Gabatarwa
Dr Habibullah Part 1 Complete Hausa Novel · about 69 min read
[1/1, 2:21 PM] Aunty Usee: *_🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_*🤝🏻
```{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/Kainuwawritersassociation
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
*_DR. HABIBULLAH_*
_Writing by_📚✍🏻
*_Ameena Musa_* _(GARO)_
*_🌹 Ameena firstlady 🌹_*
*_Wattapad_*
@Ameenafirstladyy
[email protected]
*_Not edited_*📵
1
Kanta kife yake bisa jakar Kayanta ta Ghana,.
Kuka takeyi kamar ranta zai fita duk da a bakin titi take hakan baisa taji wani tsoro ko fargabar kasancewar ta a wajan ba.
"Ina ma mutuwa nayi na irin wannan rayuwar, meyasa banbi iyayena ba nake raye har yanzu" saurin istigfari tayi tunawa da tayi da wannan Sabo ne hakan Allah yaso ya ganta amma meyasa ita rayuwar ta kullum cikin jarrabawa take ne,..
Tambayoyin da basu da amsoshi ta dinga yiwa kanta a bakin titin duk da dare ya fara yi amma sam batajin tsoro ko kaɗan dan batama san a wanne gari take ba tasan dai birni ne duba da Yadda yanayin shi yake.....
Gudu yake shararawa kamar zai tashi sama dan yasan hankalin mommy yana gareshi tunda yakai dare a waje abinda bai saba ba gashi ita kaɗai ya baro a gida. A hankali yake bin wakar turawan dake tashi Daga cikin motar tashi, amma duk da haka bai rage gudun ba saboda yadda dare yayi masa....
Tsugunne take kamar yadda take tun ɗazu kusan awanta guda a wajan harta fara tunanin tashi taci gaba da jan kafar ta takai koma inane danta samu abincin da zata saka bakinta dan idan bata manta ba rabonta da abinci tun ranar jiya shima ba wani abin kirki taci ba.
Tun daga nesa ya hango alamun mutum harya kusa karasowa nan ya tabbatar da zargin shi kuma abin da yafi bashi mamaki macece kuma da alamar tana cikin matsala.
Harya wuce saikuma ya reverse ya tsaya saitin ta.
Fitowa yayi daga motar ya tsaya yana kare mata kallon, lallai tana cikin damuwa to amma me takeyi a gefen titi tana matsayin mace mai daraja.
Waigawa ya fara yi hagu da dama yana kallon titin da motoci suka fara ɗauke wa sai lokaci zuwa lokaci suke wucewa.
A hankali ya tako har zuwa kusa da ita sannan ya rankwafo dai dai fuskar ta.
"Baiwar Allah, Baiwar Allah..."!
A hankali cikin nutsuwa ta ɗago kyakkyawar fuskar ta, yunwar da takeji ne ya hanata sukuni hakan yasa bata nuna firgici akan fuskar taba.
Katse mata tunanin ta yayi ta hanyar tambayar ta.
"Me kikeyi anan haka, dare fa yayi bai kamata kizo kan titi ki zauna ba"
Tunda yafara Magana take kallon shi amma bata fahimtar abinda yake cewa dan ji takeyi kamar ba duniyar takeba.
"Pls ki tashi zan kaiki gida idan mota kika rasa"
"Ka kyaleni kawai gara mutuwata ta riske ni a nan" tana faɗa ta mayar da kanta kasa taci gaba da kukan ta.
Tuni zuciyar shi ta karaya dama shi Sarkin tausayi balle akan mace dayake kallon su masu rauni.
Ganin hankalin ta baya tare da ita gashi dare na karayi yasa yace "shikenan dan Allah kizo muje gidanmu idan yaso zuwa safiya saina kawo ki gida.."
Abin mamaki ko gama rufe baki baiyi ba ta mike tana kallon shi alamar su tafi ɗin.
Cikeda mamakin ta ko tsoron shi bataji duk shidin namiji ne kuma saurayi amma ko ɗar bataji ba.
Saida ya ɓude mata ɓangaran mai zaman banza sannan shima ya zagayo ya shiga ya tayar da motar ya fara tafiya.
Lokaci zuwa lokaci yana kallonta saidai ita sam bashi take kallo ba hasali ma idanuwanta a rufe suke tanajin yadda cikin ta ke kugi,.
"Lallai wasu iyayen dole suci wuta ta hanyar wofantar da amanar da Ubangiji yabasu, ga yarinya kyakkyawar ajin farko amma ta kare a bakin titi kuma ko tsoro bata alamun tanaji, duk yasan mommy bazata yi masa faɗa ba saidai ma taji daɗi". Kallonta ya sakeyi sannan ya mayar da hankalinsa kan driving ɗin dayake yi.
Itako ko gezau bataji ba saima daɗi da taji koba komai tasan zata abinci taci ta koshi ko iya hakan ma ta godewa Allah.
Wani tafkeken gate light Ash naga yayi horn, da sauri mai gadin ya bude masa, yana shiga ya wuce wajan faka motocin ya aijye.
Sam batama San sunzo ba idanuwanta na rufe ta faɗa kogin tunani,.
Ganin batasan ma yazo gida ba yasa yace "baiwar Allah munzo"
Kamar mai bacci a ɗan firgice ta tashi sannan ya zagayo ya buɗe mata motar.
Tunda ta fito take kallon tsaruwar da kyaun gidan kamar a turai, katon gida ne mai shegen kyau da tsari kusan part uku ta iya gani duk da lokacin dare yayi, saidai kyan gidan yasa yanzu tafara tsoro "shikenan yau kuma gidan ƴan shan jini na kawo kaina, Allah ka fitar dani"....
"Muje mana." Muryar shi ta katse mata sauran tunanin ta.
Jikinta a sanyaye duk lakar jikinta ta saki yunwar tuni ta gudu tsabar tsoro,.
Shikam ya saka ta a gaba ganin sai waige waige takeyi, yana bayanta yana dariya kasa ƙasa.......
*_comments dinku shine zaisa naci gaba_*✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
*_DAGA ALKAMIN FIRST LADY🌹_*✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
08112138112
_for adjustment and WhatsApp only_
[1/1, 2:21 PM] Aunty Usee: *_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_*
```{United we stand and succeed: Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

_By_📚✍🏻
*_Ameena Musa_*
*_🌹 Ameena firstlady 🌹_*
*_Wattpad_*
@Ameenafirstladyy
[email protected]
2
Mommy gaba daya hankalin ta gama tashi dan yaronta bai taɓa kaiwa haka yana waje ba danko dinner baiyi ba gashi wayarshi taƙi shiga , tana cikin zagaye palour taji karar tsayawar motar shi sannan ta saki wata ajiyar zuciya ta zauna...
Cikin sanɗa take tafiya kamar ɓarauniya, ganin alamun a tsorace take ne yasa yayi gaba yabarta a baya.
Shi mamakin yakeyi dan yaga da farko bata tsorata ba amma tunda suka sauka yaga dukta sauya ta tsorace.
"Kana ganin iyayen ka zasu yadda na kwana a nan kuwa "?
Yayi mamakin jin Muryar ta dan baiyi tunanin tanada daɗin Murya hakaba,.
Saida ya riƙe handle ɗin kofar da zata sada shi da main palour sannan ya jiyo yana kallonta murmushi yayi yace "mommy na zata yarda karki damu" sannan ya Tura palourn ya shiga.
"Hibban ina kaje ne hak...!" Maganar mommy cak ta tsaya tana karewa yarinyar da hibban ya shigo da ita, sai boyewa takeyi a bayanshi tana jiran taji abinda mommy zata ce dan tasan shikenan korarta zasuyi.
"Haba sweet Mom kinsan ai ina nan dawowa gareki" ya ƙarasa maganar yana jiyowa da kallon shi ga yarinyar da suke tare dan yaga mommy takasa zama tana neman ƙarin bayani danko Amsar daya bata bata saurara ba.
"Hibban Ina ka samo kyakkyawar yarinya haka, kuma meya haɗa ka da ita"?
"Zauna Mom zanyi Miki bayani daga baya, yanzu dai I'm hungry kuma itama tanajin yunwa"
"To shikenan kuje dining room abincin ka yana can har naci nawa dana gaji da jira"
"Yauwa mommy nah I love you so much"
"Naji nidai jeka ci abinci kuje tareda ita sai kuci tare" mommy tace tana janyo ƙatuwar wayarta.
"Muje ko, ki ajiye kayan naki a nan"
Bata bashi amsa ba saidai ajiye kayan tayi tabi bayanshi tana tafiya a hankali dan ji takeyi kamar zata faɗi saboda tiles ɗin da aka makaka a palourn.
Mommy tana lure da ita har suka shige dining room ɗin sannan ta mayar da hankalinta kan wayarta.
"Yau kuma yar ƙauye ya kawo min, Allah yasa dai ba halin nashi ne ya dawo ba." Mommy ta faɗa a zuciyar ta...
Hibban saida ya zauna yafara cin abincinsa sannan ya ɗago kai Yana kallanta yadda take ta kalle kalle takasa zama.
"Zauna mana" ya katse mata kallanta.
Kujerun wajan take kallo sannan tabi dining ɗin da kallo an shaƙe shi da abinci kamar na mutum goma.
Kamar mai koyon zama haka ta zauna a kujerar, da kanshi ya tashi yayi zuba mata.
Kallan abinci takeyi kamar maisan tuna wani abu, "bazaki iya ci bane" ya tambaye ta.
Daga masa kai tayi dan bata taɓa ganin irin abincin ba saidai yau.
Tashi yayi yafara buɗe mata cooler abinci duk wanda ya buɗe mata saitace a'a.
"To wanne zaki iya ci saina taso kuku ya dafa miki"
"Kabarshi zanci wannan ɗin kawai, ngd" ta faɗa tana cire spoon ɗin tafara ci da hannu.
Abin har mamaki ya bashi yadda take cin abincin kamar tayi sati bata ciba tsayawa kallanta yayi cikeda da tausayin ta harta gama.
"Kin koshi"
"Eh" kawai tace dan har Yanzu bata gama sakin jikinta ba.
"To tashi muje na nuna Miki inda zaki kwanta naga kamar bacci kikeji"
Da sauri ta tashi tace "a'a daka barshi ma kawai, yanzu zan tafi na gode da taimakon ka gareni"
Mamaki ne ya kama shi yama rasa mai zaice mata, kallan wrist watch ɗin dake hannun shi yayi sannan ya mayar da kanshi gareta.
"Kibari zuwa safiya saina kaki har gida, karfe kusan daya yanzu bai kamata ki fita a matsayin ki na mace ba" ya ƙarasa maganar yana kallan yanayin ta.
"Ko biki yarda dani bane, kina ganin zamu Cutar dake ne.."? Ya faɗa yana gyara tsaiwa...
"A'a shikenan zan kwana na gode" tace tana wasa da yatsun hannunta.
Bakaramin daɗi yakeji ba a duk lokacin da tace ta gode yana ganin hankalin ta ƙarara saidai akwai tarin damuwa a tattare da ita.
Baiyi magana ya nufi hanyar fita tana binsa a baya har palour, yadda suka bar mommy haka zo suka sameta itadai tana bayansa a boye.
"Mommy zan kaita ɓangaran ma'aikata zata kwana acan"
"A'a kabarta anan mana ai kamar bakuwa ce kaita wancan ɗakin" ta nuna masa wani daki dake palourn.
Kayanta ya dauka suka nufi ɗakin, tana biye dashi tana jinjina mutumci irin na taddijuwar nan.
"Ga ɗakin da zaki kwana idan kina bukatar wani abu ɗakin mommy na upstairs saiki ke ki tambayeta, ki saki jikin ki mommy mutuniyar kirki ce kinji"
Daga masa kai kawai tayi dan ta fahimci mutanen arziki ne su duka ga mutumci da karamci.
Harzai fita tace "ina ne wajan wanka inaso zanyi wanka"
Murmushi yayi yace "I'm sorry mantawa nayi" ya faɗa sannan ya nuna mata bathroom din ya fice.
Lallai wannan yanada mutumci ha fara'a sannan ga hakuri.
Bathroom ɗin ta shiga wanda ya tsaru kamar bana dakin baƙi ba, a cikin bathroom manne yake da toilet duk waje ɗaya.
Ta daɗe tana tsaye dan dakyar ta iya amfani da kayan bathroom ɗin ji takeyi kamar a mafarki take saida ta dade sannan tagama wankan ta tsaya tana karewa banɗakin kallo.
"Ikon Allah harda wani madubi (mirror) a bayi ga wani tawuli nidai bazan iya saka wannan na fita ba ai sainaji kunyar kaina ma" ta faɗa a ranta Sannan ta fito.
Nan ma gaban madubi ta tsaya tana kallan kanta duk da ba kayan kwalliya dana shafa amma saida ta dade a tsaye a wajan.
Komai cikin kauyanci takeyi ta taɓa Wannan ta taɓa wancan kamar wata yarinya.
Saida tagama komai sannan ta kwanta kan Italian bed ɗin dake ɗakin, a hankali tafara tunanin iyayenta dakuma rayuwar da tayi.
Hibban kuwa yana zuwa palour ya ƙarasa kusada mommy dake zaune har lokacin tana jiran fitowar shi.
Saiji tayi ya sako kanshi ta gefen wuyanta "mommy I'm very tied, I want to sleep"
"Babu inda zakaje saika yimin bayanin inda kasamo wannan yarinyar"
Zagayowa yayi yana dariya "oh mommy! Dama nasan tunda kika ganmu tare zaki fara zargi na kuma nina yi muku alqawarin bazan sake bin wata mace ba ko shan wani ba"
"Naji, amma faɗamin inda kasamo ta"
Labarin yaɗuwar yabata itama ta tausaya mata sosai kuma take taji yarinyar ta kwanta mata dama Mommy Akwai san yara mata saidai Allah bai bata ba hakan yasa duk sanda hibban ya kawo mata yara take karbar su saidai daga baya su gudu.
"Shikenan da safe saimu tambayeta labarinta idan batada kowa ne saimu riketa dan naga da nutsuwa a tareda ita"
"A'a fa mommy haryanzu kinasan zama da wata ne bayan kinsan yaya Habibullah ya bayasan wannan kwashe kwashen nawa ko so kike idan ya dawo ya koreni daga gidan Gaba ɗaya" ya tambaye ta cikin sigar tsokana.
"Ai kaine da kwashe kwashe kaita tsinto yara marasa hankali saina saba dasu sai suyi min sata su gudu".
Dariya sosai hibban yayi sannan yayi mata sallama ya nufi part ɗinsa.
Mommy ma tashi tayi ta haye sama dan kwanciya.
Hibban saida ya kwanta sannan ya fara tunanin yarinyar, kwarai tanada hankali da nutsuwa sannan daga gani bata kebewa da wani namiji ba dan ya fahimci takasa sakin jikinta ne dan batada sabo da hakan.
Yasha gogayya da yammata kala kala kafin yayan shi ya hanashi wannan dabi'ar saidai bai taɓa haɗuwa da mai kamun kai kamar wannan ba Allah yasa ta zauna tare dasu koba komai zai samu abokiyar hira.[1/1, 2:21 PM] Aunty Usee: *_🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_*🤝🏻

3
Cikeda da tunanin yadda zasu kaya da yayan nashi idan ya dawo bacci ya sace.
Da asuba ta tashi sam ta manta a ina ma ta kwana, tana buɗe ido tayi saurin tashi tare da addu'ar tashi daga bacci a bakinta.
Sake bin dakin da kallo yayi, "wai yau ni JIDDAH ce a irin wannan gidan" ta faɗa a ranta.
Tashi tayi ta nufi bathroom tayi alwala.
Tana idar da Sallah ya nufi palour dan taya Mommy aiki.
Dai dai fitar ta mommy ma tana saukowa daga upstairs.
Har ƙasa ta duƙa ta gaida mommy cikeda kunya.
Itama mommy da fara'a ta amsa tana tambayar meyasa ta fito Yanzu.
"Mommy na fito tayaki aiki ne"
Murmushi mommy tayi sannan tace "ayya, bani nakeyi ba ai yan aiki ne Amma muje ki tayani zan haɗa coffee"
Ba musu tabi bayan mommy har kichine ɗin, kallan kichine ɗin tayi "lallai su komai nasu na masu kuɗi ne" ya faɗa a ranta.
Mommy na haɗa coffee itakuma tana gefe tana kallanta dan batasan ma menene wani coffee ba.
Hibban ne ya shiga kichine ɗin sanye da ƙananan kaya da suka amshi jikin shi yayi kyau sosai da hibban ba baya bane wajan kyau da gayu.
Saida ya gaida mommy sannan JIDDAH ta gaida shi a kunya ce.
"Bakuwa tazama yar gida kenan harda su shigowa kichine" ya faɗa ta sigar tsokana.
Murmushi kawai bata tanka masa ba.
Kansa ya mayar ga mommy yana kada key ɗin motar sa "mommy nizan fita"
"Ka kira kasha coffeen Mana" mommy tace.
"No mommy kema kinsan ni wannan bai dameni ba, kema yaya Habibullah ne ya koya miki dan da bahaka kikeba"
"Gaskiya kuwa Habib ne ya koya min"
"Jiddah ko zaki raka yayan naki ne"
"A'a mommy, sannan ta mayar da kanta gareshi daya kafeta da ido.
"Nagode da taimakon da kayimin sosai"
"Babu komai ki jira na dawo saina kaiki bakin titi" daga haka bai sake magana ba ya fice.
Suma fitowar sukayi itada mommy suka nufi dining room.
Saida mommy tagama Shan coffeen sannan ta ɗago ta kalli JIDDAH dake zaune kanta a kasa ta kasa shan coffeen tun ɗazu.
"jiddah meyasa kika baro gida a irin wannan daran kina matsayin mace..."?
Shiru jiddah tayi ma wani lokaci dan bazata iya kin faɗa musu gaskiyar wacece itaba hakan yasa tafara ba mommy labarin cikeda nutsuwa.
Iyayena Asalin Fulanin Adamawa ne sana'ar fata ce ta dawo dasu Kano, babana yanada rufin asiri sosai, gida daya suke zaune da kanin sa kawu Audu da matar sa Inna marka.
Iyayena sun rasu sanadin rusau ɗin da akayi a wata damina hakan yayi sanadiyyar rayuwar su.
Nasha kuka sosai na Rashin iyayena dan Ni kaɗai suka haifa MAHAIFIYATA ta rasu da tsohon ciki.
Haka ragamar kula dani ta koma hannun kawuna, kawu Audu.
Da farko ya nuna min so kamar yarda ya haifa amma daga baya kuma sai komai ya sauya Sakamakon rashin dacen mata da baiyi ba, sam inna marka ta tsaneni dama can ganin idon iyayena ne.
Saida na koma abin tausayi kamar jaka wajan aiki tun ina yarinya ta na iya aikin wahala iri iri duk da babu wani talauci mai tsanani a tareda mu.
A haka ta dinga ziga kawuna tanamin sharri tun baya yarda harya koma yana yarda.
Talla kuwa saida na koma harda shigowa birni tallan fura.
Har girma na tana azabtar dani itada kawu Audu saidai ban taɓa tunanin guduwa ba saidai na tasa hoton iyayena nayi ta kallo ina kukan rashin su danayi.
Tun ina da shekaru goma sha Bakwai manema suka fara zuwa wajena, dole inna Marka tasani nake fita wai ai ba jikani zasuyi su sha ba.
Ana haka watarana wani Alhj Lawan daga nan birni ya shiga ƙauyen mu ya haɗu dani.
Tunda yazo ya samu inna marka shikenan kullum yazo da duka take kora ni sainaje dan kullum yazo saiya bata kuɗi, shikuma kawu Audu baya iya tsawatar mata saidai ma ya ƙaramin.
A haka suka tilasta min saina aure shi, babu yadda na iya na amince aka saka rana.
A ranar dana gudu kwana biyu kenan da saka rana a matsayin watanni huɗu masu zuwa, na dawo daga aiken da inna marka tayimin na dauko markade naji suna magana kasa ƙasa da Alhj Lawan a zaure yana faɗa mata shifa ba aurena zaiyi ba kawai yazo ne ya lalatamin rayuwa, inna marka kuwa saiji nayi tana fadin wai dama tun tuni tasani amma karya sake ya nuna ya bari ranar da aka daura auran saiya sake Ni a ranar Bayan bukatar shi ta biya.
Na razana sosai saidai ina shiga zauran ban nuna naji komai ba.
Duk jikinsu yayi sanyi a tsorace inna marka tafara zubamin ashar ma fadi gaskiya kona jisu nikuma fafur na nuna banji komai ba.
Dama ba kullum suke bani abinci ba hakan yasa ban damu ba na shirya kayana tsaff bayan uban kukan da naci nayi alkawarin bazan kwana a wannan ƙauyen ba, inna marka na fita makwabta na kwashe yan kuɗin danake tarawa na fito, ban tsaya ko inaba sai tasha daga nan na shigo birni.
Kafin nan kusan gida uku naje amma duk wanda naje bana iya zama dan ba gidan zama bane, hakan yasa nafara tunanin ko rayuwata a jarrabawa zata ƙare.
Lokacin da yaya hibban ya haɗu dani nan ma gudowa nayi daga gidan wani dan iskan mutum Allah ya kwaceni shine na fito bakin titi yunwar danake ji ne tasa nakasa tare mota ya sameni anan.
Takarasa labarin tana goge hawayen da suka maƙale mata tun ɗazu.
Ba mommy kaɗai ba har Hibban dake tsaye tun ɗazu yaji komai basu san shigowar shi ba bakaramin tausayin ta sukayi ji ba Musamman mommy mesan Yaya mata.
Saijin maganar shi sukayi a kusada dasu "kiyi hakuri JIDDAH dama kowanne dan Adam Akwai tashi jarabawar"
Mommy ma cikeda da tausayi dakuma jin wani sabon san yarinyar ya shigar mata zuciya.
Ta kamo hannun ta cikin nata "lallai na daɗe rokon Ubangiji yabani ya mace koda ta tsuntuwa ce sai gashi yanzu ya amsa addu'a ta, dan Allah JIDDAH ki zauna tareda mu zamu maye Miki gurbin iyayen ki da kika rasa"
Cikeda da karfin guiwa ta daga wa mommy Kai alamu ta amince dan su ta yarda dasu ɗari bisa ɗari.
Cikeda farin ciki mommy tace "shikenan yanzu kije ki huta kafin agama breakfast sai hibban ya kaiki ki siyo abubuwan da kike buƙata"
"A'a mommy bana bukatar komai"
Mommy ce ya katse ta da "banasan musu kuma daga yau banaso kiyi abinda zanji kamar bani na haifeki ba kamar yadda bazan taba nuna bani na haifeki ba"
"Shikenan mommy Nagode" sannan ta tashi ta nufi ɗakin ta.
"Mommy Amma kina ganin yaya Habibullah zai amince da wannan maganar kuwa" hibban ya tambaye ta.
Murmushi yayi "zai yarda Habib yanasan duk abinda nakeso waɗan can ma dan yaga ban damu dasu bane sosai dole yanzu zai yarda"
"Tabb yarda yake mugun nan ai wlhy idan ya dawo kila da kanta zata sake guduwa dan wannan koni bai kyale ba Balle yadda ya tsani yaga wata rabe shi, sai anyi magana ya nuna shi mata basu dame shi ba bayan ba wanda yasan me yake aikatawa acan ɗin"
Bugu mommy takai masa ya kauce yana dariya.
"Saina faɗa masa idan ya dawo, kuma wlhy bai isa ya takurawa yarinya taba saidai shi ya koma inda ya fito kuma dole jiddah ta rabe shi tunda ta zama ya a gidan itama"
Hirar Habibullah suka dinga yi sannan hibban ya fice daga gidan Bayan mommy ta jaddada masa Lallai ya dawo da wuri yakai jiddah shopping.
[1/1, 2:24 PM] Aunty Usee: *_🌈 KAINUWA WRITERS✍🏻 ASSOCIATION🤝🏻_*

🌹🌹🌹🌹
*_DR. HABIBULLAH_*
🌹🌹🌹🌹
_Story and writing by_📚✍🏻
*_🌹 Ameena firstlady 🌹_*
*_WATTPAD_*
@Ameenafirstladyy
[email protected]
*_NOT EDITED_*📵
4
Kamar yadda mommy tace Hibban lokacin ma tasowar shi baiyiba ya nufo gida dan kai Jiddah shopping,.
Jiddah na zaune a dakinta tayi shiru tana ta tunanin yadda rayuwa ta sauya mata lokaci guda taji an turo kofar ɗakin ta.
Idanuwan shi a kanta harya karaso kusa da ita sannan yace "jiddah tunanin me kikeyi haka"
"Babu komai ya Hibban"
"Ok ki fito ina jiranki mu tafi" ya faɗa yana ficewa.
Hijab ɗinta kawai ta dauka tabi bayan shi,.
A palour ta sameshi shida mommy a zaune da alamar magana sukeyi.
Tashi hibban yayi yace su tafi, sannan tayiwa mommy sai sun dawo suka fice.
A hankali hibban yake tafiya dama can baya gudu sosai idan yana driving, tafiya suke suna hirar su cikin nishadi da annashuwa, dama ita sajida akwai saurin sabo.
Babban Mall yakaita da kanshi ya jidar mata kaya kamar hauka sannan suka wuce shagon saida drinks nan ma siyo mata kayan kwaɗayi iri iri.
Kafin su dawo tuni jiddah ta saki jiki da Hibban musamman data lura bashida wata matsala ga fara'a da iya hira ga ban dariya sosai.
A gajiye suka shigo gida su duka biyun tareda kaya niki niki.
"Sannu daughter jekiyi wanka kizo muyi lunch"
"To mommy nah" jiddah ta faɗa tana tafiya dakinta.
saida tayi wanka sannan ta shirya kayanta da suka siyo, kayan kwalliyar kansu ba ƙananan kudi hibban ya kashe mata ba.....
acikin sati biyu sabo mai tsanani ya shiga tsakaninsu da hibban dan wani lokacin ko wajan aiki ya tafi ita take kai masa abinci suyi ta hira acan abinsu, mommy kuwa kamar yar cikin ta haka ta dauki jiddah duk Friday saita ɗauke ta sun fita gyaran jiki da kitso wani lokacin har wajan shakatawa mommy ke kaita hakan yasa cikin kankanin lokaci jiddah ta zama kamar yar gida har shagwaba mommy shikuwa Hibban saidai yayi ta dariya yana ce mata yarinya.
Yau tunda takaiwa Hibban abinci yagama ci ta ɗauki excuse a wajan aiki ya ɗauke ta suka dinga yawo har gidajan kawayen mommy saida sukaje, sai bayan la'asar suka nufo gida bayan uban siyayyar kayan chocolate da yayo mata.
Suna shiga palour suna zauna suna mayar da numfashi kamar waɗan da suka sha aiki, jiddah kuwa kusa da mommy ta zauna tana faman nishi.
"Ina kukaje ne haka"? Mommy ta tambaye shi fuska a haɗe.
"Mommy Ina office Mana"
"Karya kake Hibban na kira layin wajan aikin su ancemin ka ɗauki excuse kun fita ina ku kaje"? Ta maimaita tambayar Tata.
Kallon kallo suka farayi da jiddah sun rasa ƙaryar da zasuyi dan tahana su zuwa ko ina bayareda Sanin ta musamman yadda tasan halin dan nata a baya.
"Mommy nice nace ya kaini gidan kawar nan taki naje gaida ta kinga rannan tace na sake zuwan mata fa" Jiddah ta faɗa tana taɓe fuska kamar zatayi kuka.
Mommy ce ta dawo da kallon ta kan jiddah sannan tace "na kirata na tambaye ta.."?
Da sauri suka hada baki sukace "Eh!" DAN sun san sunje ɗin.
"Shikenan basaina tambaye taba nasan jiddah bazata yi min karya ba, amma daga Yau karku sake zuwa wani waje baku fadamin ba kuma bazan sake aika ki kai masa abincin ke kaɗai ba saidai na haɗa ki da driver kuje ku dawo tare, ina fatan kina jina"
Marairaice murya tayi sannan tace "to mommy"
"Jekiyi wanka ki fito zaki gyara min dakina"
Da sauri ta tashi tana faɗin to sannan ta wuce dakinta.
Sai yanzu ta dawo da kallonta wajan Hibban dake zaune kamar baya magana fuskar nan a haɗe, tunda taga haka tasan ranshi ya ɓaci tunda shi mutum ne da koda yaushe yake cikin fara'a da dariya ba kamar dan uwansa ba.
Nuni tayi masa da yazo kusa da ita, babu musu ya ƙarasa ya zauna.
Fuskar shi ta kamo ta juyo da ita tana fuskantar Tata, murmushi tayi masa sannan tace "kayi fushi dani ne"?
Baisan sanda shima ya mayarwa da mommy murmushin ba yace "mommy tayaya kike tunanin zan iya fushi dake kawai naji zuciya ta tayimin zafi dana fuskanci har yanzu keda yaya Habibullah kuna zargin ina aikata sabo bayan tuni Allah ya shiryi danki, koda zanbi mata ai bazan iya bin jiddah ba dan yanzu na ɗauketa a matsayin yar uwata ta jini" ..
Jikin mommy ne yayi sanyi tareda wani farin ciki a zuciyarta kiss tayi masa a goshi sannan ta sake kallan shi tace.
"Hibban na daina zargin ka tuni a zuciyarta saidai ina kare mutuncin Jiddah ne saboda sharrin shaidan, amma yanzu na yarda dakai dari bisa.."
Kwanciya yayi saman cinyar ta yana murmushin wanda yakara masa kyau.
"Yanzu kaima jeka shirya ka fito ku duka mu fita shopping ɗin drinks ya kare na gida"
"Mommy kibari naje ni kaɗai Mana"
"A'a tare nakeso mu fita"
"Shikenan mommy bari naje na shirya" ya faɗa yana ficewa daga palourn.
Mommy ma sama ta haye Dakin ta dan shiryawa.
........ wani haɗaɗɗen palour ne wanda faɗar tsaruwar shima kaɗai bata lokaci ne, tafka tafkan kujeru ne zagaye da palour, palourn dana sake hangowa ne yasa na fahimci ashe gidan palour biyu gareshi wanda kowanne kalar kujerun su ya bambanta dana dayan, komai na palourn iri dayane har capet ɗin dake malale kasan floor ɗin tsakar palourn.
Idanuwana ne suka kai kan wani gayen saurayi dake kwance saman kujera mai mazaunin mutane uku wato (three sitter).
Tsayawa nayi kallon shi, gayan ya haɗu iya haɗuwa sajen fuskar shi ya kwanta luff sai sheki da yakeyi eye lashes ɗinsa kuwa baƙi sidik wanda yayi daidai da yawan gashin girarsa. Doguwar fuskar shi na ƙalla mai dauke kyakkyawan lips ɗinsa Wanda yayi kamar ansa masa Pink lips color,..
Kwance yake yana tunanin yau kwana biyu Kenan bai Kira gida ba gashi yayi matukar kewarsu harda kaninsa wanda yakejin shi har cikin zuciyar shi.
A hankali ya buɗe idanuwan shi tarr, Masha Allah sai yanzu naga kyawawan idanuwan nashi farare tarr dasu.
Tashi yayi zaune sannan yakai hannun shi kan tafkekiyar wayarshi kirar _iphone11 pro Max_ a hankali yaje latsa wayar kamar bayasan latsawa, lambar mommy yafara Kira saidai shiru yaji ana faɗa masa a kashe take.
Sam shi bayasan ya kira waya yaji a kashe amma saboda mommy ce bai damu, kamar karya kira kanin nashi danshi bayasan raini ko kaɗan,saikuma ya tuna bai taɓa kiran sa ba saidai shi hibban ɗin ya kira shi wani lokacin yayi picking wani lokacin kuma yana ganin kiran yake kin dagawa, danshi bayasan surutun nan na Hibban.
A haka dai ya dannawa hibban kira.....
Dakin mommy jiddah ta shiga tana tambayar ina hibban, mommy tace ya tafi yayi wanka zasu fita, hakan yasa jiddah fitowa dan komawa dakinta.
Har zata shiga dakinta taji karar wayar Hibban daya bari kan Centre table,da sauri takarasa bata tsaya duba waye ba ta daga kiran tareda sallama dauke a bakinta.
Har zai yanke kiran saboda tsabar bakin ciki wato shine bazai daga kiran ba kenan, baikai da yanke war ba yaji Muryar mace nayi masa sallama.
Cikeda mamaki mai tsanani HABIBULLAH ya dauke wayar daga kunnen sa yana sake duba number daya kira, number Hibban dince dai hakan yasa ya sake karata a kunnen sa yayi shiru.
"Waye ne"? JIDDAH ta sake faɗa jin anyi shiru kuma mai kiran yana kallan layi.
"Me wayar ya shiga wanka idan ya fito za'a faɗa masa ankira" bata tsaya jin wani abu ba ta yanke kiran dai dai shigowar hibban ɗin yana gyara cufflinks din rigar shi.
Ganin wayar shi a hannun jiddah ne yasa ya daga mata gira "ya akayi ne ko bincike kike min ne"
Taɓe baki tayi tace "Ni ina ruwana da wayarka kiran ka akayi.."
"Waye." Ya sake tambayar ta.
"Oho nidai na daga naji anyi shiru kuma abin haushi ma mai kiran yana jina yayi banza dani dan rainin wayo"
A zabure Hibban ya karaso haryana hadawa da tuntuɓe ya amshi wayar yana duba recieved call dinshi, aikuwa gabanshi ya fadi ganin Sweet bro a kiran karshe.
Jiddah na tsaye gefe cike da mamakin yadda yake ta faman barin jiki,.
"Me kika ce masa.."? Ya tambaye ta yana kallon ta.
"Babu komai kawai nace ka shiga wanka ne amma idan ka fito zaka kira shi.."
"Ya Salam shikenan nashiga uku wajan Yaya Habibullah" ya faɗa yana zama kan kujerar kusa dashi.
Ita kuwa jiddah ko ajikinta saima taɓe baki ta kuma ta nufi ɗakin ta dan dauko mayafi.
.....barin rai tareda wani zafin zuciya ne suka taru suka yiwa Habibullah yawa, waishi yau mace ke masa magana haka kuma ma karuwa.
"Wato Hibban bai dana Bin mata ba kenan, harta kai yana mace waya ta amsa masa kira...
Wani irin huci ya furzar cikeda haushin Hibban, "lallai dole na ɗauki matakin ladabtar dashi, tunda bazai iya rike marairaicin shiba..."
Tashi yayi ya nufi ɗakin dan watsa ruwa,.
Ya dade shower na zuba kanshi, dan duk lokacin da ranshi ya ɓaci saiya sakarwa kanshi shower yake jin dadi, saida ya daɗe ruwan na zuba kanshi yaji ya samu sauki kaɗan a zuciyarsa sannan ya shiga bath tub yafara wanka...
Tsaye yake a gaban mirror yana gyara sumar kanshi, sannan ya shafa lotion mai daɗin ƙamshi..
Nan ma ya dade yana kalkale jiki sannan ya saka light Ash na wani tsadaddan ya feshe jikinshi da turare mai daɗin da saukin ƙamshi dan bayasan yaji kamshi ya hau masa ka.
Ƙatuwar motarshi ya shiga kirar Ferrari New model.sannan ya yakama key zai tayar saikuma ya tsaya yana tunanin.
"Har karuwar bazan kyale ba saina nemo ta tagane wa tayiwa iskanci.." ya faɗa yana yiwa motar key ya fice a guje......
Harta dauko mayafinta yana zaune inda tabar shi, har zatayi magana taji Muryar mommy tana fadin su tashi su tafi ta fito.
Gaba dayansu suka fice, mommy ke driving jiddah na gefen mommy shikuma Hibban yana baya........
[1/1, 2:24 PM] Aunty Usee: *_KAINUWA WRITERS✍🏻 ASSOCIATION_*🤝🏻

_story and writing by_✍🏻
*_🌹 Ameena firstlady 🌹_*
*_Wattpad_*
@Ameenafirstladyy
[email protected]
*_Yawan comments dinku shine yasa naci gaba da wannan Novel din, Ina godiya sosai dan comments dinku shine yake karamin Kwarin guiwa_*😍😍😍
```Ban yarda wani ko wata ya juyamin labari na ta wani fanni daban ba kokuma a cire wani abu daga cikin sa batareda neman izinin naba, kuma duk wanda ya siyarmin da Novel din ban yafe ba danni ban siyar dashi ba saboda haka kar wanda ya siyarmin```❗
*_Not edited_*📵
5
_________________________
Babban shagon saida drinks mommy takaisu, sosai suka kwashi lemuka iri iri sannan suka nufi gida dan yamma lokacin tayi.
Jiddah tana lure da hibban kamar ranshi a bace yake, mommy ba ta lura da hakan saidai tasan fushin hibban bashida wani tasiri musamman akansu.
Horn mommy tayi a tangamemen gate ɗin nasu, cikin kankanin lokaci mai Gadi ya buɗe musu yana musu sannu da dawowa.
Kai tsaye Hibban bai kulasu ba ya nufi ɓangaran shi, zuciyar shi kamar yayi kuka haka yake ji.
Jikin jiddah duk yayi sanyi sam takasa sakin jikinta, mommy ma ɗakin ta ta wuce dan yin sallar magrib itama zuciyarta nasan sanin abinda ya hada hibban da jiddah duk irin shirin da sukeyi.
.....har dare hibban bai sake zuwa part din mommy ba, mommy harta gaji da jira tacewa jiddah dake gefe tana wasa da wayar mommy din.
"Jiddah tashi muje muyi dinner naga hibban bashida niyyar dawowa gashi wayar shi a kashe"
"Na koshi mommy" jiddah ta faɗa ko dagowa batayi ba.
Cikeda mamaki mommy tace "bangane kin koshi ba, meyake faruwa ne keda yayan naki, ko faɗa kukayi"..
Jiddah Sarkin hawaye tuni hawaye ya zubo mata sannan ta fadawa mommy abinda ya faru.
Murmushi mommy tayi dan sai yanzu tagane matsalar, dama tasan bazai wuce hakan ba dan dazu ta jiyo su.
Janyo jiddah tayi jikinta tana lallashin ta, "kiyi hakuri kiyi shiru, yanzu ki tashi kici abinci saiki kai masa nashi ɓangaran shi sannan kibashi hakuri kuma daga yau kidena daga masa waya".
Jiddah batayi musu ta tashi mommy na rike da hannun ta suka nufi dining room.
Saida suka gama tsaff mommy na kallan yadda take tsakurar abinci duk ta wani damu, itadai mommy murmushi kawai takeyi, suna gamawa ta haɗa mata nashi ta bata.
Yauce rana ta farko da jiddah ta taɓa shiga ɓangaran Hibban, tana yin nocking ya buɗe mata yana ganin itace ya saki handle ɗin kofar ya koma ya zauna.
Kallon palourn nashi take wanda yafi nasu haduwa kuma ba laifi Hibban yanada tsafta ga ƙamshi tako ina yana tashi, daya daga cikin manyan kujerun dake palourn ta zauna tana wasa da yatsun hannunta.
Hibban idanshi na kanta danjin abinda ya kawo ta dan yaga alamar magana a bakinta.
"Lafiya naga Kamar kinasan yin magana" ya faɗa yana kare mata kallo.
"Dan Allah yaya Hibban kayi hakuri, bazan sake daga maka waya ba nayi alkawari"
Har zuciyar shi yaji tausayinta Musamman daya lura duk ta wani daburce kamar zatayi kuka.
Murmushi ne ya suɓuce masa harta jiyo sautin fitar shi.
Ɗago kai tayi, sai taga yana murmushi.
"Ni bakiyi min laifin komai ba jiddah saboda haka ki daina damuwa"
Mamaki ne ya cikata "to kodai yayanta yanada aljanu ne, mutum kamar mai iskokai yanzu fa yaketa faman cin magani amma kiji wai banyi masa laifi ba"
"To amma naga kanata fushi dani tunda na daga wayarka dazu"...
Gyara zaman shi sannan yace "jiddah abinda yasa kika ga na nuna banji daɗi ba saboda nasan yaya Habibullah ranshi zai bashi fiyeda tunanin ki, bashida uzuri ko kaɗan sannan bashida hakuri mutum ne wanda kanshi kawai ya sani, nikuma banasan bata masa rai saboda ina sanshi fiyeda yadda nake san kaina...."
Sai yanzu jiddah tagano dalilin dayasa yake fushi da ita tun ɗazu wato saboda yayan shine.
"Amma ai naji bai damu ba" ta faɗa with full confidence.
Murmushi kawai hibban yayi sannan ya jawo abincin data kawo masa.
"Mugama cin abincin saina faɗa miki waye yayana dan naga alamar kema baki ciba"
Batayi musu ba suka fara cin abincin dama dazu damuwarsa ce tasa takasa ci din.
Saida suka gama sannan yace su tafi part din mommy suyi hirar acan dan yasan hankalin mommy yana kansu....
Aikuwa suna shiga palourn suka samu Mommy na jiran dawowar jiddah, tana Ganin su tare tace "dama nasan fushin naku hutu ne shiyasa ban shiga ba balle naji kunya" ta faɗa tana hayewa upstairs dakinta....
Cikeda da nutsuwa hibban yafara bata Labarin Habibullah.
Mahaifin mu Alhj Nasir mutum ne mai arziki da mutane, ya taka mataki iri iri a gwamnati, yayi minister bangare daban daban sannan yana da kamfanoni biyu a Russia, hakan yasa muka tashi cikin gata da wadata da arziki wanda bazan iya kayyade Miki irin tarin dukiyar da mahaifin mu ya mallaba.
Abuja Maitama anan gidan mu yake, shekarar iyayen mu shida sannan Allah yabasu haihuwa.
Ranar suna aka sawa Yaro suna HABIBULLAH wanda ya gata iya gata wajan abokan Papa, anyi shagali iya yi a wajan lunch din da akayi na murnar haihuwar yaya Habibullah.
Cikin kauna da tarairaya yaya Ya tashi, lokacin daya fara wayo halayen shi suka fara bayyana wanda hakan yasa Papa tura shi Russia karatu tun yana yaro....
Da farko yaya Habib mutum miskili ko su mommy maganar shi tsada take musu bayashi da fara'a ko kaɗan ga saurin fushi sannan bayasan wasa a al'amuran shi..
Bashida wani abokin hira dan koda yaushe yana zaune shi kadai da zarar mutane sun wuce biyu to bazai iya zaman waje ba...
Yaya Habibullah kyakkyawan ne ajin farko dan mutane da yawa suna mamakin irin kyan da yaya Habib yake dashi, Papa kam abin har mamaki yake bashi da irin halayen shi kamar kurma wanda bayaji baya gani, dole yasa Papa yakai shi Russia duk irin san da suke masa, amma haka suka tura shi a cewar su kila bai samu abokan hira bane amma acan tunda abokin papan yanada yara dai dai shi ya saba dasu ya saki jikinshi...
Tun yana yaro ya tafi Russia acan ya fara karatun shi tunda matakin yarinta, a wannan lokacin aka haifeni kowa yayi murna amma banda yaya Habibullah danshi baka gane farin cikin shi balle bakin ciki saboda koda yaushe fuskar nan tashi yadda take haka take....
Ni inada barkwanci da surutu da saurin sabo hakan yasa lokaci guda nayi mutane kuma tun ina yaro nayi abokai sosai..
Papa da mommy suna nuna min so fiyeda yadda kike tunani saboda Ni a gabansu na tashi koda yaushe ina tareda su hakan yasa nafi shakuwa dasu sosai kamar yadda suma suka fi shakuwa dani..
Saidai duk da haka soyayyar yayana tana cikin raina koda yaushe magana akansa ne, saidai shi bazaka taɓa tunanin yana damuwa akaina ba..
Lokaci guda mahaifin mu ya tashi da cutar ajali, wanda yayi sanadiyar tashin hankali na nakasa jurewa, yaya Habibullah ma saida yazo cikin ikon Allah kwana biyu da zuwan shi Allah yayiwa Papa rasuwa, wadda ta girgiza jama'a da yawa ciki harda ni da mommy.
Shi kanshi yaya Habibullah wannan lokacin saika tausaya masa yadda yakara shiga cikin wani yanayi na rashin Papa, abinda yabani mamaki sai a lokacin naga irin soyayyar da yaya Habib yakemin, baya bacci saiya nayi baya iya cin komai saiyaga naci, baya nuna damuwarsa a gabana saboda kwantar min da hankali lokaci da dama yakan shigo dakina ya tsaya yana kallo na ma tsawon wani lokaci yana tausaya min saboda yasan sainafi kowa jin rashin Papa a lokacin....
Saida komai ya wuce yaya ya koma Russia dan karashe karatun sa na likita kamar yadda yakeda buri tun yana yaro, sannan nafara shiga wani yanayi wanda har mommy bataso hakan.
Nakasa rike maraicina nakasa hakuri da mantawa da rashin papa, nafara bin abokaina zuwa club..
Duk wani babban club da garin Abuja keji dashi nasan da zaman shi, a hankali nafara bin mata,kuɗi da kyau da aji tareda ilimina yasa mata kebi na, mommy tayi fadan harta gaji, saidaga baya sannan ta sanar da yaya Habib....
Duk da lokacin yaya Habibullah yana tsaka da karatu haka ya biyo jirgi yazo Nigeria, Tunda naganshi jiki na yabani mommy ta faɗa masa komai dan yadda naga fuskar shi kamar baisan menene Dariya....
Nasha bakar wahala sosai sannan mommy tabani tausayi hakan yasa nayi musu alkawarin bazan sake shan komai ba kuma bazan kara bin mace ba,.
Cikin ikon Allah a sati biyu da yaya Habib yayi na daina komai, kuma lokacin lauyan Papa yazo da shaidar dukiyar da Papa ya yabari tareda takardun kamfanonin shi biyu...
A lokacin na daɗe yadda da irin san da yaya Habib yakemin dan kuwa cewa. Yayi ya barmin duk wani abu nashi na daga dukiyar Papa Dan shi Russia zai koma...
Mommy taji daɗi sosai tasa masa albarka, sannan ya tsayar da ranar komarsa...
Duk irin wannan halin nawa danayi inajin tausayin mace kuma ina darajanta ta, suma wadancan su suka zubar da tasu darajar, kamar yadda na sameki sau biyu na taɓa kawo wasu su biyu wadanda mommy ta amshe hannu biyu² amma daga baya suke guduwa,..
Tun daga lokacin yaya Habibullah ya hanani kwashe kwashe Nan danshi a rayuwarsa bayasan damuwa ko ya take....
Na takaice Miki yaya Habibullah ya wuce duk yadda kike tunanin shi, mommy kaɗai yanzu yake iya sarrafa kanshi a gabanta, bayasan raini ko kaɗan..
Yanzu ma da kikaga na damu nasan gamuwa ta dashi, dan yanzu zaiyi tunanin ban daina halina bane............
Wani irin ajiyar zuciya jiddah ta saki, "wannan wanne irin halitta ne kenan, da alamar shine silar barina gidan nan dan bazan jiri wulakancin shiba..." Ta fada a ranta...
Murmushi hibban ya sakeyi danya fahimci kamar tafara tsorata dashi..
"Kinga shifa duk irin wannan halin nashi saidai idan ke kika shiga sabgar shi, amma shi ko kallo baki ishe shi ba.."
Taɓe baki jiddah tayi abin ma haushi yabata "Ni dama nace zan shiga sabgar tashi ne.."
"Atoh dai gyara ma hakan, dan yaran ministoci da commissioners sunyi sun gama amma baibi takansu ba.."
Cikeda takaici jiddah ta tashi tana wani yamitsa fuska, "naga alamar wannan yayan naka da alamar shine zai cinye gasar kyakkyawan duniya na wannan shekarar" ta faɗa ta nifar Dakin..
Dariya sosai hibban yakeyi danya fahimci haushi taji shine ta mayar masa da baka...
Tana shiga ɗakin ta tayi tsaki "aikin banza saidai yayiwa wani iskancin shi amma badai Ni jiddah ba"
Ta haye saman Royal bed dinta bacci mai ya sace ta...
Hibban ma part ɗinsa ya nufa ya kwanta cikeda tunanin yayan nashi.
*_ALKALAMIN FIRSTLADY 🌹_*✍🏻✍🏻✍🏻
[1/1, 2:24 PM] Aunty Usee: *_kainuwa writers association_*🤝🏻

_writing by_*
*_🌹 Ameena firstlady 🌹_*
*_WATTPAD_*
@Ameenafirstladyy
[email protected]
6
Da sassafe hibban ya shigo palourn mommy, mommy ce kadai Zaune tana shan coffee,.
Waige waige yafara Yi yana neman jiddah.
"Good morning mommy"
"Morning too dear"
"Mommy zan wuce office zanyi breakfast acan.."
"Shikenan saika dawo"
"Ameen mom" ya faɗa.
Har zai fita mommy takira sunan shi..
"Hibban"!
"Na'am mom" ya dawo ya zauna.
"Dama cewa zanyi Yakamata ka nemawa jiddah school zaman gidan bashida wani amfani tunda babu abinda takeyi"
Shiru yayi yana tunanin sannan yace "haka ne mommy zanyi wa abokina magana zuwa gobe"
"Shikenan Allah yayi albarka"
"Ameen Mommy" ya tashi ya fita.
Dai dai fitar shi jiddah ta fito daga ɗakin ta.
Gaida mommy tayi sannan tace ina yaya hibban.
"Yanzu ya fita, yace zaiyi breakfast acan office, sannan yace zai nemo miki school na tambaye ki idan kinaso"
Cikeda farin ciki jiddah ta rungume mommy tana ihun murna dama burinta kenan a rayuwa karatu, amma tunda tagama primary school iyayenta suka rasu bata sake tunanin karatu ba.
Sai ya yayanta zai nema mata.
.... Gudu yake shararawa kamar wanda zai tashi sama tsabar bakin ciki, lokaci zuwa lokaci yakan ciji lebensa na kasa sannan ya fitar da wani huci mai dauke da baƙin ciki.
A haka ya isa wata babbar anguwa dake Russia, wani katon gate yayi horn aka ɓude masa gate din, saida ya samu waje yayi Parking sannan ya buɗe mirfin motar tashi.
Saida ya kusa mintina goma sannan ya fito fuskar nan tashi fayau mai dauke da kyakkyawan sajen shi.
A hankali Kamar wanda bayasan taka ƙasa ya nufi main palour dake kafcecen gidan.
Tun Kafin ya ƙarasa ya ciro wayar shi yana kiran abokin nashi.
Bugu biyu ya daga yana faɗin "guy ya akayi ne" abokin nashi ya faɗa wanda ke zaune a wani madai daicin daki.
"Pls open the door" ya faɗa kawai yana katse wayar shi.
Murmushi Sultan yayi yasan halin abokin nashi bayasan yin nocking shiyasa ya kira shi.
Yana bude kofar ya ganshi tsaye fuskar nan a haɗe.
Kai tsaye dakin Sultan suka nufa sannan ya cire siririn farin Glass ɗin dake idanshi ya zauna kan kujerar dake cikin dakin yana huci.
Sun kusa minti biyar babu wanda yayi magana sannan Sultan ya kawo masa ruwa mai sanyi a ajiye masa tareda dogon Glass cup.
Bai kula Glass cup ɗin dake gefe ba ya daga ruwan jirkan yana sha.
Saida ya kusa shanyewa tass sannan ya ajiye yana maida numfashi a hankali,.
Lumshe kyawawan idanuwan shi yayi kamar mai bacci.
"Meya faru ne Habib,"? Sultan ya tambaye shi yana mayar da hankali kanshi.
Tsaki yayi dan bayasan yawan tambaya gashi Sultan da shegen tambaya kamar dan jarida.
"Nothing" kawai yace.
"Kaidai wlhy Habib halinka bazai taba sauyawa ba, shikenan mutum kullum cikin dacin rai kamar wani mala'ikan mutuwa". Sultan yaketa faman mita.
Cikin takaici Habib ya tashi ya dauki car key dinshi yayi hanyar fita daga ɗakin.
Da sauri Sultan ya tare shi yana bashi hakuri, sannan ya sakeyin tsaki ya koma ya zauna.
"Habib ka rage fushi dan Allah Ni banga abin fushi a magana taba"
Habib bai kula shiba balle yabashi amsa.
Saida yayi sallar magrib sannan ya nufi dankareren gidanshi.....
******
Hibban bai dawo gida ba saida ya tabbatar ya samawar gurbin karatu wata private school.
Makaranta ce ta yaran masu kuɗi, secondary school ce kawai, jiddah taji daɗi sosai musamman da hibban yakaita taga yanayin makarantar.
Saida ya biya komai sannan suka tafi gida, akan zata fara zuwa ranar Monday.
Ranar mommy saida tayiwa jiddah faɗa kan ihun mirnar da takeyi..
Hibban kuwa dariya yake ta yimata dan ya gano yarinta ce tasa jiddah ke wannan tsalle tsallen.
Ranar Monday kuwa ta fara zuwa makarantar, hibban shike kaita kuma lokacin tasowa nayi zai ajiye ayyukan shi ya dawo da ita gida.
Har tausayin shi takeji yadda ya damu da al'amarin ta.
Mommy yau ji tayi tanasan jin lafiyar danta, wayarta ta ɗauko tafara neman layin shi.
Habib na zaune gefen bed ɗinsa yaji karar wayar shi, jin ring din da sawa mommy kaɗai yasa ya dauki wayar yana dagawa.
Dai dai shigowar jiddah dakin mommy taga tana waya tsayawa tayi tagama wayar.
"Hello Mom"
"My son"
Gaida ta yayi cikin ladabi sannan tace "shikenan wannan karatun yaki karewa ka dawo gida Habib"
Shiru yayi na wani sakanni sannan yace "very soon zan dawo"
"Yaushe kenan zaka dawo kullum maganar kenan zaka dawo"
"Inshallah Nanda 3weeks"
"Shikenan Allah yakaimu" mom tace.
"Ameen mom"
"Ina fatan kana waya da hibban" mommy ta sake tambaya.
Nan ma "eh" kawai yace,.
Mommy tasan karya yake sarai amma saita ce "to Allah yayi maka albarka, good night"
"Night too momma" ya katse wayar shi.
Jiddah sarai tagane dawa mommy take waya yadda taji suna maganar ba wani armashi "wannan ko mommy ma bai kyaleba nidai zanso naga wannan sarautar"
"Jiddah ya akayi ne kin shigo ina waya da first born dina" mommy ta katse mata tunani.
"Mommy muna jiranki a downstairs"
"Kije Ina nan saukowa"
Bata sake magana ba ta fice ta samu Hibban na jiransu.
"Ina mom din"
"Yanzu zata sauko tagama waya da yaya Habib ne"
Yayi mamaki jin ta samu Habib yanzu amma saiya share.
"Amma yaya hibban meya dawo daku Kano, kuma"
"Yaya Habib ne yasa muka dawo Kano dan ya rabani da abokaina na can"
"Tabb" ta faɗa tana taɓe baki.
Saida suka gama lunch din sannan hibban ya fice, ita kuma ta fara ba mommy labarin makarantar su.
Kwanci tashi yanzu jiddah tana jin karatun ta sosai, har tayi kawaye su biyu khairat da afnan, karatun ta takeyi hankali kwance bata da wata damuwa dan hibban da mommy sun tare mata komai.
Yau ta dade tana jiran hibban yazo daukarta, yana zuwa ta shiga motar ta haɗe rai.
"Afwa yar kanwata mommy ce ta sani nemo masu aiki"
Saida taji uzurin shi sannan ta saki fuska suka fara hira.
Tayi mamakin ganin yadda ake ta gyara gidan harda masu saban fenti, gidan kamar za'ayi biki.
Da mamaki ta kalli hibban, sai taga hankalin shi baya tareda ita hasali ma yiwa ma'aikatan magana yake yadda zasu tsara wajan.
A palour ta samu mommy anata gyaran palourn har kujeru an sauya musu zama.
"Mommy lafiya kuwa"
"Kalau daughter jeki shirya ki fito"
Ba musu ta wuce dakinta wanda taga shima yasha gyara.
"Lallai da alamun tambaya, amma ai sanda na tafi school tsaf naga gidan amma yanzu na dawo naga anata gyara harda part ɗin yaya hibban dana yaya Habib Allah yasa dai baki zamuyi" ta fada tana cire socks ɗinta.
Angyara ko ina a gidan ya zama kamar saban gida, ya ƙara kyau kamar bashi ba, sai dare sannan kowa ya samu nutsuwa.
Zaune suke zasuyi dinner su duka.
"Mommy wai yanaga yau anata gyaran gida ne ko baki zamuyi ne"
Murmushi mommy tayi tace "a'a Habib ne zai dawo jibi Nima sai dazu ya kirani ya faɗa min"
Damm taji gabanta ya fadi batasan dalilin hakan ba,.
"Amma shine sai an gyara gidan haka"
"To sarkin tambaya, duk lokacin dazai dawo dole sai an gyara gida dan bayasan yaga komai kamar yadda yabari"
"Ikon Allah" ta faɗa kawai sannan tafara cin abinci cikeda mamakin irin wannan rayuwa ta Habibullah.
"Daughter gobe zaki je ki duba abinda ma'aikatan basu shirya masa ba saiki gyara, dan nasan ba komai zasuyi shi perfectly ba"
"To momma Allah ya kaimu"
Suka masa da Ameen ...
```Team din HABIBULLAH saiku fara shiryawa dan tarbar shi, saidai kila ya sage muku guiwa😂😂😂
``` ```pls SHARE, COMMENTS and VOTE```

_by_✍🏻
*_🌹 Ameena firstlady 🌹_*
*_WAATPAD_*
@Ameenafirstladyy
[email protected]
7
Kamar kullum jiddah da sassafe ta shirya cikin uniform ɗinta da sukaji masifar yi mata kyau, suna breakfast Hibban yace su tafi.
Sannan tayiwa mommy sallama suka fice.
"Yaya hibban nifa gaskiya yau saika gaisa da su afnan"
"Meyasa kanwata"
"Kullum sai afnan tacemin ina yayana sainace ka yafi Amma yau ka tsaya ku gaisa plsss" ta marairaice murya.
"Ohhh little sis badai rigima ba, shikenan naji zan tsaya, ina fatan shikenan"
"Yes that's all," ta faɗa da murnar ta.
Har cikin makarantar yakaita sannan yace taje ta kirasu su gaisa ɗin,.
Mintina Kadan ya hango su, har suka karaso sannan su khairat da afnan suka gaida shi ya amsa fuskar shi a sake.
"Pls ku kularmin da kanwata banaso naki wani abu ya sameta fa"
Dariya sukayi su duka har jiddan sanan ya ciro kudi baima san nawa bane ya basu.
Kin karba sukayi suka bar wajan sannan jiddah ta amsa tace zata basu.
"Shikenan sis idan akwai matsala ki fadamin kafin na tafi"
"Babu wata matsala bro nidai kawai ka tafi karkayi letti"
Dariya yayi dan yasan korar shi takeyi danta koma wajan kawayen ta.
Sallama yayi mata sannan ya shiga motar shi kirar zenvo Ts1,.
Saida taga ficewar shi sannan ta juya ta koma wajansu afnan.....
Russia, Moscow.
Azimut hoyel:-
Fitowar shi kenan daga swimming pool, farar vest da swimsuit, Zaune yake yana karanta jarida, sam baiji zuwan Sultan ba saida ya matso ya mashe jaridar sannan ya tashi yana kallon shi da sleepiness eyes ɗinsa Kamar wanda baya samun bacci.
"Ya akayi guy wannan irin tunanin haka"
"Babu"
"Naji dama nasan ba fadamin zakayi ba, yaushe tafiyar taka 9ja ne"
Wani siririn numfashi Habib yaja sannan yace.
"Tomorrow"!
"Nima da nayi tunanin na bika amma bazai yiyu ba inasan saina gama da wannan zancen sannan..."
Kallan neman karin bayani yayiwa Sultan batareda yace kala ba..
Ganin irin kallan da yake masa ne yasa Sultan cewa "kaifa Kanada matsala wlhy yanzu harka manta da magana Angelina din.."
Cikeda takaici Habibullah yayi tsaki wanda yasa Sultan sakin baki yana kallanshi.
"Kana nufin wai haryanzu kai bakasan soyayya ta da ita ne."?
"Eh haka nake nufi" Habibullah yace yana barin Wajan.
Da sauri Sultan yabi bayanshi har zuwa cikin kayataccen palournshi, zama sukayi kujera daya.
Sultan kam kasa shiru yayi dan yafara tunanin Habib yanada matsala yadda yaran turawa kyawawa masu kuɗi da aji keta faman binshi amma yaki sauraran su sai gashi yanaso shima ya raba shi da Angelina ɗinsa .
"Kadai kaje kaita zama haka, Nan gaba da kanka zaka fadamin ga wacce kakeso...."
Cikin jin haushin Sultan, Habib ya tashi yana nuna masa hanyar fita "pls fitar min a gida plss"
Sultan daya saba da halin Habib ko damuwa baiyi ba saima murmushi yayi yace "zan fita dama ko baka ceba, ka gaida min da mommy idan kaje" yana kaiwa karshen maganar shi ya fice abinsa.
Jagwab ya zauna kan kujerar yana maida huci "meyasa wai samarin yanzu basuda aiki sainayin aure da wuri su tarawa kansu damuwa ne, nasan zanyi aure amma har yanzu banga wacce tayimin da sunan wani abu waishi soyayya ba infact ma bansan menene soyayyar da suke hauka akanta ba.." ya faɗa a ransa tareda jan wani karamin tsaki ya nufi ɗakinsa dan shirya kayansa.
....... Yau da wuri hibban yaje ya dauko jiddah, suna zuwa gida kan abinci tayi birki dan wata irin yunwa dama take ji.
Saida ta gama da Cikinta sannan ta shiga dakinta, wanka tayi ta shirya sannan ta fito.
Mommy na zaune ita da hibban dake danna computer, tana zama mommy tace "jiddah ba zama zakiyi ba jeki gyara ɓangaran Habibullah"
"Oh sorry momma na manta ne jiya kin fadamin" sannan ta tashi .
"Yaya hibban ka rakani plss"
Wata harara ya maka mata yace "saboda ni sa'anki ne ba, shine saina raka ki duk inda zaki ko.."
Dai dai mommy ta Miko mata key ɗin tace "sorry yayana da wasa nake fa."?
Bai sake kulata ba itama ba sake cewa komai ba ta fice.
Saida Tasha wahala kafin ta bude palourn nashi...
Cikeda mamaki ta tsaya tana karewa palourn kallo, komai iri dayane a palourn yasha gyara an canja komai har Chinese capet ɗin dake malale a kasa, .
Kujerun kansu saida ta tsaya tana kallo ikon Allah wannan palourn aka narkawa kudi ba namu ba Kenan.
Ta daɗe tana surutu ita kadai sannan tafara gyare gyaran wurin,.
Duk dakunan a gyare suke sai guda daya da taga a rufe yake.
Keys din hannunta tafara gwadawa harta samu nashi ta bude.
Tana sako kafarta cikin dakin idanuwanta suka sauka kan wani picture Wanda yasa ta ɗauke numfashin ta na wani sakanni.
"Ya Allah badai wannan ne Habibullah ba" ta faɗa yana karasa kusa da hoton.
Ta kusa mintina shida tana kallan picture din, bakaramin kyau Habibullah yayi ba ji tayi duk irin kwadawar da hibban yayi mata saitaji kamar ma bashi ya siffanta mata ba dan wannan yafi wancan kyau,..
Jin kamar alamun tafiya tayi saurin ajiye wa tafara gyara katon bed ɗinsa.
Ɗaki Kamar na mace ya sha alatu saikace a gidan ba .
Saida tagama sannan ta shiga bathroom ɗinsa, nanma saida ta daɗe a tsaye sannan ta fito dan ita bataga abin gyarawa anan ba.
A palour ta samu Hibban zaune, yana jiran fitowar ta.
Tana fitowa ya tashi yace su tafi.
"Yaya hibban ya kuma naga ka biyo NI"
Murmushi yayi yace "shi ne nima ban sani ba ganina kawai nayi anan"
Dariya sosai jiddah tayi danta gane waskewa yayi.
Bin bayanshi tayi har gaden ɗin dake bayan part ɗin Habibullah, waje ne babban sai shuke shuke wadanda suka wajan yayi sanyi, har swimming pool din dake gefe kadan yayi matukar birge jiddah.
Lallai ashe sune a ƙauye a cikin gidan...
Sun daɗe anan sannan suka koma part ɗinsu.
Itadai jiddah yau taga ikon Allah, dole Habib yaji kanshi shi wani ne....
Har dare jiddah na tunanin picture din da tagani a part ɗinsa, duk lokacin data tuna sai taji murmushi ya suɓuce mata.
....yau jiddah da wuri ta shirya ta fito dan zasuyi submitting wani assignment, hibban ma tuni ya shirya, yana ganin fitowar ta ya tashi.
"Jiddah ki tabbatar kinyi breakfast banaso ki zauna da yunwa dan nasan halin ki"
"Rungume mommy tayi "inshallahu zanyi mommy naaa" ta faɗa tana sakin mommyn ta fice da gudu.
Dariya mommy tayi "Allah ya shirya minke jiddah," sannan ta kalli hibban.
"Kasan yau Habibullah zai dawo saika dawo da wuri".
"To momma, Amma ke zaki dauko shi ko."?
"Eh Ni zanje da kaina"
"Shikenan saina dawo mommy tace to A dawo lafiya Allah ya kiyaye"
"Ameen" yace yana ficewa dan yasan jiddah nacan na jiran shi...
Tunda suka fita mommy tafara Shirin tarbar Habib, wanda sai 2:00pm jirgin su zai sauka.....
Yau gidan kowa saida yasan Habibullah zai dawo, dan aiki sukeyi sosai, kuku kuwa saida sukayi kala kala kamar wanda mutane da yawa ne za suci.
Ko ina na gidan ƙamshi yake 1:30pm mommy ta shirya cikin shiga ta Alfarma sannan ta dauki car key ɗinta ta nufi airport...
2:00pm jirginsu Habibullah ya sauka, A hankali mutanan jirgin suka fara fitowa,.
Idanuwan mommy ne ya sauka kan dan nata dayake saukowa a hankali kamar bayasan saukowar.
"Masha Allah" mommy ta furta ganin yadda dan nata ya sake zama cikakken namiji kyaun shi da haibar shi suka sake bayyana.
Sanye yake cikin light blue din suit wacce ta amshi fatar jikin shi.
Fara rarraba fararn idanuwan shi yayi dan ganin wanda yazo daukarshi, akan mommyn shi idanuwan shi suka sauka, murmushi daya kara masa kyau yayi sannan ya nufo ta.
Itama da murnar ta fal ciki ta tarbe shi tana rungume shi.
"Welcome back my son"
"Thanks momma"
Hannuwanshi ta kama suka nufi motar Tata, ba bata lokaci mommy tafara driving suka tafi gida.
"Hibban fa mommy,"
"Yana wajan aiki shiyasa nazo Ni kaɗai"
"Amma mom ina drivern ki"
Murmushi tayi danta gane me yake nufi.
"Nina sallame shi saboda nafi san driving da kaina"
Bai sake magana ba ya kwantar da kanshi kawai yana lumshe ido....
Sai 2:30 sannan hibban yaje dauko jiddah dan aiki ne ya riƙe shi yanzun ma excuse ya dauka ya fito dan yasan tana jiran shi...
.... ma'aikatan sai kwasar gaisuwa sukeyi ko kallo basu ishe shiba saima komawa yayi yana dakatar dasu da hannu kawai yakeyi.
Palourn mommy ya sauka, saida ya kusa mintina shida sannan yace zai je part ɗinsa yadan huta.
"Shikenan dear, jiddah ta gyara maka dama"
Sam ba kawo watace jiddah ba yayi tunanin cikin yan aiki duk da bayasan yan aikin ma'aikata shiyasa lokaci da dama hibban ke gyara masa.
Amma baice komai ba ya fice hannun shi dauke da suit din daya cire.
Kallan palourn nashi yayi ba laifi yayi masa kaɗan dan babu wani dirty sosai.
Ɗakinsa ya shiga, sannan yafara bin ko ina da kallo Kamar maisan ganin wani abu,.
Mamaki ne ya cika shi ganin picture ɗinsa ba inda yasaba ajiye shiba, tsaki yayi sannan ya mayar dashi mazaunin shi.
Bathrobe ya dauka kawai ya shiga wanka.
Saida ya nitsa sannan yasa kaya marasa nauyi ya nufi part din mommy sai zuba ƙamshi yake.
Mita sosai jiddah tayiwa hibban kamar zatayi kuka, sai hakuri yake bata tana zuba masa shagwaba har suka karaso gida tana saita faɗawa mommy..
Da gudu ta shiga palourn tana kwadawa mommy Kira,..
Kam ta tsaya kamar wacce aka dasa, kallon shi takeyi kamar wacce taga dodo tsoron shi da kwarjinin shine suka sa takasa koda motsa kafarta.
Shima Habibullah kallo daya yayi mata ya dauke kai cikeda tunanin wacece ita haka ta shigo kai tsaye tareda kiran mommy.
Tunawa yayi da mommy ta bashi labarin wata yarinya da suka tsinto may be itace wannan ya faɗa a ranshi yana jin haushi dan dazu bakin ciki ne yasa ya amsawa mommy kawai....
Jiki a sanyaye ta shige dakinta, tana shiga ta cillar da hijjabin ta gefe ta zauna ta zuba uban tagumi.
"Gaskiya Allah yayi halitta anan wannan hoton ma rage masa kyau yayi,"
"Na yarda da maganar yaya hibban, wannan mutumin daga gani bashida mutumci ko kaɗan"
Ta dinga sake sake a ranta sannan ta shige bathroom danyin wanka da alwala....
````ku biyoni A sannu zakuji yadda zata kaya tsakaninsu
DAGA```
*_ALKALAMIN FIRSTLADY 🌹_*✍🏻
[1/1, 2:24 PM] Aunty Usee: *_🌈KAINUWAWRITERSASSOCIATION_*

_By_✍🏻
*_🌹 Ameena firstlady 🌹_*
*_WATTPAD_*
@Ameenafirstladyy
[email protected]
8
Tana idar sallar taji ana nocking din dakinta.
Hibban ne tsaye ɗauke da murmushi fuskar shi,.
"Sweet sis, meyasa baki fito ba munata jiranki.."
"Babu komai yaya hibban"
"Muje to" ya faɗa yana bata hanya.
Tana gaba yana Binta a baya suka shigo palourn, kamar fadi idanuwanta ya sauka kan na Habibullah wanda ke zaune bashida alamun tashi a wajan.
Harara ya maka mata yana wani kankance ido, cikeda da tsana danshi Gaba daya jiyayi ya tsaneta dan suffar munafukai gareta.
Ganin irin hararar da yayi mata yasa ita kuma ta taɓe baki a zuciyarta tace "nidai ba abokiyar yinka..." Kafin ta gama zancan zuci taji saukar wani gigitaccen mari Wanda yasa ta juyo a firgice.
Habib ne tsaye yana huci kamar wani zaki idanuwannan nashi yayi ja kamar garwashin wuta.
Daga hannu yayi zai kuma marinta mommy tayi saurin janyeta jikinta,.
"Meye haka Habib, daga dawowarka zaka takurawa yarinya me tayi maka da zaka yi mata irin wannan marin..." Mommy ce ke ta faman yiwa Habib faɗa kamar zata ari baki.
Cikin wani irin yanayi Habib ya fice baice komaiba, kai tsaye part ɗinsa ya wuce, bathroom ya shiga ya sakarwa kanshi shower yana huci mai cikeda bakin ciki da bacin rai....
Hibban kuwa dake zaune kamar an dasa shi, ji yayi kamar ya zubar da hawaye dan bakin ciki, shima tashi yayi ya fice kamar zai tashi sama.
Jiddah kuwa na jikin mommy tana kuka dan bakaramin zafin marin taji ba, "dole ta fita harkar wannan mutumin dan kuwa nan gaba babu abinda bazai iya yi mata ba"..
"Kiyi hakuri JIDDAH dama nasan haka zata faru Habib yanada zafin zuciya saidai ki fita harkar shi kidaina shiga sabgar shi kinji ko"
Jiddah kai kawai ta dagawa mommy sannan mommy tace ta tashi suci abincin saita kaiwa hibban nashi dan shima ranshi ya ɓaci.
Saida ya kusan 20mnt sannan ya fito ɗaure da towel jikinshi, ya daɗe yana gyara jikinshi sannan ya jura sleeveless shirt, car key ɗinsa kawai ya dauka ya fice dan bazai iya cin komai a gidan ba gyara yaje restaurant ya nemi wani abun yace.
Dakyar jiddah ta iya cin wani abu, sannan ta dauki na hibban ta wuce part ɗinsa.
Kwance ta same shi yana ganinta ya tashi ya amshi kayan hannunta.
Fuskar ta yabi da kallo yadda yaga harta dan tasa, murmushi jiddah ta ƙaƙalo sannan ta zauna kujerar kusa dashi.
Hibban abincin yake ci amma lokaci zuwa lokaci yana satar kallon jiddah, har ya gama.
A hankali yafara janta da hira har saida tadan sake sannan ya tashi ya raka ta...
Habib babban restaurant yaje ya cika cikinsa sannan ya shiga motarshi yayi hanyar gida cikeda sake sake a ranshi akan wannan yarinyar....
Ganin dare yayi lokacin yasa ya nufi ɓangaran mommy yayi mata saida safe kamar yadda ya saba.
Babu kowa palourn hakan yasa kai tsaye ya haura upstairs.
Fuskar mommy ba yabo ba fallasa ta amsa masa, har yayi hanyar fita ta kira sunan shi a nitse.
Amsawa yayi sannan ya koma ya zauna yana sauraran ta fuskar tashi a haɗe.
"Habib meyasa baka iya rike fushi ka akan komai, yarinya daga zuwanka zaka fara damun rayuwar ta harta gaza zama damu itama ta gudu kamar yadda kayiwa wadancan, to wlhy daga yau banaso na kara jin kayi mata wani abu da zai sa taji ba dadi harnaji kaji na faɗa maka.."
Daga kai kawai yayi sannan ya tashi ya fice yana zayyana abubuwa a ranshi.
Kai tsaye part ɗinsa yaje ya kwanta cikeda bacin rai lallai wannan yarinyar tasamu matsayi da yawa" ya faɗa a ransa sannan yayi wani murmushin mugunta yana gyara kwanciyar shi....
Saida hibban ya tabbatar ta saki ranta sannan yayi mata sallama ya wuce ɗakin shi danyin bacci...
Jiddah kuwa ta dade bacci bai sace taba tana tunanin yadda zata saba da wulakancin Habib sannan bacci yayi awon gaba da ita.......
*************
Kwana biyar kenan da dawowar Habib babu abinda ya sake shiga tsakaninsu, saidai ko gaida shi tayi baya amsawa sai idan mommy na wajan zai amsa a dakile,.
Kullum kuma Hibban ke kaita school sabo kuwa sai abinda yayi gaba dan ko abinci daya baya iya ci idan babu ɗaya....
Yau suna gama breakfast yace taje ta gyara masa ɗakinsa, cikeda mamaki ta kalli fuskar shi babu alamun dariya fuskar tashi amsa masa tayi da "to".
Har zuciyar Hibban baiso haka ba dan yasan kila wata muguntar ya shirya mata amma sai yayi shiru abinsa baice komai ba.
Fita yayi dan bai fiye zama cikin palourn ba, yana fita itama ta nufi part ɗinshi da sauri kafin ya dawo yace ta bata masa lokaci.
Buɗe palourn tayi tana bi da kallo dan ita bataga abin gyarawa a wajan ba, ɗakinsa ta nufa tana shiga ta taɓe baki,.
"Niban ga abin gyarawa anan ba, kawai dai so yake ya batamin lokaci har malamina yazo yayita jira..." Faɗa tana karasa kusada gadon,.
Kallon picture dinnan tayi wanda ya sauyawa wajan ajiya,.
"A haka kamar babu ruwan shi amma mugun sai cin zali kamar..."
Jin an fizgo hannunta da karfi an murde ne yasa tayi saurin sakin kara.
Habib ne tsaye kamar wanda aka aikowa da sakon mutuwa, a hankali ya lumshe idanunsa sannan ya buɗe su jajir yana wani huci cikin bacin rai.
Kuka sosai takeyi wanda ya kara hassala shi ya jefata jikin wardrobe din dake gefe.
Kyawawan mari biyu ya bata, tuni ta fara bashi hakuri tana kuka kamar ranta zai fita.
Wata iska ya fesar dan kukan nata dada bashi haushi yakeyi,
"Waye mugu..." Ya faɗa yana kafeta da sexy eyes ɗinsa.
"Wlhy bada kai nake ba, plss I'm sorry Yaya Habib.."
Murmushi yayi jin yadda take rantsuwa bada shi take ba, can kuma ya sake bude baki zaiyi magana sai kuma ya fasa yayi mata nuni data fice.
Da sauri tayi hanyar fita,.
"Keeh"!
Taji ya dako mata tsawa wanda yasa tayi saurin dawowa tana dukawa kusa dashi.
"Share wannan hawayen.." yace yana yi mata wani wulakantaccen kallo.
Share hawayen tayi sannan yace "oya smile"
Ba shiri ta sake ƙaƙalo murmushin dole tayi sannan yace ta fice da wannan mummunan fuskar Tata.
Kamar zata faɗi ta fice da gudu gudu sauri sauri, tana fita ta nufi part din hibba.
Dai dai hibban zai fito yaga shigowar ta kamar an jefo ta.
"Lpy jiddah, meya faru waya taba ki"
"Yaya Habib ne" ta bashi amsa a takaice.
Shiru hibban yayi sannan ya nuna mata waje ta zauna.
Hakuri sosai ya bata sannan su nufi part din mommy...
Habib kuwa tana fita yayi tsaki dan harta sa kanshi yafara yi masa ciwo da wannan shegen kukan nata, kwanciya yayi saman bed ɗinsa sannan ya lumshe idanuwan shi yana tsaki lokaci zuwa lokaci.
Sam Habib yaki fara aiki dan tuni angama gina private hospital din dazai fara aiki, a cewar shi hutawa yake dada yi.
Sultan ma tuni ya dawo Nigeria bayan ya gama saita maganar auran shi da Angelina.
Sosai Habib yake jin haushin yadda mommy ke nunawa jiddah so, wani lokacin har mamaki yakeyi saidai yanzu ko inda jiddah take baya kallo, kuma ko yaya kuskure yake bakaramin wahala yake bata, harta fara sabawa da cin mutuncin shi.
Palourn mommy ya shigo sanye da ƙananan kaya Wanda suka amshi fatar jikin shi, ita kadaice a palourn tunda ya shigo ta kalle shi tayi ƙasa dakai.
"Mutum har mutum amma zuciyar shaidanu ne dashi" ta faɗa a ranta tana taɓe fuska.
Ko inda take bai kalla ba ya wuce sama wajan mommy danya sanar da yau zai fara fita aiki.
Mommy na ganin shi tayi murmushi, "Habib ka fito"
"Eh maa"
"Ina zakake ne haka."
"Mommy zan fara fita aiki yau".... "Aiki" mommy ta maimaita.
"Allah to ya taimaka, ka tafi da jiddah ka ajiye ta a gidansu kawarta tun ɗazu takesan zuwa nace ta bari hibban ya dawo amma tunda fita zakayi saika ajiye ta acan"
Habib ji yayi wani abu ya tsaya masa a wuya tsabar takaici.
Mommy kuwa bata bi ta kanshi ba ta fice tana kiran jiddah.
"Na'am mommy"
"Tashi ki shirya Habib ya ajiye ki gidan su afnan ɗin"
Da sauri tace "a'a mommy na fasa ma ai.."
Kallon tuhuma mommy tayi mata sannan tace "banasan shashancin banza tashi ku tafi"
Badan taso ba ta tashi ta shige ɗakinta dan dauko hijjabin ta.
Shikuwa Habib yana saukowa ya fice yana jiranta cikin mota.
Kamar munafuka ta shiga baya ta zauna,.
Kusan mintina shida yaki tayar da motar, can kuma yayi wani tsaki sannan ya fito ya bude bayan ta dake zaune ya fizgo ta da karfi har tana bigewa, sannan ya mayar da ita gaba ya zagaya ya tayar da motar ya figeta a guje.
*_pls kuyi manage da wannan_*👈

*https://www.Facebook.com/Kainuwawritersassociation
🌹🌹🌹🌹
*_DR. HABIBULLAH_*
🌹🌹🌹🌹
_By_✍🏻
*_🌹 Ameena firstlady 🌹_*
*_WATTPAD_*
@Ameenafirstladyy
[email protected]
9
.....gudu yake shararawa kamar zai tashi sama, lokaci zuwa lokaci yake jan wani siririn tsakin takaici.
Jiddah kuwa kasa tayi da kanta tana addu'ar Allah ya sauke su lafiya dan a yadda yake gudun nan saidai fatan sauka lafiyan, driving ɗinsa kawai yakeyi ko kallan gefenta baiyi ba...
Tun fitarsu mommy ta daɗe tana saka da warwara, sannan ta koma dakinta ta kwanta cikeda kwarin guiwarta...
A kofar gidansu afnan Habib ya sauke ta, harta fita zata shiga taji ya dako mata tsawa.
A firgice ta juyo tana zaro dara daran fararan idanuwanta da suka nuna tsoro karara a cikinsu, fuskar nan tashi babu fara'a yace "zan dawo mutafi saura idan kinga dama kuma ki tafin".. bai jira amsar taba ya tayar da kura yabarta nan a tsaye kamar an dasa ta...
"Ikon Allah kamar wanda zaibar kasar nidai tunda ka sauke ni can ka karata..." Ta shige gidan tana buga uban tsaki...
Afnan taji dadin ganinta, hirar sosai sukeyi har yayan afnan ɗin ya shigo yana faɗin "zan iya zama ayi dani.."
Afnan ce tace eh mana yaya Kabir, jiddah bataso hakan ba dan yadda ya kafeta da ido kamar zai cinye ta.
Kabir Mutum ne wanda babu ruwan shi yana da saurin sabo ga fara'a aikuwa tuni jiddah ta saki jiki suna hira kamar sun saba,, sam Kabir baiyi wasa da damar shi wajan baiyana wa jiddah abinda ke ranshi ba,....
Ba bata lokaci jiddah ta amshi soyayyar shi danta fahimci Kabir gwani ne wajan iya soyayya......
Babban hospital ne wanda yaji kayan aiki, an kayata shi sosai da manyan ma'aikata masu sanin makamar aiki, Habib yaji dadin ganin yadda asibitin yake dan komai yadda yaso haka ya kasance, saida yagama shirya komai sannan ya wuce gidansu Sultan wanda ya dameshi da kira akan yazo ya taya shi tsara yadda auran nashi zai kayatar....
Habib yana zuwa Mama (mahaifiyar Sultan) ita kaɗai ya samu a palour.
Gaida ta yayi sannan ya tashi zai nufi ɗakin Sultan.
"Wato Habibullah saida bikin abokinka yazo sannan kasan kazo gidan ko, ina fatan dai kaima naka na hanya" Mama ta faɗa tana dariya.
Murmushi kawai Habib yayi sannan ya nufi ɗakin Sultan ɗin baice komai ba dan yasan yanzu Mama faɗa zata farayi masa..
Zaune yake saijin shirmen Sultan yake yi harya gama sannan yayi gyaran Murya yace "kaga Malam kabar duk wani abubuwan daka Jero kayi dinner kawai is enough for you..." Ya faɗa yana ci-gaba da kallan wayarshi.
"Nifa daman nasan wlhy shawara dakai sainaji haushi ka tsaya muyi magana yadda zan fahimta saika dinga wani abu kamar wanda bayasan bani shawarar..."
Murmushi Habib yayi yace "shikenan kaje kayi duk abinda zakayi ba saika nemi shawarata ba" ya tashi ya nufi hanyar fita.
Sultan ma tashi yayi yabi bayanshi yana faɗin muje nima na gaida mommy kwana biyu bana zuwa, kaima Mama tayi fushi wai baka zuwa saida bakina yazo...
"Ai naji zata farayi min faɗa ɗazu"
Daga haka suka shiga motar Habib suka fice.
Kai tsaye gidan daya sauke jiddah ya nufa, cikin Sa'a ya gane gidan batareda yasha wata wahala ba, Sultan dai na gefe yana mamakin abinda yasa Habib zuwa gidan.
Mai Gadi ne ya fito jin anata horn kuma motar taki shigowa, "ya akayi ne ko wani ake nema?"
"Amm... Baba dan Allah bakuwar dana kawo za'a kiramin.."
"To shikenan bari naje saina sanar mata" mai gadin ya faɗa yana shigewa gidan..
Lokacin jiddah na zaune itada Kabir suna zuba soyayyar su, dan tuni afnan tabasu wuri.
Ganin mai Gadi ne yasa Kabir yace "ya akayi baba".
"Wai jiddah ta fito ana jiranta a waje"
Ai kafin ya ƙarasa jiddah ta tashi tana ɗaukar hand bag ɗinta.
Sallama tayi masa zata fice "ki bari na raka ki Compound Mana"
"A'a Nagode, ka fadawa mamee da afnan na wuce" bata sake magana ba ta fice.
Habib harya fara kuluwa jin shiru cikeda fushi ya buɗe motar zai fice saiyaga ta fito,.
Sultan da mamaki ya kafe shi dan baiyi tunanin jiddah suka zo ɗauka ba, tunda yasan bawani shiri takeyi da Habib ɗin ba.
Tana shiga motar ya tayar suka tafi kamar kurame ita kuwa a tsorace take yadda ya haɗe rai tasan ta shiga uku dan cewa zaiyi ta bata masa lokaci.
Suna zuwa gida shida Sultan suka wuce part ɗinsa, ita kuma ta nufi part ɗinsu tana sauke ajiyar zuciya dan ta kubuta Allah ya taimake ta dan jarabar baiyi mata kome ba.
Tana shiga mommy tayi mamaki dan batayi tunanin Habib zai dawo da ita ba, hibban kuwa da murmushi yace "kanwata yanzu mommy take cewa naje dauko ki"
Dariya tayi tace "dama nasan yayana da mommy na hankalin su na kaina" ta faɗa tana kwanciya gefen mommy daketa faman murmushi.
"Waya faɗa Miki na damu, kawai banaso naga abokiyar tsokanata bata kusa ne" ya faɗa yana makewa..
Gwalo tayi masa tana fadin "nadai gano"
Tsuke fuska yayi sannan ya tashi yana yin hanya fita "nama fasa baki wayar dana siyo Miki"
Aida gudu jiddah tabi bayanshi tana bashi hakuri, amma yayi fuska yace saita durkusa.
Haka dai hibban ya dinga tsokanarta sannan ya ciro sabuwar ƙatuwar waya ya bata.
Tsalle tsalle tafara yi tana ihu a bakin palourn,.
Sam batasan Habib ya taho shida Sultan ba saiji tayi ta bige mutum a bayanta...
A firgice ta waigo idanuwan nan nata kamar su fito tsabar kaduwa tuni hawaye ya wanke mata fuska, wanda yaba kowa mamaki. Banda mommy da tabar palourn tun dazu.
Habib kuwa duk da tuni ranshi ya ɓaci mamaki ne ya kamashi ganin tun kafin ya taba tafara kuka.
Sultan kuwa samun waje yayi ya zauna yana kallan yadda take kuka wiwi.
Cikeda takaici da bacin rai Habib yakai mata wani wawan marin dayasa ta zauna bata sani ba tana dafe da wajan.
"Sharri zakiyi min ehh! " Ya faɗa yana kara bata wani marin tareda riko kunnen ta ta miƙar da ita tsaye.
Azaba ce tasa ta saki wani kara wanda yasa Habib saurin toshe kunne tareda rinste ido.
Yana sakin ta tayi sama da gudu wajan mommy tana kuka..
Mommy na ganinta tasan itada Habib ne shiyasa batayi Magana ba.
Gadon mommyn ta faɗa tana kuka rike da wayar da hibban ya bata...
Habib jinjina kai kawai yayi sannan ya fice yana huci kanshi na sara masa Saboda ihun har cikin kanshi yaji shi.
Hibban kuwa sam ji yayi baiji daɗi ba a haka mommy take faɗin suyi zaman tare wanda yasan jiddah ce zata cutu karshe ma ta sake guduwa batareda sanin su ba ina wannan baizai yiyu ba yafice shima daga palourn.
Sosai Sultan ya bashi hakuri sannan ya bashi magani ya tafi....
"Kema jiddah meyasa bakyajin magana ne sau nawa nake faɗa miki ki daina tsalle tsalle amma shine yau ma kikayi ai gashi nan yau kin jama kanki.." mommy tace.
Idanuwanta duk sunyi ja tsabar kuka, "mommy wlhy mommy bazan karaba Amma kiba Yaya Habib hakuri karya dokeni plsss"
"Naji yanzu tashi kije kiyi wanka ki huta to"
Batayi musu ba tanufi dakinta, wanka tayi sannan ta shirya cikin wata goguwar riga baka wacce ta tafi da shape din jikinta ta amsheta sosai.
Wayar da hibban ya siyo mata ta kunna, number shi ce saita mommy da Habib kawai a ciki.
Tsaki tayi tace "me zanyi da numban wannan mugun" har zata goge sai kuma ta barta tana kuma yin tsaki....
Har lokacin dinner yayi sannan mommy tace ta Kira Hibban yazo suci abinci, cikin Sa'a ta taji wayar da kuɗi.
Yana daga wayar tace "yaya hibban muna jiranka fa"..
"Ok gani nan"
Ta katse kiran sannan tace "mommy Yaya Habib fa...."
Kallan mamaki mommy tayi mata "wato bakiyi zuciya ba"
Shiru tayi batace komai ba dan itama batasan meyasa tayi maganar shina .
"Ki kyale shi ko ankira shima yanzu yana cikin fushi bazai zoba" mommy tace... godiya sosai tayiwa hibban sannan ta amshi number mamansu afnan ta wuce dakinta..
Saida suka gama waya da afnan sannan afnan ɗin tace zata ba yaya Kabir number wayanta Dan ya dameta da maganar jiddan.
"Ba matsala ki bashi, kawai" sannan sukayi sallama ta kashe..
Ciwan kan dakyar yabar yayi wanka yayi Sallah sannan ya kwanta yana lumshe idanuwan shi, dan sosai yakejin ciwan kan, magani ya kuma sha sannan ya kwanta amma yakasa baccin.
Mommy kuwa tana shiga ɗakinta ta dauki wayarta ta kirashi.
Jin Muryar shine yasa tace "meyake damunka Habib," ta faɗa a dan firgice.
"Babu komai mommy ciwan Kaine kawai kuma nadan samu sauki.."
A'a Habib bari nasa hibban ya kaika hospital.
Bata jira amsar shiba takashe wayarta.
Tana fadawa hibban yasan dama hakan saita faru sam Habib kamar mai cuta a ƙwaƙwalwa bayasan ihu ko kaɗan hakan na iya samai ciwan kai tun yana yaro.
Da sauri ya tashi ya nufi ɗakin jiddah yace ta kawo masa abinci.
✍🏻✍🏻✍🏻
[1/1, 2:24 PM] Aunty Usee: 🌹🌹🌹
*_DR. HABIBULLAH_*
🌹🌹🌹
*Writing by*
*_🌹 first lady 🌹_*
*WATTPAD* @Ameenafirstladyy
*Kainuwawritersassociation*
10
..... jikin jiddah duk yayi sanyi dan taji dalilinta ne yanzu bashida lafiya, ga hibban duk ya rude.
A haka ta fita palour ta haɗa masa abinci sannan tabi bayan Hibban zuwa part ɗinsa.
Kwance yake idanuwan shi a rufe ya riƙe kanshi da hannu.
Jin an bude kofar ɗakinsa ne yasa ya dan buɗe ido a hankali sannan ya mayar ya rufe.
"Yaya muje hospital pls karka ce a'a" hibban yace cikin tausayin yayan nashi.
A hankali ya sake bude idon nashi, sannan yayi murmushi dan kwantar da hankalin kanin nashi.
"Karka damu Hibban I'm feeling better now"
Sosai Hibban ya takura daga karshe Habib ya rubuta masa magunguna yace yaje ya siyo masa yanzu ya kawo...
Sai yanzu hibban yakai dubansa kan jiddah dake labe a gefe kamar munafuka dauke tiran abinci jikinta a sanyaye.
"Kiyi saving ɗinsa jiddah kafin na dawo" hibban yace yana ficewa.
Yana fita jiddah ta zauna gefen stool ɗin dake kusa dashi sannan tafara zuba masa abincin.
Tura masa gabansa tayi sannan tace "pls Yaya Habib kaci abincin.."
Dauke kai yayi yana daɗa lumshe ido baice komai ba.
Duk yadda taso yaci abincin ki yayi karshe ma yace ta fice mai a ɗaki.
Ba shiri ta fice daga ɗakin sannan tayi tsaki tace "mutum bashi da lafiya ma saiya yi faɗa.." ta wuce ɗakinta ta kwanta sannan ta kira sahibinta wato Kabir suka fara wayar soyayya.
Hibban daya dawo dakyar ya samu yayan nashi yaci abincin kaɗan sannan ya bashi magani yayi masa sallama ya wuce part ɗinsa......
Da sassafe jiddah ta shirya cikin uniform ɗinta, ta fito da ainihin kyaun ta.
Sam batayi tunanin ganin Habib a palourn ba a wannan lokacin ganin wani lokacin sai 11am yake shigowa sometimes.
Gaida shi tayi amma bai kalli inda takeba balle ma tasa ran zai amsa mata.
Itama ko ajikinta tunda ta saba,.
"Jiddah yau amma saikin yi breakfast ko" mommy ta tambaye ta.
"Mommy zan makara fa" ta faɗa cikin shagwaba.
Habib yana jinsu saidai hankalin shi yana kan waya, kallon gefen ido yayi mata sannan ya taɓe baki dan shi yarinyar har mamaki take bashi ga shagwaba ga saurin kuka ga kuma shegen tsoron tsiya amma sai taurin zuciya bala'i.
Tareda hibban suka tafi a jiye ta a school sannan ya wuce office bayan ya gaisa dasu afnan,.
Afnan ce take tayi mata tsiya wai jiya soyayyar tasa ta tafi bata sani ba.
"Ke yaya Habib ne yazo dauka ta, kinsan halin shi dana tsaya yi miki sallama dana shiga uku ai" dariya sukayi mata su suka "lallai wannan yaya Habib ɗin naki ko mu tsoron shi mukeji mutum ba fara'a" inji afnan.
"Kai amfa guy ɗin ya haɗu, ni wlhy dazai soni da bazan damu da halin shiba ko kadan" khairat ta faɗa cikin serious ɗin nan.
Sororo jiddah tayi tana kallanta cikeda takaici da wani irin bakin ciki tace "to Bama zai soki ba gyara ma kiyi hakuri"
Dariya suka sakeyi sannan suka wuce aji...
Habib zaune a gaden ɗinsa, A hankali yake shan coffeen shi, lokaci zuwa lokaci yakan yi murmushi idan ya tuna jiddah yadda take zaro idanuwanta cikin tsoro, sam baiji shigowar Sultan ba, saijin maganar shi yayi a kanshi.
"Me kake tunani ne haka Habibullah."
"Babu" kawai yace yaci gaba da shan coffeen shi.
"Shikenan, next week za'a yi dinner na gama komai lokaci kawai ake jira.." Sultan yace yana zama kusa dashi.
"Hakan yayi" shima ya mayar masa da amsa......
Kwana biyu kenan hibban baya samun dauko jiddah saidai Kabir ya kawota babu wanda ya sani dan ko mommy Bata sani ba,.
Yau lokacin tasowar su nayi mommy tace Habib yaje ya dauko ta daga school,.
Shi kaɗai ya tafi yana zuwa ya tsaya bakin gate din bai shiga ba, jiddah kuwa suna tafe tare da su khairat suna hira suka nufi bakin gate dan bazasu iya school Bus ba, suna fita daga gate din jiddah gabanta ya fadi ganin Habib zaune saman motar shi da alama turawa yayi a nemo ta gashi tasan yanzu Kabir yana kan hanyar zuwa daukar su itada afnan.
Ganin tana kallan waje guda ne yasa su khairat kallan wajan suma sunyi mamakin ganin shiya zo daukar ta.
Tun fitowarsu Habib ya gansu tsaff ya kalle su sannan ya mayar da kanshi kasa kamar bai gansu ba, jiki ba Kwari ta karasa tace "sannu yaya Habib ashe yau kaine kazo..." Bata karasa ba ya balla mata harara sannan ya sauko daga saman motar.
Yanaji kawayen jiddan na gaida shi amma ko kallan inda suke baiyi ba ya shige motarshi.
Sallama tayi musu da sauri ta shiga gaban motar dan ta hango motar Kabir tana zuwa.
Iya mamaki Habib yayi dan sarai yagane motar data tsaya ne yasa take wani sauri sauri, take ranshi yafara ɓaci "lallai kuwa ranki zai ɓaci idan ma samari kika fara kulawa yarinya" ya faɗa a ransa..
Har sukaje gida babu wanda yace komai, yana jinta ta saki ajiyar zuciya ganin sun wuce motar..
Suna zuwa gida ta fice shikuma yaja motarshi a guje ya fice...
Kofar school tasu ya koma saidai Baiga motar ba, kwafa yayi sannan ya koma motar tashi cikeda takaicin rashin Ganin mai motar "waye a cikin motar, meyasa take sauri tabar wajan..." Ya jerowa kanshi tambayoyin da basu da amsa.
Shi sam zuciyar shi bata yadda da kawayen nan nata ba shegu yara kamar munafukai gashi ya fahimci kwana biyu tana yawan zuwa gidansu kawayen nata ko menene dalili...?
Habib cikeda damuwa fal cikin shi yaketa faman tunanin ji yayi kanshi harya fara ciwo sannan ya fara driving ɗinsa tareda Jan wani tsaki "akan me ma nake damuwa" ya sake yin wani tsaki yana dukan steering motar....
Yana gama yin Parking ya wuce part ɗinsa, kwanciya kawai yayi sannan ya lumshe idanunsa yafara tunani kamar yadda ya saba.....
***** ***** ******
Yanzu bikin Sultan ya matso, amma dole ya kale Habib Dan yasan bayasan hayaniya sosai, amma saidai yace dole gobe ya halarci dinner da za'ayi, Habib bai Musa ba ya amince yace zaizo.
"Nifa gaskiya afnan bazani bikin nan ba ina tsoro kar yaya Habib ya sani.." jiddah ta faɗa kamar zatayi kuka.
"Dilla can Yaya Kabir fa kinsan bazaiji daɗi ba tunda shiyace mu raka shi, kuma harda ke yasa akayi mana ankon dinner din ki tambayi mommy zaki kwana anan saimu je bafa dadewa zamuyi ba".
Shiru jiddah tayi sannan tace to bari na kirata.
Wayar mommy ta Kira ta faɗa mata zata kwana gidansu afnan.
Dakyar mommy ta bari,.
Cikeda murna tace "Amma pls mommy karki bari yaya Habib ya sani"
"Shikenan naji ki kula sosai jiddah kuma da sassafe zan turo hibban ya dauke ki".
"To momma byeee" ta kashe wayar...
Murna sosai sukayi, sannan suka fara shirin ganin lokaci ya gabato...
Hibban baiso jiddah zata kwana acan ba, amma dole ya hakura ya kirata yayi mata nasiha akan ta kula da kanta sannan sukayi sallama ya kashe wayarshi.
Fitowar shi kenan daga wanka jikin shi sanye da bathrobe ya nufi mirror yafara kalkale jiki.
Sosai ya shirya cikin wani blue ɗin suit sai faman zuba ƙamshi yakeyi,.
Sumar kanshi ta kwanta luf sai zuba sheki takeyi, sajen nan nashi masha Allah, Habib yayi kyau kamar wani Balaraben Sudan, (Aeisher initial lady, anga saurayi sai tsuma akeyi😂😝)
Dai dai yana daura wrist watch dinshi na gold Wanda ya saje da fatar hannun shi wacce gashi yake kwance luff, kiran Sultan ya shigo.
Tsaki yayi sannan ya daga yayi shiru.
"Waje da ya cika Malam ga yammata tako ina kyawawa kayi maza kazo mana"
Tsaki ya sake yi yace "Kanada damuwa Sultan,".
"Ohhh na manta dawa nake waya fa I'm sorry Habibullah na manta kai ba yammata a gabanka amma pls kayi sauri mana nasan mata da yawa zasu rude wlhy" kafin ya gama yaji kit Habib ya katse kiran.
Sam bayasan zuwan dan dai shi bai iya karya alkawari bane, dan dole yayiwa mommy sallama ya tafi..
Cikin takun shi irin na isa ya shiga motarshi ya kwasheta kamar wanda ake jira..
Jiddah ansha make-up kamar ba itaba da ta saba da light makeup, tayi kyau iya kyau kamar yar tsana, wasu hadaddun gown suka saka itada afnan sannan suka fice dan tuni Kabir ke jiransu...
Suna shiga motar yaja suka fice, jiddah dake gaba sai hirarsu suke yi da Kabir hankali kwance dan yauce rana ta farko da zata taɓa zuwa wani taro....[1/1, 2:24 PM] Aunty Usee: 🌹🌹🌹
*_DR. HABIBULLAH_*
🌹🌹🌹
_writin by_📚✍🏻
*_🌹 Firstlady🌹_*
*WATTPAD*
@Ameenafirstladyy
*_🌈Kainuwa writers Association_*
11
Motarsu na Parking afnan ta wuce batareda data jirasu ba, da kanshi ya zagayo ya ɓude mata motar.
Jiki a sanyaye Jiddah ta fito, Kabir yace "muje ciki" harya juya zai tafi yaga takasa daga ƙafa.
Ji takeyi sam batasan ƙarasawa ciki batayiwa mommy adalci ba data zabga mata karya.
Wani kallo Kabir yabi ta dashi na tsantsan soyayya sannan ya gyara tsaiwa yace "jiddah ko bakyasan zuwan ne na takura miki"?
Girgiza kai kawai tayi batareda tace komai ba...
Habibullah kuwa da shigowar shi kenan fitowa yayi daga cikin lafiyayyar motarshi, rufewa yayi tareda juyowa dan shiga cikin hall din.
Dumm yaji kanshi tareda saurin cire siririn farin glass dinshi.
Tabbas jiddah ce tareda wani wanda baisan waye ba, hasken fitilar dake haskaka wajan ne yasa ya gane jiddan ce dai tsaye duk da kanta a kasa yake...
"Jiddah ki ɗago idanuwanki ki kalle ni kiyi min magana idan bakyasan zuwan ne saina mayar dake gida..."
A hankali ta ɗago kai ta sauke idanuwanta kan nashi, da sauri ta janye su tana kawar da kai dai² saukar idanuwanta cikin na Habibullah.
Lokaci guda gumi ya fara jika mata fuska nutsuwar ta fara kaucewa dan yadda taga ya ɗaure fuska yana jingine jikin motar shi amma idanshi na kansu...
Saida ya gama kallesu sannan a zafafe ya koma motarshi yaja ta da gudun tsiya kamar zai tashi sama..
Tana ganin tafiyar shi ta dawo da kanta wajan Kabir wanda yaketa faman magana tun ɗazu daya fahimci hankalin baya tareda ita.
"Pls Kabir ka mayar dani gida yanzu"
Da mamaki ya kalle ta "lafiya jiddah lokaci guda kin rude haka"
"Pls nidai muje ka mayar dani dan Allah" ta marairaice mai Murya.
Ganin hankalin ta ya tashi yasa Kabir yace ta shiga su tafi,,,, ba bata lokaci ta shige tana jin gabanta na faduwa...
Gudu sosai yake shararawa tuni kanshi ya fara ciwo dan baya daukar pressure sosai, lokaci zuwa lokaci yakan yi ajiyar zuciya tareda wani huci mai zafi.
Kai tsaye part ɗinsa ya wuce ya sakarwa kanshi shower, ya daɗe sannan ya fito.
Saman bed ya faɗa tareda rintse ido yanajin wani zafi a cikinsu musamman idan ya tuna fuskar saurayin dake dauke da murmushi...
Kabir har gida ya kawo jiddah motar na tsawa ta fice bayan tayi masa godiya, jikinta sai tsima yakeyi tana buga gate din mai Gadi ya buɗe.
Ko juyowa batayi ba ta shige sannan Kabir ya tayar da motar shi ya bar wajan zuwa dinner...
Tana shiga ɗakinta ta wuce, wanka tayi sannan ta kwanta hawaye na zubo mata "meyasa nayiwa su mommy karya gashi nan najawa kaina yaya Habib ya ganni" ta faɗa hawayen na sake zuba..
Mommy da batayi bacci ba tayi mamakin jin dawowar jiddah tunda taji bude dakinta da sauri mommyn ta fito dan jin ko lafiya ta dawo.
Jiddah na kwance taji bude dakinta, a firgice ta tashi ganin mommy ce yasa da gudu ta taso ta faɗa jikinta.
"Lafiya jiddah meya faru meya dawo dake yanzu".
"Mommy Dan Allah kiyi hakuri nayi kuskure"
Cikeda mamaki mommy tace "fadamin meya faru".?
Tana kuka ta fadawa mommy gaskiya sannan ta faɗa mata ganin da Habib yayi Mata.
Murmushi mommy tayi sannan tace "kinyi kuskure jiddah meyasa kika yimin karya, dakin fadi gaskiya ma da kaina xansa Hibban ya kaiki ki bari kwanta yanzu bari nake gun Habib ɗin" mommy tace tana kwantar da ita..
A kwance ta samu Habib idanuwan shi a rufe jin alamun shigowar Mutum baisa ya buɗe ido ba.
Zama mommy tayi gefensa sannan ta kamo hannunsa cikin nata.
"Habib" ta kira sunanshi a hankali..
Shima a hankali ya buɗe idanuwan shi tar a kanta amma bai amsa ba..
Murmushi mommy tayi dan yau ta tabbatar da zargin ta akan Habib duk tasan abin mai wuya ne.
"Habib jiddah ta faɗa min komai banaso naji kayi mata wani abin kayi hakuri ka kyaleta dan akwai yarinta a kanta"
Rufe idanuwan nashi ya sake yi gam sannan ya gyada kai kawai baice komai ba.
Mommy kuwa tashi tayi ta nufi ɗakin jiddah wadda tayi bacci tun fitar mommy.
Da sassafe Sultan ya kirashi ya karaci masifar shi Habib bai saurare shiba saima kashe wayar shi dayayi.
Jiddah na ganin shigowar shi sum sum tabar palourn yana lure da ita, taɓe baki yayi tare jan tsaki dan haushin ta yake ji jira yake wani abu ya sake shiga tsakaninsu taga yadda ake ramuwar hukunci.
"Mugu badai shiga sabgar ka zanyi ba Balle ka samu tamari" jiddah tace tana shiga daki.
Hibban kuwa yau da kanshi ya dauke ta suka fice shopping, sun sha yawo sannan ya jibgo mata siyayya, suna zuwa gida mommy tace " waiku bakwa gajiya da yawo ne da zarar kaga bakada aiki sosai saika kwashe ta ku fita.."
"Mommy ita kadai gareni fa kanwata" hibban ya faɗa yana ficewa.
Itama jiddah suna gama Magana. da mommy ta wuce dakinta tanawa mommy dariya wai zatayi bayani ne idan ta auri miji mara fitar..
Sakamakon yau ba makaranta jiddah na zaune itada mommy mai Gadi ya shigo.
"Ya akayi malam isya" mommy ta tambaya.
"Ana kiran jiddah ne Hajiya"
Jiddah gabanta ne ya fadi jin mommy batace komaiba.
Jiki a sanyaye Jiddah tace "to baba" sannan ta nufi ɗakin ta dan dauko mayafinta.
Mommy na zaune ta wuce ta,,.