka kawai,"
Shiru yayi dan farin ciki ya hanashi sake yin magana,.
Sallama mommy tayi masa sannan ta kashe wayan nata..
A ranar Habib kowa ya ganshi yasan yana cikin farin ciki duk mutum ne shi mara nuna condition dinsa saidai yau kowa ya fahimce sa musamman abokan zaman sa dake cikin hotel din wadanda yake mu amalla dasu..
Cikin ikon Allah jarabawar su ta fita suka fara kagara yayi su gama saboda kawai ya koma yaga jiddansa da dansa ko yarsa saidai bai taba kiranta ba saidai ya kira mommy yaji yadda take..
Abin duniya ya ishi jiddah kullum sai tayi kuka sosai saidai Mommy tayi ta Bata baki da hakuri saidai bata sauraran nasihar mommy saboda yanzu haushin cikin kanshi take yadda ya hanata rawan gaban hantsi abinci ma ba sosai takeci ba duk a takure take jinta,,, tuni tagama yanke shawarata a ranta dan bazata iya daukan wannan wulakancin daga Habib ba sannan tanaso tayi karatu yadda ya kamata saboda yau ta shirya tsaf dan tafiya makaranta,.
Hibban da yazo daukar ta tace ya tafi zata tafi da kanta saboda zata biya gidan kawarta su tafi tare..
Haka hibban ya tafi batareda ita ba, ita kuwa tana gama shirinta tayiwa mommy sallama ta taci ta tare me napep,,, kai tsaye wani private hospital da wata kawarta (Amra) tayi mata kwatance ta nufa taci Sa'a tana zuwa aka tabbatar mata da likitan da take nema yana nan yazo babu bata lokaci ta nufi office din Nasa...
*_pls manage da wannan_*👈
ɪɴᴀ ᴊɪɴ ᴅᴀᴅ ɪɴ ᴄᴏᴍᴍᴇɴᴛ ᴅɪɴᴋᴜ sᴏsᴀɪ ᴋᴜᴍᴀ ɪɴᴀ sᴀɴᴇ ᴅᴀᴋᴜ ᴀʟʟᴀʜ ʏᴀʙᴀʀ ᴋᴀᴜɴᴀ ɪɴᴀ ᴀʟғᴀʜᴀʀɪ ᴅᴀᴋᴜ,, ᴍᴜᴄʜ ʟᴏᴠᴇ ʏᴏᴜ ❤❤❤
*ᴀᴍᴇᴇɴᴀ ғɪʀsᴛ ʟᴀᴅʏ*✍🏻
[1/1, 2:25 PM] Aunty Usee: 🌹🌹🌹
*_DR. HABIBULLAH_*
🌹🌹🌹
вч
*🌹fírѕt lαdч🌹*
*ⓒ* ᴀᴍᴇᴇɴᴀ ᴍᴜsᴀ sʜᴜ'ᴀɪʙᴜ
*wαttpαd*
@Ameenafirstladyy
25
.....Zaune take gaban doctor bayan ya gama koro mata bayanin yanayin yadda abin yake, sannan ta nisa tana kallan dan dattijon wanda jin dadi ya ratsa shi da alamu..
"Pls nidai doctor koma yane ina so a cire shi"!
"Gaskiya hajiya akwai haɗari babba saboda cikin ya fara kwari za'a iya samun matsala babba inaga kawai ki hakura" ya karasa maganar yana kallan face ɗinta.
Cikin yanayin damuwa tace "Yanzu babu yadda za'a yi kenan"!
Make kafada docton yayi sannan yace "akwai mana idan kikace kinaso ayi kin amince zaki dauki kowanne irin matsala idan ta biyo baya"!
Da sauri tace eh doctor ayi inshallah babu wata matsala da za'a samu by God grace..
"Shikenan ki dawo next week zanyi Miki allura tareda magani wanda zaki sha"
"Ok thank you doctor" tace tana tashi bayan ya faɗa mata payment din...
Jiddah cikeda farin ciki ta koma gida hankali kwance babu wanda ta faɗawa saidai mommy ta lura ta dan rage damuwa kwana biyu..
*Russia*
Sultan ne dake gefe a zaune cikeda mamaki yake kallan Habib wanda yake hada kaya cikin nutsuwa fuskar tashi wasai,, "wai man da gaske kake yi tafiya zakayi"!
Ɗago eye ball dinsa yayi ya kalli Sultan batareda yace komai ba, saida ya gama abinda yake tsaf sannan ya zauna ya fuskanci Sultan ɗin da mamaki ya gama kamashi..
"Sultan bazaka gane yadda nake ji a zuciya taba, Saboda haka dole na koma na nawa matata da yarona kulawa ta.."
"Amma karatun naka fa"
Kallan Sultan ya sakeyi na tsawon wasu sakanni kamar mai tuna wani abu, sannan yayi ajiyar zuciya yace "nima bansani ba"
"Kamar ya baka sani ba kana nufin bazaka dawo ba"?
Cikin ƙosawa da tambayoyin da Sultan yake masa ya danyi tsaki yace "banida tabbacin zan dawo ko a'a, koda na dawo ma zan karasa makaranta ta kamar yadda na fara"
Jinjina kai Sultan yayi dan yasan tsarin makarantar da Habib keyi ba irin sauran Makarantun gida Nigeria bane shiyasa yakesan ya tafi dan yasan bashida wata matsala ta ɓangaran karatun nashi..
"Shikenan yaushe zakayi tafiyar"?
"Next week inshallah"
"Amma shine ka hada kaya tun yau" Sultan ya faɗa yana dariya tsokana.
Shiru Habib yayi dan ya gaji da ba Sultan amsa kuma yasan ko zasu kwana bazai gaji da tambayar shi abubuwa ba.
Sultan ne yaci gaba da surutun shi saidai sam Habib ba kula shi yake ba, cikin jin haushi Sultan ya tashi yana faɗin "nifa kaga abin dayake hadani dakai, kaga nina tafi wajan matata muyi hirar" Sultan ya faɗa yana ficewa..
"Mata"? Habib ya maimaita kamar baisan me kalmar take nufi ba,,,
Wani murmushi yayi tareda lumshe sexy eyes ɗinsa Sannan ya lashi lips ɗinsa. "Ohhh next week come quickly"!!! Ya faɗa yana daɗa lumshe ido,,,,,,
"Jiddah lunch is ready, tashi muje kici abinci" mommy ta faɗa tana kallan jiddah dake cin biscuit tun ɗazu.
Yamitsa fuska ta ɗanyi "a'a mommy I'm full"
"Da kika ci me"? Mommy ta Tambaye cikin nuna kulawa.
"Biscuit"
"Banasan shashanci tashi ki wuce muje kar ranki ya ɓaci"
Dariya jiddah tayi tana tashi da sauri ta nufi dining room.
"Waike jiddah ko nauyin jikin ki bakyaji ne, bana hanaki irin wannan tashin ba.."!
Jiddah da har takai bakin shiga ta tsaya tana langabe kai "sorry momma bazan sake ba"
"Kima sake mana"..
Tare suka zauna saidai jiddah takasa taba komai a wajan sai mommy ce tayi saving ɗinta cikeda kulawa sannan ta Turo mata plate din abinci"
Jiddah kamar tayi kuka dan tasan kotaci ma ba zama zaiyi ba,, kallanta mommy tayi tace "eat Mana"
"Allah mommy zuciyata ma harta fara tashi sam banasan wannan abincin"
"Shikenan me kikeso sai a dafa miki"
"A'a mommy bari na gwada cin wannan ɗin""
A hankali ta fara ci saidai loman ta uku ta tashi da dan gudunta ta nufi bathroom din wajan,,
Cikeda tausayinta mommy suka koma palour, dan itama mommyn har abincin ya fita a kanta saboda bakaramin so mommy kewa jiddah ba shiyasa ko zazzaɓi jiddah keyi hankali mommy tashi yake sosai ballantana yanzu da ko abincin kirki bata iya ci duk ta dan rame..
Hawaye ne suka zubowa jiddah masu zafi da tuna irin tsanar da Habib yayi mata harta kai yabi mata ta karfi amma sai gashi dalilin hakan tana dauke da cikin shi,..
Ɗagota daga kan cinyarta mommy tayi tana share mata hawayen, "jiddah banaso naga kina kuka kin sani, yanzu kuma kukan na mene bayan kinsan kowacce mai ciki hakuri takeyi ko kinaso hankalina ya tashi ne"
Girgiza kai tayi tana dada zubar da hawaye,, "a'a mommy banaso hankalin ki ya tashi, saidai ina tsoron yaya Habib mommy baya Sona tayaya zai so abinda ke cikina ki duba fa irin abubuwan da tayimin kafin barinshi kasar nan, nasan kashe nine kawai bazaiyi ba idan yaji wannan maganar"
Da sauri mommy ta girgiza mata kai "a'a waya faɗa miki Habib yaji dadin Wannan maganar sosai ma kuwa saidai yace ranki zai ɓaci idan bakyacin wani abin kirki"!
Dan murmushi tayi kawai danta nunawa mommy ta yarda amma har zuciyarta tasan mommy kawai faɗa tayi dan karta tayar mata da hankali.
Tayaya ma zata yarda bayan tasan waye Habibullah mutum mai san zuciyarshi da mugunta da wulakanci iri iri...
Suna nan zaune har bacci ya dauke jiddah sannan mommy ta gyara mata kwanciyarta..
Yanzu jiddah tagama Shirin komai kuma ko mommy Bata faɗawa ba, school kuwa yanzu ko fashi batayi kullum saita je,..
Habib da Afnan kuwa sai tattalin nasu cikin sukeyi Gwanin sha'awa haka rayuwar su take tafiya,,.
Next week
Jibi ne takama jiddah zata koma hospital Kamar yadda doctor yace mata shiyasa tun yau ta tsarawa kanta yadda zataje batareda kowa ya sani ba danta kudurta a ranta dole ma ta rabu da cikin ko zata rasa Rayuwar ta saita zubar data fuskanci wulakancin Habib..
......... ........
Habib kuwa ya gama shirin tafiyar shi tsaff yau, sai dare sannan ya kira mommy Wanda yake da tabbacin bata tareda jiddah saboda yasan Nigeria yanzu dare ne sosai..
Cikin alamun bacci Mommy ta daga Kiran ganin Habib ne batayi wani mamaki ba tunda tasan halin shi,, shi juyayyan mutum ne..
"Lafiya kuwa Habib"? Mommy ta jefa masa tambaya bayan ta amsa sallamar shi.
"I'm sorry momma, gobe zan dawo inshallah that's why I called you"
"Cikin mamaki mommy tace gobe kuma Habib"?
"Yes mommy pls don't no"
"Shikenan wanne lokaci zaka sauka"
"By 6pm Flight dinmu zai sauka"
"Shikenan Allah ya kaimu"
Ameen yace tareda katse wayar tashi..
Suna gama wayar mommy taci gaba da baccin ta, koda safe har jiddah ta fita school mommy Bata fito ba shiyasa jiddah batasan zancan ba,..
Mommy na saukowa down stairs ta Kira Hibban ta sanar masa da dawowar Habib saboda haka ya kawo masu gyara gidan tunda ka'idar Habib dole sai an sauya komai na part ɗinsa kafin ya dawo..
Ba bata lokaci hibban yazo da ma'aikata suka fara aikin su cikin kankanin lokaci...
Sai 3pm jiddah ta dawo duk a gajiye, Bata kula da masu aikin ba ta shiga ga palour tana cire mayafinta.
"Wash mommy I'm tired"
"Sannu da hanya"
Kallan mommy tayi da mamaki ganin an sauya musu tsarin palourn nasu.
"Mommy badai kece kikayi wannan aikin ba"
Murmushi mommy tayi sannan tace "baki kula da masu aiki bane, yau da yamma Flight dinsu Habib zai sauka kinsan halin shi da tsafta bayasan ya dawo ya samu komai yadda ya barshi"
Tunda mommy tafara Magana gaban jiddah yayi mummunan faduwa cikinta ya hatsina shikenan tashiga uku gashi gobe ne sukayi da doctor zataje Yaya kenan..
"Yadai jiddah, na faɗa miki wlhy wannan shegen tsoron naki shine yasa Habib yake dada ganin kamar bakida gaskiya akan komai"
Murmushi jiddah ta ƙaƙalo sannan tace "to momma zan kiyaye barina shiga na watsa ruwa" bata jira amsar mommy ba ta wuce ciki da sauri..
Tana rufi kofar dakin nata ta jingina tareda sakin wani ajiyar zuciya, "bazan taɓa fasa abinda nayi niyya ba" ta faɗa tana karasawa jikin bed ɗinta..
ғᴏʟʟᴏᴡ ᴏɴ ᴡᴀᴛᴛᴘᴀᴅ ᴘʟs
ᴍᴏʀᴇ ᴄᴏᴍᴍᴇɴᴛs ᴍᴏʀᴇ ᴛʏᴘɪɴɢ✍🏻
ᴛᴀᴋᴜ ᴄᴇ
*ᶠᴵᴿˢᵀ ᴸᴬᴰᵞ*🌹✍🏻
[1/1, 2:25 PM] Aunty Usee: 🌹🌹🌹
*_DR. HABIBULLAH_*
🌹🌹🌹
вч
*🌹fírѕt lαdч🌹*
*ⓒ* ᴀᴍᴇᴇɴᴀ ᴍᴜsᴀ sʜᴜ'ᴀɪʙᴜ
*wαttpαd*
@Ameenafirstladyy
( *_wannan page din gaba daya sadaukarwa ne gareku sweets dears_*
_Sha'awanat Auwal Ƴar mutan garo_
_Nusee na'ala_
_Maman Hajiya_
_Ruky gabari_
_Pretty 1_
_Pretty 2_
_My sweet sis Hussaina ibadan_
*_so much love you_*🌹🌹🌹
26
.....kai tsaye wanka jiddah ta shiga ta sheka wankan ta ta fito ɗaure da towel, tsaf ta shirya cikin riga da skirt na atamfa Wanda ya amshi jikinta kallan kanta tayi a mirror sannan ta kalli cikinta, duk sai taji jikinta yayi sanyi sam ita wannan cikin duk lokacin data tuna da dashi saitaji haushin kanta da shi kanshi cikin.
Tsaki ta ɗanyi sannan ta dauki mayafinta ta fito palour..
Tana shigowa palourn taji daddan ƙamshim abincin da mommy keyi duk ya cika palourn,, kitchen din ta shiga tana fadin "mommy yau gidan duk ya cika da ƙamshi"
Murmushi mommy tayi tana jiyowa tace "kinsan halin Habib ba lallai ma yaci komai ba kila wahalar banza mukeyi"
Dan taɓe baki jiddah tayi sannan ta nufi hanyar fita, Muryar mommy taji tana tambayar"zaki bi hibban ne ku taro shi"
Da sauri ta girgiza kai "a'a mommy zanyi assignment ne"
Daga kai kawai mommy tayi jiddah ta fice da sauri ta koma ɗakinta ta kwanta cikeda da tunanin iri iri tareda fatan Allah yasa ayi komai lpy batareda wata matsala ba cikin kankanin lokaci bacci ya dauke ta hankali kwance tafara baccin ta..
Tun 5:30 Hibban ya isa airport yana jiran lokacin saukar su Habib, 6pm dai dai jirginsu Habibullah ya sauka..
Cikin isa da kasaita yake saukowa daga jirgin, fuskar tashi ba yabo ba fallasa saidai zaka iya hango kwarjini da haibar dake tattare da kyakkyawar fuskar shi, cikin nutsuwa ya sauko yafara waige waige cikin takaici ya fara tsaki tareda zaro tafkekiyar wayarshi daga aljihun rigar shi.
Cikin sauri hibban ta karasa kusa dashi dai dai ya daga wayar zuwa kunnen shi.
Yana ganin hibban ya sauke wayar fuskar shi a haɗe ya danyi tsaki.
"I'm sorry Yaya" hibban yayi saurin bashi hakuri dan ya gane meyake nufi.
Amsar jakar hannun shi yayi sannan suka wuce mota Habib yana tafiya kamar bayasan taka ƙasa saidai zuciyarshi a zake take da zuwa gida dan ganin abubuwan alfaharin shi..
Hibban keta faman surutu saidai Habib ko sauraran bayayi,, karshe ma sai hararan hibban ɗin yayi yace"zaka iya min shiru"?
"I'm so sorry Yaya" hibban yace yana maida hankali kan tukinsa..
Cikin garage din gidan hibban yayi Parking sannan ya fice ya dauki kayan Habib ɗin ya shige ciki..
Saida Habib ya dauki mintina sannan ya fito cikeda izza ya fara tafiya,, dakatar da ma'aikatan gidan kawai yake da hannu da suke ta faman Miko masa gaisuwar Barka da dawowa.
"Mommy Ina jiddan kuma"
"Tana daki hibban kasan yanzu ta fiye bacci sosai".
"Ai dama duk haka suke itama afnan sai Ni nake mata..." Kasa ƙarasawa yayi tunawa da yayi rashin kunya zaiyi sannan ya kalli dake faman murmushi.
"Amm.. ina nufin saini nake abinci".. ya faɗa yana sosa keya..
Dariya mommy dai dai shigowar Habib palourn..
Hugging din juna sukayi "i miss You momma"
"Miss you dear"
Dan kallan palourn yayi kamar maisan gano wani abu sai kuma ya fiske ya zauna a saman kujera..
Sallama hibban yayi musu akan zasu dawo shida afnan ɗin zuwa gobe sannan ya tafi bayan yayiwa Habib welcome back...
Da kyar mommy ta lallabi Habibullah ya Dan ci abinci sai yamitsa fuska yake Kamar wani yaro,,.
"Habibullah bakasan cin abinci kamar wani yaro, ga jiddah ma sam batasan cin abinci sosai..."
"What, amma shine aka kyaleta.." Habib ya faɗa da dan saurin shi dan ji yayi ranshi ya ɓaci me take nufi kenan tanaso ta wahalar masa da babynsa kenan kome.
"Kaga kwantar da hankalin ka kowacce mace haka take fuskanta a lokacin da take dauke da ciki"
Shiru kawai yayi sannan ya tashi zai fice..
"Mommy kisa ta kawomin coffee anjima" ya fice batareda ya jira amsar taba..
Kallo mommy tabishi dashi sannan ta tashi ta haye upstairs..
Sai bayan magrib sannan jiddah ta tashi, wanka ta sake yi sannan ta fito palour, babu kowa a palourn kai tsaye kitchen ta shiga ta haɗa ruwan Lipton Kamar yadda ta saba ta fito palour tana sha dai dai saukowar mommy.
"Sannu mommy"
"Yauwa jiddah kin tashi"
"Eh momma"
"Yayanki ya dawo, ki haɗa coffee ki Kai masa sannan ki dawo kici abinci"
Gabanta ya fadi dan sai yanzu ta tuna da dawowar tashi. "Yadai lafiya"?
Murmushi ta ƙaƙalo tace "babu komai mommy, Amma nifa bazan iya cin komai ba"
"Shikenan dama na faɗa masa ai, saiki tanadi amsar bashi"!
A tsorace ta kalli mommy tareda zaro idanuwanta "nashiga3"!
Tashi mommy tayi batace komaiba tabar jiddah a wajan..
Haɗa coffee take saidai zuciyarta a tsinke take "tayaya zata fuskanci Habib da cikin nan, wanne irin wulakanci zata fuskanta daga gareshi, ya Allah"!
Harta gama hada coffeen ta fice zuwa part ɗinsa amma zuciyarta harbawa take a hankali..
Saida Habib yayi sallar isha sannan ya shiga bathroom ya fesa wanka ya fito ɗaure da towel jikinshi yana tsane jiki.
Ta daɗe a tsaye a palourn sannan ta nufi ɗakin nasa cikin dakewa.
Yanajin shigowar ta saidai ya juya baya yana hango ta ta mirror,.tana shigowa taganshi da towel da sauri ta juya zata fice.
"Jiddahhhh.."!
Wata faduwar gaba taji wanda yasa saida taji kanta ya sara dan yauce rana ta farko daya taɓa kiranta da sunanta.
Cak ta tsaya saidai ta kasa juyowa,.
Dan taɓe baki yayi sannan ya nufo ta, daf da ita ya tsaya yace "ajiye saiki fitan"
Badan taso ba ta juyo ta ajiye sannan ta saci kallanshi, "masha Allah gaskiya yaya Habib karshe ne fagen komai, ta ko ina ya hadu ya cika cikakken namiji maiji da kyau da cikar haiba"!
"Zaki iya fita" yace yana haɗe fuska tareda yin dan tsaki..
"Keee" ya sake kiranta.
A dan tsorace ta juyo da fararan idanuwanta.
"Mommy ta fadamin bakyasan cin abinci"!
Shiru tayi tana mazurai da idanuwanta.
"Sorry yaya..."
Dakatar da ita yayi sannan yace ta fita ta bashi waje kafin ranshi ya sake ɓaci.
Babu shiri ta fice da sauri ganin ya fara sauyawa..
Dan murmushi yayi yana lumshe idanuwan shi tunawa da cikin nata da yayi, ya fahimci har wani irin kyau cikin yasa ta gashi takara yar kiba boobs ɗinta sun Kara girma..
Lips ɗinsa ya lasa yana wani kasaitaccen murmushi sannan ya fara sipping coffee ɗinsa a hankali.
Da sassafe jiddah ta shirya zuciyarta fes, tana gama shiryawa ta kira hibban.
"Yaya hibban ba saika zo daukana ba"
"Why" hibban ya Tambaye ta.
"Yaya Habib ne yace zai kaini"!
"Ohh manta fa, ashe yau zan huta da tawa matar dama duk an takura min"
Dariya jiddah tayi tace "saina faɗa masa kuwa"
"So what, abinda nasan ko kwakwaran numfashi bakyayi idan yana waje"
Dariya ta sakeyi tayi masa sallama ganin zai bata mata lokaci.
Da sauri sauri jiddah ta fito palour, mommy kaɗai ta samu a palour.
"Mommy zan wuce"!
"Bazaki jira hibban ɗin ba"
"Yace na same shi a gida"
"Ok shikenan saikin dawo"
Bata sake magana ba ta fice da sauri dan 8am sukayi da doctor kafin aiki yayi masa yawa yace tazo..
Me napep ta tare tayi masa kwatancen hospital din suka dau hanya..
Tana fita Habib ya shigo, gaida mommy yayi sannan ya fara bin palourn da kallo.
Lura da yadda yake waige waige mommy tayi, murmushi ta ɗanyi danta fahimci yanzu Habib bashida kunya akan cikinsa.
"Jiddah ta tafi school"
"Waye ya kaita"?
"Hibban mana bashi kasa ya dinga kaita ba"
Shiru ya danyi saboda tunawa da yanzu hibban ɗin ya kira shi ya gaida shi saidai baiji alamun driving yake ba.
Ji yayi bai gamsu tafiyar tata ba Amma saiyayi shiri kawai.
"Yadai naga kamar ranka ya ɓaci"!
"Nothing, kawai dai nasan hibban baya tafiya a hankali ne kuma kinga ba ita kadai bace"!
Da mamaki mommy ta kalle shi saidai yayi kasa da kai alamun kunya.
"To ai saika dinga kaita da kanka, saiku fita tun 6am saiku kai 8 baku isa ba tsabar tafiya a hankali.."! Mommy ta faɗa tana barin palourn..
Murmushi yayi shima ya koma part ɗinsa Dan ba abinci zaici yanzu ba,..
Zuciyarshi fal da tunanin jiddah da cikin jikinta,,, tabbas lokaci yayi dazai nunawa jiddah kulawa kodan cikin dake jikinta, yanajin soyayyar cikin har zuciyarshi yanaji kamar yafi zaifi kowa farin ciki ranar da aka haife masa cikin da wannan tunanin bacci ya dauke shi..
Har cikin asibitin mai napep ya ajiye jiddah sannan tace ya jira ta fito saiya maida ta sannan ta biya shi.
"To Hajiya" mai napep yace.
Kai tsaye office din docton ta shiga...
✍🏻✍🏻✍🏻
[1/1, 2:25 PM] Aunty Usee: 🌹🌹🌹
*_DR. HABIBULLAH_*
🌹🌹🌹
вч
*🌹ᴀᴍᴇᴇɴᴀ ғɪʀsᴛ ʟᴀᴅʏ 🌹*
*ⓒ* ᴀᴍᴇᴇɴᴀ ᴍᴜsᴀ sʜᴜ'ᴀɪʙᴜ
*wαttpαd*
@Ameenafirstladyy
_____________________________

https://www.Facebook.com/Kainuwawritersassociatio
_____________________________
27
Zaune docton yake sanye da siririn farin glass, zama tayi a kujerar dake gabansa. "Doctor pls kayi kokarin kar a samu matsala"!
"Banida tabbacin samun matsala ko akasin haka, kawai dai zan baki magani wanda zakiyi Amfani dashi zuwa anjima yanzu kuma zanyi miki allura"
"Yauwa doctor" tace tana ciro kudin dake jakarta..
Babu bata lokaci doctor yayi mata allurar tareda wasu irin magunguna tablet kananu,, sosai tayi masa Godiya sannan tace "zan iya tafiya yanzu"
"Eh mana idan kinji wata matsalar saiki kira Ni"
Batareda ta sake cewa komai ba ta fice daga office din..
Habibullah sosai ya samu bacci sai azhar sannan ya tashi yana miƙa tareda addu'ar tashi daga bacci dauke a bakinsa,, kai tsaye wanka ya faɗa sannan ya fito ya shirya zuwa part din mommy,.
Babu kowa a palourn hakan yasa yayi zamansa tareda lumshe ido yana mai jin dadin zama a palourn yadda yaji shiru babu wata hayaniya..
Yana nan zaune mommy ta sauko downstairs.
"Habib ka shigo Kenan"
"Eh mommy"
Kujerar dayake zaune ta samu kusa dashi ta zauna sannan ta kamo hannuwanshi cikin nata, ta ɗago kai tana kallan shi taga shima ita yake kallo.
Cikin nutsuwa da lallami mommy tafara masa magana. "Habib dan Allah karka nunawa jiddah bakasan cikin nan, takasa sakin jikinta da wannan cikin koda yaushe maganar ta baya wuce yadda zakuyi da ita idan ka dawo,, saboda haka banaso naji kayi mata wani abu dazai sa azo a samu matsala pls"
Dan murmushi Habib yayi sannan yace "inshallah mommy babu abinda zan nuna mata"
Kiss ta manna masa a saman goshin shi "good my boy" ta faɗa tana barin palourn zuwa kitchen.
Tana barin palourn Habib ya saki wani kayataccen murmushi har fararan haƙoran sa suka bayyana sannan ya sake lumshe idanuwanshi cikeda farin ciki yake jin kansa yau Kamar bashi ba.
"Allah kasa jiddah ta haife lpy" ya faɗa yana sake zaman shi..
Makaranta jiddah ta wuce sai lokacin tashi sannan ta nufo gida dan batajin dadin jikinta saidai bata wani damu ba tunda tasan dalilin cutar tata..
Hankalin Habib yakasa kwanciya sai faman kai kawo yake a palour jira kawai yake jiddah ta dawo tasha faɗa dan Gani yake kamar yawo kawai ta wuce.
"Mommy dama suna kaiwa wannan lokacin"?
"Eh mana, dayake bakayi karatu anan ba shiyasa bakasan hakan ba"
Wayar shi ya ciro tareda dannawa hibban kira,, bugu daya hibban ya daga cikeda tsoron kiran..
"Wai bakasan lokacin da suke tashi bane"?
"Ai.na..yi tunanin zaka koma ka ɗauko ta ne"!
Ran Habib ya fara ɓaci da wannan rainin hankalin..
"Ok Nina kaita kenan, ko kuma sa'an ta ne dazanje dauko ta"..
A dan tsorace hibban yace "yaya nayi tunanin kai ka kaita ai, nace zan kaita tace kai zaka kaita. .."!!!
Katse wayar Habib yayi cikin fushi da bacin rai,..
Jin yana fitar da wata iska mommy ta kalle shi.
"Me kuma ya faru"! Shiru yayi mata yakasa bata amsa,, ganin haka yasa mommy ta share shi itama dan tasan ba amsa zai bata ba, karshe ma ta barmasa palourn.
Da sauri jiddah ta biya mai napep kudinsa sannan ta shige gidan,, ganin motarshi saida gabanta ya fadi "kenan yana gida bai fita ba,, ya Allah ya tamkeni kar tayimin wani abu"!!
Zaune ta same shi a palourn ya ɗan jingina da jikin kujera idanuwan shi a rufe saidai ta hango tsantsan bacin rai a fuskar shi..
Kamar munafuka haka tafara sanɗa zata wuce, wani irin fizgo ta taji anyi har saida ta tsorata,.
Tar ya bude idanuwan shi a kanta yana mata wani irin kallo wanda yasa tafara hawaye tana yarfar da hannu.
"Daga ina kike"?
Kasa Magana tayi dan batasan amsar bashi ba saidai tuni hawaye ya gama wanke mata fuska,, har zuciyarshi yaji zubar hawayen nata..Dan kawar da kanshi yayi gefe saidai yana tsaye gabanta da alamu tunanin matakin da zai dauka yakeyi....
Kasa yi mata komai yayi saidai zuciyarshi kamar ta fito dan bacin rai da bakin ciki..
Ganin haka yasa tayi saurin barin wajan kafin ya sauya ra'ayinsa ya kai ga marinta..
"Habib kaida waye ne" mommy ta tambaya tana saukowa daga upstairs..
Girgiza kanshi kawai yayi sannan ya fice daga palourn..
Dakin jiddah mommy ta shiga, "bai miki komaiba ko"?
"Eh mommy" jiddah ta faɗa da kyar tana dan rufe ido yadda taji marar ta na juyawa..
Kallanta mommy tayi tsaff"lpy kike kuwa"
Ƙaƙalo murmushi tayi dan kar mommyn tagane halin da take ciki..
"Babu komai fa"
"Shikenan ki fito kiyi lunch naga yamma tayi kuma nasan bakici komaiba"
"To momma"
Mommy ta fice daga ɗakin nata..
Da kyar tayi wanka ta fita palourn, abinci ma kadan taci sannan ta kwanta a palourn kan kujera duk dan kar mommy ta gane..
Ya dade shower na sauka kanshi yana huci a hankali,, da kyar ya samu yaji zuciyarshi ta ɗanyi sanyi sannan ya fito zuwa Masallaci jin ana kiran magrib..
Sai bayan isha ya shigo, ko abinci baici ba ya koma part ɗinsa ya kwanta,,..
Sai 10pm jiddah tayiwa mommy sallama ta nufi ɗakin ta, kwanciya tayi batasha maganin ba danta manta ma,,, bacci mai daɗi ne ya dauke ta duk da batada lafiya saidai ta danji sauki marar Tata...
Cikin bacci jiddah taji marar ta na dan karta mata, kamar an tsikareta ta tashi zaune, abu kamar wasa saiga jiddah tafara juye juye tana zuba uban gumi,..
Cikin kankanin lokaci jiddah ta jigata, sunan Allah kawai take ambato,. Jin ana kiran sallar asuba ne yasa jiddah rufe idanuwan ta cikin azabar ciwo,,.
Sosai ta godewa Allah da bata sha maganin ba tabar shi a cikin jakarta da shikenan tasan yau mutuwa zatayi..
Wasa farin girki jiddah Kamar ana karo ciwan tun tana iya buɗe ido har takasa motsa bakinta ma, tanaji wani abu mai dumi yana bin kafarta saidai ina batasan ko menene ba juye juye kawai takeyi tana kiran sunan Allah a ranta dan tasan yau mutuwa ce kawai..
Da sassafe mommy ta sauko kamar yadda ta Saba, kafin masu girki su tashi ta shiga kitchen Dan da yunwa ta tashi yau..
Habibullah ma yau da sassafe ya shigo part ɗinsu mommy tayi mamaki sosai ganinshi a irin wannan Lokacin.
Sai 7am sannan mommy ta fito daga kitchen din, cikeda mamaki ta kalli Habib"jiddah kuwa lpy naga yau bata fito ba zata makara fa, dama naga jiya kamar batajin daɗi" .
Ai Habib a zabure ya tashi ya nufi ɗakin nata, sau biyu yayi nocking saidai babu alamar da mutum a cikin ɗakin..
Cikeda da takaici ya tura kofar dakin, har zai fara nuna fushin sa saidai kuma komai ya tsaya masa cak ganin jiddah cikin jini babu alamar motsi a tareda Ita..
Cikin wani irin sauri Habib ya karasa kusa da ita yana duba numfashin ta saidai ina babu alamar numfashi ko kaɗan..
Kamar wanda ya dauki kara yana Habib ya dauki jiddah ya fita cikin tashin hankali da razana..
Salati mommy tayi itama hankali a tashe tabi bayan Habib zuwa Mota, dakatar da shi mommy tayi ta amshi car key ɗin ganin yanayin dayake bazai iya driving ba duk ya fita hankalin sa...
Asibitin Dr Ahmad suka nufa, kai tsaye emergency room suka nufa da ita dan ceto rayuwar ta,..
Sosai mommy ta koma lallashin Habib ganin yadda ya koma jikinsa duk yayi sanyi idanuwan shi sunyi ja sosai alamun tashin hankali da damuwa..
Saida doctor Ahmad suka dauki lokaci sosai sannan ya fito yana share gumin goshinsa..
Zaune suke a office ɗinsa yafara Yi musu bayani.
"Alhamdulillah saidai mu godewa Allah cikin bai zube ba sabo.. shiru ya danyi sannan yayi murmushi yace Finally dai Habib ka kwantar da hankalin ka cikin matarka yana nan bai zube ba saidai zai maimaita lokacinsa kamar yadda nasan ka sani"..
Ba Habib kaɗai ba har mommy saida taji wata iska mai daɗi ta kada saɓanin ɗazu da sukejin zafin garin..
"Yanzu tana dakin hutu zuwa anjima zaku iya ganinta" ya faɗa yana kallan fuskar Habib da take nuna farin ciki wanda ba kowane zai iya ganewa ba.
"Alhamdulillah mungode Allah, saidai ba wani matsalar kodai wani abu taci wanda ba'a so masu ciki suci" mommy ta Tambaya.
Dr Ahmad wanda bazai iya faɗa musu gaskiyar abin ba dan yasan matsala hakan zai haifar musamman daga wajan Habib,, shiyasa bai faɗi dalilin dayasa cikin yayi barazanar zubewa ba ya bari ne har saita farfaɗo sannan yayi mata nasiha, sannan yabata shawarwari sosai, wannan ya barshi a matsayin sirri tsakanin su tunda yasan ko mommy bazataji Dadi ba musamman yadda take,san jiddah kuma take daukar ta kamar yar cikinta...
"Babu komai mommy saidai Yakamata a lura da abubuwa da take ci"
Habib duk ya lura dashi kamar yana boye musu wani abu...
Dr Ahmad kuwa Ganin irin kallan da Habib ke masa ne yasa yace " kai tsabar kaduwa ma zaka rasa first born har mantawa kayi da matsayinka na babban likita duk ka wani rude kazama abin tausayi."..
Dariya sukayi su duka saidai banda Habib wanda yayi murmushi wanda iya karsa lips ɗinsa kawai.. sannan suka fice shida mommy zuwa dakin da aka kwantar da jiddan...
```NOT EDITED📵```
```Follow me on Wattpad```
Comment,, share and vote pls..
[1/1, 2:25 PM] Aunty Usee: 🌹🌹🌹
*_DR. HABIBULLAH_*
🌹🌹🌹
*🌈K͎a͎i͎n͎u͎w͎a͎ W͎r͎i͎t͎e͎r͎s͎ A͎s͎s͎o͎c͎i͎a͎t͎i͎o͎n͎*
вч
*🌹ʄɨʀֆt ʟǟɖʏ🌹*
*wαttpαd:ameenafirstladyy*
{29}
Kai tsaye fita yayi ya siyo komai saidai zuciyarshi a cikeda bakin ciki,, palourn mommy ya shiga tana zaune itada jiddah wacce ke kwance cinyar mommyn, tana jin sallamar shi ta tashi zaune tana kasa da kanta dan bataso su hada ido dashi.
"Munafuka dole mana ki ƙasa dakai"! Ya faɗa a ransa.
"Yadai ka tsaya kazo mana kayi aikin ka" mommy ta faɗa masa..
Kamar mai koyon tafiya haka Habib ya ƙarasa ya ciro alluran,,, saidai yana kawo hannu jiddah tafara kuka tana fadin batasan alluran,.
Sai lallashin ta mommy keyi amma ina taki mika hannun Habib kuwa takaici ne ya cika shi tsabar takaici baisan sanda ya fizgo hannunta ba ya caka mata allura fuskar nan a haɗe kamar bai taɓa dariya ba, toshe baki jiddah tayi tana kuka sosai tunda tasan ba san kara yake ba, haka ya gama sannan ya nunawa mommy Maganganun da yadda zata sha sannan ya fice daga palourn dan zuciyarshi tunzura shi takeyi yayi abinda bayasan yi yanzu..
Da kyar jiddah tayi shiru sannan ta wuce dakinta tana ajiyar zuciya tareda jin haushin Habib danta lura harda mugunta ya haɗa Mata....
Kwana takwas jiddah ta kwashe tana jinya bata zuwa school sai ranar Monday ta shirya tsaf ta fito palour da ɗan saurin ta, Habib na zaune yana sipping coffee saidai yana ganinta ya ajiye coffeen yana Binta da ido,.
Gaida shi tayi kamar mara gaskiya zata fice duk da bai amsa gaisuwar tataba,, dakatar da ita yayi ta hanyar kiranta da keee.
Juyowa tayi tana wasa da kasan mayafinta sannan ta matso kusa dashi tana fadin "gani yaya Habib"
Wulakantaccen kallo yabita dashi sannan yace ina zaki a irin wannan shigar"?
Kasa bashi amsa tayi, ganin ya mike ne yasa tayi baya da sauri tana zare ido cikin in Ina tace "school zanje"
Baice komaiba ya raba ta gefenta zai ya wuce saida ya kai bakin kofa sannu taji yace "ki canza shiga ina jiranki a mota"
Da sauri ta koma ɗakin Tata dauko hijab Sannu ta same shi a mota yana jiranta..