Sashe 1
Dikko Ahmad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*DIKKO AHMAD*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
Na
*Maryam ismail majidadi*
*_________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*_________________________________*
Bismillahir rahmanur rahim
Dedicated to DIKKO AHMAD (DK Excellency)
Gajeran labari
Page 1
Tsayawa Ummi tayi jikin k'ofar d'akin D'an nata tana murmushi,matace da bazata gazawa shekara 45 ba tasha wanka cikin tsadadden leshinta juyanta da hannayenta duk gwalagwalai kallo d'aya zaka mata kasan cewa dukiya ta ratsata da Kuma hutu,k'arasa shigowa tayi cikin d'akin ,ko kad'an beji shigowarta ba,sai da ta k'araso ta janye head phone din da yakebin wak'ar daya rairai,bud'e lumsassun idanuwansa yayi masu Kama dame jin barci ya saukesu akan Ummi din tashi,fara'ar fuskarsa ta yawai yace"Ummi yaushe kika shigo?",zama tayi gefen bed din tace"DIKKO ya za'ayi kasan na shigo kana nan kana sana'ar taka"gyara zamansa yayi tare da sosa kai yana dariya yace"Ummi kinsa wak'a fa burina ce,kuma farin cikina",gyad'a kai tayi tace"nasan wannan,Kuma kasan ni da Abbanka da y'an uwanka duka muna goyon bayanka ,tunda haryin wak'a besa ka watsar da karatunka ba,yanzu ka tashi muje kaci abinci saika dawo ka daura daga inda ka tsaya"hannunsa ta ja zuwa main parlo na gidan.Dikko kyakyawan namiji ne,ba fari bane ba kuma zaka kirass bak'i ba,dogone sai dai ba zaka kirasa mai jiki ba,a ko wanne gefen fuskarsa yana da alamar lotsawa wato dimful,fuskarsa dauke da saje Wanda ya k'ara k'awata kyawun fuskarshi,dai dai gwargwado DIKKO namiji ne Wanda ko wacce mace zatayi burin mallaka a matsayin mijinta.su ukku ne a wurin Mahaifinsa Alhaji Ahmad Canji,babban yayansa Aliyu sai shi sai kuka k'anwarsu Zainab.suna cikin farin ciki da k'aunar junansu,a parlo suka samu duka y'an gidan nan fa suka fara fira ba k'akkautawa cike da zallar soyayya suke gabatar da komai.
"Fatyma wai yanzu ba makaranta zakije ba?,shine kika tsaya kallon wak'a a TV"Umma ta fad'a rike hab'a.
Wacce aka Kira da Fatyma ta juyo da sauri ta kallon Umma,ganin Umma tayo kanta yasa tayi waje da gudu tana dariya.Dariya Abdul ya saka yace"kai Umma har yanzu baku daina wasan kwaikwayon nan ba kenan?",dawowa Umma tayi ta zama a d'aya daga cikin chairs din parlon tace"wallahi Abdul abun yarinyar nan harya fara damuna,ada ina dauka yarinta ce,ashe ba haka bane bata da abunyi saijin wak'ar wannan yaron ,inko taga pic dinsa ko video dinsa yadda kasan zatayi hauka haka take komawa,ina tsoron ranar da Daddynku zai iya gane wannan nasan daga ni har ita bazamu tsira ba".sosai Abdul ya tattaro hankalinsa ga Umma yace"kedai kiyi mata addu'a kawai,sannan Kuma yadda Daddy yake son Faty nasan zai iya sadaukar da komai akanta ,insha Allah komai zaizo da sauki"Gidan Alhaji Kabir babban gida ne kallo d'aya zaka masa kasan an zuba nera tayi kuka a gidan,matansa biyu da yara hud'u,Umma itace Babba tana da yara Abdul da Fatyma,sai Aunty tana da yara Aysha da Salma,Abdul shine Babba a gidan sai Aysha sannan Fatyma sai Salma Auta,suna zaune cikin fahimtar juna da kwanciyar hankali Wanda bazaka tab'a iya cewa gidan Wai kishiyoyi ke rayuwa ba kansu a had'e yake,sai dai matsaloli na yau da gobe Wanda baza'a rasa ba.
Kallon Faty Aysha tayi tace"Allah yayi kin fito kenan?,saura kad'an nace Driver ya tafi ya barki can kwa had'e da Umma,tunda bakya da aekin yi".dariya Faty tayi tace "haba Yaya Shooly ae nasan kece me hana a tafi a barni,tunda dai kinsan a dole na kalli muradina kafin na iya aekata komai a safiyar nan".binta da kallo Aysha tayi harta shiga mota girgiza kai tayi zuciyarta cike da tausayin k'anwar tata.
Koda sukaje scul nasha mamaki da ganin sunan da kowa ke Kiran Faty da shi FD(FATYMA DIKKO),wani ma besan ainahin sunanta ba.
Tana zama ta kalli Zainab tace"k'awata Allah yasa yau baki manto da Album din ba?"
"Inafa zan manto kihauni da neman rigima,kaini na k'agara ayi hutu ko zan samu na koma gida kuwa"
Wani kallo Faty tabi zainab dashi tace "kajimun yarinya sai kace ba jiya kika dawo daga Abujan ba,amma har kin Kuma son gida?"
Dariya Zainab tayi tace"wa yak'i gida,aeni kam zaman kano dole kawai ya zame mani"
"Yanzu dai ba wannan ba,ki bani abunda kika kawo mun".
Girgiza kai Zainab tayi ta ciro albums guda biyu na wak'ok'in Yayan nata ,Wanda bata so ko da wasa Fatyma tasan gidansu d'aya ,ta mik'a mata tace"ke ae baki da wata tsaraba data wuce wannan".
K'ara fara'a Faty tayi ta karb'a tana jerowa Zainab addu'o'i kala kala.
Faty kyakyawar yarinya ce,ba zata gazawa shekara 18 ba,y'ar gatace a wurin iyayenta musamman Daddynta yana matuk'ar sonta,tana da matsakaicin jiki haka ma tsawonta,farace ita,gata kyakyawa ajin farko,tun ranar data fara jin wak'ar DIKKO ta makance akan tsananin soyayyarsa bata da burin daya wuce ta gansa a rayuwarta ko da sau d'aya ne.wannan kenan.
Tunda suka dawo daga scul ta kure volume da sautin kid'an a d'akinta sai juyi takeyi tana jin wani matsanancin farin ciki a ranta.
"Wai waye kejin wa'an nan wak'ok'in ne?kinsan bana son wanann abubuwan,meye ma a tare da wannan mabaratan"Daddy ya fad'a.
"Mabarata Kuma Alhaji "Umma ta maimaita.
"Kwarai kuwa ,ae duk mawak'a mabarata ne,meye wanann inba rok'oba da rashin abunyi,shashanci da b'ata lokaci"ya Kuma bata ansa.
Jinjina kai Umma tayi hakika tasan tabbas Alhaji Kabir ya tsani talakka ya Kuma tsani mawak'a a cewarsa mabarata ne da Kuma rashin aekinyi yasa sukeyin haka,cikin sanyin murya tace"Fatyma ce ,kasan ita kad'ai kejin waka haka".
Tofa koya zata Kaya ga wannan sark'ak'iya,kudai ku biyoni danjin ya zata kasance.
Taku har kullun majidadi
Show me some luv by sharing dis.
Jorderh majidadi

*Dedicated to DIKKO AHMAD (Dk Excellency)*
Page 2
Masu neman wak'ok'in Dk Excellency zaku iya tuntub'ar wannan number din 07033636337
Ummu batace komai ba ta wuce d'akin Faty ta kashe wak'ar da kanta,d'agowa tayi da sauri da niyyar zabga masifa sai kawai taga Ummu saurin sunkuyar da kanta tayi ta kasa cewa komai sai faman shagwab'e fuska takeyi.
Ummu kam ficewa tayi tana hasaso abunda ke shirin faruwa a gidan nasu.
Tashi Faty tayi ta wuce part din Auntynsu dan tasan Daddy yaukam ba wurinta yake ba,da sallama ta shiga anan ta samu duka y'an gidan nasu suna fira,kallonta Yaya Abdul yayi yace"tofa y'ar gidan Daddy yau Kuma meke faruwa ne?"
Dariya Salma ta saka tace"yo ta wuce Ummu ta hanata sana'ar nata kasan shi kad'ai ke b'ata mata rai"
Wani uban harara ta zabgawa Salma tace"wallahi zanci k'aniyarki a gidan nan,toma yaushe na zama k'awarki".
Shiru Salma tayi tasan nan fagen ba wasa indai akan DIKKO ne.
Murmushi kawai Aunty tayi tace"kinga y'ata yi hakuri kije d'akina babu kowa sai kiji abunki a tsanake"rungume Aunty tayi ta baya tace"I love u Auntyna"sanann ta ruga da gudu kamar wacce ake tillawa rashin k'ibarta yasa ko kad'an Faty batajin nauyin jikinta.
"Ni banga abunson zuwa a taron nan ba Dikko,baka gajiya da tafiye tafiye,wallahi wannan kad'ai yasa nake shakkun wak'ar nan taka"Ummi ta fad'a tana gyara zamanta.
Matsowa kusa da ita Dikko yayi ya Kama hannuwanta duka biyu yayi k'asa da murya yace"Ummina ta kaina,kinsan iyakata Kano fa,Kuma wannan taron yana da mahimmanci a gareni a matsayina na mawak'i,wannan taron zai tara manyan mutane da manyan mawak'a Kuma kinsan na riga na gabatar da wak'awa ta Fyad'e illa ga mata,ina jerin wa'anda zasuyi wak'a a wurin,ki sakamun albarka kawai Ummina".
Kallonsu Aliyu yayi yace"Allah Ummi ba wata damuwa yaron nan wannne gari ne baya zuwa sai nan da kano kice a'a ,nima zanje ammafa ni bazan kwana ba"
"Shikenan na yarda yaje amma saidai ka zauna gidan Aunty balaraba inda Zainab take zaune,Kuma ka kula da kanka sosai,bana son shirmen yaran zamani ka rik'e tarbiyar da muka baka,amma in kaje yaushe zaka dawo?"Ummi ta fad'a tana kallonshi.
Shiru yayi alamar tunani sannan yace"Ummina ina kewar Kano zanyi kamar 2weeks acan"Dikko ya fad'a.
Zaro ido Ummi tayi tace"haba Son zaka tafi ka bani kewa har haka?"
"Gaskiya Son 2weeks yayi yawa,zaka barmu mu kad'ai"Abba ya fad'a Wanda shigowarsa kenan,zama yayi kusa da Dikko cikin tsananin soyayya yace"anya zan iya hak'ura har 2weeks kuwa,kasan fa a gidan nan kaine kawai kayi karatu a garin nan,ko Aliyu zuwa jibi zai wuce gidan zaiyi babu dad'i".
Dariya Dikko yayi cikin tsananin kaunar iyayensa yace "to Abbana bazan kaiba insha Allah,nima zanyi kewarku sosai".
Murmushi Aliyu yayi yace"yaro kamar wani jariri ko mace kullun yana gida tare da ku bakwa barinsa yaga duniya".
"Ae Son baya da maraba da jaririn"Ummi ta fad'a tana dariya tare da shafa kanshi.
Shagwab'e fuska yayi yace"ni dai Ummi na girma yanzu ae".dariya duka sukayi.
Next day
Tun da wuri suka fito da shirin tafiya,a mota aka saka masa kayansa sai yaransa da suke aeki tare suka shiga motarsa ,shi kuma suka shiga shi da Aliyu driver yaja suka dauki hanyar kano,wurin k'arfe 3 suka isa Kai tsaye gidan Aunty Balaraba suka wuce,dan k'arfe 4 ake fara program din.da gudu Zainab ta fito tana masu oyoyo,"ke har yanzu baki girma Mai goshin jirgi"tsuke fuska Zainab tayi tace"Allah Yaya D ka daina,nasan na fika kyau ae".waro dara daran idanuwansa yayi tare da bud'e baki yace"tab dana daina fita yarinya"ya Kama hanyar wucewa ciki.dariya Aliyu yayi yace"Allah ta fika haskawa yar Beautyn Ummi".
"Lallai yau muna da babban bak'i a gidan nan,ni wallahi Dikko har nayi fushi ae".sosai Kai yayi yace"Aunty B kin dai San Ummin ce bata so inayin nisa".
"Aeni Ummi abun nata gaba yakeyi,aeko aure zamuyi maka kabar mata gidan muga ya zatayi to".haka sukaita fita kwanin birgewa sai da suka dawo sallah sannan suka soma shirin taiya wurin taron.