← Book details Dikko Ahmad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 5

Sashe 3

Dikko Ahmad Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*
Shiru Munnir yayi yana tuna kalaman Fatyma,harga Allah yaji yana matuk'ar sonta sai dai ya hango tsantsar gaskiyarta a kwayar idonta,to waye wannan Wanda take so?,yayiwa kansa tambayar da bata da ansa,jiki ba kwari ya mike yabar gidan.
Babu yarda y'an gidan basuyi ba akan Faty ta bud'e k'ofa amma sam ta k'iya hasalima shiru tayi ta gyalesu,cikin kankanin lokaci wani irin zazzabi da ciwan kai suka rufeta da k'yar take iya d'aga ido kwananta biyu a d'aki rufe,in taji jinwa sai dai ta sha chocolate da biscuits da take ajiyewa duk ta rame ta fice a hayyacinta .
Kayane riki riki aketa shigowa dasu Kama daga biscuits,sweet da dai sauransu kaya jibge aka ajiye a parlon sama,kallon Daddy Ummu tayi tace"wannan kayan Kuma fa na menene?".sai da ya zauna sannan yace"kayan saka ranar auren Fatyma ne da Munnir nan da 2weeks za'ayi bikin".ba Ummu kadai ba sai da kowa ya raxana a wurin,Faty da tun shigowar Daddy take lekensu ta window ta saki ihu ta soma b'ari da duk wani kayan daya tari gabanta,kwalaben turare taketa jifa dasu duk abunda ya tari gabanta sai ta zubar dashi,kwalba duk ta fashe mata hannu jini yanata d'iga,muryarta ta dishe tsananin tashin hankali ko hawaye d'aya ya kasa d'igowa daga idonta,kawar da kai Daddy yayi lokacin da kowa yayi wurin d'akin yana bubbuga k'ofar tare da Kiran sunanta,tashi yayi yabar gidan gaba d'aya.
Shigowar Zainab kenan gidansu Faty dan tanata gwada number dinta amma a kashe,ita da gudu ta k'arasa saman tace"Ummu lafiya?,meyake faruwa ne?".hawaye kawai kebin kuncin Ummu ta kasa furta komai cikin Kuka Salma tace"Yaya Faty ce yau kwana ukku tana rufe a d'aki,Wai dan Daddy ya saka ranar aurenta da Wani,gashi sai jiwa kanta ciwo takeyi".ba k'aramin firgici Zainab taji ba,buga k'ofar tayi da karfi tace"Fatu ki saurareni kada ki illata kanki,indai Yaya Dikko ne kin samu kin gama yanzu ma shine ya aekoni wurinki,ki saurareni dan Allah,Shima yana matuk'ar sonki kinji"tunda Zainab ta ambaci sunan Dikko Faty ta tsaya cak sai dai ta kasa motsawa daga inda take.zainab taci gaba da cewa"baki yarda dani bane yanzu zakiji shaida",da gudu ta koma cikin parlon hannunta na k'yarma ta kunna CD din da tazo dashi ta saka volume yarda zai kai har wurin Faty.
Na tantance bugun zuciyata Fatyma ce take rud'ani,dan Allah ki yarda na turo gidan ku dan ayo mana baiko,duk cikin sahun y'an mata Fatyma ke nasa a gabana ,Babu ke a tare Dani ki sani tamkar bulo sunana.
Haka taji muryar Dikko yana ratso ko wanne sak'o na jikinta yana sakar mata kalamai dake fallasa sirrin zuciyarsa zuwa gareta.ae da gudu ta k'araso kofa ta fito bata kula kowa a wurin ba tayi parlo,tsayawa tayi tana kallon TV din kamar zata gano Dikko a ciki,duka tsigar jikinta ya gama tashi sak'onninsa suna ratsa duk wata kafa ta jikinta.cikin rawar murya wadda tasha kuka bata fita sosai tace"I...n...a kika....gan...shi".Kama hannuwanta Zaibab tayi tace"ki tuna nace maki Babu abunda bazan iyayi saboda ke ba,Dikko Yayana ne uwa d'aya uba d'aya,na tsaya ne inga wanne irin so kike masa shin ya cancanci na baki shi,Kuma naga Babu wata y'a mace data dace da Yayana bayan ke,Ina maki albishir da cewa Yayana yana matuk'ar kaunarki".
"Never,abunda bazai tab'a yiwuwa ba kenan in har ina da rai,bazan tab'a aurawa maroki kaskantacceba y'ata mafi soyuwa a gareni,har abada hakan bazata faruba,meya mallaka ?meke gareshi?,ko matsayin mai aekin gidan nan be kaiba balle kuma ya nemi auren Faty,wannan wani shirmene kukeyi,hakan bazai faru ba".wani irin gigitacciyar k'ara Faty ta saki ta fad'i a wurin sumammiya.
Da gudu sukayo kanta,Aunty Amarya ta fashe da kuka tace"mun gaji da wannan ra'ayin cutar da yaran naka,shin kaima ae Allah ya baka kud'in,kuma Shima baka San tanadin da Allah yayi masa gaba ba,zaka kashe y'arka da kanka saboda wani ra'ayi na daban".ganin Faty bata numfashi yasa suka kwasheta sai asibiti kai tsaye akayi Emergency da ita.ko da ta fara farfadowa Babu abunda take fad'a sai sunan Dikko kawai.
Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe
Stylish star
Jorderh majidadi
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*DIKKO AHMAD*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

Na
*Maryam ismail majidadi*

*_________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*
End
Chapter 3 · 0% Book details