← Book details Bintu Diyar Bayice Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 16

Sashe 9

Bintu Diyar Bayice Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fad’in Gwaggo Munari cikin gazawa da halayyar Bintu dan kuwa idan ba ta yi da gaske ba ko shakka babu asirin su mai tonuwa ne. A sanyaye Bintu ta ce
‘’ina tuba....’’
‘’ba tuban ki mu ke buk’ata ba!’’
Gwaggo Munari ta katse Bintu, kana ta k’ara da
‘’ Aikin ki mu ke buk’ata Gimbiya! Wanda za ki fara yanzu ta hanyar zama Gimbiya ba d’iyar bayi ba. Allah ya mi ki zubi irin na jinin mulki, kowa ya gan ki ya san hakan nan Allah ya yo ki, ba ki gada ba amma Allah ya baki su a halittar ki, Dan haka tak’ama da isa shi na ke so daga gare ki, ki saka a ran ki wannan dama ne da Allah ya baki dan jin dad'in rayuwa da kuma taimako ga Masarautar mu, idan asirin mu ya tonu gaba d’aya farin cik’in masarautar mu ne zai koma ga zubar jini, ina fatan kin fahimce ni?’’
Bintu ta gyad’a kai. Kana Gwaggo Munari ta dafa kafad’ar Bintu ta ce

‘’madallah da d’iya ta gari. Sai ki yi shiri yanzu su Ladiyo za su zo su had'a mi ki ruwan wanka. Hakuri za ki yi na san kin saba yiwa kan ki komai amma daga yau komai yi mi ki za ake yi, ki jure Bintu wata rana sai alkhairi’’
Bintu ta dad’a jinjina kai. Ana hakan kuwa su ka ji an sake turo kofa an shigo. Maimakon Ladiyo da Gwaggo Munari ta ce, Lantana ce baiwar da Yarima Nuhu ya za6a ta musammam domin kular masa da al’amran Bintu ta shigo ta zube gaban su. Gwaggo Munari na mai duban ta tace
‘’Lantana gide ke ce mai shirya ruwan wankan ne? yo to ina sauran? Kar dai sun tsaya kallan kauye mu ka biya ku fa sai mu makara!’’
Lantana waccen ita dama da ka gan ta ka ga zubin munafunci, dan ko magana ka ke da ita haka za ka ga ta na sinsin da idanu sam ba ta bari a ga kwayar idanun ta. Ta kada baki ta ce
‘’ai ga su nan tafe, sauri na yo dama na shirya ruwan wankan kada a makara’’
Jin haka Gwaggo Munari na mai mata nuni da bayan gidan da ke cikin d’akin ta ce
‘’yauwa madalla da ke, maza je ki ga bayan gidan can shirya mata gide’’

Sim sim ta shige bayan gida. Sai da ta fara taran ruwa sannan ta shiga had’a ruwan da turaruka iri iri kamar yanda su ka saba had’a ruwan wankan Gimbiyoyi. Ko da ta zo kan turaren karshe, sai ta faki idanun Gwaggo Munari ta tabbatar hankalin ta na kan su Ladiyo da shigowar su ke nan, ta na mu su bayanin yanda ta ke so su kasance wajan taro. Sannan ta jawo kofar bayi ta rufe. Gefan zanin ta ta kwance, ta dauko wani kullin magani, cikin sauri da azanci ta bud’e maganin ta na mai zazzage shi cikin ruwan wankan Bintu. Tuni wani irin bakin hayaki mai wari ya taso daga ruwan yayi sama, ita kan ta Lantana sai da ja baya ta na mai toshe hancin ta cikin tsoran kada fa su Bintu su ji duk da dai Yarima Nuhu ya tabbatar mata babu wanda zai ji warin bayan ita da ta zuba. Sai da ruwan ya dena kumfa da hayaki sannan ta mayar da sauran kullin maganin cikin zanin ta ta kulle, ta fito hankali kwance kamar ba ta aikata komai ba.

🐫🐪🐫🐪🐫🐪
[8/29, 9:33 PM] ‪+234 803 440 2664‬: ®
✏📖
​FIKRA WRITER'S ASSOCIATION​

🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE!(2)
🐪🐪🐫🐪
🐪🐫🐪🐫🐪🐫
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪

GARGA'DI

KUNGIYA MAI SUNA A SAMA, BATA YARDA WANI KO WATA YA MAYAR DA DUK WANI LABARI MAI 'DAUKE TAMBARIN SUNAN TA IZUWA DOCUMENT BA, YIN HAKA KARYA DOKA NE, WANDA HAKAN KA IYA JAWO YANKEWAR LABARIN. DAN ALLAH MU KIYAYE.

9⃣

Sidiya ce......✍🏼

Fitowar ta ba da dad’ewa ba Gwaggo Munari ta sanya Bintu wankan dole dan kuwa ba da san ran ta ba. Da taimakon su ladiyo da Hansai Bintu ta fito fes cikin doguwar riga ruwan d'orawa, rigar da Goggon nan ta aiko mata. Material ne mai tsada ke, sai kuma mayafi kore mai turawa da ratsin ruwan d'orawa. Gwaggo Munari ruke da hannun ta domin kuwa ita ta ke gane mata hanya su ka fito, Su Ladiyo biye da su yayinda aka mu su iso zuwa babban zaure in da mata da iyalan Sarki ke jiran isowar su.

Babban zaure ne wanda ya fi k’arfin a k’ira sa da zure sai dai ko d’akin taro, tsawon sa kamu d’ari, fad’in sa kamu hamsin. Haka kuma ko wacce kusurwa na zauren an masa ado da itacen al’ul a bisa ginshishik’an sa. Bayan ga dadduma mai kulliyar jikin damisa da ke shimfid’e tun daga fari har zuwa k’arshen zauren da kuma tintin masu adon jikin damisa da ke baje bisa daddumar, akwai duwatsu wanda aka auna sa’an nan aka yanka su da zarto ciki da baya daidai da juna, aka jera su zagaye cikin zauren tamakar kujerun zama irin na zamani. Haka kuma bangon zauren zane ya ke da tambarin Masarautar Fabarusa.
Cikin zauren su ka tadda dukkanin iyalan Sarki Abdulrahman tare da y'anuwa da abokan arziki wanda su ka zo domin ta ya su murna. Matan Sarki Abdulrahman uku wanda su ka had’a da Goggon nan (uwar fada), sai ta biyu wacce su ke kira da Goggo ta dole(uwar dole) sai ta ukun wacce ake kira Uwar Soro, wacce itace mai k’arancin shekaru cikin matan sarki. Kowacce hakimce, k’ishingid’e bisa tuntin. Gaban su kuma wani tulu ne wanda aka masa ado da azurfa cike da ruwa mai d’auke da turare da garin lallel.

Haka kuma ‘ya’ya da jikokin sarki da na su wajen daga gefe wanda d’irga su ba k’aramin aiki ba ne kasancewar ‘yay’an sa mata ma su aure da ‘ya’ya sun kai su goma sha takwas, kuma dukkanin su ba su yi k'asa a gwaiwa ba haka su ka zo da sassa da yankunan Jamhuriyar Nijar domin tarbar amaryar d’an uwan na su. Duk da dai ciki akwai mu su bakin cikin lamarin kasancewar ciki d’aya su ke da Yaremi Sadauki. Musammam Yaya Mai Soron Baki, babbar d’iyar Sarki Abdurahman da mai bin mata wato Yaya Jidda wanda su 'ya'yan Goggon nan.

Wajan da aka tanadarwa Bintu gaban su Goggon nan aka zunar da ita. Tun da ta yi wanka da ruwan nan na Lantana hankalin ta ya ke a tashe, gashi gaban ta sai fad’uwa ya ke, ta na son fad’awa Gwaggo Munari amma ta tsoran za ta yi zatan fad’an da aka mata ne be shige ta ba, dan haka a dole ta hakura da ikon Allah. Maimakon Gwaggo Munari ta zauna gaban ta, sai gani ta yi ta ja gefe daga wajan su Gwaggon nan. Cikin girmamawa ta mik’a gaisuwar ta tare da damk’a amanar Bintu gare su bisa ga al’ada. Goggon nan wacce a ran ta ta yi farin cikin fasa auren d'iyar Sarkin Sa'ayrasa da Sarki Abdulraman yayi, ta kuma yi bakin cikin aurar da aka aurawa Barde a maimakon d'an ta Sadauki, ta fara kar6ar amana ta hanyar saka hannu ta bud’e mayafin Bintu da ke gaban su, tuni Bintu ta yi k’asa da idanun ta cikin fad’uwar gaba. Sai da ta kalli fuskar Bintu na d’an wani lokaci ta na mai yamutsa fuska ta saki mayafin ba tare da ta rufe fuskar gaba d’aya ba. Kana ta ce

‘’ni Munzaratu jikar Sarki Abdulrahman na difa, d’iyar Sarki Abdulmuminu iii na Agadez, matar Sarki Abdulraman ii na Fabarusa, na bud’e fuskar amaryar dan mu, d’iyar Sarkin S’ayrasa, Sarki Sule Inuwa Magaji da zannuwa hamsin, kallabi hansin tare da bayi guda uku’’

Jakadiya ta rangwad’a gud’a, yayinda waje ya d’au sowa. Ita Bintu ta yi k’asa da idanun ta, ji ta ke kamar ta dan ta k’arasa rufe fuskar ta gaba d’aya. Amma me za ta ji? Goggo ta dole ce ta sa hannu ta k’ara yin baya da mayafin Bintu yanda za ta ga fuskar Bintu da kyau, kafin ita ma ta jero sunan ta da nasabobin iyayen ta, ta bud’e fuskar Bintu da silallan gwal. Ita kuwa Uwar Soro da tashi na ta bajintar da dawakai tare da rak’uma ta bud’e fuskar Bintu. Tuni Bintu ta zama mai arziki da kadarori, su Ladiyo cikin ran su sai mamakin baiwa da Allah yayiwa Bintu, su na jin ina ma dai su ne.
Bayan da matan Sarki suka gama budar ka, sai kuma sauran 'yan uwa da abokan arziki, yayye da k'Annan Barde su ma su ka nuna ta su bajimtar.

Bayan an gama ne Jakadiya ta mik’a wa matan Sarki tulu. Matan sarki su ukun nan su ka tsaya bisa kan Bintu su na mai tsiyayo mata ruwan cikin tulun kad’an kad’an bisa kan ta, yayinda Jakadiya ke bada wak’a jama’ar wajan na amsa mata

"Ayyare daure jure
ayyaraye daure jure!
zaman gidan wani tilas ne!
ba kan ki ne aka fara
ba da kan ki ne aka fara ne
da kin ci kuka kin k'oshi
ke yar tsohuwa mai 'yar tulu
Allah ya kar ki watan gobe
Mu ci gumba’’

🐫🐪🐫🐪🐫🐪
[8/29, 9:37 PM] ‪+234 803 440 2664‬: ®
✏📖
​FIKRA WRITER'S ASSOCIATION​

🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE!(2)
🐪🐪🐫🐪
🐪🐫🐪🐫🐪🐫
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪

GARGA'DI

KUNGIYA MAI SUNA A SAMA, BATA YARDA WANI KO WATA YA MAYAR DA DUK WANI LABARI MAI 'DAUKE TAMBARIN SUNAN TA IZUWA DOCUMENT BA, YIN HAKA KARYA DOKA NE, WANDA HAKAN KA IYA JAWO YANKEWAR LABARIN. DAN ALLAH MU KIYAYE.

1⃣0⃣

Sidiya ce....✍🏼
Chapter 9 · 0% Book details