← Book details Dikko Ahmad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 5

Sashe 5

Dikko Ahmad Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

An sallami Dikko daga asibiti,bayan zaryar da Alhaji Kabir da iyalansa sukai tayi wurin dubasa,ba arziki yabar Faty ko yaushe tana wurin Dikko har aka sallameshi,tare su duka suka koma gidan Aunty Ba.hakuri Alhaji Kabir yaita bawa Abba,kallonsa Abba yayi yace"ya wuce ae,sai dai a tari gaba kawai a Kuma kiyaye irin wannan,wlh nayi niyar daukarwa yarona fansa to sai Kuma naga Kaine shiyasa na hak'ura,amma maganar Aure a barta Allah ya had'a kowa da rabonsa".da sauri Dikko ya kallesa yace"No Abban DK i still luv her,dan Allah kayi hakuri kada ka rabamu"jinjina kai Abba yayi yace"Amma kasan anyi baikonta da Munnir ko".kafin kowa ya bada ansa sukaji muryar Munnir dake shigowa yanzu yace"nikam na hak'ura,Babu amfanin rabasu,insha Allah ni zan auri Aysha inhar ta amince".albarka su kaita saka mashi da jinjina kokari irin nashi.kallon Daddy Ummu tayi tace"to Alhaji ina so kasan yin waka ko film ko rubutu ko makamancin haka muradine ,da cikar buri,zai iya zama kuma mafarkin mutun,Kuma Koda baka da ko sisi hakan baya nufin dan kayi irin sana'o"in nan ya zama kai mabaraci ne,yin hakan wata baiwace daga Allah Wanda ba kuma kowa keda irinta ba sai Wanda Allah yaso ya bawa,ga misali ka gani a kanka wak'a ta zama cikar burin Dikko badan ya rasa komai ba,kasan har jikokinsa ba zasuyi talauci ba Koda kuwa bayayin aekin komai,yabi ra'ayinsa ne Allah yasa mu dace".

*Dole iyaye su canza kallon da sukewa sana'o'in da suke bawa maza auren yayansu,su daina kaskantar da sana'a koya take,Allah shiya halicci mai kudi da talakka komai akan ikonsa ne,Allah yasa mu dace*.

Take a nan aka saka auren Dikko da Faty,Aysha da Munnir,komai ya daidaita,Kuma kowa cikinsu ya d'auki darasi .

Alhmdllh na godewa Allah daya bani ikon gama wannan gajeran labarin nawa,Allah ya yake mani kurakuren dake ciki,Allah yasa Kuma mutane su amfana da abunda suka karanta.

Ayi azumi lafiya jama'ar musulmi baki d'aya.
Jorderh majidadi
Stylish star
Chapter 5 · 0% Book details