← Book details Dikko Ahmad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 5

Sashe 2

Dikko Ahmad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwance take tayi rubda ciki tana jin wak'ar na ratsata tako ina,shigowa Salma tayi d'akin tana kiran"Ya Faty,Ya Faty"amma shiru zare ear piece din kunnenta tayi tace"aeta magana bakiji Yaya Faty".
Wani uwar harara Faty ta zabga mata tace"bansan Iskanci Salma,wai ke bazaki daina mun irin haka ba ko?".
"Kiyi hakuri dama Yaya Aysha tace na duba ko kin shirya zakije wurin taron".
Tsaki Faty taja a hassale tace"bazanje ba,kuyi tafiyar ku".juyawa Salma tayi ta tafi ba jimawa saiga Yaya Aysha ta shigo kallonta tayi tace"dallah tashi ki shirya,kinsan taron yana da mahimmanci Kuma zaki iya ganin masoyin naki a wurin,kinsan taron manyan mawak'a nefa".
Zunbur Faty tayi ta diro da sauri tace"wallahi Yaya na manta banyi tunanin haka ba "da gudu ta fad'a toilet.

Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe.

Stylish star
Jorderh majidadi

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*DIKKO AHMAD*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

Na
*Maryam ismail majidadi*

*_________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*

Page 3

Dedicated to DIKKO AHMAD (DK Excellency)

*Happy birthday Hayat Baba zubair,Allah yaiwa rayuwa albarka*

Cikin mintina kad'an Faty ta shirya tsab cikin tsadaddiyar leshinta kamar ruwan madara bubu ce rigan tayi masifan yi mata kyau sai pattern din pink ,hakan yasa shoe da mayafinta da bag suka kasance pink ,lite make-up tayi amma ta haska sosai sai zuba k'amshi takeyi,kamar wacce zataje gasar kwalliya,kallonta Aysha tayi tace"Masha Allah kai,Faty wannan kyau haka?,Anya mun kera dake kuwa?",dariya Faty ta saka tace Yaya muje kada lokaci ya k'ure mana.sun isa akan lokaci dan haka suka shiga tare da samun wuri suka zauna Faty kam sai raba ido takeyi.babu b'ata lokaci aka fara program din,anyi jawabi sosai akan illar Fyad'e ga mata da matakan daya Kamata a dauka sannan mawak'a suka fara baje basirarsu a wurin,lokacin da kunnuwanta sukaji an ambaci sunan Dikko Ahmad a matsayin mawak'i na gaba wani irin bugawa gabanta yayi da k'arfi duka tsigar jikinta ya tashi da k'yar ta hadiye numfashi ta mik'e tsaye zunbur tana fara kallonshi tun daga k'asa,sanye yake cikin gizna blue colour sai shoe covers bak'ak'e ,hulace dara ya murza a kansa ita kalar bak'a ga tsadaddiyar agogon hannunsa ,lokacin da idonta yakai akan fuskarshi batasan ta saki hawayen farin ciki ba,yaune rana ta farko a rayuwarta data tab'a ganin mamallakin zuciyarta,ji takeyi duk duniya babu Wanda ya kaita sa'a ko farin ciki a yau,duk abunda takeyi Yaya Abdul da Yaya Faty na kallonta ganin abun zaiyi yawa yasa Yaya Aysha girgizata tace"Wai meye haka?ki zauna dan Allah kada ki bada kanki a wurin nan".ina ko jinta Faty batayi idanuwanta da hankalinta suna ga Dikko ga wak'arsa dake ratsa duk wani sassa na jikinta(ga masu buk'atar wannan wak'a ko wak'ok'in sa zasu it's tuntub'ar wanann number kamar haka 07033636337).samu tayi ta zaunar da ita amma gaba d'aya Faty ta gama zauncewa da susucewa a wurin,neman hanyar kaiwa ga Dikko kawai takeyi shine zai iya sakawa ta samu sauki a zuciyarta.harya gama ya koma ya zauna amma bata daina binsa da Kallo ba.
Da misalin k'arfe 6 na yamma taron ya tashi,juyowar da Salma zatayi taga babu Faty wayam a inda suke,zaro ido tayi tace"Yaya ina Yaya Faty,badai ta tafi wurinsa ba?"."Salma nima ina zan sani kin dai san halinta ae".
Takawa takeyi a hankali harta k'arasa inda yake tsaye da yaransa,kasa furta komai tayi sai kawai taji wani kuka ya sub'uce mata tayi saurin toshe bakinta da hannunta,Dikko kam tunda ya kalli inda take sau d'aya be Kuma kallonta ba yaci gaba da aekin danna wayarsa.Zainab dake bayansa sarai ta gane Faty Kuma tasan halin Yayan nata dan haka ta fito da sauri taja hannun Faty gefe tace"meye kike k'ok'arin yi?,Wai abun har yakai haka?"Zainab ta fada.kukan Faty ta ida saki tace"Zainab zan mutu idan be kulani ba,tabbas mutuwa zanyi,ki tab'a zuciyata kiji yadda take harbawa,dan Allah ki taimakeni kada ya tafi banyi magana dashi ba".zaro ido Zainab tayi tayi matuk'ar tausayawa Faty duk ajinta da kyanta da irin mazan dake binta amma yau itace take kuka akan wani D'a namiji.hannu tasa ta goge mata fuskarta tace"ki nutsu zamuje ku gaisa yanzu,nayi maki alk'awari komai xaiyi daidai"godiya Faty ta soma zubawa Zainab kamar wacce tayi mata wani aeki,hannunta taja har zuwa gaban Dikko tace"uhm ga bak'uwa zaku gaisa,k'awatace".ya dauki tsawan minti ukku kafin ya d'ago ya sauke fuskarsa kan Faty yad'an saki fuska yace"bak'uwa sannu".ji Faty tayi numfashinta zai dauke lokacin dataji muryarsa ,murya na rawa tace"ya...yauwa,ina wuni".da lafiya kawai ya ansa,daurewa tayi tace"wak'a yayi Allah ya k'ara basira,sunana Faty".murmushi ya Kuma sakar mata yace"nice name,n gode,sai anjima"ya juya yayi gaba abunsa.wani ihun dadi Faty ta saki ta fad'a jikin Zainab tana saka mata albarka.da k'yar su Yaya Abdul suka jata zuwa gida sai da yayi mata alk'awarin zai samo mata number din Dikko sannan ta yarda suka wuce gida,sai zuba masu surutu takeyi a kanshi tana washe baki.
Suna shiga gida da Daddy suka ci karo a parlo,gaishesa sukayi har zasu wuce ya Kira Faty tare da ajiye jaridar dake hannunsa yace"ki shirya anjima zakiyi ba'ko yaron aminina ne Alhaji Abbas wato Munnir zaizo ya ganki zamu saka ranar aurenku in Allah yaso next week"be kula da yanayin da take ciki ba ya mike ya fice abunsa.wani uban ihu Faty ta saki ta fad'i k'asa tana rike saitin zuciyarta ta fara rolling a k'asa tana k'walawa Umma Kira.

Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe
Stylish star
Jorderh majidadi
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*DIKKO AHMAD*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

Na
*Maryam ismail majidadi*

*_________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*
A gigice Umma da Aunty Amarya suka fito suna tambayar ko lafiya,cikin sauri Aunty Amarya ta k'arasa gareta tace"Shima dai Alhaji sai da na fad'a masa kada yayi wannan kuskuren"dafe zuciya Faty takeyi tana fad'an"Aunty wallahi bana sanshi mutuwa zanyi,dan Allah ku cewa Daddy a'a,ni dai ya barni".Umma kam mutuwar tsaye tayi dan bata tab'a tunanin abun zai kai haka ba,da k'yar Yaya Abdul ya lallashe suka samu bacci ya dauketa kowa yana hango gagarumar matsalar dake doso gidan.
Zama Zainab tayi tsakiyar Dikko da Aliyu tace"Yaya kaiwa Ya Dikko magana dan Allah ko sau d'aya ya saurareni mana",kallonta Aliyu yayi yace"akwai wata matsalar ne?",shikam Dikko wayarsa yake latsawa kamar bema san Allah ya halicci mutane a kusa da wurin ba,a zahiri wayar yake latsawa amma sam a cikin zuciyarsa surarta yake gani ,gizo kawai takeyi masa,tunda ya sauke idanuwansa akanta ya tsinci kansa da matsanancin sonta a yanzu baya gane yareyen da sukeyi nema Faty kawai yake maimaitawa a ransa."Yaya k'awatace ke San Yaya Dikko,wallahi ina tausayinta ban tab'a ganin wacce take yin so irin haka ba, yarinyar nan tana da tarbiyyah bata rasa komai ba,amma da tazo gaisheshi baka ga yarda ya ansa mata ba "ta k'are maganar cikin shagwab'e fuska kamar zatayi kuka.murmushi Aliyu yayi yace" to ke meye naki a ciki?,ki lallab'ashi ki gane ko yana santa shine kadai mafita". girgiza hannun Dikko tayi tace"Yaya pls"cikin basarwa yace"me Kuma ya faru sarkin rigima?"kuka Zainab ta saka tace"Yanzu Yaya baka ma san me nake cewa ba"ta daura hannu saman kai zata fasa masu ihu.ko kad'an Dikko baya son hayani gashi yana matuk'ar son Zainab da sauri ya toshe mata baki yace"lil dan Allah ki rufamun asiri ban shirya ciwan kai ba yanzu,ki gayamun meye kike so?".turo baki tayi tace"Yaya kace kana santa,wannan wacce mukazo kuka gaisa"."to Zainab in banda abunki ni ya za'ae na gane Mata nawa sukazo gaisheni?,bazan iya tunata ba,amma indai tayi maki ,to bana da matsala da wannan".tsalle Zainab ta daka ta rungume Dikko tace"that's why I luv u sweetheart".wayarta ta dakko ta soma nuna masu hotunan Faty,Aliyu yace"masha Allah".kawar da kai Dikko yayi yana yatsina fuska yace"nifa basai na wani ganta ba"ya mike zai bar wurin.cikin sauri Zainab tace"Yaya dan Allah kayi mata wak'a ina so sakon soyayyarka ya isa gareta ta wata hanya daban".kai kawai ya gyad'a mata ya wuce d'akinshi,yana shiga ya jingina kansa da k'ofar d'akin wani k'ayataccen murmushi ya saki tare da dafe saitin zuciyarsa yace"Faty,Fatyma,tabbas ina zuwa gareki,Kallo d'aya nayi maki na gane kinyi daban da saura,kedin bugun zuciyata ce".ba k'aramin farin ciki ya kasance a ciki ba,kawai ya soma raira mata wak'a.
Da yamma Aunty ta lallashi Faty ta shirya cikin atamfa riga da siket tayi matuk'ar kyau duk da idanuwanta a kumbure suke saboda kukan da tasha.mayafi Aunty ta yafa mata tace"kije kiga bak'on bana son ran Daddynki ya b'aci in yaso daga baya ni zanyi masa bayani da kaina cewa baki sanshi,amma sai kinyi mun alk'awarin bazaki kuka ba ko Kuma wani abunda bai dace ba". gyad'a kai kawai Faty tayi tana k'ok'arin mayar da hawayen dake son zubowa ga xuciyarta dake bugawa da k'arfi.kamar marar lakka haka ta nufi d'akin da Munnir yake,can ciki tayi sallama tun kafin ta shiga k'amshin turarensa ya cika hancinta k'arasa tayi ta zauna can nesa dashi d'ago kanta tayi ta kalleshi babu laifi babu wacce zata kalli Munnir tace beyi ,katse Mata tunani yayi da cewa"Malama Fatyma barka da yamma,fatan na sameki lafiya?".can ciki tace"Alhmdllh ,Ina wuni".da lafiya ya ansa sannan yaja dogon numfashi yace"ina tsammanin kinsan dalilin zuwa nan wurinki?"gyad'a masa kai akwai tayi .yace"baki zaki bud'e kiyi magana,nikam dai Alhmdllh kinyi mani Kuma ina fatan zaki karbeni hannu bibbiyu".hawayen da take b'oyewa ne suka zubo cikin rawar murya tace"Munnir kayi hakuri,babu maccen da zata ganka tace bata sanka ko Kuma bakayi mata ba,sai dai ina mai baka hakuri na riga na kyautar da zuciyata bana tunanin zan iya k'arbota daga inda na badata ,da hakan zai yiwu dana hak'ura na faranta ran mahaifina,sai dai Kuma na gagara yin haka,kayi hakuri"saurin toshe bakinta tayi jin kuka na niyar kwace mata tayi waje da gudu,kai tsaye d'akinta ta shiga ta saka key ta fad'a saman bed ta rushe da kuka mai cin rai.
Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe
Stylish star
Jorderh majidadi

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*DIKKO AHMAD*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

Na
*Maryam ismail majidadi*

*_________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
Chapter 2 · 0% Book details