← Book details Dikko Ahmad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 5

Sashe 4

Dikko Ahmad Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kawar da kai Daddy yayi ya kalli Ummu yace"kisan yarda zakiyi y'arki ta daina kiramun sunan mabaracin can"kai tsaye yabar wurin."kai Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un,Wai me yake damun Alhaji ne?,baya duba halin da y'arsa take ciki sai kawai ya biyewa wani ra'ayinsa na daban"Aunty ta fad'a.dama bekai ga tafiya ba dan haka ya dawo ya nuna Aunty da yatsa yace"ki shiga hankalinki ,dama Ashe da saka hannunku duk iyan shegen da yarinyar nan takeyi?,to bari in gaya maku ko gawar Faty ce sai an kai gidan Munnir sannan a wuce da ita mak'abarta,ita tayi kad'an ta zubarmun da daraja ta,wannan Sam bazai yiwu ba"ya wuce fuuuu,shiru sukayi yayin da Faty taci gaba da Kuka San ranta,ganin Daddy yabar wurin yasa Aunty tace"yanzu Ummu kina ganin zamu zuba ido yarinyar nan ta mutu?,bazai yiwu ba yaskiya zanyi komai dominta in yaso yamun duk hukuncin da yaga dama".kallon Abdul tayi tace"ka karb'i number Dikko wurin Zainab ka kirasa dan Allah yazo ya ceci ran yarinyarmu"ba wani canza shawara kam ya Kira wayar Dikko,ganin be d'aga ba yasa Zainab kiransa da kanta yana dauka ta fashe da kuka tana fad'in"Yaya Allah gatanan a asibiti,Yaya karta mutu kazo sunanka kawai take Kira Yaya ka taimake mu"."Wai meye kike fad'a Zainab?,yanya kina cikin hankalinki kuwa?".wani kukan ta k'ara fashe mass dashi ta gaya masa in da zai sameta,be wani b'ata lokaci ba ya k'araso wurin.Zainab na hangoshi tayi kanshi ta rungume tare da kara sakin wani kuka."ya isa haka,bana San kukan nan,ae gani nazo komai zaiyi daidai da yardar Allah,ina Fatyman take?"nuna masa d'akin tayi tun a waje ya hango su Umma k'arasawa sukayi cikin ladabi ya duka ya gaishe su.cike da fara'a da mutunta mutane suka ansa kafin Aunty tace"Dikko ka taimakemu yarda Allah ya taimake ka,ka ceci rayuwar y'armu mafi soyuwa a garemu".k'asa yayi da kansa yace"Aunty ae umarni zaki bani ba roko ba,ae kin girmeni".take dukan Wanda ke wurin yaji son Dikko danya k'ara tabbatar masu cewa mawak'a ma suna da tarbiya da Kuma ganin mutuncin manya.har cikin d'akin Abdul yaja hannunsa ya shiga da shi,daidai saitin fuskar Faty ya duk'a a hankali yace"Fatyma,Fatyma".kamar a mafarki taji ana Kiran sunanta da muryar da take muradin ji a ko wanne second na rayuwarta zumbur ta mik'e zaune tana jujuya ido,a hankali ta soma bud'e kyawawan idanuwanta farare tas Wanda ko b'acin rai baya canza masu launi sai dai su dan kumbura kad'an Wanda hakan kyau yake k'ara mata,tun d'aga k'afarsa take kallonsa tanajin zuciyarta kamar zata fito fili harta sauke idonta akan fuskarshi wacce take dauke da murmushi da haske na annuri,hannu tasa ta k'ara murza idonta bakinta na rawa tace"D..i..k..ko"tana nunashi da hannu,hannun nata ya Kama ya had'e da nasa yana murmushi kamar ko yaushe,ido d'aya ya kashe Mata yace"Faty Dikko,y'an Matan Dikko ba mafarki kikeyi bafa,nine dai naki a gabanki yau cikar burinki yana tare da ke".rasa abun fad'a tayi ta kuma kasa dauke idonta a kanshi gani take kamar data dauke ido daka kanshi zai b'ace yayi Mata yarda ya sabayi a mafarki,hannunsa ya had'a tare da bugawa a gaban fuskarta yace"bafa mafarki kikeyi ba farin cikina".wasu zafafan hawaye ne suka soma zarya akan fuskarta a hankali ta furta "Alhmdllh ya Allah".b'ata fuska Dikko yayi tare da shagwab'e fuska yace"ni gaskiya bana son kukan nan"yasa hannu yana share Mata hawaye,fad'awa tayi cikinshi ta kuma sakin kuka da k'arfi.bashi da zab'in daya wuce ya karb'e a wannan lokacin dan haka ya saka hannuwansa tare da soma bubbuga bayanta a hankali a kunne ya rad'a mata"Farin cikina zanyi kuka nima inhar baki daina ba,inajin kukanki tamkar ana soyamun zuciyata,kedin kaddaratace,kedin tawace bana da wani burin daya wuce na sameki a matsayin matana tun daga lokacin Dana daura idanuwana akanki,kedin ta dabance Kuma kinyi daban,to dan Allah a sassautawa zuciyata wannan wahalar da ake bata bana bukatar kukan nan".kamar an ingizoshi haka ya shigo d'akin yace"karya kakeyi mabaraci,mai shirya zance nanma din studio ne ?,ni Alhaji kabir zaka yaudarar wa y'a harka wuce ko ina ka k'araso inda take kana makaskanci Wanda sai ka sayar da muryarka kake samun abunda zakaci kai da iyayenka sannan Kuma kazo wurin y'ata?.wayarsa ya dauka yayi magana kad'an babu Wanda yaji abunda yace kawai sai ganin y'an sanda sukayi sun shigo da yawa,kai tsaye kan Dikko sukayi suka hau kansa da duka kamar Allah ya aeko su.wani irin razannaniyar k'ara Faty ta saki ta fad'a akan Dikko tana kare masa duk dukan da aka kawo,rungumesa tayi kwarai taki ta sakeshi,kuka su Ummu suka saka Aunty tace"Alhaji ka duba girman Allah ka hana dukan nan,yaran nan be aekata maka komai ba"."ke kiyimun shiru,kema ina zuwa kanki dan dole ki karb'i hukuncin karya dokata".da kyar aka banbare Faty daga jikin Dikko tana ganin y'an sanda sun kwashesa jina jina ta sulale wurin a sume.shikam a mota kamar zasu zare masa rai dan tsananin dukan da sukeyi har suka isa office dukanshi sukeyi kafin suka jefashi cell.Ummu kasa cewa Daddy komai juyawa kawai tayi tabar masa d'akin.waya Zainab ta dauka ta Kira Aunty Balaraba dan Yaya Aliyu ya tafi gida tun d'azu a can police station suka had'u ,idanuwan Zainab sun kumbura sunyi jajir saboda tsabar kuka.ko da suka shiga da ky'ar aka basu damar ganinshi,Aunty B na ganin yarda duk jikinsa ya fashe dama ga jikin Dikko ba San wahala yakeyi ba hutu ya gama ratsa shi,ta saki kuka tana tab'a fuskarshi data kumbure lokaci d'aya tace"me suka yi maka ?,wannan Sam ba adalci bane ba"cikin dauriya da rashin son nuna ba damuwa ba yace"Aunty B kada ku damu ni tawa jarabawar a soyayyah kenan,komai zai wuce".girgizashi Aunty B tayi tace"kayi hauka ne?,ka gaya masu baka son Faty,ae ba ita kadaice autar Mata ba,kana da kudin da kyau da ikon da duk macen daka taya zata soka,ko cikin wad'anda suke kawo maka kansu Dikko zaka iya zab'a,me Alhaji Kabir ya tara bare harya wulak'antaka haka,yako san ko kai d'an waye?,sannan kai kanka meka mallaka?"."ya isa Aunty maganar so akeyi ba alfahari ba,Aunty bazan it's rabuwa da Faty ba,Kallo d'aya na Mata na kamu da matsanancin sonta,dama ae komai ya gaji jarrabawa to zan jure ko wacce iri ce,rayuta fansace akan soyayyarta".basu k'ara wata magana ba aka janyeshi aka mayar dashi Cell,da kuka suka fito wurin,cikin kyarma Aunty B ta Kira Abba a waya ta shaida masa abunda ke faruwa.a razane ya mike yace"bazai yiwuba ,bazan tab'a d'agawa Wanda ya wulak'anta D'ana haka ba ko waye shi"."me yake faruwa Alhaji?"Ummi ta tambaya,kallonta kawai yayi yace "ki dauko gyalenki zamu Kama hanya yanzu"kawai ya fice.Ummi Kam sai faduwa gabanta yakeyi gashi ya ki gaya Mata komai.tunda taga sun nufi hanyar kano zuciyarta ta cinke tunanin mafi soyuwar yaranta takeyi kawai Dikko.cikin y'an awanni suka isa Kano,dan ba k'aramin gudu Driver din yayi ba nisa umarnin Abba,kai tsaye gidan Aunty B suka wuce ,ba wani b'ata lokaci ta gaya masu abunda ke faruwa,Kuka Ummi ta saka tace"sai da nace karyazo,meye wata Faty yarona da ko magana bayayi shine aka wulak'anta haka saboda mace?"."ki kwantar da hankalinki zasuga Dikko yana da gata,zasuga Uba irin Wanda ake ado dashi,tabbas yau sai sunyi Dana sanin tab'amun D'ana".daga shi sai Zainab da masu tsaranshi suka je police station din.tun daga waje manyan mutane da manyan y'an sanda suke tarbarshi da gaishe shi suna bashi girma, office inspector Anas aka kaishi danshi yakeyin case din,bak'in k'ofa ya tsaya,da sauri Alhji Kabir ya mike yace"a'a ranka ya d'ad'e,yau kai da kanka a garin namu,naga munyi waya d'azu baka cemun zaka shigi ba Kuma".murmushi ya sakar masu ya k'araso ciki tare da zama musabaha sukayi yace"wallahi zuwanne babu tsari a gaggauce ya kamani,D'an wajena aka Kama a nan"."subhanallah aeda kayi waya zanzo na karbeshi da basai kazo ba".shigowar Zainab yasa kowa d'agowa turus tayi ganin yarda Abba da Daddy suke gaisawa tace"Abba kabar gaisawa dashi,shine ya Kama Yaya Dikko yasa aka masa duka ,yana ce masa mabaraci dan yanayin waka".kallonsa Abba yayi amma bece komai ba, inspector Anas ya kalla yace"a kawo mun Dikko Ahmad"wani irin xaro ido Daddy yayi sai yanzu ya tuna da sunan Dikko Wanda yawanci komai na Alhaji yake da sunan yaron,sai yanzu tunaninsa ga kawo masa cewa Dikko shine yaron Alhaji Ahmad Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un in haka ne tabbas ya tabka babban shirme,ganin yarda aka janyo Dikko ya bugu da ky'ar yake iya d'aga kai yasa Alhaji Ahmad mik'ewa da sauri yayi kanshi yana Kiran"Dikko shine aikayi maka haka?",Dikko Kam jikin Abba ya fad'a tare da sumewa.farar rigar jikin Abba dukta b'aci da jini,d'aukar D'an nasa yayi be kula takan kowa ba yaui mota da gudu da shi kai tsaye asibiti suka nufa akayi Emergency dashi,Babu abunda Dikko yake Kira sai sunan Faty.."hajiya nayi kuskure, Alhaji Ahmad shine karfin arzikina shine Wanda da taimakonsa na kai wannan mataki har gobe shi take bani kaya,shi yake bani kudaden da nake juyawa ina d'aukar ribar". murmushi kawai Ummu tayi tace"ae ba'a yanke hukunci da zafi haka,kaga yarda ake musaltawa ko kusa baka tara abunda Dikko ke gareshi bama balle Kuma mahaifinsa".
After 1 week
Chapter 4 · 0% Book details